Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da gidan talabijin xin qasar Indiya ‘MAULA-TV’ ya yi a kansa a shekarar 2015.

Ya ce “Asalin iyayenmu sun fito ne daga Magrib (Morocco kenan ta wancan lokacin)…. Sun tashi daga sassa zuwa sassa har suka zauna a Mali, Malin da ba Malin yanzu ba. Ana cewa suna daga cikin Sulala xin Imam Hasanil-Mujtaba (AS), wanda suka zauni nan qasar Magrib tukuna suka gangaro suka zauni Mali, sannan suka gangaro suka zo nan (Nijeriya)”.

Tun kafin Shaikh (H) ya bayyana shariftakarsa a fili, an samu wasu masana da suka sha cewa shi jinin Manzon Allah (S) ne, sai dai Shaikh Zakzaky (H) bai shelanta Shariftakarsa ba sai a wajajen shekarar 2004, bayan ya yi tafiya takanas zuwa qasar Mali don sada zumunci ga danginsa da kuma qarasa bincike akan nasabarsa mai alfarma.

A ranar da Shaikh Zakzaky (H) ke ayyana siyada ko shariftakarsa a wajan wani taron Maulidin Sayyida Zahra (SA) da ‘yan uwa mata suka shirya a Fudiyya Islamic Center (F.I.C Zaria), ya karanto ruwaya da ke cewa; “Allah ya la’ani wanda yake shi tsatson Annabi (S) ne amma ya voye nasabarsa, sannan ya tsinewa wanda ya nasabta kansa ga tsatsontaka da Manzon Allah (S) alhali qarya yake yi”. A fakaice, Shaikh (H) ya nuna cewa lalura ce ta sa zai ayyana Shariftakarsa ba don alfahari ko neman xaukaka ba.

Tattare da haka, Shaikh (H) ya nuna cewa ba zai sa baqin Rawani ba, saboda a al’adar mutanenmu (Hausawa), baqin Rawani bai da kima, domin bayin Sarakunan gargajiya ne ke sanya shi, dan haka mu anan ba zai dace jikan Annabi (S) ya sanya baqin Rawani ba, maimakon haka, sai Shaikh (H) ya ce zai riqa anfani ne da “Koren Qyalle” na ratawa a wuya, wanda zai zama shi ne alami na Siyadar jikokin Manzon Allah (S) a wannan qasa tamu.

Wannan shelanta Shariftaka ta Shaikh Zakzaky (H) ta vuvvugo da abubuwa da dama na raya al’amarin nasaba ga Manzon Allah (S), da bada kima ta musamman ga jikokin Annabi (S) a wannan al’umma tamu.

Istibsarinsa :

Duk da cewa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) tsatson Manzon Allah (S) ne, to amma yanayi na Biy’a (Inviroment) ya sa an haife shi a cikin Sunni, kuma hatta karatuttukan addini da ya taso da su na Mazhabar Malikiyya ne ta Ahlis-Sunnah.

Babu tabbataccen batu game da takameme lokacin da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi riqo da Mazhabar Ahlul-Bait (AS), to amma ta bayyana ga mutane cewa Shaikh yana bin tafarkin Ahlul-Bait (AS) ne a shekarar 1980, a lokacin yana da shekaru 27 da haihuwa. Almajiransa (wanda kusan baki xayansu Ahlis-Sunnah ne) sun soma gunaguni game da yadda suka ga Shaikh xin ya soma yin wasu abubuwa sabbi da ba su sani ba a cikin Alwala da Sallarsa a wancan lokacin.

Shaikh Zakzaky (H) da kansa ya tava bada labarin wannan rashin fahimta da sashen almajiransa suka nuna a wancan lokaci, wanda hakan ke tabbatar da cewa ya fara fitowa fili yana aikata koyarwar Ja’afariyya a ibadarsa ne tun a 1980, ya ce; “Na san tun 1980 lokacin da aka yi “Funtua Declaration” akwai waxanda suka zo suka same ni, cewa sun ga na yi Alwala amma na shafa qafa ne, sai na qyale, sai wani ya ce musu; ai shi Shi’a ne, shi ya sa yake shafa a qafa, amma ni ban ce musu komai ba, (sai) wani ya ce ya ga ina Qunuti ina xaga hannu, shi ma na qyale ban ce masa komai ba, wani kuma ya ce ya ji ni ina Tasbihi a Ruku’u a bayyane, shi ma sai na qyale, duk dai na qi in amsa masu.

“Wani lokaci kuma mun tafi Sakkwato a dai cikin shekarar 1980, sai nai Sallar Azuhur da La’asar, sai na karanta “Bismillahir-Rahmanir-Raheem” a bayyane, wani sai ya tambaye ni, ya ji a cikin Sallah na yi Bisimilla a bayyane, sai na ce masa e, Manzon Allah (S) ya kasance yana yin haka, saboda su mutane akan wannan, sai su yi faxa, ko kuma su ce addininka daban ne, saboda haka ni ban so tun farko mu fitinar da mutane (ba)” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 154).

A wani zama na Khass da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi da wakilan ‘yan uwa na manyan Da’irori a wancan lokaci, ya bayyana musu cewa; “Ana jira in ce ni Shi’a ne domin a tarwatse, to, ni Shi’a ne! Tun da can ni Shi’a nike akai, a Shi’ar ka sanni, in ba ka sanni a haka ba to ba ka da basira! Saboda haka a Shi’a nike, kuma Insha Allah a Shi’a zan mutu, kuma ina fata Allah ya tasheni da Shi’a a ranar Qiyama, ya kai ni mokomar Shi’a!” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 155).

Kenan, a bisa wannan jawabi, duk wanda ya fahimci Da’awar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), to ya shigo ne ya samu Shaikh (H) a bisa aqidar Shi’a da Wila’a ga Ahlul-Bait (AS) da kuma biyayya ga koyarwarsu, amma saboda maslaha ta Biy’ar da yake rayuwa a ciki, da kuma tausayin kar mutane su fitinu su nesanci tafarkin tsiransu, ya sa Shaikh (H) bai bayyana wannan aqida da Mazhaba ta Ahlul-Bait (AS) a fili ba, ya bar abin ga kansa kawai, sai da yanayi ya kyautata sannan ya shelanta tare da ayyana tafarkin da yake riqo da shi a fili, wanda sakamakon hakan ya sa miliyoyin almajiransa suka rungumi aqidar ba tare da qyama ba. Wannan ya sa Shaikh Zakzaky (H) ya zama mutumin da ya fi kowa nasarar canza akalar aqidar miliyoyin mutane daga Sunnah zuwa Shi’a a tarihin Musulunci baki xaya!

Uwargidansa :

Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana da mace xaya, wannan kuwa ita ce Malama Zeenatuddin Ibraheem, ita ce mahaifiyar duk ‘ya’yansa, wato daga gareta zuriyarsa ta samu. An haifi Malama Zeenatuddin ne ranar 14 ga watan Ogusta na shekarar 1961, a unguwar Sabon Gari da ke cikin garin Zariya. Sunan mahaifinta Malam Ibrahim, sunan mahaifiyarta Malama Maryam, su huxu ne a wajan mahaifiyarsu kuma dukkaninsu mata, Nafisa Ibraheem, Maryam Ibraheem, Zeenatuddeen Ibraheem da Khadija Ibraheem.

Malama Zeenatu ta fara karatun firamare ne a wata firamare ta Mishon da ke Sabon Gari Zariya, daga baya ta koma Firamaren Jafaru, wato St, George Primary School Zaria, daga 1967 zuwa 1973. Daga nan ta tafi “Commercial College, Zaria” a shekarar 1977, ta kammala a 1979, sai ta tafi CAST Katsina, ta shekara biyu a can, daga nan sai ta shiga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a shekarar 1981 inda take karanta fannin aikin Banki, amma ba ta samu damar qarasawa ba sakamakon korarsu da makarantar ta yi saboda harkokin addini a sekarar 1982.

Daga nan Malama Zeenatu ta tafi karatu a wata “Hauza Ilmiyyah” da ke qasar Iran, daga shekarar 1982 zuwa 1984. Malama Zeenatu baiwar Allah ce ma’abuciyar hidima ga addini da tsayuwa akan hadafi, mace ce haziqa mai tsananin riqo ga karantarwar addini da fikirar Harka Islamiyya. An shaideta da yawan ibada da kishin addini da tsananin tausayawa mata.

Aurensa :

Malama Zeenatuddeen Ibraheem ta fara sanin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne a shekarar 1977 lokacin da take karatu a makarantar kwalejin koyon sana’o’i, “Commercial Collage Zaria”, a lokacin Shaikh Zakzaky (H) yana xalibta a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, kuma kasancewar yana xaya daga cikin jagororin qungiyar xalibai musulmi MSS (wato Officials), kuma yana xaya daga cikin masu gabatar da jawabai da wa’azozi na qungiyar, a irin wannan jawabai da yake gabatarwa ne Malama Zeenatu ta san shi.

Amma Shaikh Zakzaky (H) bai san Malama Zeenatu ba sai a shekarar 1979, lokacin da aka je taron “Islamic Vocation Course” (IVC) na qungiyar MSS a Legos, a nan ne ya fara ganinta, saboda ta zo taron ne daga Zariya, amma ba wata mu’amala da ta shiga tsakaninsu a lokacin. Mu’amala ta fara shiga tsakaninsu ne a birnin Bauchi a wannan shekarar ta 1979, lokacin da aka zo wani taron IVC na musamman, Malama Zeenat ita ce kaxai mace da ta zo wannan taro daga wata jaha, kasancewar daga taron IVC na Legos aka wuce Bauchi kai tsaye, kuma xalibai da yawa ba su san da wannan shiri na wucewa Bauchi daga Lagos ba.

Dan haka da Malama Zeenat ta wuce Bauchi daga Legos sai kuxin mota da na guzurinta ya qare a Bauchi, da aka kammala taron, sai ta nemi ganin Shaikh Zakzaky a keve a matsayinsa na xan garinsu (Zariya), ta koka masa qarewar kuxinta, ta nemi ya bata aron kuxin mota, in sun koma Zariya za ta biya shi, sai Shaikh ya bata kuxin da zai wadaceta komawa Zariya da cin abinci da sauran buqatu. Bayan sun koma Zariya da ta samu kuxin ta mayar masa sai ya qi karva, ya ce tun asali kyauta ya bata ba bashi ba, wannan ce mu’amala ta farko da ta shiga tsakaninsu.

Kasancewar Malama Zeenat haziqa ce mai basira da qumaji, sai aka riqa gayyatarta taron kevantattun membobin MSS na musamman waxanda Shaikh Zakzaky (H) yake karatun gina fikira (Ideology) da tarbiyyar addini da su. Wannan ganawa ta kevantattu da ake kira EED ana yin ta ne a duk taron IVC da aka je, kuma Shaikh Zakzaky ya fara gayyatar Malama Zeenatu zuwa wannan taro na EED ne a IVC na Wudil cikin shekarar 1979, sai kuma na Funtuwa (wanda Shaikh xin ya shelanta Bara’arsa ga tsarin kafirci) duk dai a shekarar 1979/1980.

Bayan tafiya ta yi nisa ne, Shaikh Zakzaky ya bayyanawa Malama Zeenatu cewa yana sonta da aure, wannan ya faru ne a shekarar 1980, to amma sai Malamar ta nuna cewa ba ta fara tunanin yin aure yanzu ba tukunna, sai Malam ya haqura da batun. Amma bayan wani lokaci mai tsawo, sai ta yi ta ganin isharori ta hanyar mafarki na dacewar aurenta da shi, wannan ya sa ta canza shawara, ta niqi gari ita da babbar qawarta a lokacin (Fatimah Yunus), suka je har Kurkukun Enugu (inda Shaikh xin ke tsare a lokacin) a 1981, ta nemi afuwarsa kuma ta nuna amincewarta ga aurensa.

An xaura auren Shaikh Zakzaky (H) da Malama Zeenatu ne a watan July na shekarar 1984, wanda ya yi daidai da watan Shauwal 1404 hijira, bayan dawowarta daga karatu na tsawon shekaru biyu a qasar Iran.

Zuriyarsa :

Allah Ta’ala ya yi baiwa ga Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ta hanyar azurta shi da zuriya mai albarka, domin ya haifi ‘ya’ya har guda tara (9), bakwai daga ciki maza ne, yayin da biyu kuma mata ne. Sai dai azzaluman hukumomin Nijeriya ba su bar mafi yawan ‘ya’yan nasa sun yi rayuwa mai tsawo a duniya ba, domin sun kashe shida daga cikin ‘ya’yansa maza guda bakwai a cikin shekara xaya, kenan, a cikin ‘ya’yansa guda 9, yanzu 3 suka rage, mata biyu da namiji xaya.

MUHAMMAD IBRAHEEM ZAKZAKY : Sayyid Muhammad shi ne babban xa wato xa na farko a wurin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). An haife shi ne a shekarar 1985 (a lokacin mahaifinsa yana tsare a kurkuku sakamakon kamun da shugaban qasa na lokacin Janar Buhari ya yi masa). Ya yi karatun Firamare da Sakandire a Nijeriya da qasar Ingila, kuma ya je qasar Iran inda ya karanta darasin “Fasahar Gine-gine” da ake kira “Architecture” a babbar Jimi’ar Tehran (wato University of Tehran) da ke birnin Tehran.

Sayyid Muhammad qwararre ne a yaren Turanci, Farisanci da Hausa. Mutum ne mai tsananin shiru da kawaici da rashin son hayaniya, yana da xabi’ar kauda kai ga abin da bai shafe shi ba, yana da kaifin basira da hangen nesa, kuma mutum ne mai taka tsantsan akan al’umuran rayuwa. Ya yi aure a watan Mayu na shekarar 2016, a lokacin mahaifinsa yana tsare a kurkuku sakamakon kamun da shugaban qasa Muhammadu Buhari ya sake yi masa a 2015.

NUSAIBA IBRAHEEM ZAKZAKY : An haifi Sayyida Nusaiba ne a ranar 21 ga watan Afirilu na shekarar 1987 bayan fitowar Shaikh Zakzaky daga gidan kurkuku, ita ce ‘ya mace ta farko ga Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), kuma ta biyu a jerin ‘ya’yansa. Ta yi karatun Firamare da Sakandire a Nijeriya, ta fara karatun Jami’a a qasar Malesiya, daga nan ta wuce Jami’ar qasa da qasa da ke birnin Dubai na haxaxxiyar daular Larabawa (United Arab Emerate). Sayyida Nusaiba haziqa ce mai basira da hangen nesa, an shaide ta da yawan haquri da kawaici.

AHMAD IBRAHEEM ZAKZAKY : Sayyid Ahmad shi ne xa na uku a jerin ‘ya’yan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). An haife shi ne ranar 15 ga watan Oktoba na shekarar 1990. Ya yi karatun Firamare da Sakandare a Nijeriya, daga nan ya tafi jami’ar Kimiyya da Fasaha ta “Xhenyang University of Technology” da ke birnin Zhenyang a qasar Chaina, inda yake karanta darasin fasahar sarrafa sinadarai, wato “Chemical Engineering”, yana shekarar qarshe ta kammala karatu a Jami’ar ya yi Shahada.

Sayyid Ahmad ya yi shahada ne ranar Juma’a 25 ga watan Yuli na shekarar 2014, wanda ya yi daidai da Juma’a 28 ga watan Ramadan na shekarar 1435 Hijra. Ya rayu a duniya ne tsawon shekaru 23 kacal, kuma ya yi shahada sakamakon kisan gillar da sojojin Nijeriya suka yi masa a lokacin Muzaharar Qudus ta nuna goyon baya ga Falasdinawa a birnin Zariya.

Sayyid Ahmad ne kwamanda na Mu’assasar Abul-Fadal Abbas. Haziqi ne mai kaifin qwaqwalwa da basira, yana kama da mahaifinsa sosai a yanayin halitta da hazaqar qwaqwalwa, da yanayin xabi’u. Mutum ne mai tsananin son qananan yara, an shaide shi da jarunta, yawan ibada, da hidima ga addini.

HAMEED IBRAHEEM ZAKZAKY : Sayyid Hameed shi ne xa na huxu a jerin ‘ya’yan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). An haife shi ne ranar 17 ga watan Janairu na shekarar 1992, ya yi karatun Firamare da Sakandare a Nijeriya, daga nan ya tafi Jami’ar “Zain University of Technology” da ke birnin Xain a qasar Chaina, inda yake karanta darasin qera jirgin sama wato “Aeronautical Engineering”, yana shekarar qarshe ta kammala jami’ar ya yi Shahada.

Sayyid Hameed ya yi shahada ne ranar Juma’a 25 ga watan Yuli na shekarar 2014, wanda ya yi daidai da Juma’a 28 ga watan Ramadan na shekarar 1435 Hijra, ya rayu a duniya tsawon shekaru 22 kacal, kuma ya yi shahada ne sakamakon kisan gillar da sojojin Nijeriya suka yi masa a lokacin Muzaharar Qudus ta nuna goyon baya ga Falasdinawa a birnin Zariya.

Sayyid Hameed haziqi ne xan baiwa irin wanxanda ake kira “Genius”. Kafin rasuwarsa an tabbatar da cewa zai iya qera jirgin sama saboda hazaqa. Mutum ne mai tsananin natsuwa da kawaici, ya fi sha’awar rayuwar shiru da kaxaici, yana da qarancin magana, kuma ba ya son hayaniya.

SUHAILA IBRAHEEM ZAKZAKY: Sayyida Suhaila ita ce ‘ya ta Biyar a jerin ‘ya’yan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), amma ta biyu a ‘ya’ya mata.

An haifi Sayyida Suhaila ne ranar 8 ga watan Agusta na shekarar 1993. Ta yi karatun Firamare da Sakandare a Nijeriya, ta fara karatu a Jami’ar “Usman Xan Fodiyo” da ke birnin Sakkwato a Nijeriya, amma daga baya sai ta tafi wata Jami’ar qasa da qasa “International University” da ke qasar Malesiya, inda ta karanta darasin “Halayyar xan Adam” wato “Sociology”. Sayyida Suhaila haziqa ce mai fasahar magana, an shaideta da kawaici, qwazo, da himma a fagen addini.

MAHMOUD IBRAHEEM ZAKZAKY : Sayyid Mahmoud shi ne xa na Shida a jerin ‘ya’yan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), a makarantarsu xalibai suna kiransa “Gentle Man”, a gida kuma jama’a suna masa laqabi da “Shehu” saboda natsuwarsa da sauqin kansa da riqo da addini. An haifi Sayyid Mahmud ne ranar 20 ga watan March na shekarar 1995. Ya yi karatun Firamare da Sakandire a Nijeriya, kafin ya yi Shahada yana aji uku a jami’ar “Al-Mustapha International University” da ke birnin Beirut na qasar Lebanon.

Sayyid Mahmud ya yi shahada ne ranar Juma’a 25 ga watan July na shekarar 2014, wanda ya yi daidai da Juma’a 28 ga watan Ramadan na shekarar 1435 Hijra. Ya rayu a duniya tsawon shekaru 19 kacal, kuma ya yi shahada ne sakamakon kisan gillar da sojojin Nijeriya suka yi masa a lokacin Muzaharar Qudus ta nuna goyon baya ga Falasdinawa a birnin Zariya.

Sayyid Mahmud mutum ne qwararre a fagen ilimin kwanfuta da sadarwar zamani, haziqi ne mai tawali’u da tsananin riqo da addini, ya fi sha’awar karatun addini fiye da na zamani. An shaide shi da sauqin kai da kyawun hali da kyawawan xabi’u da yawan ibada. An yi hasashen da ya rayu, da shi zai gaji Shaikh Zakzaky (H) a fagen ilimin addini mai zurfi.

HAMMAD IBRAHEEM ZAKZAKY : Sayyid Hammad shi ne xa na Bakwai a jerin ‘ya’yan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). An haife shi ne ranar 10 ga watan Disamba na shekarar 1997. Ya yi karatun Firamare da Sakandire a Nijeriya, kuma ya yi karatun addini a gaban mahaifinsa.

Ya yi shahada ne ranar Litinin 14 ga watan Disamba na shekarar 2015, wanda ya yi daidai da ranar uku ga watan Rabi’ul-Auwal na shekarar 1437. Ya rayu a duniya tsawon shekaru 18 kacal.

Kafin shahadarsa shi ne kwamandan rundunar qananan yara masu tasowa da ake kira “Kasshafa”. Ya yi shahada ne sakamakon kisan gillar da sojojin Nijeriya suka yi masa a gaban mahaifinsa a unguwar Gyallesu da ke cikin birnin Zariya. Haziqi ne mai kaifin qwaqwalwa da basira. An shaide shi da yawan ibada, iya mu’amala, da kula da qananan yara.

ALI HAIDAR IBRAHEEM ZAKZAKY : Sayyid Aliy-Haidar shi ne xa na Takwas a jerin ‘ya’yan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). An haife shi ranar 15 ga watan Satumba na shekarar 1999. Ya yi karatun Firamare da Sakandire a Nijeriya, kuma ya yi karatun addini a gaban mahaifinsa.

Sayyid Ali yana cikin waxanda waqi’ar Qudus ta 2014 ta rutsa da su, tare aka kama shi da ‘yan uwansa guda biyu aka tafi da su barikin soji aka yi ta azabtar da su, shi ne kaxai ya kuvuta da ransa a cikinsu bayan an yi masa harbi da dama tare da dagargaza qafarsa ta hagu, wanda ya jaza dole sai da aka fita da shi waje aka yi masa aiki.

Sayyid Aliy-Haidar ya yi shahada ranar Litinin 14 ga watan Disamba na shekarar 2015, wanda ya yi daidai da Litinin uku ga watan Rabi’ul-Auwal na shekarar 1437 Hijira. Ya rayu a duniya tsawon shekaru 16 kacal, kuma ya yi shahada ne sakamakon kisan gillar da sojojin Nijeriya suka yi masa a gaban mahaifinsa a unguwar Gyallesu da ke cikin birnin Zariya. Sayyid Aliy-Haidar haziqi ne mai kaifin qwaqwalwa da basira. An shaide shi da yawan ibada, son karatu, son wasannin motsa jiki, da sauqin kai a mu’amala.

HUMAID IBRAHEEM ZAKZAKY : Sayyid Humaid shi ne xa na Tara kuma xan auta a jerin ‘ya’yan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). An haife shi ranar 22 ga watan Yuni na shekarar 2001, kuma ya yi shahada ne ranar Litinin 14 ga watan Disamba na shekarar 2015, wanda ya yi daidai da Litinin uku ga watan Rabi’ul-Auwal na shekarar 1437 Hijira. Ya rayu a duniya tsawon shekaru 14 kacal, kuma ya yi shahada ne sakamakon kisan gillar da sojojin Nijeriya suka yi masa a gaban mahaifinsa a unguwar Gyallesu da ke cikin birnin Zariya.

Ya yi karatun Firamare da Sakandire a Nijeriya, sannan ya yi karatun addini a gaban mahaifinsa. Haziqi ne mai kaifin qwaqwalwa da basira, an shaide shi da jarunta da rashin tsoro, ga sakin fuska da girmama na gaba.

A taqaice, wannan ne tsokaci akan rayuwar ‘ya’yan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) guda tara, wanda shida daga ciki suka yi shahada, uku ne kacal ke raye, xaya namiji biyu mata. Muna roqon Allah ya wanzar da zuriyar Shaikh Zakzaky ta cikinsu, Ilahiy Ameen.

Fara Da’awarsa :

Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya fara wa’azi a bainar jama’a ne a wani babban taro da aka yi a makarantar “Provincial Arabic School” da ke unguwar Kwarbai a cikin birnin Zariya. Wannan taro an yi shi ne a watan Afrilu na shekarar 1972 don kafa qungiyar samarin Musulmi, kuma ya haxa manyan mutane ciki har da sarakunan gargajiya. Wannan shi ne wa’azi na farko da Shaikh Zakzaky ya fara yi a bainar jama’a, a lokacin yana da shekaru 19 kacal a duniya.

To, amma Da’awa ta fikirar Harka Islamiyyah, wato kiran mutane zuwa ga bin koyarwar addini da qauracewa tsarin jahiliyya, ya fara shi ne a shekarar 1977, wato tun bai fi shekara xaya a Jami’ar ABU ba, sai dai a lokacin yana Da’awa ta sirri ne ba tare da shelanta manufarsa a fili ba (Da’awa Sirriyya). Ya shafe shekaru uku a wannan mataki na Da’awa ta sirri (1977-1979), sa’annan daga baya ya shelanta manufar Da’awarsa a fili a farkon shekarar 1980 a Funtuwa.

Shaikh Zakzaky (H) ya shelanta Da’awarsa da manufarta a fili ne cikin watan Jimada-Ula na shekarar 1400 Hijira, wanda ya yi daidai da watan Yuli (?) na shekarar 1980. Ya shelanta wannan Da’awa ne a wani babban taro na qungiyar xalibai musulmi ta qasa “Muslim Students Society” (MSS) a garin Funtua. A jawabin ya shelanta miqa wila’arsa ga Allah da Manzo (S), tare da Bara’a ga duk tsarin da ya savawa nasu, ya kuma shelanta qyamarsa ga zalunci da azzalumai. Wannan bayyana Da’awa da ya yi ita ake kira “Shelar Funtuwa” wato “Funtua Declaration” a turance.

Bayan shelanta Da’awarsa a taron xalibai na Funtuwa, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi wa’azinsa na farko ga al’umma ne a wani gangamin wa’azi da aka yi a masallacin Kwarbai dake Zariya a cikin watan Rajab na shekarar 1400 Hijira (1980), wanda shi ne wa’azi na farko xauke da fikirar Harka Islamiyya da Sheikh Zakzaky (H) ya gabatar wa mutanen gari.

Bayan shelanta wannan qira nasa ya fuskanci tsangwama mai tarin yawa ta fuskoki da vangarori da dama, kama daga azabtarwa daga vangaren hukuma, da kuma matsin lamba daga dangi da makusantansa. A wani jawabinsa yana cewa; “Wani ma ya ce min “ba za ka koma Jami’a ka yi karatu ba!” (sai) na ce masa; to ai wannan aikin da kake so na yi akwai masu yi, amma wannan (Da’awa) da nake yi ba mai yi! Saboda haka gara wannan shi ma a tsaya a yi shi” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 18).

Dalilin Fara Da’awarsa :

Kowa zai so sanin yaya aka yi Shaikh Ibrahim Zakzaky (H) ya fara wannan Da’awa tasa, wato meye dalili, ko ya aka yi tunanin fara yin Da’awar ya zo masa?

Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya sha amsa wannan tambaya ga ‘yan jaridu, yakan ce, shi a farko bai tava tunanin zai zama mai Da’awa ko ya zama malamin addini ba, tunaninsa shi ne in ya gama karatunsa na boko zai zama ma’aikacin gwamnati ne ko malamin jami’a, domin rayuwar ma’aikatan gwamnati da ta malaman jami’a tana burge shi, rayuwa ce ta natsuwa wacce ba hayaniya a cikinta, kuma shi yana sha’awar rayuwa ta kaxaici da natsuwa, ba ya son a san shi ko ya zama wani fitaccen mutum, domin ba ya son hayaniya da xawainiyoyi da yawa.

To, ya aka yi tunanin Shaikh Zakzaky (H) ya canza daga zama ma’aikacin gwamnati ya koma malamin addini mai Da’awa da gwagwarmaya? Shaikh Zakzaky ya amsa tambayar kamar haka; “Ina iya cewa (zama mai Da’awa da na yi) qaddara ce ta Ubangiji da kuma ayyukan waxanda suke ganin za su ga bayana, su lalata ni, su hana ni magana….. Domin lokacin da na shiga jami’a, akwai qalubale da yawa da suke fuskantar Musulunci, akwai masu aqidar gurguzu a wancan lokacin, (yanzu babu su ya’alla a harabobin jami’a ne ko a ko’ina), a wancan lokacin suna caccakar duk wani abu da ya shafi Musulunci da shi kansa addini gaba xaya.

“To, sakamakon na taso da ilimin addinin musulunci, na san suna sukar Musulunci ne kan abin da bai da laifi, suna da aqidar cewa addini kamar qwaya ce mai bugarwa ga mutane, kuma da shi ake fakewa ana zaluntar jama’a, suna kawo misali da sarakunan da suke da mata barkatai da saxakoki, kamar wannan kawai Musulunci ya qunsa, sai muka ga bai kamata mu yi shiru kan irin wannan zarge-zarge ba, dan haka muka fara kare addini, ta haka wannan Da’awa ta fara, wato kare addini, kuma a lokaci guda da koyar da mutane haqiqanin manufofin addinin.

“(Domin) mun gano akwai ‘ya’yan musulmi da ba su san mene ne addinin Musulunci ba, wanda masu wannan farfaganda za su iya yaudararsu da waxannan aqidu, hasali ma da dama ko mafi rinjayen (masu aqidar Gurguzun) ‘ya’yan musulmi ne suka dawo suna zargin Musulunci da zaluntar xan adam, alhali a xaukacin tarihin xan adam ba wata aqida ko tunanin da ya tseratar da xan adam kamar Musulunci.

“Wani vangare da suka fi kwarmato akai shi ne batun mata, sun zargi Musulunci da tauye mata,

1 Comments On SHAIKH ZAKZAKY IKON ALLAH
avatar
shuraihu-usman-1

1 year ago

Reply

sss

Please Login or Register in order to submit comment