Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma turarukar da nabawa Mahaifanshi yayi musu daɗi.
Da dare akazo kwanciya nan Mama kilishi ta bani wani haɗi da madara nashanye sannan ta korani side ɗinshi ɗakin Hajiya na koma naje zan kwanta murmushi tayi cike da kunyata tace.
"Maryam tashi kitafi gurin mijinki nima gurin nawa mijin zani."
Wani bamu kamar guba tabani naci, nafita duk kunya ta kamani tura baki nayi naje falon nasameshi shi ɗaya,

    A babban kujeran falon na kwanta, yana gama abinda yake ya tashi yabar min falon, hadirine ya taso aka fara iska, witar gidan ya ɗauke.
                     Wani uban tsawa akayi da gudu nafarka na shige ɗakin dake kusa dani na haye gadon, bansan da mutum ba shima tsawarce ta farkar dashi, daga barcin da yake ya tuna dani a falo, ji nayi an laluboni, aikkuwa na fasa mashi ihu  ( nifa ban gajiya da kara😎)
     Toshe min baki yayi ya janyoni jikinshi, nan jikina ya shiga rawa "Relax my dear babu abinda zan tsinta a kwailar jikinki."

          "Toh ni kyaleni na sauka kasa bantaɓa kwana a kusada namiji ba."
  Matseni yayi da jikinshi,

                Dan dole nayi shiru a tare muke sauke ajiyar zuciya,  dakyar barci yayi gaba dani, shi kuwa gaba ki ɗaya na kuna mishi danjan shi sai shafa baya yake har aka fara ruwa dakyar barci yayi gaba dashi ina makele da Mai Lucky na.

    Da asuba kuwa ya rigani tashi kallon fuskana yayi a hankali yake shafa fuskar har na fara buɗe idona shagala yayi da kallon Eyelasher na, wanda suke cike kuma a tsatsaye gyara murya yayi cikin dakewa yace.
"Tashi kinzo kin makale min, kamar kinsami wani mijinki nidai ba mijinki bane, eyye dan idan na kyaleki a cikin gidan Iyayena ɓatani zakiyi kisani jin kunyar su."

      Zaro ido nayi na mike, sai lokacin na ga ashe duk kusan tumbur na kwana rigar barcin ta yaye, gani na kanenaye shi, kirjina na gogan nashi a kunyace na sauka a gadon yace.
"Gulmamiya kinzo kin ɓata min rayuwa shine zaki gudu."

     Ban kuma jin batunshi ba na fice a side sai gurin hajiya da take sallar raka'atun fijr, nima alola nayi nazo na fara muna gurin har aka kira asuba, muna idarwa muka sunkuya azkar har na fara gyangyaɗi nuna min ɗaya ɗakinshi tayi na mike naje na kwanta tun da nashiga nake sinsino kamshinsa, a katifar nayi masauki tuni barci yayi gaba dani,

                     Koda yazo gaida ita sun ɗan taɓa hira ya tashi ya shige ɗakin wanda nayi kanekane a tsakiyar gadon, fasa shiga yayi yana juyawa yaga babu hajiyarsu a falon shiga yayi ya gyara min kwanciya sannan ya raɓa gefena ya kwanta tare da maidani jikinshi ajiyar zuciya na sauke shima kuma haka, barci sosai mukayi har aka fara shirin zuwa fada muna ɗakin muna barcin asara Alhajinsu ya shigo da shirinsa yake tambayar Mama kilishi da " Rukayya ina ɗanki."
      "Ai tunda ya shigo bayan ya dawo masalaci ban kuma ganinshi ba Yaya ko yana ɗakinshine?."
Ta tambayi umma wacce kunya ya hanata sakat, dakyar tace.
"Yana tare da Maryam sajida kuma ina tunanin barc...."

    "Toh ai ba damuwa haka ma yayi, idan ya farka yasameni a fada," yayi gaba abinshi, Murmushi mama kilishi take doka, cike farin ciki ta goge kwallar dake shirin sauko mata tace.
"Yaya kinga ikon Allah, daga xuwa ta fara sauya alamura kaii wannan abu yayi min daɗi."

       Murmushi hajiya tayi daga nan basu kuma cewa komi ba.

        ........Wayyo Allah na sami katifa a tunanina ashe, jikin mai lucky ne sai kara shigewa nake, barci yayi daɗi, kusan sha ɗaya saura ya farka ganin yanda na shige, agogon ɗakin ya kalla ya rasa yanda zai rabani da jikinshi, kawai sai ya cusa hannunshi cikin rigana, yana min tafiyar tsutsa buɗe idanuna nayi dakyar ganin hannuna na zagaye, da wuyarshi ga fuskana a gurin yasani wartsakewa babu shiri dan abinda yake min zai kunce min tunaninane. Mikewa zanyi ya dawo dani, tare da matse ni yace.
"Waye ya aikoki ɗakina, dan gulma kinzo kin wani manne min, ana ganinki kamar wata musulman kwarai nan kuwa tantiriya ce ke ɗin, ji yanda kika sakaleni."
      Oho nifa maganar bata bani haushi ba, asalima mamakin yanda yake zare magana yake, ɗago kaina nayi tare da tura bakina gaba nace.
"Nifa kazo kasamu a dakin kuma kace waye ta aikoni, ince yanzun ma hannunka ba wani guri yake kokarin zuwa ba."

           Zaro ido yayi cike da mamaki yace.
"Hmm bari na tura hannun nawa inda basu sani ba."

         Hmmm gulmame haka da wayo yayita latsani son ranshi, da nagaji nasa mishi kuka dan yana murjeni yana yaɓa min magana, wai.
"Oho ni Yunusa dama haka kike ban sani ba, kinji namiji a kusadake sai wani rufe idanunki kike ke gaki, yar hannu toh kwalelanki dan babu abinda zanyi da yar karamar budurwa irinki, kwaila ma irin mi namiji zaiji a jikinki indai ba ɓatawa kanshi lokaci zaiyi ba."

     Dan renin hankali, yana matse kwaila yake wannan maganar, kuka nasaka tare da tureshi nace.
"Sauka min a jikina kaje gurin iyay...."

              Shiru kake ji, kwallq kuwa suka shiga wasan tsire a idanuna, Hmm mai nasara ya damki bakina sai taunesu yake yanda yayi mishi hannunshi kuwa, sunki barin aika aika.

          "Aunty Mom nifa na gaji, ki tashi ki tada Daddy an fara hawar sallah." Inji Huda.
   
        Breaking kiss ɗin yayi can kasar makoshinsa yace.
"My Queen gamu nan zuwa."

            "Ok daddy kuhanzrta dai."
  Shigowar Hajiya taji yanda yace.
"Ok"
          Tasan halin ɗanta sarai ba haka muryanshi yake ba jan huda tayo waje ta dangware kanta tace.
"Amma anyi shashasha, wace ki je musu kai amma dai rukayya Allah ya kintsa mana ke."

         "Amin Hajiyalle." tana gama faɗar haka ta juya abinta.

    ........
      Dakyar ya ɗaga a kaina tare da sumbatar goshina, duk naji ni daban kamar akwai abinda ke bin jikina, "tashi ki haɗa mana ruwan wanka."

     A kunyace na mike, na shige ban ɗakin na haɗa ruwan zan fito har ya shigo, sunkuyar da kaina nayi,  dan na ganshi ɗaure da towel.
            Riko hannuna yayi muka shiga ruwan a ciki ya zaren min rigar jikina kifa kaina nayi a kirjinshi haka muka ɓata lokaci a gurin, da shirme.
"Malama bazaki kyaleni ba ana jirana fa a fada."
D'ago kai nayi ina kallon fuskarshi, idanunshi a lumshe kamar bashi yayi magana ba, kuma ya matse ni a jikinshi.
"Zaki daina kallona ne ko ya-ya." kutt lallai ma kuwa, fuuu na mike a cikin ruwan zan fita ya maidani ciki tare da wani tsare fuskarshi ciki ciki yace.
"Kin manta bakiyi wankar tsarki ba, kuma naga kin."
Ai wallahi bansan lokacin da nafita daga ruwan ba, na tsaya a gaban shower na sake ruwa nayi wanka, jinshi nayi a bayana ya zagayo hannunshi ya ɗaura a kuguna, tare da goga kirjinshi a bayana da sauri na gama wanka, dan naga wannan mutumin ba kirkine dashi ba. Ina gamawa na ɗauki towel ina ɗaurawa ya kunce ya wani ɓata fuska yace.
"Jirana zakiyi nima nayi nawa."
Juya bayana nayi ina kunkuni har ya gama ina jin hannunshi ya buɗe kofar muka fita, rigar barcina na fita daga ɗakin huda na samu a falon Umma ta ɓata rai, kallon a gogon nayi cikin rarrashi nace.
"Kiyi hakuri ba laifina bane nima."

"Ok muje mu shirya dan an rigada an fara wasan."

Tace min,

A gurguje mukayi kwalliya inda na muka saka lace, golder sai tamin ɗauri bayan ta gama min kwalliya, nace.
"Ina hijab ɗina."

Zaro idonta tayi waje, cike da mamaki tace.
"Toh babu saka hijab sai alkyaba, dan kinsan Daddy shine wakilin Alhaji kuma duk wani wakili yana zuwa yakan je gaban matarshi ya nuna mata bajinta da iyawarshi akan doki kuma asalima daddy ɗan wasa polone kinga ta ko ina ya iya sarafa doki don Allah Aunty Mom nuna mishi kema zaki iya abinda sauran matan suke dan zaki gani da idonki."
         
"Toh ja'ira sai kufito ko, dan bakwana zamuyi ba garin damina ne." Inji Mama kilishi.

Alkyabana kalar milk ne sa ratsin golder muna fitowa shima ya fito da uban shirgi bayan yasaka farar shadda, ya ɗaura shakwara akan na dark blue akan janfar. Sai rawanin da yayi inda aka kafa mishi hular akabi da naɗi sosai, sannan aka ɗaura ɗamara ajikinshi na wasu kyaƙekyalen yadi mai ɗauƙar ido.
Ajiyar zuciya na sauke tare da janye idanuna akanshi,
"Woww Daddy kaga yanda kafito kaman saraki kuwa Aunty mom don Allah zomuyi hoto."

Jan hannuna tayi ta ciro wayarta ta mannani da jikinshi, itama ta koma gefenshi muka ɗauki hoton sai da Sulaima Ya shigo, tsaki yaja cikin masifa yace.
"Amma Wallahi baka da kirki kasan tun yaushe muke jiranka wato ga maraina wayo kazo kana ɗauƙar hoto yayi maka kyau."
Ina jim lokacin da ya tura hanunshi cikin alkyabar ya lakuci kwiɓina, sai da na zabura tafiyar shi yayi yana isa bakin kofa ya juyo ya kashe min ido, sunkuyar da kaina nayi nace.
"D'an renin latsi."

Suna fita muma muka fito, motar Alhaji yabar mana, muka tafi a ciki, dakyar muka sami gurin parking inda ake taron muka isa kowani mai rawani wanda matsayinshi babba bane a fada da gurin zamansu.

Haka ma sauran wakilan sarki da wakilansu, kujeran Wakilin Marafan zazzazau aka nuna mana wanda matarshi xata zauna da iyalanshi, kowani wakili haka ake basu duk shekara Huda ce ke zama a gurin sai gashi wannan shekaran na zauna ita ta zauna kusadani, nan muka cigaba da kallo, a hankali wakilan suka shiga kai gaisuwa,

Janyo wani pink warm Huda ta ajiye a gabana tace.
"Aunty Mom yanzun zaki ga yanda Mata ke nunawa mazajensu luv."
Can ana fara wasa na shiga ganin salon a gun matan mamaki ya hanani na fahimtar komi daga wacce idan mijinta yazo zata tashi ta kai mishi ruwa, sai masu tura yaransu, ana haka Sulaiman yazo a guje matar shi Safina ta mike ta kaimishi ruwa da fanta,

Buɗe kular Huda tayi ta ciro lemon power horse, ta mika min, murmushi tayi tace.
"Ga Daddyna can, yakusan zuwa amma zai kai gaisuwa ga sarkin zazzau."

A sukwane ya tawo da dokin inda yayi tirjiya a gabanmu, takobin hannunshi ya wurga sama, yana kallona.

Cikin sauri huda tace.
"Sumbaci hannunki ku hura mishi iska plsssssss"

Jikina na rawa na kai hannuna bakina na sumbata tare da hura mishi, kafin takobin ya iso Mai Nasara ya amshi sakona tare ds zillewa yacafke takobin yaje gaban sarki hannunshi ɗaya da takobi ɗaya damke da abinda na aika mishi yana, kuma bai rike linzamin dokin ba ya mika gaisuwarshi, kowa ya razana da ganin abinda yake aikatawa toh ya za'ayi masanin dokine. Yana mika gaisuwar, ya kamo linzamin ya dawo a guje ya juya yasake tafiya ya sake dawowa, da wani irin gudu yacewa.
"Mazaje kaiwa Gimbiya Maryam Gaisuwar bada kyautar da tayi."

Aikuwa shaiɗanin dokin da gudu yaxo ya daga kafarshi sama yana aniniya da gaisuwa a gaba, Ihu Huda tayi tace.
"Tashi ki mika mishi ki buɗe bakin ki kurɓa, ki nuna kin amshi gaisuwarsu."

Buɗe lemon nayi sai da naje kusadashi na kurɓa har jan bakina ya kewaye bakin tin ɗin,
Mika mishi nayi, karɓa yayi tare da murza hannuna, da sauri na janye hannuna, kafa kanshi yayi ya shanye tare da zagaye ni da doki, duk sai naji kunya ta kamani, sauka naga yayi daga dokin yazo gabana dan na kasa ko motsi, riko hannuna yayi, in passionately ya rike ya kain har inda nake zaune kwalla ce ta dauko daga idanuna ya sauka a hannunshi.
"No need."
Ya faɗa min da wani irin murya, hanky ya ɗauko a aljuhunshi ya goge min kwallar ya sunkuyo da kanshi daidai fuskana yace.
"Karki soma ɓata min kwalliyana dan zan biya kuɗinshi har da kari."

Yana faɗar haka ya juya ya haye dokinshi, Yar banza huda ɗaukarmu tayi a hoto ta ɗaura a Instargram, Face Book, da Whatsp.
Taging ɗin hotan tayi tace.
"Masoyan shekaran 2019, My Daddy nd Aunty Mom."
Sannan tayi wasu rubutu akansam hotunan...

****
Aman sun tafi maiduguri suma acan sukayi sallah, yana cikin kallo wani abokinsu ya kirashi cike da tsugudidi yace.
"Kaiii Yaushe Yunus Marafa ya fara luv ko zama da kune jeka page ɗin Huda Mai Masara na instagram nima yanzun Fatima ta nuna min."
Wato matarshi. Kashe kiran Aman Yayi ya kuna data,

Pagen huda ya fara lekawa dan yaga mai nasara yana yan rubuce rubuce idan yarinyar tayi posting kuma dake tana da hankali bata ɓata wayonta ba yasa abokan uban suke tofa albarkacin bakinsu.

Rike baki Aman yayi cike da mamaki, daga hotunan da mukayi a gida har wanda ta ɗauka a gurin taron.

Rahila ya taɓa ya nuna mata, zaro ido tayi cike da Mamakina Yaushe Sajida ta wayw haka...

Copy ɗin hoton tayi ta tura a wayarta itama ta ɗaura A status tare da rubutu kamar haka.
*Tabbas ada kallon sukuwa muke mata A yanzun kuwa sai dai Mu kirata da Sarauniyar Shekara, idan aka sami gaurayen wayewar Addini dana zamani toh ba makawa akan iya sauya wasu alamuran gareki our beloving Sister happy Sallah*

Duk wani pic sai da ta ajiye masa rubutu kafin tayi send,

Take yayunmu suka shiga comments Ya kabir da ya dawo gida, ɗaukar hoton yayi ya mikawa Mama Amarya tana gani tasake murmushi Umma aka mikawa, gwalesu tayi, ta cigaba da hidimar gabanta. Amma a kasar zuciyarta ita kaɗai tasan yanda take ji.

Rahimah da taga hoton ai da tayi kuka dan farinciki.

*****
Ana cikin hawar aka fara ruwa, ya sauko kamar da bakin kwarya dole aka tashi sauka yayi daga doki ya bawa saminu ya kai mishi, filin polo dake garin zaria.

Mikewa mukayi, sabida ruwa mota yakawo ya ɗaukemu gida yaje ya sauke huda, dan Mama kilishi zata shiga fada, sannan ya juya damu filin polo. Ina son magana amma tsoro ya hanani cewa komi. Dama kwarin gwiwar huda ce ke bani.

Muna shiga ya rage kayanshi a motar sannan yasa hannu ya zuge min alkyabar jikina, mai da kaina nayi jikin window, yana gamawa ya bud'e mortar ya fito, kofana yazo ya bud'e sannan ya mika min hannunshi NA mika mishi nawa ,a hankali ya janyoni waje,

Inda ake ruwa kamar me, faɗawa jikinshi nayi sabida karfin ruwan rufe kofar yayi ya saka gannunshi ya sunkuceni sakala hannuna a kafaɗarshi nayi ina kallonshi.

"Don Allah karki cinye ni ki kalli gabanki."
Abinda ya faɗa min kenan nayi maza na sunkuyar da kaina, ina rike dashi.

Har bargan dawakan muka je ya fito da mazaje, bayan ya sauke ni.

Sirdi yasaka mishi sannan yace min.
"Zo nan."
Tsoro da faɗuwar gaba yasa nakasani kasa motsawa zuwa yayi ya sunkuceni ya ɗaurani akan dokin, a jiyar zuciya na sauke bayan ya hau bayana.

Kaɗa linzamin dokin yayi ya zaburemu da gudu, k'ame wandonshi nayi, jin haka da yayi ya kai kanshi kunnena yace.
"Ki rike sirdin yar kauyen Damagaran kawai."

Ina rikewa yasake min a tsoroce nace.
"Daddyyy bazan iya ba."
Hannunshi nakan kuguna yace.
"Idan na kwaɗa miki mari zaki sani kaman kirike linzamin."



*.............Idan da hali zan iya ce muku barka da juma'a ya iyalanmu da yarorinmu, Allah yayi musu albarka nagode da jimirin bin Matar so sai Monday Insha Allah😂*

[8/25, 3:00 PM] Real Mai Dambu: 🌹🌹🍀
         *MATAR SO*
                 🌷🌷🌻

*MAI_DAMBU*
*Wattpad:Mai_Dambu.*
*HAZAKA WRITER'S ASSO*
(HWA)

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai....

Sadaukarwa Ga Yan grp ɗin Matar So....
Dedicater To Hafsat Abubakar💋

     _Wannan buk ɗin hakk'in masu shine idan kinsan baki saya ba karki karanta, mai fitarwa kuma ki duba girman Alkawarin da kika ɗauka na cewa bazaki fitar ba, tunda nace idan kinsan zaki saya ki fitar na Yafe ba sai kin saya ba_

*BOOK 1👈*

Page....21

           Jikina ne ya ɗauki rawa, sakamakon, yanda yake kara gauraya min sabin hayalarshi. Ga baki ɗaya narasa mizanyi kwalla ne ya cika min ido bakina na rawa nace.
"Daddy nifa ban iyawa."
         Ina jinshi ya saukar da zif ɗin rigana, ya sumbaci bayana, yarrr nayi aikuwa naja linzamin dokin kamar zamu faɗi.
"Wayyo Ni Yunus kashe ni zakiyi, idan baki iya abu ba ai kya faɗa min, amma baki nemi hallakawa Huda  Babanta ba, Yarinya kinji daɗin namiji shine kika zaucce nidai na faɗa miki ni ba sa'an aurenki bane, ki nemi dai dai dake, zaifi miki dan nan gaba zan rabu da ke ne, na nemi Babbar mace ba kwaila ba."

             Raina yayi masifar ɓaci wato duk wannan abinda yake min, ba shine yake ba nice ma nake.
    Dukda karfin ruwan da ake bai hanani ware murya nayita zuba mishi kuka da ihu ba.
"Wallahi ka saukeni, kaje kanemi Uwar matan kuma muna komawa gida nabar gida....."
         Jin hannunshi yana saɓule bra ɗina ne, tare da murza nipples ɗinsu yasani komawa jikinshi na sake linzamin dokin tare da rintsa idanuna gam, ina kokarin rike rigarshi.
 
     "Karasa rashin kunyar mana, tunda ni sa'an yinkine,."
                   Yana gama faɗin hk ya sanya harshenshi cikin kunena, ajiyar zuciya nake saukewa akai akai,
         "Mazaje tsaya a gurin motarmu gimbiya ta gaji," cak shaiɗanin dokin ya tsaya, sauka yayi ya gyara min rigana, sannan ya saukeni ya kama linzamin dokin zai maida bargansu kama wacce aka sani aikuwa nabisu.

    Yana kaishi gurin shima dokin ya nufi gurin matarshi goɗiya, shafa bayan dokin yayi ganin yanda dokin ke shinshina wuyar matarshi, juyawa nayi cikin sauri yace.
"Malama kinga tsaya."

      Share shi nayi na kara aguje, tsawar da akayi yasani tsayawa cak.
      Yana zuwa ya sakalo hanunshi kan cikina yana murmushi, yace.
"Allah nagode maka, da ka dakatar mun da ita."

    Zamewa nayi daga jikinshi na sheka a guje, bai ce min komi ba saima tawowa da yayi, a nutse.

            Yana zuwa ya buɗe motar nima buɗewa nayi na shiga ciki. Duk na jike,
                        Kallon agogowan wayarshi yayi yaga karfe ɗaya da rabi.

  Jan motar yayi bai tsaya ko ina ba, sai Saban garin zaria a can yana da gida babba. Anan wani sa'in yake sauka, shiga yayi da motarshi bayan an buɗe mishi har kofar da zai shiga dakai falon yayi parking.

            Fitowa yayi ya buɗe inda nake yace.
"Ki saka alkyabar."

   Sakawa nayi jikina na rawan sanyi, na fito buɗe gidan yayi da wani ɗan mukuli da na gani ya ɗauka a motar muka shiga har lokacin ruwa ake, hotunanshi na gani na polo. Birjin babu adadi.

            Tsayawa nayi ina kallonsu har ya haye saman inda ɗakinshi, sai atishawa nake akai akai.
       "Keee Jinjira!!! Zo nan."
   D'aga kaina nayi na kalle shi na juyar da kaina wani gurin daban na cigaba da kallon hotunan.
       Sake maimaita kiran yayi, ni kuwa ya bani haushi nasakai zan fita daga gidan ashe ya rufe kofar fita zamewa nayi ina kuka sosai,kamar wata karamar yarinya.

          Yalura da yanda ya bani haushi sai gashi ya sauko har inda nake ya cincinɓe ni. Zai haura dani sama.
   "Ni Wallahi na gaji ka sauke ni, haka ai kana guzumayen matanka kaje kayi yanda kake so dasu, ni kuma jinjira ka mai dani gurin Ummana ta cigaba renona, Wallahi an cuce ni, an haɗani da wanda bai san darajata ba, sai wulakantani yake. Kamar wata aba mara daraja ka sauke ni nace."

           A tsakiyar ɗakin shi yayi min ma sauki ya shiga cire min alkyabana aikuwa na shiga kare kaina ina kuka.

            Ganin na ririke mishi Hannunshi faucewa yayi ya wurgani gadon cike da zuciya da zafin rai yace.
"Ina wasa dake ne? Eyye dan kinga ina taɓa jikinki shine zakina min abinda kika gadama, ance miki jinjira ur very stupit, nonsense kawai, kina min rashin kunya any how wato dan ina taɓa wasu teenage nononki shine bari ki renani ko, na lura tun ranar da na fara kaina hannuna kike fara min rashin kunya, bari na haɗako da ummantaki tunda itace kike ganinta da girma."

    Wayar shi da ya shigo da ita, ya kunna bansan inda yasami nomber Umma ba, ya kirata suka gaisa cikin laluma sannan yace mata.
"Umma don Allah ki tambayi maryam kowani abu na mata, wallahi ta reni a cikin kwanakin nan rashin kunya take min soɓ ranta ga bakakken maganganu."

     Mika min wayar yayi ya shiga wanka, ya barni a gurin.

    "Allah Ubangiji ya shirya min ke Sajida ni zaki watsawa kasa a idanu, kisa mijinki a gaba da tashin hankali Yaushe idanunki suka buɗe kika fara zaginshi, wato kina son rabani da rahaman Ubangiji shine kike wulakanta mijinki nagode kiyi yanda kike so, bazan hanaki ba Allah ya gani na fita hakkinki akan zaman takewar Aure."
   
    "Umma walla..."
Katse kiran tayi, na fasa ihu ina yarfe hannuna, ina cewa.
"Wayyo Allah na, na shiga uku na lalace."
               Wankanshi yayi a nutse ya fito ganin ina kuka wiwi, bai kalle ni ba yasaka kayanshi zai fita ya wurga min wani shirt ɗinshi a leda yafita.

        Dakyar na fada ban ɗaki nayi wanka na gyara

Please Login or Register in order to submit comment