Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Abinda zata cewa Anwar sai dai tace "Allah yayi mata sakayya wannan tozarcin da yayi mata cikin jama'a
[08/06/2019 7:42 PM] ®Binta Umar Abbale: Shi kuma Abdul, ta barshi da Allah yadda yaci amanarta bazata taba yafe masa ba, in ta tuno wai ita matar aure ce kuma matar Nasir sai gabanta yayi ta mugun faduwa, Ya Rabi tayi tayi da ita tayi shiru abin ya gagara ,




Malam ya shigo yana sa6e babbar riga kana ganinshi kasan yana cikin tsantsan farin ciki



Kawai ya taddasu sunyi jingum jingum sai kace gidan makoki, ya bisu da kallo daya bayan daya kana ya mayar kan Maryam wacce ke rakube gefan kujera tana shirgar kuka kamar wacce a kai ma mutuwa



Ranshi ya baci ya daka mata tsawa gami da cewa"kukan mai kikeyi Maryamu"?




Ya Rabi tace"wallahi kuka take tun da taji labarin abinda ya faru, anyi anyi tayi shiru taki yi"



Zama yayi cikin kujera yana fuskantar ta yace" wani irin kuka zakiyi Maryamu ke da Allah ya rufawa Asiri lokacin da a kaso a tona miki, tabbas nasan a kwai abinda Allah ya boye a wannan al'amarin,
Abinda nakeso dake shine ki kwantar da hankalinki kina tare da albarkamu insha Allahu zakiga alkairi a rayuwarki mutukar kika yimana biyyaya, nine mahaifinki na kuma karbi sadakinki na kuma bawa Nasiru Auranki a madadin Abdul"
Malam ya karashe maganar gami da zira hannu cikin aljihun malin malin din dake jikinshi ya ciro kudi yace"ga kudin sadakin ki Maryamu Allah yayi miki albarka ya baki zuri'a tagari tare da "yar uwarki abokinyar zamanki"

Maryam tana kuka ta sanya hannu bibbiyu ta karbi kudin dake hannun mahaifinta
[09/06, 19:26] +234 808 996 5176: [09/06/2019 2:23 PM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*113*
Da kyar Ya Rabi ta rarrashi Maryam ta bar kukan da takeyi ta sanyata tayi Wanka ta fito mata da wani uban les blue colour yayi mugun yi mata kyau abinka da farar fata ta sata tayi kwalliya dai-dai misali dama Maryam bata da matsalar gashi kullum cikin gyarashi take, dan haka Ya Rabi ta kara gyara matashi sosai ta fito mata da mayafi pink colour hade da yari da sarka fashion munti colour set din Takalmi da jaka iri daya masu bala'in kyau da tsada,kan kace kwabo Maryam tafito Amarya sosai tayi kyau, haka "yan uwan mahaifiyarta suka sanya ta a gaba suna ta bata baki kan ta godewa Allah akan sauyin da yayi mata, dama haka shi yafi alkairi a rayuwarta




Lokacin da Mubina taji labarin abinda ya faru sai da takusa yin dan Karamin hauka, kamar ita ace zatayi kishi da wannan yarinyar tasan tafita komai na rayuwa ilimi kudi wayewa nasaba uwa uba kyau ita a ganinta tafi Maryam komai da komai sabida haka taci alwashin akan sai dai Nasir ya zaba ita ko Maryam din domin bazata taba yin kishi da wannan jahilar ba.




Kwayenta sai zugata sukeyi kan in taje kar ta saurarwa Maryam kuma kar ta sake ta yadda su zauna gida daya da ita domin babu aji.

Hanifa kuwa dariya take tana farin ciki a fili tafito tace"wallahi haukan bazan kike domin ko makawo ne ya sha fa ki ya shafa kishiyarki yasan tafiki kyau, nesa ba kusa ba sabida haka ki daina wani hura hanci"



Mubina ta rika zaginta kamar "yar maguzawa a kan me zatace Maryam tafita ita irin matan nan ne masu San kansu komai sun fi kowa iyawa



A waya ta kira Nasir din tace masa ita Sam bazata zauna gida daya da wata wallahi kuma sai dai ya zaba Ita ko Maryam




Lokacin yana tare da Momynsa kuma duk taji abinda Mubina tace hankalinta ya tashi, tun ba'aje ko ina ba Mubina tafara shigo da tsirfa dama kwata kwata ita tasan Maryam ba zata damu ba
Mubina ce abin ji


Ganin Nasir din bai bata amsa ba ya kashe wayarsa tace"My son wane mataki zaka dauka ne nifa banason rigima kuma ba nasan abinda zai daga maka hankali"
[09/06/2019 2:42 PM] ®Binta Umar Abbale: Tsaki yaja yace"Momy karki damu babu macan da ta isa tasa na sauka daga kan ra'ayina , mutukar Mubina tana San zama dani dole tabi umarnina, Momy bani da ra'ayin raba gida kuma bazan raba ba tare zasu zauna da juna shikkean nagama magana"



"Myson ina ganin ka raba musu gidan kawai zaifi alkairi"


"Momy ki kyaleni Dan Allah wallahi Momy Mubina bata isa tasa ni nayi abinda banyi niyya ba, kawai ki bar maganar,ke dai kawai ki cigaba da min addu'a"



"Toum shikkenan My son Allah ya taya riko ya baka ikon yin adalci a tsakaninsu"



"Ameen Momyna abinda nake so inji kenan"

"Yanzu cikin Estet din zaka zauna ko zaka fita"?




A jiyar zuciya ta sauke gami da cewa "gidan Dady dake Tarauni nan nasa a gyara dazu munyi waya da mai akin za'a mishi fanti ko wane part kowa zai dau daya tunda uku ne shikkenan naraba gaddama babu wacce zata ga "yar uwarta sai taso"




"Kayi dabara Myson"
Momy tafada ta cigaba da cewa "yanzu ni kadai zaka bari a gidan nan ko"


Dariya yayi yace"Momy ko kinaso in zauna nan din"?


Itama dariya tasa tace"A'a babu ruwana ni bana son zama da sirika, Myson ina nan ina maku fatan alkairi


Murmushi kawai yayi yana girgiza kai
Ya mike tsaye gami da cewa "zan shiga inyi Wanka in fito yanzu zan Dan fita a kwai wasu baki da za muyi daga Fatkwat abinda ya hana Abbas halarta daurin auran kenan, gashi na kashe wayoyina dole nasan zasu nemeni"




Momy tace" Yau dai daya su yi maka uziri yau ranar auranka ma sai ka fita My son"


Murmushi yayi yace"Momy kenan"
[11/06, 11:02] +234 808 996 5176: [10/06/2019 6:00 PM] Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*114*

Wanka yayi ya sanya wata shadda mai uban tsada wagambari fara kal ya sanya hula fara takalmi mai gidan dan tsaya baki sai a goganshi na silver mai mugun tsada sosai dressing din yayi mishi kyau kana ganinshi kasan ango ne hannushi rike da farin glass ya fito sai zabga kamshi yake
Momy na zaune tana waya da mutananta tana fada musu yadda al'amarin ya kasance, yace"Momy zan fita ni sai bayan isha'i zan dawo"



Momy ta mike ta biyo bayanshi tace"yanzu yaushe zasu tare iyalin naka"?


"Gobe insha Allahu
Za'ayi komai a gama"

"To Allah ya kaimu lafiya"
Momy tafada cikin farin ciki


Sai da ta ga fitarshi daga gidan sannan ta koma ciki


Ban garansu Mubina kuwa buki suke sosai da sosai babu yadda bata dayi da Nasir ba a kan ta shirya party tanaso ya hallata amma yace mata babu inda zashi dan bashi ya sata ba, haka dai tayi hidimar bikin ita da kawayenta



Wata kawar Ya Rabi ce tazo ta dauki Maryam ta kaita gidanta ta dauko mai mai kunshi gami da gyaran jiki, kunshi yayi kyau sosai baki da ja daki guda ta sata ta turara mata jiki gami da gyaran fata sai da fatar Maryam tayi mulmul sosai Hajiya Aisha ta shirya Maryam sosai sannan ta dauketa a motarta suka nufi wani hadaddan boutique ta dinga jidar mata kananun kaya masu kyau da tsada.



Hajiya Aisha tana dreving ta kalli Maryam dake kusa da ita tace"kinga wannan kananun kayan da na sai mai ki in kinje gidan mijinki su zaki riqa amfani dasu, kar ki tsaya kunya kinji ko tunda kinga kina da kishiya




Kiyi kokari ki kama mijinki a hannu tunda dai Allah ya qaddara wannan yaron Mijikin ne sai ki godewa Allah, yanzu sauran yaki yana gareki
[10/06/2019 8:00 PM] Binta Umar Abbale: Hajiya Aisha ta dage tana koyar da Maryam dabarun zama da miji da yadda a ke kula dashi tace "su mazan wannan zamani da kike ganinsu sai da rarrashi da siyasa, sabida haka sai in zage damtse gurin ganin kin kama mijinki a hannu"



Maryam kuwa sunkuyar da kanta tayi tana jin kunya Hajiya Aisha jin irin abinda take fada ita kam kunya take ji tana ganin bazata iya amfani da wadan nan kananun kayan ba




Sai daf da magariba suka shiga gida,

Ya Rabi taji dadin abinda kawarta kuma aminiyarta tayi mata ganin yadda Diyarta Maryam take walwali ga wani mugun kamshi tana zabgawa duk inda ta gifta





Bayan sallah magariba Ya Rabi tace ai ya kamata su shiga bangaran Momy domin su gaisheta kuma suyi mata godiya da fatan alkairi





Duk su ukun suka shiga gurin Momy ta karbe su cikin mutumci gami da kyautatawa


Ya Rabi tace" Hajiya sai mukaji wannan abin alkairi kuma"



Momy tayi dariya tace"ai haka Allah ya tsara dukkanin abinda Allah ya tsara babu mahalukin da ya isa ya hana, Allah yayi Maryam matar Nasir ce"




"Wannan abu haka yake hajiya, Ubangiji Allah ya sanya alkairi ya basu zaman lafiya Allah ya bashi ikon kyautata adalci a tsakaninsu"


"Ameen ya rabbi nagode sosai"
Momy tafada tana kallonsu cike da murmushi




Ta cigaba da cewa gobe insha Allahu zasu tare a gidanshi dake tarauni kar ku wahalar da kanku komai an tanada a gidan, Maryam kadai muke bukata,insha Allah kayan lefanta ma zataje ta tadda a can"





"Hajiya Allah ya saka da alkairi ubangiji Allah ya kara arzuqi da wata mukan babu Cabinda zamuce daku wallahi"
Aunty tafada tana sunkuyar da kanta




Momy tace "nasan dai Dota bata da matsala yarinyar tana da nutsuwa amma dai sai a kara ja mata kunne sabida ba ita kadai zasu zauna ba a kwai "yar uwarta duk abinda zata gani ta kauda kanta wataran sai labari






"Insha Allahu za'a yi mata fada Hajiya duk da cewar Maryam bata da kwarfinaya da yawa, amma yau da gobe ta wuce wasa
Hajiya Aisha tafada cikin nutsuwa da dattako


Hira suka cigaba da yi cikin fahimta gami da wayewa dake Hajiya Aisha wayayyiyar Mace ce kuma "yar boko shine dalilin da yasa Momy ta ji hankalinta ya kwanta da ita
[11/06, 13:58] +234 808 996 5176: [10/06/2019 10:17 PM] Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*115*
Nan sukayi sallahr isha'i Momy ta sanya mai aikinta Uwani ta hada musu abinci dole babu yadda suka iya suka zauna suna ci suna mamakin karamcin Momy





Karfe takwas na daran rabar Lahadi Maryam ce durkushe gaban mahaifinta tana kuka sosai shi kuma yana mata fada kan ta kula da auranta kuma tayiwa mijinta biyyaya da dukkanin abunda ya umarce ta.




Aunty ma tayi mata addu'a sosai sannan tayi mata nasiha irin tama ta mata yi nayi bari na bari


Yaya Rabi daman ita kullum Cokin yiwa Maryam din nasiha


Dake babu jama'a sosai sabida basu wuce su biyar ba sai Momy tacewa drevar ya dauki babbar mota kawai ta isa


Haka Ya Rabi ta sanya Maryam cikin mota tana gursheken kuka kamar ranta zai fita wai yau ita ce ta auri Wanda bataso Wanda yayi mata muguwar tsana a rayuwarshi
[11/06/2019 7:09 AM] Binta Umar Abbale: Momy ta rungume ta a jikinta tace "kiyi hakuri Dota ki zauna da mijinki lafiya da "yar uwarki nice mahaifiyar Nasir nafi kowa sanin halinshi duk wani abu da kike tunani zai faru babu shi sai alkairi, ni da kaina zan damka masa amanarki shine ki kwantar da hankalinki in kika iya zama da Nasir zaki ji dadinshi sabida yana da saukin kai duk ranar da kika ga ya tashi yana muskilanci to mybe da akwai abinda yake damunshi ke zaki dinga bibibyarshi tunda shi zurfin ciki gareshi, dan Allah Maryam ga amanar Nasir nan Na damkata a hannunki kamar yadda ba bashi taki amanar ki lura da cinsha da shansa domin Sam baya son cin abinci sai na tsaya a kanshi sannan"




Wani irin tausayin Momy ne ya kama Maryam babu abinda Momy zata nema ta Gaza yi mata shi a rayuwarta sabida haka tayi alkawarin ko da Nasiru zai yankata gunduwa gunduwa za ta tsaya ta rike amanar da ta karba



Wani irin gida ne mai bala'in kyau da tsari plate ne mai dauke da part uku sai katowar haraba gurin ajiye motaci ma na mussaman ne can gefe lambu ne an kewaye shi da wasu karafuna sun sha ado gurin gress kafet ne a ko ina na gurin yanayin gidan kamar irin gina ginen kasashan waje ko ina tsaf tsaf Ma'aikatan gidan sai kaiwa suke suna kawowa ko wanne da aikinshi




Nura tayi parking din mota Momy ta fito hannuta rike da Maryam Ya Rabi da sauran jama'a suka fito suna bin gidan da kallo cike da kauyanci sabida kalar faint gidan ma abin kallo ne Momy ta fito da waya tana neman Nasir ta kira ya kai sau uku ba'a daga ba, gashi tana ring sai ta kashe wayar tana tuna in wane part din ne na Maryam tana tsaka da tunani motoci suka fara shigowa gidan dauke da amarya Mubina da ta wagarta, motoci sun kai goma






Kan kace kwabo gurin ya cika da hayaniya dangin Mubina suka dinga fitowa daga mota kamar bazasu kare ba.




Wata yar Momynta ce ta hangi Momy tsaye jingene da mota ,abin ya bata mamaki yanzu yanzu sukaje can gidanta domin su mikamata Mubina a matsayinta uwar miji ba ta nan abin mamaki sai gata anan ko mai ya kawota oho




Har kusa da Momy ta karasa inda Momy take tace"Hajiya Aminatu ashe kina nan, yanzu yanzu mukaje domin mu mika miki amarya kamar yadda al'ada ta gadar ba mu same ki ba"





Cikin nutsuwa da sakin fuska Momy tace"wallahi kuwa ai sabani mukayi domin bamu Dade da fitowa daga gida ba nayi tunanin zan sameku anan, ai babu matsala ga "yar uwar tata ma yanzu zan hadasu in yi musu nasiha"
Momy tafada tana kara damqe hannun Maryam






Hajiya Abu wato yayar Momyn Mubina ta dago kanta cikin mamaki tana kallon Momy kana ta mayar da kallonta kan Maryam wacce sukayi kafada da kafada da Momy cikin zuciyarta tace wato ita ce ta dauko ta ma lallai yarinyar tana da fada a gurin Momy




Sai ta hau yaqen karya tana danne abinda yake zuciyarta kamar gaske tace"Masha Allahu haka yayi, bari mu bude part din Mubina sai mu shiga ciki tunda dai ita ce uwargida"




"To babu matsala"
Momy tafada cikin nutsuwa da dattako





Hajiya Abu ta kauce daga gurin cikin dinbun mamaki dole sai sun zage damtse kan Hajiya Aminatu in ba haka ba burinsu baxai cika ba a kan Nasiru dole ne su ci arzigi su bar arziqi a mazauninsa.
[11/06/2019 7:49 AM] Binta Umar Abbale: Momy taja tsaki abinda ba halinta ba tace"wallahi wasu mutanen suna bani mamaki wai sai mutum yazo ya tadda mutane a guri ya kasa gaidashi sabida girman kai Allah ya kyauta"




Ya Rabi tayi murmushi tace"Hajiya kenan aiko mutane kowa da irinshi sai hakuri"



"Allah ya sawaqe ameen"
Momy tafada tana kara kiran wayar Nasir din a karo na biyu
Gashi tana ring bai daga ba Momy jikinta ya bata babu lafiya amma ta barwa zuciyarta addu'a kawai take masa




Hajiya Abu ta dawo gurin a karo na biyu tace"Hajiya Bisimilah"
Dukkaninsu suka rufa mata baya




Farlo a cike sai hayaniya suke Momy ta nufi wani bedrom dake falon tace"a shigo mata da Mubina




Nan Hajiya Abu ta kamo Hannun Mubina wacce ke cikin kawayenta sai shewa sukeyi

Kwata-kwata babu kunya irin ta amare a tare da ita fuskarta tasha kwalliya kamar me ga wani uban gashin ido da tsa in ta kalleka tamkar wata aljana mayafin dake jikinta ma figigi ne sai taunar jingam takeyi abun dai babu arziqi






Cikin nutsuwa Momy take binta da kallo tana nazarinta tabbas Mubina bata da da'a ko kadan tana zaune kan kujera har da Dora kafada daya kan daya babu abinda ya dameta





Momy ta sauke ajiyar zuciya tace"Mubina sauko kasa ki zauna kusa da "yar uwarki"




Sai da ta bata lokaci sannan ta sakko kasa tana wani ya mutse-ya mutse





"Alhmdullhi Allah kai ne abin godiya daka nuna min wannan rana da raina da lafiyata"
Momy tafada tana sauke ajiyar zuciya ta cigaba da cewa "Mubina ga kanwarki Maryam a matsayinki na babba wacce kika darata shekaru da hankali ga amanarta na baki a matsayinta na "yar uwarki domin bazan kirata kishiyar ki ba sabida banason kuyi zaman kishi ke da ita, inaso Ku zauna da juna tamkar "yan uwan juna, nasan Maryam yarinya ce Mara hayaniya in kika rike girmanki da kambunki na uwar gida zakiji dadin zama da ita"





"Ke kuma Maryam ki dauki Mubina matsayin "yar uwarki kada kiyi kuskure ta yi miki gyara kiyi mata rashin kunya duk da nasan ba halinki bane yi nayi bari na bari kinga Mubina ta girme ki nesa ba kusa ba , da shi kanshi Wanda ya ajeku, sabida haka ki bata girmanta, Ku zauna lafiya don Allah in kukayi haka kungama burgeni sabida zaku kwantar da hankalin gudan jinana wato Nasir gashinan na damka muka amanarsa Ku kulamin dashi"






"Momy duk abinda kikice naji insha'Allah zanyi kokarin bin maganarki"
Maryam tafada kanta a sunkuye




Mubina ko sai da tagama yangarta sannan tana tabe baki tace"Momy duk naji abinda kikace ni mutukar mutum bai shiga hurumina ba to babu ruwana dashi sannan Momy ki jawa Nasir kunne bana son rainin hankali mutukar yana son zaman lafiya a gidanshi to ya rika bani girmana"





Cikin mamaki Momy tace"ya baki girma ko ki bashi girma, ai yanzu sai dai ke ki bashi girma tunda a karkashinsa kike kuma duk inda namiji yake komai kankantarshi to babbane ko dako ka girmeshi, in na fahimci abinda kikeso kice kinaso kice min kinaso Nasir ya mutun taki ko a matsayinki na wacce ta darashi shekaru
[12/06, 14:48] +234 808 996 5176: [11/06/2019 10:31 PM] Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*116*

shiru tayi kawai bata kara tankawa Momyn ba, amma ta kudurta a ranta ba zata zauna tana ji tana gani Nasir yana rai na mata hankali dole zata zage ta kwaci "yan cinta a matsayinta na babbar yarinya mai aji da wayewa

Momy ta cigaba da yi musu nasiha mai ratsa jiki daga bisani ta ce su maida Mubina dakinta, itama Maryam din nata part din zata mikata

Haka dai suka mike duk jikinsu babu kwari danginsu Mubina ganin babu fuska gurin Momy




Suna fita harabar gidan Momy takara kiran wayarshi a karo na uku tana mamakin dalilin da ya hanashi daukar wayarta



Sai da takusa tsinkewa sannan ya daga gami da yin sallama




Momy ta sauke ajiyar zuciya tace"Myson kai ko ina ka buyu tuntuni ina Kiran waya shiru kaqi dagawa"




Numfashi ya sauke yace"Afuwa Momyna wallahi miting muka shiga shiyasa kika ji ni shiru amma gani kan hanya"



"Aa mukan baza mu tsaya jiran isowarka ba Wallahi tun dazu muna waje tsaye da yarinyar nan kabi ka kulle duk part din, ko ina kakeso mu ajeta oho maka"




Ganin yadda Momynshi ta harzuqa da yawa yasa yace"sorry Momah nawa part din a bude yake Ku ajeta a can dazu mantawa nayi lokacin da nashigo ban baki key din part din nata ba wallahi sai da naje gurin Mubina sannan nagani, lokacin kuma na makara mutane na ta jirana"




Momy ranta yayi fati ganin yadda ya karbi abun tace"ai ya huce Myson amma da rai na ya baci wallahi"



Dariya yayi kawai yace" Momy Allah ya huci zuciyarki"


"Ai na hakura"tafada cikin farin ciki, ta cigaba da cewa" kace part dinka a bude yake ko"?




"E akwai key a jikin kofar da manta ban cire ba, amma bedroom dina a rufe yake"




"Ok babu Matsala my son zamu ajeta nan amma don Allah ka dawo gida da wuri"





"Insha Allahu Momyna"


Momy ta kashe wayar tana kallonsu Ya Rabi tace"kuyi haukri dan Allah ni nasan dama akwai abinda ya tsareshi, yanzu zamu ajeta s part dinshi kafin yadawo ya bude mata nata"




"Haba Hajiya ai babu komai Maryam matar Nasir ce yana da iko da ita, mu duk inda zai ajeta bamu da horomi da zamu hanashi burinmu kawai yarinyarmu ta zauna lafiya gidan Mijinta"
Hajiya Aishatu tafada tana gyarawa Maryam din lulllubin mayafinta.
[11/06/2019 10:54 PM] Binta Umar Abbale: Kai tsaye part din Nasir suka nufa da Maryam,
Momy ce a kan gaba, duk wannan turka turka dake faruwa Maryam naji shiru kawai tayi sabida tasan sabida ya tozarta ta yayi mata haka zai ce wai ya manta da key tasan rashin mutumci ne kawai, yasa ya barta a waje tsawon a wa guda a matsayinta na amarya

Wani irin sanyi-sanyi da dadin kamshi ne ya ziyarci lokacin da Momyn tabude falo nan Nasir kafafunsu suka lume cikin wani haddadan kafet Wanda ni kaina ban taba ganin irinshi ba , komai na falon Milk ne hatta da kujerun da suke kewaye a falon kayan kawa da more rayuwa babu abinda babu ko ina ka kalla haske da walwali ne yake tashi



Momy ta zaunar da Maryam a kujera sannan ta zauna kusa da ita gami da dafa kafadarta



Maryam kuwa gabanta ne yake dukan uku-uku domin tunda aka fara lamarin bata tabajin fargaba da tashin hankali ba kamar na yanzu, innalilahi kawai take maimaitawa




Momy tace"ki kwantar da hankalinki Dota ki zauna nan kafin yadawo ya bude miki naki gurin ina fatan dukkanin nasihar da nayi miki kin riketa"




Daga kai tayi kawai tana kokarin danne kukan da yakeso ya kufce mata



Momy ta mike tsaye suma suka mike da nufin tafiya Yaya Rabi tace"zamu tafi Allah ya Baku zaman lafiya"




Maryam ta fashe da kuka ta sauko daga kan kujerar ta riqe kafafun Ya Rabi da kyau tana kuka


Da kyar Momy ta raba kafar da hannunta suka fice suka barta dur kushe a gurin tana kuka tamkar wata Mara galihu
[12/06, 14:48] +234 808 996 5176: [12/06/2019 9:33 AM] Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*117*

kuka Maryam take sosai na tausayin kanta sabida batasan wace irin rayuwa zatayi da mutumin da baya kaunarta baya kaunar ya bude ido yayi tozali da ita



Tafi rabin a wa zaune a gurin sannan ta mike ta koma kan kujera ta zauna gami da lullube jikinta da mayafinta har kafafunta yanzu tsoran falon takeyi duk da cewar ko ina ta kalla haske ne tar wai



Ashe duk wannan abun dake faruwa a idan Mubina domin ta window din dakinta babu abinda bata gani ba, harsu Momy suka fito daga part din Nasir din akan idonta, kawayenta kafin su tafi sai da su gama tunzurata kan taje taci mutumcin Maryam din kafin angon nasu ya dawo ai ita yafi kamata a kaita part dinsa tunda itace uwargida, sabida haka cikin sauri tayi Wanka ta kimtsa cikin wasu "yan iskan kayan bacci tafito daga part din nata kai tsaye part din Nasir ya ta nufa




Maryam na qudun dune cikin kujera takasayin kwakwkwaran motsi sabida tsabar tsoran da takeji sai taji ana kokarin bude kofar dakin



Gabanta ya rinka faduwa duk a zatonta Nasir ne , cikin zuciyarta tace"ko da wane wulakanci ya shigo min"



Kawai sai taga inuwar mutum a tsaye a kanta


A furgice ta mike zaune tana kallon Mubina cikin tsananin tsoro da faduwar gaba




Mubina tayi mata wani dan iskan kallo tace"ke "yar gidan fukara'u "yar gidan mai gadi mai dattin hula to masu gadon mayyata, karuwa mutsiya ciya "yar iska, wato har kin samu filin da zaki mike kafa ki kwanta kan kujera kina bacci ko"?




Maryam zuciyarta ta dinga bugawa zata iya jurar komai amma banda zagin iyayenta



Ta yunkura zata mike kenan Mubina ta kwashe ta tafadi kasa rigib tace"wato ina miki magana kin mayar dani "yar iska har yaushe matsayinki ya kai haka"




Cikin zafi zuciya Maryam ta mike ta kai wa Muniba wani ba hagon mari Wanda ya dauke mata hankali na wucin gadi




Kafin Mubina ta dawo hayyacinta Maryam ta nufi kofar fita da sauri, suka ci karo dashi ya shigo tayi saurin kaucewa tana kallonshi, shima ita yake kallon Na tsawon minti biyu kana ya mayar da hankalinshi kan Mubina dake tsaye tsakiyar falo hannunta dafe da kumcita sai numfarfashi takeyi




Ganin yana kokarin shigewa ciki batare da ya tankawa kowa ba yasa Mubina tarar gabanshi tana matso kwalla har yanxu hannuta na dafe a kumcinta



Maryam kuwa bude kofar falon tayi tayi ficewarta gwara ta kwana a waje kan ta kwana a gurinshi domin bata San wace irin musiba ce zata biyo baya ba
[12/06/2019 9:46 AM] Binta Umar Abbale: Cikin kukan kissa Mubina tace"Nasir kaga dalilin da yasa nace bazan zauna gida daya da matarka ba ko, sabida nasan bata da mutumci yanzu kamar ni zata tsinkawa Mari daga gaya mata gaskiya"




Kallonta yayi cike da mamaki yace"ke mai ya kawoki nan ina ce Na baku mukuli ko"?



"Yaya baza ka ganni ba dawa a kafara daura maka aure ne"?
Tafada tana tsareshi da ido har da rike qugu


Tsaki yaja yace"ban sani ba shashasha kawai kina girma kina cin kasa"
Ya wuce bedroom dinshi


Tarar gabanshi tayi tace " ni

1 Comments On YARO DA KUDI
avatar
magaji-2

1 year ago

Reply

Allah Yakara budi

Please Login or Register in order to submit comment