Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya wanke masa; “A bisa al’adarsa, yakan jiqa wanki a bokiti tun safe, sai da yamma sai ya wanke, to in ya jiqa ya fita sai in wanke in shanya masa kafin ya dawo, sai ya yi mun magana cewa ba buqatar hakan, to amma ni sai na kasa bari. Washegari da ya jiqa sai na sake wankewa na shanya, da ya dawo ya gani sai bai ce komai ba, bayan kwana biyu da wankin ya sake taruwa, da ya jiqa sai ya xau bokitin ya shigar da shi cikin falonsa ya kulle, ala tilas na haqura ina gani yana wankinsa da kansa, a garin wannan wankin da yake yi ne ma ya tava samun hatsari da bokiti har ya karye a hannu”.

Shi ma Malam Nuraddeen Aliyu Alqaleri (xaya daga cikin almajiran Shaikh Zakzaky) ya labarta mana cewa; “A lokacin da Shaikh ke zaune a unguwar Kwarbai a Zariya, na tava zuwa na same shi yana xibar ruwa a bokiti daga Zawiyya yana kaiwa gidansa, sai na je zan karva, na yi na yi in karva amma ya hana ni, ya ce; “Ba damuwa, na gode!”, ya ci gaba da xiban ruwansa da kansa”.

Shaikh Zakzaky (H) yana ban ruwa ga filawowin gidansa da kansa, kuma yana bawa tsuntsayen gidansa abinci da kansa, kamar yadda yake shara da dafa abinci ga iyalinsa. Tabbataccen abu ne cewa zurfin tawali’un Shaikh (H) ya kai ga yana yin aikace-aikacen da suka shafe shi ne da kansa, kama daga wanki, xiban ruwa, shara, renon yara, har ma da dafa abinci. Wannan yana nuna sauqin kai da qanqantar da kai irin na Shaikh (H).

ZUHUDUNSA :

Kamar yadda yake qa’ida cewa, duk wani Malami na Allah ba a rasa shi da zuhudu (wato gudun duniya, ko xaukar duniya ba a bakin komai ba), to shi ma Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) haka yake, zahidi ne da dukkan ma’anar zuhudu, domin dukkan xabi’unsa na zuhudu ne, tattare da irin yanayi na qasa da al’ummar da yake rayuwa a cikinta.

Ga wanda ya san haqiqanin rayuwar da Shaikh Zakzaky ke yi, ya san cewa bawan Allah ne mai zuhudu, ga abin da xaya daga cikin manyan xalibansa ke cewa; “La’alla za ku ga Malam haje-haje da shaddodi, ga mota Marsandi (ko Jif), sai mutum ya zaci ko Malam baida zuhudu, ka tambayi na kusa da shi ka ji, sai a kwana uku ko huxu ba a hura wutar dafa abinci a gidan Malam ba, ba a samu abin da aka xan tava ba, ba kuma za ka gane ba, kuma har yanzu ma maganar nan da muke yi wani lokaci haka ne!” (Malam Zakzaky: Rayuwarsa da Karamominsa, shafi na 10).

Xaya daga cikin almajiran Shaikh Zakzaky (H) ya tava labarta cewa; “Wata rana ya samu Rogo, sai ya ga ya kamata ya kai gidan Malam, da ya kai Rogon sai Malam yake cewa; “Allah ya saka da alkairi, yau kwana uku kenan gidan nan ba wani motsi”. (Malam Zakzaky: Rayuwarsa da Karamominsa, shafi na 10).

“Kuma sau xaya yake cin abinci a rana, wannan ko ka yarda ko kar ka yarda haka ne, musamman ma mafi yawancin lokuta ranar Juma’a, sai wajan qarfe uku sannan ya karya kuma sai gobe, in kuma tafiya za a yi, za a tafi tunda safe kamar qarfe shida, to ko ma ina ne za a, Malam ba ya karyawa sai an je wannan garin, ko za a kai faxuwar rana ne!” (Malam Zakzaky: Rayuwarsa da Karamominsa, shafi na 10).

Marubucin littafin ‘Malam, Malam Ne’ yana cewa; “Malam shi ko abinci bai dame shi ba, don sau da yawa Malam a gida yakan yi wasu kwanaki bai ci abinci ba. Na san wata rana za mu je Maulidi da daddare, sai ya ce; “Ku xan jira ni in jefa wasu ‘yan lomomi, saboda rabo na da abinci tun shekaran jiya”. (Malam, Malam Ne, shafi na 15).

“Sannan Malam a gidansa a xakinsa ba ya da katifar da yake kwanciya, ba kuma don bai da kuxin da zai saya ba ne, amma dai shi ba ya zo kwanciya (a duniya) ba ne!”. (Malam Zakzaky: Rayuwarsa da Karamominsa, shafi na 10).

Marubucin littafin ‘Malam, Malam Ne’ yana cewa; “Malam Zahidi ne mai gudun duniya, ba ka bi na bashin rantsuwa, amma Wallahi! Malam bai da ko katifa a xakinsa na kwana balle Gado! A qasa yake kwana. Da ya je ziyara wata jaha a arewa maso yamma, sai Gwamna ya je masaukin Malam da sassafe don ziyara, da gwamna ya shiga xakin da Malam ke kwance, sai ya tarar da shi kwance a qasa, wannan abu ya yi wa gwamna tasiri ba kaxan ba, shi ganau ne ba jiyau ba, ya ce; “Wannan irin sauqin kai haka!”. (Malam, Malam Ne, shafi na 28).

“Wani mai kuxi ya yi wa Shaikh Zakzaky (H) tayin gina masa gida mai kyau, sai Shaikh ya ce shi ba ya fatan ya bar komai (na duniya) wanda wani xansa zai gada. Fulotin da xan uwan ya ba shi ma, sai ya ce ba nasa ba ne, na al’umma ne, ko ya mutu ‘ya’yansa ba su da gado akai, to, ka ga ni fa!” (Malam Zakzaky: Rayuwarsa da Karamominsa, shafi na 11).

Akwai lokacin da a wani jawabi (Shaikh Zakzaky) yake cewa; “Duk wanda ya fuskantar da zuciyarsa ga Allah Ta’ala, zai ga komai (na duniya) wulaqantacce ne, zai ga sutura wulaqantatta ce, zai ga komai a wulaqance, kai, duniya baki xaya ba za ta kai darajar fuffuken quda a wajensa ba”. (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 32).

“(Shugaban qasa na mulkin soja), Janar Ibrahim Babangida, ya shahara da rufe bakin Malamai da kuxin rashawa, watarana sai ya tura wa Shaikh Zakzaky (H) saqon magudan kuxi, amma sai Shaikh (H) ya yi musu gatse irin yadda Annabawa da Mujaddadai suke wa Xagutai. Ya dubi kuxin ya cewa wanda ya kawo saqon; “Ai kuxin ba su kai yadda suka ambata ba”, wanda ya kawo saqon jiki na rawa ya ce; “Wallahi Malam ba a tava komai a ciki ba”, sai Shaikh (H) ya ce; “Na duba ne ban ga Aljannar Allah a cikin abin da ka kawo ba”. Nan take xan saqo ya gane abin da Shaikh (H) ke nufi, sai ya ce; “Allah gafarta Malam, wannan kam babu”, sai Shaikh (H) ya ce; “To, a maida masa abinsa tunda babu Rahamar Allah a ciki, dama ni ita nake nema”.

Xan saqo ya kwashi saqon Ubangidansa cikin kunya da qasqanci, yana tambayar kansa ashe akwai Malamin da zai qi kuxi irin wannan?”. (Jaridar ALMIZAN, bugu na 1256, shafi na 21.).

Wani abu da zai qara nuna mana zuhudu da tsantseni na Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) shi ne; wata rana ya yi tafiya zuwa wata qasar waje, bayan ya kammala abin da ya kai shi, da zai dawo gida sai ya je qaton shagon sayayyar kayayyaki na komai da ruwanka, wato “Super Market” don siyo tsaraba da sauran kayayyakin da yake buqata. Ashe lokacin da ya shiga “Super Market” xin wani daga cikin almajiransa na qasar ya gan shi, sai almajirin nasa ya zaga wajen mai karvar kuxi na “Super Market” xin wato “Cashier” ya ba shi katin cirar kuxi na ATM xinsa, ya ce masa “Duk abin da Malamin can ya xauka, ku yi lissafi ka cire a akawunt xina, kar ka karvi ko kwabonsa”, sai ya juya ya fita ya tafi don ma kar Shaikh (H) ya ganshi.

Shi kuma mai kula da shagon “Super Market” da yake yana so ya yi babban ciniki, sai ya je ya samu Shaikh Zakzaky (H) ya ce masa; Ya Shaikh, wani mutum ya biya maka kuxin duk abin da za ka xauka, dan haka ka kwashi duk abin da kake so!” Da Shaikh (H) ya ji haka, sai ya fasa sayan duk abubuwan da ya zo da niyyar saya, ya xauki abin share zufa “Handkerchief ” guda xaya rak, ya je wajan “Cashier” ya ce; “Ga iyaka abin da nake buqata!” Mai shago ya ce; “Yallavai ko ba ka fahimci bayanin da na yi ma ba ne?” Shaikh (H) ya ce masa; “Na fahimta sosai”, sai mai shago ya buxe baki yana kallon Shaikh Zakzaky (H) yana mamaki!

Ataqaice waxannan abubuwa suna nuna yadda Shaikh Zakzaky (H) ya xauki karikitan duniya a matsayin shirme, tattare da cewa a zahiri yana mu’amala da wasunsu, amma baida “Ta’alluq-Qalbiyya” wato xanfara zuciya garesu.

TAWAKKALINSA :

Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) mutum ne mai matuqar tawakkali ga Allah Ta’ala da siqa gare shi, duk wanda ya san zantukansa, to ya san shi da yawan maida al’amarinsa ga Allah. A farkon-farkon Da’awarsa, wani malami ya tava ce masa wannan Da’awa da yake yi gara ya dena ta ya nemi wani abin yi, domin abin da yake kira a kai na kafa gwamnatin musulunci, abu ne da ba zai tava yiwuwa ba samsam!

Sai Shaikh Zakzaky (H) ya ce masa; “To, kana nufin akwai abin da ya gagari Allah ne, wanda shi wannan abin Allah ba zai iya yinsa ba samsam? Da ma ba cewa na yi ni ne zan yi ba, cewa na yi Allah Ta’ala ne zai yi, in kuma akwai abin da ya gagari Allah to ka faxa mani!” wannan amsa tana nuna zurfin siqar Malam da Allah Ta’ala ne.

Wani abu da zai qara nuna mana zurfin tawakkalin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da tsananin dogaronsa ga Allah shi ne, a shekarar 2014, lokacin da Jami’an leqen asiri na Nijeriya da haxin gwiwar na qasashen waje suka tsananta xane-xanen tarko na qoqarin kashe shi a hanyarsa ta zuwa Hussainiyya wurin karantarwarsa, sai almajiransa na “Dandalin Ahlid-Duthour” suka zartar da shawarar saya masa motar da harsashi ba ya hudawa (Bullet-Proof) don samun kariya daga harsashin maqiya. Har sun tuntuvi kanfanin sayar da motocin a qasar Jamus, sun ma yi ciniki sun gama za su biya, sai labari ya iske Shaikh Zakzaky (H) kan wannan yunquri da sashen almajiransa ke yi na saya masa motar da harsashi baya hudawa don sama masa kariya.

Sai Shaikh (H) ya ce musu; Lallai yana godiya bisa yunquri na bada gudunmawarsu ta kariya a gare shi, Allah Ta’ala ya saka musu da alkairi, amma ba buqatar saya masa mota “Bullet-Proof”, domin Allah Ta’ala ne mai kariya kuma yana nan, Insha Allah zai ci gaba da karewa har zuwa wa’adi”. A haka ya rufe wannan batu na saya masa mota “Bullet-Proof”. Babu shakka wannan matsaya ta Shaikh (H) zai nuna mana zurfin tawakkali da tsagwaron dogaronsa ga Allah!

A shekarar 2015 jami’an tsaron Nijeriya da haxin gwiwar na Amurka da Isra’ila sun tsananta xana tarko na qoqarin buxewa Shaikh Zakzaky (H) wuta a hanyarsa ta zuwa zaman makokin Ashura na tsawon kwanaki 50 da yake gabatarwa a “Hussainiyyah Baqiyyatullah” da ke birnin Zariya, don ganin sun kashe shi ko ta halin qaqa.

Sun yi ta xana tarko don cimma wannan buri nasu, to amma sai Allah ya yi ta kunyata mummunan shirin nasu, duk lokacin da suka ajiye ‘yan ina da kisa akan hanyarsa, sai ya zo ya wuce ba tare da sun yi la’akari ba. Sai suka qara yin wani mummunan shiri na musamman, suka tsara ajiye makasa a wurare da dama, ta yadda in ya wuce waxannan to ba zai wuce na gaba da su ba.

Da rahoton hakan ya zo ga Shaikh Zakzaky (H), sai ya yi jawabi ya fallasa shirin nasu, sannan ya tabbatar musu cewa; “Zan ci gaba da zuwa zaman makokin Ashura sai na kai har qarshen watan! Zan nuna muku cewa; AKWAI UBANGIJIN DA KE KARENI! Ba zan tava fasawa ba! kuma hanyar da nake bi nan zan dunga bi (ba zan canza ba)!” (Yaumus-Shuhada, 1436-2015). Mai karatu, kalli zurfin tawakkalin Shaikh a wannan matsayar!

Haka nan, a lokacin waqi’ar 2015, bayan sojoji sun kashe xaruruwan almajiran Shaikh Zakzaky (H) da ke ba shi kariya, sun tunkaro gidansa, sai xansa Shahid Hammad ya shiga wajansa ya ce masa; “Mun qiyasta cewa nan da awa xaya sojoji za su shigo cikin gidan nan”. Sai Shaikh Zakzaky (H) ya ce masa; “Mu wannan ba a hannunmu yake ba, mu abin da ke kanmu shi ne mu dogara ga Allah kawai, ba mu san me zai faru nan gaba ba, namu shi ne mu yi iyakar qoqarinmu, kuma mu dogara ga Allah, amma batun yaushe sojoji za su shigo, ba namu ba ne, saboda haka duk wanda ba ya wani abu musamman na taimakawa, to ya ci gaba da addu’a kawai”.

Zuwa xan lokaci kaxan sojoji suka iso qofar gidansa suna kisa ba ji ba gani, sai sashen almajiransa suka shiga wajansa suka nemi ya amince su fita da shi ta baya don tseratar da shi daga mummunan nufin sojojin; sai ya yi murmushi, ya ce “Ai ba batun gudu ko vuya, su yi iyakar nasu qoqarin, mu kuma mu dogara ga Allah… in Allah ya tsara mutanen nan za su shigo su qarasa mu ne, to shi ne nasararmu, idan kuma ya kasance za su tsaya ne, to haka Allah ya tsara. Mu dai muna neman afuwa ne a wajen Allah, kuma mu yi addu’a da tunanin muna neman afuwa a wajen Allah. Idan Allah ya tsara zai bar mu mu ci gaba da aiki a tafarkinsa, za mu tsaya, idan kuma za mu tafi ne (mu yi Shahada), to hakan ya tsara mana”. (Jaridar ALMIZAN, bugu na 1240, shafi na 7).

Ana cikin haka, sai wani ya kira shi a waya daga qasar Iran don jin halin da yake ciki, sai ya ce shi yana cikin gidansa bai je ko ina ba, kuma anan zai tsaya ba zai je ko ina ba, Allah ne kawai zai kare shi! “Only Allah Alone Can Deliver me!” Lallai waxannan zantuka na Shaikh Zakzaky (H) suna nuna zurfin tawakkali da maida al’amuransa zuwa ga Allah Ta’ala ne a kowane yanayi.



YAQINI DA SIQARSA :


Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) mutum ne mai tsananin yaqini da siqa ga Allah Ta’ala. Yawancin marubuta da manazarta rayuwar Shaikh Zakzaky (H) suna jinjinawa da qarfafa batu akan zurfin yaqini da siqarsa ga Allah Ta’ala.

A mafi yawan jawabansa yana tabbatar da cewa ba wanda ya isa ya dakatar da tabbatar addinin musulunci, wato duk da tinqaho da qarfin kafircin duniya, bai isa ya hana kafuwar addinin Allah a wannan zamanin ba, domin a yanzu Allah ya ga damar addini ya xago. A wani jawabinsa na “Yaumul-Arba’in” yana cewa; “Su (azzalumai) suna ganin za su iya hana Allah tabbatar da abin da ya so, saboda suna da bindiga sun iya kisa! To da kisa yana hana addini tabbata da tun a Karbala an kashe Musulunci!”


Haka nan, a jawabin “Yaumus-Shuhada” na 2015 yana cewa; Insha Allah kamar addinin nan ya kafu ma daram an gama!” Wato Shaikh Zakzaky (H) sam bai da shakku ko kokwanto akan tabbatuwar addini.


Wani abu ma da zai qara nuna mana siqar Shaikh Zakzaky (H) da Allah shi ne; A lokacin waqi’ar Abacha, yana tsare a gidan yari, sai mutanen gidansa suka aika masa cewa, masu gidan haya sun matsa musu cewa su tashi daga gidansu, (wato sun shiga halin da ake cewa halin Lahaula wala Quwata), amma amsar da ya ba su ita ce cewa, “Tunda ku ka ga an matsa mana akan gidan (haya), to insha Allah muna gab da mu soma ba da kyautar gidaje!”. (Malam, Malam Ne, shafi na 06).

Wannan yana nuna siqar Shaikh (H) da Allah ne, domin a lokacin da ake karanta masa tsanani, qunci, matsi, da qalubalen da ake ciki, shi kuma yana bushara da albishir na farin cikin da zai biyo bayan quncin ne! Wannan halin sai waliyyan Allah!


Yaqinin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) bai taqaita akan al’amuran yau da kullum kawai ba, a’a, hatta a ibadarsa yana yin ta ne da cikakken yaqini. A lokacin da gwamnatin Nijeriya ta sa hannu kan wani shirin kashe shi a shekarar 2009. Shaikh Zakzaky (H) ya yi nasiha ga almajiransa a qoqarinsa na kwantar da hankalinsu, a ciki yake cewa; “Alhamdulillah! Allah ya yi min wannan baiwar, na san ko mutum ya qi ni, in dai mun yi yarinta (tare), ya san tun ina yaro na taso ina ibada ne, kuma na san yau shekaru 40 cur ina ibada da YAQINI kamar ina ganin zahiri! Saboda haka tafiya in ta zo ‘Falillahil-Hamd’, an kashe waxanda suka fi ni!”. (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 176).


Wannan jawabi na Shaikh Zakzaky (H) ya nuna zurfin xanfaruwarsa da Allah Ta’ala, da irin siqa da yaqininsa cikin bautar da yake yi, ba mai iya faxin wannan magana in ba salihin bawa ba.


HAQURI DA JURIYARSA :


Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) mutum ne da aka shaide shi da haquri da juriya, misalan haquri da juriyarsa suna da ximbin yawa, amma ataqaice za mu bada misali guda uku kacal;


A tsawon shekarun Da’awar Shaikh Zakzaky (H), gwamnatin Nijeriya kai tsaye ko a fakaice ta hanun ‘Yan tauri, ‘Yan Banga, zauna gari banza, Sarakunan gargajiya ko ta hannun malaman Fada, sun sha rusa makarantun almajiransa a wurare daban-daban! An sha abkawa a raunata ximbin almajiransa a garuruwa daban-daban, an sha qona dukiyoyin mabiyansa ba iyaka a lokuta daban-daban, an sha xaurewa kuma ana ci gaba da xaure almajiransa a gidajen kurkuku daban-daban, an kori ximbin almajiransa a wuraren aikin gwamnati, an kori xalibai almajiransa daga manyan makarantun da suke karatu, an mayar da dubban ‘ya’yan mabiyansa Marayu, an mayar da dubban mata almajiransa Zawarawa, an mayar da ximbin masu arziqi a cikin almajiransa faqirai! Amma duk waxannan abubuwa da aka yi masa a tsawon waxannan shekaru kusan 40 bai tava ramawa ba, bai tava cewa almajiransa su xau fansa ba.


A shekarar 2014 sojojin Nijeriya qarqashin mulkin shugaban qasa Goodluck Jonathan bisa jagorancin Kanar M.S Oku suka kashe haziqan ‘ya’yan Shaikh Zakzaky (H) guda uku, tare da almajiransa guda 30, sun yi hakan ne da nufin su fusata Shaikh Zakzaky (H) su ingiza shi ga yin bore da tada hankali, amma sai Shaikh Zakzaky (H) ya yi bayani cikin natsuwa da mayar da al’amari ga Allah, ya lallashi almajiransa cewa kada kowa ya mayar da martani ko ya yi wani abu da sunan xaukar fansa.


An ce, a ranar da sojoji suka kashe ‘ya’yansa uku, labarin Shahadar biyu daga cikin yaran ya zo masa ne bayan sallar Isha, kuma adaidai lokacin da ya zauna don yin buxa baki da almajiransa. Ya tsiyayi ruwan shayi zai sha kenan sai wayarsa ta yi qara, yana xauka sai aka ji yana cewa “Innalillahi wa Innaa’ilaihi Raji’un!” ya maimaita sau uku.


Bayan ya sauqe wayar sai ya shaidawa almajiransa cewa an qara kashe ‘ya’yansa biyu Ahmad da Hameed, nan take gun ya kaure da kukan baqin ciki, amma shi Sheikh (H) babu ko xigon hawaye a idanunsa, ya yi shiru na tsawon lokaci bai motsa ba (alamun yana munajati da Allah), har ya tashi ya shiga gida ba a ga hawaye a fuskarsa ba, duk da tsananin so da qauna da shaquwar da yi da yaran nasa. Wannan juriya da ya nuna sai da ta zama abin tattaunawa a tsakanin almajiransa.


Shekara xaya rak bayan haka, wato a shekarar 2015, sai ga bataliyar sojojin Nijeriya qarqashin Janar Tukur Yusuf Burtai, sun zo Zariya takanas suka aiwatar da mummunan ta’addanci akan Shaikh Zakzaky (H) da iyalansa da al’majiransa, inda suka kashe xaruruwan almajiransa, suka qara kashe ‘ya’yansa uku maza, suka kashe yayarsa Goggo Fatimah, suka yi masa ruwan harsashi shi da matarsa Malama Zeenatu, suka qona gidansa bayan sun harbi gidan da Gurneti, suka rusa masa cibiyon karantarwarsa irin su Hussainiyyah Baqiyatullah, Darur-Rahma, Fudiyyah Islamic Center, da Hubbaren mahaifiyarsa da ke unguwar Jushi.

Sannan suka kama shi suka tafi da shi a mummunan yanayi, amma bayan ya farfaxo ya samu sauqi daga raunukan da suka yi masa, sai ga shi ya aiko gaisuwa da jinjina ga almajiransa da suka dake akan wannan tafarki na gwargwamaya. Kuma ya yi musu Wasiyya cewa su tsaya akan nizamin Harka Islamiyyah, kar a ce za a xauki fansa, kawai a ci gaba da abin da ake yi da kuma addu’o’in neman sakayyar Ubangiji. Wannan ya nuna yadda Shaikh (H) ke da zurfin haquri da qarfin juriya ne.


AFUWARSA :


Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) mutum ne mai yawan afuwa da shanye laifi, yana da yawan kauda kai da bada tazara. Duk wanda ya san shi zai iya bada shaida ga yawan afuwarsa, misali; A lokacin fitinar ‘yan Zuhudu, akwai waxanda suka yi (munanan) maganganu ga Shaikh (H), wasu ma suka yi rubutu. To, daga baya wasu sun farga (da kuskurensu), saboda haka sai suka zo wajen Shaikh (H) domin ya yi musu afuwa, sai ya yafe musu, shi ne ma lokacin da ya zo jawabin rufe Ijtima ya yi magana, a ciki yake cewa; Duk wanda ya san ya ce wani abu gare shi, ba sai ma ya zo ya ce ya yafe masa ba, shi ya yafe masa!” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 30).


Haka nan, wasu daga cikin almajiransa sun valle masa a shekarar 1993, suka yi masa tawaye, suka riqa sukarsa da aibata shi da yi masa qazafi da sharri iri-iri, amma da ya zo jawabinsa na cikar Harkar Islamiyyah shekaru 25 da kafuwa, sai ya ce; “Ina ‘yan Tawayiyya ku dawo! Duk wanda ya fita (daga cikin Harka Islamiyyah) to muna kiransa ya dawo, qofar da ya gani a wangale ya fita, to yanzu ma tana buxe a wangale ya dawo, in dai ni ne (game da qazafofi da cutarwar da kuka yi mani) na yafe!”


“Ka duba ka ga ‘yan Tawayiyya yadda suka cutar da Malam, kai sun yi niyyar kashe shi ma a masallacin Juma’a na Jami’ar Bayero da ke Kano, to amma Malam da me ya saka musu? Lokacin da ya je aikin Hajji, addu’a ya yi musu a Ka’aba, ya ce, “Ya Allah in waxannan suna da rabo a lahira, to ka dawo da su mu ci gaba da abin da muke yi tare, kuma ni na yafe musu duk abin da suka yi mini”. (Malam, Malam Ne, shafi na 16).


Haka nan, a wajajen shekarar 2010, an kawo wa Shaikh Zakzaky (H) muryar da aka naxa ta wani mutum da yake nuna yana tare da shi, amma a gefe kuma yake sukarsa yana aibata shi, yana faxin munanan maganganu akansa. Bayan Shaikh ya ji maganganun sai bai ce komai akai ba, ya kauda kai daga abin. Sai sashen almajiransa da ke tare da mutumin suka nuna rashin amincewarsu ga abin da mutumin ya yi, aka soma samun rashin jituwa a tsakaninsu har dai batun ya zo gabansa.


A jawabin da ya yi wa almajiran nasa ya nuna musu cewa, wannan abin da mutumin ya yi ba komai ba ne, “Na so a ce ni kaxai na ji waxannan maganganu da mutumin ya yi a kaina, da ba wanda zai san an yi su! Zan xaga qasan filona ne kawai in jefa kaset xin, ba wanda zai ji labari balle a samu rigima, domin ba shi kaxai ne ke irin wannan maganganu ba, suna da yawa, muna da labarinsu, amma ba mu tava cewa komai a kansu ba, mun kauda kai daga garesu, ba za su cutar da mu da komai ba, kowa yana aiki ne don kansa”. Wannan jawabi na Shaikh Zakzaky (H) yana nuna mana zurfin kauda kansa ga al’amura.


Sau da yawa in aka yi anfani da wasu wawayen mutanen gari suka abkawa ‘yan uwa, ko suka lalata dukiyar ‘yan uwa, sai Shaikh Zakzaky (H) ya ce, “In ba don tausayi ba, da sai mu yi musu addu’a” amma don gudun lalacewa da asarar lahirarsu, Shaikh (H) ba zai musu addu’a xin ba, sai dai ya yi akan azzaluman da ke ingizo su.


A shekarar 2011 wani xan jarida ya tambayi Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ko ya yake ganin mutanen da suka cutar da shi ta hanyoyi daban-daban?

Sai Shaikh (H) ya ce: “Ni ina ganin (waxanda suka zalunce ni a matsayin) su mutane ne da sam ba su son canji, suna ganin hakan zai shafe su, mu a namu gefe muna qoqarin jawo hankalinsu, amma su kuma suna son murqushe mu (su kashe mu)… wannan shi ne tunaninsu, a ce ba mu nan, mu kuma a gefe guda ba mu fatan xaya a cikinsu ya mutu, mun fi son su rayu, su fahimci abin da muke qira akai, muna so mu jawo ra’ayinsu ne, amma su suna so su murqushe jikkunanmu ne, mu (kuma) muna son mu rinjayi ruhunansu ne”…Saboda haka in mutum ya

1 Comments On SHAIKH ZAKZAKY IKON ALLAH
avatar
shuraihu-usman-1

1 year ago

Reply

sss

Please Login or Register in order to submit comment