Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amma bisa xan ilimin da muke da shi, mun san wannan ba gaskiya bane, duk da cewa abin da waxansu musulmi suke yi ga mata za a ga kamar haka (musulunci yake), amma wannan ba yana nufin Musulunci ne ya koyar da hakan ba. To, zan iya cewa da haka muka fara (wannan Da’awa) a jami’a, kuma ga alama (abin da muke yin ba ya yi musu daxi), ba su son wannan ci gaba da aka samu, don haka suka fara musguna mana tun muna xalibta, ta kai ga an kama mu an tsare…

“Kuma ina iya cewa wannan (Da’awa xin) qaddara ce daga Allah, idan muka karanta tarihin Annabi Musa (AS), za mu ga yana qoqarin kare xan qabilarsa ne (ta kai ga) ya banke ma’aikacin tsaro na Fir’auna ya mutu. Wannan ya tilastawa Annabi Musa (AS) yin hijira, kuma akan hanyarsa ta dawowa ne Allah ya yi masa wahayi da Annabta, wannan qaddara ce ta Ubangiji cewa hakan zai faru. A nawa gefen ma ina iya cewa qaddara ce ta Ubangiji cewa hakan za ta faru, amma ban tava tunanin faruwar hakan ba, ban tava tunanin zan zama malamin addinin Musulunci ba, abin da kawai na yi tsammani shi ne ko dai in zama ma’aikacin gwamnati, ko malamin jami’a, sai na tsinci kaina a abin da nake kai a yanzu”. (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 02 zuwa 03).

Bayan Shaikh Zakzaky (H) ya soma gwagwarmaya da masu aqidar Gurguzu da ke sukar fikirar addini, tare da tuhumar musulunci da kushe shi kan abubuwa da dama, wanda kuma cikin qanqanin lokaci suna ta gurvata aqidun ‘ya’yan musulmi ta hanyar falsafa da hikimomi irin nasu, sai ya zamo in Shaikh Zakzaky (H) ya xauki Alqur’ani yana karantawa sai ya ji kamar da shi ake magana, kamar Allah Ta’ala yana umartarsa ne da ya tashi ya kare addini ta hanyar karantar da mutane haqiqanin addini da nuna musu hanyar shiriya.

A wata hira da “Mujallar Gwagwarmaya” Shaikh Zakzaky (H) yana cewa; “A lokacin in na karanci Alqur’ani sai in riqa fahimtarsa ta wata mahanga da ada can ni ban gane ba. Ba zan manta ba, a lokacin har nakan riqa kallon aya sai ina ganin kamar a lokacin aka sauqar da ita… wato sai Allah sanya mini fahimta, in na karanta (aya) sai in ga kamar ana magana da ni ne!” (Mujallar Gwagwarmaya, fitowa ta 3, shafi na 09).

Kenan, idan mun lura da waxannan bayanai, za mu ga cewa abubuwa biyu ne suka zamo asasin wannan Da’awa ta Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), qoqarin kare addinin Musulunci da fikirarsa, don ceto al’ummar musulmi daga gurvacewar aqida, da kuma qaddarawar Allah Ta’ala wacce ya riga ya zartar, wannan su ne tushe ko mu ce asalin abin da ya sa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya fara wannan qira na Harka Islamiyyah a Nijeriya.

Manufar Da’awarsa :

Da’awar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) wani yunquri ne na sauqe haqqin Allah Ta’ala, ta hanyar biyayya ga umarninsa da hanuwa ga hane-hanensa, da kuma qaqarin kawo gyara a cikin al’umma don a gudu tare a tsira tare a gobe qiyama.

Al’umma ta yi nisa cikin ximuwa da rashin sanin haqqoqin Allah a kanta, an ajiye umarnin Allah a gefe ana ta rayuwa cikin son zuciya da makanta, wannan ya jaza ximbin matsaloli a tafarkin rayuwar al’umma, kama daga munanan xabi’u da halaye, qeta da fin qarfi, zalunci da danniya, jahilci da makanta, rashin sanin addini da rashin sanin alqibla, da kuma uwa uba fuskantar mummunar makoma a gobe qiyama.

Wannan ya sa Shaikh Zakzaky (H) ya tashi don kiran mutane zuwa ga addini wanda a cikinsa ne kawai mafitarsu ta ke, a cikinsa ne kawai al’umma za su samu duk abin da suke nema na kwanciyar hankali, yalwar arziqi, tarbiyya da kuma kyakkyawar makoma a gobe qiyama. Dan haka manufar Da’awar Shaikh Zakzaky (H) ita ce xora mutane akan koyarwar addinin musulunci da kyautata hali da xabi’unsu.

A jumlace kuma a dunqule, manufar Da’awar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) shi ne kawo gyara don kyautata rayuwar al’umma, da kuma neman uzuri da tsira gaba ga Allah a ranar alqiyama.

✳✳✳ ✴✴✴ ✳✳✳

BABI NA BIYU

BAIWA DA XABI’UN SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY (H)

HAZAQARSA :

Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) tun tasowarsa a yarinta fasihi ne haziqi, Allah ya wadata shi da hazaqa da fasaha, domin duk a cikin ‘ya’yan mahaifinsu ya fi su hazaqa. Malam Badamasi Yaqubu shi ne qanin da ke bin Shaikh Zakzaky, ya faxi a wata hirarsa da ‘yan jarida cewa; “Malam ya taso da son karatu, kuma lalle kam duk a cikin ‘ya’yan mahaifinmu ba haziqi kamarsa, domin zan iya tunawa, yana da yayye kamar guda biyu maza, akwai Malam Abdulqadir Yaqubu, akwai Malam Sani Yaqubu, lalle akan gaya musu karatu su manta, mahaifinmu yakan koyar da su karatu su manta, shi Malam bai kai inda suke ba, amma idan sun manta (karatun) shi suke tambaya ya tuna musu… kuma ya iya karatun boko ba tare da ya yi firamare ba, sannan kuma duk wani littafi da ake yi a (karatun) zaure, lallai Malam ya yi shi” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 63).

Wani lokaci mun kai wa Shaikh Zakzaky (H) ziyara, yana mana hira cikin raha, sai magana ta biyo ta kan yaranta, sai yake cewa: “Lallai ni ina tuna abubuwan da na yi lokacin ina xan shekara huxu zuwa biyar da haihuwa, nakan tuna abubuwa da dama”. A raina sai na ce “Ku kenan masu ‘Extra Ordinary’ Qwaqwalwa, amma mu kam ai sai a hankali!.

A wani jawabi Sayyid Badamasi Yaqub ya faxi cewa; “Wani lokaci in ana hirar yarinta, Malam (H) yakan ce mun a lokacin da aka haifeka kaza da kaza ya faru, wato, yana bada labarin wasu abubuwan da suka faru a lokacin da aka haife ni, wanda ya gani da idonsa, alhali tsakani na da shi shekara uku ne kacal”.

Tabbataccen abu ne cewa, kaifin qwaqwalwa da hazaqar Shaikh Zakzaky (H) ba su misaltuwa, domin a wani jawabi da ya yi wa qananan yara a taron IVC na shekarar 2013 a Darur-Rahma, ya faxa musu cewa; “Lokacin da ina yaro xan shekaru goma sha, qwaqwalwata kamar mayen qarfe take game da xaukar karatu. Na yi qidaya a Kano a 1973 a (qaramar hukumar) Fagge ta kudu, ta kai ma da a ce wani abu zai samu takardun (su vace), to, duk mutanen unguwar zan iya rubuta su da sunayensu da shekarunsu!” (Al-Mizan, bugu na 1093, shafi na 18).

Ba shakka wannan bayani zai haska mana waye Shaikh Ibraheem Zakzaky a qwaqwalwa da fasaha da hazaqa da zalaqa, domin duk wanda zai iya haddace sunayen xaruruwan mutanen unguwa, da yawan shekarun kowannensu, da lambar gidajensu, da kalar addininsu a lokaci guda, to ba shakka zalaqa da fasaha da hazaqarsa ta kai maqura!

Haka nan, sakamakon da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya samu a kammala digiri xinsa a shekarar 1979, har zuwa wannan shekara ta 2016 ba a samu xalibin da ya samu irin wannan sakamako a darasin “Economics” a jami’ar Ahmadu Bello ba. Magayaqin Zazzau Alhaji Abubakar Jibrin ya ce; “Muna da labarin cewa a jami’a sakamakon digiri xinsa ya yi kyau sosai! Domin ya samu “1st –Class” (daraja ta xaya) ne akan sanin tattalin arziqi (Economics), wanda kusan shi ne mutum na qarshe da ya tava samun irin wannan takardar digiri xin. Domin an ce tun daga kansa ba a qara samun xalibin da ya samu sakamako irin nasa ba har zuwa yau (2016) a wannan jami’a (ta Ahmadu Bello da ke Zariya)”. (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 82).

Hazaqar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) baiwa ce daga Allah, amma wannan baiwar tasa ta xanfaru da naci na son sanin komai a haqiqarsa. Madaucin Zazzau Alhaji Ahmad Shehu, wanda tare suka yi yarinta da Shaikh Zakzaky (H) yana cewa; “Malam Ibraheem a cikinmu ya banbanta a tsakaninmu, tunda shi ya taso ne da neman ilimi da kuma neman sanin tarihin kowane abu da sanin asalinsa!... Malam shi mai son yin nazari ne akan kowane abu, don duk abin da bai san shi ba, in dai yana da alheri, za ka ga ya nemi iliminsa, sannan ya yi nazari akansa” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 80).

Malam Abdulqadir Yaqubu, wanda shi ne babban wa ga Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana cewa; “Muna masu alfahari da wannan qane namu, ya kasance wanda ya fara haddace Alqur’ani a zuri’armu tun bayan kakanmu Malam Aliyu, shi ya cikata addu’a da babban burin da kakanmu ya mutu da shi”. (Mujallar Gwagwarmaya, fitowa ta 3, shafi na 24).

Wani abu da zai qara nuna hazaqar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) shi ne yadda ya iya haddace Alqur’ani da qira’o’i biyu, wato bayan ya dace Alqur’ani da qira’ar ‘Hafs’, sai kuma ya sake dawowa ya haddace shi da qira’ar ‘Warshu’. Wannan ba qaramar baiwa bace, marubucin littafin ‘Malam, Malam ne’ yana cewa; “Malam hafizi ne na Alqur’ani, kuma Alaramma ne, don kuwa da hannunsa ya rubuta Alqur’ani a lokacin da ya zauna a kurkukun Fatakwal na farko daga 1986 zuwa 89”. (Malam, Malam Ne, shafi na 11).

Da marubucin littafin “Mujaddadin Wannan Qarnin” ke magana game da hazaqar Shaikh Zakzaky (H) ya ce; “Malam (H) bai tava shiga aji ya koyi “Computer” ba, amma ya san “Computer” fiye da wanda ya shekara biyar yana karanta ta. Kuma duk wani fanni na ilimin zamani in Malam (H) yana magana akai sai ka rantse da Allah a kansa ne ya yi digiri, saboda kawai yadda ya san fannin!” (Mujaddadin Wannan Qarnin, shafi na 49).

FIKIRARSA :

Marubucin littafin “Tarihin Harkar Musulunci” yana cewa; “Duk wanda ka gani, to zantukansa da ayyukansa da kuma xabi’unsa sakamakon fikirarsa ne, wato tunaninsa. Ashe kenan fikira sahihiya kuma salimiya, wadda ta yi daidai da koyarwar addinin musulunci tana da gayar muhimmanci ga mutum, tunda zantukansa da ayyukansa sakamakonta ne”. (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 25).

Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) wani bawa ne da Allah ya keve shi da wata irin baiwa ta sahihiyar fikira ta musamman, duk wanda ya nazarci rayuwar Shaikh Zakzaky (H) zai tabbatar da cewa bawa ne da Allah ya azurta shi da salimiyar fikira da ingantaccen tunani, domin ba ya tufqa da warwara a cikin zantuka da ayyukansa, kullum akan tafarki xaya yake tafiya. Sau da yawa wasu abubuwa kan bijiro bagatatan ba zato ba tsammani, jama’a su ruxe kowa yana neman mafita, amma shi sam baya ruxewa, duk abin da ya bijiro, to Shaikh yana da ingantaccen tunani akansa, kuma yana da qwaqqwarar mafita a game da shi.

A shekarar 1990 lokacin yaqin Tekun Fasha tsakanin Iraqi da Amurka, kan al’ummar Nijeriya ya rabu gida biyu, suna ganin yaqi ne tsakanin Musulunci da kafirci, dan haka suka sava kan waye mai gaskiya tsakanin shugaban Amurka Gorge Bush da kuma shugaban Iraqi Saddam Hussain. Wannan ya jawo varaka a tsakanin musulmi ya su- ya su, wanda har ya kai qungiyar Izala ta rabu kashi biyu, masu goyon bayan Amurka, da kuma masu goyon bayan Saddam Hussain.

Adaidai lokacin da ake wannan ruxani, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya fito fili ya yi wa al’ummar musulmi bayani cewa wannan yaqi bai da wata alaqa da Musulunci, kawai savani ne aka samu tsakanin karen farauta da ubangidansa, faxa ne na kare muradi da kuma qoqarin cimma wani muradin, ba faxa ne tsakanin musulunci da kafirci ba. Wannan abu ya jawowa Shaikh Zakzaky (H) hujumi daga malamai, amma daga qarshe bayan kammala yaqin sai jama’a suka gano lallai matsayar da Shaikh Zakzaky ya xauka ita ce gaskiya!

,Haka nan a shekara 1999, bayan kafa mulkin farar hula a Nijeriya, gwamnonin wasu jihohi na Nijeriya qarqashin jagorancin gwamnan Zamfara Alhaji Ahmad Sani Yariman Bakura, sun qirqiro batun Shari’a, inda suka ce za su riqa hukunci da Alqur’ani maimakon hukunci da Kwansitushin a jihohinsu. Wannan ya ja hankalin ximbin al’ummar Nijeriya, musulmi suka fito qwansu da qwarqwata suka nuna goyon bayansu kan hukunci da Alqur’ani, su kuma Kiristoci suka ja daga a gefe guda suka ce ba su yarda ba.

A tsakanin wannan hayaniya, Shaikh Zakzaky (H) ya fito ya yi wa al’ummar Nijeriya jawabi, ya nuna musu cewa sam ba ta hanyar siyasa ake kafa gwamnatin musulunci ba, shari’a da Alqur’ani yana da matakai da marhalolin da ake bi kafin a samar da shi, dole sai an bi sunnar Manzon Allah (S) kafin a samar da duk wata gwamnatin musulunci a kowane zamani. Ya ce wannan siyasa ce kawai ta yaudarar mutane da xauke hankalinsu daga abin da ya kamata a yi musu na kyautata rayuwa da samar da cigaba, domin Shari’a a qarqashin tsarin kafirci mai cikakken iko, abu ne da ba zai tava yiwuwa ba!

Nan da nan malamai suka yi masa caa suna sukarsa da aibata matsayarsa, amma bayan shekara xaya kacal da qaddamar da Shari’ar, sai mutane suka gane cewa ashe lallai an yaudare su ne an wawaitar da qwaqwalensu, ba wata shari’ar musulunci da ake yi a jihohin sai shegantakar ‘yan siyasa kawai. Daga baya wasunsu suka gaskata Shaikh Zakzaky (H) suka jinjinawa matsayarsa da zurfin fikirar da Allah ya yi masa.

A lokacin da Amurka ta kai hari kan tagwayen benayen cibiyar kasuwanci ta duniya (World Trade Center), da cibiyar tsaro ta Pentagon a 2001, da yake kafafen yaxa labarai sun xora alhakin harin kan wasu musulmi qarqashin Usama bin Ladin, al’ummar musulmin duniya musamman Nijeriya sun yi tsalle suna murna da farin ciki, malaman addini musamman Wahabiyawa suka rinqa kwatanta aikin a matsayin babban jihadin addini, suka rinqa yabawa Usama tare da nuna goyon baya da jinjina a gare shi.

Amma ta vangaren Shaikh Zakzaky (H) tun washegarin ranar da abin ya faru, wasu sashen almajiransa suka kira shi a waya don jin matsayinsa game da abin da ya faru, nan take ya ce masu; Ai kar ku ruxu da wannan abin, wani makirci ne na yaqi da musulmi da Musulunci Amurka da Isra’ila suka kitsa! Shiryayyen shiri ne na yaqi da addini, su suka kitsa harin, ba wani wanda ya kai musu hari!”. Wannan ya nuna yadda Allah Ta’ala ya kimsa shiriya a fikirar Shaikh Zakzaky (H), ta yadda ba a ruxarsa balle a wawitar da qwaqwalwarsa.

Haka nan, a shekarar 2009, ba zato ba tsammani, sai ga wani makirci na qoqarin rage yawan musulmin Nijeriya ta hanyar kisa. Kwatsam wata qungiyar ta’addanci da ta kira kanta da suna “Ahlis-Sunnah Lidda’awati Wal-Jihad” wacce aka fi sani da “Boko Haram” ta bayyana, wai manufar qungiyar shi ne kafa gwamnatin musulunci. Amma maimakon qungiyar ta yi jahadin kawar da gwamnatin zalunci ta Nijeriya, sai kawai ta vuge da ayyana arewacin Nijeriya inda musulmi ne tsantsa a matsayin cibiyar jihadinta !

Kuma a jihadin ta’addanci da ‘yan qungiyar ke yi, suna kashe kowa da kowa ne, suna kashe manya da yara, maza da mata, jarirai da marassa lafiya, suna kashe dabbobi da lalata gonaki da qone duk garin da suka kama qurmus! Suna kai hare-haren Bom a masallatan Juma’a da na “Khamsu-Salawat” adaidai lokacin da ake Sallah, su kashe duk masallatan. Suna kai hare-haren Bom da na kisan gilla a kasuwanni, da asibitoci, da tashoshin mota, da wuraren cin abinci, da wuraren bukukuwa, da gidajen Sinima, da wuraren qwallon qafa, da gidajen mai, da bankuna, da duk inda mutane ke taruwa, kuma a dukkan hare-haren da suke kaiwa sama da kashi 90 na mutanen da suke kashewa musulmi ne, amma wai jihadin Musulunci suke yi!

An ruxi mutanen Nijeriya cewa da gaske wata qungiyar musulmi ta “Ahlis-Sunnah” ce ke yin wannan aika-aika, kuma jama’a duk sun yarda. Amma sai ga Shaikh Zakzaky (H) ya fito fili ya yi wa mutane jawabi, inda ya ce “Boko Haram” qarya ce! Dirama ce kawai jami’an tsaron Nijeriya da haxin guiwar CIA da MOSSAD na Isra’ila suka shirya don shafe al’ummar musulmin Nijeriya daga samuwa, da mallake kafofin arziqin Nijeriya, da kuma vata musulunci a idon duniya, ba ruwan musulunci da wannan aikin, aiki ne kawai na ‘yan mulkin mallaka da masu shan jinin raunana!

Shaikh Zakzaky (H) ya ambaci misalai da shaidu masu yawa da ke tabbatar da cewa “Boko Haram” shiri ne tsararre na kafircin duniya da ke samun goyon bayan gwamnatin Nijeriya, wannan ya sa ximbin al’ummar Nijeriya sun farka daga mayen da aka sa qwaqwalensu a ciki, suka gane cewa “Boko Haram” qarya ce, wani makirci ne kawai na zaluntar musulmi da sabon salon mulkin mallaka.

Wannan misali ne kawai na irin baiwa ta ingantacciyar fikira da Allah Ta’ala ya yi wa Shaikh Zakzaky (H), ta yadda shi ba ya ruxuwa da ruxin masu ruxi, ba a iya yaudarar tunaninsa ko cusa masa wahami, ba a iya wawitar da fikirarsa ko a gina shi akan holoqo. A wata magana tasa yana cewa, bisa baiwa ta Allah Ta’ala gare shi, tunda yake bai tava samun matsalar fikira ba, ya ce; “Wannan fikira ba wai wani qoqari ba ne, ko ilimi ko jarunta ko kuma dabara ba, a’a, baiwa ce daga Allah Ta’ala wacce ya yi mana”. (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 25).

Marigayi Dakta Kalim Siddiqy (shugaban majalisar musulmin Birtaniya) ya tava cewa; “Bai tava haxuwa da mutumin da cikin ‘yan mintoci zai gaya maka manufarsa, kuma ka fahimce shi, kamar Shaikh Ibraheem Zakzaky ba”. (Malam, Malam Ne, shafi na 30).

TSABTARSA :

Duk wanda ya san Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya san shi da tsananin tsabta da qin qazanta da datti. Mutum ne da tsabta ta zamo xabi’a tamkar jinin jikinsa, duk inda yake rayuwa za ka ga wuri ne gyararre mai tsafta da ban sha’awa, hasali ma Shaikh Zakzaky (H) ne ya raya xabi’ar ado da kwalliya da Fulawa a cikin al’ummar Hausawa, domin akan yi ado da fulawa a motarsa, da wuraren wa’azozinsa, da wuraren zamansa, da ma ko’ina a cikin gidansa. Kuma Shaikh Zakzaky mutum ne da ke tsananin adawa da wari ko qarni ko duk wani abin da ba qamshi ba.

Shaikh Muhammad Turi (RA) ya labarta tsananin tsaftar Shaikh Zakzaky a wata hirarsa da ‘yan jarida, ya ce, bayan an kama su tare da Shaikh Zakzaky a lokacin mulkin Abacha, sai aka kai su kurkukun Kaduna, aka sa su a wani waje mummuna mai matuqar qazanta; “Wurin ga shi da qazanta qwarai da gaske, sam wurin ba shi da kyawu, wurin shi ne mafi muni (a cikin kurkukun), sai mutum ya yi (babban) laifi a cikin kurkukun ne za a kulle shi a wurin… nan da nan Malam ya tura waje aka zo da farin fenti (aka fente wurin baki xaya), aka zo da fulawowi da sauransu, wurin babu ko wutar lantarki, aka jawo wuta, nan take dai aka gyara wuri, sai ga shi ya fito fes-fes.

“Ina iya tunawa, wata rana (ko Konturola Janar ne) ya kawo ziyara kurkukun, yana shigowa wurin, sai ya cika da mamaki, ya ce; “Ah, wurin nan kamar za a kawo Amarya!” Saboda shi ya san wurin a baya can, shadda ne kawai za a iya cewa wurin, amma sai ya ga yanzu an yi fenti har da Fulawowi da sauran kayan qawata wuri, nan fa ya jima yana cike da mamaki, to shi ne sai Malam yake cewa; “Shi wannan bai san akwai mutanen da idan aka sanya su a shadda, shaddar nan sai ta yi qamshi ba?”. (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 100).

“Ka duba ka ga yadda Malam ya gyara inda ya zauna a gidan yarin Kaduna, ya yi fenti a wurin, ya shuka filawa, ya ja wutar lantarki, har wadoji na cewa wurin ‘Presidencial Villa’ wato “Fadar Shugaban Qasa”. (Malam, Malam Ne, shafi na 11).

Rayuwar Shaikh Zakzaky (H) gaba xayanta cike take da qamshi da tsafta, xakinsa qamshi, falonsa qamshi, gidansa qamshi, motarsa qamshi, duk inda zai zauna sai an qamsashe shi. A duk sa’adda ya yi “Brush” sai ya yi anfani da “Mouth Freshner”. Komai nasa mai qamshi kuma tsaf-tsaf gwanin ban sha’awa, sam ba ya son wari da datti da rashin tsafta.

“Malam mutum ne mai yawan anfani da turare, don Malam ko wucewa ya yi ta wuri za ka sani saboda qamshin turarensa, balle a ce wani abin da ya fito daga hannunsa, qamshi za ka ji yana yi, duk abin da ya tava sai ya yi qamshi. Wata rana matata, Malama Zeenat ta sa ta zubar da ‘Dustbin’ (shara) na xakin Malam, to wallahi qamshi (sharar) take yi!”. (Malam, Malam Ne, shafi na 10).

Mai karatu ka ji fa! Sharar xakin Shaikh (H) ma qamshi take yi! Editan jaridar Almizan Malam Ibrahim Musa ya ce; Shaikh (H) ya tava bani kyautar rediyo qarama ta xaukar magana, rediyon ta daxe a wurina tana qamshi”. Wannan misali ne kawai na tsabtar Shaikh Ibrahim Zakzaky (H).

TAWALI’UNSA :

Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) fitacce ne a fagen Tawali’u da qanqantar da kai, sam ba a shaide shi da girman kai ko jiji da kai ba, sai wanda ya kusance shi ne zai iya sanin zurfin tawali’unsa. Misali, duk wanda ke zuwa gidan Shaikh Zakzaky (H) a Gyallesu zaman yamma, ya san cewa Shaikh xin ne da kansa ke zubawa mahalarta zaman Shayi a kofuna a mimmiqa musu su sha, kuma wannan ya zama xabi’arsa.

Shaikh Muhammad Turi (RA) yana cewa; “(A zaman da muka yi tare da Shaikh Zakzaky a kurkukun Kaduna), duk lokacin da aka kawo abinci, shi Malam ne ke raba mana abincin. Ba ni mantawa, akwai wani shugaban Wadoji a nan kurkuku xin, wata rana ya shigo haka kwatsam, a daidai lokacin Malam yana rabon abinci, sai ya yi ta mamaki, har yana cewa “Leadership by Example”, yana ta mamaki…..

“Kuma wata rana a lokacin irin tarukan makon haxin kan nan, akwai wani malami daga cikin waxanda aka gayyata ya zo, a irin lokacin cin abincin nan, sai ya ga Malam shi da kansa yake xiban nasa abincin yana zubawa a kwanon da zai ci, sai shi malamin yana ta mamaki, har yake cewa; “Ah, ya za ku bari Malam yana xiban abinci da kansa, ba za ku amsa ku zuba masa ba? Haka nan, wata rana mun yi tafiya a cikin dare a wata jar mota, lokacin ina ga ‘Bluebird’ ce, sai muka kafe, sai duk muka sassauko domin mu tura motar, kafin mu ankara, ashe har malam ya sauko ana tura motar tare da shi”. (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 101).

Daga cikin Tawali’un Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yakan ziyarci majinyata daga dangi ko maqwabta ko almajiransa, kuma yakan je ta’aziyyar rasuwa, ko dubiyar marassa lafiya, ko ziyara ga waxanda ke tsare a gidan yari. Xaya daga cikin manyan almajiransa, ya bayyana irin farin cikin da ya ji lokacin da Shaikh xin ya tava kai masa ziyarar ba-zata a kurkukun Benin lokacin da yake tsare, ya ce; “(Daxin da na ji lokacin da Shaikh (H) ya ziyarce ni a kurkukun Benin), Wayyo Allah, ai ban san ma yadda zan misalta abin ba, ai daxin da na ji ba kaxan bane, mance ma inda nake na yi, na manta da komai da komai, kuma har na baro gidan yarin nan tasirin wannan ziyara tana nan”. (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 111).

A wani misali na tawali’un Shaikh Zakzaky (H), Malam Yaqubu Yahya yana cewa; “Akwai wani wuri da ake ce ma Zawiyya (a gefen gidan Malam), Malam yakan xan sauqar da baqi a wurin, ni ma ina daga cikin baqin da ake sauqarwa. To, akwai wani zuwa da na yi, Malam da kansa ya shinfixa mani Katifa, ya xauko zanin gado ya sanya mani, ya kukkunna mani fitila, abin ya ba ni mamaki! Haka kuma in na yi bankwana zan tafi, sai Malam ya yi mani rakiya, sai in ji kamar in nutse qasa (saboda jin nauyi)”. (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 112).

A wata hira da jaridar Al-Mizan, xaya daga cikin almajiran Shaikh Zakzaky (H) Malam Dawud Aliyu ya ambaci wani misali na Tawali’un Shaikh xin, ya ce; “Zan iya tunawa, akwai wani lokaci, tun Malam yana Kwarbai, na zo na sami Malam (H) ya fito, akwai wani gida da yake tafiya can wajen yana yin abubuwa na karance-karance da wasu hidimomi, Malam ya xauke ni a mota muka tafi wancan gidan, muka je muka shiga, akwai kayansa da ya jiqa zai yi wanki, na nemi in karva in wanke masa, amma ya hana ni, da kansa ya wanke kayansa ya shanya”. (Shekaru 60 masu Albarka, shafi na 158).

Wani tsohon hadimin Shaikh Zakzaky (H) mai suna Abdullahi Manu, ya faxi cewa tun asali Shaikh Zakzaky (H) da kansa yake wanke tufafinsa, ba ya bari wani

1 Comments On SHAIKH ZAKZAKY IKON ALLAH
avatar
shuraihu-usman-1

1 year ago

Reply

sss

Please Login or Register in order to submit comment