Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

har nice zan dauko maka kayan da zaka sa,to sai dai a kwana a haka,amma kai baka isa kasani abinda banyi niyya ba"


Idanshi tsaye a kanta har ta kare maganar

Ranshi a bace yace"Na nawa kuma yarinya ,Wanda yayi silar zuwanki duniya ma gashi can bakin get yana min gadi,ballantana ke!!"
Ya karashe maganar yana nunata da hannu cikin izgili

Kuka ne yakeso ya Kufcewa Maryam jin cin mutumcin ya shallake kanta ya dawo kan Mahaifinta


Tace"tabbas kafadi gaskiya mahaifina ba komai bane ,kuma ba kowa bane a duniyar nan ,muna nai man tsari da dukiyar da zata samu mu manta da Allah mu shagala da duniya murika sabon Allah a cikinta"


"Ke kika sani dai yarinya na get out malama"
Yafada yana nuna mata kofa


Maryam ta bude kofa ta fice batare kawai tana girgiza kai cikin takaici wulakancinsa



Momy na tsaye da hijab a hannunta tana kokarin sawa tace"yawwa dama yanzu nake kokarin in shiga in miki magana kifito mutafi naji shiru,nace Allah yasa bawani abin yayi miki ba"


Cikin kokarin danne abinda yake taso mata Na bacin rai tace "babu komai wallahi Momy nayi duk abinda kika Sani"


"Yawwa Allah yayi miki albarka"
Momy tafada
Sannan suka fita a tare
Momy ta daukesu a motarta har Malam Ya'u suka nufi asibitin



Mikewa yayi bayan fitarta ya nufi tolirt a gurgije yayi Wanka ya fito ya nufi inda kananun kayanshi ,ya kwana biyu bai sasu yau sai yaji yana sha'awarsu ,tsaf ya shirya cikin wani mugun wando jins mai mutukar tsada blue colour shart din ma haka ta matse masa jiki sosai power dinshi ya fito ya gyara sumarshi tsaf sannan ya dauki agogonshi ya daura,ya nufi inda takalmanshi suke ,sai da ya sanya safa sannan ya saka wani mugun takalmi fadar kudinshi ma aiki ne ,sosai Yayi bala'in kyau ,sabida yadda dressing din ya karbe shi ,sabida yadda ya yi qiba jikinshi ya murje sosai ya fito ,ya nufi inda motarshi take shima babu inda yayiwa tsinke sai hospital din yanaso yaje ya duba marasa lafiyarsa ,sannan ya wuce can gurin Abbas domin cigaba da tsare tsarensu na bude sabon gurin shakatawa da zasuyi
[06/06, 01:45] +234 808 996 5176: [26/05/2019 9:51 AM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*90*

Alhamdullihi jikin Baban gida yayi sauki sosai ,yana zaune gefan gado su aunty a kusa dashi , su Momy sukayi sallama cikin dakin, Yaya Rabi ta amsa tana yiwa Momy sannu da zuwa, fuska a sake Momy ta karasa cikin dakin tace"A'a lallai jiki yayi sauki Baban gida Allah ya kara afuwa"
"Alhamdullhi kam jiki ya samu wallahi"aunty tafada tana bawa Momy gurin zama Momy ta zauna suna gaisawa da Yaya Rabi cikin mutumci , aunty ma suka gaisa cikin sakin fuska Yaya Rabbi ta kalli Maryam dake tsaye jikinta a sanyaye tace"ke kuma abinda kikayi kin kyauta cikin dare ki fita ,kisa mi ta nai manki ko duk kin daga mana hankali"

Maryam ta sunkuyar da kanta kasa ,domin bata da abin cewa,tasan in tafadi abinda ya faru ba yadda zasuyi ba



Momy tace"subahanallahi kamar yaya tafita cikin dare"?


Aunty ta girgiza kai cikin bacin rai tana kallon Momy tace"wai daga cewa in uncle dinta ya shigo taje tabashi hakuri kan irin rashin kunyar da tayi masa jiya,shine da ta fakaici idon mu taga munyi bacci shine ta gudu gida ,sabida tana ganin kyashin ta tsaya tabashi hakuri"


Momy tayi murmushi tace "Laifin mai tayi da har zaki titsiyeta kice lallai sai tabashi hakuri ,waya gaya miki anawa yara haka,? Ni sam banga laifin ta ba ,Dan yaro ya tsare kare martabar iyayenshi sai ace yayi laifi ,karki kara yin haka Suwaibah wannan ba hukunci ba ne"


Malam Ya'u yana tsaye jikin gadon da Baban gida yake kwance ,ya sauke ajiyar zuciya yace" nima abinda nakeso ince mata kenan abinda tayi bai yi dai-dai ba ,jiya misalin uku shaura Na dare naganta ta shi go gidan a furgice,hankali na ya tashi sosai ,duk Na tambaye ta dalili shine take fada min


Yaya Rabi tace"kwarai hakan ba dai-dai bane wallahi kar kiso kiga yadda hankalinmu ya tashi jiya

Sai da asubah da nace ta kira Babanta ta sanar dashi halin da ake ciki ,shine fa yake cewa gata a gida mu kwantar da hankalimu"


Momy tayi ajiyar zuciya tana kallon Maryam din tace "kar ki kara aikata irin haka,yanzu inda wani Abu ya sameki Na tsautsayi kice mai,Allah ya kiyaye ameen"


Maryam tace"insha Allah Momy bazan karaba"

Momy tace"ga kayan kari nan Rabi"

Yaya Rabi tace" to angode Hajiya Allah yakara girma ya jikan magabata"

Nan Momy tasa a ka hadawa Baban gida abinci a kabashi sannan tabashi magani da kanta,suna hira kadan kadan,Nasir ya shi go cikin dakin Dr Sofia na bayanshi hannunta rike da wasu takkadu
[26/05/2019 10:18 AM] ®Binta Umar Abbale: Sama-sama ya gaida su aunty hankalinshi na kan Baban gida,Dr Sofia kuwa babu wanda ta gaida a cikinsu sai Momy ,to Momy Sam bata kawo komai ba , sabida tasan yarinyar dama can ba wani hausa takeji ba sai turanci amma dai duk da haka inda mutumci yadda ta gaida ita ta gaida sauran da suke tare

Aunty ma jikinta ne yafara sanyi sabida ta lura da irin kallon raini da Dr Sofia take musu ita da Yaya Rabi,amma sai ta daurewa zucuyarta tace ko Dan yarinyar ba musulma bace shiyasa batasan darajar Dan adam ba.



Maryam ko taci alwashi sai ta ci mata mutumci ko da me take takama wallahi bazata raina mata iyaye ba,tana addu'ar Allah yasa kafin su gama zaman asibitin wani abu ya hadasu da'ita sai ta wulakantata
Dama gashi tana jin haushin yadda take wani shishshigewa Nasir din Dan wani lokacin tana lura jikinsu har haduwa yakeyi


Ya karasa bakin gado yana duba shi sosai Ya kalli aunty kadan yace"anbashi magani ko"?


Aunty tace"eh yanzu Momy tabashi"

Shiru yayi kawai ,ya dauke idonshi daga kan Baban gida ya dora kan Momy ,fuskarshi kamar ko da yaushe yace"Momy ina ganin zan sallameshi tunda ya dawo normal So sai ya cigaba da karbar magani a gida ,sabida ni banaso ana cika min asibiti kullum"
Duk cikin turanci yake maganar in banda ita Momy din da Dr Sofia da Maryam babu Wanda ya fahimci abinda yake fada


Cikin turancin Momy tace"Why My Son mai yasa kake haka ne suwaye mutane ,ni ko kuwa iyalan wannan bawan Allah ,uhumm! Wulakanci fa babu kyau"


Ya mutse fuska yayi kadan yana duba a gogo yace" Momy bafa haka nake nufi ba please kinsan komai nawa a tsare yake ,wallahi kwata kwata tunda suka shigo hospital din nan daga jiya zuwa yau komai ya sauya,gwara kawai su koma gida ,sai in cigaba da kula dashi"

Dr Sofia tasa baki ita ma cikin ya mutse fuska cikin turancin ta tace"yes Bama bukatar hayaniya a wannan guri Momy sabida duk yawanci marasa lafiya suna bukatar huto da kwanciyar hankali"


"Momy tayi kwafa tana kallonta rai a bace tace" wato koya min yadda aikin asibiti yake zakuyi ko kuwa tun kafin a haifeku nake wannan aiki"


"Sorry Mom ba haka bane , kiyi hakuri in maganar tayi miki ciwo ,in babu damuwa abar mana Mara lafiyar shi kadai kawai bama bukatar "yan jiya ,sabida a kwai masu kula da..

"Ya'isa"! Maryam tafada a hasale tana nuna Dr Sofia da hannu cikin turanci tace"ko kunce ko baku ce ba dole Baban gida zai bar asibitin nan tunda ba Ku zaku bashi lafia ba , ni nan na isa in kula dashi tunda nima abinda na karanta kenan baku kadai Allah ya bawa ilimin ba,akin banza aikin wofi ,sai anyi magana ki dinga yiwa mutane turamci banza da wofi da wani rubban bakin ki da yagaji da shan giya da kayan maye"
[26/05/2019 12:07 PM] ®Binta Umar Abbale: Shiru dakin yayi duk sun zubawa Maryam ido


Momy taji dadin abinda Maryam tayiwa Dr Sofia ,sabida ta lura yarinyar tana da girman kai


Dr Sofia ta kalli Nasir ranta a bace tace"kaji abinda wannan yarin take cewa ko, kamar ni zata dinga zagi tana fadawa magana ,ina kan aiki na"


Shiru yayi kawai baice mata komai amma ranshi yayi bala'in baci da abinda Maryam din tayi ,wato duk kokarin da yakeyi a kansu bata gani,ya lura zaqewarta tayi yawa amma zai taka mata burki


Fita yayi daga dakin batare da kara magana ba Dr Sofia tabishi a baya itama ranta a bace , duk suka bisu da kallo,


Maryam ta sauke ajiyar zuciya tanajin dadi ko babu komai ta'amayar da abinda yake damunta



Ko da Nasir ya fita ,kai tsaye bakin get ya nufa Dr Sofia Na bayanshi ya samu Sucurity ya kalle ta cikin turanci yace"kuje tare dasu ki sasu su fito da wannan yarinyar ayi waje da ita ,ita kadai nace kiyiwa haka banda sauran, zan fita ki kula da kowa ,sannan ki duba wannan takkadun da suke hannunki duk Wanda kikaga ya cancan ci a dauke shi aiki sai ki dauki sunanshi ,ki kirashi domin kiyi masa intervio"


Cikin jin dadin hukumcin da ya yanke tace" OK za'ayi duk abinda kace,sai kadawo"


Nasir ya shige motarshi ranshi a bace


Dr Sofia ita da Security din suka nufi cikin Asibitin


Suna zaune shiru kowa yana sakawa da kwancewa ,mussaman Malam Ya'u yana tunanin mai nene mifita a rayuwarsu Suka ji an turo dakin an shi go


Cikin bada Umarni Dr Sofia ta nuna Maryam da hannu tamkar wacce tayi gagarimin laifi cikin turanci tace "kuyi waje da ita"



Kafin Momy tayi magana tuni sunyi kan Maryam suna zare ido



Momy ta daka musu tsawa tace"kar Wanda ya kuskura ya taba ta wallahi ranku zai baci"


Daya daga cikinsu yace"Madam umarni ne daga oga"


"Ok Umarni ya baku Nasir din cewar kuzo Ku fita damu"?
Duk cikin turanci suke maganar.


Yace"No ita kadai yace mu fita da ita"


"To shikkenan Momy tafada rai abace tace nice Mahaifiyarshi ,ba Maryam ya kora ba ni ya kora kuma zan fita yanzu"


Dr Sofia tace"Mom kiyi hakuri , wan can yarinyar ya bada umarni a fitar masa ,ba ke ba please mom


Momy tace "rufe min baki bana son zan can banza"


Malam Ya'u dake tsaya jikinsa a sanyaye duk da bayajin turanci amma ya fuskanci abinda yake faruwa ba mai dadi bane ,gashi yaga ana nuna "yarshi da hannu Allah yasa bata wani laifi tayi ba


Ya tari Momy wacce take ta faman fada da turanci,yace duk da dai bana fahimtar abinda kuke cewa Hajiya ina ganin abin duk bai kai na daukar zafi haka ba,ina ganin tunda Baban gida yasamu lafia zamu bar asibitin nan mungude da karamchi Allah ya kara girma"



Momy ta sauke ajiyar zuciya tace "ai ko baka fada dole zamu bar asibitin nan yanzu, shi kuma Nasir din zaizo ya same ni"



Abin mamaki duk da tsawar da Momy tayiwa Sucurty din ,ta kuma ce musu ita mahaifiyar Mai asibitin ce ,hakan bai sa sun kauce daga kanta ba su tsaye kikam ! Suna jira ta tashi. Ita ko Maryam Sam abin bai mata ciwo ba domin tasan Dan ya bata mata rai ya yanke wannan hukunci, sai ta kalli Momy tace "kiyi hakuri Momy wallahi ni kaina narasa wace irin qiyyaya uncle ke min amma babu komai"



Momy tace"ai ke zan bawa hakuri Maryam kinji ,babu komai zaizo ya same ni, tafada tana mikewa tsaye tana gyara zaman hijab din ta


Su aunty ma mikewa sukayi ,Yaya Rabi tana kokarin tashin Mahaifin nata, Malam Ya karaso gurin ya tasheshi ya mike jikinshi babu kwari sosai ,sai ya jin ginar dashi a kafarshi suka na kokarin fita daga dakin

Suma suka biyo bayansu kowanne da rai a bace, Dr Sofia ko babu abinda ya dame ta, haka wannan Sucurty suka tasasu a gaba har sai da sukaga sun fice daga asibitin sannan suka dai na binsu sai kace wasu masu laifi.
[06/06, 01:46] +234 808 996 5176: [26/05/2019 9:16 PM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*91*

Wannan abu da Nasir yayi ya 6ata ran Momy sosai, tunda take dashi bai taba mata abinda ya ta6a mata zuciya ba irin na yau,kwata-kwata ta lura Nasir bai san darajar dan'adam ba ko kadan ,giyar kudi tana dibanshi ya nawa kowa kallon kaskanci,amma wannan karon dole ta nuna masa bacin ranta, rai a bace suka karasa gida,dukkaninsu suka fito daga motar bayan Momy tayi parking,kai tsaye part dinta ta nufa ,batare da ta tsaya a gurin ba domin wani irin nauyi da kunyar mutanan takeji, gashi dai kullum Nasir din zai yi musu rashin mutumci amma sabida karamci da dattako basa nuna wani bacin rai a tare dasu,

To bayan Momy ta wuce Malam ya shiga da Baban gida wajansa ,su aunty suka gyara masa ko ina ,sannan suka fito,suka barshi tare da Malam Ya'u suna hira ,Baban gida ya kalli Ya'u yace"dama a kwai maganar da nadade inaso muyi da kai"


Malam Ya'u ya gyara zama yana fuskanta Baban gida cikin girmamawa yace"ina sauraron ka Baba"


Baban gida ya sauke ajiyar zuciya cikin alamu na marasa lafia yace"lokaci yayi da za'a ce ka tsaya da kafarka ma'ana ka dai na ci a karkashin wani , tun lokacin da Marigayi Alh yana raye naso ka karbi kasuwanci kamar yadda shi Alh ya so a lokacin ,kai ka nuna kafison ka zauna a bakin get ko"


"Kwarai kuwa Baba ni kai na sai yanzu nasan na tafka babban kuskure wallahi"


Baban gida yace"dama ba wani abin ake gudu ba sai mutuwa"

"Kwarai kuwa Baba"


"Yanzu abinda za'ayi a kwai wata gona ta can garinmu albasu zan siyar da rabi sai in baka kudin ka fara juyawa ko yaya kace"


"To madallah Allah ya saka da alkairi,wallahi nima tuntuni nake shawarwarin yaya za'ayi"

"Abinda za'ayi kenan ai "
Baban gida yafada yana gyara kwanciyarsa

Nan dai Malam Ya'u yayita godiya suka tsayar da maganar cewar zasuje can albasu garinsu Baban gida domin a siyar da gonar sabida sauran "yan uwanshi duk suna can shine kawai yafito nai man abinci cikin gari a wancan zamanin har ta kaishi da yin aure ya haifi su Yaya Rabi da aunty Lokacin da mahaifiyarsu ta rasu aunty da girmanta a lokacin Yaya Rabi a kayiwa aure ,to bayan rasuwar mahaifiyar tasu sai auntt ta cigaba da kula da mahaifinta har lokacin da ta auri malam Ya'u



Malam Ya'u ya gyara masa kwanciya ya mike ya fito cikin farin ciki ya nufi bangaransu,


Ya na zuwa ya sanarwa da aunty halin da a ke ciki


Suma sun goyi da bayan haka sabida dama tun dazu abinda suke tattauna kenan


Maryam tana kicin tana aikin hada musu abinci ita ma taji dadin wannan lamari dama burinta bai wuce ta dai na ci a karkashin Nasir ba ,Dan rainin hankali.
[26/05/2019 9:38 PM] ®Binta Umar Abbale: Nasir kuwa sai wajan sha biyu na dare ya shigo gida.

Kai tsaye part dinshi ya wuce domin yayi wanka ga wata irin yunwa yana ji


Momy tana falo tana jiran dawowarsa ,tana jin shiguwar motarsa ta mike ta nufi part din nasa.


Fitowarshi kenan daga toliet yana tsane kanshi,Momy ta tura kofar dakin nashi ta shiga da sallama


Abin ya bashi mamaki ganin Momyn shi da daddaran nan ,sai ya tsaya yana kallonta ta karaso ta zauna gefan gadonsa ita ma shi take kallo kamar yadda take kallonsa


Yace"Momyna lafiya dai ko"?

Tace "lafia lau tunda gani ka ganni Allah ya dawo dani gida bayan korar karan da kasa akai mana"


Cikin namaki yaje ya zauna kusa da'ita yace"Momy waye yayi miki korar kare,ban fahimci abinda kikecewa ba"


Tace"dazu bayan fitarka waye ya turo Sucurty suzo su wulakanta Maryam"


Momy"wacece Maryam"

" Ok zakayi min rainin hankalin da kasaba ko"?
Momy tafada a fusace!


Dauke kai yayi yana nazari na minti biyu yace"Momy please ban fahimci me kike nufi ba wallahi , dazu dai nasan nasa Dr Sofia tasa ka Sucuty su fitar da yarinyar nan ganin tana nema tayi mana katsaldan a kan aikinmu ,ba na son bacin rai shiyasa na yanke wannan hukunci"


Momy ta hararashi tace"wannan ba hukumci bane wulakanta mutum ne abinda kayi Sam Baka kyauta ba, kamar ni ince musu ,su kyaleta suka qi ,ji sukayi mana tsaye a ka har sai da sukaga mubar asibitin sannan suka dai na bin mu sai kace wanda mukayi gagarimin laifi"


Ranshi ya baci jin abinda Dr Sofia tayi kafin ya tafi sai da yafada mata ga yadda zata yi


Yace" Kiyi hakuri Momy ba laifinsu bane ,ni na isa in sa a kore ki Momy ke nake gani nake jin sanyi a zuciyata Momy nayi missing din Dady Sosai ,kwalla ta taro a idanshi yana kokarin mayar da ita,amma sai da ta fito ,ya sa Dan ya tsanshi daya yana daukewa


Ita ma Momy zuciyarta ce ta karye sabida Nasir ya fama mata mikin da yake cikin zuciyarta ,sai tafara goge hawaye


"OK" "OK Momy yi shiru na dai na please ki dai na Dan Allah"
Nasir yafada yana marai rai cewa


Cikin kuka Momy tace"My Son Bakajin magana ko,ka manta wasiyyar dady din ka"
[06/06, 01:46] +234 808 996 5176: [27/05/2019 1:19 PM] ®Binta Umar Abbale: [27/05/2019 10:35 AM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*92*

Momy ta cigaba cewa My son baka kewar mahaifinka, da ka kayi missing din nashi da gaske da baza ka wofintar da wassiyar shi ba, nima kanaso ka dora hawan jini ,ko ka kasheni in na mutu ka huta ai"Momy ta karashe maganar tana goge fuskarta.
Nasir hankalinshi ya tashi sai ya rungume ta sosai yake kokawa da zuciyarsa sabida bayason hawayen da yake kokarin dannewa su zubo masa har Momyn ta gani hankalinta ta tashi,yace "a'm Sorry Momy bazan karaba ki yafe min, ni kaina ,Wasu abubwan da nakeyi ba'a son raina ba ,amma Momy kar kira zubar min da hawaye dan Allah"


Tausayinsa ya kamata ance tsakanin da da uwa sai Allah

Ta shafa kanshi kamar yaro tace"Na yafe maka ,amma Dan Allah kar kara wulakanta mutanan ,kaga mahaifinka har ya bar duniya tsakaninsa dasu mutumci ne,kuma duk Wanda ya taimaki wani shima Allah zai taimakeshi"



"Momy ki kwantar da hankalinki insha'allahu zanyi kokarin ganin na faranta miki"


Momy tace"yawwa Allah yayi maka albarka"

"Ameen Momyna"

Tace"kaci abinci kuwa,domin jikina yana bani bakaci abinci ba"


"Uhum Uhumm Momy Wallahi banci ba yanzu hakama yunwa nakeji sosai"
Nasir yafada tamkar wani yaro karami


Momy ta Dan mari fuskarsa tana dariya tace"ai halinka zama da yunwa sai da kai tafaman cin biscut sai kace wani yaro"

Dariya yayi har fararen hakoranshi suka bayyana ,kasan habarshi ya loba yana kanne mata ido daya yace"Momy nifa har yanzu yaro ne a gurunki"


Momy ta girgiza kai kawai tana murmushi tana tuno hirarsu da dady kafin rasuwarsa inda yake son yara kananu,

Ta kalleshi tace"Myson inaso ka haifa min yara da yawa kaji ko"


Shiru yayi fuskarshi dauke da murmushi yace"Momy ni a tsarina banason taron yara wallahi a kwai damuwa"


Momy ta harareshi tace "albarkace damuwa my son"?

Yayi murmushi yace" Momy da gaske nake wallahi da daya ko biyu sun isheni"

"Baka isa ba"Momy tafada, tacigaba da cewa kai dai kawai ka nemi zabin Allah"


"Insha Allahu Momy,Allah ya kawo masu albarka"

"Ameen amee"

Tace"tashi ka kimtsa muje kaci abinci"

Ya mike tsaye yace" Momy muje kawai haka

Mikewa tayi itama suka fita.


Momy ta hada masa abinci sosai tasashi a gaba sai da yaci ya koshi sannan ta kyaleshi yaje kwanta
[27/05/2019 10:56 AM] ®Binta Umar Abbale: Washe gari da wuri ya tashi ya kimtsa tsaf cikin yanayin shigarshi irin ta jiya kwana biyu abin ya motsa mishi,ya fito ya tadda Momy zauna cikin kujera tana duba wanni littafin turanci fuskarta manne da farin tabarau

Ta kalleshi da murmushi a fuskarta tace"Kwana biyu kuma abin ya motsa maka ne"


Yayi murmushi gami da zama kusa da ita yana gyara wata katowar hula ta sanyi mai uban tsada yawanci turawa ne suka fi amfani da ita mussaman da sanyi, yasanya ta a kanshi har sai da rufe masa kunne , hannuwanshi ma safa ce kalar hular ,yace "Momy yau garin antashi da sanyi wallahi kinsan banason wannan yanayi duk jina nake a takure"

Momy tace"shine ka jibga riguna a jikinka haka"


Dariya yayi yace"yeah Momy to ke ya kikaga wankan"?

Momy ta tabe baki tace"babu laifi dai"

Yana dariya yace" Momy in a America nake ,wannan dressing din nawa ,mai tsada ne sai nasamu wanda zai'siya,


Momy tace"ai ban ce komai ba"

Yace"nan din ma bari kiga in fita ,yadda zan hada Gslow mussaman Na mata"


Dariya Momy tayi tace"baka da dama My son ,zan so inga Sirika ta,wai ko da Hanifa za'ayi ne ko da Mubina wacce kazaba a cikinsu"


Nasir ya hade fuska yana turo baki kamar wani Yaro yace"Momy rabuda Wa "yan nan "yan iskan yaran dan Allah"


"Yan uwanka ne "yan iska "? Momy tafada cikin mamaki

"Yes " Nasir yafada ya cigaba da cewa
Momy in ba iskanci ba wai a gurin taro Mubina ta mike ta kefadawa dady tana sona ko kunya ba taji cikin jama'a"



"Laifi tayi kenan dan tace tana sonka"?


"Momy nifa a tsarina bana son in auri shashashar mace Mara kamun kai ,shiyasa ma har yanzu ban fara dubawa cikin matanmu nan domin babu abinda suka iya sai shirme da kazanta gami da shafa man bleecing"


Momy dariya take sosai ganin yadda Nasir ya hakikan iya gaskiyarshi


Shima yana dariya yace"Allah kuwa Momy inajin haushin "yan matan wannan zamani kiga sun dage suna shafe shafen banza,karshe ya jawo musu cuta,nafison mace naturel "

Momy ta tabe baki tace "to ai sai kaje kauye ka nemo mata ina ganin can zai fi maka"
[27/05/2019 1:36 PM] ®Binta Umar Abbale: Ya mutse fuska yayi yace"haba Momy kauye fa kikace,ni nayi kala da matan kauye yanzu"?


Momy tace "au matan kauyen kalarsu daban take da ta "yan birni,ashe bakasan sunfi tarbiya ba, in ka amince sai insa Uwani ta duba maka a garinsu kaga Uwani kyakykyawa ce gata bafulatana"


Dariya yayi kawai yana girgiza kai yace"Momy kenan indai zaki iya zama da'ita shikken ki samomin"


Dariya tayi tana nunashi da hannu tace"dubeshi kamar gaske"


Cikin dariya dai ya mike ya nufi dainnig teble yace"da gaske ne mana"


Momy ma mikewa tayi tabi bayanshi tafara hada masa kalaci suna hira cikin so da kauna irin ta uwa da danta,yace"Momy mun kammala komai fa Dan gane da bude Hotel dinmu ni da Abbas yanzu kawai za mu tanadi ranar da zamuyi bikin budewa,bayan haka kuma munyi odar Motoci Masu kyau Sosai da nagarta suna gareji ,kiyi mana addu'a Allah yasa mu fara a sa'a"


Momy tace"Allah ya dafa muku yayi riko da hannuwanku yasa Ku fara a sa'a"

"Ameen Momy"

Miftahu ne yayi Sallama ya shigo cikin falo, yana sanye jallabiya mai ruwan tuka kanshi da hula irin ta Larabawa, yaron yafara girma yanzu yana shekara sha Uku zuwa sha hudu ,cikin nutsuwa ya karaso yana gaida Momy


Momy ta amsa fuskarta a sake ,ya mikawa Nasir hannu gami da cewa "uncle barka da asubah"


Nasir ya bashi hannu sukai musabaha tace" ka tashi lafiya Boy"

Miftahu yayi dariya jin sunan da uncle din ya kirashi dashi yace"lafiya Lou uncle"

"Masha Allah"
Nasir yafada yana cire hannusa ya cigaba da cin abincinsa


Ya kalli Momy yace"Dama Baba ne yakeson yayi magana dake"


Momy tace" to kace ya shigo mana, in banda abin Malam Ya'u sai ya aiko ka, ai anzama daya"
[06/06, 01:46] +234 808 996 5176: [27/05/2019 6:28 PM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*93*

Miftahu ya fita domin ya sanar da mahaifin nasa abinda Momy tace.
Tare suka shigo falo Momy ta mike daga kan kujerar cin abinci tace "Yanzu malam har sai ka turo yaro yayi maka iso sannan zaka shigo"?
Tafada tana nuna masa gurin zama, Malam Ya'u ya zaune cikin kamala da dattako yana murmushi yace"ai dole ne hakan domin haka shari'a tace" Momy tace"e kayi gaskiya Malam"

Malam Ya'u ya gyara zama sosai yana fuskantar Momy yace"Hajiya wata muhimiyar magana ce nake tafe da ita"

Momy tace "To Allah yasa ta alkairi ce ,ina sauraronka"

"Hajiya inaso kiyi wa magana ta kyakykyawar fahimta wallahi ban shirya wannan Abu da wata manufa ba,sai Dan ina ganin haka shine mafita a gare ni"

"Babu komai Malam ina sauraron ka"

"Dama na yanke shawarar cewar zan bar aiki anan zan shiga kasuwa in sha Allah"


Momy tayi shiru tana tunani a cikin zuciyarta,dama tasan wannan lokacin yana nan zuwa


Ta sauke ajiyar zuciya tana kallonsa tace"Masha Allah arrama ,bazan hanaka ka fita nema ba ubangija Allah yabada masu amfani"

Cikin farin ciki malam yace"ameen Hajiya nagode da fahimta ta da kikayi"

Momy tayi murmushi tace"ai nasan gaskiya Malam wallahi babu komai"

Duk wannan abin Nasir Na zaune yana cin abinci yana jin duk abinda suke cewa ,kala bai ce musu ba,har Malam ya tashi yanawa Momy sallama sannan ne ya hangi Nasir din yace"A'a Nasiru baka fita ashe"?


Nasir ya dago kai yana kallonshi babu yabo babu fallasa yace"e arrama yanzu dai nake kokarin fita"

"To masha Allahu,Allah ya tsare"

"Ameen ameen Arrama"
Nasir yafada ya cigaba da cin abincinsa

bayan Momy tace "My son kana

1 Comments On YARO DA KUDI
avatar
magaji-2

1 year ago

Reply

Allah Yakara budi

Please Login or Register in order to submit comment