Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gamawa, yayi mata godiya da zai tafi yace mata.
"Idan mai gidan ya dawo kice ya sauya kofar gidan nan bai dace da gidan ba."

Bayan mai gidan ya dawo wato Annabi Isma'il ta faɗa mishi wani tsoho mai kama kaza mai kala kaza ga abinda yace, aikuwa Annabi Isma'l yace mahaifina ne kuma yana min ishara da na rabu dake."

Next zuwanshi yasamu Annabi isma'il yayi wani auren daga zuwanshi matar ta tarɓeshi ta shiga mishi alkhairi da kyautata mishi haɗi da faɗar alkhairin Mijinta ta ɓoye sharrinsa ta nunawa kowa mijinta na kyautata mata sama da komi.....

Ban kawo maka wannan maganar dan ka zauna dole da Maryam ba dan nima nafi son ka saketa nabawa sulaimanu, ita shi zai iya zama da ita komin muni halinta, dan nasan shi ɗin mai biyayya ne da muradin Iyayenshi. Sati biyu jal na baka kawo min takardanta kaje ka zauna da wayayyun matan, sannan kuma kar na kuma ganin kafarka a cikin gidana indai ba da takardan saki ba, tashi ka tafi Allah ya bamu alkhairi."
Tashi yayi ya fita jikinshi a sanyayye, dan bai wani ji ba daɗi ba.

........Ni kuwa zafi jikina yayi sosai amma na boyewa huda har tayi barci amma ni na gaggara barci.

.......Shiru Alhaji yayi kafin yace.
"Miskili yana sonta bai san yanda zai janyo hankalinta bane amma bari muga gudun ruwanshi."

Mikewa sukayi kowa ya nufi inda zai kwana amma nikam barci yaki idanuna.
Har aka kira sallar asuba a lokacin jikin yayi zafi fiye da jiya, dan nonon sun kumbura sabida famasu da nayi ga zogi azaba, tun ina kuka har na daina na lumshe idanuna koda Huda ta tashi taɓa goshina tayi tajishi da zafi ta fita ta kira Mama, suna zuwa aka fito dani, shirya jikina sai da huda ta taimaka min, aka fadawa Alhaji,, asali bansan miye duka ba a rayuwata ba, kuma dukar da yayi min a kirjina ya haifar min da ciwo ga jikina da yayi mugun tsami.

Dakyar muka fito zuwa gurin motar Alhaji, dai dai shigowarshi daga masalaci kenan, tsura min ido yayi tare da lasar bushashiyar laɓɓashi, ɗago kaina nayi idanunmu ya sarkafe da juna, kwalla ce ta zubo daga idanuna na kauda kaina, shiga motar mukayi na kishingiɗa ina sauke ajiyar zuciya.

Yana son magana Amma Mama kilishi ta tsare gida, haka muka fita muka barshi a gurin, wani asibitin kuɗi aka kaini take, aka shiga bani taimakon gaggawa, daga allurai da drip.
......... Muna fita shima ya haɗa shirginshi sai kaduna......
*****
"Kaii Abban Chuchu baka gajiya ne da abu ɗaya nifa cikina ya fara ciwo." Inji Rahimah da take kwance a jikin Ahmad bayan ya gama murzeta son ranshi, a gidanshi dake Cikin gidan iyayenshi a garin katsina
Dariya yayi sosai sannan yace.
"Yarinya zakiyi bayani ma raguwa kawai amma kina kokarin taimaka min gurin samin nutsuwa, nagode Rahimahta."

K'amk'ame shi tayi tana murmushi, rungumeta yasake yana shafa abinda yake bala'in so a jikinta ganin haka ta gyara kwanciyar yq cigaba da yin hidimarshi dasu.
****
A garin maiduguri cikin Rahilah ya fito sabida bata da jiki, zama tayi a gaban Mamie tana cin abincin da aka mata da safe Mamie sai murmushi take cike da jin daɗi tace.
"Rahilah, ina Aman banganshi bane."
Murmushi tayi kanta a sunkuye tace.
"Mamie ai yana sama, aiki yake a can yasa baki ganshi ba."

"Kema yunwar cikinki ya koroki da bazan ganku ba sai rana." Inji Mamie, dariya Rahilah tayi, kawai.

Dukkansu suna cikin farin ciki da jin daɗi.

.........
Ya isa garin kaduna karfe bakwai da rabi ya tattara al'amarina ya watsa gefe, ya shiga hidimar gabanshi.

........Sai da na kwashi kwana biyar asibiti, aka sallameni, nan huda ta shiga haɗa kayanta zata koma, kamar nace zan bita amma nayi shiru, dakyar muka rabu ita kuka ni kuka, haka na dawo kamar kurma.
Bana zama a cikin mutane sai a ɗaki, dakyar nasami wayata na kuna kullum ina online, muna hira dasu Rahilah amma ban faɗa musu abinda ya faru ba dan nabarshi a sirrin gidana.

**** Sati ɗaya babu shi babu dalilinshi, har aka shiga sati nabiyu aka cinye kwanakin, da yamma Hajiya takirashi cike da masifa tace.
"Kaiii Yunus kafita idanuna ka turo min sakin yar mutane wato ga dattawan banza ko nabaka nan da kwana ɗaya kazo min da takardanta ko nina zo maka." kashe kiran tayi abinta.

.......Yana zaune a office takirashil, lumshe idanunshi yayi cike da tashin hankali yake jinta, idanun nan kamar jan gauta, Aman ne yace.
"Mr Marafa lafiya?"
Tashi yayi ya zauna dakyar ya iya faɗa musu halin da yake ciki, shiru sukayi Ahmad yace.
"Ka daketa kuma, sabida tana Period taɓata maka ɗaki, Mai nasara, lallai da kaine da Hafsa da ka harbeta."
Nan ya faɗa musu abinda tayi mishi na rufe mishi datayi zaro ido sukayi, murmushi yayi yace.
"Kuma naki saketa, ina kallonta da abinda tayi ni kuma naxe mi? Gaskiya baka kyauta ba, gwara kasake musu yar mutane gari da yawa mayye baya cin kanshi, zata sami wanda zai riketa tsakani da Allah, wai ma kai miye matsalarka da itane kaga yanda Yan uwanta suke kokarin kyautatawa Rayuwarmu."

"Rabu da ɗan iska, don Allah ka saketa zan nimawa wani cousin broda na aurenta kuma kaga shi ba anan yake da zama ba ɗan kwallon Real Madrine kuma karamin yaro dan 29 ne bakai da kake niman 42 ba, zai iya janta nisan zango har sau uku ko hudu."

"Zanci abu kazan kazanka shege ɗan iska, matar tawa kake faɗa min wani namiji zaiyi sex da ita har sau hudu a dare billahilazi sai naci Uban tsinane."
Inji mai nasara, take yashiga fasa duk wani abu na cikin office ɗin, ya fita zuwa gidanshi, yana zuwa yasami gidan a rufe nan ya tambayi maigadi ina matan gidan, shiru mai gadin yayi kafin yace.
"Ai sun koma gra nazata kasani ne, yau sukayi parking."

Jan motarshi yayi yana huci sai yaci mutuncinsu, Yana isa gidan ya sami falon kaca kace, Sameer ya hargitsa kuma yana kai a tsaye uban na shigowa ya kalleshi shekeke, ya cigaba da ɓarnan shi.

Ranshine ya kara ɓaci sakamakon hango kitchen ɗina abuɗe anyi kaca kaca da komi na ciki kamar an basu ajiyar,

Ajiye jakarshi yayi ya haura sama, dukkansu suna ɗakinsu sai Balkisu da take kishingiɗe. Rike k'ugu yayi cikin azalazaliyar ɓacin rai yace.
"Wani shegene ya baku izinin dawo gidan nan ba tare da sani ba, kuma wata Yar iskace ta shiga kitchen ɗin Maryam Sajida."

Shiru tayi cike da mamaki yaushe mai nasara ya zama haka,ta lura tun dawowarsh sallah a zaria yake niman abokin mutuwa ya rasa, sai tayi shiru tana kallonshi.

"Nice nan na shiga kitchen ɗinta, kuma akan yarinyar da aka cusa maka kake wannan zage zagen sai kace wani sonta kakeyi yarinyar da nasami labari ka mata dukar kaw...."

"Ya isa wucce kije ki m gyara inda kika bata kafin naniki dukar mutuwa." Ya faɗa mata azafaffe.
Kallon reni Fareeda tayi mishi kafin ta taɓe baki tace.
"Bazan gyara ba."

Sam baisan mi yasa tunda aka ce mishi ya rabu ds Maryam yake jin haushin kowa ba, fincikar hannunta yayi suka sauko kasa ya wurgata kicin ɗin yace..
"Minti goma ki gyara kafin na shiga jikinki."

Dariya tayi tare da cewa
"Hehehehw yeenanaye, Kana taɓani zan baka mamaki,har ka isa kace zaka taɓa ni kai namijine da zai nuna ikonshi a gidan nan toh bari na fada maka wallahi idan ka duke wancar jakar ka kwana lafiya ni bazak..."
"Tabbas bazan taɓa ki ba, amma kije gidanku sai nazo"


"Karya knn wallahi sai dai kai kafita min a gida dan nice mai ɗa namiji, a gidan banza lusari kawai."

Runtsa idanunshi yayi, nutum ɗaya ce takira shi da lusari yayi hakuri bayan ita bayq jin zaiwa wani hakuri a kirashi lusari ba.

Buɗe idanunshi yayi wanda suka ciko da kwalla yace.
"Kije na sake ki saki ɗaya................"

"Wayyo Allah na, ni kasaka" Yunus ya faɗa da karfi " get out."
Take kowa ya kama kanshi, kitchen ɗin ya shiga yana kallon yanda aka hautsina komi, take jikinshi yayi matukar sanyi, sana ya koma ya buɗe ɗakina yasami Mufida sai hautsina ɗakin take,

Harɗe hannunshi yayi a kirji, yace.
"Kin mata ajiya ne."

Juyawa tayi a tsorace, tace.
"Babu." a shagwaɓe, zuwa yayi ya kamo kununta ya murɗa sai da tasaki fitsari aikuwa ya falla mata mari, ihu take tare da kuka yace.
"Ki ɗauko mopp ki goge mata ɗakinta kuma ki maida kayan if not."

Fita yayi daga ɗakin, yana jin cin kaniyar kows duk wanda ya kawo mishi wargi.

A daren ya shirya zuwa zaria bai faɗawa kowa ba.

****
Ina kwance bayan sallar isha ina bin kira'a sheik Abdul rahman sudais. Idanuna a lumshe dake hajiya da Mama sun fita ɗazun gaida wata yarsu da aka kwantar a asibiti.

Ban ji sallamarshi ba sai ganin mutum nayi a kaina mikewa nayi salati.
Zama yayi akasar kafet ya zuba min ido, tsuke fuskana yayi cike da tsiwa nace.
"Mi haka zaka shigo kan mutane babu sallama, ayi magana ka rufe mutane da duka." na karshe maganar tare da murguɗa bakina.

Murmushi yayi sannan ya mike yazo inda nake zaune yace.
"Su mutane har nawane a gurin da ban gansu ba."

Hannunshi naji yana turawa cikin zanina na tureshi tare da ɓata fuska nace.
"Bana son iskanci, nayi magana a zane ni da belt."
Matsawa yayi sosai ya shiga kokarin haɗe jikinmu na kai mishi duka a kirji tare da tureshi, amma ko gizau saima kokarin sumbatar bakina yake naki tsayawa.

"Shika musu yar mutane" Inji Mama mikewa yayi yana sosa kai yace.
"Kun dawo lafiya."

"Lau ina sakin yar mutane yake " Ta mika mishi hannunta,

"Mama don Allah kuyi hakuri mana magana baya wuccewa ne yanzun na bata hakuri fa."

"Dake mune sa'anka shine zaka rena mana hankali fitar min a falona."

Gurin Umma ya nufa itama tayi mishi koran kare, Alhaji na dawowa ya haɗa mishi nashi zafin, kamar zaiyi hauka kuma yana binsu da suyi hakuri amma firr suka ki kulashi sai ma koranshi da sukayi,

Washi gari da ya shigo basu amsa gaisuwarshi ba sai mika mishi hannu alhaji yayi cikin tashin hankali yace.
"Alhaji kuyi hakuri bazan iya ba."
"wallahi tunda ka iya faɗa mana nakasunta na rashin wayewarta sai ka saketa ko kuma na baka mamaki ka bani takardanta"

"Alhaji wallahi bazan iya ba, ka taimaka min kuyi hakuri."

"Tashi kabar min gida kar na kara ganinka sai da sakinta ko kuma na baka mamaki mutumin banza, kawai."

Hmmm kamar mahaukaci haka ya koma a cikin kwana biyu, Ahmad da Aman sun zo Alhaji yaki kulasu saima koran da yayi musu, ina ɗakin hajiya sanye da 3qtr, da riga mai dogon hannu amma kirjin a buɗe. Ya shigo dakesu hajiya suna falon Alhaji suna hira.
Kaina yayo kamar wani kura, ko tsorata banyi ba, niman taɓa ni zaiyi cikin tsiwa nace.
"Anga banza, ko? Toh baka isa ba koda wasa ka taɓa ni sai na maka ihu."

"Wai mi kuke sonayi ne, na basu hakuri sunko abokaina sunzo sunki, Don Allah mi zanyi muku ne na gaji da izayarku ni kizo mutafi, gida."

"Babu inda zani, koda zan tafi gidan iyayena zani."

Shiru yayi, kafin nace wani abu ya saɓeni a kafaɗarshi, yayi waje dani.

A tsakar gida muka haɗu dasu Hajiya ina cewa.
"Sauke ni babu inda zan bika ai kasan da haka ka min shegen duka."

"Sauketa!!... Kuma sai ka saketa yanzun ko nayi maka Allah ya is."

A razane na sauko a kafaɗarshi na kare shi ina girgiza kai kwalla na zuba idanuna nace.
"Hajiya Ubangiji muna masa laifi ya yafe mana, balle kuma mu ya mu, yan adam."

Zubewa nayi a gabansu tare da fashewa da kuka nace.
"Idan Iyayena suka ji haka wallahi Umma sai ta zare ni a cikin Yaranta horon yay...."

"Tashi ki bani guri, sake kine sai yayi fa. Kuma na baka nan da awa biyu ko kuma na maka Allah ya isar. Kema ɓace min da gani."
. Da gudu na mike zuwa ɗakin da nake na rufe, shi kuma ya fita...

*****Washi gari da safe Mama tasani a gaba sai kaduna Gidan Mamie ta faɗa mata komi, sannan tayi min nasiha tare da nuna min dalilinsu na haɗa mishi zafin kai.....

😂😂😂😂😂😂
[8/25, 3:00 PM] Real Mai Dambu: 🌹🌹🍀
         *MATAR SO*
                 🌷🌷🌻

*MAI_DAMBU*
*Wattpad:Mai_Dambu.*
*HAZAKA WRITER'S ASSO*
(HWA)

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai....

Sadaukarwa Ga Yan grp ɗin Matar So....
Dedicater To Hafsat Abubakar💋

     _Wannan buk ɗin hakk'in masu shine idan kinsan baki saya ba karki karanta, mai fitarwa kuma ki duba girman Alkawarin da kika ɗauka na cewa bazaki fitar ba, tunda nace idan kinsan zaki saya ki fitar na Yafe ba sai kin saya ba_

*BOOK 1👈*
Page....23
      

      Duk sai naji ba daɗi wallahi abinda akewa Mai nasara yayi yawa, tunda na dawo kaduna nake kuka amma a ɓoye ga wasu mahaukatar gyaran da Mamie ta min.

              .......
   Zaune yake ya buga mugun tagumi, duk ya tara uban kasumba kamar wani mahaukaci yayi shiru miskilancin ya sake ka ruwa fiye da, baya magana ake amma yaki magana kuma akan kasuwancinsune. Amma ko ɗaga kai bayi ya kalli Ahmad dake bayani ba.
                Cusa hannunshi yayi cikin sumar kanshi da ya tara, yaki komi fa, banda wanka da sauya kaya Yunus baya komi dan kyamar ɗakinshi yake babu mai gyara mishi, ga gidan ya koma tankar gidan mutuwa dan daga Aneesah da Balkisu kowacce ta shiga hankalinta, sai iyayen fareeda da suketa bibiyarshi ya mai da ita firr yaki sauraransi.

       Karshe zaria Ubanta yaje sukayi magana da Alhajinsu yace.
"Kyale shi ta koma ɗakinta laifi yayi muka hukuntashi, shne ya dira akanta kuma ya kamata su kiyayye abinda zai shiga tsakaninsu na rashin fahimta tunda kaga ya iya saketa toh matukar suka cigaba da shige masa zai botsere musu."

     Da haka sukayi sallama koda mahaifinta ya dawo ya tambayeta mi ya haɗa su da Yunus ta shiga kame kame karshe dai ya fahimci bata da gaskiya take ya sunketa yayi mata tasss sannan yace.
"Kamar yanda kika zo da kafarki haka zaki koma babu me maidake."
          Haushi ya cikata gidan kawarta kubra taje ta faɗa mata.
"Hmmm ke kina ganin mi ya sauya shi lokaci ɗaya, mutumin da bayi magana shine har da saki."

           "Hmmm dan nace ya daki jakar Amaryanshi, kuma na gaya mishi magana fa dan har lusari na ce mishi."

            "Tashi ki tafi gidanki bazan iya rakaki ba, sabida baki san darajar aure ba mi kika nima kika rasa, komi na rayuwa Allah ya baki shine kikewa kanki bakin ciki tashi ki koma Allah ya tsare na gaba."

            *****
      Yau ta kama sunday, ɗakina ya koma da zama dan shine a tsaftace zama yayi yana shakan kamshin turarena wato Jameela,  ya rasa ta inda turaren yake fitowa, kamar ance ɗaga pillow.

  Sai ga Bra da pant ɗina, wanda na cire ana saura kwana biyu tafiyarmu zaria zan sakasu na ajiye nasaka wasu da Huda ta nuna min, dan har na fesa musu turare.

     Lumshe idanunshi yayi ya janyo su, tare da ɗaura akan fuskarshi damke yayi yana jin wani irin kewana a jikinshi da jininshi, tuna yanda yake shakar kamshin a jikina, babu abinda ke gigitashi yasaka kanshi a kirjina ga kamshi da ɗumin jikina, ji yayi kanshi zai kunce magana ya shiga yi shi ɗaya yace.
"Miye take dashi da sauran basu dashi? Mi nake ji a jikin tane? Banda kuka da reni mi tasani?"

          Take wani gefe na zuciyarshi yace mishi.
*Nutsuwarka da kwanciyar hankalinka duk suna gareta, tana da abubuwa da kai baka san dasu ba, hakuri, juriya, duk ta haɗa ga kyakyawan mu'amala, itace zaka taɓata bata ce maka wani abu ba ka tashi ga barcin da kake, ka dubi kanka ka dubi ɗakinka mana, kaima gudun hijira kayi sabida kaxamtar matanka tunda gashi babu wacce tayi tunanin gyara maka da itace kuwa kai kanka har saurin ka dawo gidanka kake..*

Mikewa yayi ya dafe goshinsa sauka yayi a gadon,  ban ɗakin ya shiga ya ɗauki shaving cream ya shafa a kasumbarshi ya shiga haskewa, yana gamawa yayi wanka ya fito..

   Bai zamd ko ina ba sai ɗakinshi ya,zaro shadda sabuwa gal fara sol,yasaka sannan ya ɗauki bakin takalmi ya zura sama sama ya gyara fuskarshi ya fita daga ɗakin, yana fitowa falo ya cikaro da Fareeda, kara tsuke fuska yayi cikin masifa yace.
"Uban waye ya baki izinin dawowa?"

   Sunkuyar da kanta tayi tana kokarin ɓoye ɓacin ranta tace.
"Alhajin Zaria."

   Raɓa gefenta yayi ya fice, gidan Aman Yaje ya kirashi a waya lokacin yana fama da Hindu tayi wanka sai rena mishi hankali take, kuma baya son zuwa ga Rahilah dan karsu shiga hakkin Hindu.

           A mota yasami Mai nasara, gyara zama yayi yace.
"Allah ya taimaki wakilin marafa, Mi kake bukata."

     Banza dashi yayi kamar bazai magana ba ya juyar da kanshi, har na wani lokaci.

   Harzuka Aman yayi cikin jin haushi yace.
"D'an iska lokacin da ka daketa kasan zaka shiga ukune ai na faɗa maka jinjira bata da sauki ni zan fita dan yau hutu ake tunda baka da abin fada."

    Buɗe murfin kofar yayi, maza mai nasara ya rike shi.
"Mi yasa ku baxaku fahimci halin da nake ciki ba? Mi yasa kuke jin zafina? Koma mi nayi ban kamaci wulakantawarku ba, duk matsalarmu iri ɗaya ce, amma mi yasa kuke ganin laifina."

      Juyawa Aman yayi cikin tausayawa yace.
"Eh laifinka muke gani, sabida ka gaza hakuri da yar sha bakwas, amma kana zaune da yan talatin da wani, Yunus bazan ɓoye maka ba kai ka lalata rayuwarka da na gidanka, kuma daga auren Maryam wasu halayarka naga ka ragesu, musaman rashin sake fuska, haka kawai zaka zauna kayita murmushi kai ɗaya, kana son Maryama amma kake bawa kanka wahala."

"Kaii Wallahi ko sau ɗaya bana sonta, dai ina jin ba daɗine akan rashinta, ka yarda dani."

  Wani irin kallo Aman yayi mishi, me ɗauke da renin sense, ga soyayya kuru kuru har da rantsewarshi taɓe baki yayi ya buɗe motar zai fita.

     Mai nasara yace.
"Aman kaima juya min baya zakayi?"
                  Murmushin gefen baki Aman yayi sannan yace."Kowani cuta da maganinshi sai dai mituwa ce babu maganinta Yunus You are in love amma kake musanta min magana well zan baka shawara kaje zaria ka samo kanta idan haka ta faru zan baka final shawara."

Yana gama faɗa haka ya juya yafita,

   Jan motarshi yayi sai zaria,nan ya tarda kwandon bala'i har sai da ya kusan zubda kwalla.
"Wato dan ka maida mu marasa mutunci shine muka nemi sakin kaki bada ko Yunus ka bani sakin Yar mutane ko na saɓa maka, wai shin mi kaida Mutane ne abokan wasanka har kana sake ɗayar matarka muda muka ce ka bamu sakin maryam sai ka saki Fareeda toh bani takardan Yar mutane mara mutunci saɓo tumaki ɓallo jaki bani, kaje mugun halinka ya taimakeka."..

    Shi kanshi abin duniya ya dame shi, muka ya kasa magana mikewa yayi ya bar falon Alhaji, zuwa falon Hajiyarsu nan yayita raba ido bai gani ba,

     Karewa mikewa yayi zuwa ɗakin hajiya ya sami ɗakin Wayam, babu ni babu alamata.

Gurin Mama ya dawo tace.
"Kazo dubawa kotana nan  ne? Toh mun ɗagata daga gidan nan kafin ka shiga rayuwarta."

"Amma..."
"Dakata fitan min a ɗaki kaje can..."

      Fata fata suka mishi dawows kaduna yayi ya kira Aman ya faɗa mishi, halin da Yake ciki.
      Dariya Aman yayi yace.
"Ka wucce gidansu kasami Iyayenta da maganar, zaka sha mamaki yau duk inda Maryama take a chest ɗinka zata kwana.".
Kashe kiran yayi ya nufi, tudun wada, a kofar gida yayi parkin ya tura yaro akan mijin Maryam ya zo.

     Ya kabiru ne yazo ya shiga dashi cikin gidan, aka shimfiɗa mishi taburma ya zauna, gaisawa sukayi da Umma da Mama.

     Cikin nutsuwa ya faɗa musu  halinda yake ciki, tare da nuna musu shine da laifi amma iyayenshi sunce ya sake maryam don Allah ayi hakuri bazai kuma ba.

               D'aga labule umma tayi taga karfe biyu da rabi, kallonshi tayi kafin tace.
"Zuwa karfe shida na yamma Kabir zai kiraka."
        Godiya yayi sosai sannan ya tashi zai tafi ya ciro kuɗi zai ajiye tace.
"Yunus ɗauki abinka, mu y'a muka baka ba abin hannunka muka duba ba."

Duk yanda yaso ta amsa amma fir suka ki karɓa koda suka fita da Ya kabir sun taɓa hira har zuwa matakin karatu, mika mishi card ɗinshi yace.
"Kazo da takardunka, dama muna niman wanda zai zauna mana a kamfaninmu na Abuja kuma mun samu."

    Godiya kabir yake kaman yayi ihu dan murna, haka sukayi sallama,

          ....... A cikin gida kuwa ɗaukar waya Umma tayi takira Mamie suka gaisa, cikin tsautsayi Mamie tace.
"Maryam Sajida, duba min miyar nan nakan gas,"
"Toh Mamie"

    Aikuwa kashe kiran Umma tayi tasaka hijab dinta sai gidan Mamie, muna tsaka da hira mamie na faɗa min.Umma takira fa, take naji yan hanjina

Please Login or Register in order to submit comment