Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lura da mu, mu ba mu xauka wani ne muke faxa da shi ba, gaskiyar magana kenan, mu muna qira (Da’awa) ne, amma wasu ne suke faxa da mu… suna faxa da abin (da muke yi) ne” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 04 da 14).


Wannan ya nuna yadda zuciyar Shaikh Zakzaky (H) ke cike da hasken alkairi ga kowa, sam ba ya nufin kowa da sharri, hatta masu gaba da shi, da waxanda suka cutar da shi fatan alkairi yake masu, madalla da irin wannan zuciya ta bayin Allah na gari.


ADALCINSA :


Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) mutum ne mai adalci a komai nasa, sam bai da son zuciya ko fifita kai ko wani abu nasa, misali; A shekarar 1993 wasu sashen almajiransa sun juya masa baya suka yi masa tawaye saboda zargin cewa yana qoqarin Shi’antar da su da canza musu alqibla daga mabiya Sahabbai zuwa mabiya Ahlul-Bait (AS).


Bayan sun shelanta valle masa, sai suka lashi takobin sai sun wargaza wannan Da’awa tasa ta kowane hali, suka shiga yin wa’azozi unguwa-unguwa na cin zarafi da aibata Shaikh Zakzaky (H) da Da’awarsa. Da Shaikh (H) ya zo yin magana akansu, sai ya faxi manufofinsu da dalilansu na valle masa, a qarshe sai ya yi addu’a ya ce; “Ya Ubangijin Musa da Haruna! Idan abin da waxannan mutane suke akai, shi ne daidai, shi ya fi soyuwa a gareka, to ka wargaza nawa ka tabbatar da nasu, idan kuma abin da nake yi shi ya fi kusa da daidai, ya fi soyuwa a gareka, to ka wargaza nasu ka tabbatar da nawa!”. Idan mun lura a wannan addu’a ta Shaikh Zakzaky (H) akwai tsabar adalci da rashin son kai a cikinta.


Harwala-yau, a wata ganawa ta keve da ya yi da mawaqa a tsakiyar shekarar 2015, Shaikh Zakzaky (H) ya ce; “Ba mu ce wannan Da’awa tamu ita ce kaxai hanyar tsira ga mutum ba, shi ya sa ma ba mu kafirta mutane ba, amma abin da muke cewa shi ne, in za ka bar Harkar, to ka tabbata inda za ka je xin ya fi nan inda ka bari, abin da ka bari a nan za ka samu wanda ya fi shi a can inda ka je!”. Ba shakka a cikin wannan zance na Shaikh (H) akwai babban abin la’akari na adalci!


HAIBARSA :


Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) bawan Allah ne mai matuqar kwarjini da Haiba, wani mawaqi yana cewa, “Kwarjininsa wane Zaki!”. In kana magana da shi ba za ka iya kallon cikin idonsa ba saboda tsabar Haiba. Sau da yawa mutane kan kasa magana da shi in sun zo gabansa.

Ni kaina haka ta tava faruwa da ni, da ma na daxe ina jin ana cewa magana da Shaikh (H) sai an samu Sabati, domin kwarjininsa yana rikita mutane su mance muhimman bayanan da suka zo da su. To, wataran da za mu je ganawa da shi, sai na gama tsara abubuwan da zan faxa masa, na haddace abubuwan tsaf, sannan na yi ta addu’o’in samun Istiqama da rashin ruxewa, amma bayan mun isa falonsa, da ya zo ya zauna ya kalle ni ya ce bismilla, duk sai na manta abin da zan faxa, ina ta kame-kame, ba ya jin ma abin da nake faxa, Haiba da kwarjininsa duk sun lulluve ni!”.


Haka nan, wasu da suka je ganawa da Shaikh (H) kan wasu matsaloli, sai mai gabatar da batutuwan ya kasa gabatar da su yadda ya kamata, bayan sun fito sai wasu suka ce masa ya ba ka ambaci kaza da kaza ba? sai ya ce musu; “Hmnn, ba ku san magana da Shaikh (H) ta fi dutsen Uhudu nauyi ba ne? Ai Haibarsa tana rikitawa mutum lissafi”.


Wani xan uwa cikin kundin adana bayanansa (Diary), ya rubuta labarin yadda ya fara ganin Shaikh Zakzaky (H) a rayuwarsa, da irin Haiba da kwarjinin da ya kama shi. Ya ce; “Na daxe ina jin labarin wannan Malamin, amma ban tava ganinsa ba, sai na ce lallai ina so in gan shi tunda an ce anan cikin Zariya yake zaune… Da isata gidansa na tarar da wasu mutane (a falo suna zaune)… zuwa can sai Malam ya fito, ina ganinsa jikina ya xau rawa, na ji numfashina ya xauke, wani sanyi ya sauqa a zuciyata. Malam ya zauna ya kalle ni ya yi mani sallama, na amsa masa… tun daga wannan haxuwa ne na ji wani Ruhi na sanin waye ni ya shige ni, wata tsima ta neman ‘yanci ta shige ni, wani so ga Allah da sallamawa dokokinsa ta lulluve ni, na ji ba ni da buqatar in tuna baya!” (Wakilin Manzo a Doron Qasa, shafi na 24-26).


Wata rana wani Laccara na “Islamic Studies” ya shigo aji, ya yi karatu akan nazarin ingancin hadisin da ke cewa; Ubangiji na da wasu bayi waxanda da zaran an ambace su sai a girmama Allah (a ce ‘Allahu Akbar’)”. Laccara ya ce; Wasu Hadisai da bayanan Malamai sun tabbatar da cewa, sai “Waliyan Allah na qoli ne ke kai wa wannan matsayi, domin kuwa su Allah ne ke son su har ya mayar da lamarinsu da an ji sunansu ko an gan su sai a tuna Allah”. Sai Laccara ya tambayi xalibai, “A cikin malaman da kuka sani, wa ke da wannan matsayin?”

Sai wani xalibi ya ce “Allah gafarta Malam sai shugaban ‘yan Shi’a xin nan! Shi ne saboda sadaukarwarsa ga addini daga an faxi sunansa ba ka sanin lokacin da bakin ka zai girmama Allah”. Sai Laccara ya tambayi xalibin, “Ya sunansa?” xalibin ya ce “Sunansa Shaikh Ibraheem Zakzaky!” ai yana faxin haka sai baki xayan xaliban ajin suka xauka “Allahu Akbar!” daga ranar Laccara ya shiga nazarin rayuwar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) don sanin sirrinsa. (Tasarrufi daga littafin Wakilin Manzo (S), 01-27).


MARTANINSA :


Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) mutum ne Fasihi mai hikima da hangen nesa cikin maganganu da furucinsa, sam ba ya fusata a yayin da ya fahimci an yi abu ne dan a tunzura shi. Tarihin rayuwar Shaikh Zakzaky (H) cike take da suka da kai farmaki ga Da’awarsa da ra’ayoyinsa da aqidunsa daga Malaman hukuma da duk masu adawa da shi, amma abu mafi armashi shi ne irin raddi da martanin da yake mayar wa masu sukarsa daga lokaci zuwa lokaci, domin martani ne mai cike da Fasaha da Hikima da Juriya, wannan yana cikin abin da yake burge jama’a game da shi.


Misali; A shekarun farko-farko na Da’awarsa, malaman hukuma sun yi ta suka da aibata shi da kushe fikirarsa, wani babban Malami ya tava aibata shi a kafafen yaxa labarai cewa; “Su Al-Zakzaky masu cewa sai an yi shari’a da Alqur’ani ‘yan yara ne qanana, kuma ba malamai ba ne ba su da wani ilimin addini mai zurfi!”.

Da Shaikh Zakzaky (H) ke mayar da martani ga malamin sai ya ce; “To, ai waxannan abubuwan da aka aibata mu da su ba aibi ba ne, kuma ba su ne ma’aunin da za su nuna mutum yana kan vata ba, domin yarinta ba laifi ba ne, tunda muna raye ai wataran za mu girma, da ma ba a haihuwar mutum a tsoho, daga yaro yake girma har ya tsufa.


“Sannan rashin zurfin ilimi ma ba aibi ba ne, ba dai muna karatu ba? To, da sannu wataran za mu zama malamai, aibi shi ne a ce ba ma karatu, kuma muna gaba da ilimi, in mun ga littafi ma yagawa muke yi, wannan shi ne laifi, amma in dai muna karatu, to ai da sannu nan gaba za mu zamo malamai!”. Ba shakka akwai hikima da basira a wannan martani na Shaikh (H), ka yi nazari!


Wahabiyawa da Salafawa a shekarar 2002 sun cika kunnuwan jama’ar qasa da farfaganda cewa wai shugaban qasa na wancan lokacin Olusegun Obasanjo ya naxa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a muqamin ‘Shugaban Zaman Lafiya’ na tarayyar Nijeriya, sun yi ta shelanta wannan magana a wuraren wa’azozinsu da kafafen yaxa labaru.


To, a wata hira da gidan Rediyon tarayya na Kaduna suka yi da Shaikh Zakzaky (H) sai suka tambaye shi ko zai mayar da martani ga masu wancan iqirari? Sai Shaikh (H) ya ce; “Akwai wani abu da na yi ta ji irin wannan, sai daga baya na fahimci asalin maganar. Akwai Ibrahim Musa Gashash, yana da wata qungiya wacce da turanci ake ce mata “National Tranquility Movement” da Hausa sai aka fassara ta da “Qungiyar Wanzar da Zaman Lafiya”. Wani qila sunan Gashash xin bai saba ji ba, kuma Zakzaky ma bai saba ji ba, sai ya xauka shi Gashash xin shi ne Zakzaky, duk kuma akwai Ibrahim a sunanmu, ina tsammanin daga nan fa aka ce ai Al-Zakzaky shi ne shugaban zaman lafiya!

“Har nake cewa waxannan surutan da ake yi, ya kamata in har da gaske ne gwamnatin qasar nan ta yi wata qungiya mai suna “Qungiyar Zaman Lafiya” kuma har ta naxa Al-Zakzaky a matsayin shugabanta. To, ai ya kamata a taya ni murna ne, ba a yi ta yi min surutu ba, sai a ce Alhamdulillah, ka ga yanzu za ka samar da zaman lafiya a qasa. Amma sai ya zama suka suke yi, ma’ana yanzu sun fahimci cewa ita hukuma abin da take yi ba daidai ba ne, bai kamata ya zama wani mutumin kirki yana tare da ita ba, ina tsammanin haka suke kallo, shi ya sa ma suke neman su aibata ni akan cewa ina yi wa hukuma aiki!” (MujaddadinWannan Qarnin, shafi na 36). Kalli yadda Shaikh ya mayar da martani cikin ruwan sanyi da hikima kan wannan batu.


Lokacin da aka fara “Tattakin Arba’een” daga kusurwowin Nijeriya guda huxu zuwa Hussainiyya Baqiyyatullah Zariya a shekarar 2011. Qasar ta xau xumi ta hanyar surutai da aibatawa kala-kala daga malaman Wahabiyawa, suka yi ta cewa wannan abin da ‘yan Shi’a almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ke yi na Tattakin xaruruwan kilomitoci cikin yunwa da qishin ruwa, suna tafiya da qafa suna dukan qirjinsu sanye da baqaqen kaya, bautar da kai ne da azabtar da jikinsu ga aikin banza, wanda baida lada balle la’ada!


Da Shaikh Zakzaky (H) yake mayar musu da martani a wani jawabinsa sai ya ce musu; “Ina ruwanku! Me ya dame ku da abin da muka sa kanmu? Da qafar wa muke takawa a Tattakin? Ba da qafar mu bane? Qirjin wa muke duka? Ba qirjinmu ba ne? Cikin wa yake shan yunwa? Ba cikinmu ba ne? A jikin wa muka sa baqaqen kayan? Ba a jikinmu ba ne? Waxanne idanu ne suke yin kuka? Ba idanunmu ba ne? To, meye naku a ciki? Meye naku na qorafi da surutu? Kusa mana ido mana kawai?” Mai karatu, kai ya ka gani?

KYAUTARSA :


Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) tamkar ruwan sama yake a fagen kyauta, duk abin da ya mallaka, to na kyautarwa ga al’umma ne. Kyautar Shaikh Zakzaky (H) tana buqatar a yi wallafa ta musamman a kanta, amma tunda komai taqaitawa muke yi, bari ita ma mu taqaita da ‘yan misalsali;


A shekarar 2014 sojojin Nijeriya suka kashe manyan ‘ya’yansa guda uku, to, a lokacin da ake zaman karvar gaisuwa ta shahadar yaran, wata tsohuwa ta shigo ta yi wa Shaikh Zakzaky (H) ta’aziyya, bayan ta yi masa ban haquri tare da yi wa yaran addu’ar samun rahama, sai ta sa hannu ta xauko xari biyu ta bayar ta ce a miqa masa. Da Shaikh ya karva ya yi godiya, sai ya sa hannu a aljihu ya ciro adadin wasu kuxi masu yawa ya miqa mata, ya ce ga shi ta sai goro. Tana qirgawa sai ga Naira dubu Ashirin cif! Da wani jikanta ya samu labarin abin da ya faru sai ya ce mata; Da xari biyar kika ba shi, da dubu 50 za ki samu! Domin “Man’jaa’a Bil-Hasanati, Falahu Asharu Amthaliha”.


Wani xalibi ya samu takardar izinin shiga jami’a “Admission”, amma sai ya zamo shi da iyayensa ba su da kuxin yin rijista, ga lokaci yana ta qurewa, sai aka shawarci xalibin cewa ya je ya kai kukansa ga Shaikh Zakzaky (H), sai kuwa ya zo ya samu Shaikh ya nuna masa takardar ‘Admission’ xin da ya samu na shiga jami’a amma baida kuxin yin rijista.

Sai Shaikh (H) ya ce masa, “Bari in shiga gida in gani ko Allah zai bada mafita”, zuwa can Shaikh ya fito da ambulan a hannu, ya ce ina xalibin nan? Aka ce ga shi nan, ya miqa masa ambulan ya koma cikin gida. Da xalibin ya buxe ambulan xin sai ya ga Naira dubu xari biyu cur! Ya rinqa tsalle yana murna. Ya je ya yi rijista sannan ya sayi mashin na zuwa makaranta, sauran canjin kuma ya kai wa iyayensa.


Kyauta a wurin Shaikh Zakzaky (H) ta zama tamkar jinin jiki, domin hatta manyan mutane in sun ziyarce shi ba ya bari su tafi hannu rabbana, sai ya ba su kyautar da ta dace da su, misali; da Ambasadan Iran ya ziyarce shi a gida a shekarar 2014, sai ya ba shi kyautar Alqur’ani rubutun hannu. Da Ambasadan Swiss ya ziyarce shi, shi ma ya ba shi kyautar Alqur’ani don ya yi nazari. Haka nan idan manyan malaman Ahlis-Sunnah sun ziyarce shi, yakan ba su kyautar littafin “Sahifa Sajjadiyya” da sauran muhimman littattafai. Duk dai wanda ya ziyarce shi yakan masa kyautar da ta dace da shi ne.


A shekarar 2007 ya sayawa Sarkin Makafin Zazzau da mutanensa makeken gida a unguwar Tudun Wada Zariya, sannan duk lokacin da dandazon makafin suka kai masa ziyara sai ya ba kowannensu magudan kuxaxe.


Shaikh Zakzaky (H) ya kasance yana ba matan da yake karatu da su a F.I.C kyautar kuxi akai-akai, kuma suna karatun ne a ranar Talata ta kowane mako, amma bai tava gajiyawa ba, daga lokaci zuwa lokaci sai ya ba kowaccensu kuxi mai kima. Haka nan matan da yake gudanar da karatun Daura da su duk bayan wata biyu, ya kasance yana ba duk wacce ta halarci Daurar kuxi masu kima, har ta kai ga mata sukan ci bashi su biya wasu buqatunsu in sun lura lokacin Daurah ya kusa, ko su ci bashin kuxin mota su zo, don suna da tabbacin samun kuxi muddin Shaikh Zakzaky na gari.


TAIMAKONSA :


Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya zama babban Bango majinginar bayi a Nijeriya, ya zama Baya mai goya marayu, Shaikh ya zama gatan al’umma baki xaya! Babu mai musun hidimar Shaikh Zakzaky ga al’umma ko da kuwa hassada da qiyayya ta makantar da shi, domin gudunmawar Shaikh ga al’umma ya shafi kowa ta zahiri ko ta baxini, ta kai tsaye ko a fakaice.

Shaikh Zakzaky (H) ya koyar da xalibansa hidima ga al’umma, ya nuna musu cewa wajibi ne su yi hidima ga raunanniyar al’ummar da suke zaune a cikinta, domin al’ummar tana buqatar masu yi mata hidima, kuma ya zo a hadisi cewa, “Mafi alherin mutane, shi ne wanda ya ke anfanar da mutanen”.


Albarkar wannan karantarwa ta Shaikh Zakzaky (H), dubban almajiransa a garuruwa da dama ke bada gudunmawar jini a manyan asibitoci da qanana don tallafawa marasa lafiya da majinyata. A kowane taro (musamman na Ashura da Maulidi), almajiran Shaikh Zakzaky a duk inda suke suna zuwa asibitoci su bada jininsu kyauta a xiba a sanyawa majinyata maza da mata, yara da manya, kiristoci da musulmi ba tare da nuna banbanci ba. Wannan gudunmawa da suke badawa ta sha tseratar da ximbin rayuka daga salwanta.


Haka nan, Shaikh Zakzaky (H) da kansa ya zayyana wasu ayyukan da ya kamata almajiransa su riqa yi don taimakon al’umma, kama daga gyara maqabartun musulmi, kwashe bola, tsabtace kwata, gyara hanyoyin ruwa, feshin maganin sauro da na kashe qwayoyin cututtuka, bada gudunmawar abinci da kayan masarufi ga raunana da waxanda wani bala’i ya shafa, gina hanyoyin ruwa don magance ambaliya da sauransu. Waxannan abubuwa kuwa sune muhimman ayyukan da wasu Lajanoni na almajiran Shaikh Zakzaky irinsu “Youth Forum” da “Lajanar Hurras” ke aiwatarwa a ko da yaushe cikin al’ummah, wanda hakan ba qaramin kyautata rayuwar jama’ar qasa yake ba.


A gefe guda, Shaikh Zakzaky (H) ya sha daqile fitina da tarzoma a tsakanin mutanen gari. Farkon zuwansa unguwar Gyallesu ya samu qungiyoyi biyu na matasa ‘Yan daba suna gaba da juna da faxace-faxace, wanda kusan kullum sai sun yi kisan kai a junansu. Sai Shaikh (H) ya sa aka qira su gidansa, ya yi zama da su, ya yi masu nasihohi masu ratsa jiki, ya sasanta su suka dena kashe junansu. Sannan Shaikh (H) ya hana abkawa kiristoci a lokutan zave ko na hargitsin addini, duk inda almajiransa suke, sukan baiwa kiristoci kariya da ba su mafaka don tseratar da rayukansu a lokacin rikici ko na hargitsi. Haka nan a shekarar 2011 lokacin zaven shugaban qasa, duk da cewa Shaikh Zakzaky da almajiransa ba sa zave, amma ya umarci almajiransa sun ba jami’an zave kariya daga abkawar mutane a duk runfunan zaven da ke kewaye da unguwar Gyallesu da wasu sassa na birnin Zariya.


Shaikh Zakzaky (H) ya zamo gatan marar gata a cikin al’umma, misali; A shekarar 1994 wani Sarkin gargajiya a yankin Kudan ta jahar Kaduna ya qwacewa wata tsohuwa makekiyar gonar da ta gada, sai ta kai qara wurin manya amma suka kasa qwato mata gonarta, ta kai qara kotu, kotu ta tabbatar da cewa lallai gonarta ce, amma kawai ta yi haquri dan wanda ya qwace gonar ya fi qarfinta. Tsohuwar nan ta rasa inda za ta sa kanta, alhali tana da ‘ya’ya da jikokin da take so ta barwa gadon gonar. Sai mutane suka ba ta shawarar ta zo Zariya ta sanar da Shaikh Ibraheem Zakzaky halin da take ciki, kuma ta nemi taimakonsa.


Da ta zo ta gabatarwa Shaikh Zakzaky (H) shaidunta, da kwafin takardun hukuncin kotu, sai Shaikh da rakiyar ximbin almajiransa ya je garin na Kudan ya ziyarci gonar, sannan ya yi jawabi mai girgiza azzalumai, kuma ya ce ya dawo wa da tsohuwar nan gonarta tunda kotu ma ta tabbatar da cewa gonarta ce. Daga nan azzalumin sarkin garin bai qara iqirarin qwace gonar ba, haka ya haqura!

Haka nan, almajiran Shaikh Zakzaky (H) a garuruwa da jihohi da dama sun zama gatan raunana marassa gata a yayin da aka zalunce su ko aka yi musu danniya akan wani muhimmin haqqinsu, wannan ya nuna yadda Shaikh Zakzaky (H) ya zama gata ga wannan al’umma.


CIYARWARSA :


Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) mutum ne da ba abin da yake son yi fiye da kyautatawa al’umma, musamman al’ummar wannan qasa tamu da ke fama da quncin rayuwa a vangarori daban-daban. Tun asali Shaikh Zakzaky (H) ya taso ne da burin kyautatawa mutane musamman ta vangaren ciyarwa, domin tarihinsa ya nuna tun yana Jami’a yake ciyar da xalibai da abokansa.

Marubucin littafin “Tarihin Harkar Musulunci” a shafi na 94 ya kawo cewa; A lokacin da Shaikh Zakzaky (H) yake xalibta a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, xalibai dare da rana suna yin Safa da Marwa zuwa xakinsa don su sha Shayi, ko su ci cincin da dai sauran nau’ukan abincin da yake samarwa, domin a lokacin Shaikh (H) yana sawa a yo cincin kwalla-kwalla a kawo xakinsa, domin xalibai ‘yan uwansa ba sa rabuwa da zuwa xakinsa komai dare don neman abin sawa a bakin Salati.


Haka nan, a zaman kurkukun da ya yi a Inugu, ya kasance yana ciyar da sauran ‘yan Fursuna da abincin da ake kawo masa daga maziyarta, xaya daga cikin almajiransa Shaikh Yaqubu Yahya ya labarta cewa; “A wani lokaci mun ziyarci Malam a kurkukun Fatakwal, kuma mun je masa da xan guzuri haka, soyayyen nama ne da sauransu, (bayan mun shigar masa xaki, da ya gani) sai ya ce a maida shi waje, aka dawo da shi waje, su Madara da Bonbita da sauran kayayyaki duk ya sa aka raba wa mutane, har wani (Inyamuri xan fursuna) yana cewa; “Alhaji No Dey Chop, No Dey Sleep!” wato Malam ba ya cin abinci kuma ba ya bacci!” (Malam Zakzaky: Rayuwarsa da Karamominsa, shafi na 10).


KARAMCINSA :


Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) sarkin karimci ne da Baiwa ga duk wanda ya rave shi, yana da halin girma na kyautatawa kowa fiye da zatonsa. Misalai akan karimcin Shaikh Zakzaky (H) ba su qirguwa, amma bari mu ambaci ‘yan qalilan.


Malama Jameela Auwal (uwargidan Malam Mukhtar Sahabi) ta ba mu labarin wani karimci da Shaikh Zakzaky (H) ya yi mata, ta ce; “Lokacin da zan raka ‘yata Maryam Iran bayan xaura aurenta, mun je yin Sallama ga su Shaikh (H), sai ya tambayeni ta ina za mu tashi? Sai na ce masa ta Legos ne, sai ya ce; Gobe da sassafe za ku bar Kaduna kenan tunda qarfe 2 jirginku zai tashi” sai na ce ai yau ne ma za mu kama hanya zuwa Legos, don ta mota za mu tafi, sai Shaikh ya ce; A’a, ai mota akwai wahala, a ce wa Malam Mukhtar ya yi muku bukin na jirgi gobe sai ku tafi, zan turo masa kuxin!” haka kuwa aka yi, ya biya mana kuxin jirgi muka tafi Legos ta jirgin sama, anan na qara tabbatar da cewa; “Sayyidul Qaumi Khadimuhum”. (Dandalin Khairul-Amal na Whatsapp, 2016). 


A watan Maulidi na shekarar 1437 Hijira, rundunar sojojin Nijeriya suka farwa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a gidansa da ke unguwar Gyallesu a cikin birnin Zariya, kafin su kai ga Shaikh xin sai da suka kashe xaruruwan almajiransa maza da mata har da jarirai. A lokacin wannan ta’addanci na sojoji da ya shafe tsawon yini uku suna yi, sashen mutanen wannan unguwa wacce ke cike da jami’an leqen asiri, sun bada gudunmawa sosai da goyon baya ga ta’addancin da ake yi wa Shaikh xin da almajiransa, wanda hatta wasu marubuta sai da suka kwatanta mutanen unguwar ta Gyallesu da mutanen Kufa, wanda suka ci amanar Imam Hussain (AS).


Amma abin mamaki, bayan watanni shida da faruwar abin, watan Ramadan ya shigo, sai ga Shaikh Zakzaky (H) ya aiko daga inda ake tsare da shi cewa; Lallai a rabawa talakawa da raunanan mutanen Gyallesu buhunan abinci na tallafin watan Ramadan da ya saba ba su duk shekara! Hakan kuwa aka yi, aka bi su gida-gida kowa ana ba shi abin da aka saba ba shi na Shinkafa da Masara da Gero da Sukari da sauran kayan masarufi. Wannan ya nuna yadda Shaikh Zakzaky (H) ke maida sharri da alkairi saboda karamcinsa.

Wani xan uwa ya labarta mana cewa; 


“Wata rana da yamma muna zaune a falon Shaikh Zakzaky (H), sai wani xan uwa mai hali ya ziyarci Shaikh, bayan sun daxe suna hira muna saurarensu, da ya tashi zai tafi, sai ya miqawa Shaikh makullin mota, ya ce; “Ga wata ‘yar mota can na kawo muku Hadiyya ko yara za su yi anfani da ita”, sai Shaikh ya karvi makullin motar ya ce; “Masha Allah, Allah ya saka da alkairi”.


Bayan mutumin ya tafi, sai Shaikh (H) ya ce; Motar kuwa ta yi kyau, ina ganin za ta dace da Malam wane (ya ambaci sunan wani xalibinsa da ke zaune a wurin)”, sai ya ce wa wannan xalibi; “Ai wannan motar za ta yi tafiya a Sahara ko?” Kafin xalibin ya amsa sai ya miqa masa makullin, ya ce “To a je a yi ta fama da kuxin mai”. Wannan ba qaramin karimci bane musamman ga wanda ya san cewa ‘ya’yan Shaikh baki xayansu ba wanda ke da motar hawa a lokacin, amma maimakon ya ba su, sai kawai ya ba wani almajirinsa.


Haka nan Shaikh Zakzaky (H) duk shekara yana yanka wa almajiransa Ragon layya, wato duk shekara yana yanka Rago ko Saniya a madadin miliyoyin almajiransa da Allah bai nufe su da yin layya a wannan shekarar ba, kuma yana yankawa dukkan raunanan al’ummar musulmin duniya da ba su samu damar yin layya ba Raqumi, kamar dai yadda Manzon Allah (S) ya yi wa al’ummarsa marassa galihu layya. Marubucin littafin “Malam, Malam Ne” yana cewa; “Na san duk sallar Layya sai Malam (H) ya yanka Rago, wato ya yi wa duk “Brothers” (‘yan uwa maza da mata) Layya, kuma ya ba su naman Ragon sun ci” (Malam, Malam Ne, shafi na 10).


JARUNTARSA :


Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) jarumi ne da dukkan ma’anar jarunta, tun asali bai da tsoro, bai da fargaba bare razana, domin tarihi ya tabbatar da cewa tun yana yaro qarami bai san tsoro ba. A wani biki na cikarsa shekaru 45, Shaikh Zakzaky (H) yana cewa, bai san me ya sa shi tun yana yaro baida tsoro ba, duk wani abu mai razanarwa shi ba ya razana

1 Comments On SHAIKH ZAKZAKY IKON ALLAH
avatar
shuraihu-usman-1

1 year ago

Reply

sss

Please Login or Register in order to submit comment