Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haushine duk da gurin ajiyarsu suke mirrow dinshi kaca kaca turarurruka ne masu Dan karan tsada a zube a gurin gami da mayuka sun fi kala a shirin wasu har sun fado kasa,



Toilet din tabude ta shiga ,Wai Abin sai a hankali da'alama tunda ya tafi Momy ba sosai take sawa a gyara dakin ba domin bacin da yayi,, yayi yawa gajerun wando nane sunfi kala goma gasu Nan a zube cikin Abin Tara wanki da'Alama kullum sai ya balle sabo ganin ledodinsu a gurin ,



Nan da Nan ta Tara ruwa tafara Aikin toilet din tsaf ta'hada kayan wanki dasuke gurin ,kananun kayan kuwa ta zuba su cikin ijin wanki ta kunna shi ,sannan ta ciga da Aikinta ,duk wasu tarkacan su gwangwanin turarurrukan Wanka gami da kwalayen sabulai da sauransu sai da takwashe tsaf cikin wani katon duzbin' tafito dashi can harabar gidan,



Ta koma ta matse kayan da ta zuba cikin Abin wanki ta shanyasu tsaff jikin hangar dake manne a toilet din ,takashe injin,gami da qara wanke toilet din tas sai da ta tabbatar da yayi mata yadda take so sannan tafito tafara Aikin bedroom din cikin Nutsuwar ta


Hijab din jikinta ta cire ganin yana hana ya Aiki kafin ta Ankara tafara jin kiran sallah magariba Cikin sauri ta karasa shimfida bed shirt din ta jera fililon kan tsaff ta karasa kan Mirrow din tafara gyara ka yayyakin dake Kai tsaf ta jere su gwanin sha'awa ta share dakin Tass tafitar da duk wani Abu Mara muhimanci gurin takalmanshi ma tsaff ta gyara masa dakin sai fitar da wani irin qamshi yake mai dadi ,Cikin sauri tafito farlaur din hannunta riqe da wata katuwar Leda da ta zuba tarkacan da ta sharo a dakin ,shaf ta manta da hijab din ta a dakin sabida yadda take sauri kar ta rasa Sallahr magari ba Dan gaskiya maryam bata qara'i Lokacin sallah nayi take gabatar da ita Allah ya huwace mata wannan,
*Allah kasamu a danshinta*


Turus tayi gabanta yana wani mugun duka ,ganin su da tayi a zaune su hudu da Alama shigowarsu kenan Dan ko Alama bataji shigowarsu ba,Nasir ya na kokarin bude dakin suka buga karo,da'ita da sauri ya dago kai hannunshi dafe da goshin Cikin Mamaki yaga Maryam tsaye ta zuba masa idanunta Wanda ya tsana a rayuwarshi,


Da mugun sauri ya koma da baya yana sakin ajiyar zuciya domin ya zata mafarki yakeyi Wanda ya sabayi nata duk daran duniya,yafara nunata da hannu bakinshi na rawa yaga za furta ko kalma daya,


Ganin Abinda yakeyi yasa tace Auncle nice Maryam fa Momy CE tace in zo in gyara maka shashinka yanzu na gyara maka ciki nan nakeso in gyara a nutse take maganar,



Anwar!! Anwar!! Ya kwala masa kira Cikin mugun bacin rai!!



Da sauri Anwar ya karaso gurin ,yace kai A boy wannan kira haka kaifa dadi na dakai a kwai takurawa wallah.... Kafin ya karasa idonshi yayi tozali da Maryam tsaye jikin kofar dakin nasir kanta a sunkuye tana wasa da hannuta ,bata son kallon Nasir ganin irin wulakantancan kallon da yakeyi mata,
Gashi babu hijab a jikinta a takure ta ke jinta,sai maqe jikinta takeyi jikin kofar,



Wani murmushi Anwar ya saki yana Sosa Kanshi sai wani kallon kurrula yakewa Maryam tamkar ya lasheta


Tsaki Nasir yaja ,yace ga tsuntsu daga sama ga tanan dama kana nemanta kaga ba sai kasha wahala ba yafada tana yi mata wani Dan iskan kallon raini ,cikin wata muguwar tsawa gami da kyara yace kauce min anan Fockyou mother fourkar!! yafada yana wani tsale tamkar zai kai mata duka,da sauri Maryam ta kauce ta bashi hanya jikinta yana kyarma ,ya zo ya wuce yana wani ya mutse fuska tamkar yaga kashi ,ya kakalo yawo ya taufa mata ajiki ya shige dakin gami da banko kofa,



Jikin kofar ta makale tana takure jikinta ganin yadda Anwar ya ke kusantar ta yana kokarin Rungumeta,



*✍🏻,,,,,,,*
[16/03, 07:01] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—
*YARO DA KUDI*
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸŽ—πŸŽ—



*✍🏻WRITTEN BY*
~*Binta umar*~
~*MAMAN ABDUL WAHABU*~


~*MRS AHAMAD GWADABE*~



~*DEDIGATED TO: MY FAN'S*~



*πŸ…Ώ29*




Ya karaso daf da ita yana mata wani kallo irin nasu na "yan duniya sai lasar baki yake yi tamkar wani tsuhon maye,



Hannunta ya kama ya riqe cikin nashi yace baby kin hadu fa wallahi babu karya ina son ki kina so na kema? Yafada yana kanne mata ido daya,

Kauda kan ta tariqa yai ganin fuskarsa dab da tata ,tayi shiru bata ce komai kokarin ta kawai yadda zata gudu daga hannun waddanan Azzaliman,



Sai yafara hade ta da jikin kofar dakin Nasir din da take makale ya sanya hannuwanshi duk biyun yana lalubarta, Bige hannun tayi tana kokarin fashewa da kuka,ya kara mai da hannunshi jikinta a karo na biyu



Sai tafashe da kuka cikin kuka" tace Uncle ka fito ka tai make ni zai keta min haddi ni back"yar iska bace"



Kafin ta rufe bakinta suka fadi rigib! Ita da Anwar din sakamakon bude kofar da Nasir yayi babu zato ,



Tana kan ruwan cikin Anwar din tana kokarin tashi daga kansa yayi da shi kuma ya sanya duk hannuwanshi biyun ya ruqunqume ta kam!




Tamkar wani Dan dambe haka Nasir yayi kansu a hautsi ne ya daki kafar Anwar da wani mitsayacin takalmi mai ta yoyi da yasanya a kafarshi yanzu domin Wanka ya sakeyi gami da sake wani dressing din domin sake fita,



Ya San ya hannusa guda ya dauke Maryam daga kan Anwar din yana zaginta da turanci ya fidda hannu ya dinga gaura mata tafi tamkar Wanda Allah ya Aiko shi,



A kasalance Anwar ya mike yana kokarin kwatar maryam daga Hanunsa, Ya kai masa wani kutofo,yayi taga taga zai fadi ya tsaya da kafaunsa



Da sauri Abbas da Abdul latif wadanda kecan falo suka karasa gurin domin hayaniyar da sukaji kadan daga can bedroom din Nasir Dan a zatonsu ma ko fada ne ya hautsine a tsakaninsu su biyun.


Ya kara daga hannunsa zai kara kai mata mari Abdul latif ya riqe hannun yana masa wani irin kallo,

Bai ce komai ba ya mai da idonshi kan Maryam dake takure idon ta na zubar da hawaye,


Fizge hannusa yayi yace da Allah malam sakar min hannu wannan "yar iskar yarinyar ni zata nuna wa iskanci Dan Ubanta a dakina za ta kwanta a jikin wannan Dan iskan yafada yana nuna Anwar dake zaune da jiki a mace domin ya Riga yagama kwadaituwa da yarinyar,


Cikin mamaki Abdul ya maida idonshi kan maryam a karo na biyu ,yace" Maryam mai yakawo ki dakin nan ina kuma hijab din ki?



Cikin kuka tace Momy ce tace nazo na sharewa Ancle dakinshi nayi masa gyaragare wallahi,


Ajiyar zuciya ya sauke yace "zo ki wuce ki tafi kin ji ko" dakin Nasir din tayi niyar komawa domin dauko hijab din ta,


A zabure! Yayi kan ta yana mata wulakantacan kallo ,ya tsare kofar dakin ,"yace get Out" joya wa tayi da nufin tafiya Abdul ya dakatar da ita ,ya kalli Nasir da rai a bace yace wallahi baza ta fita a haka na mahaifinta na waje a zaune Sam bai dace ba hakan"



Tsaki Nasir yaja ya shige dakinsa


Anwar yace"wai kai ina ruwanka da yarinyar ne malam naga fa kana min shishshigi a kanta wai ko son ta kake yi ne iyi ,Wallahi tunda na kwadaita da ita sai na biyawa kaina bukata ko ta halin yaya ne kai dai kafi kowa sanin halina"


Karaf! A kunne Nasir lokacin da yake fitowa daga dakin sa hijab din Maryam a qasa yana ja wai bazai dauko da hannunshi ba,
Gabanshi ne yafadi jin Furucin Anwar yariga yasan halin sa ciki da waje tamkar maye yake gurin mace zai iyayin komai a kanta Dan ta wani fanni na yafishi son mata tunda shi ba kowace mace yake kwanciya da'ita bah'


Ba Dan komai ya hana Anwar cika burin sa ba a yanzu sai Dan in ya tuno da hallacin da Uwar yarinyar tayi masa ,bazai taba cutar da jinin Aunty shi ba zai bari a cuceta ba yarinyar taci darajar malam Ya'u da Aunty shi ,Amma da badan haka ba a gabanshi zai sa Anwar ya yagalgala masa ita wallahi sabida tsabar haushin da take bashi taqi fita daga rayuwarsa kullum ya kwanta sai tazo masa cikin baccinsa ta ida nunta masu ban tsoro a cewar sa ,shine dalilin da yake ganin anya Aunty shi ba mayya ta haifa ba ,tunda shi maye ruwansa da ita,



Da sauri Abdul yaje ya cire hijab din daga kasan kafar Nasir din ya mika mata yace"maza ki sa kinji ko kiyi tafiyarki Allah ya saka miki"



Da sauri ta karbi hijab din hannuta na rawa ta zira tayi hanyar fita daga dakin tana Addu'ar Neman tsari gami da godewa Allah da ya tsareta daga sharrin su Nasir





*✍🏻,,,,,,,,*
[18/03, 13:49] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?



πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—
*🐾YARO DA KUDI*🐾
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—


*✍🏻WRITTEN BY*
_*Binta Umar*_
~*Maman Abdul Wahabu*~



~*Mrs Ahamad gwadaba*~




_*WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE NAIRA DARI BIYU KACAL IN KANA BUKATAR CIGABANSHI SAI KA TUNTUBI WANNAN NUMBAR*_
08089965176



~*DEDIGATED TO MY FAN'S*~😍


*πŸ…Ώ30*




Abdul latif ya daura idonsa kan Nasir bayan fitar Maryam Ransa A mugun bace yac" yanzu kai Nasir da kai za'a hada baki gurin cutar yarinyar can hakan da kukeyi yayi daidai kenan Abinda kuke a waje shine za kuzo gida kuyi mai Maryam tayi maka ? Yarinyar da take bala'in tsoranka wane irin Abu Aunty tayi maka zaka saka mata da haka"? Ya karashe ya Maganar yana sauke ajiyar zuciya cikin tsantsan bacin rai!!




Wani kallon banza Nasir yayi masa yana ya mutse fuska cikin izgili yace" kai karfa ka kawo min maganar banza mana ,Kai meye ruwanka da ita lokacin da kashigo A kai na kaga yarinyar da zaka daura min jakar tsaba ,mai zanyi da'ita ,Aba sai kace zabiya Mtssss! Sam Sam Allah ya tsareni ita Dan Uwarta mai yakawo ta dakina anan fa naganta har da tube hijab tamkar tana dakin Uwarta" ya karashe maganar yana wani zakuda kafada Alamar babu Abinda ya dameshi,



Dauke kansa yayi daga kan Nasir din cikin bacin rai har ila yau jin irin Furucin da yakeyi Lallai Nasir yayi Nisa!



Ya kalli su Anwar yana girgiza kai yace "Wallahi mutukar Wani Abu ya samu yarinyar nan ta dalilinku sai nayi Shara'a da Ku A kanta , kai ne mai furucin ko ta halin kaka sai ka kauda kwadayinka a kan ta ,yafada yana kallon Anwar,yaci gaba da cewa Wallahi duk in da zanshiga in fita zan shiga a kan in Daukar mata fansa.

Wani kallon banza Anwar yayiwa Abdul din yace"Kai ka isa ka hanani ae kata Abinda nayi niyya A kan waccan yarinyar Mara galihu "yar mai gadi da har kak e wani tada jijiyar wuya a kai kai a suwa Kai din banza" ya karashe maganar yana furzar da wani huci mai daci Aba kinshi,


Girgiza kai Abdul yayi yana binsu da kallo daya bayan daya ,ya kalli Anwar din A karo na biyu ganin yadda ya zaqe da yawa har yake wani rantse rantse gami da cin Alwashi a kan Maryam din Tabbas idan wani Abu ya same ta Wallahi Anwar sai ya gane bashi da wayo

Yace"OK toum tunda ka rantse ae ga fili nan ga mai doki sai ka bada himma tanan ni kuma zaka San ka tabowa kanka Abinda baza ka iya ba kana maganar Maryam bata da gata to tana da gatan Allah dani in sha'Allahu Allah zai tsareta daga sharrinku ,kai kuma Nasir ya fada yana nunashi da hannu yace "wallahi duk Abinda ya samu Maryam ka tabbata babu rufin Asiri dady sai yaji domin kanajin furucin wannan Mara mutuncin a kanta kayi shiru wato kabashi goyan baya kenan ko mai yarinyar nan tayi maka da kayi mata wannan tsanar da har zaka bada hadin kai gurin cutar da ita, nafada na kara maimaitawa kar Ku batawa yarinyar nan rayuw.....


Kai! Arrama da kata mana Dan Allah ya isa haka" Abbas yafada Wanda tun zamansa a gurin bai ce uffan ba ,sai yanzu


Ya gyara zama gami da zakuda kafada ,yaci gaba dacewa,Ubanmu ne kai wai da zaka titsiye mu kana zagi ina Ruwanka da duk Abinda zamuyi Rayuwarka ko tamu ,Malam kar kasake kawo mana maganar banza yarinyar daka ke wani tada jijiyar Wuya A kanta kana da Alaqa da ita ne kai idan baza kayi ba sai ka hanamu kai baka isa ba Wallahi
Kaii!! Kauce Malam!! Yafada A Fusace!


Tsaki Nasir yaja yana duba Wani Dan kareren agogo a daure a hannunshi bakwai shaura na Magariba Ya kalli su Abbas din yace "guys Ku tashi mu ware Ku rabuda wancan Komai Allah yace Annabi yace ko wa zai gayawa sanin Allah oho,"



Cikin Mutukar bacin rai Abdul ya fuce daga dakin yana Allah wadai da tur da wannan dabi'ar da Abokannanshi "yan Uwanshi suka jefa rayuwarsu ciki



Yana fita suka Kwashe da dariya gami da tafawa ,Nasir yace"ni narasa gane kan wancan gayan wallahi A kwai shiga Abinda babu ruwanka ko mai ya shafeshi da Lamarin yari yar oho"



Dariya Abbas yasa yace"mybe ko son ta yakeyi Dan ga Alamu nan sun bayyana"



Tabe baki Nasir yayi yace"tabbas da ya cika Dan Asara Wallahi yarasa wa zai so sai wancan yarinyar mai kama da ru66a66an tomatiri Allah ya sawaqe mai!!"


Dariya sukayi dukkaninsu gami da mikewa domin fita,Shima dariyar yasa yace"Wallahi nake gaya maka Ae irin su babu Abinda zakaji sunayi sai qarni in ka kusancesu Sam Sam yarinyar batayi ba yafada yana tabe baki,



Anwar yace"komai me takeyi sai na biya bukata ta a kanta Wallahi idan Uwar qarni ma takeyi bai da meni ba"



Gabanshi ne yafadi kadan ya Dan kalli Anwar din ta gefen ido ,jin Furucinsa har yanzu a kan Maryam din ,bai qara cewa komai ba har suka fice daga shashen gaba daya



Wata sabuwar mota suka shiga Nasir ya ware kida kamar yadda ya saba suka five daga gidan





*✍🏻,,,,,,,,,,*
[20/03, 02:30] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?


πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—
*🐾YARO DA KUDI*🐾
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—



*✍🏻WRITTEN BY*
~*Binta Umar*~
~*MAMAN ABDUL WAHABU*~


~*MRS AHAMAD GWADABE*~



_*WANNAN BOOK DIN NASIYARWA NE NAIRA DARI BIYU IN KANA BUKATAR CIGABANSHI SAI KA TUNTUBI WANNAN NUMBAR*_
08089965176



*DEDIGATED TO:MY FAN'S*😘



*πŸ…Ώ31*



Lokacin da Maryam ta fita daga dakin Nasir kai tsaye part din Mom ta nufa cikin Nutsuwarta tamkar babu Abinda ya faru.


Mom na kokarin hawa sama domin gabatar da sallah magariba ,sai ta dakata ganin shigowar Maryan din.


Cikin sakin Fuska tace" Maryam Kin gama ko?


Cikin Nutsuwarta kamar ko da yaushe tace"Eh Momy na nagama Farlour ne ban gyara ba sai gasu sunshigo game lokacin Sallar Magarb yayi zanje nayi Sallah".


Mom din ta gyara tsayuwarta tana kallon ta tace"ina fatan bai miki komai ba nasan Halin kayana"



Murmushi tayi kadan"tace Momy na kenan Mai zaiyi min Ancle din yace ne kawai in tafi tunda sun shigo "



"Daga haka fa" Momy tafada tana mata kallon tuhuma.


Sai ta duburburce tana tsoran kar Momyn ta Fahimci Abinda yafaru,yanzu gashi ita kuma qarya ba dabi'ar ta bace,


Kallon zargi Momyn take mata race"kifada min gaskiya daughter kinji ko"?


"Ok zo nan Muje sama Muyi sallah a nutse sai ki fada min"


Momyn tafada gami da karasowa inda take tsaye ta kama hannunta suka haura Sama inda dakunan su suke.


Bayan sun idar da sallahr ne Cikin Nutsuwa Mom din ta kalli Maryam tace"kifada min idan ya dake ki kamar yadda ya saba kinji doughater"


Shiru Maryam tayi tana wasa da hannunta.


Sai da Mom din takara Maimaita tambayar,sannan tace"Allah Momy babu Abinda yayi tafada A fili a zuciyarta tana Jan Istigifari.

Taci gaba da cewa ,Dama Dama Wannan Abokin nashi ne,sai tayi shiru takasa karasawa,


Ina jinki ya kikayi Shiru Momyn tafada"


Shine Yake kulani Momy nikuma bana so tafada kanta a kasa,


Momyn tace"To ae kina da gaskiya Mutuncin "ya mace tsare kanta babu ruwanki dashi ko ya kulaki ,gaisuwa kawai na lamunce kiyi dashi kinji ko kuma zanyiwa Nasir magana tunda ba kyaso tayi masa magana duk inda ya ganki Kar yakara shiga lamarinki"


Gabanta yafadi jin Abinda Momyn take fada,


Da sauri ta dago kai tace"A,a Momy ba sai kin yiwa Ancle maganar ba Dan Allah"


Harararta Momyn tayi kadan tace"ae dole in yi mishi magana yajawa Abokinshi kunne domin a kanki zan iya batawa dashi"


Sunkuyar da kai tayi tana Murmushi kadan tace"Dan Allah Momy mubar maganar bana so ki batawa Uncle rai"


Dariya Momyn tayi gami da Mikewa daga kan daddumar da sukayi sallah A kanta tace" in dai a kanki ne ran Nasir zai baci kuwa ,


Mikewa tayi ita ma tabi bayan Momyn suka sauka kasa ,a tare Maryam din na kokarin fita da niyar tafiya bangaransu Momyn ta dakatar da ita,tace Lallai sai ta tsaya sunci Abinci tare ,ba yadda ta iya haka ta bi bayan Momyn can dainnig in da kayan Abinci ke jere iri iri na haduwa na Alfarma,


Momyn ta hada Mata komai tsaf ,Cikin nutsuwa Maryam tafara cin Abincin suna hira da Momyn kadan kadan ,sai da Momy ta tabbatar da Maryam ta koshi sannan ta kyaleta ta tafi bangaransu.



Lokacin da tashiga shashin nasu Ana sallahr isha'i Aunty da su Nafi'u duk sallah suke ,sabida haka Alwala ta daura ita ma tabi sawun su.



Aunty na idarwa tafara hidimar Zubawa yara Abinci ,ta kalli Maryam dake zaune kan dadduma bayan ta idar da sallah tana Addu'a ,"kefa a zuba miki ? Nasan dai kinci gurin Momynki ko?


Daga kai Maryam tayi A nutse tace wallahi kuwa Aunty a koshe nake Amma da safe naci dumame dama yafi dadi"


Tabe baki Aunty tace Allah ya kaimu . mai kika tsaya yi a ne a can?




*✍🏻,,,,,,,*
[23/03, 00:15] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?


πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—
*YARO DA KUDI*
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—



*✍🏻writing By*
~*Binta Umar*~
~*Maman Abdul Wahabu*~

*MRS AHAMAD GWADABE*



_*WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE NAIRA DARI BIYU IN KANA BUKATAR CIGABANSHI SAI KA TUNTUBI WANNAN NUMBAR*_
08089965176



_INA MIKA SAKON TA'AZIYATA GA "YAN UWA DA IYALAN ALHJI RUFA'I GWADABE ,MUNA ADDU'AR ALLAH YAJI KANSHI YA GAFARTA MASA ALLAH YA YAFE MASA ALLAH YA KYAUTA TAMU BAYAN TASUπŸ‘πŸ»_



*πŸ…Ώ32*


Aunty Momy ce ta Sani gyaran dakin Ancle Maryam tafada cikin Nutsuwa.



Ayya to ae kin kyauta Aunty tafada.

Ancle din ma ya kwana biyu bai shigo min ba Aunty tafada tundai ranar da yadawo"



Ita dai Maryam bata ce komai ba domin Aunty bata son Laifin sa ko kadan.




****************

Karfe takwas saura na safiyar Litinin Maryam tsaf cikin Unporm dinta na Makaranta, Tana zaune gefen Babanta suna karyawa a gurguje ,ta kalli su Naf'iu tace "kuyi sauri Wallahi idan ba hakaba in tafiyata"



Ya Maryam ni dai naga Mutafi kawai Mubarshi tunda kullum sai yasa munmakara,


Duka Nafi'u ya kaiwa Miftahu jin Abinda yake cewa yace "bana hana yimin Rashin kunya ba"



Maryam tayi sauri ta riqe hannunsa tace "ai ba karya yayi maka ba ka dakeshi sai na rama masa"



Dariya Babansu yake musu yace"kai Miftahu kafiye tsokana kai kuma Nafiu sangirma kamar gyambo"


Aunty tace "Haka sukeyi si tayin koka ye kokayen shashanci"




Mikewa Maryam tayi tana gyara books din hannuta gamida da gyara jakarta tace"ai sai Ku tashi Mutafi ko"


Duk suka miqe a tare suna yiwa iyayen nasu Sallama.


Mi kewa Malam Ya'u yayi shima ya biyo bayansu Dan haka yake musu haka yake rakasu har kusa da makarantar sannan ya dawo gida dake makarantar babu nisa da gidan Alhji Huseen din.


Suna fitowa harabar gidan sosai Nasir ya fito daga part dinshi jikinshi sanye da kayan motsa jiki jikinshi a Murmurde ,sakin Fuska yayi lokacin da Idonshi yayi tozali dasu Nafi'u Yace "Morning My boys gami da dumqule hannusa kamar yadda yake musu ,Da sauri Nafi'u ya karaso yana dariya ya daki hannun Sosai yace"Morning Ancle katashi Lafiya"


Kalau Aboki na Nasir din yafada yana Jawo hannun Miftahu suna gaisawa,


Farin ciki ne ya Lullube Malam Ya'u yana tsaye Fuskarshi tamkar gonar auduga Dan dadi.



Nasir ya Mika masa hannu kamar ko da yaushe yace "Arrama Barka da Asubah"


"Barka kadai Nasiru katashi Lafiya"


"Lafiya Alhmdilahi"


Yace "kuzo in aje Ku a Skull din ko"

Yayi can inda motarshi take a je.


Ayya ai da ka barsu ma Nan makarantar tasu take bakin hanya"Malam Ya'u yafada



Ai fita zanyi Arrama Kawai su shigo na sauke su Nasir din yafada,
Ko gama rufe baki bai yi ba Miftahu yayi gaba dama yana kwadayin shiga Motar Ancle din.


Cikin sanyi Murya Maryam tace"Ancle ina kwana"?



Yanajin ta ya share ta,bata daddara ba ta kara maimaitawa,



Shiru yayi a karo na biyu yana kokarin bude mota Malam Ya'u yace' Maryam na gaishe da kai Nasir"



"Ok ya joyo Ya Dan kalli inda take yace" Lafiya Maryam yaya kike?


Dadi taji ganin yadda Ancle din ya Amsa gaisuwarta.



Tace"lafiya lau Ancle ,banza yayi da ita ya tada motar bayansu Nafiu sun shiga ko sauraron ta bai yi ba yafara kokarin tafiya.



Tace "Ancle ban shiga ba fa"


Wata harara yayi mata yaja tsaki kadan Dan ganin Malam Ya'u na gurin ya daka ta tashiga tukkuna sannan yaja motar



Malam Ya'u ya karasa bakin get din yana kokarin bude masa kofa,


Ya fice daga gidan.


Yana fita ya tsayar da Motar ya waigo yana kallonta A wulakance ,yace ke saukar min A mota"




*BINTA UMAR ABBALE*


_MARUBUCIYAR_

_*NANA KHADIJA*_

_*YARO DA KUDI*_

_*GIMBIYA BALARABA*_

πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šβœπŸ»
[26/03, 01:44] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—
*🐾YARO DA KUDI*🐾
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—


*✍🏻writteng by*
*Binta Umar*
~*MAMAN ABDUL WAHABU*~


~*MRS AHAMAD GWADABE*~



_WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE NAIRA DARI BIYU_
08089965176



*πŸ…Ώ33*



Diri diri cewa Maryam tayi jin Abinda yake cewa sai tasa masa ido tana kallo cikin tsoro!


Ya buga mata wata muguwar tsawa "get out nace kin tsaya kin sanya min ido shegiya Mayya mai kama da Aljanu kici kanki kurwa kurr!
Yafada A harzuqe!


Da sauri Maryam tabude murfin motar tafice tana jin wani mugun bakinci idan anyi duniya Dan Manzon Allah baza ta qara kula Uncle ba ko me za'ayi kuwa sai dai Aunty ta daketa a kan taqi kulashi.


Tana sauka ko sakon daya bai qara ba yafigi motarsa hade da bula mata kura! Jikin Unporm,



Wani hawayen bakin ciki ne yafara fita daga idonta tanayi tana karkade jikinta kana takama hanyar tafiya kamar yadda suka saba tunda dama skull din bawani nisa da gida.



Kan ta karasa skull tayi kokarin daina fitar hawayen Amma kana ganinta kasan tayi kuka sabida yadda idonta yayi ja!




Sukuku su nafi'u sukayi ganin Abinda Ancle yayiwa Yayarsu ,Miftahu yace "Uncle Yaya Maryam tayi maka Laifi ne?



Yana kokarin kunna kida kamar yadda yasaba yace"No" Babu Laifin da tayi min Abokina Kawai bana Ra'ayinta ne Na tsaneta!



Miftahi"yace Uncle mai tayi maka katsane ta mu kuma ba ka tsane mu ba?



Dariya yasa kadan yana mamakin tambayar kwakwa irin ta yaron yabashi hannu suka tafa yana dariya yace" Ai ba lallai sai mutum yayi ma laifi ba zakiji baka sonshi boy Yayarku tsoro take bani idan nakale ta tamkar Aljana"


Dariya Nafi'u ya qyalqyale dashi gami da dukan kafadar Nasir din sai kace wani sa'ansa yace"Lallai Aboki Yaya Maryam din ce Aljana duk kyawunta kaji kuwa yadda a skull a ke maganar kyanta A kwai Ancle Bash dinmu kullum sai yayi mata Magana bata kulashi bakaji yadda Abokai na suke cewa wai duk tafi mu kyau. Wai suna kama da wannan "yar india Ashwariya" idansu iri daya Dan Na Yaya Maryam din har yaso yafi na Aswariyyan blue,


Tabe baki Nasir yayi yana girgida kai Alamar yana jin dadin Music din dake fita kasa kasa cikin motar tasa yace"gaskiya waddan nan Friends din naka sun cuci Aswariyya da suka hadata da wan can tab!!
Da nasansu sai na Zane su da bulala domin sun batawa star ta kyawunta"

Yafada yayin da yakeyi parking. Daidai get din Makarantar.


Dariya Nafi'u yayi yana bude mota yace"to Uncle ko in kira makasu ne"

"Aa No" barsu kawai Zamu hadu ne wataran Amma kafada musu duk sanda muka gadu sai Na Zane su da kyau yafada Cikin sakin Fuska da barkwanci

Dariya yaran sukeyi suna kokarin daukar Lounch book din su Ancle din ya fito da wasu tarin Sweet masu bala'in tsada da dadi Dama ba ya rabo dasu cikin motar kasancewarsa ma'abocin son kayan zaqi ya basu yace"gashi nan kuje kura ba ko"


Cikin nutsuwa suka karba kana suka daga masa hannu suka nufi cikin makarantar,



Yana kokarin juya mota Maryam ta karaso jikinta a sanyaye ko kallon in da Motar take ba tai ba kai tsaye cikin Makarantar ta nufa,



Shi ma ya ganta yayi saurin dauke kai daga kanta gabansa na faduwa kadan bala'in jin haushin yarinyar yakeyi bai San meye dalili ba ,ko kadan bai tausaya mata ba tafiyar dasu kai suka barta.



Yaja Motarsa ya bar gurin Cikin Nishadi da'Alama yanajin dadin duniyar"





Tana Shiga cikin Makarantar Uncle bash ya tare kamar ko da yaushe,sai ta saki Fuska tace"Uncle ina kwana?
"Lafiya kalau habibty Yau kin Makara da yawa fa Yafada idonshi tsaye kanta ji yake tamkar ya lashe ta ya huta!



Dariya tayi kadan har dimful din ta ya motsa ,Abinda yake mutukar so kenan a gareta tace Uncle kenan kullum sai kace na makara dubi time fa takwas yanzu tayi tafada tana kallon Agogon hannunta,


Hannun yabi da kallo gami da kurawa fatar ta ido

1 Comments On YARO DA KUDI
avatar
magaji-2

1 year ago

Reply

Allah Yakara budi

Please Login or Register in order to submit comment