Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

biyo ni ɗakina."
Ba musu ta bishi, ban san mi ya faru ba sai dai yanda na gan take tafiya yasani shiga ruɗu. Mi yayi mata take tafiya kamar Yar kaciya.
            A ɗakinshi kuwa da ya kirata girma da arziki ya fara mata magana aikuwa ta shiga mishi ɗanye kai shine ya murɗa ya biya bukatarshi tare da doka mata gargaɗi, da kuma horon fita ko ina sai bayan sati biyu.

                 Ina zansan wainar da suke toyawa ba, sai dai sun fito min ta inda ban tsamanta ba, dan har takai Mufeeda takan iya kallon idanuna na tace min karuwa,

       Ranar a gabansu Fareeda ta faɗa min.
"Karuwa kawai wacce take kazamta da Daddy ko an ce miki banga kina saka bakinki na nash...."

    Faɗuwar abu muka ji a bayanmu ashe ya shigo gidan, wayarshi tana cikin vibrater zai ɗauka yaji abinda yarshi take faɗa sai da wayar ta tarwatse gida biyu, kaman zaki haka yayo kan Yarinyar ya shiga kwallo da ita tare da fincikar wayar kayan kallo ya shiga zabga mata inda yake shiga bana yanke fita ba, shegu munafukai guduwa sukayi, tun yarinyar na kiran Mommy kozo daddy zai kashe har tayi shiru bai fasa, haka uwar yarinyar tazo ya haɗa da ita da gudu tabar gurin.
                   Bayanshi naje na runguma tare da kwantar da kaina nace.
"Mai hakuri yana tare da Allah, duka ko zagi bashine tafarkin shiriya ba, addu'a da kai wa Ubangiji kuka shine jigon shirya, sai tarbiya tasamu yanda ake bukata."
Tsit ya tsayar da dukan tare da juyawa ya kamo hannuna ya kalle ni, cikin wani irin murya ya buɗi baki zai magana amma ya kasa, ɗakinshi na mai dashi na zaunar dashi, ruwa na ɗibo mishi na bashi yasha. Sannan na xauna ɗaura kanshi yayi akan cinyata jin ɗumin ruwa yasani shafa inda nake ji a she kwalla yake zubdawa.
         Shafa kanshi na shiga yi, har naji yana sauke ajiyar zuciya, zuwa wani lokaci naji shiru kwantar da kanshi nayi a pillow na fita waje, babu wanda yayi yunkurin zuwa gurin yarinyar wacce ta suma, ruwa na ɗauki na watsa mata, ta fasa kara tare da ɗaga hannayeta, mikar da ita nayi na kaita ɗakina na haɗa mata ruwan wanka tana dawowa hankalinta taga nice..
"Muguwa azzaluma, karuwa na faɗa miki na kuma faɗa miki naga lokacin da Daddy yake taɓa nononki mayya...."
   Bansan ya fito yabiyo ni ba, sai ganinshi nayi a tsakiyarmu, sabon kuka ne ya kamata, ya riko hannunta wanda tsabar rikon sai da tasake fitsari ya kaita ɗakin Uwarta ya cillata kan balkisun da suke Waya da Mama kilishi tana faɗa mata, abinda Yunus yake musu tunda na dawo gidan,

                          Tsabar karfin cillata da yayi sai da ta bugu da center table take goshinta ya ɓalle da jini Balkisu tace.
"Mama kinga ya kashe min, dan bai san darajarta ba."

       Zama nayi ci kuka a ranar toh idan banyi sirri da mijina ba dawaye zanyi wato har yarinyar ta gano irin abinda yake min ysr shekara goma fa, na shiga uku nace.
   Shigowa yayi na goge kwallata zama yayi kusadani, yana shafa bayana, ganin balkisu mukayi ta cilla mishi wayarta ɗauka yayi yaji Muryan Hajiya tace.
"Gobe ka haɗosu kuzo zaria.".
     "Toh hajiyata"
Ya kashe wayar, kunnena ya laluba yace.
"Kina son mukoma gurin mazaje mu hau doki."
     Juyawa nayi ina mamakin yanda yake boye damuwarshi murmushi nayu tare da jan hannunshi na naɗe cikina dasu na kwantar da kaina kirjinshi ina dariya kwalla na sauka, jin bugun zuciyarshi har yana ratsani, gyara  rikon yayi tare da sauke a jiyar zuciya, kwalla ke sauka a idanunshi zuwa ka faɗata, ina ji kuma ina gani, bazan iya hanashi ba, sabida wannan itace hanyar da zai rage damuwarshi, ta zubda kwallar kwanciya mukayi.
    Yanayin ya tafi da halin da muke ciki kuma na fahimci wani abu guda shine, yunus nada matukae fusata da zafin zuciya, amma kuma mutum ne mai iya shanye zafin da kona, juyawa nayi na kalleshi ina goga hancina kan nashi, nace.
"Daddy"

       "Shiiiiiii! Am ok."
       Gyara kwanciyana nayi ina wasa da gargasar fuskarshi, ina kuma karewa farar fuskarshi da tayi ja, a yau a hankali na tsotsi bakinshi, na kalleshi har lokacin idanunshi rufe, sake yu nayi bai buɗe ba, sai da nayi mai karfi ya buɗe shanyayyun idanunshi wnda suka kara rinewa, rike kaina yayi yana bina yanda nake mishi a hankali na shiga gwada mishi irin abinda yake min, buɗe idanunshi yayi yace.
"Maryam bari haka ya isa am not in mood."
     Janye jikina nayi na juya mishi baya, tare da fashewa da kuka, yayi yana sauraron kukan nawa, wanda yake kokarin fasa mashi dodon kunne, janyo ni jikinshi yayi ya juyani yana share min kwalla, dakyar ya iya buɗan bakinshi yace.
"Miye abin kuka kuma, kinsan bani da lafiya, ga yawan tension ga jigilar aiki ga damuwar iyali maryam da wanne dan ji, gaki kina min kallon mara adalci suma wayancan suna min kallon haka, yakuke son nayi ne? Ko so kuke kuga na faɗi hawan jini ya likani da kasa ko, yanzun kiga abinda mufe..."
                  Rufe mishi bakinshi nayi da yatsar hannuna, ina kallon cikin idanunshi, nace.
"Tun fil'azal kaine ka lalata gidanka da hannunka, Daddy baka ɗauki mace da kima ba, bata da wata daraja a gurinka kasan sabida mi yasa haka?"
     Girgiza min kai yayi cikin sanyi jiki.
"Sabida dukkanmu babu wacce ka gani kake so, duk lika maka mu akayi babu wacce ka bugi jiki ka nime aurenta dan kana sonta sai dai Hajiya susaka ka cire kuɗi su haɗa maka komi kai dai tsakaninka da mace ku haɗu bayan aure ko ba haka bane? Idan ta sami ciki magana ya kare dan zata haifa maka yara, daga nan ta haihu dama bata ita kake ba ta ɗanka ne kuma ta sauke magana ya kare, zaga zuba mata kuɗi tayi rayuwar freedom ko ba haka kace ba? Daddy knn, ka ɗauki yahudu da nasara ka lika a rayuwarka ka ɗauko *Al'adun wasu* (Aunty Batul Mamman) ka ɗaurawa rayuwarka san baka yarda da komi ba sai Rayuwar bature babu addini a ginin gidanka, wanda ya dace ka tsawatarwa basu kakewa ba sai wanda kasan ko kara kasaka bazasu gifta ba kayi nazari da kyau babu amfanin aro abu a wani yaren da ba addini ba, dan ni Musulinci shine Yarena Addina."

          Zame jikina nayi dan ganin kamar yayi barci, murmushi nayi me ciwo duk surutun da nake mutumin nan ashe barci yake ma abinshi. Fita nayi na sauka kasa, na fara girka abinda zamu ci, ina cikin girkin naji an finciko ni juyawa nayi takuwa sa hannunta ta kife ni da marin a kiɗime na riƙe fuskana zata kara min na rike hannunta, cikin kuka nace.
"Wallahi sabida huda zan kyaleki amma badan haka ba, da sai na rama akan mi, kina jin ciwon dukan da yayi mata kika gaza tsayawa ki kwaceta ba, kika gudu idan da ke uwar gaskiya ce tsayaqa zakiyi dan karɓan rayuwar Y'arki amma kika gudu kin haife Yara amma baki san miye suke ba, Yar shekara goma amma tasan mi ubanta yake aikatawa kin bar Yarinya tsakanin kishiyoyi tana kara kaina, wallahi Allah bazai barki ba kuma kika kuma kara taɓa ni zan miki hauka, babu abinda ya dame ni miji kike aure nima shi nake aure baki da hujjar taɓa lafiyata."

               Wurga hannunta nayi na cigaba da aikina, sororo sukayi suna kallona wato basu yi tsamanin zan kwaci kaina ba, gashi sun zugota so suke ta kamani da duka wato ga jakarsu.

                 Yana zaune a kan kujeran Dinner table yana jinmu, juyawa sukayi duk sai da suka razana tsabar tsoro da firgici, wato a duk lokacin da suka shirya min kata'i sai Allah ya turo min shi. Idan mutum yaga tagumin da yayi sai cikinshi yayi ciwo sabida dariya, lumshe idanunshi yayi ya zauna ya buga tagumi, fuska a sake kamar bai ji komi ba haka suka fito kamar munafukai kowacce ta ja tsintsiyar kafarta zuwa ɗakinta,

       Suna fita na fashe da kuka, sosai dan sai da na rufe kofar kitchen ɗin na zauna a kujerana ɗan tsuguno, na sunkuyar da kaina kasa ina kuka, tashi yayi ya shigo yazo bakin kofar kitchen ɗin ya murɗa hannun kofar ya leko da kanshi, yana kallon yanda nake yanda na cusa hannuna cikin gashin kaina, wnda ɗan kwalin ya warware.

                        Shigowa yayi ya jingina da kofar yana kallon yanda nake kukan, takowa yayi har gabana ya durkusa  ya jima sosai kafin ya ɗago kaina, juya fuskana yayi yaga yanda yatsun balkisu ya kwanta a kuncina sai yaji ranshi ya soma ɓaci, mikewa yayi ya juya yabar kitchen ɗin ba tare da tace min kala ba.
       A hankali na mike nima na wanke fuskana na karasa chinese fried rice, da qcumbe juice sai peppe fishi, na juye su na, jera a ture na wucce dasu sama, na baza a falona.

      Na tashi na rufo kofar na faɗa ban ɗaki nayi wanka, sosai nazo nasaka riga da skirt na roba, wannan atamfar roban nan, dai na 1500, yaji ɗinki sosai dan sai ka kure mishi kallo zaka fahimci robane(😂 Toh ynz wata sai tace akan mi matar mai nasara zata ɗaura wuta sallau, ku duba gidan da Maryam tafito kuma ma yanzun matan masu kuɗin ɗaura roba suke balle mu talakawa musu ɗauƙar rayuwa high class)

                Zama nayi na ɗaura ɗan kwalin kamar yanda zahra buhari take ya zauna min sosai(Not ɗaurin zahra buhari ba sabon trender bane sunan ɗaurin dacan Maryam Babangida, muna yara dashi Dear Mama take kahe mana Babanmu yasin kuwa😂 Allah ya mata Rahama yasan can yafi mata nan kyawawan da alkhairin da abinda ta bari muzame mata, haske akabarinta, Amin Ya Allah)

       Kwali na ɗauka na murza a idanuna wanda suka jeme da kuka, sannan na shafa hoda sleek a fuskana, zubawa madubin ido nayi, jin ana buga min kofa yasani mikewa dakyar nafito, buɗe kofar nayi ina kallonshi sanye da dark brown kaftani trouse da farar janfa kana hango black singlet ɗinshi ya zura hannun da ya buga kofae a aljuhun wando ɗaya hannun yana shafa kanshi, tsayawa nayi ina kallonshi daga sama har kasa, kamshin dior na shaka turarenshi bansan lokacin dana lumshe idanuna ba, sai da ya gyara murya yana wani munafikin murmushi, tare da kashe min ido ɗaya.
"Zaki bani hanyane ko zaki tsaya kallon Daddyn kawarki."

Buɗe mishi kofa nayi ya shigo falon, nima nabiyo bayanshi na zauna  akan kujera dake kallon nashi, kallon abincin yayi ya kalle ni, na fahimci abinda yake nufi dan haka na mike tsam nayi serving ɗinshi, zan miki ya riko hannuna yace.
"Zauna muci."

    Kallonshi nayi ina jin zafinshi da haushinsa kasa nayi da kaina nace.
"Na koshi."
       Tura min abincin yayi zai mike, da sauri nace.
"Kayi hakuri zanci."
           Saka spoon ɗin nayi hannuna na rawa na ɗibo zan kai bakina ya riko spoon ɗin zuwa bakinshi, haka nasake ya kuma juye abincin bakinshi take na fahimci abinda yake nufi ina ɗiba zan kai bakinshi, falauu Aneesah ta shigo babu sallama.
    Bai ɗago ba kuma bai fasa karɓan abincin ba, sai da tazo tasa hannunta ta ɗauki kular, ya ture hannuna ya kama hannunta, ya amshi abinci. Naga tashin hankali a duniya ban taɓa sani mutum mai shiru da rashin magana wutane ba sai a lokacin yana ajiye kular ya mike da hannunta wallahi sai danaji karan kashin hannun,  zuɓewa tayi sumamiya take na fasa ihu nayi baya jikina na wani irin rawa, babu tausayi babu komi yajata, har tsakar falon da kowa yayi cirko cirko, ya wurgata ya shigo falona ina ganinshi na fara ja da baya, jikina na rawa.
         "Zoki karasa bani abincin ban koshi ba."

Ya faɗa kamar bashi ba, girgiza kai nayi nace.
"Bazan iya kaci kawai."

               Mikewa nayi yayi, nayi bayi tsabar na razana dashi saura kiris nayi karo da show glass ɗina na turaruka, yayi maza ya rikoni ajiyar zuciya na sauke tare da tafiya baya zan zuɓe, na tsorata sosai dan ko dukar da yayi min bai sani jin tsoronshi ba kamar karya hannun Aneesah kamar ba Y'ar uwarshi ba.
       Dauka na yayi ya kwantar dani akan kujera ya tashi, ya ɗauko ruwa akaramin firij ɗin falona ya buɗe ya watsa min, firgit nayi na mike naja da baya zan hantsila, ya rikoni sosai, yace.
"Ki fahimci abu ɗaya, ni bana komi sai da dalili baki min komi ba akan mi zan taɓaki, kuma nayi alkawarin bazan taɓa barin wata taci mutuncina a gaban kowa..."
        "Mi yasa zuciyarka bata iya sarrafa fushinta?"
      "Sabida ni mutum ne kamar kowa, bana son ka taɓa ni indai ina kiyayye maka."
            Kuka nasaka tare da maida kaina nayi ina kuka, ya zuba min ido.
             "Gaskiya ina jin tsoronka.".
       "Ba damuwa tunda ni bana tsoronki kawai ki bar kukan ya isa haka ki shirya mufita."

Kamar zance bazani ba sai nayi shiru, abincin da bamu karasa bakenan, ya fita nima na tashi na shige ɗakina na sako hijab ɗina, na fito, duk suna tsaye sunkuyar da kaina nayi sabida karfin kallon da suke min, na sauka da sauri ina jin mufida tana cewa.
"Mayya karuwa, me bin maza kawai."
Uku uku na haɗa step ɗin na sauka, kallona yayi tare da guntun murmushi, nima na maida mishi na wucce ganin yayi gaba,

       Shiru nayi ina nazarin, gidan Yunus da abubuwan cikinsa, bashine matsalata ba a yanzun matanshi ne matsala, dan bana ta mufida.

         Yawo mukayi a garin kaduna, har gurin cin abinci ice cream da su snack, kan da chocolet munyi kayanshi kallona yayi, yace.
"Ko xaki gaidai da ummankine."
     Zaro ido nayi cike da murna har na manta ɓacin ran da nake fama dashi nace.
"Don Allah da gaske, kace wallahi"

           Girgiza kai yayi, yana kallon hanya rike hannunshi nayi ina wani blush da fuskana.
Jan hancina yayi, na zaro ido nace.
"Karka cire min hancin."
                Hanyar unguwarmu ya nufa sai yayi parking ya kalle ni yace.
"Haka zamuje musu hannu rabbana."
  Ina hango gida, yana shirin min bukulu raurau nayi da ido ina niman kwallar da zan sauke mishi, dungureni yayi yace.
"Magulmaciya ba hanaki zuwa zanyi ba, kawai ba daɗi muje musu haka mu koma idam muka dawo daga zaria sai na kaiki ki wuni ko?"

    Sunkuyar da kaina nayi tare da gyaɗa mishi. Jan motar yayi muka koma gidan mun sami Mahaifiyar Aneesah da kannenta sun zo, da me ɗori, sai ihu take.
   Taɓe baki yayi yace.
"Umma alti ina wuni."

Yanda ta tsare gida irin bana son tsurku.

         "Yanzun Yunus gigin auren budurwa ce tasaka karya hannun Yar uwarka." ta wurga mishi tambayar.
     
       Juyawa yayi ya kalleni ganin inata gaishesu basu amsa ba sai kallon banxa suke min.
       Gyara muryanshi yayi ya kalle step ya sake kallona, kafin ya buɗe bakinshi na kama hanya. Ciki da mamaki suke kallona, har Mahaifiyar Aneesah zama yayi, akan ɗaya daga cikin kujerun falon yayi crossing leg, yayinda ya zuba hannuwanshi sama kujeran.
            Ya lumshe idanunshi bayan ya ɗaura kanshi saman kujeran, yace.
"Malam mi gyara baka gama bane? Kuma ya,zaka shigo min gida kai tsaye idan nasaka aka kamaka waye da gaskiya."

      Mutumin bai iya bada amsa ba ya haɗa shirginshi yayi waje.

           Yana jin fitar mutumin ya ɗago kanshi kallon Munira da Juwairiya yayi, irin kallon kuma ku bani guri.

   Tura baki sukayi tare da tambayar Aneesah ɗakinta, faɗa musu tayi suka hauro sama gyara zama yayi ya saka hannunshi akan fuskarshi yace.
"Umma alti!!!" har sau uku, cike da mamaki take kallonshi, murmushin  takaici yayi ya mike ya tafi ɗakinshi ya kunna wayar Aneesah da ya kwace ya buɗe mata abubuwan da ta ɗauka namu, sannan ya kunna systerm ɗinta ya nuna mata,

Sannan ya kashe yana murmushi wanda zaka san *Da ciwo a rayuwarshi*  mikewa Ummaalti tayi ta kwalawa Munira da Jawairiya kira, da sauri suka sauko fita tayi har takai bakin kofa tace.
"Kayi kokari mada iya hannun ka karya, banyi tsamanin saki baxai biyo bayan laifin ba, duk abinds ka yanke dai daine."

Tana gama faɗar haka tayi waje cike da kunya da ɗan danasanin, zuwanta da maganar da tayi mishi.

             Ina zaune ya shigo har lokacin fushi nake dashi dan yaki kaini gurin Ummana, amma a haka alewar tsinke ne a bakina, yana shigowa na kauda kaina, tare da zare alawar lasa, sannan na maida bakin, sake cirewa nayi na lasa cike da jin daɗi, amma zuciyata ba daɗi sam, ɗaukar ledojin yayi ya fita dasu, ya kaiwa kowacce ɗakinta, a wulakance suka kalleshi.

   Koda ya dawo ya mika min nawa na amsa nace.
"Allah ya kara buɗe."

              *Allah ya haɗamu gobe a zaria😉 dan mai nasara ya zama abin tsoro*
[8/25, 3:00 PM] Real Mai Dambu: 🌹🌹🍀
         *MATAR SO*
                 🌷🌷🌻

*MAI_DAMBU*
*Wattpad:Mai_Dambu.*
*HAZAKA WRITER'S ASSO*
(HWA)

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai....

Sadaukarwa Ga Yan grp ɗin Matar So....
Dedicater To Hafsat Abubakar💋

     _Wannan buk ɗin hakk'in masu shine idan kinsan baki saya ba karki karanta, mai fitarwa kuma ki duba girman Alkawarin da kika ɗauka na cewa bazaki fitar ba, tunda nace idan kinsan zaki saya ki fitar na Yafe ba sai kin saya ba_

*BOOK 1👈*
         Page....28

               Shiru yayi jikinshi yayi matukar sanyi, shi dai abinda yake ji akaina daban ne da sauran sai dai baya jin zai iya zuwa ga abinda zuciyarshi ke tilasa shi, dukda mallakinshine ni ɗin.

                Janye jikinshi yayi  bayan ya ja hancina, yace.
"Baki da kunya kin wani makale ni sai kace wacce kika sami wani pillow common my dear zoki ci abinci."
                 Karamin murmushi nayi wanda ya karawa fuskana kyau nace.
"Allah ko Mai Nasara? Ji bika kato da kaine zan makalewa kasami jinjiran yarinya sai juyata kake son ranka, ko ba haka ba."

                        Ware idanunshi yayi nima na kashe mishi nawa nace.
"Iya gaskiya na faɗa maka babu karya ciknta, sai gaskya tsiraranta."
      Rike baki yayi yana wani gyaɗa kai kaman kadangare, sai ya bani dariya har ina rike cikina, nuna shi nayi da yatsar hannuna nace.
"Ɗaddy!! Kaga yanda kake kuwa hmmm."
        "Karki bari na kamaki, dan zakifu kowa wahala sai na kashe bakin rashin kunyarki nan.

      Murguɗa bakina nayi na fashe da dariya har ina tafa hannuna nace.
"Yo..."
         Ganinshi nayi a gabana, cak na haɗiye tsokanar ina kallonshi cikin tsoro nace.
"Daddy Am sorry, bazan kuma ba Allah yana tare da masu hakuri kaga ni har ynz am still baby."
                Sama gado yayi dani na fasa mishi ihu sai da ya toshe kunenshi, ganin haka na zille zan sauka ya kamoni, tare da jibga min nauyinshi.

       A nan idanuna suka rena fata, dan ji nayi kamar ya ɗaura min aiki.
            "Kayi hakuri ban kumawa."
        "Karya knn ina kyaleki zaki kara min wani."
      "Da gaske nake."
             Haka ya gama tumurmushime ni son ranshi kafin ya kyaleni dan yace shi ynx kukana baya damunshi kaman da.
              ****
   Kwanaki goma mukayi kuma kowacce kwana sabonta kanta take da abubuwan Al'ajabi ga dai miji nasame shi amma banzar aqidar Yahudawa ta kama zuciyarshi ko nace ra'ayi rikauu.

                Ranar da muka cika sha ɗaya muka bar garin bayan munyi tsaraba, sosai har dasu Umma Hajiyan zaria kowa dai, ya samu.
           Mun sauka a lag daga nan muka bi jirgin kaduna, muna isowa Aman yazo ɗaukarmu sai tsiya yake mashi,  yaki magana sai murmushi kawai.

             Koda isa gidan mun sami Aneesah, gaida ita nayi a mutunci tare da tambayarta ya jikinta.
    Taɓe baki tayi tare da yatsina fuska tace.
"Sauki."
         "Allah ya baki lafiya."
    Amin tace min,
            Sosai nake kallon ramar da tayi, shigowarshi ya kafeta da ido, cike da mamaki yanda ta rame ta zabge, a cikin kwanakin ds basu fi sati biyu ba.
                        Zama yayi a kusada ita tare da riko hannunta mai lafiyar Yace.
"Neesah mi yasameki haka? Ko kinyi ciwone?"
           Narkewa tayi a jikinshi tare da gyara kanta a kirjinshi, satar kallona yayi yaga sam ban sauya fuska ba saima tausayinta da nake ji.
             "Mai nasara cikine, na six wks amma nayi abortion ɗinshi sabida wahalar karta min yawa ga ciwo a hannu ga wahalar laulayi, ga rashin zuwa aikina."
    Shafa kanta yayi cikin tausayawa, yace.
"Sannu haka da kikayi shine dai dai, kuma ya kamata ki nemi wani abun kariy......"

            "Daddy!!! Kai da kanka kake kara mata kwarin gwiwa dan ta zubda kyautar Allah, wannan wani irin rayuwa ce kuke yi a gidanka, Cikin da wasu suke nima kasa kasa, har ɗakin Allah suke zuwa suna kuka Allah ya basu haihuwa, Anya kayiwa ɗan tayin da aka cire adalci wallahi Allah bazai kyaleku ba."

     Sam ya manta ina falon ya zauna suke maganar cikin.
      ......Tsawa ya buga min, tare da mikewa kamar zai cinye ni, lokaci guda jikina yayi matukar sanyi yanda yake faɗa min magana har da kirana jahils shashasha, wannan kalmar tasani kuka musaman jahilar,.saukar da kai nayi.
          "Kayi hakuri mantawa nayi manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi yace.
Karda kashi ga abinda babu ruwanku, sannan a gaba kuma yace Imanin ɗayanku baya cika har sai ya sayawa ɗan uwanshi abinda yasaiwa kanshi kuyi hakuri dan mu rabauta tare ne yasa nayi magana amma Insha Allah bazan kuma ba. Kayi hakuri Daddy."
           "Wucce ki bamu guri, sai kinyi abu ki koma kamar na Allah nan kuwa kinfi kowa salon munafucin da kinibibi, Don Allah kace  tabar min nan kaina ciwo yake "
D'ago kanshi yayi ya kalleni tun bai karasa abinda zai fito bakinshi ba, na bar falon har nakai step yace.
"Waye zai kwashe miki kayan? Ko baki ga halin da nasami Aneesah bane,oya sauko ki kwashe.?
Kamar zan fasa ihu haka na sauko nazo na kwashi kayan, na wucce da nashi ɗakinshi, nawa kuma nakai sama. Cire kayana nayi na shiga gyara ɗakina, ina gamawa nayi wnka da sllah, sannan nazo niman abinda zanci.
Duk sun halarra a falon, har da balkisu sai hira suke dukda akwai rashin sabo amma na fahimci anyi haka ne dan a nisantani dashi, kuma hakan ce ta faru.
Shinkafa da miya nayi sai salad, da zoɓo. Ina gamawa na zuba mishi nashi a warm na ajiye akan dinner na kwashi nawa zuwa sama, babban kuskurana shine rashin faɗa mishi na gama amma ai nasan dukda haka yasan na gama girkin tunda, sau biyu yana ɗaga kanshi ya duba ni daga falon sai

Please Login or Register in order to submit comment