Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na mata shegen duka, idan kina son maganin mata, kiya shema'u magana balle hajiya falmata bazata barki haka ba, naji daɗi da kika sameta a surikarki, Rahimah kema an nan za'a zo niman aurenki, saura Uwar masu gida yarana sun mata wayo."

Tana gama mana nasiha da huɗubar da yasamu cusa kai a cikin cinyoyinmu, tafita kuka Rahilah tayishi ba iyaka, musaman da aka zo ɗaukarta za'a mata wanka da lalle mai haɗi da miski, tana fitowa akasata a gaba sai da tashanye zumar nan, tana kuka tana kome,

Abin tausayi, sai muka zama kamar wasu kala aure zai rabamu da Rahilah, kukanmu yaki karewa, sai da Umma tazo ta balbalemu da masifa sannan mukayi shiru, karshe sai ga Rahilah tana janmu da hira da wasa da dariya.

****
A zaria kuwa sai da aka dangana da Aman asibiti, sabida jininshi da yayi masifar hawa, a daren suka kai shi, gari na wayewa, ya farka wajen karfe tara nasafe ya gabatar da sallah yana idarwa ya juya ga Ahmad, yace.
"Abokina ka yarda dani wallahi ban aikata abinda hindu ta faɗa ba, asalima kwato yarinyar nayi daga mugun hannun, Abokin.."

"Toh mr romeo, aimunsan da haka, kawai ka rufe mana bakinka ka tashi mu wucce kaduna dan karfe biyu da rabi za'a aura maka jinjirar da kake suma akanta." Inji Mai nasara,

Mikewa Aman yayi ya naɗe abin sallar Ahmad ya amsa, sannan ya koma bakin gadon ya zauna, ɗago jajayen idanunshi yace.
"Ba auren yarinyar bace mafita, fahimtar Mamie shine mafita, dan nasan halinta akan wannan abun zata iya daina min magana."

Shigowar likita yasasu sukayi shiru mika musu hannu yayi sukayi musabaha,, yace.
"Mr Mandara ko zaka iya kwanciya a dubaka."

Kwanciya yayi likitan ya,shiga duba lafiyarshi, ya tabbatar musu da kome lafiya sai dai ya kiyayye ɓacin rai,

Sannan ya sallamesu, daga nan ko minti ɗaya basu kara ba, sai kaduna, kwantar da kujeran yayi ya lumshe idanunshi, cikin tsananin damuwa yace.
"Dole na rabu da Hindu, dan haka ne mafi alkhairi a gareni."

"Hmm aikuwa a jaridar Aminiya za'a wallafaka wani yasaki matarshi sabida zai auri jinjira waccw bata fara kirgan dangi ba," Inji mai nasara,

Juyawa yayi ya kalli Ahmad da yake tuki, sai danne dariyarshi yake, juyawa Aman yayi ya kalle Mai Nasara cikin jin haushi yace.
"Eh gwara ni, jaririya zan aura kai da katara, jakuna a matsayin mata fa, wallahi mai nasara zan danna maka bahagon ashariya, wallahi ka kar kureni yanzun nasa Ahmad ya tsayida motar mu bawa Hammata iska,"

"Haba ina ba dani zakayi haka ba ka kwantar da hankalinka ka kusan bawa jinjira iska da cinyoyinka." ya faɗa mishi,

"Ahmad sauke ni naci uban wannan gaye, zai rena min hankali ɗan iska, wanda girman kai da miskilanci ya hanashi gyara gidanshi."
"Naji ango baby."

Haka mai nasara yayita kuna Aman har suka isa gidansu Aman, aka sauke shi ko kallon inda suke baiyi ba ya banka kofar motar, yayi gaba abinshi sauke glass Mai nasara yayi yace.
"Sauka lafiya ango jinjira,"

Cak Aman ya tsaya, a fusace yayi kam motar, ya buɗe inda mai Nasara yake cikin huci da ɓacin rai ya caccumo Mai nasara zuwa waje.
"Dan Ubanka mi kake nufi dani ne."
Fitowa Ahmad yayi daga motar yana raba tsakaninsu, luuuuuu Aman ya tafi zai faɗi, suka tare shi, cikin tashin hankali Mai Nasara yace.
"Wallahi bana nufinka da kome, asalima zolayarka nake, don Allah ka yafe min, ɓata maka rai da nayi."

Lumshe idanunshi yayi yana jinsu suka ɗauke shi a kafaɗa har cikn gidansu,, Mamie na falon tana waya da yan uwanta da suka taso tun jiya, dan tun da abin ya faru, taci alwashin aurawa Aman Rahilah, ta kira Babban Yayansu Sale Goni, ta faɗa mishi, dake suma gidansu malamai ne, da asuba ya kirata yace aure fa zai tabbata, insha Allah karta ɗaga hankalinta zasu cigaba da addu'a,

Yanzun ma da yayarta mace suke magana sun kusan isowa, dan samako sukayi,

Shigowarsu Ahmad yasa ta yanke kiran ta zuba musu,ido take suka shiga kame kame, dakyar Mai Nasara yace.
"Bashi da lafiyane, jininshi ya hawu sosai, amm..."
"Toh mi yasa baku kai shi gidanshi ba, sai nan."

Tsagalgalesu tayi sannan tasa mi aikinta ta gyara mishi tsohon ɗakinshi aka sake har su zanin gado, da labule da duk wani abin bukata,, sannan ta kira family dr ɗinsu, tace.
"Ku kaishi tsohon ɗakinshi,dake wancan koridon"

Daukarshi sukayi zuwa ɗakin dake zuba kamshi da sanyi daɗi kamar ya.

Suna zaune likitan yazo ya duba shi, yasa mishi ruwa da allurai da kuma magunguna.

Tunda aka samu yayi barci su kuma Ahmad suka tafi gidajensu da niyyar shiryawa zuwa masalaci,

****
Bayan sallar juma'a alummar musaulmin dasukayi sallar juma'a suka shaida Auren Husaina Omer Hayat, tare da Angonta Dr Aman Mohmud Mandara, auren da yazo bazata a cikin unguwarmu dama, yan unguwar suna mana lakabi da bama auren kananun mutane sai manya,
Tunda aka shigo akace Alhamdulillah, an ɗaura auren Rahilah sai gata tana shirin zuɓewa a kasa, sai da aka tareta wani fitinannen kuka tasaka wanda ya taɓa zuciyar kowa a gidan, mukan ai ba'a cewa kome,

Shigar da ita Umma tayi ɗakin Mama Amarya wacce itama ta kunshe kanta a ban ɗaki tana kuka. Kwantar dani Umma tayi a bakin gadon mama,

Buga kofar ban ɗakin Umma tayi, sai gata tafito kanta a sunkuye tana goge kwallarta murmushi Umma tayi tace.
"Gata nan, igiya ukun Aman ya ɗauru akanta, nayi iya nawa sai ki kara mata da wanda zaki kara, amma maganar gaskiya karki bari taga kwallarki dan zaki karya mata kwarin gwiwa,,"

Gyaɗa kai Mama tayi, sannan Umma tafita tsakar gida, inda tasamu ana shigo da kaya cike da mamaki, ganin Yayar Mamie Aman yasa ta sake murmushi tace.
"Hajja Yanah kece a garinmu? Barka da zuwa, ku basu guri su shiga ciki."

Dariya Hajja Yanah tayi tace.
"Malama Hasina,har yanzun kina nan da halinki na karɓan baki, fa mungode da abun arziki na bamu kyautar na musaman mungode."

Murmushi Umma tayi, cikin jin daɗi tace.
"Ai bakonka sarkin ka, batun aure kuma karawa zumuncinmu karfine mune da godiya, wanda zai auri Yarka ai ya gama maka komi, a wannan zamanin da mazan suke tsada, mune da godiya bawai dan yaran sun mana yawa ba, sai dan nasan Hajiya falmata zata iya rike mana Rahilah."

(Da fatan kun fahimci maganar Umma, kalma ɗaya mai kunshe da harshen damo bawai dan yaran sun mana yawa ba, nufinta ba wai muna niman kai da Rahilah bane ko sauran yaran, sai tasan ko babu auratayya Hajiya falmata zata rike Rahilah a matsayin Yarta🔛)


Godiya sukayi sannan suka shiga buɗe kaya, ɗaya daga cikin Auntys ɗin Aman tace.

"Ga kayan nan, amma bana lafe bane, kayan da muke na al'adace wanda akewa Uwar amarya da Uban amarya da danginta, bawai mun kawo dan ku biya mu baɓe, ai kun gama biyanmu tunds kuka ɗauki lu'ulu'u kuka bamu ko hka ma ya ishemu fatanmu nan da wata tara cif abin arziki ya sake taramu, dan mici daɗi, yanda take Husaina Allah yasa tana shiga ta juye mana, huɗu duk shekara muzo suna wallahi bazamu ki ba, ai abin daɗine haka."

Dariya akayi sannan aka musu godiya, tare da abin arziki Umma ta basu.

Har zasu fita, Kanwar Baban Aman Hajja Qoise tace,
"Mu dai bama bukatar, kayan ɗaki idan da gaske ɗaya muke, toh mun yafe, Yarmu muke bukata."

"A'a Hajja ku faɗa mana, inda za'a kai mata, kayanta koda bazatayi amfani dashi ba, itama tayi alfahari da kayan da iyayenta suka mata" Inji Umma,

Haka suka rabu cikin mutunci da fahimtar juna,
*Yaseen nasha fura da nono ya kahe min jiki idan naga da hali zuwa dare na muku amma banyi alkawarin ba* 👐👐
[8/25, 2:59 PM] Real Mai Dambu: Cigaban 8page......

      Zama sukayi aka shiga ware kayan, bandir ɗin shaddane masu shegen tsada, sai atamfofi suma haka g wasu manyan liffaya, 
     Abin gwanin burgewa, kowa sai san barka yakewa su Umma da Rahilah.

        ****
    "Wai duk wannan shirin na zuwa ɗaurin auren Aman ne, duk wancan munafikine ya koya mishi niman mata, Allah yasa bayi nasara akanka ba Ahmad." Cewar Hafsat da take kallon Ahmad na sanya wata muguwar yadin maza.

           (Wayyo mai nasara tara matanka yajanyo ana kirania da munahuki😜)

       Ganin yaki kulata yasa ta koma gefe, zuciyarta na raya mata tunda Aman yayi aure tabbas Ahmad na hanya, shima.
            Mikewa tayi ta isa bayanshi tana goga mishi kirjinta, juyowa yayi fuskarshi a haɗe ya tureta gefe, cikin dakakkiyar murya yace.
"Karki fara tunanin bazanyi aure ba, dan matukar Ummi ta amince min, hmm"
Takalminshi ya zaro ya ɗauki tissue ya goge sannan ya zura sahunshi ya fita.

               Tunda yafita ta rasa inda ke mata daɗi, sai safa da marwa akan auren ahmad tabbas zata kona gidan bashi ba hatta amaryan, sai ta babbakasu sai dai tare a jail.

         ****
   Ana gama aurin Auren Aman suka nufi gidansu, ta kofar baya suka shiga wanda Mamie tasa a buɗe sabida abokanshi.

       Da sallama suka shiga ɗakin, kowa ya nemi guri ya zauna, kallonshi suke daga shi sai dogon wando  da kuma singlet, yana rike da kofin shayi.

       "Sannun Ango Husaina Allah ya bada zaman lafiya, kaima yabaka lafiya yanda zaka mike da kafarka."
    Cewar Mai Nasara,

       "Amin, Hmm dama idan kaji sauki akwai tafiya a gabanmu zuwa china, 4weeks xamu iya dawowa mubarka a can, ka karasa mana abubuwanmu." Kallon Ahmad yayi irin baka da hankalim nan, kauda kai yayi ya cigaba da zukar shanyinshi yace.
"Ina bukatar passport ɗinta, dan zan tafi da abata ce."
      "karya kenan, mu da zamu kasuwanci kace zaka ɗauki mace aje da ita sai kace akanta zaka far..."

   "Ya isa haka, Yunus bana so kabarni nayi abinda nake so, kai kayi wanda kake so, matata ce fa don Allah ko ban samu mutunci ba, tunda ina sonta katayani mutuntata."

   Yana gama faɗar haka ajiye kofin yayi ya ɗauki towel ya shige ban ɗaki, bai fito ba sai da ya ɓata lokacinshi sannan ya fito, shigowa Aman yayi ya ajiye mishi ladar, shadda kala huɗi,  farin cikin ya ɗauka yasaka bayan ya gama tsane jikinshi, ya shirya tsaf, bayan ya murza hularshi mai taken minister,.
         Cikin gidansu suka shiga nan akayi gaishe gaishe, sannan suka nufi, gidansu Rahilah kallon Mai nasara yayi kafin yace.
"Ina son yan canji a hannuna, sabida shiga gidan biki sai da wani abu."

       Mai nasara vai ki ba, ya kaishi banki suka cire kuɗi sannan suka nufo gidanmu, inda akewa Rahilah lalle ja, mai zanen fulawa, dake manyane sai gashi sun mata raɗa raɗa.

    Muna ciki aka sheda angwaye sun zo, take gidan aka nutsu, suka shigo har ciki, aka fara gaishe gaishe, rahimah da take waje  itace tasami ganinshi, ta window na leka naga ya faɗa, fuskarshi tayi fayau, sai murmushi suke dokawa. Juyawa nayi na kalleta yanda idanunta sukayi jajawur nace.
"Rahilah!!"
     Haɗiye kukanta tayi tace.
"Kin manta ko scndry ban gama ba, balle nasan ciwon kaina"

           "Haba Rahilah kefa mahaddaciyar alkur'anine fa, da wasu litattafan addini, mi zai ɗaga miki hankali."

   "Babu my three." xama nayi a kusada ina jin ana zabga musu godiya sake lekawa nayi nasamu suna rabawa yaran yayunmu kuɗine, ina jin Umma musu ya isa hk, nan sukayi godiya suka tafita.

       Bayan sun gama gaisuwar suka fita a kofar gida suka haɗu da Yayanmu nan Ahmad ya tambayeshi ko zasu sami kananun hotonta.

        Ce musu yayi su jirashi ya shiga cikin gidan sai gashi da hotunan, mika musu yayi godiya sukayi sosai,

Sannan suka shiga motarsu, mikawa, Ahmad yayi hoton sannan yace.
"Gashi nan ku naima mata, visa china, da kuma dubai ko ni ku nema mata na ko ina ma."

Shiru sukayi babu wanda ya kuma kullashi.
.......
Kayanta da aka kaiwa tela tun dawowarmu aka amso dan har ta cire lallen..
Mikewa nayi zan fita, Aunty Shukura, tazo ta fita da ita komawa nayi na zauna, ɗakin mama Amarya suka mai ita,sabida ɗazun bata iya ce mata kome ba har tasa aka fitar da rahilah.

Tunda ta shiga Yayar Mama ta zuba mata ido, zama tayi kanta a sunkuye cikin hijab.

Mika mata, kofin tea sukayi dakyar ta amsa, ta fara sha, nan suka haɗu suka mata nasiha sosai duk abinda ake Mama bata ce kala ba, har suka gama, kanwar Mama ce ta dafata tace.
"Yaya Atika, kisa mata albarka dan anjima balallai bane a kawota."

Gyaɗa kai Mama tayi sannan tace.
"Allah ya Albarkaci rayuwar aurensu, da zuri'a ta gari ta kuma nutsu a ɗakinta shine alfarman da nake rokonta ,ta rufa mana asiri ta zauna a gidanta lafiya banda kawo kara, ta shanye ɓacin ranta, Allah zai bata madafa, sannan karki zama mai rokon abin hannunshi ki zama mai wadatar zuci da duk wani abinshi, karki zama mai yawan fushi Rahilah na rokeki ki zama daban a cikin Yan uwanki, ki zame mana abin alfahari, sannan ki zama mai yawan godiya ga Ubangiji, haka zai kara miki wadatar zuci, karki duba abinda yayiwa Iyayenshi ki ɗaura shi akan hanyar kyautatawa, yanda zai ji dukduniya idan bake ba, bazai taɓa jin daɗi ba, ki nemi Yardan Allah xaki samu yardan mijinki, ki nutsu ki nemi makamin da zaki masa illa dashi wanda duk runtsin in bake ba babu macen da take gabanshi, don Allah Rahilah karki sauya halinki karki zama mai yawan tona sirrin gidanki, karki zama me yawan faɗan sharrinsa, ki ɓoye sharrinsa ki kambama Alkhairinshi, kinga bani da lafiya karki sani kara damuwa akan wanda nake, idan kika min haka kin min komi a duniya jike Allah ya tsare a rike addu'a da azkar dan shine saiwan zaman gidan miji. Allah yayi miki albarka Husainata."

Kuka rahilah take kaman idanunta zai fita, rarrafawa tayi jikin Mama ta zube cikin kuka take cewa.
"Mamana ki yafe min, duk abinda nayi wanda nasani da wanda ban sani ba, nikam Mamana dole ne sai an kaini ni bana son tafiya na barki."

Rungumeta Mama tayi itama tana zubda kwallah, sabida akwai wani sirrintacoyar shakuwa, a tsakaninsu shiga ɗakin mukayi. Ni da Rahimah muka kwanta muna kuka,

..... Bayan sallar isha aka kaita ɗakin Malam, bai ce matq kome ba sabida shima ɓoye damuwarshi yake, kanta na cinyarshi.

Litattafan addu'o'i ya bata, sannan yace.
"Gashi na baki abokan hira amma na manta ban baki abu ɗaya ba"
Dube dube ya shiga yi, kafin ya ɗago ya kalleta Yace.
"Rahilah ban gani ba. Kisan mi nake nima."
Girgiza kanta tayi, murmushi ya sake mata tare da shafa kanta yace.
"Hakuri!!! Ashe halittace da take cikin kirajenmu da jininmu,, bazan kuma cewa komi ba amma kiyi hkr da inda zaki shiga Allah ya kara miki Hakuri."

Daga haka aka shiga fita dan motar ɗaukar amarya tazo, shaga ɗakin Umma tayi tace.
"Malam ka gama ai?"
"Eh Allah yayi musu albarka da rayuwar aure mai albarka sannan ya kauda kanshi"

Sannan ya kauda kanshi, duk cikin Yaran gidanmu munfi shakuwa da malam.

D'aki Umma ta shigo da ita ta sauya mata kaya tare da zuba mata turaruka, sannan ta naɗeta da liffaya, ta tattaro duk wani abin amfaninta, ta fito da shi,ina rike da wasu Rahimah ma haka,

Umma rungume da Rahilah ta shiga da ita ɗakin Mama fir taki ɗaga, karshe Inhelarta ta nima ta shaka, aka fita da Rahilah,

Gaskiya sun kawo mota, ba nawasa ba, motar mai nasara aka sakata, mu kuma muka shiga motar Ahmad, gaba Rahimah ta shiga, Ni da Aunty Hamdiya baya da shukrah,

Tunda ta shiga ya zuba mata ido, sai da taji haushi tace.
"Tafiya zakayi ko kallon halitta."
"Izininki nake nima" kauda kai yayi ya leka yaga an gama shiga motar har da wasu empty.

Sannan suka bi jerin gwano har gidansu Amma wanda ymyake cike da mutane,

Bayan sun isa rike Umma tayi da zasu fita a motar Umma tace.
"Ki nutsu sosai, ki kame kanki karki bari su gano wani makusa a tare dake."

Haka suka fito, inda suka nufi cikin gidan abakin kofa Umma tace.
"Kiyi addu'a sannan ki shiga da kafar dama, dukda ba gidan da zaki zauna bane naki yana g.a.r amma, kishiga da samun nasara."

Kaman yanda Umma tace mata haka tayi, har cikin falon gurin Zama umma ta nema Rahilah ta zauna a kasa, cikin sauri wata ta kawo tuntumun ta ɗagata ta zauna akai, cikin raha matar tace.
"Malama, ya kina ganin zata ragewa ɗanmu ɗumin jikinta, so take ya fara hango wata bayan ita."

Dariya umma tayi, sannan tace.
"Don Allah, Hajja Amna barni ina fama da jikoki ina ni ina fahimtar wasu sirrinku na Yan barno."

Dariya akayi gaisawa akayi kafin Umma tace.
"Hajiya Falmata ga Yarki nan, nakawo miki ita bazan tsawaita magana ba, amma zanji daɗin idan kika ɗauketa kamarsu Khalisat da Sakina, idan tayi kuskure kemai ɗaurata akan hanya ce, ni da atika ba sai munji ba, yarki ce ke zaki koya mata sanki dukda nasan idan mace takai mace, ɗan kowa natane ga Rahilah nan, bamu koya mata shan kayan mata ba, amma mun koya mata biyayya da yanda zatabu mijinta da kuma iyayenshi da danginshi don Allah idan tayi laifi ki sasanta kayanki, mun gode kwarai da gaske mun baku Yar mu bama fatar ku dawo mana da ita, burinmu a fita da gawarta, Eh sabida mun san mutuwa tana kan kowa, amma yarmu ta dawo mana babu aure zai taɓa zuciyarmu, amma idan kace a gidan aurenta ta rasu, wannan wani abin alfaharine.".

"Mungode da sosai insha Allah zamu riketa gam, ita da barin gidan Aman aisai mutuwa dan ni na hango yan uku nan da wata tara, kaiii Falmata wallahi Yarinyar nan ta haihu baki kawota maiduguri ba zaki sha mamakina." Inji Aunty Innalo.

Kanwar Baban Aman ce.

Haka akayi ta barkwace, sai da Umma ta mike rahilah ta ɗago kai cikin tashin hankali tace.
"Umma zan biku, na fasa auren ku mai dani gurin Malam."

Idanun Umma ne yayi jajur, sannan ta ciro rikon da tayi mata, ta mikawa Aunty Innalo,

Wani gigitaciyar kuka Rahilah tasake tana cewa ku mai dani gidanmu bana so.
"Keeeeeeee. keee Rahilah maza haɗiye kukanki da maganar banzan da kike gasu Maryam Sajida ai."

Luf tayi a jikin Innalo ta rufe idanunta tana sauke a jiyar zuciya sannan Umma suka fita,ɗakin su Sakina aka kaimu, tana rike da Aunty Inna.

A hankali ta zaunar da ita, kifa kanta tayi, da cinyarta,
.......
Bayan wani lokaci aka kawo mana abinci da kayan ciye ciye, ruwa kawai muka kurɓa haka muka kwana muna taya yar uwanmu kuka,

****
Tunda ya dawo yake kwance sai juyi yake dan khalisat ta tura mishi videon kawo Rahilah mikewa yayi ya saka jallaɓiyar shi, gurin ɗaya na dare.

D'akin da aka kaimu ya nufo, buɗe kofar yayi ya hangomu cure da juna, itace a tsakiyarmu shiga yayi a hankali cikin hikima da dabara yasa hannunshi ya ɗauke abarshi.

Ya fito sabida kuka da ciwon kai da takwanta dashi yasa bataji anyi sama da ita ba.

D'akinshi ya nufa da itayana sake murmushi.......... *Barka da Safiya😂 Duk wanda bai ji daɗi ba ta biyoni da bulala😂*
[8/25, 2:59 PM] Real Mai Dambu: 🌹🌹🍀
         *MATAR SO*
                 🌷🌷🌻

*MAI_DAMBU*
*Wattpad:Mai_Dambu.*
*HAZAKA WRITER'S ASSO*
(HWA)

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai....

Dedicater To Hafsat Abubakar💋

  _Idan kinsan baki saya karki karanta sabida na kuɗine, idan kika samu an sato toh karki faɗa min maganar banza dan zan iya miki Allah ya isa, duk wacce ta fitar min Na barta da Allah_

*BOOK ONE👈*

*Page...9*
     Murmushi yake dokawa tsabar yaji daɗin satota, sai wani lumshe idanun yake irin Mamie kina can da mijinki nima na ɗauko matata.

      Shimfiɗata yayi a tsakiyar gadonshi ya mike ya zare, jallaɓiyarshi tare da boxers ɗinshi., zama yayi ya shiga cire kayanta inda ya kara karfin Ac ɗinki, zubawa wadatattun kirjinta idanu yayi kaman ya fasa ihu yake ji, zare skirt ɗinta yayi har da undee, ya barta da pant da bra, ɗinta sannan ya laluɓe duvet ya rufa musu sannan ya rungumeta a kirjin, ajiyar zuciya ya sauke tare da zubawa fuskarta ido, ɓalle mahaɗin bra ɗin yayi tare da zare mata, sannan ya shiga shagalinsa sosai ya zake yana aikawa Yar Umma da Mama aika, son rashin.
      Cikin barci take jin bakon yanayi wanda yasata buɗe nauyayyun idanunta, jinta tayi jikin mutum batasan lokacin da tayi firgit ta mike ba, tare da karw kirjinta jikinta na rawa ta juya mishi baya,

             "Rahilaaaaaah mijinkine fa, ni kike kokarin juya min baya. Kinsan tanadin da Allah yayi akan mace..."   
   Bai kai karshe ba, ta kifa kanta a pillow da ke gefenshi ta fashe da kuka, matsawa yayi har jikinta sannan ya janyota jikinshi ya shiga shafa bayanta har tayi shiru,

          A hankali ya ɗagota, yana kallon fuskarta ta ɗan haske dake

Please Login or Register in order to submit comment