Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi, ko irin abin da ke faruwa bagatatan xinnan, wanda ke firgita mutane, to shi gabansa ba ya faxuwa.


Marubucin littafin ‘Tarihin Harkar Musulunci’ yana cewa; “Akwai ma lokacin da yake cewa idan Akuya za ta ba shi tsoro, to arne ko Azzalumi zai ba shi tsoro, wato tunda Akuya ba za ta ba shi tsoro ba, to, babu wani abu da ya isa ya ba shi tsoro (a duniya!)” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 29).


A wani jawabi da Shaikh Zakzaky (H) ya yi a ranar “Yaumus-Shuhada” na shekarar 2003 yana cewa; “(Mahukunta) su kan riqa yin wani gadara wai su ce; Wa ya fi qarfin gwamnati?’ To, mun fi qarfin gwamnati! In ta ce qarya ne ta zo! Iyaka dai kurkuku ne da kisa, ya wuce haka ne?....(ba ta yi harbin bane? Ba ga mu ba! Ba ta yi kamun bane? Ba ga mu ba!). To, ba ma kurkuku ba, wallahi tallahi ko da kuna da Jahannama, kuma ko da Jahannamar taku ta kai zafin ta Allah Ta’ala, a shirye muke mu shigeta! Don mun san ita Jahannamar taku mai qarewa ce, ta Allah ko ba ta qarewa. Ta Allah muke jin tsoro ba taku ba!”


Ba shakka Shaikh Zakzaky (H) ya gaskata wannan iqirari nasa, domin duk kamun da ake yi masa bai tava gudun kar a kama shi ko ya yi rakin kamun ba, maimakon haka ma, shi nuna jin daxin kamun yake yi. Misali, lokacin da aka kai Shaikh Zakzaky (H) gidan yarin azabtarwa na Kirikiri da ke Legos a shekarar 1984, ya rubutowa ‘yan uwa almajiransa wasiqa, a ciki yake cewa; “Lokacin da ake tuqani zuwa Kirikiri, na ji wani daxi da farin ciki wanda ban tava jin irinsa ba!” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 42)


Ka ji irin wannan jarunta! Kirikiri fa; Waje ne da ake kai mutanen da ake so a musguna masu, ko a azabtar da su, domin akwai karikitai na azabtarwa daban-daban a ciki. Malam yake cewa; ko sauro mutum ya kashe sai an masa bulala, za a ce masa wai ya damu yaran gwamnati” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 43). Amma da aka kama hanya za a kai shi wurin, shi ne yake cewa ya ji wani daxi da farin cikin da bai tava jin irinsa ba! Wannan wace irin jarunta ce?


Sannan bayan fitowarsa daga kurkukun Inugu, cikin jawabin da ya yi wa ‘yan uwa yana cewa; “Wani abu wanda yake shu’uri ne (wato a jiki ake jinsa), wanda sai in kai ma ka ji ne za ka iya fahimta, shi ne abin da na gani a zamana na kurkuku. (Amma) tunda ba a yarda mutum ya je ya qwanqwasa gidan kurkuku ya ce a buxe masa ya shiga ba, (da ana haka da na yi, to, amma tunda ba a yi), duk ran da aka zo aka kamani zuwa can zan yi farin ciki!” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 44). Mai karatu, ka ji mai neman shiga kurkuku, wanda bai tava tsoron xauri a gidan fursuna ba, da me za ka kwatanta jaruntarsa?


Shaikh Zakzaky (H) jarumi ne da dukkan ma’anar jarunta, domin lokacin da gwamnatin Nijeriya qarqashin jagorancin Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta kama shi ta gurfanar da shi a gaban kotu, alqalin kotun Justice Karibi White ya yanke masa hukuncin xaurin shekaru huxu a gidan kurkuku. Bayan an karantawa Shaikh Zakzaky (H) laifinsa da irin hukuncin da kundin tsarin mulki ya tanada ga masu irin wannan laifi, kafin a zartar da hukuncin, sai alqali ya tambaye shi cewa; “Ko kana da wani roqo (na neman sassauci) da za ka yi ga kotu?”

Sai Shaikh Zakzaky (H) ya ce; “Ina roqon kotu ne da ta zartar mun da mafi munin hukuncin da za ta iya, ta zartar mun da mafi tsananin hukunci na iya qurewarta! Kar ta sassauta mini!” Sa’annan Shaikh Zakzaky (H) ya fuskanci alqali Karibi White ya ce masa; “Idan kana da zavi tsakanin harbi ko xaurin rai da rai, to ka zartar mun da hukuncin harbewa!” Wannan jawabi ya girgiza alqali da duk waxanda ke cikin kotun, dan ba su tava jin wanda ke fuskantar hukunci ya faxi haka ba a tarihinsu!


Jaruntar Shaikh Zakzaky (H) za ta qara fito maka fili ne in ka san cewa; “(Saboda yawan) kame-kame na ba zata (da ake yi masa), sai da ta kai ga Malam a wani lokaci ya kai ga aje wata jaka, a cikinta ya sa sabulun wanka da na wanki, man shafawa, turare, (Makilin da Brush), da tufafi na canzawa da dai makamantansu, yake cewa jakar ba ya tava ta, tana aje ne kawai, da an zo kama shi sai dai ya xauketa (ya rataya) ya ce mu je!” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 44).

A lokacin mulkin sugaban qasa Olusegun Obasanjo (daga 1999 zuwa 2007), labaran asiri sun yi ta zuwa cewa ana shirin abkawa da kashe jogaran Harka Islamiyyah Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), da rahotannin suka yi qarfi sai wasu suka shawarci Shaikh Zakzaky (H) cewa ko zai xan yi hijira zuwa wata qasa kafin abubuwa su daidaita, sai Shaikh Zakzaky (H) ya ce; “Ko Janar aka ce masa Zakzaky zai yi gudun hijira zai ce qarya ne!!” wannan ya nuna jaruntar Shaikh Zakzaky (H) ne a fili qarara!


Tabbas Shaikh Zakzaky (H) ya gaskata wannan iqirari nasa, domin lokacin da gwamnatin shugaban qasa Umaru Musa Yar’adua ta shirya jefa Bom a gidansa cikin dare a shekarar 2010, an shawarci Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da ya bar gidan, amma ya ce wallahi ba inda za shi, sai dai su kashe shi a cikin gidansa, kuma haka aka yi, a cikin gidan ya kwana, Allah Ta’ala ya wargaza mummunar aniyarsu.

Haka nan, mummunan harin da bataliyar sojojin Nijeriya qarqashin Hafsan sojoji Janar Tukur Yusuf Burtai, bisa umarnin shugaban qasa Muhammadu Buhari suka kai gidan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a watan Disamba na shekarar 2015, inda suka kashe kusan mutum dubu kafin su iya kaiwa gare shi, tun kafin su ci qarfin ‘yan uwa an buqaci a fita da Shaikh Zakzaky (H) don tseratar da shi, amma ya ce ba inda zai je, yana nan a cikin gidansa, sai dai su zo su yi masa duk abin da za su yi!


Hakan kuwa aka yi, sai da aka shafe sama da awowi 48 ana ruwan wuta, har aka cimma gidansa, aka harbawa gidan Gurneti, gidan ya kama da wuta ya qone qurmus, amma Shaikh Zakzaky (H) yana cikin wani qaramin xaki na dakin shi da iyalansa, qarshe har suka zo kansa suka yi ruwan harsashi suka kashe ‘ya’yansa uku, suka harbi matarsa a sama da wurare goma a jikinta, shi ma suka harbe shi a wurare goma sha xaya a jikinsa, ciki har da cinya da qirji da goshi da idanuwansa biyu har sai da idonsa na hagu ya zazzago ya fito waje, sa’annan suka xauke shi suka tafi da shi rai a hannun Allah! Wannan jarunta irin ta Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) tarihi ya daxe bai ga irinta ba!


AMSA ADDU’ARSA :


Allah Ta’ala ya yi alqawarin amsa addu’ar bayinsa a yayin da suka roqe shi, tattare da haka bayin Allah managarta addu’o’insu sun fi karvuwa cikin gaggawa da sauri. Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana cikin bayin da Allah ke gaggauta karvar addu’o’insu da biya musu buqatar abin da suke nema.


Misalin hakan shi ne; A shekarar 1991 an yi waqi’a a birnin Katsina, inda jami’an tsaro suka farwa almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da suka fito muzaharar Allah wadai da zagin Manzon Allah (S) da wata jarida mai suna “FunTimes” ta  kanfanin “Daily Times” ta yi. Jami’an tsaron sun farwa ‘yan uwa suka yi ta dukansu da kulake da gindin bindiga, inda suka raunata da dama, suka kwashe su cikin jini suka je suka kulle ba tare da sun kai su asibiti don magani ba.

Bayan kwana biyu da faruwar lamarin, sai ‘yan jarida suka tuntuvi kwamishinan ‘yan sanda na Katsina a lokacin, wato Saminu Daura dan jin halin da ‘yan uwan da ake tsare da su suke ciki. Sai Saminu Daura ya ce duk waxanda ake tsare da su suna cikin qoshin lafiya da aminci, alhali a lokacin ‘yan uwa suna tsare a hedikwata da barikin ‘yan Sanda cikin tsananin galabaita da raxaxin ciwuka da raunukan da aka yi musu ba tare da ba su magani ba.


Da Shaikh Zakzaky (H) ya ji wannan hira sai ya yi raddi ga Saminu Daura, ya ce; Idan halin da ‘yan uwa ke ciki shi ne halin qoshin lafiya da aminci, to yana roqon Allah ya ba Saminu Daura irin wannan qoshin lafiya da amincin! Ba a daxe da wannan addu’a ba Saminu Daura ya kamu da matsananciyar jinya wacce wasu rahotanni suka ce har haushin Kare yake yi, zuwa xan wani lokaci ya sheqa barzahu.


Har wala yau, a Shekarar 1992, jami’an tsaron Nijeriya sun kama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano a birnin Kano lokacin da zai je wani taro a qasar Ingila. Suna kama shi suka yi awon gaba da shi zuwa kurkukun Dodon-Barrack na Legos, da nufin tsare shi har illa masha Allah. Shi kuma Shaikh (H) a lokacin yana cike da shauqin halartar wannan taro na London. Dan haka yana shiga kurkukun ya xaga hannu ya roqi Allah cewa ya tabbatar masa da wannan buri na tafiya London don halartar wannan taro da kuma haxuwa da ‘yan uwa na Ingila.


Addu’ar da ya yi tana da ma’ana kamar haka; Ya Allah, ka sani na yi zaman kurkuku a wuri kaza da kaza, amma daidai da rana xaya ban tava roqonka ka fitar da ni daga cikinsu ba, sai dai da kanka kake fitar da ni a lokacin da ka ga dama. Amma a wannan karon ina shauqin haxuwa da ‘yan uwa na Ingila da ganawa da su, ina so in halarci wannan taro da za a yi, ina roqonka ka fitar da ni da ikonka, “Ya Allah ka gaskata zatona gareka”.


Yana yin wannan addu’ar sai kawai umarni ya zo na sakinsa, kuma aka ba shi takardunsa na izinin tafiya, ya kama hanya ya fita zuwa Ingila, duka-duka tsarewar da aka masa a lokacin ta ‘yan kwanaki ce.


Sannan, a shekarar 1994, bayan wasu almajiransa sun valle sun yi masa tawaye, sai suka yi gangami suka kafa qungiyar yaqarsa da bishe hasken Da’awarsa mai suna “Jama’atu Tajdeedil Islam” wato JTI ataqaice. Sai ya yi jawabi game da su, ya fayyace musu abubuwan da suke zarginsa da su na aqidar Shi’anci daki-daki. Sannan daga qarshe sai ya roqi Allah Ta’ala cewa; Ya Ubangijin Musa da Harun, idan abin da waxannan mutane suke akai, shi ya fi soyuwa da zama daidai a gareka, to ka rusa nawa ka tabbatar da nasu, idan kuma nawa ne ya fi soyuwa gareka da zama daidai, to ka rusa nasu ka tabbatar da nawa”.


Bayan yin wannan addu’ar ba daxewa Allah ya rusa wannan gungu na ‘yan Tawayiya, ya shagaltar da su da kawukansu, suka tarwatse suka dena batun Tawayiyanci suka shagaltu da neman duniya da neman abinci, ya zamanto su da qungiyar ta su ta JTI ba su da wani tasiri a cikin al’umma, hasali ma mafi yawan jama’a ba su san da qungiyar tasu ba. Wannan ‘yan misalai ne kawai na yadda Allah Ta’ala ke amsa addu’ar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H).

KARAMOMINSA :


Allah Ta’ala ya yi wa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) karamomi masu yawa, waxanda aka sani da waxanda ba a sani ba, domin Shaikh Zakzaky (H) ya kasance mai voye karama da rashin son nuna ta, amma tattare da haka wasu karamominsa kan bayyana ba tare da nufi ba.


Misali; Kamun da aka yi masa na farko a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya cikin shekarar 1979, an kulle shi a ofishin ‘yan sanda ne na Zariya, ya shafe kwana uku ba ci ba sha, suka hana shi cin komai, bayan kwana uku sai suka fito da shi da nufin zai amsa wasu tambayoyi, da suka ba shi takarda ya rubuta jawabinsa (Statement), sai da ya rubuta musu shafi tara na amsoshin abin da suka tambaye shi, har su jami’an tsaron suna mamaki, suna cewa dubi rubutunsa mai kyau kamar wanda bai sha yunwa ba! A wata hira Shaikh Zakzaky (H) ya ce, duk da ya shafe tsawon kwanakin bai ci abinci ba, amma shi kwata-kwata bai ji yunwa ko qishin ruwa ba. Wannan karama ce babba! (Rairayowa daga Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 42)


A farkon shekarun 90s, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya je Umrah, a hanyarsa ta dawowa sai jirgin samansu ya samu matsala, (wasu sun ce da gangan aka so a halakar da shi). Jirgi ya rinqa tangal-tangal, fasinjoji suka rikice suna ihu da neman taimako, amma Shaikh Zakzaky (H) yana zaune a natse akan kujerarsa yana ta karatun Alqur’ani, sam babu alamar damuwa a tattare da shi kamar bai san abin da ke faruwa ba. Da matsalar ta qara muni, hankalin fasinjoji ya tashi matuqa, sai Shaikh cikin natsuwa ya xaga hannu sama ya yi wata gajeruwar addu’a, nan take jirgin ya daidaita, sai ga sanarwa daga matuqa jirgin cewa komai ya yi daidai. Wannan ya sa mutane da yawa a jirgin suka rinqa neman tabarrukin Shaikh (H), har wani a cikin mahajjatan ya ce “Daga yau na zama xan Buraza!” (Tasarrufi daga Malam Zakzaky: Rayuwarsa da Karamominsa, shafi na 09).


A shekarar 1992, lokacin da aka kama Shaikh Zakzaky (H) a filin jirgin Malam Aminu Kano sa’adda zai tafi Ingila, an kai shi wani wuri ne aka tsare shi ya kwana, washe gari sai aka zo da sabuwar mota aka sa shi a ciki, aka kama hanya ba tare da an ce masa uffan ko an sanar da shi inda za a kai shi ba. To, tun ba a fita daga cikin Kano ba, sai Shaikh Zakzaky (H) ya cewa jami’an tsaron da ke tafiya da shi; “Ku me ya sa ba za ku yi xabi’a irin ta mutane ba! Wannan xabi’a taku ta sava da xabi’a irin ta mutunci, domin ni mutum ne kuka xauko ba Akuya ba, idan za ka saka Akuya a cikin mota ka kai ta Legos, ba ka buqatar ka yi mata bayani, ka ce Akuya zan kai ki Legos. Haka nan idan za ka xauki buhun shinkafa, ba ka buqatar ka ce masa zan kai ka wuri kaza, sai dai ka kai shi kawai. Amma ni mutum ne (ba Akuya ko Buhun shinkafa ba), menene ya hana a jiya ku ce min, an umarceku ne ku hana ni tafiya, kuma yau ku ce, an umarce mu da mu kai ka Legos? Shi kenan!” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 45, da tasarrufi kaxan).


A wannan abun da ya faru akwai nuna Karama a ciki, domin ba wanda ya ce wa Shaikh Zakzaky (H) Legos za a kai shi, sai ga shi cikin hikima ya faxa musu cewa Legos za su kai shi, kuma Legos xin suka kai shi kai tsaye. Wannan menene in ba Karama ba?


A shekarar 1994 a wani gari da ake kira Lushi a kusa da birnin Bauchi, qasa ta kama hannun wani yaro saboda ya qaryata Shaikh Zakzaky (H). Musu suke yi da ‘yar uwarsa, shi yana cewa Shaikh Zakzaky vatacce ne kuma Da’awarsa halaka ce. Ita kuma yarinyar (wacce ‘yar Baffansa ce) tana cewa lallai Shaikh Zakzaky akan shiriya yake, kuma yana kira ne zuwa ga hanya madaidaiciya.

Sai suka yi ittifaqi cewa su yi ‘yar qasa-qasa, (wata al’adar Hausawa ce da yara ke anfani da ita don gane marar gaskiya a tsakanin mutane biyu, za a tara yashi ne ko qasa, sai wanda ake tuhuma ya cusa hannunsa iya wuyan hannu a ciki, sai ya yi rantsuwa cewa in ba shi ne akan gaskiya ba to qasa ta kama hannunsa). Sai yarinya mai gaskata Shaikh Zakzaky ta fara sa hannunta a cikin qasa, ta yi rantsuwa, kuma ta ce in ba haka bane qasa ta kama hannunta, tana zarowa sai hannu ya fito. Sai shi ma yaro ya cusa hannunsa cikin qasa, ya yi rantsuwa cewa Shaikh Zakzaky (H) akan vata yake, kuma Da’awarsa halaka ce, in ba haka bane qasa ta kama hannunsa.


Abu kamar wasa sai hannu ya maqale, qasa ta riqe hannunsa qam, har sai da aka kawo masa xauki, aka yi aka yi a cire hannu ya qi fita, yaro sai kuka yake yi, sai aka ce masa sai in ya warware wannan rantsuwar ya gaskata Shaikh Zakzaky ne kawai hannun nasa zai fita. Haka kuwa aka yi, yana gaskata shiriyar Shaikh Zakzaky (H) da ya zaro hannun sai kawai ya fito. Jaridar Al-Mizan ta wancan lokacin ta hakaito wannan labari na karamar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H).

Haka nan, a wajajen shekarar 1997, an yi wata gobara a gidan wani xan uwa a birnin Gombe, inda gobarar ta cinye komai na xakin gidan amma ta bar hoton Shaikh Zakzaky (H) da ke rataye a xakin, hatta katakon da aka sanya hoton a jikinsa bai qone ba, kuma wannan hoton shi kaxai ne ya tsira a xakin, komai ya qone qurmus. Wannan karama ta qarawa mutane da dama yaqini game da sha’anin Shaikh Zakzaky (H).


Haka nan, wani xan uwa da yake neman wata budurwa da aure, ya yi tsananin kamuwa da so da qaunarta, sai ya yi ta yin Istihara yana roqon Allah cewa; Ya Ubangiji, in aurena da wance alheri ne, ka qaddara mun shi cikin sauqi da yalwa, in kuma sharri ne, to ka rusa abin ka hana shi yiwuwa”. Yalai kuwa sai abu ya rushe, yarinya ta kawo sunan wani wanda take so, ya turo iyayensa suka biya sadaki aka sa ranar xaurin aure.


Sai wannan xan uwa ya shiga halin qunci mai tsanani saboda son wannan budurwa da yake yi, ya kasa jurewa rabuwa da ita saboda xanfaruwar zuciyarsa da ita, ba ya iya bacci balle cin abinci, komai nasa ya dagule, ya rasa abin da ke masa daxi. Watarana sai ya ce bari ya je majalisin yamma na gidan Shaikh Zakzaky (H) da nufin ko zai manta da damuwar da ke damunsa, kuma ya yi Tawassuli da nufin Allah ya yaye masa qaunar yarinyar nan da ya addabi zuciyarsa.


Ya je gidan Shaikh (H) da wuri ya samu wuri a gaba ya zauna, zuwa can sai Shaikh (H) ya fito ya zauna a wurin zamansa, yana gama gaisawa da mutane sai kawai ya kama magana akan Istihara da yadda ake yinta, ya ce; “Da yawan mutane ba su iya Istihara ba, sai su roqi Allah cewa “In abin nan alkhairi ne ka tabbatar mun da shi, in kuma sharri ne ka wargaza shi ka hana shi yiwuwa”. Wani lokaci in abin ba alheri ba ne sai Allah ya hana shi yiwuwa, amma ya bar ka da son abun a ziciyarka. Kamata ya yi mutane su riqa cewa “Ya Allah in wannan abin alkhairi ne ka qaddara mun shi cikin sauqi, in kuma sharri ne gareni ka kore shi daga gareni, kuma ka cire mun qaunarsa da sonsa a zuciyata”.


Xan uwan yana jin haka sai kunya ta kama shi, ya duqar da kai qasa yana matuqar mamakin wannan al’amari, domin shi dai bai faxawa kowa abin da ya kawo shi ba, bai kuma faxawa Shaikh (H) wannan labarin ba, amma ya aka yi Shaikh (H) ya iya fahimtar damuwarsa? Wannan tambayar har zuwa yau bai samu amsarta ba, amma dai daga wannan rana ya samu waraka daga ciwonsa na soyayya.

Babu shakka duniya shaida ce cewa Allah Ta’ala ya yi wa Shaikh Zakzaky (H) karamar Kashafi, wannan karama ta Kashafi wani abu ne da ke bayyane ga ma’abuta nazari, misali; duk wani qulle-qulle da makirce-makircen da maqiya suka qulla masa, ko suke qullawa Harka Islamiyyah, to za ka ga ya tona asirin shirin.


Wani lokaci za a qulla abin cikin tsattsauran matakan tsaro don kar abin ya fita, amma sai ka ji yana bada labarin yanda abin ya gudana, wani lokaci ma mutum biyu ne ko uku za su qulla abin, amma sai ka ji ya tona asirin shirin, har ma ya fito da takardar “Blueprint” xin shirin. Wannan hatta su maqiya da jami’an leqen asiri abin yana matuqar ba su mamaki, wani lokaci ma ba a Nijeriya ake shirya abin ba, amma zai sani, misali kwangilar da aka ba wani qwararren kanfanin kisan kai da ke Amurka, na wani xan asalin Birtaniya mai suna Patrick Williams a shekarar 2012.


ALBARKARSA :


Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) wani xan baiwa ne mai wata irin albarka wacce ba ta voyuwa ko kaxan! Komai nasa cike yake da albarka komai qarancin abin kuwa, duk wanda ya san Shaikh Zakzaky (H) zai iya zama shaida kan wannan abu da muke faxa.


Misali; qanwar Mahaifin Shaikh Zakzaky wacce ake kira Goggo Fatimah, ta faxi cewa; “Lokacin da aka haife shi mun ga abin mamaki, akwai jama’a da kuma abubuwan gudunmawa da aka samu, duk cikin ‘ya’yanmu ba a samu wanda aka samu falala (ta cikar jama’a da samun gudunmawa) irinsa ba!” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 67).


Anan, Goggo Fatimah tana cewa ne tun daga haihuwar Shaikh Zakzaky (H) aka ga albarkoki masu yawa a tattare da shi, ximbin jama’a suka halarcin bikin sunansa, kuma ba qaramar gudunmawa mahaifansa suka samu daga abokan arziqi, makwabta da dangi ba, kenan Shaikh (H) tun asali da albarkarsa ya shigo duniya.


Kamar yadda muka faxa, ba kawai Shaikh Zakzaky (H) ne ke da albarka a tattare da shi ba, duk ma wani abu mai alaqa da shi ba qaramar albarka yake da shi ba. Misali; masu sana’ar buga fosta ta hotunan manyan malamai, ba fostar da suke cinikinta kamar ta Shaikh Zakzaky (H), sam ba sa tsoron buga fostar Shaikh komai yawanta, domin sun san za ta qare, an qiyasta cewa xaruruwan mutane ne ke cin abinci ta hanyar sayar da zallar hotuna, sitikoki, littattafai da fostocin Shaikh Zakzaky (H).


Haka nan, duk lokacin da aka rubuta littafi akan Shaikh (H) ko akan wani abu da ya dangance shi, to ba a samun kwashe na wannan littafin, ko da za a yi ta maimaita bugawa, to kuwa zai yi ta maimaita qarewa! Sau da yawa idan Shaikh (H) zai je wani gari, har hanyar garin ake bi a gyara wuraren da suka lalace, dan haka hatta masu bin hanya sukan samu albarkar wucewar Shaikh (H).


Idan Shaikh Zakzaky (H) zai je wa’azi ko ziyara wani gari daga cikin garuruwan qasar nan, masu sana’o’i na abinci, da abin sha, da sauran kayan buqatu, da masu motocin haya, da masu gidajen man fetur, ba qaramar darawa suke yi ba. An tava ruwaito wani mai sayar da Shayi yana cewa; “Da Shaikh Zakzaky zai riqa zuwa garin nan duk shekara, to da zan yi arziqin da zan fi qarfin sayar da Shayi!”

Wani abin da ke qara tabbatar da cewa duk wani abu da ya shafi Shaikh Zakzaky (H) albarkarsa ba ta misaltuwa shi ne abin da ya faru a zauren “Marital Solutions” na ‘Whatsapp’ a cikin watan Yuni na shekarar 2016, inda wata ‘yar uwa ta faxi laqabin da uwargidan Shaikh Zakzaky (H) Malama Zeenatu ke kiransa da shi, wanda a sakamakon haka sai da membobin zauren suka yi mata hadaya ta wuridin Salatin Annabi (S) dubu xari biyu da hamsin a matsayin tukuici.


Mai karatu, idan faxin laqabin Shaikh Zakzaky (H) na “Khaleel” kawai zai sa a yi wa mutum Salatin Annabi (S) kwata Miliyan a matsayin tukwici, to, lallai wannan mafificin shaida ne cewa duk wani abu da ke da alaqa da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) albarkarsa ba ta da iyaka! Wani mawaqi yana cewa; Mai albarka, xan albarka, Al-Zakzakiyu kogin albarka!


TASIRINSA : 


Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana cikin zavavvun bayin Allah qalilan da Allah Ta’ala ya yi wa baiwar tasiri a zukatan al’ummar da yake rayuwa a cikinta, domin a fili yake cewa zantukan Shaikh Zakzaky (H) da ayyukansa ba qaramin tasiri suke yi ga almajiransa da ma al’umma baki xaya ba.


Misali; Tun bayan lokacin da mutane suka fahimcin cewa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana yin azumomin watanni uku masu alfarma (Rajab, Sha’aban, Ramadan) a jere, sai ya zamo ximbin jama’a sun tasirantu da hakan, sun lizimci yin azumomin watannin a jere, duk da cewa Shaikh xin bai tava umartar wasu da yin hakan kai tsaye ba, kuma abin bai tsaya ga almajiransa kawai ba, har da sauran jama’ar gari.


Haka nan, a ranar tunawa da waqi’ar Ashura na shekarar 1434 Hijiriyya, wanda

1 Comments On SHAIKH ZAKZAKY IKON ALLAH
avatar
shuraihu-usman-1

1 year ago

Reply

sss

Please Login or Register in order to submit comment