Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jin yadda mukayi da arrama ko"?

"Eh Momy inaji"

"Owk to yanzu kai mai zaka ce"?

"Momy mai zance kuwa ,ni banason takurawa mutum dama shine ya ga zai'iya ko yau ya bar aiki zan samu get man, karki damu zan fitar da kudi in bashi hakkinshi,kuma dukkanin dawainiyar da ake mishi ba za'a fasa ,sai dai in shine yace" baya bukata"


"Haka yayi Allah yayi maka albarka"

"Ameen" Nasir yace ya mike bayan ya gama karyawa yana duba agogo yace"Momy zan fita kuma inaji sai dare zan shigo"

"To Allah ya tsare"

"Ameen Momyna"
Yafada yana kokarin fita



Kai tsaye motarshi ya nufa

Maryam na tsaye kusa da Baban gida dake zaune kan bainci ,jiki yayi karfi ,sai tsokanarsa takeyi, ta hangi fitowar Nasir gabanta ya yanke ya fadi ,sai tayi saurin dauke kanta ta cigaba da magana da Baban gida amma duk da haka gabanta sai dukan uku-uku yake ,sabida yadda taga Uncle din yayi mata wani mugun kyau gaskiya kayan sun mishi kyau sosai
[27/05/2019 6:55 PM] ®Binta Umar Abbale: Gashi Malam baya guri ga get a rufe, ga Nasir ya tawo da mota zai fita yaya kenan"?

Baban gida ya mike cikin rashin qarfin jiki yafara kokarin bude get din,


Maryam tayi sauri ta dakatar dashi ta hanyar mayar dashi ta zaunar kan bainci tace"haba tsoho jikinka babu qwari ina kai ina iya bude kofa,ka kyalemu mu masu jini a jika, tafada tana dariya
Shima dariyar tayi yace"kaji ja'ira kamar wacce zata iya"




Kai tsaye gat din ta nufa cikin karsashi gami da jarumta tafara kici-kicin budewa,


Nasir tun kafin ya karaso ya hange ta tana kokarin budewa

Tsaki yaja kawai yana dariya domin shi dariya ma yarinyar tabashi gaskiya yana ganin karfin halinta


Sai ya tsayar da motar gami da zuge glass din ta zuro kanshi dai-dai sai tin da Baban gida yake zaune yace" Baban gida barka da asubah"

Baban gida ya fara kokarin mikewa yana amsawa Nasir yace"ba sai ka tashi ba ma, yaya karfi jiki"

"Alhmdullhi Nasiru Allah yayi maka albarka,ya jikan alh Huseen ameen"


Nasir yace"ameen ameen" ya mayar da glass din motar yana dannawa Maryam Hon wacce ta hakikance tana faman tura get amma kamar wacce take tura dutse kwata-kwata yaki motsi ,sai gumi take yankawa.


Dariya kamar ta kashe Nasir a cikin mota ,yana sane yake ta faman danna Hon babu ji babu gani


Maryam ta juyo a fusace tana danna masa harara taja tsaki ta cigaba da abinda takeyi,shiko yana ganin abinda tayi sai ya kara danna hon da karfin gaske
Ya bude motar ya fito a fusace, ya nufi gurin , yana zuwa kawai ya buge hannunta daga jikin get din yace"dallah matsa mana a guri kinsan baza ki'iya budewa kika batawa mutane lokaci idoit"

Maryam jikinta a sanyaye ta dinga kallonshi tana galla masa harara sai haki takeyi tsabar gajiyar da tayi ga hannuwanta sunyi ja sabida yadda take tura kofar abinka da farar fata ,tafin hannun yayi jajazir, a fusace ta wuceshi taje ta zauna kusa da Baban gida ,duk da haka bata fasa hararsa ba


Ja da yayiwa get din duk irin raurinsa da nauyinshi kuwa ,ya bude nan take, sai a lokacin Malam Ya'u ya karaso gurin, Nasir wuce yaje ya shiga motarshi ya fita daga gidan ranshi a bace yace"ai ko ka bar aiki ko baka bari ba dole in samu wani Wanda zai dinga kula da aikinshi"
[06/06, 01:47] +234 808 996 5176: [28/05/2019 10:06 AM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*94*

Baban gida ya rika yiwa Maryam dariya bayan Nasir din ya fita,yace"kin cika raguwa da kika kasa bude kofar can, nasan inda Nafi'u nasa ko Miftahu da tuni sun bude, ke kin tsaya shirme dube ki sai nishi kikeyi kamar wacce tayi aikin karfi"

Itama dariya tasa tace"wallahi kuwa na dauka zan iya budewa ashe akin babba ne ,dubi hannun fa"tafada tana nuna masa tafin hannunta, dariya kawai yake mata har Malam Ya'u yazo ya zauna a gurin,
Yace "dazu naje na samu Hajiya nafada mata halin da ake ciki"
Baban gida yace"ai haka yafi gwara tasan komai da wuri"

Hakadai suka zauna suna tattauna maganar,

Maryam ta mike ta shiga gida tanajin wani farin ciki a zuciyarta ganin zata dai na rayuwa a karkashin wani Wanda bai San darajar Dan Adam ba.


*****

Bangaran su Abdul latif kuwa lokacin da mahaifiyarsa taji abinda yake faruwa daga bakin Alh Hassan wato mahaifin abdul cewar Dan uwanshi bar wassiyar ko bayan babu ranshi a daura auran Abdul da Maryam, sai tayi tsalle ta dire tace"wallahi bata yadda ba danta bazai auri , wa"yanda ba'a san asalinsu ba ba'san daga inda suka fito ba sabuda haka indai ita ce ta haifi Abdul to bata amince ba"



Alh Hassan yace"dama bama bukatar ki amince ,dole zan cikawa dan uwana burinshi kafin ya mutu"

Rikici a ke sosai akan maganar inda Hajiya Zulai taja tunga tace bata amince ba,shi kuma yace babu abinda zai fasa

Abdul ma yaji duk halin da ake ciki ,to duk da haka yana nan a kan bakanshi sai tausar zuciyar Mahaifiyar tasa yake


Hajiya Zulai kuwa sai zugata akeyi cewar yarinyar "yar iska ce ,sabida kwanaki ma an nemeta anrasa
[28/05/2019 12:11 PM] ®Binta Umar Abbale: Sabida haka ta tada hankalinta a kan maganar, tace ita bada yawunta za'ayi wannan aure ba.



Misalin sha daya da rabi na dare Nasir ya shigo gida ,Malam Ya'u na zaune a bakin get har yanzu bai shiga gida ba sabida Nasir bai shigo ba har yanzu radio ce a hannusa yana sauraron tashar Ballo Dandago wato radio Kano kenan

Da sauri ya aje radio ya mike ya je ya budewa Nasir get, ya shigo da motar.

Yayi parking ya fito , kai tsaye bakin get din ya nufa Inda Malam Ya'u yake yana kokarin mayar da kofar ya rufe.


Muryarshi Sama-sama yace"Arrama ina son magana da kai"

Malam ya juyo da sauri Dan bai tsammaci zuwanshi gurin ba


Yace"to to ai babu matsala Nasiru ina sauraronka

Nasir ya gyara tsayuwa sosai yana kallonsa yace"dazu Momy take fadamin maganar da kukayi da ita, cewar zaka bar aiki a gidan nan ko"?

Cikin mamaki Malam ya dago kai yana kallon Nasir din yana Mamakin yadda ya tsareshi da tambaya sai kace wani ubanshi,lallai Yaron yana ji da izza, amma sabida dattako irin na Ya'u sai yace"kwarai kuwa Nasiru inaso in fara kasuwanci ne"


"Owk yanzu tsawon shekaru nawa kayi a gidan nan kana aiki ,inaso in biyaka hakki kane kamar yadda shari'a tace"
Nasir yafadi maganar kai tsaye kuma da'alama haka abin yake har cikin zuciyarsa


Cikin dumbun mamaki gami da al'ajabi Malam yake kallon Nasir din, ya nuffasa gami da cewa"kayi gaskiya Nasiru ni tun lokacin da marigayi ya dauke ni aiki a gidan nan ba muyi dashi zai biyani domin ba nai masa gadi Dan ya biyani komai sabida haka babu wannan maganar a tsakanina dashi har ya koma ga Allah"


Nasir ya sauke a jiyar zuciya, yace" ai nasan da haka, yanzu dai nine maigidan, kamar yadda zan je in dauko wani get man din in biya shi hakkinshi ya zama dole in baka hakkin ka"


Arrama yace"bana bukatar komai Nasiru nagode sosai da kulawa"

Nasir ya bude Jakar dake hannusa ya fito da kudi kimanin dubu dari biyar yace"ga wannan ka rike ka hada dasu gurin yin bussines din naka , Allah ya taimaka"


Cikin mamaki Malam ya karbi kudin shi kuma Nasir ya juya ya shige part dinsa


Da safe Malam ya fito da kudi yana nunawa aunty ,itama tayi mamaki sosai, sai tace kawai ya hada dasu tunda dai shi bashi ya nema ba


Haka rayuwa take Malam Ya'u ya fara kasuwanci cikin sa'a sosai yake samun rufin asiri, yanzu ya daina zaman get kwata-kwata da gari ya waye zai fita kasuwancinsa ,hakanan yanzu shine yake dawainiya da yaranshi gurin biyan kudin makaranta,dama su Nafi'u ne ,Maryam tuntuni ta kammala karatun ta, kafin mutuwar dady ya tsaya mata sai da tayi karatu sosai kuma takkadunta sunyi kyau sosai shiyasa take so ta samu aiki ko a karamin asibiti ne domin ta tsaya da kafafunta ita kam babu abinda zata ce da Alh Hussen kullum sai dai tayi mishi addu'a samun Rahama gurin uban giji



Abdul yana Legos ya fara aiki yanzu sai dai su yi waya su sha soyyayrsu ,yace "in yadawo za'a hado komai a kawo sai dai kawai a sanya ranar daurin aure.


Nasir kwata -kwata ta manta yau sharabon da su hadu ,sosai tayi bala'in kewarsa tun lokacin da suka hadu a bakin get bata kara ganinshi ba.


Ban garansa kuwa abubuwa ne suka sha masa kai sosai domin yanzu harkoki sun bude masa ba ya zama a gida sosai ko asibitinsa bai fiye zama ba in dai ba dole ba ,sabida yadda kasuwancinsu ya bunkasa daga sunyi odar za ka nemeta karasa ta kare sabida kyawun Motocin da suke shigo dasu da nagartarsu , kudi sosai suka yi suna shi da Abbas Nasir&Abbas Motars sunan kamfanin nasu, Nasir yayi kudi na ban mamaki lokaci guda sunansu ya zagaye kasashe ,a yanzu ma shirye shiryen da yakeyi zai tafi America domin a can ma suna so su bude sabon company shi da wasu turawa.


Momy tayi tayi mishi addu'a , shiyasa yanzu kafin kaganshi sai kayi da gaske, sabida yawan zirga -zirgar da yakeyi.
[06/06, 01:47] +234 808 996 5176: [29/05/2019 1:56 PM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*

*95*
Misalin bakwai na dare Nasir ya shigo gidan cikin wata sabuwar motarshi mai masifar kyau da tsada ,yana kwance a bayan mota drevar shi Tony yana jan shi ,gefanshi kuma daya daga cikin budy gard dinshi ne, a zaune , Tony yayi parking din motar a inda a ka tanada, Nasir ya fito daga Motar hannushi rike da wayoyinshi, yayi wani haske sosai sabida yadda hutu ya zauna yana sanye da kananun kaya as'usel kamar ko da yaushe kanshi sanye da wata person cape mai uban tsada, kai tsaye part din Momy ya nufa , Giss ya bi bayanshi rike da jakarshi da wasu takkadunsa ,kana ganin yadda yake tafiya kasan yayi bala'in gajiya, ga wata shegiyar yunwa tana sasakar cikinsa tamkar zata cinye masa "ya"yan ciki, da kyar yayi sallama falon ya zube kan kujera ,kusa da bakin kofa cikin gajiya ya ce "Ya Allah"!
Giss ya tsaya a kanshi yana zare ido, Nasir din ya waigo kawai ya mika mishi hannu batare da yace komai ba.
Da sauri ya mika masa karamar jakar hade da takkadun hannunsa , kawai yayi mishi alama ya tafi, ko da ya fita ma sai ya tsaya nan bakin kofa kawai yana bin harabar gurin da kallo


Momy ta sauko daga sama sabida jin motsi, Sam bata tsammaci shigowarsa ba yanzu, cikin mamaki takaraso inda yake zaune tana kallonshi ,tace"My Son yau da wuri haka"?


Ajiyar zuciya ya sauke yana Dan ya mutse fuska yace"Wallahi Momy nagaji ne ,ayi ta abu daya babu ji babu gani ,yau hutawa zanyi duk mai son ganina sai gobe karfe biyu na rana, domin sai nayi bacci a gida,

"Dole mana kai ne can kai ne nan ,abincin kirki ma baka tsaya kaci, ya kamata ka huta ,tukkuna"


"Momy yanzu ma yunwa nakeji wallahi'
Yafada yana kokarin mikewa tsaye


Momy tace "ai kuwa yanzu sai dai in shiga kchin in girka maka da kaina ,domin nasan baza kaci towo ba"



"Momy wa yafada miki , sosai zanci indai miyar tayi min"


Momy tayi dariya tace"dole ma tayi maka miyar ,sabida wacce tayi gwana ce a fannin girki"


Tare suka isa daining din suna hira cikin fahimta Momy ta hada mishi towon semo miyar agushi taji wadataccan naman rago ga man shanu ,sannan ta hada mushi farfusu na kan rago gefe ga lemo da ruwa mai sanyi



Nasir yaji duk yunwar da yakeji ta taso sabida yadda kamshin girkin ya cika masa ciki


Yayi bisimillah ya fara ciki


Momy tace"wai cin towa da cokali my Son, yanzu kana jin dadi a haka"


Dariya yayi kawai bai ce mata komai ba, ya cigaba da cin towonshi, yau sha rabon da ya samu abinci mai gamsarwa irin na yau
[29/05/2019 2:22 PM] ®Binta Umar Abbale: Dama shi ba gwanin cin abinci bane yafi kauri gurin kayan zaki mussaman madara da kalolin buscut da alawa , bini-bini shan sweet tamkar yaro karami , sai Momy tayi da gaske yake tsayawa yaci abinci ko lokacin da yana yaro ,dama in ya shiga gurin aunty itace take bashi girkinta irin na gargajiya lokacin, yai taci yana santi ,amma yanzu yau sharaban shi da yaci girkin aunty.


Yanzu da kyar ya cinye daya duk kurarin yunwar da yakeyi , bawai Dan towon ya gimshe shi ba, sai Dan cikinshi ya cika ,ya dauki tissue ya goge bakinshi , fuskarshi dauke da fara'a yace"Momy abincin nan yayi testing sosai da sosai naji dadinsa"


Momy tayi dariya tana nuna plate din tace"duba Dan Allah sai kace wanda yaci malmala uku ,har yaushe ka gama jin testing din nashi"


"Momy ji nake cikina kamar ya fashe yanzu, na koshi sosai amma ki aje min mai ma a kecewa"?
Yafada yana kallonta


Momy tace "dumame kakeso kace"?

Ya saki dariya yana sosa kunnenshi da key din motarshi yace"yeah Momy ki aje min shi gobe ina tashi in karya dashi"



"Allah yasa"
Momy tafada tana tabe baki


Yana dariya yace"da gaske nake Momy wallahi zanci"

"To mai nace MySon Allah ya kaimu lafiya"

"Ameen Momyna"


Momy ta gyara zama tana kalonshi sosai tace"dama a kwai maganar da nakeso muyi dai , Myson"

Cikin nutsuwa ya kalleta yace"Momy ina sauraronki Allah yasa ta alkairi ce"


"Jiya Kawun ka Alh Salisu yazo min da wata magana, wai kafin dadynka ya rasu ya ce dashi ya aura maka "yar sa Mubina, Hakane wai"


Shiru yayi kawai yana kallonta sabida rashin abin cewa da jin maganar da Momy tazo masa da ita,


"Myson kanaji na fa kayi min shiru kawai, ka sa min ido"

"Momy Idont know"

"Kamar yaya baka sani ba"

"Momy to mai kikeso ince miki ne,uhumm , kina ganin tunda dady ya rasu mutanen basu kara waiwayar inda muke ba, sai yanzu kawai zaizo miki da wani zancensa , Wanda daga ji ma kinsan tsari ne ,domin biyan bukatar kansa, Duk wani abu da sukeyi da qumbiya qumbiya duk in da labarinshi, sabida haka babu wannan maganar a iya sanina dai dady ya bar wasiyyar ko bayan ranshi a daura Auran Abdul da wan can yarinyar, ke ma a gabanki a kayi haka, amma maganar da uncle Salisu yazo miki da'ita kwata-kwata babu ita"
[06/06, 01:48] +234 808 996 5176: [29/05/2019 8:28 PM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*96*

Momy ta bata fuska tana kallonshi tace"ya zakace in daina maganar kwata-kwata babu ita, yanzu kana nufin haka zakayi ta zama babu aure,kullum a kayi maka magana sai kace kai kaza kai kaza, kasan abinda bazai yiwu bane in zuba maka ido ina kallo babu aure, ya zama dole ka fito da matar aure a wannan lokacin, in ba haka ba kuwa duk irin hukuncin da kawunanka suka yanke a kanka babu ruwana"
Momy ta karashe maganar tana sauke a jiyar zuciya.

Shima fuskarshi ya hade sosai, cikin zuciyarsa yace lallai yanzu za muyi fada da Momy.

"Momy wai duka shekaruna nawa ne da zaki bi ki daga hankalinki a kan rashin aure na, har yanzu ban kai 30yaers ba, ina 27 yanzu Dan Allah ki kwanta da hankali ,aure lokaci ne in yazo zanyi,amma ni babu wata Mubina da zan aura, sabida tayi min tsofa"


Momy ta harareshi tana Jan tsaki tace"wallahi babu ruwana kaje Ku karata da Salisu domin ba zaka jawo min zagi ba"


"Momy ki kyaleni dashi kawai"
Nasir yafada yana kokarin mikewa


"A'a ni dai bance maka kaje kayi masa rashin kunya ba domin na San halinka"


Dariya Nasir yake yana kokarin shiga bedroom dinshi dake falon yace" Wai Momy mai yasa mutum in ya kasance mai fadar gaskiya ,sai kiga bashi da farin jini, ni yanzu fadar gaskiyar da nakeyi yasa a ke ganin rashin kunya ta kuma duk suka bi suka tsaneni,


"Hummm My son bakasan duniya yanzu tazama abinda ta zama ba , Allah dai ya kyauta, kullum dai ni gargadin da nake maka shine ka rike gaskiya duk inda kake"


"Insha Allahu Momyna"
Yafada yana kokarin shiga bedroom din nasa

Tsaf dakin komai a muhallinshi in banda kamshi babu abinda yake tashi a dakin, ya zube wayoyinshi kan bed ya nufi toleit domin yin Wanka, wani irin bacci yakeji ,gashi yana so ya duba desktop dinshi sabida ya kwana biyu bai San me asibitinsa yake ciki ba ,ya San dai Dr Sofia zata kula dashi sosai to amma dole gobe ya leqa ya ga abinda yake faruwa
[29/05/2019 9:05 PM] ®Binta Umar Abbale: Wanka yayi ya fito ya cwando 3qouter ba tare da yasa ko vest ba ya zauna gefan gado yana duba wayoyinshi , jikinshi yayi sanyi jin wani irin feeling dake ta so masa yanzu-yanzu , kwana biyu abinda yake ta fama dashi kenan ,duk abinda yakeyi daurewa kawai yake, wayar ya aje gefan bed din ya kwanta rigin gine gami da Dora hannunwanshi duk biyun a saman kanshi idanshi a lumshe,shi kadai yasan halin da yake ciki, a yanzu fargabarshi ma kar ya kwanta bacci yayi mafarki da wannan fitinanniyar yarinyar tazo ta dameshi cikin bacci, shiyasa yake jin tsoran yin baccin, ya mike da sauri ya nufi firji ya dauko lemon tsami ya rabashi biyu kawai ya sanya a bakinshi yana tsotsa, a halin da yake ciki ,shi kadai ne zai iya rage masa wannan abin da yake damunshi a mararshi, ko tablet din ba zai masa abinda lemon tsami zai masa ba, shiyasa yake ajeshi da yawa cikin firjin dakin nasa



Da kyar bacci ya daukeshi mai cike da wahala da mafarkin Maryam gashi yana yin sex da'ita cikin garari, Dan haka a firgice ya farka misalin Uku da rabi Na dare, ya farka ya mike zaune sai gumi yakeyi tamkar Wanda yayi tsere jikinshi yake dubawa yana Jan tsaki, duk ya baci, babu yadda ya iya haka ya mike ya shiga toleit ya tsarkake kanshi ranshi a mugun bace ya rasa wane irin bala'i ne wannan yarinyar ta zame masa karfan kafa ,ta shiga rayuwarsa ta dabaibayeshi sai kace aljana, shi yanzu ma tsoranta yakeyi wallahi kwata-kwata baya so ya ganta domin ganinta ba alkairi bane a gareshi.
Haka ya fito ya sanya jallabiya fara kar sannan ya shimfida daddama ya tada sallah raka'atanil fajri,


Ya Jima yana addu'a wanda duk rabi ta dadynshi ce Sosai yake zubar da hawaye sabida , shi kadai yasan bakin cikin da yakeyi in ya tuno dady yayi bala'in kewarshi sosai ,yana tausayin Momynshi Sosai da sosai, shiyasa yake biye mata da duk abinda tazo




Bayan ya dawo daga sallar asuba kwanciya yayi kawai, cikin ikon Allah bacci ya daukeshi mai nauyin gaske.



Momy ta sauko daga sama misalin 8:00 na safe Uwani na ta faman goge -goge bayan ta gama shirya daining suka gaisa da Momy cikin mutumci


Tace"Kinji motsin Nasir kuwa"?


Cikin nutsuwa Uwani tace"A'a Hajiya bai fito ba"

Momy tace"mybe bacci yakeyi domin yace yau bacci zai yini yanayi"


Uwani tayi murmushi tace"ai gwara ya huta kuwa *Yaro* mai halin Manya ,abinda yakeyi wallahi Dan shekaru hamsin ba zai iya ba,ai Nasiru yana da Hankali da sanin ya kamata kuma yana da adalci ga taimako hajiya, nake fada miki kwana uku da suka wuce yasa Nura ya kaimin kayan abinci komai da komai sannan ya Dora da kudi wai nayi cefane

Momy tayi dariya tana kallon Uwani tace"Allah Na gode maka daka nuna min zuwan wannan rana"
[29/05/2019 9:47 PM] ®Binta Umar Abbale: Uwani ta cigaba da cewa "wallahi kuwa Hajiya nace ni mai zanyi da kayan abinci tunda komai ina samu a gidan nan,sai kawai na aikewa da kanwata Furera can qauye tayi ta murna har da kuka dama tana fama da mijinta , bayayin aikin komai ga yara biyar Duk ita take dawainiya dasu"


Momy tace"Assh! Uwani amma baki taba fada ba sai yanzu,gashi kullum ana fitar da abinci a gidan nan mai yasa kikayi haka"


"Wallahi Hajiya sha'anin mantuwa ne kawai amma insha Allahu zan kiyaye"
Uwani tafada tana karkade kujeru


Momy tace"shikkenan yanzu in ya fito zan mishi magana ya sa ka sunanta a lis duk karshen wata sai a dinga fitar mata da nata"


Uwani ta rika godiya kamar ta ari Baki


Momy tace"babu komai duk Wanda ya taimaki wani shima Allah zai taimakeshi"


Momy macace mai mutukar tausayi sosai kuma bata da girman kai ,tana zama da masu aikinta suyi hira cikin mutumci ,shiyasa suka saba da ita sosai.



Cikin nutsuwa take tafiya , tana sanye da hijabi harkasa kamar ko da yaushe duk kwakwar mutum ba za ka taba gane wane irin kaya ne a jikinta sabida yadda hijab din ya rufeta ruf kafarta sanye da safa as'usel idonta sakaye da niqabi, a gajiye take tafiya sabida tsananin gajiya ga yunwa taci-tacinye ta, sabida lokacin da zata fita batayi kyakykyawan kari ba,ruwan shayi kawai ta kurba ko madara babu, wata friend din ta ce jiya tayi mata waya cewa a kawai wani asibiti da suke Neman ma'aikata ,tazo suje ko Allah zaisa a dace , shiyasa ta hana idanta bacci tayi asibanci suka tafi, to sai a kayi rashin sa'a domin sun gama diba , ko zasu dauka sai an kwana biyu sabida haka ransu a bace suka fito daga asibitin kowanne yayi nashi guri

Haka take tafiya a kasa har ta shi go estet din nasu , nan ma kafin ta isa gidan da akwai tafiya ,babu yadda ta'iya ta cigaba da bin gefan kwalta.



A gogon hannunta ta kalla lokacin da ta karaso gidan 12:00 dai-dai na rana a fili tace"yanzu wannan ranar da ake kwalawa duk a kaina takare Mtssss"


Karamar kofa ta tura kai tsaye ta kutsa kanta cikin gidan.

Karaf idanunsu suka sarke guri guda.

Nasir yayi sauri ya dauke kanshi daga kanta yana Jan karamin tsaki ,sabida ya gane ko wacece duk da yadda ta boye jikinta ,ko daga bacci ya tashi sai ya ganeta,
Ya mayar da hankalinshi kan Tony suka cigaba da maganar da sukeyi


Maryam kuwa gabanta ne ya fadi lokacin da suka hada ido , zuciyarta ta ringa harbawa, yau watanta uku rabon da tasa shi a idonta, Lallai uncle haka ya zama ,kwata-kwata ya sauya mata ,yayi uban haske da kiba, ga wani quetar million da ya aje Wanda yayi wa fuskarshi mugun kyau ,sosai ta dinga kallonshi ta cikin Niqab din har tazo ta wucesu ta nufi bangaran nasu gabanta bai daina bugawa ba.


Jiki a sanyaye ta zube a tsakar gida tana sauke nuffashi, gaskiya ba ta gaji da ganinshi ba ,dole anjima ta shiga gurin Momy yadda zatafi Morewa ta kalleshi yadda ranta yakeso.


Aunty ta ce"ke kuma meye kin dawo kin zube bakin hanya"


"Wallahi aunty na gaji ga uwar yunwa tana damuna"


"To ina ruwan wani ,ko wani ne yace lallai kar ki tsaya kici abinci kafin ki fiya, haka kawai kin nace lallai sai kin yi aiki ko uwar me kike nema Wanda bakya samu oho"


Kamar zatayi kuka tace"kai aunty, don Allah kiyi min fatan alkairi , kinga yanzu ma wallahi bamu dace ba"


"Allah ya kyauta miki, ai"
Aunty tafada
Ta cigaba da cewa "wato ke ana maganar auranki kina maganar Neman aiki ko"


Maryam ta zumbura baki tace"aunty Abdul din da kansa yace in nema, kuma shima ya karbi takkadun nawa ya tafi dasu legos zai duba min a can"


Dariya abin ya bawa aunty ,bata ce komai ba kawai ta wuceta ta nifi kchin tana dariyarta ita mamakin yarinyar take sosai, tana da zuciya tana kuma da so da kaunar iyayenta, gashi ita macace. Tasan duk wannan abin da take dominsu take yi.
[06/06, 01:48] +234 808 996 5176: [30/05/2019 9:24 AM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*

*97*

Cikin mutuwar jiki ta mike ta nufi daki ita kadai ta san abinda takeji a cikin zuciyarta, Wanka ta shiga duk da cewar tayi da safe kafin ta fita , amma yanda takejin jikinta haka in ba wankan tayi ba baza taji dadi ba, tanayi tana tunanin yadda za'ayi ta kara ganin uncle din wata zuciyar tace mata ,kawai ki tafi gurin Momy kai tsaye can ne zaki fi ganinshi sosai, sabida haka cikin sauri ta ke komai , ta shirya tsaf lokacin aunty ta kammala abinci ,sai ta nufi kchin din ta dibi iya yadda zai isheta ta fito ta zauna a falo ta fara ci.
Tace "aunty ina su Nafi'u ne naji gidan shiru"

"Kin manta sun fara zama a makaranta sabida lokacin saukarsu ya matso"

'Eh hakane sai yanzu Na tuna nima lokacin da za muyi haka mukai wannan zaman"

Hira sukeyi

1 Comments On YARO DA KUDI
avatar
magaji-2

1 year ago

Reply

Allah Yakara budi

Please Login or Register in order to submit comment