Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ganin wata lafiyaryiyar fata tamkar ka matsa jini ya bulo harda wani gashi gashi a kwance,

Yace"ae nufi na kin Makara baki zo naganki da wuri ba,

Murmushi tayi tana gyara zaman hijab dinta ganin yadda yake satar kallon hannunta ,tayi gaba kawai ta rabu dashi anan domin in Dan ta daka ta tashi sai su lalace anan gurin ,gashi dokar Makarantar babu soyayya tsakanin dalibi da daliba ballantana Malami da daliba dayawa Malamai da daliban makarantar basu fahimci Son ta yakeyi ba sai suke ganin kamar haduwar jini kawai kasancewar Maryam din tana da kokari cikin skull din gami da tsabbata da ladabi da biyyaya shiyasa kowane Malami yake son ta,





*BINTA UMAR ABBALE*

_MARUBUCIYAR_

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUDI*

*GIMBIYA BALARABA*


πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š
[28/03, 00:52] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?



πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—
*🐾YARO DA KUDI*🐾
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—



*✍🏻WRITTEN BY*
_*Binta Umar*_
*MAMAN ABADUL WAHABU*

~*MRS AHAMAD GWADABE*~



_*WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE NAIRA 200 IN KANA BUKATAR CIGABANSHI GA NUMBAR NAN*_
08089965176



*πŸ…Ώ34*




Har a katashi daga skull Maryam najin bakin cikin Abinda Uncle yayi mata.



Sabida haka ranta a bace ta shiga gida tun da get Baban gida yake Jan ta da wasa kamar yadda ya saba ,Amma bata tanka mashi ba tayi wucewarta ciki ko jiransu Nafi'u batayi ba idan sun gama shirmensu sa shi go domin su ma haushinsu takeji ganin A gabansu Uncle din yaci mata mutumchi basu nuna damuwarsu ba Sai kace shashashai suka zauna cikin motar duk dai yadda suke dashi ba kamar ita ba ne.




Aunty tana kallon yanayinta tasan yau halin nata ne ya motsa idan ba'ayi sa'a ba haka zata kwana ta yini bata kula kowa ba.


Tace"Aunty sannu da gida"

"Yawwa Maryam kundawo Lafiya"? Ina su Nafi'u?


"Suna can gurin Baban gida" tafada yayin da take kokarin shiga farlour nasu,



Tabe baki Aunty tayi tace"Miskili kafi mahaukaci ban haushi"

Ta cigaba da Aikinta cikin kwanciyar hankali.



*******

To Nasir yau kwata kwata bai fita yawo ba tun safe yana part dinshi a kulle bayan ya dawo daga motsa jiki bacci yake bai tashi ba sai bayan la'asar ,yana duba wayarshi miscall din Dady Har biyar ,gabanshi ne yafadi a fili yace Lallai yau a kwai rigima a gidan nan.



Mi kewa yayi da jiki a mace ya shige toilet domin wanka Alwala ya daura bayan yaga ma wanka n yafito ya kimtsa cikin qananun kaya As'usel sannan ya tada Sallah nan cikin dakin nashi Wanda in da da ne fita zaiyi suyi tare da su Malam Ya'u



Bayan ya idar yayi Addu'oinsa iya yadda ya sawwaqa ya mike daga kan daddumar ,yaje ya dauki wayarshi yana laluben numbar Dady nashi yasan yau sai ya sha fada



Bugu daya tayi Alh Huseen ya daga gami da gyaran Murya.


Kwantar da kansa yayi kamar wani mummuni yace"Dady barka da Yam a"?


"Barka kadai" mai kakeyi tun dazu nakira wayarka ya kai sau biyar baka daga ba"? Ko kana can gurin shadgancin naka"


Shafa kai ya soma tamkar yana gabanshi yace"Aa Dady wallahi ina gida ma"


Da sauri Dady yace "kana gida kanaji ina kiran wayarka kaqi dagawa ko sabida kar in dame ka? Yafada cikin bacin rai!


"Aa No" Dady ba haka bane Bacci nake yi ne wallahi kasan A kwai gajiya a tare dani ban gama watstsakewa ba" yafada kamar gaske.


"A kwai gajiya a tare da kai Amma duk dare kana waje Dady yafada cikin tuhuma


Dariya yafara qasa qasa yace dady kenan kasan ina da Abokai sosai So Dole in Dan fita mu gaggaisa da juna"



Tsaki Dady n yaja yace" Mubar wannan Maganar duk Abinda kake ciki nasani Nasir babu Abunda zaka boye min"


"Ok dady Mubar ta tunda ba kaso" Nasir din yafada hankalinshi kwance


Dady ya cigaba da Cewa" kana sane dai dacewar Monday ta Sama zaka fara Aiki ko A sabon Asibitinka ko?


"Eh dady Ina sane "



Ok A kwa likitoci da Muka tanada Manya zamu riqa biyansu Albashi mai tsoka domin su ruqa taimakon Al'umar Musulmi" dady yafada yana sauke nuffashi



"Ok Dady ae babu damuwa nima can Ina da wasu da Nayi wa Alkwarin daukarsu Aiki Abokan karatu nane duk Mata ne Amma ba"yan Najeria ba ne
Daya a gana take daya kuma can kudu ne ban dai riq sunan garin nasu ba"


Dady yace"in dai ka Aminta dasu ae shikkenan mu dai muna bukatar wa"yanda zasu kawo mana ci gaba A gurin"



"Eh in sha Allahu Dady Teema da Mery sun San Akinsu zasu kawo cigaba"



Ok sai ka zauna dasu sosai ka yanke musu Albashi ko ?dady din yafada



"Eh in sha Allahu zan kira ko wacce a waya tazo mukara yin intervieo da su"


"Hakan yayi duk Wani shirye shirye ka gama shi kafin ranar bana son shashanci"


"Ok Dady kar kadamu duk yadda kace za'ayi haka"


Kashe Wayar Dady yayi ,


Sai yabi wayar da kallo yana sakin Murmushi ,A fili yace Dady na Momy kenan.


Ficewa yayi daga sheshen nasa kai tsaye part din Momy ya nufa kanshi a sunkuye yana faman daddana wayarshi,







*BINTA UMAR ABBALE*

_MARUBUCIYAR_

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUDI*

*GIMBIYA BALARABA*


πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š
[30/03, 01:54] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?



πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—
*🐾YARO DA KUDI*🐾
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—




*✍🏻WRITTEN BY*
*Binta Umar*
~*MAMAN ABDUL WAHABU*~


_*WANNAN BOOK DIN NASIYARWA NE NAIRA DARI BIYU IN KANA BUKATAR CIGABANSHI GA NUMBAR NAN*_
08089965176



*πŸ…Ώ35*



Daga can bakin get ya hango Mutananshi su Nafi'u sun dawo daga makarantar isilamiyya Baban gida ya tsayar dasu yana tsokanar Maryam.

Bata tanka masa tayi gaba kawai tabarsu Nafi'u gurin domin tun safe takejin dacin Rai ita a rayuwarta ta tsani wulakanci da to zarci shiyasa bata shiga sabgar "yayan masu kudin unguwar ko a makaranta suka hadu kowa harkar gabanshi yake sai kaji suna ta yadda mata da habaici su nace sai girman kai ita ba" yar kowan kowa "yar mai gadi,



Tana hango Ancle ta dakata da tayi niyyar shiga gurin Momyn ,sai tafasa sabida ganin can ya nufa shima.



Kan ta a qasa cikin Niqab kamar ko da yaushe tazo ta wuce shi tayi bangaransu,


Yayi mata wata tsawa cike da Neman fitina yace"ke Aljana a kwaba tsaya nan gurin"



Tsayawa tayi jikinta a sanyaye sabida ta tsani wannan sunan da yake kiranta dashi wai Aljana wannan tsabar qiyayya dame tayi kama.


Ya karaso gurin Cikin Yanayin tafiyarshi ya tsaya daf da ita ya sanya hannu ya fuzge Niqab din ,yana mata wani wulakantaccen kallo yace" Ke Nan gidan ba gidan "yan Shi'a bane sannan bana "yan izala bane da zaki riqa sanya Abu kina rufe fuska sabida tsabar Munafurci da Annamimanci wallahi duk randa Na kara ganinki da wannan Abin sai nasa an lalata miki fuska.

Tunda yafara maganar kanta a kasa yake ,sai da yama tadago kai ta dallare shi da idonta da suke sakashi faduwar gaba,ta zuba masa shi!



Saurin dauke kansa yayi daga kanta gabanshi yana faduwa kamar ko da yaushe in ya kalli kwayar idon ta.


Sai ta sunkuya ta dauki niqab din kawai bata tan ka masa ba ,tana da gowa ya tattaro yawo ya tofa mata a fuska yana ya mutse fuska yabar gurin yana duba wayarsa jin kira ya shigo ,Anwar ne ya kirashi,


Maryam ko Niqab din ta sanya ta goge yawon da ya tofa Mata ta nufi bangaran nasu tana kukan bakin ciki wai ita yaya zatayi da Uncle ne a rayuwarta mai tayi masa ne mai zafi a rayuwa.

Allah yasa duk wannan Abun dake faruwa su malam Ya'u basa gani sabida tazarar dake tsakaninsu da get din


"Yace yaya kai ne mutumi na"


Daga daya bangaran Anwar yace"kai Nifa wannan "yar iskar ta takura min wai yau bata ganka ba gashi takira wayarka taji a kashe shine tun safe ta addabe ni lallai sai Na kawo ta gidan Ku"


"Wa cece wai"?


"Wacece kuwa in ba Baby ba"


"Mtsss wallahi kar ka sake ka kawo ta nan Allah ranka sai ya baci Ka sake ka nunawa Baby gidan nan zata zo ne kawai ta takura min"



"To kayi mata waya kawai yanzunan tace dani gata nan zuwa wai in kawo ta" yarinya sai kace mayya ta makale maka sai kace mu ba maza bane"



"Ae kuwa zan kira ta ni kai Na fara gajiya da nacin ta wallahi"



Dariya Anwar yayi yace "wato gishiri ya salance kenan?"



"Ko daya Wallahi jarabar ta ce ta ishe ni"


"Mtssss ae sai kayi A boy kasamu dama kake wasa da ita billahillazi dani nasamu damar ka da Sai na ragargaji "yan mata iya son rai Na"

Yaci gaba da cewa yanzu "yaya zanyi gurin yaudarar my Maryam dina ne Wallahi kwana nake tunanin ta gaskiya yarinyar ta hadu da yawa,



Dariya Nasir yayi yace" kazo kawai da zuman zaka Auri shegiya daga nan sai ka Aiwatar da qudirinka a kanta yan zunan ma ta dawo daga makaranta Wai ita lallai kintsatsstiya har da rufe fuska.




_DUK WACCE TA ZAGE MU KAN TA TA ZAGA LITTAFI DAI MUN SIYAR BA MUCE LALLAI KI SIYA BA DA BAMU YADDA DA KANMU BA BAZA MUCE MUN SIYAR BA SABIDA MUN SAN A KWAI MASU SIYA IN KE BAZAKI SIYA BA DAMA BAMA BUKATAR KI SIYA DIN DOMIN BAKI DA KUDIN SIYA SHIYASA KIKE RARAGEFE KIKE NEMAN NA BATI SIDDAN KI KARANTA ,BABU YADDA ZA'AYI MU BATA LOKACINMU MU YI RUBUTU BATARE DA MUNSAN A NASIYA BA ,IN HAKANE AIKIN BANZA MUKE YI KENAN DAN ALLAH IDAN KINJI HAUSHI KIJE KI FARA RUBUTU KIJI YADDA A KEJI KI GANI KO ZA'A SAI NAKI ,HASSADA DAI GA MAI RABO TAKI CE_

_*INA ALFAHARI DA QUNGIYARMU ZAMANI WRTES ALLAH YAQARA HADE KANMU*_


*BINTA UMAR ABBALE*✍🏻
[03/04, 02:10] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?


πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—
*🐾YARO DA KUDI*🐾
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—



*✍🏻WRITTEN BY*
*Binta Umar*
_*MAMAN ABDUL WAHABU*_


*WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE NAIRA DARI. BIYU IN KANA BUKATAR CIGABANSHI GA NUMBAR NAN*
08089965176


*πŸ…Ώ37*



Ya gane wace Maryam Momy take Nufi sai ya ya tsine Fuska yace"Gaskiya Mom Bazan iya ba Sam bazan dauki kazamai ba ,ki kaita Asibitinku mana banaga kina nuna mata ba"

Kallonsa tayi cikin mamaki tana zuba mishi Abincin tace "karya kake My son kace wa Maryam kazama wallahi ko mai tsaftarka yarinyar tafika ,kullum cikin Alwala take yarinyar Na burgeni sabida Addininta"


Dariya yayi yace "Momy wancan yarinyar Mai kama da zabiyan ce tafini tsabta"?

"Yes of Couse " Momy tafada gami da tura masa plate din Abincin gabansa


6ata Fuska yayi kawai yafara cin Abincinshi yana kara jin tsanar Maryam cikin zuciyarshi wai duk tsabatarsa Yau momynshi take cewa wata ballagaza yarinya ta fishi.



Momy tace"Au!fushi kake Dan Na fadi gaskiya,

"Please Mom Dan Allah kar kikara hadani da yarinyar nan kin San yadda Na tsaneta kuwa "yafada yana wani tabe fuska,



Zama tayi Cikin kujera tace"Allah ya shirya min kai Nasir Narasa Abinda Yarinyar nan tayi maka"

Da har ina cewa ko da'ita za'ayi ne"?
Tafada cike da tsokanarsa.


Bata Fuska yayi yace"Mom bana son wannan Maganar please"
Yafada cikin shagwaba tamkar wani yaro.



Alhaji Huseen ne yayi Sallama ya shigo Farlour din Yaron shi biye a bayanshi hannunshi riqe da Jakar Sa ta Offece da sauransu.



Momy ta Amsa gami da mikewa tsaye tana masa sannu da zuwa.

Ya kalli Nasir ,Wanda ya sha kunu kamar gaske yana cin Abincinshi

Yace"me kuma ya hadaki da Dan gidan naki naga yana wani cin magani"


Fashewa da dariya Nasir yayi Sabida yadda Dady yafadi maganar.


Yace"Dady barka da dawo wa"

"Barka mutanan Momy yaya kinji"
Dady yafada tamkar da yaro karami yake.

Sunkuyar da kai kawai Nasir yayi yana cin Abinci sabida yasan halin Dady din yanzu sai yayi ta Nanata Magana.


Momy tace"Wai daga yi masa maganar Aure shine take shan kunu,

Tsaki Dady ya ja kawai yana kokarin hawa sama yace ke ce ma kika damu dashi ai dama yanzu ya dace A yi masa Aure ko da da naqi sabida yakara Hankali ya kammala karatunshi sabida haka kana fara Aiki to ka nemo matar Aure kaji Abinda nace ko"
Yafada yayi hayewarsa sama ko saurarar Nasir din bai tsaya yayi ba.



Cokali da yake cin Abinci dashi ya aje yana kallon Momy yace"kinga Abinda nake fada miki ko Mom ,nasan halin dady da daukar dumi ni yanzu yaushe Na isa Aure duk Abokai Na babu Wanda yayi Aure sai kai !!impossible ni kwata kwata ba yanzu zanyi Aure ba yafada gami da ture kujerar da yake kai ya mike tsaye kawai ya nufi kofar fita ko saurarar Nom din da Abinda take cewa bai yi ba



Yana fita motar Anwar Na sako kai cikin gidan,

Sai ya dakata sai da Anwar din ya fito ya gyara parking sannan suka wuce part din sa suna dariya gami da shaqiyanci kamar yadda suka saba.



Zama Anwar yayi cikin Sofa yana fadi wallahi yau nagaji Anya zan je club kuwa,


Tsaki Nasir yayi yace"kai!!Alhaji Dady fa yafara taro March wallahi kajifa ,wai in nemo matar Aure.


Hannu Anwar ya bashi suka tafa ,yace Allah Alh"!!

"Wallahi nake gaya maka"

"Dady din da bayason yayi maka Aure yanzu yaushe ya sauko Kuma"?

Tabe baki Nasir yayi yana daga kafada yace"oho"!! Ni dai Abinda nasani kawai shine duk yarinyar da ya matsa min Auranta zatasha wuya wallahi domin ta Amince ta shiga rayuwata A lokacin da bana ra'ayinta"


"Kai Babah!! Ka yadda kawai Auran zai zame maka garkuwa in naka Sani ba,"
Anwar yafada yana dukan kafadarsa,



*BINTA UMAR ABBALE*


_MARUBUCIYAR_

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUDI*


*GIMBIYA BALARABA*

πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š
[04/04, 14:51] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—
*🐾YARO DA KUDI*🐾
πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅


*✍🏻writting by*
*Binta Umar*
*MAMAN ABDUL WAHABU*

*MRS AHAMAD GWADABE*



*πŸ…Ώ38*



"Kai ba yanzu ba,Yasin kaji Abinda Mom take cewa ,Wai nayi Aure ko tasamu yara,nine zan haihu yanzu ,Tabb!!
Yafada yana wani zakuda kafada.


Dariya Anwar din ya fashe dashi yace"waya gan kan da da ,Tabb shikkenan girma yazo Baba Nasir"


Duka Nasir din ya kai masa yana Jan tsaki yace"Wallahi ko Aure nayi bazan haihuwa ba ,yanzu kai kanka kasan yadda Na tsani tara yara"


Anwar yace "kai kana maganar Auran ma ,ni a tsarina ai babu maganar Aure a yanzu sai nagama more rayuwata.

Hannu ya bashi suka tafa ,suna qyalqyala dariya


Ya mike tsaye ,yace bara nayi Wanka mu fita ko,
Wai ina wan can Dan iskan yake ne? Yana nufin Abbas.

Anwar yace"ka kira wayarsa mana ,ina zaton baya kusa ,domin dazu nakira wayar ba'a daga ba".


Yana kokarin bude kofar toilet din yace ,yana can Makale da wannan yarinyar tasa tamkar wani maye,

Dariya Anwar yasa yace "ni rasa Abinda yakewa kwakwa a jikin yarinyar Wallahi".


Nasir yace" in yazo ka tambayeshi mana ai ko wace mace,tana da tata Baiwar".

Yafada lokacin da yake shiga ban dak in.
Tabe baki Anwar yayi yace"ni kam banga Abin so a jikin ta wallahi ,wahalar da kansa kawai ,yake ai mata Masu Abin Fada sai yarinyar gidan nan".


Wanka yayi ,gami da daura Alwala kamar gaske ,ganin daf da kiran sallar magariba a ke.


Ya fito jikinshi daure da towul ga wani a hannusa yana goge kansa

Kai tsaye in da kayansa suke ya nufa ,yafito da wasu kananun kaya masu kyau da tsada ,da Alamar wani kamfanin A jikinsu Na kasar America da Alama kayan sabbi ne.


Ya shirya tsaf ,bayan yayi shafeshafensa kamar mace ,ya dauki tarin sargoginshi ya saka a wuyanshi ,gami da daura a gogonsa Na fama ,dama manya manyan zubunansa suna hannusa kullum
Ya saka person Cap din shi Mai bala'in tsada ,gami da fese jikinshi da turarirrika kusan kala Biyar masu Asalin kamshi da tsada,
Gaskiya Nasir yayi Bala'in kyau ba karami ba ,kayan sun Amsheshi,sosai kasancewarshi Fari cikin ,kaya Masu duhu hatta da hular kanshi baqa ce ,shiyasa ya zama tamkar ka sace ka gudu,ga kyau Amma babu kyawun zuciya.


Duk wannan Abun ,Anwar Na kwance kan bed ,din Nasir yana latse latse a wayarsa,

Ya dago kai yana kallon Nasir din,

Ya mike zaune sosai gami da bawa Nasir din hannu ,suka cafke tace"Kai A boy ka!!kauce Kaga yanda kafito kuwa Alh"
Yafada yana wata dariya,
Lallai yau Kace A kwai rigima gurin baby"

"Mtsss Nasir yaja ,yace"kai rabu da wannan yarinyar ,ita take haukanta ,domin tasan ba'auran ta zanyi ba ko da Mata sun qare"


Mikewa tsaye Anwar yayi ,yana gyara zaman wandon shi da yake sabulowa ,yana wani irin Abu da kafada ,"yace Baby kenan ai ta rikice a kanka"
"Ai sai tai tayi "Nasir yafada
Hakadai suka fice suna ta zantunkansu duk a kan baby n dai.

Bayan Sun fita harabar gidan ,Nasir ya Nufi can in da motocinsa suke aje ,shi kuma Anwar ya nufi gurin Malam Ya'u dake zaune kan benci yana daura Alwala, Baban gida tuntuni ya shiga gida.


Ya karasa Gurin gami da Mika masa hannu kamar gaske yace"Arrama barka da yamma"


Cikin Mamaki! Malam Ya'u ya dago kanshi yana kallon Anwar din ,domin tunda yake dasu ,basu taba yi masa kallon Arziqi ba,wani lokacin ma yanaji ,suna yiwa Nasir dariya gami da shaqiyanci in ya tsaya yana sauraronsa,

Sai shima ya Mika masa hannu ,fuskarsa a sake yace"barka kadai ,Anwaru ,yaya Manyan ka?

"Lafiyansu lau"Arrama
Ya Yau?

"Alhmdullahi"Malam Ya'u yafada gami da mikewa,jin za'a tayar da sallah


Sai Anwar ya zira hannu cikin Aljihunsa ya fito da tarin kudi masu yawa ,ya mikasu ga Malam Ya'u ,yace "Arrama ga wannan A dan yi hidama da yara
Abin sai ya bashi Mamaki yace"kai ko Anwaru mai zanyi da wannan kudi haka,Aa nagode kaji ko ,bana bukatar komai domin Alhji ya dauke min duk wata da wainiyar yara,

Qasqantar da kai Anwar yayi ,yace "Haba Arrama ,Dan zatin Allah ka karba mana ,ina bukatar ka sanya ni cikin Addua ne ,nima ina bukatar lada nasan da cewar dama babu Abinda ka nema karasa a gidan nan"


Tausayi Anwar din ya bashi ,sai ya dafa kafadarsa yace"karka damu ,yanzu dai jeka dauro Alwala mu shiga Masalaci ,in mun dawo sai muyi maganar.


Kafin Anwar yace komai ,Nasir ya karaso gurin ,ya mikawa Arrama Hannu suka gaisa ,sannan ,suka nufi Massalaci ,tare suka shiga cikin massalacin ,suka bar Anwar yana daura Alwala a Turin
Kamar gaske.




*BINTA UMAR ABBALE*

_MARUBUCIYAR_

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUDI*

*GIMBIYA BALARABA*
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š


_In kana bukatar cigabanshi ga number ban_
08089965176
[06/04, 00:51] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?


πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—
*🐾YARO DA KUDI*🐾
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—


*✍🏻writting by*
*BINTA UMAR*
_*Maman Abdul Wahabu*_


_Bissimillahi_rahamanin rahim_

*πŸ…Ώ39*


Bayan sun fito daga massalacin ne,Anwar ya kalli Nasir yace"A boy ka ga Na bawa Arrama kudi yaqi karba kasa baki mana"


Nasir ya kalli,Arrama Ya'u yace"haba Arrama ka lar6a mana ka sanya masa Albarka ,bai baka da wata niyya ba"


Malam Ya'u yace"ai ban qi tataku ba Nasiru kudin ne suka yi yawa ,ni Ahalin yanzu ban da bukata dasu,


"Dan Allah Arrama ka kar6a ,dani da Anwar duk daya ne kuma tamkar "yaya muke a gurinka ,Albarka kawai yakeso ka Sanya masa,"

Da kyar dai Malam Ya'u ya kar6i kudin hannun Anwar ,yana shi musu Albarka da fatan shiriya

Tare suka koma cikin gidan ,Malam Ya'u yayi ban garensu ,su kuma suka Nufi mota da nufin fita.


Suna fita daga gidan Anwar yasaki dariya ,yace"gaskya mutumin nan ya burgeni sosai Sam Na fuskanci bai da zalamar kudi.



Murmushi Nasir yayi kadan yace "kwarai kuwa Arrama yana da wadatar zucci ni zan fada maka halinsa.



Anwar ya gyara kwanciya cikin kujera yana lumshe ido ,yace"gaskya Na kwaidaitu da yarinyar nan,wai me yasa jiya baka bari Na Dan ta6a bane kafito ka hana,gaskya naji haushi ,wallahi shi Kumar wan can sarkin shisgshigin naga sai wani tada jijiyar wuya yake a kan yarinyar,


Dariya Nasir yayi har da dukan sitiyarin motar yace nafa gaya maka Abdul son ta yake duk wannan haukan da yakeyi.



Anwar ya zakuda kafada yace"Can da yawarshi Alh' Duk wani hargaginsa baya damuna Duk Abinsa ,sai dai ya Samu saura ,domin sai na cimma nufi Na a kan ta.


Shiru Nasir yayi mishi

Ya kalleshi yace"E yane!! Wai ya naga kai ma kana wani basarwa ne ,kar dai kace min ka jan ye qudirinka a kan ta"


Daga kafada Nasir yayi gami da ta6e baki yace"No kuje Ku karata kai dashi da ita babu ruwana ,sannan duk Abinda ya biyo baya Kar Wanda ya neme ni ,Babu Ruwana ,


A dage Anwar ya ke kallon Nasir din yana wani tabe baki yace"to dama wa zai sa ka ka ciki ,kai dai ka zuba ido kawai duk Abinda ya biyo baya INA da maganinshi wato kudi"Kare magana


Dariya Nasir ya saki yana dukan kafadar sa yace"baka da mutumchi fa ,wai Dan Allah mai ka gani jikin yarinyar ka gigice haka,Wanda ni duk gane gane ban ganshi ba.


Yace lafiyaryiyar Sura kyau Na Asali da Lafiyaryiyar Fata sai mitsitsin bakin yarinyar yana tafiya da imanina.


Cikin Abinda bai fi miti guda ba Nasir ya tariyo siffa da kammanin Maryam din yana so ya gazgata zan can Anwar din ,duk da cewa bai wani cika kallon ta ba sabida Tsoron da take bashi kuma har'hazar yau in ya kwanta bacci sai yaga sifarta cikin baccinsa yarasa wace irin masifa ce wannan




Gabanshi yafadi! Da ya hango yanayin durinta rabbas yasan yarinyar tanada zubi duk da take yarinyar a yanzu qirjinta a cike take babu masa ka tsinke wuyanta har da wani guru ,in ya shiga gurin Aunty wani sa'in tana zaune babu hijab yake kare ma jikinta kallo a fakaice,
Baya sakewa ya kalli fuskarta,
Shiyasa ya tsani mace tasaka hijab a cewarsa duk takurawa ne .
Amma in ba haka ba duk lokatan da yake ganinta cikin hijab da niqabi take shiyasa baya ganin wani Abu


Sai ya riqa mamaki yaushe har Anwar ya fahimci yarinyar ta Tara Abubuwan da ya lissafa.


Fuskarshi babu yabo babu fallasa yace"kai duk yaushe ka fahimci haka,kuma wa yafada maka tanan ake gane cikkakiyar Mace"


Yace jiya duk Na gane ko menene ,kar ka rai namin hankali ka rainawa kanka,kai kanka kasan Yarinyar ta hadu iya haduwa,kawai kace bata yi maka bane San koko daukar rai ,nasan in da tayi maka da tuni an wuce gurin ,yadda kake da bala'in son Mata,
Sai yasa dariya,ya cigaba da cewa kabari in Dan Dana tukkuna sai in fada maka yaya Abun yake"



Tsaki Nasir taja cikin wani bacin rai Mara dalili yace"karya kake wallahi in ci raguwarka kai kanka kasan duk bariki Na bana bin sidi sai sabo"

Kai dai da kake ganin zaka iya da yarinyar ga hanya nan ,Ai ban hana ba ,in tazo ta dafe ka shikkenan domin kamar mayya haka yarinyar take.




*BINTA UMAR ABBALE*

_MARUBUCIYAR_


*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUDI*

*GIMBIYA BALARABA*

πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š
_in kana bukatar cigabanshi ga number nan_
08089965176
[06/04, 19:30] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?


πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—
*🐾YARO DA KUDI*🐾
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—



*✍🏻Writting by*
_*BINTA UMAR*_
*Maman Abdul Wahabu*



_Bissimilla rahamanir rahim_


*πŸ…Ώ40*


"Ko ma mecece ,babu Ruwa na idan sarai Mayya ce ta haife ta Wallahi sai Na biya bukatata"
Anwar yafada yana danne danne a wayarsa Alamun babu Abin da ya dameshi.



Shiru Nasir yayi yana zan can zucci sabida yasan Halin Anwar ciki da bai ,in har ya kyalla ido ya ga mace yana sha'awa ko ta halin qaqa sai ya biya bukarsa.


Sai ya share kawai yabar maganar ,suka fada wata hirar ,Amma lokaci zuwa Lokaci yana jin faduwar gaba ,zuciyarshi tana fada masa rashin dacewar hakan.
Wata zuciyar kuma tana cewa to me ye ruwanka kawai ka kyalesu ,dama ai ka tsani yarinya,sai kawai yabi Abinda zuciyarsa take fada masa,

Haka suka karasa club din ,gurin cike da matasa Maza da mata ,sai cashewa suke ,Abin babu kyawun gani.
Suna fitowa guri ya dauki iho ,da sauri Nasir ya karasa cikin gurin,a kasa mishi kida ,ya riqa rawa Baby tazo ta Rumgumeshi tana kiss din shi kamar ta cinyeshi


*****
Daya saura Na dare Nasir yayi Parking din Motarsa ,yafito shiru harabar gidan Malam Ya'u ya shiga gida,
Sai masu gadin dake tsaro a waje,tare da karnika a kwan kwance a harabar gurin.


Dady Na jikin window din shi ta Sama tun da yaji karar motar Nasir ya taso yazo ya tsaya dama ,jiran dawowarsa yake ,
Ya saki labulen ya kuma ya zauna gefen kado ,gami da dauko waya na kokarin kiran Nasir din


Bugu daya ,ya daga cikin Sallam
Dady yace"kazo yanzu ina son ganinka"
Ya kashe wayar bai saurari Abinda Zai ce ba.


Toliet yayi saurin shiga ya watsa ruwa ,gami da wanke bakinsa sosai domin ya Dan taba ,duk da ba ya shan wacce zata bugar dashi to Amma warinta baya buya,


Yafito daga shashensa ,da nufin zuwa kiran da dady yake masa ,domin yasan Rigama ce kawai da takurawa a cewarsa dady har yanzu bai San me rayuwa take ciki ba.



A farlour ya tadda Dady a zaune
Ya karasa ya zauna cikin kujre yace"Dady barka da dare"

"Barka"Dady yace kana ya cigaba dacewa ka dawo ne"?

Sunkuyar da kai Nasir yayi domin bashi da tacewa ,ya fuskanci dady yaga lokacin da ya shi go gidan.


"Wato har yanzu kana nan a kan bakanka ko Nasir"
Yawace Yawace nan bazaka bari ba ko"
To babu Lafi ae" in sha Allahu gobe muna da taro a family house idan ka ga dama kaje" dady yakarashe maganar cikin bacin rai!


Dady yi hakuri zan je in sha Allah, Nasir din yafada

Dady yace"ae nasan Halinka ba zuwa kake ba yanzu dai ka ce zakaje ,zuwa gobe kuma ka qirqiri qarya kace kana da uziri"


Dariya Nasir yasa yace"Wallahi dady zan je in sha Allahu"

"Allah ya kaimu ,idan mun tashi daga taron zamu zaga gida Jan Marayu da Asibitoci kamar yadda muka saba"


"Owk Dady Allah ya kaimu ,karfe nawa za'a fara taro"?

"Karfe takwas ne dady yafada,yace katin yana sama,

"To Masha Allah ,Allah ya kaimu gobe ,kace zamu gaisa da "yan Uwa sosai Dan Na jima ban hadu da

1 Comments On YARO DA KUDI
avatar
magaji-2

1 year ago

Reply

Allah Yakara budi

Please Login or Register in order to submit comment