Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

KA SHAFAWA NAKA RUWA : Wannan “Karin Magana” ma Shaikh (H) ba ya anfani da ita, ya sha faxi cewa karin maganar bai dace ba, domin musulunci yana qarfafa ‘yan uwantaka ne da taimakon juna. Don haka, in gemun xan uwanka ya kama da wuta, kamata ya yi ka kawo masa gudunmawar ruwa ka taya shi kashewa, in kun kashe wutar, to, kai da shi duk sai ku shiga shafawa gemunan naku ruwa don kar wani a cikinku ya sake samun gobarar gemu! Amma in gemun xan uwanka ya kama da wuta, sai ka ja gefe ka shafawa naka ruwa, ai ka nuna halin ko in kula gare shi da son kanka kenan, alhali musulunci ya yi hani ga hakan. Ko ba a lura ba? 


SO DUK SO NE, AMMA SON KAI YA FI : Shaikh (H) ba ya anfani da wannan “Karin Magana”, domin ya savawa karantarwar addinin musulunci. Hafizahullah ya nuna cewa cikar imanin mutum shi ne ya so wa xan uwansa abin da yake so ga kansa, ayar Alqur’ani a “Suratul Hashr” Aya ta 9 ta nuna cewa mumini cikakke shi ne wanda zai hana kansa ya baiwa xan uwansa abin da yake so. Sannan musulunci ya haramta son kai, dan haka wannan karin maganar ya savawa koyarwar addini, domin yana koyar da son zuciya ne da handama. Shaikh (H) ya canza wannan “Karin Magana” da wani sabo, inda yake cewa “So duk so ne, amma son xan uwa ya fi”.   


WAL-BANI WAL-BAKA, WAL-HANANI WAL-QEMEME : Shaikh (H) ba ya anfani da wannan “Karin Magana”, domin ya savawa koyarwar addini. Wannan karin maganar yana koyawa mutane rowa ne da son kai a fakaice, don yana cewa ne, in mutum yana baka abin hannunsa, to, kai ma sai ka riqa ba shi naka, in kuma yana hana ka na shi, to, kai ma kar ka ba shi naka ko da yana cikin matuqar buqata!


A Hadisai da yawa Manzon Allah (S) ya yi umarni ga musulmi cewa; “Ka rika yin kyauta ga mai yi maka rowa, ka rika kyautatawa mai munana maka”, dan haka karin maganar “Wal-bani Wal-baka…” ya savawa karantarwar addini. Shaikh (H) ya canza wannan “Karin Magana” da wani sabo, inda ya ce; “Wal-bani wal-baka, Wal-hanani Wal-baka!”. Ko ba a lura ba?

 

IN KA YI MUN KAN KARA, ZAN MAKA NA ITACE : Shaikh Zakzaky (H) ba ya cewa azzaluman da suke cutar da shi, “Duk wanda yai mana kan kara, za mu yi masa na itace”, domin yin hakan ya savawa karantarwar addini. Addini bai hana ramuwa ba, amma ya hana wuce gona da iri akan ramuwa. In aka yi maka wani abu to ya halasta ka rama daidai yadda aka yi ma ne, amma xaukar fansa fiye da laifin da aka yi maka laifi ne a musulunci, kuma yin hakan ne abin da wannan “Karin Magana” ke koyarwa. 


YA TAKA MUHIMMIYAR RAWA : A yayin da Bahaushe ke so ya bayyana girman gudumawar da wani ya bayar, yakan ce; “Wane ya taka muhimmiyar rawa a abu kaza”. Sheikh (H) ba ya anfani da wannan karin maganar, domin taka rawa ba wani abu ne kyakykyawa a musulunci ba, sannan ko a al’adance ma mutum mai kima da daraja ba ya rawa, dan haka bai kamata a kwatanta wani abu maras kima ga wani mutum mai daraja da kima ba, maimakon “Ya Taka Rawa”, Shaikh (H) yakan ce “Ya Bada Muhimmiyar Gudunmawa” ne, ko ba lura ba?

more_vert

RefreshRate ApplicationMore Application

SHAIK IBRAHEEM ZAKZAKY (H)
Jagoran harka islamiyyah a Afrika



homeGidashareKyautarwapeopleMasaniyahelpIzinimailTuntuba





BABI NA BIYAR

RAYUWAR SHAIKH ZAKZAKY (H) A QANGIN AZZALUMAI

GWAMNATOCIN DA SUKA XAURE SHI :


Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya sha kamu da xauri a hannun hukumomin Nijeriya, an sha kama shi da azabtar da shi da xaure shi a lokuta daban-daban, ya zuwa yanzu hukumomin Nijeriya sun kama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) har sau 10, kuma jumlatan shekarun da ya yi a tsare sun doshi shekaru 15. Ya zauna a gidajen kurkuku na jihohin Nijeriya daban-daban, daga ciki ya zauna a kurkukun Zariya, Kaduna, Sakkwato, Inugu, Fatakwal, Lagos da Abuja, kuma an sha tsare shi a wuraren azabtarwa da bincike, daga ciki akwai inda ake qira “Interrogation Center” a Lagos, da kuma wuraren tsaro na musamman na jami’an leqen asirin DSS a Abuja.

Bisa abin da ke tabbace a zahiri, daga lokacin da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya fara Da’awarsa a shekarar 1980 zuwa yanzu, mafi yawan gwamnatocin Nijeriya sun xaure shi a gidan yari, wasu gwamnatocin ma sun masa xauri ko kamu fiye da xaya, yayin da wasu gwamnatocin ke gadar ci gaba da xaure shi da gwamnatocin da suka gabace su suka yi.

Gwamnatin soja ta Janar Olusegun Obasanjo ta tsare shi a shekarar 1979 a Zariya, ta kuma sake kama shi a Sakkwato ta tsare a farkon shekarar 1981.

Gwamnatin farar hula ta Alhaji Shehu Shagari ta kama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), ta xaure shi tun daga wajajen tsakiyar shekarar 1981 zuwa 1984.

Gwamnatin mulkin Soja ta Janar Muhammadu Buhari, ta xaure Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a wajajen qarshen shekarar 1984.


Gwamnatin mulkin Soja ta Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ta xaure Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a shekarar 1987 zuwa 1989.


Gwamnatin mulkin soja ta Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta sake kama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a shekarar 1992.


Gwamnatin mulkin kama karya ta Janar Sani Abacha ta xaure Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a shekarar 1996 zuwa qarshen shekarar 1998. 


Gwamnatin mulkin danniyar farar hula ta Muhammadu Buhari, ta kama Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ta tsare shi a qarshen shekarar 2015 wanda har zuwa rubuta wannan littafi a farkon shekarar 2017 ba a sake shi ba.

JADAWALIN KURKUKUN DA YA YI :


Ga tsarin gidajen kurkukun da Shaikh Zakzaky (H) ya yi, da daxewar da ya yi cikin kowannensu;




Bisa wannan jadawali, za mu ga cewa gwamnatocin Soja ne suka fi yawan kamawa da tsare Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), kuma zuwa yanzu an tsare Shaikh (H) a wuraren tsarewa aqalla goma sha bakwai, daga cikin tsarewar da aka masa, an tava tsare shi a “Dungeon” wani wurin tsarewa na qarqashin qasa wanda mutum ba ya iya banbance dare da rana.


A wata hira Shaikh Zakzaky (H) ya ce; “(An tsare mu) a wani wuri wanda yake shi wannan wurin ba akan gane dare ko rana ba, amma wani lokaci akan fito da mu (dan suna yarda mutum ya yi wanka sau xaya a mako), sai a fito da mutane wajan su hamsin duk a wuri xaya, a sa musu bokitai (su tuve su yi wanka), sai su ga ni ban fito ba saboda suna yin tsirara, har wani ya ce mun; kai ba za ka yi wankan ba ne? Sai na yi masa shiru, sai ya ce; oho, don kai musulmi ne ko? To, sai ya yarda ni in dinga yin wankana ni kaxai” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 16).


Saboda tsabar tsarewar da aka yi ta yi wa Shaikh Zakzaky (H), an haifi uku daga cikin ‘ya’yansa ne a lokutan da yake tsare a gidajen kurkuku, misali, an haifi xansa Muhammad ne yana kurkukun Kirikiri a Lagos, an haifi Nusaiba yana kurkukun Kaduna, an haifi Hammad yana kurkukun Fatakwal. An sha azabtar da shi da nau’o’in azaba a kurkuku, wanda wasu azabobin har yanzu tasirinsu yakan motsa a jikinsa daga lokaci zuwa lokaci.


YUNQURIN KASHE SHI :


Bisa lura, za mu ga an samu tazara mai yawa ta kimanin shekaru 17 (1998-2015), (wato tun fara aiwatar da mulkin farar hula na jamhuriya ta uku) ba a kama Shaikh Zakzaky (H) ba sai a qarshen shekarar 2015, wanda wasu ke ganin kamar an qyale shi ne; “A a, sun lura ne cewa duk kame-kamen da aka yi wa Sayyid Zakzaky a baya, ya daxa havaka abin da yake kira akai ne. Bisa asasin haka, sai suka ga cewa wannan kamun da xauri bai da wani anfani ga manufarsu, saboda haka sai suka canza salo da kuma makirci.


“Wannan sabon salon shi ne yunqurin kashe Sayyid Zakzaky (H). Shi ya sa in muka duba a cikin waxannan shekaru da aka samu tazara na rashin kama Malam, babban abun da suka sa ma gaba shi ne kashe Malam xin ko ta halin qaqa! Za mu ga sun yi qulle-qulle da makirce-makirce iri-iri domin su cimma wannan manufa tasu, amma Allah Ta’ala bisa ikonsa duk ya wargaza shirin nasu!” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 22).


 Misali; Shugaban qasar Nijeriya a Alhaji Ummaru Musa Yar’adua a shekarar 2008 ya bada umarnin kashe Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) cikin mako uku, amma sai Allah Ta’ala ya tona asirin shirin, wanda daga qarshe ya wargaje sakamakon kamuwa da mummunar jinyar da Yar’aduwan ya yi, wacce ta yi ajalinsa cikin qanqanin lokaci.


Bayan mutuwar Yar’adua, sai aka rantsar da shugaban qasa Goodluck Ebele Jonathan, sai shi ma ya xora a inda Yar’adua ya tsaya kan batun kashe Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), inda jami’an tsaron gida da haxin gwiwar na qasashen waje (musamman Amurka da Isra’ila) suka duqufa ka’in da na’in na ganin sun kashe Shaikh Zakzaky (H). Sun yi ta tsara hare-hare da nufin kashe shi a hanyarsa ta zuwa Hussainiyyah Baqiyatullah ko a gidansa ko a hanyarsa ta zuwa wa’azi wani gari, amma Allah Ta’ala ya riqa wargaza duk qulle-qullen nasu yana ba shi kariya, har ta kai ga a cikin duhun wani dare na shekarar 2012 sun zo da wani jirgin sama da zai yi ‘Bombing’ xin gidan Shaikh Zakzaky (H), amma Allah ya hana su ganin gidan, suka yi ta shawagi suka koma.


Haka nan, a shekarar 2012 gwamnatin Jonathan ta ba fitaccen kamfanin kisan kai (Assasins) na wani shararre kuma qwararren makashi mai suna Patrick Williams kwangilar kashe Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). Kanfanin mai mazauni a Amurka kwararre ne a fagen kashe mutane a duniya. Lokacin da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya samu labarin wannan shiri, ya yi jawabi ga ximbin jama’a a filin Idi na birnin Zariya lokacin rufe muzaharar maulidi ta 17 ga watan Rabi’ul Auwal na shekarar 1433. A ciki yake cewa, “Na farko, kai Patrick Williams sai in ce maka ‘Raina yana hannun Allah ne ba yana hannunka ba ne!’ Kuma Allah Ta’ala na yi imani da shi, ya ce “Ba ya yiwuwa ga rai ta mutu sai da izinin Allah, abu ne yankakke rubutacce!”. 


Haka nan, a farkon shekara 2015, qwararrun ‘yan ina da kisa daga cikin sojojin Amurka da aka xauko hayarsu musamman don kashe Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), sun xana masa tarko a hanyar zuwa Hussainiyya inda ya saba gabatar da Tafsiri, amma sai Allah Ta’ala ya aiko da ruwan sama mai tsanani ya wargaza shirinsu.


QOQARIN HALAKA SHI A KURKUKU :


A wasu kurkukun da aka tsare Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) an yi ta haxa shi da qwararrun makasa da masu shaye-shaye da mahaukata, (duk dai dan su kashe shi, sai su kuma hukumomi su fake da cewa hatsaniya ce ta haxa shi da wani a kurkukun suka yi faxa har ya kai shi ga rasa ransa).


Misali; A kurkukun Sakkwato, an haxa shi da wani qwararren xan ta’adda, wanda kuma xan sanda ne na ‘Mobile Police’, wanda shaye-shaye ya juyar masa da qwaqwalwa, ana kiransa Jasper, qato ne qaqqarfa. Da Shaikh Zakzaky (H) yake magana game da Jasper ya ce; “Ya tava xaukar Alqur’aninmu haka, sai muka ce masa; kai Alqur’ani ne, sai ya wurgar! Kuma sai ya kama gilas xin ido na wani xan uwa da bai gani sosai, kafin ka ce haka ya mutsuttsuka shi ya watsar… kuma sai kawai ya malala fitsari (a cikin xakin da muke), kuma in ya doki bango sai ka ji ya yi motsi! Haka dai Allah ya kiyaye mu, amma mun zauna tare da shi a xaki xaya” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 16).


Shaikh Zakzaky (H) ya sake bada labarin wani mahaukaci da aka haxa su zama a wani kurkuku, ya ce; “Haka kuma wata rana aka zo da wani tuburan, ina ga shi mahaukaci ne ma tuburan sosai xaure cikin sarqa a qafafunsa, …To, haka dai (muka zauna) ya yi ta haukatakunsa, har kashinsa yana ci, sai ya xauko fo wai zai yi kashi ya ci in gani, sai na ce masa in ka kuskura zan mangareka, to, sai na nuna masa nima mahaukaci ne, na ce masa ina fasa kan mutane! To, sai ya ji tsoron fasa kai xin, to yadda na qwaci kaina kenan, daga baya dai Alhamdulillah aka xauke shi, ban san inda aka kai shi ba”. (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 17-18 da Tasarrufi).


A kurkukun Fatakwal kuwa, an haxa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a xaki xaya da wani qwararren xan ina da kisa na CIA, Ba’amurke ne baqar fata, yana kiran kansa “Jew” wato Bayahude, amma a kurkukun suna ce masa Tony ko Sony, kuma ya daxe a hukumar ta CIA yana aiki, har ma ya tsufa. Ya yi aikin leqen asiri da na kisan kai a qasashen duniya da dama, a wata hirarsu ya faxawa Shaikh Zakzaky cewa; Bari in gaya maka gaskiya, ni an bani kwangila na kashe mutane da yawa, kuma har yanzun akwai waxanda aka ce in kashe su, kuma zan kashe sun!” Shaikh Zakzaky (H) ya ce; Ko saboda ni suka kawo shi, wallahu’a’alamu, to in ma don ni ne Allah Ta’ala dai ya hana shi (zartar da mummunar manufarsa), bai samu cimma burinsa ba” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 19-20, bisa taqaitawa).


AZABTAR DA SHI :


Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya fuskanci jarabawowi na azabtarwa a hannun azzaluman mahukunta a lokuta daban-daban a tsawon wannan Da’awa tasa ta Harka Islamiyyah. Za a iya wallafa manyan littattafai akan zallar azabtarwar da ya sha da irin jarabawowin da ya fuskanta a hannun hukumomin Nijeriya, amma bari mu xan yi tsokaci kawai a matsayin misali.


Duk da cewa Shaikh Zakzaky (H) ma’abucin tsabta ne da tsananin qin datti da dauxa, amma da aka kama shi a Sakkwato cikin shekarar 1981 aka tsare, an hana shi yin wanka da wanki na tsawon makwanni masu yawa, a wani jawabinsa yana cewa; “Lokacin da muke tsare a Sakkwato, an haxa mu Sel guda da mahaukaci, an buqatar da mu ga rashin wanka na makwanni, wankanka shi ne ka xauko hannunka ka mulmula dauxa ka jefar, muka yi makwanni a haka, ba wanka ballantana wanki, riga ba ta sawuwa sai dai na dole”. (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 213).


A wani misali da yake bayarwa na jarabawar da ya fuskanta a gidajen kurkukun ya ce; “An buqatar da ni tare da wasu ‘yan uwa da muke tsare ga qwarqwata a jiki tare da kuxin cizo, ko’ina ka shafa a jikinka kuxin cizo ne da qwarqwata, har ta kai ma lokacin da aka kai ni kurkukun Inugu sai da aka yi min aski qwalkwabo, domin duk qwarqwata ta cinye kan! Kuma an buqatar da ni zama da faxe (takalma irin na danqo), ina ta yi masa faci har shekara uku, kuma an buqatar da ni a kurkukun Inugu in yi wanka ba sabulu har tsawon wata shida, kuma ba man shafawa, har jini na ketowa (a jikina saboda bushewar fata)” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 214).


Sannan an tsare Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a kurkukun Kirikiri dake Legos tsawon watanni, shi Kiriri wuri ne na azabtarwa da sunan bincike, akwai karikitai na azabtarwa iri-iri a wurin. Shaikh Zakzaky (H) ya ce ko sauro ka kashe a Kirikiri sai an yi maka bulala, wai kana kashe yaran gwamnati, kuma hatta tufafi riga da wando ba a yarda mutum ya shiga da su ba, sai dai a shigar da mutum daga shi sai Pant.


Lokacin da aka kai Shaikh Zakzaky (H) suka ce ya tuve tufafinsa, ya ce wannan kam ba zai yiwu ba, dole da tufafinsa zai shiga, su kuma suka ce bai isa ba! suka kama shi da kokawa za su tuve masa tufafi da qarfin tsiya, kawai sai jinsa ya yi a cikin xakin tare da tufafinsa, dole suka haqura suka qyale shi da tufafin, har waxanda ya samu a cikin wurin suna ta mamaki, shi kansa Shaikh Zakzaky (H) yana cewa yana ganin shi ne mutum na farko da ya shiga Kirikiri da tufafi a jikinsa.


A Kirikirin akwai wani sashen azabtarwa na musamman, wanda sel ne a qarqashin qasa, a wajan ba a gane banbancin dare da rana, wuri ne mai tsananin duhu, wanda ko tafin hannunka ba za ka iya gani ba, a cikin wurin aka cusa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) na tsawon lokaci, Shaikh (H) ya bada labarin wurin a wata laccarsa, ya ce; “A wancan lokacin yadda na riqa yi nike gane lokutan Sallah shi ne; Suna kawo abinci da rana, in za su kawo abincin to gab da Azuhur suke kawowa, to in na ci da yake kofin ruwa guda xaya ne za a ba mutum, to sai in sha rabi in yi Alwala da rabi.


“To, sallar Magriba yadda nike gane ta shi ne, in an kawo abincin yamma, saboda galibi sukan kawo (abincin) gab da Magriba ne, to jim kaxan sai in yi sallar Magriba. To, sallar Asuba ba yadda za a yi in gane, yadda nikan yi wani lokaci (shi ne), in na yi sallar Asuba bisa tsammanin ta yi, sai in zauna in yi ta yin Azkar har lokacin da suka zo da safe suna qwanqwasa qofa suna tambayar mutum nawa ne cikin wannan xakin, to qarfe bakwai ne suke wannan, to sai in yi ‘Estimate’ (in qiyasta) daga lokacin da na zauna zuwa yanzu an yi awa nawa? To wani lokaci sai ta bayyana na yi sallar asubar ne qarfe ukku na dare, ko ma qarfe xayan dare” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 136).


Haka nan a waqi’ar Maulud ta 2015 wadda sojoji suka kashe almajiransa kusan mutum Dubu kafin su kai gare shi, da suka isa xakin da yake ciki suka yi masa ruwan wuta, harsashi ya farfasa jikinsa har sai da idonsa na hagu ya zazzago ya fito waje, shi ya kama idon ya mayar da kansa, idon dama kuma harsashi ya sauqa a samansa shi ma ya samu matsala.


An yi masa harbi a wurare daban-daban aqalla goma sha xaya a jikinsa, suka xauke shi ba rai suka tafi da shi, sai bayan kwana 4 Allah Ta’ala ya dawo masa da ransa ya farfaxo. Tattare da cewa bayan tsawon lokaci ya yi ta samun sauqin raunukan da aka masa, amma idonsa na hagu yana masa tsananin ciwo da zogi, ta kai ga ba ya iya karatun Alqur’ani saboda ba ya ganin rubutun, kuma a hakan gwamnati ta hana a fita da shi waje don yi masa aikin idon, burin da jami’an tsaro ke da shi shi ne lalacewar duk idanuwan nasa guda biyu.


Wannan kaxan kenan daga gallzawar da Shaikh Zakzaky (H) ya sha a hannun azzalumai, a taqaice, Shaikh Zakzaky (H) ya fuskanci jarabawowi na azabtarwa sosai daga vangaren azzaluman mahukunta, sun sha kama shi da xaure shi da gallaza masa ta hanyoyin azabtarwa daban-daban, amma tattare da haka bai tava saranda ko miqa musu wuya ba, hasali ma qarin yaqini da sabati yake samu akan abin da ya sa a gaba na ceto al’umma daga qangi.


YUNQURIN KASHE SHI :


Allah ne kaxai ya san iya yawan yunqurin da aka yi ta yi na kashe Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a lokuta da wurare daban-daban, kama daga yunqurin kisan gilla na zahiri zuwa kisa ta hanyar sihiri da tsatsuba. A matsayin misali, ga jerin yunqurin kisan da aka yi masa wanda suka bayyana a zahiri.


NA FARKO : Yunqurin kashe Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) karo na farko da ya bayyana shi ne wanda aka shirya shi tun Shaikh xin yana xalibta a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, wato farko-farkon Da’awarsa, wanda aka shirya yin anfani da wasu xalibai da za su je xakin da yake cikin dare su kashe shi, an samu labarin wannan shiri ne daga wani xalibi mai suna Alpha Bolaji.


NA BIYU : Yunqurin kashe Shaikh Zakzaky (H) da gwamnatin Ibraheem Babangida ta yi a lokacin da aka kai shi Kirikiri a 1992, lokacin an shirya za a yi masa kwaf xaya ne kawai a gama da shi, to amma sai Allah ya wargaza shirin, sai suka sake shi da gaggawa.

NA UKU: Yunqurin kashe Shaikh Zakzaky (H) da ‘yan Tawayiya suka yi, bayan sun rutsa shi a masallacin Jami’ar Bayero dake Kano, a shekarar 1994.


NA HUXU : Yunqurin kashe Shaikh Zakzaky (H) da gwamnatin Abacha ta yi a shekarar 1996 a kurkukun Kaduna, inda aka shirya kashe shi ta hanyar allurar mutuwa kamar yadda aka yi wa Janar Shehu Musa Yar’adua a lokacin.


NA BIYAR : Yunqurin kashe Shaikh Zakzaky (H) da gwamnatin farar hula ta Ummaru Musa Yar’adua ta yi a shekarar 2010, wacce ta tsara “Bombing” xin gidan Shaikh da kashe duk waxanda ke cikin gidan, an samu kwafin “BluePrint” ne na umarnin yin hakan.


NA SHIDA : Yunqurin kashe shi da hukumar CIA ta Amurka ta yi a ranar bikin cikarsa shekaru 63 a duniya cikin shekarar 2014, wanda suka turo qwararrun makasa jar fata rufe da fuskokinsu da “Mask” irin na “Ku Klu Klax”. Suka voye a hanya da nufin aiwatar da mummunan nufinsu, amma sai Allah Ta’ala ya aiko da ruwan sama mai tsanani ya rusa shirinsu.

NA BAKWAI : Yunqurin kashe Shaikh Zakzaky (H) da gwamnatin Ebele Jonathan ta yi ta yi a shekaru biyunta na qarshe (2013-2015), wanda a qarshe suka yi nasarar kashe ‘ya’yansa uku a shekarar 2014 a madadin gagararsu kasuwa da ya yi.


NA TAKWAS : Yunqurin kashe shi da gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi a qarshen shekarar 2015, wanda ya janyo kashe almajiransa maza da mata kusan mutum Dubu da ke ba shi kariya, da kuma yi masa ruwan harsashi a goshinsa da qirjinsa da cinyoyinsa a qoqarinsu na halaka shi, amma Allah ya raya shi da ikonsa.


Waxannan sune yunqure-yunquren kashe Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da aka sha yi, wanda suka bayyana a fili qarara kamar hasken rana, wanda duniya ta shaida kuma ake da dalilai da hujjoji na zahiri a kansu. Amma kamar yadda muka faxa a baya, ba suke nan ba, yunqurin kashe Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) Allah ne kaxai ya san iyakarsa, mun ambaci fitattu ne kawai a matsayin misali.

✳✳✳ ✴✴✴ ✳✳✳

BABI NA SHIDA

NASARORI DA XAUKAKAR SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY (H)

KEVANTATTUN NASARORINSA :


Baki bai isa ya iya faxin dukkanin nasarorin da jagoran Harka Islamiyyah a Nijeriya Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya samu a rayuwarsa ba, haka nan, alqalami ba zai tava iya rubuta waxannan nasarori ba, domin sun fi qarfin iyakancewa balle kewayewa da sani, amma tunda tsokaci muke yi akan komai na rayuwar jagoran, wannan ma bari mu yi tsokaci kaxan akai.

NASARA TA XAYA: Nasara ta farko da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya samu a rayuwarsa ita ce Shiriya! Babu shakka Allah Ta’ala ya so shi ya zave shi ya kuma fifita shi da shiriya a birbishin sauran malamai. A duk tarihin Shaikh Zakzaky (H) bai tava yin riqo da tafarkin vata ba, ya fito ne daga tsatso mai daraja, gida na malamta, zuriyya ma’abuciyar addini, da kuma tarbiyya ta gari. Duk wata nasara da xan adam ke samu a rayuwa a bayan shiriyar Ubangiji take.


NASARA TA BIYU : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi nasarar canza rayuwar ximbin mutane daga vata zuwa shiriya, daga kuskure zuwa ga daidai, ya ‘yanto tunanin mutane daga ximuwa zuwa tunani mai kyau, ya raya zukatan da suka mutu, ya farfaxo da waxanda suka suma.

Ta sanadin Da’awarsa da dama daga masu aqidar kwaminisanci sun canza zuwa aqidun Musulunci, masu kwana barci sun koyi raya dare da Tahajjud, masu yini cin abinci sun koyi azumomin nafilfili, masu mugayen xabi’u sun canza zuwa kyawawa, masu rowa sun koyi kyauta, masu son kai sun koyi Iythari, mata masu tabarruji sun koyi suturtuwa da Hijabi, mazajen da ke wulaqanta mata sun koyi mutuntasu, matsorata sun zama jarumai, jahilan addini sun zama malamai, ‘yan Malikiyya sun zama ‘yan Ja’afariyyah, nasarar Shaikh Zakzaky (H) wajan sauya al’umma ba ta qidayuwa!


NASARA TA UKU : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi nasarar canza Miliyoyin mutane daga aqidar Sunnanci zuwa na Shi’anci, wanda tarihi bai tava ganin irinsa ba. Domin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne kawai mutum xaya tilo da aka yi qiyasin ya yi nasarar canza sama da mutum miliyan Ashirin da Biyar (zuwa yanzu a nahiyar Afirka) daga aqidar Ahlis-Sunnah zuwa tafarkin Ahlul-Bait (AS). Wannan irin nasara tarihin xan adam bai tava ganin irinta ba tun bayan bayyanar Shi’anci a bayan qasa.

Batun

1 Comments On SHAIKH ZAKZAKY IKON ALLAH
avatar
shuraihu-usman-1

1 year ago

Reply

sss

Please Login or Register in order to submit comment