Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a lokacin, amma an iya isar masa da tutar don Tabarruki.


NA 12 : Gamayyar qungiyoyin kare haqqin xan na jihohin kudancin Nijeriya, wato “Southeast Based Coalition of Human Rights Organisations” (SBCHRO’s) a taqaice, wacce ta qunshi qungiyoyi 12 na kare haqqin xan adam a Nijeriya, sun karrama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da “Prestigious Award” na “Prisoner-of-Conscience” wato (POS) a taqaice. Sun yi wannan karramawa ne ranar 17 ga watan August na shekarar 2016 a birnin Ummuahia na jihar Abia.


Shugaban gamayyar qungiyoyin Mr. Emeka Umeagbalasi ya ce; Mun karrama Shaikh Ibraheem Zakzaky da wannan “Award” da ya ginu akan cika qa’idojin Majalisar xinkin duniya na wanzar da zaman lafiya da yaqi da wariya ne, bisa irin al’ummar da ya samar mai tsananin hangen nesa da aiki da hankali, “Domin an tsare shi tsawon lokaci bayan an harbe shi da kashe masa ‘ya’yansa da ximbin mabiyansa, amma har zuwa yau ba a samu yamutsi ko hargitsi ko tashin hankali da sunansa ko na mabiyansa ba!” Sun karrama shi ne duk da cewa yana tsare a kurkuku a lokacin.


Waxannan jerin “Awards” da karramawa guda 12 da muka ambata ba suke nan ba, an ba Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) “Awards” da dama a wurare da qasashe da dama, mun ambaci waxannan ne a matsayin misali.


YABO DA JINJINA A GARE SHI :


Tirqashi! Idan mutum yana so ya varo aiki, to ya nemi sanin yawan yabon da mutane daban-daban suka yi ga Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), domin linzami ya fi qarfin bakin kaza. Za a iya wallafa manya-manyan littattafai akan yabo da kyawawan zantukan mutane akan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), amma da yake komai muna taqaitawa ne, bari mu bada ‘yan misalai na yabon vangarorin al’umma gare shi.


YABON KIRISTOCI : Kiristocin Nijeriya na vangarori daban-daban sun sha yabawa Shaikh Zakzaky (H) a lokuta da dama, wannan yabo sukan yi shi a qungiyance da xaixaikunsu, sun sha kwatanta halayensa da na Annabi Isa (AS), sukan ce shi ne “Small Jesus” ko “The Saviour” ko “The Mesiah” da sauransu.


Rebaran Musa D. Musal na cocin Angilika a Gombe, ya faxi a wani jawabinsa cewa; “Xabi’un Shaikh Zakzaky irin na Annabawa ne. Kusan shekaru 20 ina tare da Shaikh, ina jin karatuttukansa, har ta kai ga na xauki Shaikh a matsayin jagorana! Akwai Shehunnai a qasar nan, amma Shaikh Zakzaky ya fita daban a cikinsu… dan haka addu’ata da zan yi ga Shaikh shi ne, Allah ya qarfafe shi, Allah ya sa shi ne wanda zai zama sanadin tsiranmu a wannan nahiya” (Rebaran Musa ya yi wannan jawabi ne a taron Mu’utamar na Matasa na qasa da aka yi a Bauchi, ranar 7-Zulqa’ada-1436).


Wani Fadan kirista, kuma shugaban qungiyar yaqi da cin hanci ta “Anti Corruption Network” a Nijeriya, Mr. Ebenezer Onyetekan ya faxi cewa; “Yadda na ga xabi’un Shaikh Zakzaky da halayensa, da kuma salon Da’awarsa, ko da Musulunci zan yi, to Shi’a zan yi!” (Ya faxi wannan ne a taron tunawa da Shahidan Qudus karo na farko, ranar Lahadi 26 ga watan Yulin 2015, a Sheraton Hotel Abuja).


Fasto Meter Peller na Cocin Anglican Abuja, ya faxi a wata hirarsa da ‘yan jarida cewa; “Malam Zakzaky ba irin sauran malamai ba ne da za su ce abu su kuma kasa aikatawa, Malam yana faxa ne da aikatawa, kuma muna gani a zahiri. Kuma lallai wannan mutumin ya kamata ya zama Uba ga kowa, kuma ya kamata ni in zama xa gare shi daga cikin ‘ya’yansa!” (Jaridar ALMIZAN, bugu na 1256, shafi na 08).


“Malam ya zama ‘Bridge Builder’ mai gina gadar fahimtar juna tsakanin kudu da arewa, da kuma tsakanin Kirista da Musulmi, Ibo da yawa sukan ce in dai za su yi Musulunci, to irin na Zakzaky za su yi, wani ma cewa ya yi “This man na freedom fighter” wato wannan mutumin mai qwatarwa raunana ‘yancinsu ne”. (Malam, Malam Ne, shafi na 18).


YABON QADIRIYYA : Limamin Qadiriyya na Afirka, Shaikh Muhammad Nasiru Kabara (RA) tun yana da rai aka ruwaito cewa, wata rana da Shaikh Zakzaky (H) ya ziyarce shi, a jawabinsa ya ce; Duk xan Qadiriyar da ya soki Da’awar Shaikh Zakzaky ya ci amanar Qadiriyya!”. Sannan kusan baki xayan ‘yan gidan Qadiriyya ba wanda bai ya bi Shaikh Zakzaky (H) da yabo kyakkyawa ba a lokuta daban-daban.


YABON TIJJANIYYA : Shaikh Murtadha Abul-Fathi, wanda xa ne ga babban jagoran Tijjaniyya a Nijeriya, kuma xaya daga cikin jigoginta na duniya, wato Shaikh Abul-Fathi Maiduguri, a jawabinsa na wani taron “Makon Haxin Kan Musulmi” da aka yi a Zariya, ya ce, duk wata kamala (Qualities) na Annabawa (AS) to Shaikh Zakzaky (H) ya siffatu da su, “Da ba don na riga na yi wa Shaikh Ibraheem Inyas mubaya’a ba, to da na miqa hannuna na mubaya’a ga Shaikh Zakzaky!”.


YABON GWAMNATI : Abin mamaki game da Shaikh Zakzaky (H) shi ne, hatta gwamnatocin da suke adawa da shi, sun sha yabonsa a fili da voye, misali; Gwamnatin jahar Kaduna ta tava ba shi takardar karramawa (Certificate) a matsayin gwarzon mutumin da ya fi kowa kawo zaman lafiya a qasa, wanda gwamnan jahar Kaduna na mulkin soja Laftanar Kanal Lawal Ja’afaru Isah ya ba shi a shekarar 1996 kafin Janar Abacha ya kama shi a wancan lokacin.


Haka nan, wasu daga cikin manyan Sarakunan gargajiya mafiya daraja a Nijeriya, sun sha yabawa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), misali, marigayi Sarkin Kano Dr. Alhaji Ado Bayero CFR, ya sha yabawa Shaikh Zakzaky, har ma ya tava fitowa fili ya yi kiran da a sake shi lokacin da gwamnatin Janar Abacha ta kama shi, kuma ya yi Allah wadai da gallazawar da ake masa.


Haka nan Sarkin Zazzau Dr. Alhaji Shehu Idrees CFR, ya tava jinjinawa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a wata hira da aka yi da shi lokacin da ya cika shekaru 30 akan gadon Sarauta, an tambaye shi ne me zai ce game da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)? Sai ya ce; “Malam Ibraheem Zakzaky yana cikin ‘ya’yanmu masana masu albarka, shi xan mu ne mai albarka!” (Al-Mizan, bugu na 657, shafi na 3, 10-Muharram-1426).


YABON ALMAJIRANSA : Yabon almajiran Shaikh Zakzaky (H) gare shi abu ne da bai misaltuwa, wani almajirinsa a littafin da ya rubuta mai suna “Tarihin Harkar Musulunci” yana cewa; “Akwai sunnoni da yawa na Manzon Allah (S), Shukran Laa-fakhran, Sayyid Zakzaky (H) shi ne asasin raya su a wannan nahiya ta mu da muke ciki, wanda ba ‘yan uwa kawai ba, a’a hatta sauran jama’ar gari, da yawa sun kwaikwayi waxannan sunnoni”.


RUBUCE-RUBUCE AKANSA :

Ta xaya janibin kuma, akwai littattafan da aka rubuta akan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da rayuwarsa, wanda littattafai ne qanana, amma sun yi tsokaci akan wasu muhimman janibobi na rayuwarsa.


NA XAYA : Littafi na farko game da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) shi ne; “Kitabul Bushra” wanda littafi ne da ya yi magana akan albishirin bayyanar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da Waliyi kuma mujaddadi Shehu Usman Bin Fodiye ya yi tun fiye da shekaru 200 kafin haihuwarsa. An buga littafin ne a shekara ta 1416 Hijira, Edita Malam Ibrahim Musa ne ya wallafa littafin.


NA BIYU : Littafin “Malam Zakzaky (H) Rayuwarsa da Karamominsa”, wanda shi kuma laccocin wasu malamai guda biyu ne akan rayuwar Shaikh Ibrahim Zakzaky (H) aka mayar da su littafi, ya qunshi tsokaci akan vangarori daban-daban na rayuwar Shaikh Zakzaky (H). An buga littafin ne a shekarar 1416 Hijira, malaman da suka gabatar da jawaban littafin su ne Shaikh Ya’aqubu Yahya Katsina, da Malam Abubakar Abdullahi Sokoto.


NA UKU : Littafin “Tauhidin Kalma Daga Rayuwar Mujaddadai”. Shi wannan littafin littafi ne na falsafa, wanda ya qunshi salo da kalmomi masu sarqaqiya, yana kwatanta dacewar salon rayuwar bayin Allah ne ma’abuta Tajdidin addini, inda ya kwatanta dacewar rayuwar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da sauran Mujaddadan addini da suka gabace shi. An wallafa littafin ne a shekarar 1997, marubucin littafin shi ne Malam Ibrahim Muhammad Potiskum.


NA HUXU : Shi ne littafin; “Yusufuz-Zaman”. Shi wannan littafin ya fito da darussa ne na dacewar rayuwar Shaikh Zakzaky (H) da ta Annabi Yusuf (AS), ta yadda ya gaji halayya da xabi’u da yanayin rayuwar Annabi Yusuf (AS) musamman ta fuskacin jarabawar garqamewa a gidan kurkuku. An wallafa wannan littafi ne a shekarar 1998, marubucin littafin shi ne Malam Ibrahim Muhammad Potiskum.


NA BIYAR : Shi ne littafin “Wakilin Manzon Allah (S) a Doron Qasa”. Shi wannan littafi an gina shi ne akan hujjoji na nassi da na hankali da na zahiri da ke nuna cewa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) magajin Manzon Allah (S) ne a wannan nahiya, domin ayyukansa da xabi’unsa da halayensa suna kama da na Manzon Allah (S). Littafin na xaya da na biyu ne, kuma an buga su ne a shekarar 1997 da 1998 Miladiyya, marubucin littafin shi ne Malam Xanjuma Katsina.


NA SHIDA : Shi ne littafin “Bayyanar Sharafuddin”. Shi wannan littafi shi ne irinsa na farko a fagen hallale bayani akan rayuwar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) daki-daki. Littafin ya qunshi magana akan Shaikh Zakzaky (H) tun daga wasiyyoyin bayyanarsa, zuwa asalin zuriyya da nasabarsa, har zuwa yarinta, karatu, gwagwarmaya, kulen da ya fuskanta, da sauran vangarorin rayuwarsa. An buga littafin ne a shekarar 2001 Miladiyya. Marubucin littafin shi ne Malam Al-Ameen Isa Al-Sakkwaty.


NA BAKWAI : Shi ne littafin “Malam Malam Ne”. Wannan littafi ya qunshi muhimman bayanai game da wasu vabgarori na rayuwar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da baiwar da Allah Ta’ala ya yi masa a vangare daban-daban. Asalin littafin rubuce-rubuce ne da mawallafin ya yi a jaridar ALMIZAN, shi ne aka tattara su wuri guda aka maishe su littafi. An buga littafin ne a shekarar 2007 Miladiyya. Marubucin littafin shi ne Marigayi Malam Haruna Shelleng.


NA TAKWAS : Shi ne littafin “Shekaru 60 Masu Albarka”. Shi wannan littafin ya qunshi hirarraki ne da mutane daban-daban akan rayuwar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) tun daga yarintarsa har zuwa cikarsa shekaru 60 a duniya. An yi hira da iyalansa, da ‘ya’yansa, da abokansa, da danginsa na jini, da almajiransa, da sauran jama’ar da suka san shi, kuma a qarshen littafin an kawo wasu rubuce-rubuce akansa. An wallafa littafin ne bayan bukin cikar Shaikh xin shekaru 60 da haihuwa a shekarar 1433, wanda ya yi daidai da farkon shekarar 2012 Miladiyya. Mawallafin littafin shi ne Edita Malam Ibrahim Musa.


NA TARA : Shi ne littafin “Mujaddadin Wannan Qarnin”. Shi wannan littafi ne da ya qunshi bayanai akan rayuwar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), da hujjoji akan zamowarsa Mujaddadin addini a wannan nahiya. Marubucin ya kawo hujjoji na naqali da na hankali da ke tabbatar da cewa Shaikh Zakzaky (H) Mujaddadin addini ne. An buga littafin ne a shekarar 2013 Miladiyya. Marubucin littafin shi ne Muhammad Nasir Miji Gombe.


NA GOMA : Shi ne littafin “Sallah Mafificiyar Ibada”. Shi wannan littafi ya xauki janibi xaya ne kacal, wato sallolin Shaikh Zakzaky (H) ya yi bayani akai, cike yake da hotunan Sallolin Shaikh Zakzaky (H) tun daga na Yaumiyya har zuwa Idi da sallar Jana’iza. An kawo dukkanin karance-karance, da addu’o’i, da Azkar, da Alqunut xin da Shaikh Zakzaky (H) ke yi ne a cikin sallolinsa, da surar yadda yake wasu ayyukansa na Sallah a cikin hotuna masu kala. An wallafa littafin ne a shekarar 2014. Marubucin littafin shi ne Abdullahi A. Hamza.


NA 11 : Shi ne littafin “Tarihin Sayyid Ibraheem Yaqub Al-Zakzaky da Harkar Musulunci”. Wannan littafi shi ne irinsa na farko a bisa salo da usulubinsa, domin littafin ya qunshi vangare biyu ne, vangaren tarihin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), da kuma vangaren tarihin Da’awarsa ta Harka Islamiyyah. A irin wannan usulubi, za a iya cewa shi ne littafin tarihin Harka Islamiyyah na farko. An wallafa littafin ne a shekarar 2015 Miladiyya. Marubucin littafin shi ne Malam Muhammad Sulaiman Kaduna.


NA 12 : Shi ne littafin “Shaikh Zakzaky Ikon Allah!” wato wannan littafin da ke hannun mai karatu, shi ya qunshi tsokaci ne akan vangarori da dama na rayuwar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da tarihinsa ataqaice. An kammala rubuta littafin ne a shekarar 2017 Miladiyya. Marubucin littafin shi ne Adamun Adamawa.

A taqaice, waxannan sune littattafan da aka rubuta kacokam akan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da abubuwan da suka shafe shi, amma akwai littattafai da dama da suka ambaci wani sashe na rayuwarsa a wasu babukansu. Sannan wannan littatafan da aka rubuta da Hausa ne kawai, banda na Larabci, Turanci, Projects, Mujallau da sauransu.


WAQOQIN DA AKA YI AKANSA :


Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana cikin mutane qalilan da tarihi zai ayyana cewa an yi ximbin waqoqin yabo a kansu, domin zuwa yanzu abu ne mai matuqar wahala a iya qiyasi ko kirdadon adadin waqoqin yabon da aka yi a kansa. Tun a qarshen shekarun 70s waqoqi akan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da Da’awarsa suka soma karaxe sassa da lungunan Nijeriya da qasashe maqwabta, kuma har ya zuwa yanzu sai abin da ya qaru.


An yi waqoqi marassa qirguwa akan Shaikh Zakzaky (H) da Da’awarsa, hasali ma akwai qungiyar mawaqa na Harka Islamiyya mai suna “Ittihadus-Shu’ara Lil Harkatil Islamiyyah”, wanda suke taimakawa da fasaharsu wajan wayar da kan jama’a game da manufar Da’awar Shsikh Ibraheem Zakzaky (H).

Babu shakka mawaqa da daman gaske sun yi waqoqi da yawa akan Shaksiyyar Shaikh Zakzaky (H), wanda zai yi wuya a iya qididdige su, to amma mawaqan da suka fi kowa yin fice akan yi wa Shaikh Zakzaky (H) waqoqi sune Alhaji Mustapha Gadon Qaya, da Malam Ammar Muhammad Xan Tinka.


Shi Alhaji Mustapha Gadon Qaya ya yi waqoqin yabon Shaikh Zakzaky (H) da dama, daga cikin wanda suka yi fice akwai; “Yaa Sharafaddeeni Maraba”. Da “Imamul Bara’ati Labbaika!”. Sai “Ya Malam Zakzaky, Ibraheemu Baban Nusaiba Tsayayye”. Sai “Ibraheem Zakzaky, Labbaika ya Zakzaky”. Sai “Ya Zakzaky qara yin Juriya Jagoran Addini Babba”. Sai “Akan Zakzaky Mu Ba Mu Shakkar Uban Kowa!”. Sai “Ya Allah Kare Al-Zakzaky Qara Mana Yin Biyayya”. Sai “Ya Hasken Allah Imamu Zakzaky Mai Alfarmaa”. Sai “Al-Zakzaky Kogin Baiwa, Sirri na Allah sai Kallo!”. Sai kuma “Sannu-sannu Dattijo, Wila’armu na gurin Allah, Bai’armu na a hannunka”. Sai kuma “Babu inda ba Allah, in akwai ku kai Malam” da dai sauransu.


Shi ma Malam Ammar Xan Tinka Zariya, ya yi waqoqin yabo da jinjina ga Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da dama, daga cikin fitattun waqoqinsa akwai; “Yaa Mujaddadi”. Da “Labbaika Zakzakiy Shehu!”. Da “Gaskiya Malam Malam ne”. Da “Haske ya Bayyana Al-Zakzaky Muna nan Bayanka”. Da “Zakzaky Taka da Laafiya!”. Da kuma “Zakzaky Aarifum-Billahi” da dai sauransu.


A gefe guda, akwai wasu fitattun mawaqa da suka yi waqoqi na yabon Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da suka yi tashe a cikin al’umma, daga ciki akwai; Alhaji Mustapha Limanci da waqarsa ta “Gaisuwa nake Jagorana Shehu Ibraheem Zakzaky”. Sani Aliyu Katsina da waqarsa ta “Lallai-lallai Mun yi Nasara, Malam Zakzaky shi Muka Riqe!”. Bello Shehu Mafara da waqarsa ta “Zakzaky Malamin Ulama’u”. Nura Shahidi da waqarsa ta “Barka da Fitowa Maulana Al-Zakzaky mai Gulbin Baiwa”. Shaheed Shafi’u Kazaure da waqarsa ta “Ni na maka Bai’a Baban su Nusaiba Zakzaky mai Haiba”. Abdullahi Andu da waqarsa ta “Imam Khumaini da Malam Zakzaky Mun Faxi Xa da Uba ne”. Marigayi Malam Rabi’u Tudun Iya da waqarsa ta “Labbaika Shehu Imam Zakzaky”.


Sai Gambo Xankaka da waqarsa ta “Mu dai Al-Zakzaky Muna Son ka Qwarai-qwarai”. Shareef Uzairu Badamasi da waqarsa ta “Kada Mage ba Yanka ba, Yaa Shehu Ibraheem Labbaika Zakzaky Mazajen Fama!”. Abdullahi Xan Lushi da waqarsa ta “Yaa Shehu Zakzaky”. Sa’idu Saqafa Potiskum, da waqarsa ta “Malamina da na yi wa Mubaya’a Jagorana, Zakzaky na!”. Sani Xan Auta da waqarsa ta “Zakzaky Kainuwa Dashen Allah, mun ji mun Gani”. Musa Qasida Gombe da waqarsa ta Fulatanci “Shehu Zakzaky Modibbo, Wala bamaxa Nder Moxivve”, da dai sauran ximbin mawaqan da ba za su qirgu ba.


Wani tabbataccen abu da nazari ya nuna shi ne, duk waqoqin da ake yi akan Shaksiyyar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ba qaramin farin jini da tashe suke yi ba, wataqil wannan yana da alaqa da xanfaruwar zukatan al’umma ga Shaikh Zakzaky (H) xin ne.


KYAWAWAN MAFARKAI AKANSA :


Babu shakka kowane bawan Allah akan samu wasu alamomin da za su zamo shaida akan Khususiyya da darajarsa, ta irin wannan salo ne aka samu isharori da dama game da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) musamman ta hanyar mafarkai, kasancewar mafarki wata hanya ce daga cikin ingantattun hanyoyin Bushara, kenan hakan zai zama abin la’akari ga ma’abuta hankali.


Mafarke-mafarke da ke ishara ga darajojin Shaikh Ibraheem Zakzaky ba su da iyaka, domin jama’a da dama sun sha yin ayyuka “A’amal”, ko su yi wasu addu’o’i na neman ganin Manzon Allah (S) a mafarki, amma maimakon haka sai su yi mafarki da Shaikh Zakzaky a madadinsa, wanda hakan ke nuna wata alaqa mai qarfi da ke tsakanin Shaikh da Manzon Allah (S).


Haka nan, jama’a da dama sun yi mafarke-mafarke da Manzon Allah (S) ko wani Imami daga cikin Ma’asumai (AS), ya umarce su da riqo da yin biyayya ga Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), wannan ya sha faruwa hatta ga waxanda ke qiyayya ga Shaikh Zakzaky (H) kamar Wahabiyawa da wasu mabiya xariqun Sufaye. Misali;


A shekarar 1995, wani Bawahabiye a birnin Bauchi ya yi Mafarki da Imam Mahdi (AF), ya ce masa; “In na bayyana kana cikin wanxanda zan yaqa!”, sai Bahwahabiyen ya fashe da kuka yana roqon Imam ya yafe masa laifinsa kuma ya faxa masa mafita. Sai Imamul-Asr (AF) ya ce masa; “In kana son tsira daga wannan, to ka yi mubaya’a ga mai Da’awar nan na Zariya Malam Ibraheem Zakzaky!”, Da sassafe Bawahabiyen ya yo sammako zuwa cibiyar ‘yan uwa almajiran Shaikh Zakzaky (H) ta Bauchi, ya faxi mafarkin da ya yi, kuma ya nemi a miqa bai’arsa ga Jagora (H).


Sannan a wajajen shekarar 2000, wani xan Ahlis-Sunnah a Sakkwato ya yi mafarki game da Shaikh Zakzaky (H), wanda ta sanadinsa ya zama almajirin Shaikh Zakzaky (H). An buga labarin mafarkin nasa a jaridar Al-Mizan. Ya ce;- “Na yi mafarkin an gina wani sabon masallacin juma’a babba a garinmu, sai na ji ana sanarwa cewa za a yi gagarumin taro na bikin buxe masallacin, kuma babban bako mai buxe masallacin, wanda kuma zai jagoranci sallar farko a masallacin shi ne Shaikh Ibraheem Zakzaky!


“Sai abin ya bani mamaki, a raina na ce; Zakzaky shugaban ‘yan Shi’a ne zai buxe mana masallacin garinmu, alhali mu Ahlis-Sunnah ne? Na yi ta tambayar kaina, me ya sa aka gayyato shi? Me ya sa ‘yan kwamitin masallacin ba su ga dacewar gayyatar kowa ba sai shi? Me ya haxa mu da xan Shi’a? A haka dai na haqura, na yi wanka na sa farar jallabiya, na tafi wajan bikin buxe masallacin.


“To, inda ake taron buxe masallacin qaton wuri ne kewaye da wata doguwar katanga, ta qofa xaya ake shiga wurin, gun ya cika maqil da jama’a, sai aka yi shela cewa kowa ya daidaita sahu za a yi Sallah, na ga Shaikh Zakzaky (H) ya wuce gaba zai ja sallah, sai na riyawa zuciyata cewa; Ni ba zan bi shi Sallah ba!

“Sai na kama hanya zan fita, ina zuwa qofa, da na hangi waje, sai na ga mugayen namun daji ne ta ko’ina! Duk wata muguwar dabba akwaita a wurin, Kura, Zaki, Damisa, Gwanki, Dorina, Aladu da sauransu, ga su nan ba iyaka! Suna ta hargowa, suna jiran in fito su cinye ni! Nan take sai na juya da hanzari na koma na shiga sahu na bi Shaikh Zakzaky (H) Sallah! Kawai sai na farka daga barcina.

“Daga nan na sallamawa Shaikh Zakzaky (H), na ce wannan ishara ce ake yi min ta yin biyayya gare shi. Alhamdulillah, yanzu ina cikin almajiran Shaikh Zakzaky (H). Allah ka tabbatar da mu a bayansa har abada! Dan darajar Manzon Allah (S) da iyalansa tsarkaka!”.


Haka nan, wani mabiyin xariqar Sufanci, ya yi mafarki da Manzon Allah (S), inda ya nuna masa cewa abin da Shaikh Zakzaky ke tafiya akai shi ne shiriya, kuma ya umarce shi da biyayya gare shi muddin yana son tsira cikin sauqi a gobe qiyama. Haka ma wani babban malami daga qasar Senegal, mai suna Shaikh Sayyid Haidar Muhammad Shamsuddeen ya yi mafarki har sau uku da Sayyida Fatimah Azzahra (SA) tana ce masa ya je birnin Zariya a Nijeriya ya yi mubaya’a ga xanta Shaikh Ibraheem Zakzaky, a karo na ukun har gargaxi ta yi masa. Shi ne a shekarar 2014 ya niqo gari daga Senegal ya zo Nijeriya ya miqawa Shaikh Zakzaky (H) mubaya’arsa don yin biyayya ga umarnin ‘yar Manzon Allah (S).


Ire-iren waxannan mafarkai akan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ba su da iyaka, mun kawo waxannan ne kawai a matsayin misali, kuma duk da cewa ba kowane mafarki ne hujja ba, to amma ire-iren waxannan mafarkai bushara ce ingantacciya.

✳✳✳ ✴✴✴ ✳✳✳

BABI NA BAKWAI

BUSHARORIN BAYYANAR SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY (H)

BUSHARA A TARIHIN XAN ADAM : 


Tarihi ya nuna cewa kafin a haifi duk wani mutum na musamman, mai baiwa ta musaman, wanda zai yi wani aiki na musamman a duniya, ko zai wanzu ya shahara, to, akan samu wasu bayin Allah masu hangen nesa da za su yi busharar bayyanarsa, kamar dai yadda aka samu wasu bayin Allah da ke busharar bayyanar Annabawa (AS), da yadda aka samu waliyan da suka yi busharar bayyanar Mujaddadi Shehu Usman xan Fodiye (RA), kuma aka samu zantuka masu busharar bayyanar Imam Khumain (QS). To, haka nan shi ma Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) an samu bayin Allah da suka yi busharori na bayyanarsa da girman sha’aninsa.

Bushara ta farko da ake alaqanta ta game da bayyanar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ita ce wacce ta zo daga Imam Muhammad Baqir (AS) wacce Imam Jalaluddin Suyuxy ya ruwaito a cikin littafinsa, wacce kuma wani manazarci ya yi fashin baqi akanta ya nuna dacewarta da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H).


Bushara ta biyu ita ce Busharar Imam Ja’afar Assadiq (AS), wacce ta zo cikin hadisinsa mai tsawo, inda ya bayyana mataimakan Imam Mahdi (AF) guda 313, ya ambaci sunaye da wasu daga cikin siffofinsu, daga cikin sunayen akwai Ibraheem Al-Magriby, wanda ake kyautata zaton Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne.

Bushara ta uku wacce waliyin Allah kuma Mujaddadin addini Shaikh Usman bin Fodiye ya yi, wacce a ciki ya bayyana siffofin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da shekarar haihuwarsa. Shaikh Usman bin Fodiye ya yi wannan bushara ne a wata waqa tasa mai Baiti Ashirin, wacce ya yi ta da harshen Fulatanci, waqar tana cikin littafin “Bushral-Ahbab” na Shaikh Usman bin Fodiye, wanda littafi ne da aka tattara waqoqin da ya yi ga waliyyan Allah na zamaninsa da wanda za su zo nan gaba.

Wani malami mai suna Shaikh Bayero ibn Muhammadu Sambo Kulwa ya fassara waqoqin littafin “Bushral-Ahbab” daga Fulatanci zuwa Larabci, bayan ya yi naqalinsu daga littafin mahaifinsa Malam Muhammadu Sambo Kulwa (wanda ya rasu a shekara ta 1248 bayan Hijira) mai suna “Kanzul-Aulaad”, shi kuma mahaifin nasa almajirin Shaikh Usman bin Fodiye ne kai tsaye.


Bushara ta huxu ita ce Busharar da waliyiya Nana Asma’u bint Usman bin Fodiye ta yi akan bayyanar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). Nana Asma’u ta yi busharar bayyanar Shaikh Ibraheem ne a wata waqarta mai Baitoci 40 cikin harshen Fulatanci, kuma an kawo wannan Bushara a cikin kundin waqoqinta da wasu Turawan Ingila suka tattara wuri xaya aka maishe su littafi mai suna; “The Collected Works of Nana Asma’u” na Jean Boyd da B.B Mark, wanda kanfanin wallafa na Sam Bookman Publishers da ke birnin Ibadan a Nijeriya suka wallafa a shekarar 1999.

Sannan akwai busharar da wani babban malamin xariqa a Zariya ya tava yi, wanda bawan Allah ne sufi taqiyyi, kafin rasuwarsa ya tava bayyana cewa “Wasu matasa daga Jami’ar Ahmadu Bello ne za su yi tajdidin addini a wannan qasa”. Wanda a fili qarara za a iya xanfara wannan bushara ga Shaikh Zakzaky (H) da almajiransa, domin tushen da’awarsa ya samo asali ne daga wannan Jami’a. Bari mu kawo uku daga cikin waxannan Busharori biyar da muka ambata, tare da yin taqaitaccen sharhi a kansu.


BUSHARAR IMAM BAQIR (AS) :


Malam Ishaq Muhammad Xan’adany (malami, manazarci mazaunin birnin Zariya), ya fitar da wani nazarinsa akan ruwayar Imam Baqir (AS) da Imam Jalaluddin Suyuxy ya ruwaito a fitaccen littafinsa mai suna “ALHAAWY LIL-FATAAWA” juz’i na uku shafi na 99, inda ya ce lallai wannan ruwaya tana Busharar bayyanar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne, ga abin da ya rubuta.


Imam Suyuxy ya ruwaito hadisi a littafinsa mai suna “Al-Haawy Lil-Fataawa” cikin zantukan jikan Manzon Allah (S) Imam Baqir (AS), ya ce; daga Abiy-Qubail (daga Imam Baqir (AS)) ya ce; “Wani jagora zai kasance a AFIRKA, (zai yi jagoranci) na

1 Comments On SHAIKH ZAKZAKY IKON ALLAH
avatar
shuraihu-usman-1

1 year ago

Reply

sss

Please Login or Register in order to submit comment