Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wallahi yanzu na gaji, gashi gurin yana mim zugi"


Shiru yayi tsawan minti biyu ya mike ya futa daga d'akin, murna ta ke tayi tunanin ko ya hak'ura ne, sai gashi ya dawo,hannushi rik'e da wani k'aton faranti cike da kayan tea
da wasu manya-manya biscut masu tsada

Ajiyawa yayi gabanta yace"ki had'a tae ki sha, tukkuna, kome ye sai ya biyo baya.


tae din ta had'a ta fara sha kad'an-kad'an, tana satar kallonsa, magana ce a bakinta, tanajik nauyi, shi kuma hankalinsa yana kan wayarsa,

Da kyar! tace"ancle Momyfa me zaka ce mata"?


Hararata yayi yace"kwartanci nayi kome, daga nan ma gida zan wuce dake babu wani gurin Momy da zan mayar dake, nima ina b'ukatar ki"
Yafad'a yana daddana waya babu abunda ya dameshi.


Shiru tayi kawai tana danne kuka dake son ya kufce mata, amma ina sai da hawayen ya zubo,sheshsheka yaji yayi saurin dago kanshi, yace Cikin fargaba ya sako daga bed din ya zauna kusa dai ta, kafad'ar ta ya kama yace "Baby Sorry stop crying"
Cikin damuwa yad'i maganar.
[26/07, 01:51] +234 808 996 5176: *YARO DA KUDI*
*153*

K'inyin shiru tayi, jikinshi ya fara kyarma sam baya son kukanta,yanzu ci masa rai yake, yace"Princess wannan kukan naki,bana son shi ki fad'amin dalili kinji, kiyi shiru please"
Yafad'a ya kaskantar da kai.
kamar bashi ba


Ita kanta Maryam din tayi mamakin shi, cikin shagwaba tace"ancle muje gidan Momy bana son komawa gidanka,wallahi tsoran kwana ni kad'ai nake"

Shima marairaice wa yayi yace"takwana gidan sauk'i Mylove ni sai in dinga tayaki kwana ko"?


"Uhum! Uhum! ita kuma Mubina fa"?
Tafada cikin shagwaba,

Shaf ya manta da wata mubina shi, yace" babu ruwanki da wannan, ke dai kawai ki amunce min please kar ki k'ara kuka kinji"?

D'aga kai tayi kamar wata yarinya k'arama, shagwabar ta tana dilmiyar dashi, yace"bari ij had'a miki tae ko"?

D'aga kai tayi a karo na biyu, kawai tana binshi da kallo, cikin mamaki wato shi dai in zaiyi sex ko wane irin ladabi da kwantar da kai ya iya abunda Maryam bata sani ba, shine ita kad'ai yakewa wannan, sabuda shi kad'ai yasan irin gamsuwar da yake da ita.


Duk ya zubar da madara a k'asa gurin had'awa ga wani uban sugar da ya zabga mata, k'arba tayi ta kurb'i kad'an sugar cau! a bakinta ya mutse fuska tayi, zuciyar ta ta fata tashi, sai kawai ta aje cup din kasan kafet ta kwanta k'asa,

Cikin mamaki ya bita da kallo ganin yadda ta lanjare, a kasa, yana d'aya daga cikin abunda yasa ya tsani cikin jikinta,sabuda yasan shine ya jawo mata,wannan kasalar, dole ne ma yasan yadda zaiyi dashi,


Kwanciya yayi kusa da ita ya mannata bayanta a kirjinta sai shinshina ta yake, yace" wannan yana d'aya daga cikin abunda yasa bana kaunar cikin jikinki, sabuda zai shiga rayuwata, nima ina b'ukatar a kula dani, jin abunda yace"yasa tayi saurin juyo wa tana fuskantar shi, ta bude baki kenan zatayi magana ya had'e bakinta da nasa, ya shiga sarrafata cikin kwarewa babu yadda ta iya haka ta hakura sabuda tana bukatar ya bar mata cikinta, nan kan kafet yayi ta wasanninsa da ita, sannan ya dauke ta suka koma bed, nan na futo na barsu nima.



Sai kusan sha biyu saura na rana, sannan Nasiru ya sararawa Maryam, tana kwance laka-laka kan bed cikinta sai kullewa yakeyi wani irin amai! mai k'arni yana yunkuro mata, bakintq duk ya cika da miyau, kafin tayi yunkurin mikewa amai ya kece mata nan tai tata kwarashi kan bed, mai wahalar gaske, lokacin Nasir yana toilte yana wanka, yana futowa idanshi ya sauka kanta,tq dafe k'irji tana kakari, ya mutse fuska yayi, yai saurin dauke kanshi, yana jin tashin zuciya, jin k'arnin amai ya cika d'akin.


Da towol din a jikinshi ya futa daga dakin da sauri ko sauraron ta bai ba, tana yunkurin amai,kamar zata amayar da "yayan cikinta.
[26/07, 01:51] +234 808 996 5176: *YARO DA KUDI*
*154*

Da kyar! ta samu amai ya tsaya, ta mike a hankali, jikinta nan nad'e da wani k'aramin towol iya cinya, bedshirt din ta cire daga kan bed d'in ta nufi toilet dashi, tana mamakin rashin imani da tausayi irin na Nasir, cikin abun wanki ta sakashi ta hada ruwa tayi wanka, bayan ta gama, sai ta wanke bedshit din dake a kwai gurin shanya a ciki ta shanya, ta futo, kayanta da ta cire du ta mayar, ta zauna kasan kafet ta had'a ruwan tae babu suga sai lipton shi take sha'awa sabuda yadda take jin cikinta kamar an mata yasa, kurb'a takeyi k'adan-k'adan ya shigo dakin cikin Sallama, daga shi sai treeQutar sai wata d'amammiyar vest kana ganin shi kasan yana cikin farin ciki sai annuri ne yake sauka a fuskar shi, bakin kofa ya tsaya yana karewa dakin kallo, ganin ta dauke bedshit din ta sanya wani, yasa ya shigo d'akin yana wata irin tafiya irin tasu. sunkuyar da kai tayi, kawao tak'i kallonsa, kwanciya yayi kan bed din yana kara gyara eir pix din dake kunnenshi, babu abunda ya dame shi, Maryam bata taba sanin namiji mayaudari bane sai yau lallai wato bukatar sa ta biya shikkenan har ya manta da ita.
sai da tagama shan tea dinta sannan ta dago kai tana kallonshi a nutse ta kira sunanshi, kasancewar da eirpic a kunnahi bai jiba, sai da ta buga gadon da hannunta sannan ya ankara cire eir pix din yayi yace"Ya akai"?

Shan kunu tayi tace"ka maidani gida"?

"Wane gidan"?
Yafada cikin sigar rashin mutumci

" Gidan Momy"
tafada muryarta tana rawa.

"Momy ce take auranki ko ni"?
yafada fuskarshi babu walwala,

" Kaine, kake aure na, amma ai ba haka kukayi da Momy ba"

"Ok to babu ruwanki da yadda mukayi da Momy, ni babu wani mayar dake da zanyi, kina nan ma, ita Mubina ta zauna can, in anjima in nafuta zansa Giss ya kawo miki kayanki"
yafad'a yana maida eir pix dinshi kunne,


Kuka tasa sosai tace"ai ba haka mukayi ba, ni wallahi bazan zauna dakai ba gwara gidan Momy ko gidan Mubina, ni bazan zauna kusa da kai ba ina ciwo baka damu dani ba, in ma mutuwa zanyi in mutu babu abunda ya dame ka"



Dariya yasa yace" Kinjiki da wata magana,nifa bazaki sanya ni a maganar cikinki ba, haka kawai ina hutawa ta, tunda dai ke kinji kin gani zaki iya kiyi, amma kar ki saka ran dan kina amaye-amayen ki zan taimakamiki babu ruwana yarinya"
yafad'a yana karkad'a kafa da alama music din da yake ji yana ratsa shi.


Cikin kuka tace"to wayace kayi min cikin kasan baka son haihuwa,kuma yanzu dan rashin imani da tsoran Allah kace a zubar, ai nagane dadin bakinka dan kana neman bukata ne kuma ka biya bukatar ka saura me"?


Mikewa zaune yayi yana kallonta fuskarsa dauke da murmushi na rainin hankali yace"zo nan kusa dani, in fada miki wata magana, kinji Mylove"


K'i tayi sai da ya kara magana sannan ta tashi taje ta zauna kusa dashi, d'ora ta yayi kan ciyanrsa yana mata wani d'an isakan kallo yace" kamar yadda kika fada min hakane, ciki nawa ne amma bana bukatarsa a yanzu, sai nan gaba, ke kuma da yake macace mai kwan haihuwa sex guda kin dauki ciki baki mori kuruciyar ki ba, ki amunce kawai a zubar dashi, ni kuma nai miki alkawarin nuna miki kulawa da soyyaya, kuma ko nan gaba kece uwar yaya na, kinga yanzu tun kafin tafiya tayi nisa kin fara shan wahala, na lura kina da laulayi, to nan gaba kuma ya zakiyi, uhhm, kawai ki yadda a zubar tun baiyi kwari ba, sai muci gaba da more rayuwar mu"

Cikin raunin zuciya tace"ancle kayi hakuri kabar wannan maganar dan Allah, wannan d'an da zan haifa baka sani ba ko shi kad'ane d'anka a duniya nima haka kuma bakasan irin baiwar da yake tafe da ita ba, ni dai ina son abunq gaskiya"


Tunkud'e ta yayi ta kusa fad'uwa k'asa cikin fushi yace"sai kije ki tayi banza bagidajiya kawai waccae batasan me duniya take ciki ba, dube ki don Allah ko 22years baki yi ba, amma kike sha'awar haihuwa, wallahi kinji na fad'a miki mutukar baki yadda an zubar da cikin nan ba sai nayi miki wulakanci anan daga ni sai ke, a gida"


Cikn kuka tace"Wallahi bazan baka goyan baya ba gurin sab'awa mahallinmu, duk abunda zakayi sai dai kayi, wannan cikin kamar na haife shi nagama"


Mari ya kai mata ta kwace da sauri ta matsaya can gefe tana kuka, gwanin tausayi,

A zafafae! yace"get out from my room.

Da gudu ta futa tana kuka, shi kuma ya koma ya kwanta, yana tunanin mafuta, domin shi yanzu bai shirya haihuwa ba,amma yarinyar nan tana nema ta cuce shi.
[26/07, 01:51] +234 808 996 5176: *YARO DA KUDI*
*55*


Mik'ewa yayi da sauri ya futo farlo tana tsaye jikin kofa tai saurin matsawa gefe, yayi mata wani kallon banza ya shige wani had'adan bedroom k'ananun kaya ya sanya, ya futo farlo hannusa rik'e da waya, ya zauna yana kunnawa ko kallon inda take bai yi ba, kunna wayar yayi yafara kiran Giss yace yazo yanzu ya sameshi a gesthouse din sa, Abbas ya kira sukayi magana sama-sama, ya kashe wayar yaje ta kusa dashi, tana tsaye tana kallonsa, duk abunda yake, Wayarshi tayi k'ara alamun kira, Dr Sofia ce, "Ya akayi?
abunda ya fad'a kenan yana ya mutse fuska, tace" Dr kashi hospital yanzu a kwai aikin gaggawa"

"Menene"?

" Wata matace zata haihu d'an ya futo ta k'asa yanzu haka sai suma take"

gabanshi ya fad'i ya d'an kalli inda take tsaye, yayi saurin kauda kai, yace"haihuwar fari ce"


"Eh"
Dr Sofia ta fad'a da sauri

kashe wayar yayi ya kalli Maryam dake tsaye sakato yace"d'auko mayafin ki muje"


Jikinta babu kwari ta shiga d'akin taje ta d'auki mayafin ta futo,


Gaba yayi ta biyo shi a baya, suka shiga mota kusan tare, waya yayi wa Giss yace ya sameshi a Hospital, ya wuce, babu wanda yacewa da d'an uwansa komai har suka je asubutin.



Dr Sofia ce ta karaso gurin da sauri, sai taga Maryam ta futo daga mota, kallon-kallon a ka farayi tsakaninta da Maryam da sauri ta yi k'asa da kanta sabuda bata mance karan battasu da ita ba, Hannunta Nasir ya kama suka nufi cikin asubutin, rai a bace Maryam tabisu a baya, shi kuwa Nasir yana sane yayi mata haka dan ya bata haushi, tare suka shiga treatar duk su Uku, Maryam ta tsorata da yadda ta ga halin da matar take ciki nan take sai jikinta ya soma b'ari, tasbihi kawai takewa Allah cikin zuciyar ta gabanta sai fad'uwa yake, haka suka fara aiki, Cikin kwarewa da sanin makamar Aiki Nasir ya mai da d'an cikin mahaifiyarsa, ya zura hannusa a nutse ya dai-dai ta kan dan dai-dai inda zai futo, Maryam na saman gadon matar cikin k'arfin hali take d'an matsa mata ciki, Dr Sofia kuwa tana tsaye kusa da Nasir, hannuta rike da wata tasa mai dauke da wasu allurai da zarirrika, tace"Dr matar nan ta galabaita fa, dole ai mata k'ari kaga ta kasa motsi, ku yunk'uri, kallon Maryam yayi yana d'an hararata yace"d'iro kanta a cinyar ki, ki danno samman cikin a hankali,jikinta na rawa tayi yadda yace d'in, matar sai wani jan numfashi take, na wahala bakinta duk ya bushe, hannun Maryam ta ruke tamau da kyar tace"ki tamaika min zan mutu wayyo Allah na, sai nuffashin ta ya d'auke, Maryam ta gigice sosai bakin ta narawa tace Ancle gaka ta suma, da sauri Dr Sofia ta karaso gurin tana duba matar, kallon Maryam d'in yayi yace"ki cigaba da abunda na saki"
Cigaba da matsa cikin tayi tana kokarin mayar da kwallar da taro a kwarmin idonta

Cikin ikon Allah matar taja wani nuffashi, wanda yayi dai-dai da fadowar jaririnta, da sauri ya kauce daga gurin, Dr Sofia ta karaso gurin ta dauke jaririn sakkowa Maryam tayi ta na duba matar, sai nishi take, alamun mahaifa zata fad'o sannu kawai take mata jikinta yayi sanyi, ta tsorata dama haka haihuwa take, ko lokacin da suke makaranta basu tab'a treining na unguwar zoma ba shiyasa bata san yaya ake ba, kawai dai sun karanta abun, futa yayi yana ya mutse fuska zuciyarsa sai tashi take, in ba dole ba, sam yaki jinin kazantar haihuwa, Maryam kuwa tana tsaye ta fara jin wani abu mai d'umi yana bin cinyoyin ta, da sauri ta kalli k'asan k'afafunta sai taga d'ogon jini, cikin tashin hankali ta nufi toilet dake cikin d'akin gabanta na dukan uku-uku
[26/07, 01:51] +234 808 996 5176: *YARO DA KUDI*
*156*


Tsugunawa tayi a toilet d'in gami da sab'ule pant din dake jikinta, jini ne ya cigaba da zuba,kuka ta sanya, ta mik'e tsaye da sauri tana innalilahi wa inna ilaiyi rajiun ledar pad ta bude ta sanya d'aya ta futo tana sharar k'walla, Dr Sofia na tsaye kan matar tana gyara ta, Maryam ta futo da kallo ta bita dashi, tana tab'e baki, ita kam ta kanta take dan bata san tanayi ba, tana futa ta ganshi a zaune wata k'ujera yana duba wasu takkadu, watw narse tsaye a kansa, bakin ta na rawa ta tsaya a kanshi, tace"mu tafi gida" dago kai yayi yana kallonta a ya mutse yace"in munje gida me zaki dallah matsa daga kusa dani"

Tana tsaye,bata matsaba, shi kuma har gama duba takadar, ya mikawa narse d'in ya mik'e tsaye, da sauri ta rik'e hannusa ya waiwayo zai mata masifa, sai yaga hawaye shab'e-shab'e a fuskar ta, abunda ya tsana kenan, kukanta, jikinsa a sanyaye yace"Wai mene kike kuka ne"?


"Ancle jini ne yake zubar min Allah yasa ba b'ari zanyi ba"

Tsaki yaja yace"sai me, in kinyi b'arin dama haka nakeso kinga zai futa cikin dad'in rai"
Yana gama fad'ar maganarshi ya shige ofis d'insa

Tayi tsayuwar minti goma a gurin, gashi tana jin zubar jinin a jikinta, cikin tashin hankali ta futa, daga asubiti, ta tsaya tana neman abun hawa wata rana ake kwalawa wacce tasa ta zubewa a gurin,jiri yana d'ibar ta, Cikin hajijiya ta hango wani d'an adai-daita ta tsayar dashi, bakinta na rawa tafad'a masa unguwar da zai kaita, yace"shigo dagani baki da lafiya"

Ita dai Maryam batace masa komai ba, ta shiga ta zauna,wanda yayi da-dai da futowar Nasir da mota, yana nemanta, ransa a b'ace ya bi bayan adai-dai ta da gudu, Maryam, ta mirrow din a dai-dai ta ta hango motarsa, tace"ka k'ara gudu, inaso inje gida da wuri, Aikuwa gudu ya falfalawa a kan titi.
[26/07, 01:51] +234 808 996 5176: *YARO DA KUDI*
*157*

Har cikin estet din mai a dai-dai ta sahun ya shiga da ita, da Sauri ta shiga gidan ta k'aramar k'ofar batare da tsaya sauraron me a dai-dai ta ba balle ta biyashi hakkinsa, kallo ya bita dashi cikin mamaki daga bisani ya kunna a dai-dai tasa ya juya zai futa, wanda yayi dai-dai da shigowar motar Nasir, alama yayi wa mai a dai-dai ta ya tsaya, parking motar yayi ya futo da rai a b'ace baiyi wata-wata ba ya tsinka masa mari hagu da dama, cikin fushi yace"wane shegen ne yaba izinin d'aukota dan uwarka"
Cikin jin zafin marin da yayi masa yace"Oga itace tace na kawo ta ba wani,a yi hakuri Oga" cikin tsawa yace"b'ace min dagani" da sauri ya shiga a dai-dai tarsa ya kunna ya fafara da gudu, shi kuma a sukwane ya shiga gidan ta k'aramar kofar, get man sai gaida shi yake yayi masa banza,


kafin Maryam ta k'arasa farlo jikinta duk ya jik'e da jini, jiri ne kawai yake d'ibarta da kyar ta bude kofar ta shiga,sai ta zube bakin kofa tana rik'e ciki, Kyauta me aiki ce ta futo daga kchin ta ganta, hankali a tashe ta aje abunda yake hannuta tazo ta ta rairayen ta, tana d'aga ta sai taga jini ya b'ata gurin, salati tayi tana sallallami, wanda yayi dai-dai da shigowar Nasir, Kyauta tace"Uban gidana tare kuke ne,da ita mai ya faru take zubar da jini, Allah yasa ba b'ari zatayi ba"
"Ina Momy take"?
yafad'a yayin da miyan bakinsa ya bushe k'amas

" Tana sama yanzu ta hau tace zatayi sallahr walha"


jin abunda Kyauta tace yasa ya fara k'okarin daukar Maryam d'in ba tare da yayi tunanin zai b'ata jikinsa ba, zamewa tayi ta koma ta zauna bakinta sai motsi yake,tana jin a zaba, cikim sigar yaudara yace"Mylove kiyi hakuri muje in dubaki kinji ko"
Hannusa ta cire a jikinta ta kwanta kasan tayal ita kad'ai take jin abunda takeji,na azaba k'okarin daukarta yake a karo na biyu ta fara kuka gami da cewa"Baba Kyauta kar ki bari ya d'auke ni daga nan zai cuce ni"


Shiru Kyauta tayi, sai kuma tayi sama da gudu domin kiran Momy, ita kuma, Momy dama ta ji hayani sama-sama da carbi a hannuta ta sakko suka ci karo da Kyauta, can ta hango Nasir jikinsi duk jini ga Maryam a kwance a k'asa, da Sauri ta kalli Kyauta tace"lafiya wai meke faruwa? "Hajiya babu lafiya, da sauri ta sakko batare da ta saurari k'arshan maganar ba,


Maryam na kwance kamar ruwa,sai malele kuwa take Momya tayi salati ta kamata ta rugume ta cikin tashin hankali tace" dauke ta ka kai min ita sama, jikinshi na kyarma! ya dauke ta suka nufi sama,da sauri Momy ta had'a wata allura tayi mata, ta tsaya a kanta jikinta duk yayi sanyi addu'a take Allah yasa kar cikin nan ya zube, b'acin rai baisa ta kalli inda yake tsaye ba, shi kuwa cikin zuciyarsa farin ciki ne tsantsana da alamu cikin ya zube, ganin yadda ta zubbada jini da yawa, wani wawan bacci ne ya dauke ki Maryam din mai tattare da wahala, Momy ta nufi sif dinta ta ciro wata doguwar riga cotton ta zo ta zauna gefan gadon ta d'agota ta fara sa mata, Maryam bata san tana yi ba, bayan ta gama sa mata kayan ta d'ago kai tana watsa masa kallo tace"tsayuwar me kake min aka"

Shiru yayi da kai a sunkuye, "ka fuce min daga d'aki banason ganin ka"


dago kai yayo gwanin tausayi yana kallonta,

Hararasa tayi gami da d'auke kai, sai ya zube a gabanta gwiwa bibbiyu ya rik'e hannuta yace"Momy ba laifina bane kar kiyi fushi dani, fushinki a gareni bazai min kyau ba"
[26/07, 01:51] +234 808 996 5176: *YARO DA KUDI*
*158*


Cikin fushi da b'acin rai Momy tace"jiya daka futa da ita ina ka kaita? yanzu ashe dama kananan da k'udirinka sai ka zubar da cikin baka fasa dama,shine kaje kabata magani ko Myson"


"Momy wallahi babu wani magani da na bata ki fahimce ni Momy Gesthouse d'ina kawai naje da ita bayan na kaita ta gaisa da iyayenta kamar yadda kika buk'ata.


" My son nice nace ka kaita Gesthouse d'inka,me kaje kayi mata domin ni yanzu na daina yadda da k'arya da k'arairayin ka"


"Momy babu abunda nayi mata wallahi ki bari ta tashi sai ki tambaye ta"

"Ok kace babu abunda kayi mata, sabuda ka raina min hankali, ka d'auki " yar mutane,kaje ka isheta da jarabar ka, ba dole ciki ya zube ba"


Sunkuyar da kai yayi gwanin tausayi, har yanzu hannuta na cikin nasa,fuzgewa tayi tace "tashi ka bani guri, wallahi cikin nan ya zube zaka fuskanci b'acin rai"
Momy tafad'a cikin tsawa, d'in tashi yayi ya k'ara gyara zama, a gurin mik'ewa tayi tabar gurin, kallo ya bita dashi,cikin mamaki Momy bata tab'a fushi dashi ba,




Bacci a wa uku Maryam tayi ta tashi, tana jin kamar anyi mata yasa a ciki, lokacin Momy ta sauka k'asa sai shi kad'ai da sauri ya mik'e daga inda yake,yaje ya zauna gefen bed d'in ya rik'e hannuta, wani irin tausayinta yakeji yarasa wace irin gaddama da taurin kaine da yarinyar da ta yadda anzubar da cikin da tuni haka bata faru ba, "Sannu Mylove" yafad'a yana murza hannunta, rufe idonta tayi tana jin wata irin tsanarsa a zuciyarta yanzu ji take bata da babban mak'iyi sama da shi,



Momy ce ta shigo ta ganshi bakin gadon cikin tsawa tace"me kakeyi anan d'an anace, wato zaka k'arasata ko"?



"Momy wace irin magana ce wannan"
yafad'a da damuwa a fuskarsa



" Tashi ni kabani guri"
tafad'a yayinda take k'arasowa gurin mikewa yayi jikinsa a sanyaye ya sauka k'asa kwanciya yayi cikin kujera yana sak'e sake, na neman mafuta, domin har yanzu yana nan a kan k'udirinsa in cikin nan bai zube ba, sai ya k'ara d'aukar mataki.





Momy ta zauna tana me rike hannuwan Maryam d'in cikin tausayi tace" Dota sannu kinji ko yaya jikin? yanzu me yake miki ciwo"?





"Momy bana jin ciwon komai, yanzu sai rashin kwarin jiki, Momy baby na ya lalace ko"?
tafad'a hawaye yana gangaro mata




Momy ma hawayen take sharewa tace" insha Allahu bai futa ba, ai na duba naga jinin ya daina zubah ko"?


D'aga kai tayi gwanin tausayi Momy tace"tun misalin k'arfe nawa kika fara bleeding d'in?



"Momy wajan 8:00 am ne, ya fara zuba k'adan-k'adan"


Shiru Momy tayi tace"da alama babymu yananan naga alamu har yanzu a tattare dake"



Rufe fuska Maryam tayi cikin jin kunya, murmushi me ciwo Momy tayi tanaiwa Yaronta addu'ar neman shiriya tace"me kikeso kici yanzu"?



"Momy ruwan tae zansha baba madara, a samin milo kawai"


" Ok sai me kuma"

Shiru Maryam tayi daga bisani tace, "Kyauta tayi min k'osai ina sha'awarsa"


"Yanzu zan sanya ta tayi miki insha Allah"



K'asa ta sakko suka had'a ido dashi yana zaune duk ya furgice, kallo ya bita dashi, tayi saurin d'auke kanta, ta nufi kchin inda take jiyo Kyauta na aikace-aikace"

Momy na fad'a mata, ta hau gyara wake, tace"yanzu kuwa zan yi mata, Allah sarki yarinyar arziki ai tasha wahala d'azu
Futa daga cikin d'in Momy tayi ta koma sama gurin Maryam suka cigaba da hirarsu, Momy tace"zan tambayeki kinji ki fad'amin gaskiya"


D'aga kai tayi, Momy tace"me yabaki kikasha wanda ya sanya ki bleeding"



Shiru Maryam tayi, daga bisani tace"Momy babu abunda ya bani"


" Wato bazaki fad'amin gaskiya ba ko"?


"Allah Momy bai bani komai ba"


"Ok toum wane irin aiki kikayi har ya janyo miki haka"?



" Babu Munje hospital dai wata mata zata haihu,tare dashi muka k'arbi haihuwar, shine hankalina ya tashi, Momy matar tabani tausayi, wallahi"
ta karasa maganar tana kuka.
[26/07, 02:03] +234 808 996 5176: [7/24, 3:23 PM] BintuBatula,BintUAbble👄: *YARO DA KUDI*
*159*

Momy tace"idan na fahimce ki kina so kice min ganin wannan matar ne ya saki tsorata har jini ya yanke miki ko"?


D'aga kai tayi cikin jin nauyin Momyn

"Ki kwantar da hankalin ki kinji ko my Dota daga yanzu kar ki k'ara yadda ya yaudare ki yace kizo kuje wani guri, ni nagane dalilinsa na tafiya dake hospital d'in kuma insha Allahu bukatar sa baza ta biya ba"
Momy ta karasa maganar tana kwantar mata da hankali


Tsaf Kyauta ta gama had'a komai ta haura sama inda suke,shi kuwa gajiya yayi da zama ya mike ya futa, ga wayar da Mubina take masa ta dame shi, duk ya rasa yaya zaiyi wani shashe na zuciyarsa yana nuna masa abunda yayi bai kyauta ba,yanzu Momyn shi ita kadai ta rage masa aduniya dole yaje ya bata hakuri in ta huce, ka tsaye gida ya nufu jikinsa duk babu k'wari,sai tunanin yadda zai bullowa al'amarin yake


Mubina na hakimce a farlo tayi shigar k'ananun kaya nonowan ta duk sun furfito ta saman riga,abunda yake rud'ar Nasir kenan, amma abun mamaki sai taga ya d'auke kansa ya tafi ya kwanta cikin kujera jikinsa babu kwari



Cikin kwarkwasa ta mike ta karasa inda yake ta zauna saitin kansa tana shafa sumar kansa had'e da fuskarsa sai wani lumshe ido take, tace"my only kana yi mun abunda gaka dama fa, tun jiya rabon da in sanya ka a idona, kana gurin waccan yarinuar da bata da mamora ajiki"


Idonshi d'aya ya bud'e yana kallon fuskarta, tayi masa inkiya da ido, wai ya kalli k'irjinta,aikuwa ya zubawa k'irjin ido sosai yana jin wani feeling a jikinshi amma yasan yanda yake cikin damuwar nan ko yace zaiyi wani abu ba iyawa zai yi ba, yana leb'anshi na k'asa ya lasa yace"my Mubina yunwa nake ji sosai ki bani abunci"

A haukanta wai ta zaci yunwar sex yakeji saboda tasan halin mutumnin ta,kawai sai ta d'ora hannsa kan k'irjinta tana shafawa tace"muje in baka abunci ka"


Cire hannunsa yayi da sauri yana k'okarin mikewa zaune yace"dallah matsa, ina miki maganar ina jin yunwa kina min wata magana sam baki iya komai ba ke kam

Mik'ewa tayi tace"to shikkenan bari in je in maka girki, ni kasan ban iya komai ba, sai dafa indomee"


"Sai ki koya kuwa domin nagaji da cin abunci a waje, sai kace wani mara galihu, mara gata

Kchin ta wuce tana wata irin tafiya,

1 Comments On YARO DA KUDI
avatar
magaji-2

1 year ago

Reply

Allah Yakara budi

Please Login or Register in order to submit comment