Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

3Q da vest wacce ta dame shi yazo ya tsuguna kusa da ita ,har gwiwarsa tana taba tata ya zuqi tabar ya fesa Mata afuska idanshi jajazir ya kalleta gami da cewa"ke mai kikayiwa babban yaro haka ya shi go dake ya ajiye ,gaki kyakykyawa,Vrysoon, nan ba gurin kuka bane ki tashi muje kiyi Wanka ki more kuruciyarki ,in kina fama da talauci zan baki kudi masu tsoka kiyi rayuwa tunda na ganki naji kin kwanta min a raina inaso ki zama yarinyata ,zan baki million biyar da farko in har na tabbatar da cewa kidin budurwa ce ,babu namijin da ya kwanta dake ,tabbas dagani nasan zakiyi tes"
Ya karashe maganar yana lumshe ido gami da lasar lebanshi kana gani kasan a buge yake


Maryam tayi saurin matsawa gefe tana jan jiki ta sa gefan hijab dinta ta toshe hancinta dashi sai tari take,duk addu'ar da tazo bakinta tana yi"



Ya kwashe da dariya yana nunata da hannunsa yace"ke "yar kauye mai ye haka kikeyi ai a hankali zaki saba,nasan dai ko ba'ataba yin sex dake ba ,kin tabayin romcing sabida haka kar ki raina min hankali , baby"



Kuka Maryam tasa tace"Allah ya tsareni daga sharrinku ,insha Allahu ni nafi karfinku ni ba "yar iska bace ,kuma ina muku addu'ar Allah ya shiryeku shirin addinin musulunci"



"Ke!! Kifquit" yafada cikin tsawa hade da mikewa tsaye yana nunata da hannu yace"kamar ni Indan dan! Zaki tsaya kina gaya min magana Dan uwarki ko shi Nass din bai isa ba sabida yasan ko ni wanene ,a wannan guri duk yarinyar da nagani inaso batayin gadda ma sai ke ,da me kike taqama iyee!!
Tafada cikin qaraji yana kaiwa da kawowa tare da yin tsalle


Maryam ta tsorata ,sai kuka takeyi tabi ta kamkame jikinta a cikin hijabinta


Cikin bada umarni yace "tashi muje ko insa karnikancan su yagalgala min namanki"



Kallonsa tayi taga babu alamun rahama a tartare dashi sannan ta waiwaya ta kalli inda wasu girda gurdan karnika suke su kusan goma suna kwance kowqnne wuyanshi rataye da sarqoqi rakwacam sai dallaro da harshensu sukeyi
[23/05/2019 6:45 PM] Binta Umar Abbale: Ta mike da gudu tayi bakin get din gurin inda masu gadin gurin suke zaune suna kallon duk abinda yake faruwa a gurin.

Babu abinda ya damesu

Shima ya bita da gudu suka kasa tsere ya cimmata ya tare jikin get din gami da danne ta da jikinshi ,sai shinshina ta yakeyi kamar wani tsohon maye ,Maryam ta dinga kauda kanta sabida yadda take jin hucin numfashinsa yana wani mugun wari zuciyarta ta dinga tashi, sai kau da kai takeyi



Fuskarta ya riko da dukanin hannuwansa ya kura mata jajayen idonsa masu kama da gauta so yakeyi yahada bakinsa da nata


Daf yake da ya hada bakinsu guri guda ,yaji anyi masa wata muguwar bangaza wacce tasa ya kusa faduwa da kyar ya tsaya da kafafunshi ,sabida jikinshi babu kwari, ta juyo a fusace yanaso yaga wane dan iskan ne yayi mishi wannan iskancin,


Nasir ne tsaye ya kura masa ido sai huci yakeyi kamar wani Dan dambe,


In dan dan yace" kai wane irin iskanci ne wannan yaya ina jin dadina zaka zo ka wani bige ni"


Babu abinda Nasir yace dashi tsabar bakin ciki ya kalli Maryam wacce take makure jikin bango jikinta sai makyarkyata yakeyi zuwa yanzu hawayen ya daina fita daga idonta zuciyarta ta kekashe"


Cikin bada umarni yace"wuce mutafi"
[06/06, 01:44] +234 808 996 5176: [24/05/2019 8:47 AM] Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*

*86*


Da gudu Maryam ta je ta 6oya a bayan Nasir din zuciyarta sai harbawa takeyi ,cikin kuka tace "uncle wannan macuci ne kai tai makamin zai keta min haddi"
Nasir ya kara daka mata tsawa a karo na biyu yace "yau kinga bariki kinga abinda a keyi marakunyar banza kawai"Maryam ta rikeshi tamau ta bayansa sai kuka takeyi sabida ta tsorata da al'amarin

Ya rike hannunta suka fita da ga gurin shi ko in dan dan yana tsaye tamkar wanda a ka dasa a gurin yakasa tabuka komai lailai Nasir bai mutumci yadda ya kwadaitu da yarinyar shine zaizo ya watsa masa shiri amma babu komai Allah ya kai damo ga harawa

Nasir ya bude mota ya shiga yana jiranta ta shigo ,sai ya ga kawai ta dauki hanya tana tafiya sai kace wata zautacciya


Ya kunna mota yabi ta ya tari gabanta da motar ,tayi saurin kaucewa taci gaba da tafiyarta ,cikin talatainin dare baka jin komai a gurin sai haushin karnuka


Kashe motar yayi ya fito yana bin ta a baya har ya cimma ta

Ya sha gabanta ya tsaya yana mata wani Dan iskan kallo na raini


Ita ma tsayawa tayi tana kallonsa ,sunfi minti goma suna kallon kallo sannan ya bude bakinshi da kyar yace"ke wuce kishiga mota mutafi ko in baki mamaki yanzu"


Cikin jajircewa gami da jarumta Maryam tace"Allah ya tsare ni da shiga motar asharari kuma fasiki"



Wani murmushi Nasir yayi mai dauke da ma'anoni da dama,yace"OK kinaso ki koma can gurin kenan ,dan ma kin samu nadawo daukarki, har kina da bakin yimin rashin kunya ko"?


"Nasir da,dai ina ganin mutumcin ka da darajarka amma banda yanzu ,ai ba nice nace kadawo ka dauke ni ba"

Sabida haka ka kauce ka bani hanya na wuce na tafi mugu azzalimi,allah sai ya saka min wallahi"


Fuskarshi a murtuke yace"wato bazaki dai na zagina ba ko"

"Anzage ka din"
Tafada jikinta na tsuma

Girgiza kai yayi ya kawai bai ce mata komai ba ya wuceta ya shiga motarsa ya kunnata ya fixgeta yazo ya wuceta fuuuuu


Maryam tayi sauri tabi motar da kallo gabanta yana faduwa ,sai tafara bin gurin da kallo babu kowa a gurin Tsit!!


Da sauri ta fara tafiya tanayi tana hadawa da gudu sai waiwayen bayanta takeyi , tayi rantsuwar bazata shiga motarsa ba sabida batasan irin muguntar da ya shirya mata ba
[24/05/2019 9:13 AM] Binta Umar Abbale: Tafiya take tana kuka sam batasan in da take sanya kafafunta ba kuka take sosai tana rokan Allah ya kawo mata dauki a wannan daran.


Nasir can wani guri yayi parking din motarsa Sam ba zai iya tafiya ya barta a gurin ba, yarinyar tana da taurin kai ,lokuta da dama ita ke sashi yayi mata abinda bai niyya ba ,yana da tausayi sosoi musamman a kan "yaya mata sabida yafi kowa wanene su shiyasa yake rangwanta mata
Ko dazu ma lokacin da ya Kai ta Hotel din ranshi ne yayi mugun baci yadda take fada masa magana son ranta wai shi take kira dan iska,shiyasa ya kaita bariki taji yaya take amma kuma yana komawa gida sai yaji bazai iya barin ta takwana a gurin ba, wata zuciyar tace ka kyaleta tayi wasu "yan awanni a gurin sabida kasan a kwai kurayen mata a gurin dole za'akawo mata cafka ,wannan shine dalilin da yasa ya kyaleta ta samu awa biyu a gurin,sai yaje ya tadda ,mutsiyacin nan Dan Dan a kanta ,lokacin zuciyarsa ji yayi kamar zata fasa kirjinsa tafito waje sabida yadda take masa radadi yana masifar kishin yarinyar sosai da sosai yarasa wace irin musiba ce wannan.


Yana zaune cikin motarsa ya bude murfi daya ya ziro kafarshi daya hannunsa rike da Karan sigari yana zuqa idanshi yayi jajazir sosai jiran karasowar ta yake ,sabida yasan a kwai tazara sosai da gurin da ya barta


Tafi minti talatin tana tafiya yanzu ma ta daina kukan idonta ya bushe kamas! Ta barwa Allah lamarinta


Tunda can nesa ta hango motarsa ,sai taja ta tsaya tana kalle-kalle gurin so take taga ko a kwai wata hanya da zata sanja dan kar ya ganta ,abinda bata sani kuwa yana kallonta duk abinda takeyi

Can taga wata siririyar hanya jikin gatangar wani gida ,nan take tabi gurin, yana kallonta ya fito daga motar gami da kullewa hannunshi rike da sigari ya durfafi inda tabi shima,


Maryam na tafiya taga mutum ya sha gabanta,

Cikin firgici ta kwala kara!!
Nan take ta silale a gurin tafadi ta sums

Nasir ya tare ta tafadi jikinshi ,cak ya dauke ta ya sa6a a kafada cikin tashin hankali ya nufi motarsa da ita.
[06/06, 01:44] +234 808 996 5176: [24/05/2019 11:40 AM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*

*87*

Motarshi ya nufa da ita hankalinshi a tashe Maryam ta sanqame masa a jiki ,yana zuwa ya bude motar ya kwantar da ita a kujerar ba ,da sauri ya zagaya mazaunin driver ya dauko ruwan gora wanda yake ajewa domin bukatar kanshi,ya bude shi cikin sauri ya fara zuba mata a fuskarta, tsaf ruwan ya kare a kanta amma bata dawo dai-dai ba ,jikinshi na rawa ya shiga motar sosai gami da dago ta ya rungume ta a jikinshi yana tunanin wane irin taimako zai mata a karo na biyu

Wata zuciyar tace kayi mata irin Wanda kayi mata kwanaki baya

Batare da ya tsaya wani tunani ba kawai ya dago fuskarta ya sa bakinta a nasa yana hura mata iskar dake bakinshi

Yafi minti goma yana abu daya sannan taja wata shegiyar a jiyar zuciyar numfashinta ya dawo dai-dai idanunta a rumtse taki yadda ta budesu

Qirjinta ya kalla ganin yadda zuciyarta take bugawa fat!fat ,bai San sanda ya dora hannunshi a kai ba yana dannawa

Maryam ta bude idonta da sauri jin kamar Hannun mutum a jikinta kuma a kan kirjinta,ido hudu sukayi da Nasir Wanda ya zuba mata idonshi sosai yake kare mata kallo yau.

Saurin dauke kansa yayi daga kanta domin bayason yana kallon idonta da daddare,

Ta yunkura zata tashi takasa ,sabida yadda yayi mata rikon tsauri


Da kyar ta bude baki tace"ka sakar min jikina domin ni ba lalatarciya bace,kuma Allah ya isa taba min jiki da kayi"


Shiru yayi na minti uku yana dai dai ta nutsuwarshi domin kusancinsu da ita ya tayar mai da tsumammiyar sha'awarta ta shekaru da dama ,

Ya kwantar da ita sosai cikin kujera ,sannan ya fito ya maida kofar ya rufe ya zagaya mazauninshi ya zauna ya kunna motar,


Kai tsaye gida ya nufa da ita


Da kyar ta samu ta mike zaune jikinta a mace sakamakon tafiyar kafa da tayi abinda bata saba ba ,kallon hijab din ta tayi Wanda ya jike jagab da ruwa ,mamaki takeyi mai ya jika mata jiki haka

Ta kalleshi ganin ya nufi gida da ita tace"ka maryar dani asibiti domin aunty tanacan tana nemana nasani ko wannan hakki ma nasan Allah bazai barka dashi ba"


Babu abinda yace mata kawai ya cigaba da tukinshi batare da ya sauya hanya ba

Haka har suka je gida ,ya fito kawai ya kulle motar batare da ya kalli inda take zaune ba yayi shigewarsa part dinshi


Tafi minti goma a cikin motar tana saqawa tana kwancewa, sannan tafito jikinta duk yayi mata nauyi ta nufi part dinsu tana addu'ar Allah yasa kar taga Malam ya fito sallar dare domin yanzu ne lokancin tashinsa,
[24/05/2019 12:04 PM] ®Binta Umar Abbale: A kuwa Malam Ya'u na tsugune a tsakar gida yana daura alwala,Maryam ta shigo
Gabanta yafadi ,addu'ata bata karbu ba


Kallonta yakeyi cikin mamaki yace"Maryama kece da dadaranan ,Allah yasa lafia
Domin ya kawo ko Baban gida ne rai yayi halinsa


Cikin ina ina tace "e nice Baba, aunty ce lallai sai na bawa uncle hakuri wai nayi masa rashin kunya,shine Na tawo gida nazo na bashi hakuri"

Cikin mamaki yake nazarinta yace"aunt taki ce tace"lallai kizo kibashi hakuri da daddaran nan,ai a bari sai da safe"


Daga kai tayi ,yace "shikkenan ai wuce ciki,zamu hadu da ita"


Maryam ta shige simi simi kamar wacce kwai ya fashewa a ciki

Malam ko ya dade yana tunanin abin ,daga bisani ya daura alwalarsa ya mike daga gurin


Maryam ko tana shiga dakinta toleit ta shiga tayi wanka da ruwan zafi ,sannan ta dauro alwala tafito ta shirya tsaf ta hau kan dadduma ta tada sallah, tadade tana addu'oi a kan Allah ya kawo musu dauki ita da iyayenta ,sannan ta kwanta, tana tunanin abinda ya faru da ita a wannan dare


Fuskar Nasir kawai take gani yana mata gizo lokacin da tafarka daga suman da tayi ta ganta a kwance a jikinshi ga fuskarsa daf da tata, zuciyarta ra rinqa bugawa , tunda Allah ya hallice bata taba son wani kamar yadda take sonsa ba ,amma ta bawar zuciyarta sabida ta naganin yafi karfinta bayan haka kuma kwata-kwata bata sha'awar auran namiji manemin mata, sabida tana da kishi sosai shiyasa tun lokacin da taganshi da "yan matansa takeji kamar takashe kanta ta huta.


Babban abinda yake hadata dashi shine rashin ganin girman iyayenta da bayayi ita duk mutumin da baya ganin darajar iyayenta to itama bazata ga girmanshi ba,shiyasa take ganin girman Abdul sabida yadda yakeson ta yake ganin girman iyayenta baya gudun talaucinsu, duk son da takewa uncle baza ta bari ya wulakan tamata iyaye ba,


Tun tana yarinyar "yar shekara bakwai baxata taba mantawa ba lokacin uncle din ya zo Hutu daga da ya shiga gurinsu aunty take fada mata shine a uncle dinta to tunda ga lokacin takejin wani Abu a zuciyarta a game dashi har yanzu tanajin abun ,sai dai taki yadda abin ya bayyana ya fito fili sabida tasan Nasir din ba tsaranta bane
[06/06, 01:45] +234 808 996 5176: [25/05/2019 10:06 AM] ®Binta Umar Abbale: [25/05/2019 9:49 AM] ®Binta Umar Abbale: [25/05/2019 9:16 AM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*

*88*

To shima nasa bangaran tunanin da yakeyi kenan tun da ya taso a rayuwarsa yayi hulda da mata iri -iri amma bai ta ba cin karo da yariyar da take caza masa kai ba kamar Maryam tunda ya daura idansa a kanta a lokacin da yazo hutu lokacin tana shekara bakwai a duniya yakejin wata muguwar tsanarta a zuciyarsa, haka kawai yaji baya son ganinta ko gilmawarta a guri ,dalili kuwa tun ranar ya fara mafarki da ita in har ya kwanta bacci, duk tsawon shekarun nan bai fasa mafarkin taba, shiyasa yake kauce wa abinda zai hadasu guri guda, amma can kasan zuciyarsa yana jin wani matsanan cin kishinta wanda yake sawa yaji kwata-kwata baya kaunar ya bude ido ya ganta da wani namiji.


Haka yayi ta juye juye kan bed yana jin wani iri a jikinsa yarinyar ta tayar masa da sha'awa wacce ta sanya masa kasala yaji ko Dan ya tsansa baya son ya daga, haka yayi ta taune lebanshi na kasa idanshi yayi ja ya mike da kyar ya nufi toleit ya dinga zubawa kanshi ruwan sanyi ko yaji sauqin abin amma abu yaci tura tamkar karawa kansa wata sha'awar yakeyi ,gashi yayi alkwarin ba zai sake kusantar wata mace ba mutukar ba matarshi bace

Ya fito a daddafe ya fara laliban magani ya balli biyu ya sanya a bakinshi batare da ruwa ba haka yake tsotsa ya fadi kan bed din rigif! Hannuwanshi dafe da mararshi

Wajan minti goma sha biyar abin ya fara lafa masa ,sai gumi yakeyi tamkar babu Ac a dakin a haka bacci ya dauke shi na wahala.



Washe gari Maryam da wurwuri ta tashi tayi Wanka tsaf ta shiga kchin ta na hada abin karin kumallo Malam ya leqo yace"kiyi sauri ki kammala mutafi ,dazu da'a suba aunty taki tayo waya hankalinta a tashe ,wai an ne meki an rasa, nace mata ta kwantar da hankalinta gaki nan a gida"


Gabanta ne ya fadi tana jin tsoran haduwarta da aunty ,sabida tasan dole sai tayi mata fada, tafi jin tsoran aunty ta a kan Malam sabida shi bashi da zafi kamar aunty


Muryarta a sanyaye tace"to Baba yanzu zan gama insha Allahu"


Ficewa yayi daga kchin din hannunshi rike da carbi yana ja ya nufi bakin get din


Nasir ya fito jikinsa sanye da kayan motsa jiki , ya nufi bakin get din


Fuskarshi babu yabo babu fallasa ya mikawa Malam hannu domin su gaisa kamar yadda suka saba


Mamaki Malam yakeyi sabida Nasir din a kwanaki baya bashi hannu

Sai ya mika masa hannushi shima yace"Nasiru ka tashi lafia"


"Lafiya arrama "
Nasir din yafada yana kokarin zare hannusa

"To masha Allahu
Jiya kuma sai naga wannan yarinyar cikin dare wai aunty ta ce tazo ta Baja hakuri, Dan rashin hankali, nace bata bari gari ya waye ba"
[25/05/2019 9:48 AM] ®Binta Umar Abbale: Gabanshi ne ya fadi kadan yana addu'ar Allah yasa kar yarinyar ta fada masa abinda ya faru ita dashi


Sai ya gyara fuska yace"Owk ai ni bangan taba ma kwata kwata a jiya"

Cikin mamaki Malam yace"tace kuma tazo gurinka tabaka hakuri"

Girgiza kai yayi kai tsaye yace"batazo ba"

Kawai ya fice ya bar Malam tsaye a gurin yana binshi da kallo

Zama yayi kan bainci dake gurin yana al'ajabin wannan abu ,amma zai zaunar da Maryam din ya tuhume ta yasan yarinyarsa tsarkakkiya ce kuma ba zatayi masa karya ba.


Nasir kuwa Can wani guri ya nufa cikin estet din nasu da suke motsa jiki yafara motsa jikinshi babu abinda ya dameshi.


Tsaf tagama hada komai tafito jikinta sanye da katon hijab dinta kamar yadda ta saba,ta aje kayan dake hannunta kusa da Malam tace"Baba bari inje mu gaisa da Momy ko"


"To babu Laifi "
Malam yafada yana bin ta da kallo


Kai tsaye part din Momy ta nufa

Momy na zaune kan kujarar daining ita dasu Nafi'u sun shirya tsaf , Uwani mai aikinta tana hada musu breakfast ,Maryam tayi sallama


Momy ta amsa mata fuska a sake tace"Dota shigo mana kika tsaya nan"


Kanta a sunkuye ta shiga ciki farlo sosai ta karasa gurin Momy din ta durkusa har kasa tana gaida ta


Momy tace"Nima yanzu nake cewa Nafi'u ya gama karyawa yaje ya kirawo min ke"

Murmushi tayi batace komai ba


"Ina fatan kin karya ko"
Momy tafada tana kallonta

"Eh Momy na karya ga abinci can ma nayiwa su aunty"


Momy tace"ai da baki bawa kanki wahala ba ,tuntuni nasa Uwani tayi musu"

"Laa Momy ai babu komai sai su hada da nawa"

Dariya Momy tayi tace"to shikkenan sai ki jiramu mu gama karyawa a nutse sai mu tafi"

"To Momy"
Maryam tafada gami da mikewa taje ta zauna cikin daya daga cikin kujerun farlo

Ko minti uku batayi da zama ba Nasir ya shigo farlo

Idansu ya tsarke guri guda

Da sauri ta dauke kai ta mayar kan kayuwat TV plasma dake manne a farlo din, ta cigaba da kallonta


Fuska ya hade sosai yana namakin mai yakawo yarinyar nan da sanyi safiyar nan , zuciyarsa yace mybe ko Momy ce ta jajibo ta yasan halin Momynsa da kwashe kwashe

Kai tsaye Tv ya je ya kashe batare da ya saurari gaisuwar da su Nafi'u suke masa ya shige dakinsa dake farlon


Baki a sake Momy take binshi da kallo tana namakin abinda yake nufi, girgiza kai tayi kawai tacigaba da cin abincin ta

Bai fi minti biyu da shiga ba sai gashi ya fito yana ya mutse fuska hannunshi rike da wayarsa yana daddanawa ya tsaya daga bakin kofar dakinshi yana kallon Momy yace"Momy wai Dan bana amfani da room din nan sosai shine ba'a gyara min, yanzu inaso in shiga toilet na tadda ko ina kaca-kaca"



Hararasa Momy tayi tace "sannu Ubana kashigo ba ka kula kowa ba shine yanzu zakazo ka titsiye ni da tambaya"
[25/05/2019 10:06 AM] ®Binta Umar Abbale: Please Momyna kisa a gyara min dan Allah ,Wanka nakeso inyi zan fita"

Yafada yana karasowa inda take zaune

Momy tace"ko jiya sai da nasa, Kyauta, mai yimin goge goge ta gyara maka dakin kai dai kawai kace zakayi min iyayi"


Dariya yayi kadan abinda ya Dade bai yi mata ba ,yana kallonta yace"Momy kinsan halina banason kazanta,wallahi tunda na shigo Farlon nan nakejin karni na tashi nake kamar zanyi amai wallahi"
Ya karashe Maganar yana ya mutse fuska

Kowa yayi zagi a kasuwa yasan da Wanda yake ba Maryam kadai ba ita kanta Momy ta tsargu da Nasir din domin tunda take dashi bai taba yi mata irin wannan maganar ba ,kasancewar a ko da yaushe ko ina na gidan cikin kamshi yake sabida Allah da yayi Momy a kwai San kamshi.

Sai tayi shiru da bakinta domin bataso ta kara wata maganar Nasir din ya kwabo wata maganar tasan zuciya batada kashi dole wata rana Maryam din tafara mai da martani kamar yadda tafara ramawa jiya a asibiti


Minti biyu farlo yayi tsitt Maryam sai kokarin danne zuciyarta takeyi ,sabida yadda take jin kamar ta tashi tabar gurin ,tana jin kunyar Momy ne kawai kuma tana ganin mutumcin ta, amma ranta ya yi mugun baci da wulakancin da Nasir yake mata idanta ya Tara kwalla sai kokarin mayarwa takeyi ,kawai tajiyo Muryar Momy tana cewa Maryam Dan Allah shiga ki gyara masa dakin kafin mu gama kinji ko"

"Don Allah"
Tafada maganar cikin zuciyarta

Yanzu Momy ce take hadata da Allah

Allah sarki Momy ,albasa batayi halin ruwa ba

A nutse ta mike tsaye tana gyara hijab din ta juyo ,fuskarta a sake tace"to Momy karki damu yanzu zanyi abinda kikace insha Allahu"
[25/05/2019 2:00 PM] ®Binta Umar Abbale: "Yawwa Dota Allah yayi miki albarka"
Momy tafada cikin farin ciki yarinyar tana burgeta sosai ,tanada hankali kwata-kwata bata biyewa Nasir din da abinda yakeyi


Cikin nutsuwa ta nufi bed din ,Nasir ya dago kanshi dake sunkuye yana kallon wayarshi ya bita da kallo yana ya mutse fuska ,yace"ke!"


Maryam ta juyo a nutse tana kallonsa

Yace "kar ki kuskura kiyi min binkice a daki domin a kwai muhiman abubuwana a ciki , duk abinda na nema narasa to sai kin biya ni"


Shiru Maryam tayi a tsaye tana tunanin ta shiga ko tafasa tunda zargi ya shigo ciki

Momy tace"wai mai yasa kake hakane my Son mai Maryam tayi maka kuma kake mata wani zargi na daban"


Shiru yayi baice komai ba ya cigaba da danne dannensa a waya babu abinda ya dameshi


Momy tayi kwafa kawai ranta a bace tace"Dota yi hakuri kinji ko ,kar ki dakata ta halinshi kiyi domin ni"


Maryam tayi dariya mai ciwo race"Momy karki damu ai uncle yana da gaskiya , kar inje inga wani abu nasa mai muhimanci in share ko in zubar, kwata-kwata raina bai baci ba"


Momy tasan Maryam din dannewa tayi kawai sabida kawaici irin nata,sai tace "to shikkenan Maryam je kiyi sauri ki kammala muwuce ko"


Maryam ta wuce dakin ranta yana mata suya tarasa inda zata sa ranta sabida yadda takeji a yanzu zata iya fito na fito da Nasir din ko dame yake taqama Kuwa



Babu wani datti a cikin dakin na kuzo mu gani ko ina tsaf in banda bedshit din da yayi datti kadan kasancewarsa mai kalar haske ,cikin sauri ta dauke shi gami da zare rigunan filillikan tabude sif ta Ciro wani sabo a ledarsa ,ta shimfida tsaf, sannan ta wuce toilet din shima babu wani datti


Sai jirwayen sabulu na Wanka shima ba sosai ba asalima in banda kamshi babu abinda yake tashi a ciki na irin kalolin sabulan da yake amfani dashi gurin Wanka da wanke sumarsa


Tsaf ta wanke ta sanya turaran wuta Na ban daki ,sannan tahada masa kananun wan dunanshi da vest dinshi a cikin abin wanki ,afili tace "wallahi bazan wanke ba masa Dan iska kawai,Dan rainin hankali"


Ta fito tana Jan tsaki kai tsaye kofa ta nufa domin fita daga dakin,suka ci karo dashi,zai shi go


Maryam tayi baya da sauri tana dafe goshinta sakamakon yadda suka gabza karo,ya shigo dakin yana bin ta da wani mutsiyacin kallo Na kaskanci ya mayar da kofar ya rufe yana bin dakin da kallo ,fuskarshi a hade



Bata kalleshi ba ta sanya hannunta a Karo na biyu tana kokarin bude kofar


Taji ta a kulle gam!

Sai ta waigo tana kallonshi fuskarta a murtuke

Kallon kallo sukeyi minti biyar tukkuna yace"kika kuskura kika fadama mahaifinki abinda yafaru jiya wallahi sai na kaiki inda baza ki iya dawowa ba kin tafi kenan"


"Kashe ni zakiyi Kenan"?
Maryam tafada kai tsaye tana kallonshi babu kifta wa


"Yes"
Yafada yana zare mata ido

Dariya ce ta subuce mata bata shirya ba ,tace "wallahi da naji dadin haka kaga dana huta da ganinka a duniyar nan domin bana kaunar in bude ido in ganka a rayuwata"


Shiru yayi yana bin ta da kallo Sam maganganunta basu bata masa rai ba so yakeyi ya kirkiri abinda zai bakan ta mata rai yanzu

Zama yayi gefan gadon yana ya mutse fuska yace "Ke boyi boyi na zo nan Dan Ubanki ki fito min da kayan da zansa yanzu nan"


Wani mugun shocking Maryam taji a jikinta lokacin da ya kirata da wannan Kalmar Boyi-Boyi ,har da zagin Ubanta,lallai yau zata nuna masa tasan darajar iyayenta
[06/06, 01:45] +234 808 996 5176: *YARO DA KUDI*

*89*


Maryam ta juyo a nutse tana kallonsa fuskarta babu yabo babu fallasa,tace "Nasir inaso kasa ni, ni Maryam wallahi nafi qarfin in zama boyi-boyin ka ,dukkanin abinda kaga ina yi maka ina yi makane kawai sabida darajar Momynka,amma kasani cewar kudinka ko takamarka basu isa su sa na yi maka bauta ba ,wallahi in

1 Comments On YARO DA KUDI
avatar
magaji-2

1 year ago

Reply

Allah Yakara budi

Please Login or Register in order to submit comment