Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da fahimtar juna.


Sannan duk garin da ya je don wa’azi ko halartar wani taro, yakan je ziyara ta sada zumunci da neman kusanci da fahimtar juna ga manyan malamai na garin, yakan ziyarci malamai ne mabanbanta na qungiyoyin musulmi. Sannan ya hana almajiransa warewa ko gina masallatansu na qashin kansu, don hakan zai qara kawo rarraba da farraqa ne a tsakanin musulmi, wannan ya sa duk inda almajiran Shaikh Zakzaky (H) suke, suna Sallah ne a masallatai na al’ummar musulmi, kuma a bayan limamai na waxannan sassan musulmin, tattare da cewa suna riqo ne da tafarkin Ahlul-Bait (AS) wato Ja’afariyyah.

KIRISTOCI: Ko ba a faxa ba duniya shaida ce game da kyakkyawar alaqar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da Kiristoci da ma sauran mabiya addinai a Nijeriya, domin in banda Shaikh (H) ba wani malami da Kiristocin Nijeriya ke yabawa salon Da’awarsa kamarsa. Qungiyoyin Kiristoci daban-daban sun sha rubutawa Shaikh Zakzaky (H) takardar yabo da godiya bisa gudunmawar da almajiransa suka ba su, na tseratar da rayukansu, ko na kariya ga dukiyoyinsu ko ga wuraren kasuwancinsu a lokutan rigingimun addini ko na qabilanci ko na siyasa.


A wurin Shaikh Zakzaky (H) hanya mafi dacewa ta yin jihadi ga Kiristoci ita ce hanyar isar musu da saqon musulunci na haqiqa ta kyakkyawar hanyar da za su fahimta su gamsu, ba wai ta hanyar hantara ko far musu da kisa ko qona dukiyoyi da wuraren ibadarsu dan kawai sun zavi su zama kiristoci ba.


MUTUNTAWARSA GA MATA :


Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne alami mafi girma na ‘yancin mata da tausaya musu a wannan al’umma ta wannan nahiya, domin ya kawo gagarumin sauyi akan yadda al’ummar wannan nahiya suka xauki mata, da yadda suke kallonsu, da irin mu’amalar bawa da maigidansa da ke gudana a tsakanin mata da mazajensu. Sannan a gefe guda Shaikh Zakzaky (H) ya yaqi munanan al’adu na qasqanta mata da mayar da su haja ta biyan buqata kawai. Wanda ya san rayuwar Bahaushe da iyalinsa, da yadda Shaikh (H) ya kawo sauyi a cikinta ne kawai zai iya fahimtar abin da muke faxa.

A matakin farko, Shaikh Zakzaky (H) ya darajta mata ne ta hanyar koya musu sanya suturar Musulunci (Hijab), wanda kafin Da’awarsa ba a san sanya hijabi a wannan nahiya tamu ba. Daga nan sai ya fito da su daga zaman dirsham na hidimar mazaje a gidajensu, zuwa fagen addini da sa’ayi kafaxa da kafaxa da maza wajan neman yardar Allah da gwagwarmayar ceto al’umma, wanda kafin Da’awarsa, a wannan nahiya tamu an manta cewa mata suna da wata damar bada gudunmawa a harkokin addini. Albarkacin Da’awarsa ne har mata suka samu damar riqe sifika su yi wa’azi, suka samu ‘yancin yin karatu suna gidajen aurensu, wanda kafin Da’awarsa an takura damar matan aure ta yin karatu da neman ilimi a makarantu.

Shaikh Zakzaky (H) ya bada gudunmawa sosai ta hantar mutunta mata da raya darajarsu a cikin al’ummar Hausawa ta aqalla fuskoki uku;


NA FARKO : Ya kare su daga yawan saki barkatai ba tare da bin qa’ida ba, domin a wani jawabin da yake matuqar nuna damuwarsa game da yadda maza ke yawan sake mata ba bisa qa’ida ba a Nijeriya, Shaikh Zakzaky (H) ya tava cewa; “Da ina da iko, to da na sa wata qa’ida a sakin aure, idan mutum zai saki matarsa, sai an sa rana, ya buga katin gayyata ya raba, an yi ta sanarwa a gidan rediyo, cewa wane xan wane, ya sa ranar kaza ga watan kaza a matsayin ranar da zai aikata abin nan da Allah Ta’ala ke qi, wato Saki! A taru kamar yadda ake xaura aure, mai shela ya yi shela cewa; Ga wane xan wane, ba tare da jin kunyar Allah ba, ba tare da jin kunyar Manzon Allah (S) da Mala’uku da Muminai ba, zai aiwatar da abin nan da Allah ba ya so, wato zai saki matarsa!


NA BIYU : Ta vangaren aure ma Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya qarawa mata kima da daraja a wajan maza, domin kuwa a bisa al’ada, a Nijeriya da qasashe maqwabtanta ana biyan kuxi ‘yan qalilan ne a matsayin sadakin mace, kai akwai ma al’adar bayar da ‘ya mace kyauta ko sadaka ga namiji ya aureta ba tare da wata wahala ko xawainiya ba, hatta sadakinta ma ubanta ne ke biya masa, shi kawai a siddan za a kawo masa matar!

Wannan al’ada ta tsananin arhar aure ta haifar da matsaloli masu yawa a zamantakewar auren al’ummarmu. Na farko ta haifarwa auren rashin kima, ta yadda an mayar da shi kamar wasa, daga mace ta xan savawa miji ko da bisa kuskure ne sai kawai ya saketa, domin ya san zai samu wata sabuwa cikin sauqi. Na biyu kuma hakan ya sabbabawa mazaje auren mata barkatai, alhali ba sa kiyaye haqqoqin matan kamar yadda musulunci ya tanada, hakan ya taimaka qwarai wajan jefa mata cikin halin tagayyara da qaqanikayi a gidajen aurensu.

Don taqaita wannan mummunar xabi’a ta wulaqanta mata, sai Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya raya sunnar biyan Sadaki mai kima ga mata, don aqalla mace ta samu darajtawa daga namiji, kuma hakan ya rage yawan saki barkatai ba tare da bin qa’ida ba, sannan ya taimaka wajan daqile tara mata rututu ba tare da kiyaye haqqoqi da dokokin Shari’a ba.


NA UKU : Shaikh Zakzaky (H) ya tarbiyyantar da al’umma (musamman almajiransa) dangane da tausayawa iyayen ‘ya mace, ya nuna cewa; Idan iyaye suka haifi ‘ya mace, sukan kula da rayuwarta da tarbiyyarta baki xaya, su yi ta xawainiyar ciyar da ita, tufatar da ita, kula da iliminta da lafiyarta da sauransu har ta girma. To kuma in an zo batun aurenta, sai iyayen sun sha wata baqar wahala ta kashe magudan kuxi, wani lokaci ko iyaye ba su da hali sai sun ci bashi sun yi xawainiya.


Dan haka, kamata ya yi su masu neman aure, su riqa tausayawa iyayen yarinya suna hutar da su daga manyan xawainiyoyi a lokacin biki. Ma’ana, ya zamo wanda zai auri mace ya biya sadaki mai kima sosai, wanda zai isa iyaye su yi wa mace duk abin da ake buqata a gidan mijinta, sai ya zama a qalla iyaye ba su riqa wahala sosai a lokacin aurar da ‘ya’yansu mata ba, an taimakawa iyaye kenan wajan hutar da su daga xawainiya mai galabaitarwa a lokutan bikin ‘ya’yansu mata.


Madalla da wannan darajtawa ta Shaikh Zakzaky (H) ga matan al’ummar nahiyarsa, madalla da wannan cigaba da ya samarwa mata, kuma madalla da wannan hutu da ya nemawa iyayen ‘ya’ya mata !

TAUSAYINSA GA MATA :


Shaikh Zakzaky (H) mutum ne mai matuqar tausayawa mata bisa halin da suka samu kansu a wannan al’umma tamu, yana yawan nuna damuwarsa game da cutar da mata da mazaje ke yi. Kullum yakan yi kira ga maza da su riqa tausayawa mata, su dena cutar da su, su dena bautar da su, su riqa musharaka da su cikin ayyukan gida, su riqa biya musu buqatunsu na rayuwa, su riqa kyautata musu har su shagwava su.


A wani jawabinsa na “Ranar Mata ta Duniya” wato “Makon Zahrah”, ya yi nasiha ga mazaje da su shagwava matansu ta hanyar tsananta kyautata musu, a ciki yake cewa, maza su riqa sayawa mata gwalagwalai na ado, in suna son mota ku saya musu, in suna son zuwa Hajji ku kai su, duk abin da suke so ku yi musu, ya ce idan maza suka yi wa matansu haka, sai kuma ya zamo matan sun nuna butulci, to a lokacin shi kuma zai yi wa matan faxa ya ba su rashin gaskiya.

Kullum Shaikh yakan tausayawa ‘yan uwa mata idan ya wuce ya gansu akan titi suna tafiya da qafa za su je wurin taro, musamman idan wurin taron da nisa, wani lokaci ma har tsayar da tawagar motocinsa yake yi ya umarci matan da ke tafiya a qafa da su shiga a rage masu hanya, in kuma suna da yawa yakan cire kuxi ya ba su ya ce su hau Tasi.

Wani xan uwa ya bada labarin yadda Shaikh Zakzaky (H) ya tava taimakawa wata mace mai ciki tun a shekarun baya, ya ce; “Ina da wasu dangi a cikin garin (Zariya), kullum suna gargaxi na game da bin Malam Zakzaky (saboda shi Shi’a ne). Ran nan sai kawai na ji mahaifiyar mai gidan ta ce ita ma ta zama ‘yar Shi’a, na ce meye dalili?


Sai ta ce “Ai ran nan xaya daga cikin ‘ya’yanta mata sun dawo daga unguwar Ban Zazzau (a cikin garin Zariya), ga goyo kuma ga ciki ruqu-ruqu, (tana tafiya da qyar da wahala), sai Malam ya zo wucewa a motarsa Bitil, ya tsaya ya xauko ta da xanta har zuwa kusa da gida. Ta ce yana tuqi sai karatun Alqur’ani yake… Wannan shi ne dalilin xaura xamarar neman sai ta koyi karatun Qur’ani ta iya kuma ta haddace shi” (Wakilin Manzo (S) a Doron Qasa, Juz’i na xaya, shafi na 26).


Tausayin Shaikh Zakzaky (H) ga mata bai taqaita ga mata ma’abuta addini ba, hatta mata masu zaman kansu Shaikh (H) yakan tausayawa rayuwarsu qwarai, “Akwai lokacin da na ji yana cewa, lokacin da yana zaune a kurkukun Kaduna, yana sauraron BBC sashen Hausa, sai ya ji ana tattaunawa da wasu ‘yan mata musulmi, waxanda suka maida fasiqanci a matsayin sana’a, suka ce kuma da abin da suke samu ne suke xaukar xawainiyar kansu da ma na iyayensu, shi ne Sayyid (H) ya ce da ya ji hirar, saboda tausayinsu sai da ya zubar da hawaye” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 31).


HIDIMA GA IYALANSA :


Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana da hali irin na Manzon Allah (S) na taimakawa iyali a ayyukansu na cikin gida da hidimta musu, domin ya kasance yana yi wa iyalinsa wanki da guga, yana xiba mata ruwa ya cika randuna, yana sharar xaki da gyara shinfixar kwanciyarsa da kansa, kuma yana dafa abinci ga iyalansa.

A wata hira da ‘yan jarida, uwargidansa Malama Zeenatu ta shaida musu cewa; “Qila kuna da labari cewa; Malam yakan girka abinci da yin sauran ayyukan gida. Tunda muka yi aure muna raba aiki ne ni da shi, ba wai komai ni nake yi ba, bilhasali ma wasu abubuwan shi yake mani, kamar wanki, (guga), da sauransu, sai ya ce in tara kayana in sun yi datti, shi sai ya wanke… kuma yakan ce kar a tava masa girkinsa, wato in yana girki ba ya so a sa masa hannu, ya fi so ya yi abinsa ya gama” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 41).


A wani jawabi Malama Zeenat tana cewa; “Shi (Malam) bai yarda mu ce komai mu za mu yi, shi ba zai yi ba, kuma Malam bai tava cewa in ba shi kaza ba, bai tava cewa xauko min kaza ba, kai ba ma ni ba, har yaransa ba ya aikensu, har da su Zainab (Hameed) in za su gyara masa xaki, to sai in ya fita za su shiga su gyara. Bai tava ce mun xauko min kaza ba, ko bani ruwa ko menene ba, shi kawai yana so ya yi komai da kansa ne” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 128).


Haka nan Malama Zeenatu ta tava bayyanawa ‘yan uwa mata misali na hidimar da Shaikh Zakzaky (H) yake mata hatta a cikin barcinta, ta ce; “Kun ga ni mai yawan jin zufa ce, waxanda muke tare sun sani, kuma ana yawan xauke wuta, kuma idan aka xauke wuta ba mu kunna AC da Janareto, don kar mu matsa masa, sai dai mu kunna fanka. To, duk lokacin da NEPA suka kawo wuta zai zo ya kunna min AC, ya kulle min windo, sannan ya koma (vangarensa), wani lokaci yana komawa sai a qara xauke wuta, shi kuma ba shi da nauyin barci, ko canza wuta aka yi yana tashi, sai ya zo ya kunna min fanka, ya kashe AC xin, ya bubbuxe windunan, kuma har yanzu yana yin hakan. Sannan kuma da abubuwa da dama, wanda mutum zai yi mamaki (in ya ji su)” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 129).


Shi ma Shaheed Sayyid Ahmad xaya daga cikin ‘ya’yan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), ya faxi yadda Shaikh xin ya rene shi tamkar uwa, wato yana masa duk wata hidima da xawainiyar da uwa ke yi wa xanta, ciki har da reno da sauransu. Ya ce; “Da yake ni ina da qani, sai ya zama an haife shi shekara xaya bayan an haife ni, sai ya zama ni an yaye ni tun kafin lokacin da ya kamata ya zama an yaye ni, sai ya zama Umma tana ji da qanina, sai ya zama ni kuma Abba ne yake ji da ni, sai ya zama da wanka da duk wasu abubuwa da ka san uwa tana yi wa yaro, to ni Abba ne yake min, har ya zama na fi sabawa da shi Abban fiye da Umman” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 55).


Malama Maryam Sani, wacce makusanciya ce ga Malama Zeenat (uwargidan Shaikh Zakzaky) tana cewa; “Malam har girki yana yi (a gidansa), da yawanmu in ana wani “Programme” mun sha cin girkin Malam. Akwai ma lokacin da wata Yayata ta zo guna, amma sai ta sauqa a gidan Malam, sai ta ga malam ya shiga kicin ya yi wanke-wanke ya dafa abinci, aka kawo musu suka ci, ba ta ga Malama (matar Malam) ta shiga kicin xin ba ma, da ta komo take ce min ashe haka malaminku yake? Wannan ba qaramin tasiri ya yi mata ba” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 196).


Ita ma Malama Maimunatu Abdullahi (uwargidan Shaheed Shaikh Muhammad Turi), ta labarta yadda Shaikh Zakzaky (H) ke hidimar gida ga iyalansa, ta ce; “Shi Malam rayuwarsa ta sha banban da yadda ‘yan uwa suke… Malam yana girki, sannan yana kula da ‘ya’yansa. Akwai wani xansa ma da yakan kwana a xakinsa, shi ne yake kula da shi, ya yi masa wanka da sauransu, ko kuma idan ana goyon yaro Malam yakan fito falo wurin ‘yan uwa ya canza masa nafkin, ya yi masa tsarki, ya nuna ma ‘yan uwa yadda ake wanke nafkin, da yadda ake saka shi… (Mun tava ziyartar Malam a gidansa) Sai muka samu yana girki, ya xora miyar taushe da tuwon shinkafa, har ma ya dafa mana shayi (muka sha), sai muka ga duk al’amuran da Malam ke yi addini ne” (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 206).


Wannan shaida ta iyalan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da almajiransa, game da hidimar da yake wa iyalansa na ayyukan cikin gida da reno da kula da sauransu, babbar shaida ce ta koyi da halayyar Annabi (S) da Shaikh Zakzaky (H) ke da ita. Kuma a gefe guda, hakan na nuna karimci da maxaukakan halaye da xabi’unsa managarta, lallai rayuwar Shaikh Zakzaky sanfur ce ga al’ummah.


KARANTARWARSA :


Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) mutum ne da ya yi fice a fagen karantarwa, domin bai da aiki a rayuwarsa face karatu da karantarwa ga ximbin xalibansa. Yana da tsarin karantarwa na dindindin a vangarori biyar, kama daga tafsirin Alqur’ani mai girma, karatun Nahjul-Balagah, karatun Daurori, da kuma Muhadharorin da ya saba gabatarwa a kusan ko da yaushe.

Tunda farko dai, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya assasa Harka Islamiyyah ne akan karantarwa ta gina fikira da kyawawan xabi’un musulunci. Wannan karantarwa wacce ake kira ‘TA’ALIM’, ta cikinta ne ake sanin jauharin manufa da hadafin Harka Islamiyyah, ita ce asasi ko matakin farko da ake so kowane xan Harka Islamiyyah ya bi ta kai kafin isa ga sauran karatuttukan Shaikh (H).


TAFSIRIN ALQUR’ANI : Shaikh Zakzaky (H) yana gabatar da tafsirin Alqur’ani mai girma a kowace ranar Laraba ta mako, wato yana da zaunannen tsari na yin tafsirin Alqur’ani wanda ba wani abu da ke sa ya xage tafsirin in ba tafiya qasar waje ya yi ba, hatta a lokutan gudanar da taruka da suke xaukar tsawon mako guda ana aiwatarwa, akan ware ranar Laraba a matsayin ranar tafsirin Alqur’ani ne a jadawalin, haka nan, ko ana ruwan sama ba ya xage tafsirin sai ya gudanar da shi.

Salon tafsirin Shaikh Zakzaky (H) ya sha banban da na dukkan malamai, misali; A tafsirin Alqur’ani na farko da ya yi, tun daga “Suratul Fatiha” har zuwa “Suratun-Nass”, ya yi shi ne a salon Tarjama, inda ya riqa gabatar da taqaitattun bayanai game da ma’anonin ayoyin Alqur’ani ba tare da kawo ra’ayoyin masu tafsiri ko savaninsu ba.


Amma da ya zo zagaye na biyu na tafsirin, sai ya riqa yin tafsirin a bisa doron bayanan Ahlis-Sunnah game da ma’anar ayoyin, wato idan ya karanto aya, sai ya yi tafsirinta ta mahangar Shi’a, sa’annan sai ya karanto tafsiri ko ruwayoyi da zantukan malamai da jagororin Ahlis-Sunnah da suka dace da wannan fassara ta Shi’a.

Sa’annan, da ya sake dawowa zagaye na uku na tafsirin, sai ya zamo a wannan karon, yana tafsirin ne kawai da zallar ruwayoyi da hadisai na Ahlul-Bait (AS), da kuma zantuka da fahimtar jagorori da malaman Shi’a (Radhiyallahu Anhum). Wannan ya nuna wata baiwa ta Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) na Ihaxar iliminsa da kuma salon da yake bi wajan shiryar da al’umma. 


NAHJUL BALAGAH : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana gabatar da karatun littafin “Nahjul-Balagah” a duk ranar Litinin ta kowane mako, shi ma karatun “Nahjul-Balagah” kamar na tafsirin Alqur’ani ne, ba abin da ke kawar da shi sai in tafiya qasar waje ne.


A wannan karatu na “Nahjul-Balagah” Shaikh Zakzaky (H) yana faxaxa bayanai sosai, tare da zurfafawa wajan hallale ma’anoni na kalmomin da littafin ke qunshe da su, kuma yakan zo da littattafai daban-daban dan faxaxa bayani ko qara bada haske kan wani abin da yake magana akansa, wannan ya sa zuwa yau an kwashe tsawon shekaru da dama Shaikh xin bai iya kaiwa ga sauke littafin ba har yanzu.


DAURAR AMIRAI : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana gudanar da karatu mai zurfi a fannonin ilimummukan addini da dama tare da manyan almajiransa daga lokaci zuwa lokaci, shi tsarin wannan karatu da ake kira “Daurah”, ya kevanta ne kawai ga manyan almajiransa, musamman wakilan ‘yan uwa na manyan Da’irori, da sashen masu wasu Mas’uliyya a Harka Islamiyyah, da makamantansu.

Shaikh Zakzaky (H) yana gudanar da wannan karatun Daurah ne ga manyan almajiransa duk bayan wata uku, kuma yakan shafe makwanni uku ne yana musu karatun a keve, a lokacin Daurar akan tattauna tare da zartar da muhimman shawarwari.


DAURAR ‘YAN UWA MATA : Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yakan gudanar da irin wancan karatun Daurah ma ga ‘yan uwa mata masu Mas’uliya a Harka Islamiyyah. Ita ma wannan Daurah ta ‘yan uwa mata akan gudanar da ita ne tsawon makwanni uku, kuma akan shigeta ne da zarar an kammala ta ‘yan uwa maza, wakilan ‘yan uwa mata daga dukkanin Da’irori na faxin qasar sukan halarta.

MUHADHARORI: Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yana gabatar da Muhadharori masu yawan gaske a rayuwarsa, kusan a kullum ba ya rasa gayyata ta gudanar da wata Muhadhara a wani taro, sannan a gefe guda yana da zaunannun Muhadharorin da yake gabatarwa shekara-shekara. Kamar zaman makokin Ashura na tsawon kwanaki 50, da Muhadharar Yaumu-Arba’een, da wafatin Manzon Allah (S), da Maulidin Shaikh Usman bin Fodiye, da Maulidin Manzon Allah (S), da Wafati da Maulidin Sayyida Zahra (SA), da Maulidin Imam Ali (AS), da Yaumul-Mab’ath, da Nisfu-Sha’aban, da Wafatin Amirul-Muminin (AS), da Dahwil-Ardh, da Eedul-Ghadeer da sauransu.

Sannan a kullum yana cikin gabatar da Muhadharori ga Lajanoni da vangarorin Harka Islamiyyah, da halartar Mu’utamarori, da zuwa taruka da sauran gayyace-gayyacen da ake masa a ciki da wajan qasa. A taqaice, waxannan abubuwa suna daga cikin aikace-aikace da hidimar yaxa ilimi da koyarwar addini da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ke gudanarwa a rayuwarsa.


WALLAFE-WALLAFENSA :


Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) bai yi fice a fagen rubuce-rubuce da wallafe-wallafen littattafai ba, wataqil hakan yana da alaqa da yawan ayyukansa da qarancin samun dama da lokaci na zaman yin rubuce-rubucen. A wata magana da ya tava yi game da wallafa, ya yi ishara cewa a kowane fage da kowane fanni an yi ximbin rubuce-rubuce masu kima da gamsarwa, sun wadatar wajan sanin duk abin da ake neman masaniya a kansa, wataqil wannan falsafa ce ta sa Shaikh (H) ya fi maida hankali wajan tafiyar da lokutansa ga ibada fiye da zaman yin rubutu.

Amma tattare da haka, Shaikh Zakzaky (H) ya rubuta littattafai guda uku da hannunsa, xaya na Turanci, xaya na Larabci, xaya kuma na Hausa, littattafan su ne;-

“THE MISSION OF MAN ON EARTH”, wato “Manufar Halittar Xan Adam a Bayan Qasa”.

“TARIHIN ZAZZAU” wato “The History of Zazzau”, wanda yake rubutawa da harshen Hausa.

“AD’IYAATU NAWAFILIR-RAMADAN” wato “Addu’o’in Nafilfilin watan Ramadan” wanda ya rubuta da Larabci.

A cikin waxannan littattafai guda uku, xaya ne aka samu damar kaiwa ga xab’insa, wato “Ad’iyaati Nawafilir-Ramadan”, sauran biyun zuwa yanzu bai iya samun damar kammala rubuta su ba.

Amma a gefe guda, akwai ximbin littattafan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) cikin harsunan Turanci da Hausa, wanda laccocinsa ne da yake gabatarwa a wurare da lokuta daban-daban ake rubutawa a maishe su littafi. Ba za mu iya ambatarsu gaba xaya ba saboda yawa, amma daga cikin fitattun akwai; “Nasihohi ga ‘Yan Uwa Musulmi”, na xaya zuwa na biyar, sai “Nijeriya Ina Mafita?” (wanda an ce har wani gwamna ya tava ba shi lambar yabo akan wannan littafin), sai “Rayuwar Imam Khumain (QS)” da sauransu.


Sannan akwai jerin laccocin da yake yi a ranar tunawa da Shahidai “Yaumus-Shuhada”, wanda kowace lacca ana mayar da ita littafi xauke da sunan “Shahada Maganin Mutuwa”, akwai kuma laccocin da yake gabatarwa a zaman makokin Ashura da ake mayar da su littafi xauke da sunan “Jawaban Ashura”, akwai laccocin da yake gabatarwa ga matasan Harka Islamiyyah a lokutan taronsu na shekara-shekara, wanda ake mayarwa littafi xauke da sunan “Zuwa Ga Matasa”, akwai laccocin da yake gabatarwa a makon tunawa da Imam Khumain (QS), wato “Imam’s Week” da ake mayar da su littafi xauke da sunaye daban-daban.

Akwai laccocin da yake gabatarwa a ranakun Maulidi da ake mayar da su littafi xauke da sunan “The Meassage”, akwai jerin laccocin da yake gabatarwa a wa’azozin dare a garuruwa, da laccocinsa na rufe tarukan Mu’utamar, da laccocinsa na tarukan qarawa juna ilimi da ake mayar da su qananan littattafai ana rabawa jama’a a bisa kulawar cibiya mai suna “Cibiyar Wallafa da Yaxa Jawaban Shaikh Zakzaky”, akwai ma jerin littattafai na zavavvun zantukansa da ake tattarawa wuri guda ana maishe su littafi da dai sauransu.


HAUSARSA :


Harshen Hausa shi ne yaren da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ke magana da shi a rayuwarsa ta yau da kullum, duk da cewa yana jin harsuna aqalla huxu, wato Hausa, Turanci, Larabci da Fulatanci.


Kamar yadda aka sani, Shaikh Zakzaky (H) xaya ne daga cikin bayin Allah waxanda Allah Ta’ala ya yi wa baiwar faxaka da lura da la’akari cikin komai na rayuwa, domin hatta a  furuci Shaikh (H) yana anfani ne da zavavvun kalmomin Hausa a jawabai da mu’amalolinsa, ba kawai yakan yi anfani da kalmomin da ya ji Hausawa suna furtawa ba ne, a’a, kafin Shaikh ya yi furuci da wata kalmar Hausa sai ya tantance ma’ana da kamalar kalmar, wato yakan yi anfani ne kawai da kalmomin da suka dace da koyarwar addini da tarbiyya.


Kullum Shaikh (H) a faxake yake kan Hausar da yake furtawa. A wasu lokuta yakan yi magana kan rashin dacewar furta wasu kalmomi ko ‘Karin Magana’ na Hausa, a wasu lokuta kuma nazari da la’akari ne zai tabbatar maka cewa baya anfani da wasu kalmomi na Hausa. Ga ‘yan misalai akan haka;-


DODO GUDA SUKE YI WA TSAFI : Shaikh (H) ba ya anfani da wannan “Karin Magana” a yayin da yake magana kan mutanen kirki, ko ma duk wani musulmi mai aqidar Tauhidi, wataqil kai ma za ka iya fahimtar rashin dacewar anfani da kalmar in ba ga maguzawa ma’abuta tsafi ba.


RIGA MALAM QALU-BALE  : Shaikh (H) ba ya anfani da wannan “Karin Magana” a yayin da yake so ya kushe gaggawar wasu mutane, domin riga Malam zuwa masallaci abu ne mai kyau a musulunci, dan haka bai kamata a kushe yin hakan da “Karin Magana” ba. 


QALU-BALE : Shaikh (H) ba ya nafani da kalmar Qalu-bale a yayin da yake so ya nuna ko ya yi wani “Challenge” ga wasu, domin in an bi zirin ma’anar ‘Qalu-bale’ za a taras kalmar ba ta da wani ma’ana in an kwatanta ta da ma’anar da aka xorata a kai, yakan yi anfani ne da kalmar “Kule” a madadinta. 


IN GEMUN XAN UWANKA YA KAMA DA WUTA, TO,

1 Comments On SHAIKH ZAKZAKY IKON ALLAH
avatar
shuraihu-usman-1

1 year ago

Reply

sss

Please Login or Register in order to submit comment