Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ayi dace mun haɗa ido.
Ina zaune a falona nasaka abincin a gaba, sai ga Mufeeda ta shigo ko sallama batayi min ba, ɗago kaina nayi tare da murmushi nace.
"Lafiya mufeeda?"
Tsaki tayi min, sannan tace.
"Ki sauka da abincinki kasa daddynmu nakiranki, yaran talakawa kawai."
Lumshe idanuna nayi sabida kaifin maganarta tafi ta reza ko wuka.
Tana gama faɗar haka tafita, shiru nayi ina nazarin kiyayyar da suke min, wanda nidai Allah ya gani bana nufin cutar dasu amma a hakan suke kokarin ganin sun kuntattamin.

D'an zaman da nayi a gurin ba tare da tashi naje naji sakonshi ba, ya sake ja min fitina.
Daukar abincin nayi na sauka kasa, yana zaune akan table ɗin sai juya abincin yake da cokali, duk sun yanyame shi, kallona yayi dan dama idanunshi nakan step ɗine, yayinda suke ta zuga shi ya cika fam fuskarshi har wani ja tayi, tunda na kalli cikin idanunshi na hango wutar bala'i sai na shiga nanata kalmar Innalillah...da wasu addu'o'i har na isa gurin. Lumshe idanushi yayi bayan ya shaki kamshin turarena, mutum ne mai masifar son turare dan matukar zai shaki kamshin turare yakan tsinci kanshi da samun nutsuwa.
Buɗe rinanun idanunshi yayi, ya sauke a kaina. Shiru yayi ya cigaba da juya cokalin, araina nace.
*Hali zanen dutse, yau kuma miskilancine ya motsa*

Duk suka shiga hankalinsu dan basu san irin hukuncin da zai min ba, amma in so samune basu ki yayi min shegen duka ba, tunda mugun laifi nayi.
Can da nagaji da tsayuwa nace.
"Daddy ka kirani, kuma kayi shiru. "
Yanda nayi maganar in low voice ya sashi ɗago kanshi ya kalleni, sannan ya mai da idanunshi kujeran dake kusadashi.
Nufinshi na zauna ajiye abincin nayi wnd na sauko da shi akan table, zama nayi ina kallonshi. Tura min filet ɗinshi yayi ya janyo kular shimkafar da ta miyar, ya zuba a wani filet ina kallonshi a nutse ya fara cin abincin, sai da yayi spoon uku sannan yace.
"Kici nagabanki."
Jikina ne ya ɗauki rawa, duk suka zuba min ido. D'ibar abincin nayi a cokali nakai bakina, wani masifaffen yaji da gishiri suka kama min, kan harshena da bakina baki ɗaya rike bakina nayi zan mike ya maidani ta hanyar take min kafana cikin fushi yace.
"Sai kincinye kuma kika kuskura kika dawo min dashi zan miki dukar da sai kin kwanta a gadon asibiti."

Dakyar na haɗiya tare da jan kofin ruwa nakafa kaina, aikuwa na fara amai. Wnda yasashi dole barina na mike, gashi na kware numfashi na ya ɗauke cak, zuba gwiwa na nayi kasa ina fincikar numfashi, dukda hankalinshi a tashe yake ganin halin da nake ciki, maganar da Fareeda tayi yasashi kauda tausayina da yake ji ya faɗi abinda yake ranshi.
"Laaaa cikine ashe da ita."
Aikuwa ya juya ya dalla mata harara, yace.
"Ke kika mata cikin, wannan Yar yarinyarce zata iya ɗaukar ciki ko ta ɗauka zubda shi za'ayi dan bata da hankali da nutsuwar renon wani yaro itama yaushe ta reni kanta, kar na kuma jin wannan maganar, dan ni ban ɗauketa a mata ba ina kallonta a matsayin Y'ar cikina ne."

"Indai haka ne. Toh kar takuma shiga d'akinka ko kuma tayi maka girki, dama bason girkin Johson kake ba sai ta karɓi aikinshi, da kuma kula dani tunda kaga bani da hannun da zan iyayin komi." Inji Aneesah.

D'aga kai nayi ina kallon yanayinshi, kuma ina jiran abinda zai ce sai kawai naji yace.
"Ok haka yayi ma"

"Wallahi baxanyi ba."
Na faɗa kai tsaye,
"Mi kika ce?" ya tambaye ni.
Shiru nayi ban kula shi ba, riko hannuna yayi ya haura dani sama, nomber mama kilishi ya kira ya faɗa mata, abinda nayi mishi mika min wayar yayi, ya fice a ɗakin.
"Maryam ya muna yabanki sallah zaki kasa alola, ko kina son Malama taji abinda kikewa mijinki ne, yau kuka dawo amma zaki haɗa mishi rigima da matanshi, ai balkisu ta faɗa min komi don Allah ku xauna lafiya kece karama kece kuma za'a sami matsala dake, toh ki nutsu kar ya kuma kawo min karanki."
Cikin kuka nace.
"Insha Allah..." ban iya magana ba sai kuka.
Kashe wayar tayi, na rasa mike min daɗi. Ummana nakira a wayata, na cigaba da kuka tanq jina bata kashe ba, nima ban kashe ba sai kuka kawai nake mata sai na buɗe baki nace Umma sai kuma kuka ya kwace min, munfi awa guda kuma batayi min magana ba, saida taji ina ajiyar zuciya sannan tace.
"Yau ɗaya danaji muryanki cikin kuka, toh ki maida kukanki nafili zuwa kukan zuci karki kuma bari kukanki yafito. Kiyi hakuri dan ko kin faɗa min damuwarki toh ba makawa, hakuri zan baki da kuma nasiha, maryam kowani mutum da irin nashi kaddaran kowa hakuri yake da zaki tambayi Rahilah ko Rahimah miye matsalarsu zasu faɗa miki, dikda kulawar da suke samu bai hanasu shiga damuwa ba, Maryam kasancewarki mace matar aure bazai hanaki fuskantar kalubale ba, ina ga ko iya haka nabarki kin fahimci abinda xance miki shine hakuri idan shi kikawa laifi ko yayi miki kije ki bashi hakuri, idan kuma abokan zamankine ki basu hakuri yau kaine gobe bakai bane kiyi hakuri wata rana sai labari."

Tana gama faɗar haka ta kashe wayar, kifa hannuna nayi saman goshina da yayi min nauyi, tunda muke wayar naji kamshinsa amma ban damu da na katse wayar ba,

Duk yana jin abinda umma tace min, dan haka ya shigo ya ɗauki wayar zai fita a hankali nace.
"Kayi hakuri ban sakewa."

Murmushin gefen baki yayi sannan yafita.

***
Akala wata biyu kenan zaman gidan Yunus na shirin fin karfina, ana cikin haka hidimar sallah laya tazo, ana sallar saura kwana biyu Huda tazo da farin cikina nake ganin karewar wasu matsalar, ashe wutar matsalace zata kuno min, dan tsakanin ɗa da Mahaifi sai Allah tunda Uwarta ta kitsan mata magana a ɗaki shi knn ta daina shiga damuwata, ga Aneesah da kullum sai taci min mutunci. Karshe ta haɗa ni dashi ya ci min mutunci sosai.

Abubuwa sun min yawa, dakyar wata labara ya barni zuwa gida, cike da farin ciki na haɗa kayana tsaf na bar gidan, sai gidan Aunty Shema'u.

Tun da ta ga yanda nazo tasan ba lafiya, dake anyi salla ganin yanda nake zare ido yasa ta tirkeni da tambaya mi ya kawo ni.
Sunkuyar da kaina nayi kwalla na zuba daga idanuna nace.
"Aunty nagaji da zaman aurene."
Sallamar matar abokin mijinta yasata amsawa tare da juyawa ta kalli kofar falon da bakuwar zata shigo.
Da fara a matar tashigo ta nime guri ta xauna, gaisawa sukayi sannan nima na gaisheta,

Dawo da hankalinta kaina Aunty Shema'u tayi tace.
"Auta mikika ce."
Ta zuba min ido, rike bakina nayi nasake mai maita mata, abinda nace.
"Bata bincike ni ba, ta shiga min faɗa min faɗa, ainu ita da bakuwarta. Ka basu ji ta bakina ba suka min tass, da yamma tayi suka sauke ni a gidan. Ji nake kamar na gudu nabar gidan duk na kare nafita hayacina. Haka kwanaki suke tafiya cike da abubuwan al'ajabi.

Tunda suka ga sun kasara tsakaninmu sai kowacce ta fecce ta cigaba da uzurin gabanta, dama da suka nemi shiga tsakaninmu haɗe kansu sukayi inda suka amshi dutyn su gurin kulawa dashi, bashi duk wani hakkinshi da duk wani abinda zan mishi, suka ɗauka.
Girki kuwa nice keyi duk gidan a kullum zanyi sau biyar a safiya, wai takaitawa nayi, dan kowcce da abinda take so. Gana yaransu daga falon sama zan fara shara har falon kasa, ɗakinshi kuwa shida kanshi ya haramta min shiga cikinta.

......Ada nake kallon matsalar gidan labcecciyar amma a yanzun bana damuwa da kowa, na tara kowa na zuba a gefe, har shima na tarashi a wani gefe guda.
Kimanin wata huɗu kenan ina cikin damuwa, Allah cikin ikonshi ya sauki rahilah lafiya, inda ta haifi ɗan namiji.
Anyi haihuwar kwana huɗu, sannan nasami labarin haihuwar dan yasani sai da yakai duk matanshi suka ga baby,
Ina zaune a gurin cin abinci suka shigo, suna raha.
"Ai Maman Huda nayi mamakin yanda matar Aman ɗin nan ta haifi katon yaro haka, koda yake bazanyi mamaki ba, tunda ai mace ce zata iya ko muma ta gidan nan da tasami Mai nasara ai itama haihuwar zatayi."

Shiru nayi ina shan fruit, nan suka juya suna kallona tare da fashewa da dariya. Toh ya zanyi tunda ya kwace wayar, haka sukayita hiransu,

.....
A can kuwa kowa mamakin rashin zuwa na yayi tun Umma na kawaici har ta kalli Ahmad tace.
"Ahmad wai Maryam bazata zo bane, yau kwana huɗu muna asibiti dan ma Haihuwar tazo da matsala, da lafiya ta haihu ai sai dai kowa yaje ya dubasu a gidansu."

"Kiyi hakuri Umma zan duba shi, tunda naga ya kawo sauran tayu ita ya kawota daga baya." ya faɗa mata,

Koda yasami Mai nasara da maganar biris yayi bai kaini ba, har ana gobe suna sai ga Mamie.
Sun sani a gaba shida matanshi suna tsigeni,dan nayi musu abinci gishiri yayi yawa, ina durkushe sai kuka nake.
Ta danno kai da sallamah, basuji ba dan zuciyarsu ya raja'a da mugun nufi,
Yana zaune matan sun zageye ni kowacce da abinda take faɗa, Mamie tashigo gidan, tsayawa tayi a bakin kofa tace.
"Sannunku da kokari"
D'ago kai nayi na kalleta bansan lokacinda kukana ya kwace ba, mikewa nayi tace.
"Koma ki zauna."
Komawa nayi muryana na tashi a falon, cikin ko in kula ta kalleshi da ya sauka akan kujeran yana gaida ita, dakatar dashi tayi sannan tace.
"Ai nasan haka kawai Maryam bazataki zuwa duba Rahilah da ɗanta ba,sai sa dalili da Ahmad yayi maka magana kayi shiru ashe kana azbtarmu da Y'a ce,,ba zan faɗawa Iyayenta abinda kayi mata ba, dan nasan bazasu iya hukuntaka ba, sai dai ka kiyayyi ranar da zata kwaɓe maka, da iyayenka da iyayenra zaka nemi damar sulhu bazaka samu ba, domin duk wanda aka gina mishi zuciya da kuntatawa toh tabbas yafi kowa fusata, Sajida jeki ɗsuko kayanki da zakiyi amfani dashi gobe suna."

Kallonshi nayi a hankali, na girgiza kai nace.
"Mamie bani da lafiya, ki bata hakuri zanzo bayan suna." Wani irin kallo tayi mishi me cike da tsantsar ɓacin rai tace.
"Allah ya kara miki hakuri."

Tana faɗar haka tafita, mikewa nayi na koma ɗakina, na zauna ina kuka, ga koshi ga kwanar yunwa.

Shigowa yayi ya buɗe wardrob ɗina ya shiga ciro min kayan da zansaka. Duk sun min yawa, ina kawa zasu nemi faɗuwa. Dalilin ramar da nayi yasa shi kin kaini, kallona yayi bayan ya ciro wani doguwar riga ya mika min yace.
"Idan muka je kowa ya tambayeki mi yasameki kice baki da lafiya ne idan naji wata magana bayan haka zaki gamu da ɓacin raina"

Shiru nayi bance komi ba, ya ajiye min kayan kallonshi nayi cikin sanyin murya nace.
"Wallahi babu inda zani, kawai kaje bana son magana, ai na faɗawa Mamie bazanzo ba."

"Kina hauka ne ina magana kina cewa bazaki ba tashi." ya daka min tsawa, sam banji komi ba nace.
"Na rantse da Allah wanda rayuwata da mutuwata take hannunshi baxan je ba, kawai karabu dani, idan kuma ka matsa na fita toh bazan dawo ba na tafi kenan, dan zan faɗawa Iyayena bazan dawo gidanka ba."

Cike da takaici ya fincikoni ya shiga zare min rigar jikina ina kokarin, kwatar kaina sai da yarabani da kayana ya zuba min ido, zai kai hanunshi kirjina nayi baya tare da jan zanin gadon na kare jikina nace.
"Mi zakayi da sa'ar Yar cikinka, ko zubda kima."
Fauce bedsheet ɗik yayi ya shiga niman saka min kayana ina tirjiya, nidai banga amfanin saka min kayan ba, dan da wayyo da dabara yagama matseni tass toh ya jima baiyi ba, yau kuma an fake da guzuma an harbi karsana. Ya more watanin hudunshi da bai taɓa ba.

Yana gama shiryani ya fita, abinda nake jira knn nasawa kofar falon key na barshi a jikin kofar, nazo na ciki ma haka. Dama akan abinci rana ne, banyi na dare ba, na kule kaina.

Da yazo yayi bugun duniyar nan naki buɗewa, karshe yace zai kira Umma fitowa falon nayi nace.
"Sai ka faɗa mata kace nayi abu naki kaga indan taxo da kanta zata ga irin uƙubar da kuke gana min kaida Iyalinka idan kuma Mama kakira itama sai tazo taga halin da nake ciki."

Jin haka ya sauke murya ya shiga rarrashina, har da kawo min misali da halayar mata nagari daga kan Nana Asiya har zuwa kan nana Fatima, yanda nake masa kallon holuko ashe yasan abinda yake, dakyar nafito muka tafi gidan mamie dan acan rahila take, koda muka fito ban kula matanshi ba, da suke jefa min magana ba.

Muna isa gurin motarshi sai ga Mufeeda da gudu, zan buɗe gaba ta bangaje ni yayi kaman bai gani ba, na koma baya na zauna.
Har muka isa kofar gidan su Aman wai yana jiran abuɗe mishi, nayi wuf nafito na rufe mishi kofarshi nayi cikin gidan. Da sanyin jiki na shiga falon Rahipah na zaune ana mata lalle Angon karni ya kasa ya tsare, da ɗanshi a hannu, tun Mamie na magana har ta zubawa Aman ido, dan babu ruwanshi da kunya,

Ganin Rahilah fess da ita yasani jin kwalla ya cika min ido a hankali ta buɗe min hannunta na faɗa ciki ina kuka, sosai Nace.
"Hilah kiyi hakuri bani da waya bani da hanyar da zanzo gurinki, infact komi."

Sai na kuma cusa kaina a kan cinyarta, ina kuka sosai shiru Aman yayi yana nazarin abinda nace, shigowar mao nasara da Mufeeda yasasu ɗago kai tare da amsa sallamarshi.

Kallona yayi yanda na ke kwance cinyar Rahilah ga Aman ya zuba min, ido yasashi ɗauke wuta. Munafikin kishinsa ya motsa.
D'agani Rahila tayi bayan ta ja hijab ɗinta ta rufe jikinta gaisawa sukayi, sannan ya amshi baby yana hararana.
Buɗa bakin Mufeeda tace.
"Halin munafurcin da aka saba shine akazo a nuna a duniya dan niman suna."

Shiru falon yayi banyi manakin jin haka ba dan tana tsakiyar manyan mata, dole ta faɗi haka, kuma kalmar da fareeda ta wurgeni da shine kafin mufito shine har ta rike tayi amfani dashi.
Sai ga kunya ta kama shi kamar ya nutse kasa, mikewa Aman yayi yace.
"Yunus muje ina son muyi magana."
Dan koda Mamie ta dawo ta gaya mishi abinda ta gani ga kuma abinda yarshi tayi min, mika min Yaron yayi tare da take min sawuna lumshe idanuna nayi kawai.
Bayan fitar uban muma muka dasa hiranmu, wanda muka ki ɗago komi dan yarinyar, tsaki tayi ta fara zagina. Kallo ɗaya Rahilah tayi mata, cikeda ɓacin rai tace.
"Kul idan zakiyi rashin kunyarki kije gidanku idan kuma kika ki zan miki shegen duka,, kuma naga Ubanda yaisa ya rama miki, kema Maryam kika kyale wannan yar aban take miki ɗiban albarka kina matar ubanta."

"Allah kiyayye daddyna yayi using ɗin wannan karuwar." Mami da qasu bakinta da suke ɗakinta tare da Rahilah da suke falon duk suka zaro ido waje.
Murmushi yake nayi sannan na mike tare da barin falon, kitchen na nufa nasha ruwa nafito. Mamie da kawayenta sai salati suke suna karawa, fitowa Mamie tayi ta kira Mai wankinsu. Tace.
"Maza kira min Aman."
.....
"Yunus mi ka ɗauki Maryam har yanzun bata ci darajar iyayenta bane da zaka zauna da ita. Yanzun akan idanunka Yarka take faɗa mata magana babu faɗa balle tsawatarwa."
. "Ka ga Aman nifa dama bason Maryam nake ba nayi tunani da nazari sai naga ashe kawai sha'awarta nake ji kuma yanzun ina taking drugs Alhamdulillah ai duk matsayinsu ɗaya ne, aurene ya banbantasu da Yaran da na haifa amma ni Maryam bata cikin tsarina dan munyi magana na fahimtar juna dasu Aneesah kuma sun bani shawara, kamata yayi na barta tayita musu aikace aikac.."

Zuciyar Aman ce take bugawa kamar zata fito waje. Sai Sha'ibu mai wanki yace.
"Yallaɓe kazo maza inji Mamie."
Da sauri suka nufi cikin gidan.
......D'aukar ɗan yaron nayi wanda yake rikici, nasa Hajiya Yabi ta ɗaura minshi a baya na goyeshi ina jijjigashi, Yau gani ɗauke da Yaron Rahilah sai kwalla ke sauka a idanuna, ina ɗan tap ɗinshi har yayi shiru. Ita kuwa mufeeda sai wuliwuli take da idanunta, shigowa su kayi lokacin mi lalle tagama Mamie tq mika mata kuɗinta,

"Lafiya Mamie gamu."
Nuna mishi Mufeeda tayi tace.
"Haka abokinka ya shahara gurin tarbiya, ku tambayeta mita faɗawa Naryam."
Kallon Yunus Aman yayi cike da takaici yace.
"Mamie bazan ji mai maici ba, ni ina ganin mi zai hana tunda kece kika musu jagora gidansu Maryam kisashi ya,sake musu Y'a ai babu dole rayuwa tana da zabi wallo kyakyawa ko mummuna, akan mi zaka rike musu Y'a kana cutarwa sai anyi magana kafi kowa shi damuwa watanin baya har zubewa kayi baka da lafiya sabida munce kasaketa mu nemawa yan uwanmu, Yanzun kuma kace tayi yarinya karama. Har shawara kayi da matanka suka ce ka bata aikace aikace ba tsaran aurenka bace, Ka ɗauki Yarka kafita mana a gida Maryam kuma insha Allah gobe zan faɗawa Iyayenta komi, su san halin da take ciki, Ai dama Mami kece kika kaita Zaria,fine gashi nan ta dawo gida. Kuma abinda na fahimta babu Iddarka akanta, Alhamdulillah sakinta baxai gaggara ba."

Yana gama faɗar haka ya buɗe kofar ta nunawa Yunus da yafitan musu a gida. Kallona Yunus yayi, wanda yake nufin zo mutafi. Shiru nayi narasa makama, "Sunce goyan kibishi."

Inji Mamie. Jikina nane ya ɗauki rawa, haka na kwance yaron ina kallon, Rahilah da take kuka nima nake shirin kuka,
"Amma Mamie."
"Barshi ba,damuwa duk yana cikin rayuwar aure."
Ina sauke yaron mamie ta jani zuwa ɗaki, shiru tayi haka ma yan uwanta sukayi shiru, wani bokiti ta ɗauko da wasu tarkace, Wata Yar uwsnta ta mika min wani Humrah mai suna shu'umar Humra na Ha'uwa'u Jidda Aliyu Usman, wanda ake kawo mata daga Sudan. Ta mika min.
Haka suka haɗa min kayan cass na fito nasiha tayi min ta rakoni har jikin mota,

Aman ya rigashi fita, gidan Ahmad yaje, suka shiga tattaunawa, dariya Ahmad yayi yace.
"Ka rabu da shege gobe zamu mishi final, insha Allah xoka rakani."

Hmmm ai kuwa tsiya suka kula mishi tun a yau dake gobe idan anyi raɗin suna akwai liyafa na maza.

Koda mamie tazo inda yake tace.
"Kaji tsoron Allah."

Tana faɗar haka jikinshi yayi sanyi muna fita ya kama min masifa ko ina sai na faɗawa kowa sirrin gidanshine, shiru nayi bance komi ba tunda naji abinda ya faɗawa Aman na gane bana tsarin yunus, kaddara da rabon aure ya kawoni gidanshi..
Koda muka isa gida, na fita da kayana. Shima haka dan bazan je sunar gobe ba, dukda monday ne sunan. D'akina na nufa na zauna, ina mai cigaba da zurfafa tunanina mi yasa Yunus ya rena min matsayina na mace.
Haka na gama lalluɓena ban sami komi ba, dan haka nayi kwanciyarta ban fita ba,

Girkin dare kuwa take away yayi musu, ina kwance ya turo mufeeda da nawa tana zuwa ta wurga min, tayi waje yanda ta jefa min haka ya shigo yasamu, kallona yayi a fusace.
"Abincin ne zaki wulakanta min dake baki san darajar nima ba"
"Ni bansan abinci bane, tana zuwa ta cillamin tayi waje, da ni da ita ai kaman Yarane kaga hankali da nutsuwa bai wadaccemu

Please Login or Register in order to submit comment