Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shekaru sha biyu, kuma a bayansa Fitina za ta kasance. Sa’annan wani namiji wankan Tarwaxa (launi tsakanin fari da baqi) zai mulketa ya cikata da adalci. Sannan ya tafi zuwa ga Mahdi (AF) ya miqa masa biyayyarsa (Bai’a), kuma ya yi yaqi a qarqashinsa” (Al-Haawy Lil-Fataawa” Juz’i na 03 shafi na 98-99).

Abubuwan la’akari da lura a wannan ruwaya sune; Mutum biyun da aka yi Busharar zuwansu ‘yan Afirka ne. Na farkon zai yi Mulki na tsawon shekara sha biyu, sai Fitina ta biyo bayansa, sai wani namiji ya zo (a bayansa) ya tabbatar da adalci, kuma shi wannan mutumin zai riski Imam Mahdy (AF) ya miqa masa Bai’a, sa’annan zai yi yaqi a qarqashinsa.

To, a bisa nazari, za mu ga cewa wannan ruwaya ta Imam Baqir (AS) kamar tana magana ne akan Shaikh Usman Bin Fodiye (RA) da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), domin na farko; Shehu Usman bin Fodiye da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) duk ‘yan Afirka ne.


Na Biyu : Shehu Usman da almajiransa sun fara samun Nasara a jihadinsu ne a shekarar 1805 Miladiyya, wanda kafin nan Shehu da almajiransa sun ci karo da wahalhalu sosai, kama daga tsananin yunwa da rashin wurin zama, wanda saboda tsananin yunwa har ta kai ga hijira ta gagari wasu saboda hatta dabbobinsu ba za su iya wannan tafiyar ba, sai da wani Buzu ya taimaka da raquminsa wajan kwasarsu zuwa garin Gwandu, inda Shehu da almajiransa suka tare don yin Noma da Kiwo.


Shehu Usman ya samu cikakkiyar nasarar kafa Gwamnati da ikon gudanarwa ne a shekarar 1805, sannan ya yi wafati ne a shekarar 1817. Kenan, in mun lissafa daga 1805 zuwa 1817 za mu samu shekaru 12 ne daidai.


Na uku ; Bayan wafatin Shehu xan Fodiye fitina ta biyo baya tun daga kan wanda zai gaje shi (kamar yadda tarihi ya tabbatar), wanda hakan ya kawo rarrabuwar kai a almajiran Shehu, har ya yi sanadin raunanar Musulmi, a qarshe (babbar fitina, wato) Bature ya zo ya ci su da yaqi ya rusa xan sauran abin da ya ragen.


Na huxu ; Bayan tsawon lokaci, sai ga wani namiji a wannan nahiya ta Afirka ya tashi yana Da’awa da fafutukar tabbatar da adalci a tsakanin al’umma, qiransa ya ratsa qasashe da dama na nahiyar Afirka, wannan kuwa shi ne Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), wanda kuma shi mai cikakkiyar xa’a ne ga Imam Mahdi (AF), kuma akan biyayya ga Imam xin yake gina almajiransa.


Na biyar ; Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) bai da burin da ya wuce Allah ya sanya shi cikin mataimakan da za su yi yaqi a qarqashin Imam Mahdi (AF), ba ma shi ba, hatta almajiransa ba su da burin da ya wuce haka. Sannan wasu Busharori na Waliyan Allah sun nuna yana cikin mataimakan Imam Mahdi (AF) 313, kamar yadda ya zo a hadisin Imam Sadiq (AS) da zantukan su Shehu Xan Fodiyo (RA).

Kenan, in mun duba da kyau za mu ga wancan hadisi na Imam Baqir (AS) tamkar yana bushara ne na bayyanar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), domin kusan dukkanin abubuwan da hadisin ya ambata sun dace da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). Allah ne masani ga haqiqanin al’amura. (Ishaq Xan’adani Al-Rafidhiy, rubutunsa a Wattsapp ranar 04/09/2016).


BUSHARAR IMAM SADIQ (AS) :


Bushara ta biyu wacce ake kyautata zaton Busharar bayyanar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ce, ita ce busharar bayyanar wani Ibraheem Al-Maghriby cikin jerin mataimakan Imam Mahdi (AF) da Khalifan Manzon Allah (S) na shida, wato Imam Ja’afar As-Sadiq (AS) ya yi, marubucin littafin “Bayyanar Sharafuddin” ya yi bayani akan wannan Bushara kamar haka;-


“Akwai wata daxaxxar Bushara wadda Imam Ja’afar ibn Muhammad Assadiq (AS)- watau Imami na shida daga zuriyar gidan Manzo mai tsarki (SAW)- ya yi kan zuwan Malam (H). Wannan busharar kuwa ya yi ta ne tun shekaru xaruruwa da suka shuxe kafin bayyanar Shehu Xan Fodiyo (RT). Wannan busharar ta fito ne a cikin littafi mai suna “BUSHRAL ISLAM” wanda yake littafi ne da ya yi bayanai a kan bayin Allah waxanda za su bayyana a duniya tun bayan wafatin Manzo mai tsarki (SAW) har zuwa qarshen duniya.


“Yadda lamarin ya kasance kuwa, wani ne ya zo wajen Imam Sadiq (AS), yana neman sanin ilimi kan bayyanar Imam Mahdi (AS), sai Imam Sadiq (AS) ya fayyace masa bayanai daki-daki har ya kai ga ambata masa sunayen mataimakan Imam Mahdi (AF) su 313, daga ciki ya ambaci sunan Ibraheem Al-Maghriby, watau Ibraheem na yammacin duniya, wanda kai tsaye za a iya cewa yana nufin Malam (Ibraheem Zakzaky) (H) kenan!” (Bayyanar Sharafuddin, Babi na 6, shafi na 40).


Marubucin bai tsawaita bayani akan wannan Bushara ba, sai dai nazari zai iya tabbatar da haka, domin ya zuwa yanzu ba wani Ibraheem da aka yi a Magrib (wato Afirka) da ya fi Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) zama kusa da kasancewa cikin mataimakan Imam Mahdi (AF). Domin na farko dai yana riqo ne da tafarkin Imam Mahdi (AF) wato Shi’a Imamiyyah, kuma ayyukan da yake aiwatarwa tamkar shinfixawa Imam Mahdi (AF) hanya ne, wato yana gwagwarmaya da zalunci da azzalumai, da kuma qoqarin wanzar da adalci a cikin al’umma. Kuma hatta Husainiyyarsa ma wacce ta fi kowace Hussainiyyah girma a nahiyar Afirka, sunan da ya sa mata shi ne “Hussainiyyah Baqiyyatullah”, wato ‘Hussainiyyar Imam Mahdi’ wanda wannan babban alami ne na alaqa da kusancinsa ga Imam Mahdi (AF).

BUSHARAR SHEHU USMAN XAN FODIYE (RA) :


Shaikh Usman bin Fodiye (RA) ya rubuta waqa Baitoci goma da ke bayani akan wasu manyan waliyyan Allah da suka gabata da kuma waxanda za su zo nan gaba, to a ciki sai ya ambaci wani waliyi Ibraheem da zai bayyana, wanda ya ce sunansa na baxini shi ne Sharafuddeen, kuma za a haife shi ne a shekara ta 1370 bayan hijira. Ga sashen Baitukan nasa:-

(Waliyai) masu zuwa a bayan waxancan sune;


Ibraheem wanda shi ne Sharafuddin da kuma Jamalul-Badry Husamuddini.

Shi Husamun nan da aka ambata shi ne;

Wanda aka ba cikamakon Waliyai Kamilai akan muqaman addini.


A shekara ta 1370 bayan hijira zai bayyana,

Wato shi Ibraheem mataimakin Imam Mahdin.


Shaikh Bayero Sambo Kulwa ya yi taqaitaccen sharhi ga waxannan Baituka guda uku, ya ce; “(Ibraheem xin da zai bayyana), Sharafuddeen shi ne laqabinsa wato sunansa na baxini, saboda addini zai xaukaka a lokacinsa…”


“Shi kuma Husamuddin xin nan da aka ambata, shi ne wanda aka ba muqamin cikamakon waliyai kamilai akan muqaman addini. An tambayi Shehu Usman dangane da wannan Husamuddin xin, sai ya ce shi ne Imam Mahdi da ake jira… shi shugaban kowa ne a zamaninsa…”


“An tambayi Shehu Usmanu da ya yi qarin bayani akan (abin da zai faru a shekara ta 1370) sai ya ce; “Wannan shekarar ita ce shekarar bayyanar Ibraheem, wanda shi ne mafi girman mataimakan Imam Mahdi da ake jira, amma Allah ne kaxai ya san lokacin jihadi da yaqi na sojojinsa tare da kafirai, fajirai, fasiqai da ma’abuta munafunci” (Kitabul-Bushura, shafi na 04).


To, bayan Shehu Usman bin Fodiye ya kammala waqar, sai aka tambaye shi qarin haske game da Ibraheem xin nan da ya ambata, shi ne sai ya qara rera wasu baitoci goma sabbi, inda ya hallale bayani daki-daki game da Ibraheem xin da siffofinsa, ya nuna cewa zai zo da albarkoki masu yawa. Ga yadda baitukan na Shaikh xan Fodiye (RA) suke bayan an tambaye shi qarin bayani game da Ibraheem Sharfaddeen;


Wani mutum zai bayyana a qasar yamma,

Yana kuma da jama’a masu taimakon Mahdi.


Wannan mutumin da zai fito daga yamma manisanciya,

Da mabiyansa sune mutanen (Imam) Mahdi.


Duk lokacin da wannan mutumin ya bayyana,

Ku da shugabanninku ba za a muku xa’a ba sai dai ga Mahdi.


Cikin shekarar 1370 ne wannan mutumin zai bayyana,

Shi ne kuma babban mataimaki (ga Imam) Mahdi.


Wannan mutumin yana da faffaxan goshi tare da alama,

Ka fahimci haka ya kai mai tambaya akan siffofin (mataimakin) Mahdi.


Shi wannan mutumin fatar jikinsa baqa ce,

Gemunsa da qirjinsa kuma mayalwata ne (Nasirul Mahdi).

Kuma yana da idanu kamar na Mussa (Mage).


Wannan mutumin zai yawaita ziyarar mafi alherin halitta (SAW).


Laqabinsa shi ne Sharafuddeeni,

Ibraheem kuma shi ne sunan mataimakin (Imam) Mahdi.


Waxannan Baitoci na Shehu Usman bin Fodiye (RA) sun hallale bayani akan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), tare da tabbatar da cewa lallai shi ake nufi a wannan Bushara, domin ba wani Ibraheem da ya tattara waxannan siffofi in ba shi ba.


DACEWAR SHAIKH ZAKZAKY (H) DA BAITOCIN XAN FODIYE :


Manazarta sun yi nazarin waxannan Baituka na Shehu Usman bin Fodiye (RA), inda suka yi sharhohi masu faxi ta fuskoki da dama. Marubucin littafin “Kitabul-Bushura” da mawallafin “Bayyanar Sharafuddin” da marubucin littafin “Mujaddadin Wannan Qarnin” duk sun yi dogayen bayanai da suke tabbatar da cewa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne kawai ya cika waxannan siffofi da Shehu Usman xan Fodiye ya zayyana.


NA FARKO : Shehu ya ce za a haifi Ibraheem mataimakin Imam Mahdi (AF) ne a qasar yamma manesanciya. To, idan mutum ya duba hadisan da suka yi maganar bayyanar Imam Mahdi (AF), zai ga cewa duk sun tabbatar da cewa Imam Mahdi (AF) zai bayyana ne a Makkah, kuma mataimakansa guda 313 za su je can ne su yi masa Mubaya’a.


To, in aka yi dubi ga Makkah a matsayin wurin da Imam Mahdi (AF) zai bayyana, kenan za a iya cewa qasar da mataimakinsa zai fito wato Nijeriya “Qasar Yamma Manesanciya”, domin in dai za a auno Nijeriya daga Saudiyya, za a iya qiranta qasar yamma mai nisa.


NA BIYU : An ce Ibraheem xin zai bayyana a shekarar 1370 bayan Hijira, sai ga shi an haifi Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a shekarar 1372 bayan Hijira. Wannan ya dace sosai da zancen Shaikh xan Fodiye, domin in za a fassara abin da Shehu ya faxi daga Fulatanci ko daga Larabci zuwa Turanci, to cewa za a yi; “Za a haifi Ibraheem Sharafuddeen ne a shekarun saba’inoni wato (Seventes) bayan Hijira” wanda hakan yana nufin ba lallai ne sai an haife shi a 1970 daidai ba, a ko da yaushe aka haife shi daga 1970 zuwa 1979 duk a 70s aka haife shi.


Sannan kuma, in ma mun tafi akan cewa yana nufin za a haife shi ne a 1370 daidai, to dole mu yi la’akari da cewa Shehu Usman bin Fodiye waliyyi ne ba Annabi ba, Ma’asumi ne kawai in ya faxi magana take tabbata cif da cif, su waliyai ana iya samun abin ya gaza da kaxan ko ya qetare da kaxan.


NA UKU : An faxi siffofinsa kamar cewa shi baqin fata ne, kuma mai faxin goshi, mai alama a fuska, mai mayalwacin gemu, mai faxin qirji, kuma mai manyan idanu farare kamar na Mage. Waxannan siffofi suna iya xaukar ma’anoni biyu, na zahiri da na baxini, kuma duk biyun sun dace da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H).

Misali;Duk mutumin da ya san Shaikh Zakzaky (H), ko ya ga hotonsa, to zai ga cewa a zahirin halittarsa baqin fata ne, kuma yana da faffaxan goshi, kuma yana da alamar Sujjada a fuskarsa, kuma yana da mayalwacin gemu, kuma yana da faxin qirji, kuma yana da manyan idanu farare, da dai sauransu.


Amma a fassara ta baxini, ba zahirin halitta Shehu Usman bin Fodiye ke nufi da waxancan siffofin ba, aron kalma ne ya yi a matsayin lamiri. Kenan, da ya ce mai faxin goshi, yana nufin mai yawan Sujjada na bautar Allah ne. Da ya ce mai alama a fuska, yana nufin mai Haiba ne da kwarjini da hasken fuska. Da ya ce mai yalwar gemu, yana nufin dattijo ne a maganarsa, (wato duk abin da ya faxa gaskiya ne kuma zai tabbata). Da ya ce mai faxin qirji, yana nufin mai tarin masaniya da zurfin ilimi na fannoni daban-daban ne. Da ya ce mai manyan idanuwa, yana nufin mai ganin shiriya ne a haqiqarta, da kuma xora mutane akan tafarkin shiriya madaidaici. Duk waxannan siffofi kuwa sun dace qwarai da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), ka yi nazari ka gani!


BUSHARAR NANA ASMA’U ‘YAR XAN FODIYE (R) :


Waliyiya Nana Asma’u bint Usman bin Fodiye (R) wacce ta rayu tsakanin 1793 zuwa 1864, ta jaddada Busharar bayyanar mujaddadi Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), ita kam ma bayan ta ambaci sunan waliyi Ibraheem, da shekarar haihuwarsa, da dangantakarsa da Imam Mahdi (AF), sai ta qarfafa zance akan yadda wa’azinsa zai sha banban da na sauran malamai, da kuma uwa-uba nau’in sabon ilimin da zai bayyanar a cikin al’ummarsa, wanda wannan ke nuna ilimin tafarkin Ahlul-Bait (AS) ne, wanda Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ke yaxawa yanzu haka a wannan nahiya.


Ga nassin Busharar Nana Asma’u a waqenta mai Baiti 40, amma mun naqalto daga Baiti na 17 ne zuwa na 30 kamar yadda mawallafin littafin “Bayyanar Sharafuddeen” ya yi, wanda sune ke qunshe da batutuwa akan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H);


A cikin shekarar Hijira ta 1400 (1979) ne,

Wani Mujaddadin Musulunci zai bayyana.


Usman (Xan Fodiye) ya faxi zuwansa,

A lokacin da yake maganar Mahdi.


Zukatan da suka haskaka za su fahimci wannan,

Waxanda kuwa ke a cikin duhu ba sa fahimta.


Ana jiran lokutan (bayyanarsa) tun,

Shekaru xari uku da suka shuxe.


Haqiqa an haife shi a shekarar hijirar,

Annabi ta 1370 zai bayyana.

Yana da matsayi mai girma,

Don haka dole ne a girmama shi.


Littattafansa sune hujjarsa,

In kana musu to ka karanta su (ka jiya).


Ganinsa kawai zai iya bayyanar maka,

Da ko shi wanene (idan har ka kula).


Kowa (ya kamata) ya so shi,

Ya kuma kula da amfanonin da zai zo da su.


Ba ko shakku cewa akwai alamomi,

Musulmi ku kula kuma ku fahimta.


Ka da ku kula da ‘yan qananan abubuwa,

Ku kula da hankali kuma ku karanta littattafansa.


Ka da ku ce, “Mu ba mu gaji wannan ba”,

Sannan kuma mu (sam) ba mu fahimce shi ba.


Duk yadda lamari ya kasance ku karanta littattafan,

Kuma ku sanya zukatanku a cikin aminci.


Ya Allah Ta’ala ka tsare mu daga jahilci,

Ka kuma kare mu daga wahalhalun (Duniya).


(The Collected Works of Nana Asma’u. Na Jean Boyd & B.B Mark, naqali daga; “Bayyanar Sharafuddin”, shafi na 48, bisa tasarrufi da tsari).


NAZARIN BUSHARAR NANA ASMA’U (RA) :


Idan muka nazarci waxannan Baituka da kyau, za mu ga akwai qwararan shaidu na zahiri da ke tabbatar da cewa Nana Asma’u (RA) ta qara bayyana wasu siffofi ne na Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a wannan Bushara tata, kuma ta fito da abin a fili qarara ta yadda ba za a iya kore dacewar waxannan siffofi ga Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ba.


Misali, bayan ta faxi shekarar da za a haifi Mujaddadin a 1370, tare da tabbatar da cewa zai jaddada addinin Musulunci, da kuma cewa zukatan da Allah ya nufa da haske za su fahimci Da’awar wannan mujaddadi da aka shafe kusan shekaru 300 ana jiran bayyanarsa. Sai ta faxi wasu sabbin abubuwa guda biyu wanda Shehu Usman bai faxe su a tasa Busharar ba.

Abubuwan kuwa su ne; Bayyanar Mujaddadin a shekarar hijira ta 1400 wacce ta yi daidai da shekarar 1979 Miladiyya, sai kuma yawan littattafan Mujaddadin, da kuma sabon ilimin da zai zo da shi, wanda ta ce lallai mutanen zamaninsa su karanta littattafan, kuma kada su ce wa sabon ilimin da ya kawo “Mu ba mu gaji wannan ba”. Sannan ta qarqare da cewa, lallai mutane su yi anfani da hankali wajan nazarin rayuwa da ayyukan wannan Mujaddadi idan ya bayyana, kar su riqa la’akari da ‘yan qananan abubuwa.


Waxannan muhimman abubuwa guda biyu ba wani Malami a Afirka da ya siffatu da su sama da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), domin a shekarar 1979 ne Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya bayyana, wato a shekarar ne ya shelanta Da’awarsa a wani babban taron qungiyar xalibai musulmi da ya gudana a garin Funtuwa, kuma a shekarar ne duniya ta fara jin xuriyarsa da sunansa a karon farko, sakamakon rikicin “K-GUYS” da ya faru a Jami’ar Ahmadu Bello da ke birnin Zariya, lokacin da Shaikh xin ya jagoranci matasa musulmi suka wargaza taron qungiyar mashaya giyar kwakwa da suka saba yi duk shekara. A lokacin manyan jaridu (ciki har da na qasashen waje) da sauran kafafen yaxa labarai duk sun yaxa wannan abu da ya faru, tare da ambatar sunan Shaikh Zakzaky (H) a matsayin wanda ya jagoranci abin.


Sannan da Nana Asma’u ta ce zai kasance mai yawan littattafai, wanda take cewa ya kamata mutane su karanta su, wannan zai iya xaukar ma’anar yawan wa’azozi, da laccoci, da huxubobi, da Muhadharorin da Shaikh Zakzaky (H) ke ta yi ne, wanda yanzu kusan shekaru 40 kenan yana yi, amma da yawan mutane ba su ma sauraron jawaban, balle su ji me yake faxa, balle su fahimce shi. Na’am, idan ma tana nufin littattafai ne na zahiri, to akwai ximbin littattafan Shaikh Zakzaky (H) akan batutuwa daba-daban, wanda laccoci da muhadharorinsa ne aka maishe su zuwa littafi.


Abu na uku shi ne nau’in sabon ilimin da zai bayyanarwa musulmi a zamaninsa, wanda Nana Asma’u take gargaxin cewa kar mutane su ce su ba su gaji irin wannan ilimin a wajan iyayensu ba. Wannan a zahiri yana nufin ilimin tafarkin Ahlul-Bait (AS) ne, wanda ake qira Shi’a, domin shi ne nau’in sabon ilimin da Shaikh (H) ya bayyana a wannan nahiya, wanda kuma sashen musulmi ke faxa da shi bisa hujjar cewa su ba su yarda da shi ba don ba akansa suka tarar da iyayensu ba.


Kenan, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) shi ne mujaddadin da Shehu Usman bin Fodiye da ‘yarsa Nana Asma’u suka yi Busharar bayyanarsa, domin shi ne kaxai ya cika sharuxxa da siffofin da waxannan waliyyan Allah suka zayyana a Busharorinsu, amma idan wani na da ja, sai ya kawo nasa gwanin a xora shi akan waxancan sikelin a gani!

more_vert

RefreshRate ApplicationMore Application

SHAIK IBRAHEEM ZAKZAKY (H)
Jagoran harka islamiyyah a Afrika



homeGidashareKyautarwapeopleMasaniyahelpIzinimailTuntuba





KAMMALAWA

Alhamdulillahi Auwalan wa Aakhiran, a wannan xan qaramin littafi, mun yi tsokaci a vangarori da dama na rayuwar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), kama daga busharorin bayyanarsa, zuwa haihuwa da yarintarsa, zuwa Da’awa da salon gudanar da rayuwarsa, zuwa gallazawar azzalumai gare shi, har zuwa kan sauran abubuwan da ke xanfare da rayuwarsa, muna fatan Allah ma ji roqon bayi ya tabbatar da mu tare da shi Abadan wa Sarmadan!


Muna roqon Allah cikin qasqantar da kai, ya qara kariya mai yawa da tsaro ga Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), ya tsawaita rayuwarsa tsawaitawa, ya qara masa garkuwa da kariya daga makirce-makirce da mugun nufin maqiya da azzalumai, ya fisshe shi sharrin zamaninsa, ya qara masa qoshin lafiya da inganci, ya qara masa daraja da xaukaka da martaba, ya qara masa yarda da kusanci gare shi, ya qara masa Nasara akan mahassada da abokan gabarsa, Yaa Allah ka cika burin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a rayuwarsa, ka hutar da zuciyarsa da cikar burinsa, ka kwaranyar masa da damuwa da qunci a zuciyarsa, ka zamo gatansa akan komai ya Rabbal Alameen! Bihaqqi Muhammadin wa Aailihix-Xahireen! “Allahummah Swalli Ala Muhammadin, wa Aali Muhammad!”. 

more_vert

RefreshRate ApplicationMore Application

SHAIK IBRAHEEM ZAKZAKY (H)
Jagoran harka islamiyyah a Afrika



homeGidashareKyautarwapeopleMasaniyahelpIzinimailTuntuba





MANAZARTA

1. BAYYANAR SHARAFUDDIN: SHEIKH IBRAHIM ZAKZAKY (H).

Al’Ameen Isah Al-Sakkwaty, I.M Publications, 2001.


2. TARIHIN SAYYID IBRAHIM ZAKZAKY DA HARKAR MUSULUNCI.

Malam Muhammad Sulaiman. GDP-Printers, 2015.


3. MALAM ZAKZAKY (H): RAYUWARSA DA KARAMOMINSA.

Mal. Yaqubu Yahya, da Mal. Abubakar Abdullahi, 1994.


4. SHEKARU 60 MASU ALBARKA NA SAYYID ZAKZAKY (H).

Mal. Ibrahim Musa (Edita), I.M Publications, 2012.


5. MALAM, MALAM NE.

Malam Haruna Shelleng, Sauqi Press Kaduna, 1428 – 2007.


6. MUJADDADIN WANNAN QARNIN: Sayyid Ibrahim Zakzaky (H).

Nasir Miji Gombe, Babu Maxaba’a, 2013.


7. KITABUL-BUSHRA: Busharar Bayyanar Sheikh Zakzaky (H).

Mal. Ibrahim Musa (Edita), I.M Publications, 1416 Hijra.


8. WAKILIN MANZO (S) A DORON QASA (Malam Zakzaky).

Muhammad Danjuma Katsina, I.M Publications Zaria, 1998.


9. Jaridar ALMIZAN, da Mujallar GWAGWARMAYA.


10. KASETOCI Da INTANET Da SOCIAL MEDIA.


✳✳✳ ✴✴✴ ✳✳✳


TALLA

Mai karatu ! Kana son sanin tarihin Harkar Musulunci a Nijeriya cikin sauqi kuma daki-daki dalla-dalla? Maza tanadi kuxinka don mallakar sabon littafi mai fitowa, mai suna “TARIHIN HARKA ISLAMIYYAH”. Shi wannan sabon littafi ya hallale bayanai akan Harka Islamiyya ne zalla, da munufarta, da ayyukanta, da qudurorinta da kuma bayyana ayyukan kowace Lajana ta Harka Islamiyyah.


Littafi ne da zai fito daga Cibiyar Wallafa da Yada Jawaban Shaikh Zakzaky (H), wanda zai haskakawa mutum masaniya game da tushen Harka Islamiyyah, Manufarta, Ayyukanta, Lajanoninta da inda ta dosa. Ku dai ku tanadi kuxinku kawai kafin littafin ya shigo kasuwa!


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


1 Comments On SHAIKH ZAKZAKY IKON ALLAH
avatar
shuraihu-usman-1

1 year ago

Reply

sss

Please Login or Register in order to submit comment