Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya yi daidai da shekarar 2012 Miladiyya, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya sauka a motarsa ya yi tattaki da qafafuwansa ba tare da takalmi ba daga qofar Doka zuwa babban masallacin Idi na Zariya. Ya yi wannan Tattaki ne akan kwalta kuma a lokacin ana tsananin zafin rana. Wannan tattaki da Shaikh Zakzaky (H) ya yi ya zama wata Sunnah abin xabbaqawa ga almajiransa da dama, ta kai ga akwai waxanda suke Tattakin Arba’een tun daga garuruwansu har zuwa Husainiyyah Baqiyatullah Zariya, wanda tafiya ce ta kwanaki, amma ba tare da takalma a qafafunsu ba, dan kawai koyi ga aikin jagora (H).


A wasu lokutan baya, Malam ya ziyarci garin Lokoja, inda ya ziyarci qaburburan wasu sarakunan Musulunci da Bature ya kai su garin Lokoja suka rasu a can, irin su Sarkin Kano Aliyu xan Abdullahi, da Sarkin Zazzau Aliyu xan Sidi, da su Sarki Kwasau da Sarkin Bida da na Gwandu.

“Sadda Malam ya je da farko duk waxannan qaburbura sun zama Bola da wurin kewayawa da gidajen vera da burgu, an manta da su, musamman ma Sarkin Kano. To amma cikin hukuncin Allah zuwan Malam ke da wuya sai kowace masarauta ta tashi haiqan da gyara maqabartar Sarkinsu, misali, na Kano sun gine wurin, an yi azuzuwa, kuma an kewaye wurin da gini, mai buqata ya je ya gani.


“Na Zazzau su ma ba a bar su a baya ba, sun gina masallaci a wurin qabarin Aliyu xan Sidi, da wasu azuzuwa. Kafin ziyarar Malam Zakzaky waxannan qaburbura lallai an manta da su, don kafin mutum ya shiga wurin sai ya rufe hanci don wari da qazanta. Wannan abu da na gani a Lokoja na sanya shi a cikin nasarorin Malam Zakzaky!” (Malam, Malam Ne, shafi na 36).


Tasirin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) bai tsaya ga almajiransa da sauran al’umma kaxai ba, hatta gwamnatin Nijeriya a wasu lokuta in ta fito da wani tsari da ya shafi al’umma wanda take so ta cimma nasarar aiwatar da shi, ba mutumin da take sauraron tsokacinsa akan shirin nata kamar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), domin da zaran ya yi magana akan abu, to al’ummar qasa sukan samu waraka game da abin, idan ya kushe abin ko ya nuna illarsa, to al’umma za su bijirewa abin, gwamnati ba za ta tava iya cimma nasarar aiwatar da shirin ba (allrar Poliyo ta isa misali), amma idan ya yi shiru akan lamari, to, gwamnati kan samu qarfin gwiwar aiwatar da shi. Wannan tasiri na Shaikh Zakzaky (H) ga al’umma yana xaya daga cikin abin da ke xagawa gwamnatin Nijeriya hankali, domin tana ganin ya za a yi a samu wani mutum ya fi hukuma tasiri ga al’umma?


Tasirin Shaikh Zakzaky (H) ya haifar da canje-canje da dama a sassa da vangarorin al’umma masu yawa, kama daga vangaren Malamai ta sashen wayewarsu, ‘yancinsu, da salon tsaronsu. Zuwa vangaren xalibai, talakawa da sauran vangarori. Tasirin da Shaikh Zakzaky (H) ya yi a sassa na rayuwar jama’a ne ya sa manazarta ke cewa ya riga ya yi nasarar juyin juya hali “Ravolution” a Nijeriya.


A taqaice, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi matuqar tasiri a kowane fanni na rayuwar al’ummar qasarsa, domin za ka ga jama’a suna matuqar koyi da shi a dukkan sassa na rayuwarsa, kama daga tsabtarsa, adonsa, zamantakewarsa da iyali, har ma da kwaikwayon salon kalmomi na maganarsa. Wannan tasiri da Allah Ta’ala ya ba Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana xaya daga cikin abubuwa mafi muhimmanci da suke jan hankalin hukumomi da manazarta akan rayuwar Shaikh Zakzaky (H) da dalilan da suka sabbaba masa wannan tasirin.


RAHARSA :


Babu shakka, wasu mutanen da ke hangen Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) daga nesa, za su xauka mutum ne mai kaushi da tsanani, amma ga duk wanda ya kusance shi, zai gane cewa shi mutum ne mai tsananin sauqin kai da raha, ba yadda za a yi ka zauna tare da shi na tsawon mintuna 15 ba ka mance da duk damuwowin ka ba, domin mutum ne mai matuqar hikima da raha, duk inda ka gan shi a cikin jama’a muddin ba lokacin juyayi ba ne, to za ka ga annuri da alamar fara’a a fuskar duk na tare da shi, domin tabbataccen abu ne Shaikh (H) zai sanya nishadi da farin ciki ga kowa ta hanyar raha mai cike da ilimantarwa da hikima.

Shaikh Zakzaky (H) mutum ne mai sauqin kai matuqa, wani Fasto da ya tava kawo masa ziyara gida, bayan sun daxe suna tattaunawa cikin raha da nishaxi, sai ya ce; Gaskiya Malam yadda muke hangenka daga nesa ba haka kake ba, mu ba mu xauka kana da sauqin kai haka ba, da a musulmin qasar nan na tsane ka fiye da kowa, amma yanzu na ji ina son ka fiye da kowa!”.


Shi kuwa Fasto Meter Peller na cocin Abuja, cewa Kiristoci ‘yan uwansa ya yi; “Kiran da zan yi ga al’umma da sauran Fastoci shi ne, ya kamata kowa ya buxe qofa ga waxannan jama’a (‘yan Shi’a almajiran Shaikh Zakzaky) don a fahimci juna, abin da ke tsakaninmu shi ne rashin fahimta, duk wanda ya nazarci kiran Malam (Zakzaky) to ba zai tava muzanta shi ba, dole ne ya yarda da kiran Malam! Wasu za su ji kamar ina siyasa ne ko wani abu mai kama da haka, amma (na tabbata) idan har suka samu ganawa da Malam, to lallai su ma sai sun zama ‘ya’yan Malam kamar yadda na zama!” (Jaridar ALMIZAN, bugu na 1256, shafi na 08).


Marubucin littafin “Malam, Malam Ne” ya labarta cewa; “Wani xan jarida, bayan saduwarsu da Malam ya ce; “(Wannan) ko cutar da quda ba zai iya ba” (He can hardly wound a fly)” (Malam, Malam Ne, shafi na 15). Wannan xan jarida ya ga sauqin kan Shaikh (H) ne da zurfin ilimi da fikirarsa.


WASIYYARSA :


Bisa al’ada akan ambaci Wasiyyar mutum ne bayan ya bar duniya, to amma babu laifi ga ambatar Wasiyyar mutumin da ke raye a duniya ma, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi buxaxxiyar Wasiyya aqalla guda biyu.

Buxaxxiyar Wasiyyarsa ta farko ta faru ne a watan Ramadan na shekarar 1430 (2010), lokacin da rahoton sirri ya zo masa cewa an gama duk wani shiri na halaka shi a wannan dare da zai shigo, har ma ya samu kwafin takardar “BluePrint” da shugaban qasa Umaru Musa Yar’aduwa ya sawa hannu na zartar da “Operation” xin a wannan dare.

Shaikh Zakzaky (H) ya yi Wasiyya ga vangarori uku na al’umma, ya yi Wasiyyar gargaxi ga azzalumai, ya yi Wasiyyar juriya ga almajiransa, ya yi Wasiyyar farkawa ga al’ummar musulmi, sa’annan a qarshe ya yi albishir ga almajiransa, ya ce; “Ba zan qarqare maganar nan ba sai na yi muku albishir, ko an qi ko an so addinin Allah zai tabbata! Ba yadda za a yi a ce wai bakin bindiga ko bom zai tarwatsa Da’awa zuwa ga Allah!”


Wasiyya ta biyu ta Shaikh Zakzaky (H) ita ce wacce ya yi wa ‘ya’yansa uku da suka rage a duniya, wato Sayyid Muhammad, Sayyida Nusaiba da Sayyida Suhaila, a ranar da sojoji suka kai hari gidansa, suka kashe kusan mutum dubu daga almajiransa, kuma suka kashe ‘ya’yansa maza uku, da babbar Yayarsa, suka harbi matarsa, shi ma suka yi masa ruwan harsashi, da yake bai xauka zai rayu ba, ya yi kevantacciyar Wasiyya ga ‘yarsa Sayyida Suhaila wacce yake tare da ita a lokacin.


Ta ce, daga cikin Wasiyyarsa gareni ya ce; “In kula da Sallah, sannan mu xau fansar abin da aka yi mana, kar mu qyale abin da aka yi mana ya tafi (a banza), kar mu yi shiru akan abin da aka yi mana. Sannan in yi haquri, in kalli rayuwar Sayyida Zainab (SA), in yi haquri irin nata, in yi rayuwa irin yadda ta rayu. Ya yi batun komawa makaranta, yana wannan halin ya riqa qarfafamu ni da Sajida akan muhimmancin ci gaba da karatunmu, ya ce in mun rayu mu tabbata mun koma makaranta, kar mu ce ba za mu koma ba, kar mu tsayar da komai namu dan abin da ya faru, amma kar mu qyale abin ya tafi a haka nan (siddan)” (Jaridar Al-Mizan, bugu na 1240).


Jumlatan a waxannan Wasiyyoyi na Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) shiryar da al’umma ne a cikinsu, za mu ga yadda ya yi Wasici da kula da Sallah, da dagewa da neman ilimi, da rayuwa tare da ruhin gwagwarmaya da zaluncin azzalumai.

✳✳✳ ✴✴✴ ✳✳✳

BABI NA UKU

ALAQAR SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY (H) DA YAWAN IBADA

IBADARSA :


Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) bawan Allah ne mai tsananin ibada, mutum ne da duk wanda ya san shi ya shaide shi da yawan ibada musamman salloli da azumomi da Azkar da yawan zuwa aikin hajji da umrah (kafin kafircin duniya ya sa shi a tarko). Yakan ce, awa 24 na yini da kwana sun yi masa kaxan, da da yiwuwar a qara da zai so haka, ya ce “Duk duniya ba abin da ya kai Sallar dare daxi, da azzalumai sun san daxin da muminai suke ji (a Tahajjud), da sun ce ba su yarda (a riqa yi) ba!” (Malam, Malam Ne, shafi na 07). Bari mu ambaci ‘yan misalai na yawan ibadarsa a fagen Sallah, Azumi, Hajji da sauransu.


SALLOLINSA :


A fagen sallolin nafilfili Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) tun yana qarami ya lizimci yin “Nawafilil Yaumiyyah” wato nafilolin da ake yi tare da kowace sallar farilla kafinta ko bayanta. Wato duk wanda ya san Shaikh Zakzaky (H), ya san shi da yin Nafilfilin dare (Tahajjud) raka’a 13, Nafila raka’a 8 kafin Azahar, raka’a 8 kafin La’asar, raka’a 4 bayan Magriba, raka’ar Wateera bayan Isha’i, in an haxa da raka’o’i 17 na sallolin farilla guda biyar, zai zama kenan a kullum Shaikh (H) yana yin Sallah Raka’a 51 a qalla.

Wannan banda kevantattun Salloli na kowane dare da na kowane yini da yake yi, kuma banda raka’a biyun da yake wa iyayensa, da raka’a biyu ga ‘ya’yansa, da raka’a biyu hadiyya ga shahidai, wannan a kowane dare ne, kuma banda salloli na musamman a ranar Juma’a da ranakun Idodi da sauransu. Kenan, a kowane wata Shaikh Zakzaky (H) dubban raka’o’i yake yi na sallar Nafila.

Sannan yana yin kevantattun nafilfili na dararen watanni uku a jere (Rajab, Sha’aban, da Ramadan) kamar yadda aka ruwaito su a littattafan ibada, sannan yana yin kevantattun salloli na darare na musamman a kowane wata.

Lokacin da ya saba tashi don yin sallar Tahajjud shi ne qarfe 2 na dare, wannan shi ne “Normal Time” xinsa a kullum, xaya daga cikin manyan almajiransa yana cewa; “Ta vangaren Mujahada kuwa, wannan kam ko yau daren nan ko gobe, Malam qarfe biyu na dare ya tashi, kuma ba zai kwanta ba har sai bayan rana ta fito, ni ban san iyakar shekarun da ya xauka yana yin wannan ba” (Malam Zakzaky, Rayuwarsa da Karamominsa, shafi na 08).

Amma a darare masu falala da alfarma ta musamman (kamar daren Juma’a, dararen haihuwar Ma’asumai (AS), dararen Mab’ath, Dahwil-Ardh, Nisfu-Sha’aban, Ghadeer, da kusan gaba xayan dararen watan Ramadan), ba ya ma bacci kwata-kwata a cikinsu. (Tasarrufi daga Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 07).

Marubucin littafin ‘Malam, Malam Ne’ yana cewa; “Yana da yawan Sallah, musamman da dare, kai barcinsa in ma yana yi, to fa kaxan ne, sau da yawa za ka ji yana cewa; “Rabo na da barci tun kwana kaza”, ya ambaci wasu kwanaki” (Malam, Malam Ne, shafi na 08).

Shaikh Zakzaky (H) yana da wata alaqa ta musamman da Sallah, domin a rayuwarsa ba abin da yake son yi kamar Sallah, na tava ji a wata ziyara da aka kai masa yana cewa; “Da za a tambayeni, me ka fi so? Zan ce Sallah! Da kuma za a tambaye ni, me ka fi jin daxinsa, zan ce Sallah!” wannan da kunne na na ji Shaikh (H) yana faxin haka. Marubucin littafin ‘Malam, Malam Ne’ yana cewa; “Akwai wani mutumin Iran da ya ga Malam Zakzaky (H) yana Sallah, ya ce; “Wannan yana Sallah irin ta Annabawa da Waliyyan Allah” daga nan suka shaqu da Malam” (Malam, Malam Ne, shafi na 08).

Za ka tabbatar da alaqar Shaikh Zakzaky (H) da Sallah in ka karanta labarin waqi’ar Maulud ta 2015, cewa, duk ruwan wuta da sojojin Nijeriya ke yi suna kashe almajiransa (a lokacin da suke qoqarin isa gare shi don kashe shi), shi ba abin da yake yi a falonsa sai Sallah. ‘Yarsa Sayyida Suhaila tana cewa; “Daga lokaci zuwa lokaci ana sanar da mu abubuwan da ke faruwa, mu kuma sai mu shiga mu sanar da Abbah (Shaikh Zakzaky) haqiqanin halin da ake ciki, da yawan lokaci in na shiga sai in tarar Abbah yana Sallah, sai in sanar da Ummah akan in ya yi sallama ta faxa masa” (Al-Mizan, bugu na 1240).


AZUMINSA :


A fagen Azumi, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya ginu akan lizimtar Azumin Litinin da Alhamis na kowane mako, (tun daga watan Shawwal zuwa qarshen Jimada-Thani), kenan yana yin Azumi 77 na waxannan raneku. Sannan yana azumin kwanaki tara na farkon watan Zulhajji, kuma yana yin azumin baki xayan watanni uku a jere, wato Rajab, Sha’aban da Ramadan, kenan yana yin azumin kwana 90 a jere.


Shaheed Hafizu Dauda (xaya daga cikin masu rakiya ga Shaikh Zakzaky), ya faxi cewa, “A bisa al’ada, in Shaikh (H) zai gabatar da Muhadhara (jawabi) yakan zo da ruwan shansa, in ba mu gan shi da ruwa ba, to mun san a ranar yana azumi. To, kuma mun lura, daga ranar xaya ga Muharram ba ya zuwa wurin zaman makokin Ashura da ruwa har sai ranar Arba’een (20 ga Safar) muke ganin ya zo da ruwan sha a tare da shi”. Wato yakan yi azumin watan Muharram baki xaya (in banda ranar Ashura), da kuma kwanaki 20 na Safar, jimilla yakan yi azumin kwana 49 kenan a jere.


Sannan yana yin Azumi na dukkan ranakun haihuwar Ma’asumai 14 (AS), yana kuma azumtar muhimman ranakun idodi na shekara, irinsu ranar Mubahala, ranar Ghadeer, ranar Mab’ath, ranar shinfixa qasa, ranar Nuzuri da sauransu. Jumlatan, a kowane kwanaki 360 da ke cikin shekara, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana azumtar tsakanin kwanaki 230 zuwa 260 a cikinsu. Kenan, in dai Shaikh Zakzaky (H) yana zaune a gida ba tare da tafiya karatu ba, yana azumi aqalla na sama da wata takwas a cikin watanni 12 na shekara.


Qanin Shaikh Zakzaky (H) wato Malam Badamasi Yaqubu yana cewa; “Na san Malam (tun) sama da shekaru 40 barcinsa qanqani ne, kuma na san cewa tunda ya taso ya ga mahaifinmu yana yin azumin wata uku a jere, wato Rajab, Sha’aban, da Ramadan, (shi ma) tunda ya taso yake yi, kuma har yanzu Malam bai daina ba, tun kamar shekaru 40 da suka wuce yake yi, kuma har yanzu yana ci gaba da yi” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 64). A wani jawabi Malam Badamasi ya ce; Tun Shaikh Zakzaky (H) bai balaga ba yake azumin wata uku a jere.

Wani da suka yi zaman Fursuna tare da Shaikh Zakzaky (H), ya faxi cewa; Lokacin da suka yi zaman gidan kurkuku, Malam ya kwashe wata tara cur yana Azumi, kuma abinci kimantacce yake ci!” (Malam Zakzaky: Rayuwarsa da Karamominsa, shafi na 10).


KARATUN QUR’ANINSA :


A fagen karatun Alqur’ani za a iya cewa Shaikh Zakzaky (H) mutum ne na musamman, domin shi ba ya gajiya da karatun Alqur’ani, sai dai kawai sauran hidimomi su tilasta shi ya ajiye, uwargidansa Malama Zeenat tana cewa; “Na san a da (Shaikh) yana sauqe Alqur’ani ne cikin kwana bakwai (wato mako guda)” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 130).


Marubucin littafin “Tarihin Harkar Musulunci” yana cewa; “Sayyid (H) ya kasance mai yawan karatun Alqur’ani, akwai ma lokacin da yake cewa, lokacin da yake zaune a kurkuku, yakan so ya sauqe Alqur’ani a qasa da kwana uku, amma tunda Sunnah shi ne qarancin sauqa kwana uku ne, to yakan tsaya akan hakan” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 26).


Idan muka nazarci wannan magana ta Shaikh Zakzaky (H) za mu ga zurfin xanfaruwarsa da karatun Alqur’ani mai girma, domin yana cewa ne, da ba don Sunnar Annabi (S) ta koyar da mu sauqe Alqur’ani cikin kwana uku zuwa sama ba, to da shi zai riqa sauqe Alqur’ani ne a qasa da kwana ukun, wato a kullum zai riqa sauqe Alqur’ani, amma tunda abin da Sunnah ta koyar kwana uku ne, to ya tsaya a haka!


ADDU’ARSA :


Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ma’abucin yawan addu’o’i ne, ya yi imani da addu’a fiye da komai a rayuwarsa, komai nasa sai ya yi addu’a kafin ya yi shi da bayan kammala shi. Yana bin dukkanin ladubba na karanta addu’a akan komai, kama daga addu’o’in Alwala, wanka, bacci, sanya sutura, zama, tashi, hawa abin hawa da komai na rayuwarsa.


Sa’annan ya lizimci yin addu’ar kowane dare, da addu’o’in ranakun mako, da addu’o’in kwanakin wata, da kuma addu’o’i na musamman a wasu lokuta na musamman, ko a wasu fitattun ranaku masu alfarma. Ya wallafa littafi ma na nafila raka’a dubu da addu’o’insu na musamman da ake yi a watan Ramadan, mai suna “Ad’iyaati Nawafilir Ramadan”.

Shaikh Zakzaky (H) ya yi fice wajan yawan karanta sashen addu’ar nan ta Iftitah daga daidai “Allahummah Innaa Narghabu Ilaika Fiy Daulatin Kareemah…” zuwa qarshen addu’ar, da kuma addu’ar Sabati da Istiqama ta “Yaa Allahu, Yaa Rahmanu, Yaa Muqallibal Quloub Thabbit Qalbiy Aladeenika”, da sauran addu’o’in tuba da na neman shiriya da taimako ga Allah, sannan ya lizimci yin addu’ar “Allahummah wa Qadshamalana Zaigul Fitan” a Alqunut xinsa na Sallah.

A fagen addu’o’in murqushe kaidin azzalumai da ganin bayansu kuwa, Shaikh Zakzaky (H) ya yi amanna da addu’ar “Al-Qamah”, da addu’ar “Sahmul-Lail” da addu’ar “Ahliththugour” da kuma addu’ar “Xairal Ababeel”. Sannan yana yawan karanta addu’o’in halaka azzalumai musamman na Imam Zainul Abidin (AS).

Shaikh Zakzaky (H) yana da yawan addu’o’in alkairi ga almajiransa, malamansa, iyayensa, al’ummar musulmi da kuma Shahidai, duk wanda ya san Shaikh ya san ba abin da yake roqon a yi masa sai Addu’a, saboda zurfin imaninsa da ita.

MUJAHADARSA :


Mujahada na nufin qoqari ko wani qarfin hali na musamman a fagen ibada. Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) mujahidi ne na musamman a fagen ibada, domin banda yawan ibadar da yake da, a gefe guda kuma yana da naci da dagewa a tsawaita ibadar, wato ba ya hanzari ko shaf-shaf a lokacin ibada, yakan tsawaita tsayuwar karatu, da Ruku’u, da Sujjada da sauransu a tahujjud xinsa.


Misali; Shaikh Zakzaky (H) ya shafe shekaru masu yawa yana aiwatar da dukkanin azumin watan Ramadan a Haramin Makka ko masallacin Annabi (S) da ke Madina, wato duk shekara yakan tafi Umrah tun a cikin watan Sha’aban, ba ya dawowa sai bayan Sallah (Idil-Fitr), yakan shafe gaba xayan watan Ramadan ne a cikin masallacin Harami, ba abin da yake yi sai ibada.


Wani mutum ya labarta yadda ya ga ibadar Shaikh Zakzaky (H) a masallacin Annabi (S) dake Madina. Akwai wani ginshiqi a cikin Raudha na masallacin Madina da ake qira ginshiqin Abu-Lubaba, anan Shaikh Zakzaky ke zama ya yi ta ibada, lokacin da mutumin ya ga Shaikh a wurin, sai ya yi ta zuwa sawu-sawu dan yana so ya samu damar yin magana da shi, amma duk sa’adda ya je wurin sai ya tarar yana ibada, hatta lokacin tsayawa cin abinci ma bai da shi, sai dai ya xan ci Dabino ya sha madarar gwangwani ko xan wani abu marar nauyi, amma ba ya fita waje don neman abinci.


Mutumin ya ce; “Wallahi duk sadda na je sai in iske shi yana Ruku’u, ko ya yi Sujjada, ko yana karatun Alqur’ani, sam ba ya zama haka nan (shiru), akwai ranar da na ga ya yi Sujjada da tsakiyar dare, har aka fara qiran sallar Asubahi bai xago ba, har na yi tunanin in je in qwanqwasawa Askar su zo su xauke shi ko ya rasu ne, (na yunqura zan je) sai na ga ya taso ya zauna ya maida nunfashi, a lokacin ba dan tsoron Askarawa ba da na ce “Labbaika ya Al-Zakzaky!” (Malam Zakzaky, Rayuwarsa da Karamominsa, shafi na 09).


Wani xan uwa daga cikin almajiran Shaikh Zakzaky (H) ya rubuta labarin mujahadar Shaikh xin kamar haka; “Na daxe ina samun matsaloli na rashin fahimta tsakani na da Babana, lamarin bai yi sauqi ba sai da wata rana wani abokin Baban nawa ya dawo daga aikin Umrah, suna zaune suna hira sai ga ni na zo wucewa, sai na ji yana faxa masa cewa; “Kai Alhaji, a wannan shekarar na ga shugaban ‘yan Shi’a (Shaikh Zakzaky) a Umrah, yana ibada kai ka ce Mala’ikan mutuwa ke jiransa, yana ibada ba ji ba gani, da ka gan shi sai ka ji so da qaunarsa ta shigar maka rai” ya ci gaba da ba Babana labarin cewa “Larabawa sai zuwa suke zunxensa, ana faxin ga wani baqin fata yana ibada ganga-ganga, da wata irin baiwa wacce samunta sai a kundayen tarihi” sai na ji Babana ya yi shiru, daga lokacin ya fara canzawa, yana saurare na da hujjojina” (Wakilin Manzo (S) a Doron Qasa, juz’i na xaya shafi na 26-27).


Daga cikin Mujahadar Shaikh Zakzaky (H) akwai cewa, shi ba ya umartar wani da yin wani aiki na ibada har sai wannan aikin ya zamo jiki a wurinsa. Misali; a lokacin da ya fara yi wa almajiransa magana akan falalar yin Sallah Raka’a xari a wasu darare masu alfarma, irinsu daren Nisfu Sha’aban da dararen “Layaliyal Qadari” da sauransu, to shi ya fi shekara goma yana yi. Haka nan, sai da ya shafe sama da shekara goma yana yin sallar nafilar nan mai raka’a Dubu ta tsakanin Magriba da Isha’i a watan Ramadan, kafin ya sanar da ‘yan uwa muhimmancin yin wannan Sallar, har ma ya wallafa xan qaramin littafi na yadda ake yin sallar da addu’o’inta.


Sannan tarihi ya nuna cewa shi ne mutumin da ya raya I’itikafi a aikace a qasar nan, kafin tasowarsa ana karanta batun I’itikafi ne kawai a littattafan fiqihu, amma ba a san wani mutum na shiga I’itikafi ba. Kenan, a sama da qarni guda da ya gabata Shaikh Zakzaky ne ya fara shiga masallaci ya yi I’itikafi tun yana yaro xan shekaru 15, daga nan sannu a hankali yin I’itikafi ya bazu a cikin al’umma, yanzu yin I’itikafi ya zama jiki a wurin dukkan vangarorin musulmin Nijeriya.


Yayar Shaikh Zakzaky Shaheeda Fatimah Yakubu (Goggon Qaura) ta faxi cewa; Tun yana yaro yake shiga masallaci ya yi I’itikafi, tun 20 ga watan (Ramadan) sai Sallah yake fitowa. Ni dai ban san wani da yake shiga I’itikafi ba a lokacin sai shi” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 71).

✳✳✳ ✴✴✴ ✳✳✳

BABI NA HUDU

WASU SASSA NA RAYUWAR SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY (H)

TAFIYE-TAFIYENSA :


Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi tafiye-tafiye zuwa qasashe masu yawa a sassa da dama na duniya, kusan ma ba wani sashe na duniya da bai je ba, kama daga Asiya, Turai, da qasahen Afirka. Misali, a yankin Asiya ya je qasashe kamar su; Iran, Iraqi, Saudi Arabiyya, Dubai, Lebanon, Malesiya da sauransu. A qasashen Afirka kuwa ya je Sudan, Ghana, Saliyo, Mali, Habasha, Nijar, Kenya, Afirka ta Kudu, Libiya da sauransu. Sannan ya je manyan qasashen duniya masu tinqaho irinsu Birtaniya, Amurka, Rasha, Faransa da sauransu. Dukkanin waxannan tafiye-tafiye ya yi su ne ta hanyar gayyata bisa dalilai na addini, ko halartar tarurrukan qarawa juna ilimi.


“Haka nan in muka dawo nan cikin gida za mu ga cewa Sayyid Zakzaky (H) ya je birane da qauyuka masu yawa a cikin qasar nan don isar da wannan Da’awa da yake yi, kai mutum ma zai iya dukan qirji ya ce a jihohin qasar nan musamman ma na arewawacin qasar, to, ba jihar da bai je domin isar da wannan saqo na Allah Ta’ala ba” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 23).


ALAQARSA DA AL’UMMAH :


MUSULMI : Abu ne sananne ga kowa cewa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya fi kowane malami a Nijeriya kyakkyawar alaqa da sauran musulmin da ba fahimtarsu xaya ba, domin ko kaxan ba ya qyamar musulmi na kowace Mazhaba ko Aqida, hasali ma ya fi kowa jin zafi bisa rashin jituwar da ke tsakanin qungiyoyin musulmi. Kullum a cikin sa’ayi na haxa kan musulmi yake, damuwarsa ita ce, aqalla musulmi su yarda su dena aibata juna da sukan juna da kafirta junansu. Daga cikin qoqarin Shaikh Zakzaky (H) na haxa kan musulmi ya sunnantawa kansa da almajiransa ziyarar Malamai na qungiyoyin musulmi daban-daban, daga lokaci zuwa lokaci Shaikh (H) yakan tashi takanas ya je gidajen manyan malamai ya ziyarce su don neman kusanci

1 Comments On SHAIKH ZAKZAKY IKON ALLAH
avatar
shuraihu-usman-1

1 year ago

Reply

sss

Please Login or Register in order to submit comment