Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Sama-sama Maryam tace"auntt zan leqa gurin Momy mu gaida"

"Sai kin dawo kice ina gaishe ta"


"Zataji aunty"

Maryam ta mike cikin nutsuwa ta nufi part din Momy,

Kan ta a kasa take tafiya sai tafara jiyo wani mugun kamshi tayi saurin daga kanta.

Nasir ta hango tsaye shida wani , Wanda baza ta taba mantawa da fuskarshi ba wato tony daya daga cikin yaran Nasir ne

Kallonshi takeyi sosai yana cikin suit Masu tsadan gaske hannushi duk biyun suna zube cikin aljihun wandon dake jikinshi, suna magana da Tony Sam bai ganta ba sabida ya bawa hanyar da tafito baya,


Cikin zuciyarta tace Allah yasa ba fita zai yi ba.

Tony ya rika satar kallonta har ta karaso daf dasu, kanta a kasa

Nasir yanawa Tony magana amma yana can yana kallon wani guri


Tsawa ya buga masa yace"ya ina maka magana kana kallon wani gur....
Kafin ya karasa maganar yaji ana kokarin bude kofar falon yayi sauri ya juya, gabanshi ya fadi lokacin da sukayi ido hudu da ita ,yanzu babu niqabi hakanan babu hijabin babu safa , tana sanye cikin doguwar Riga irin ta Larabawa ta nan nade kanta ,rigar baka ce wuluk mai manyan stons jajaye ,Maryam tayi bala'in kyau sosai, Nasir tsaf yaga yarinyar ta koma (Nancy Shararriyar mawakiyar nan ta kasar saudia)

Sai yayi saurin dauke kanshi yana Jan wani mutsiya cin tsaki


Maryam kuwa taji dadi sosai sabida tun daga nesa ta kare masa kallo tana kokarin bude kofar ta shiga ya daka mata wata mutsiyaciyar tsawa, yace"Ke ubanki ki aje a ciki zaki shiga, Allah a fuska fir'auna a zucci"


Maryam ta tsaya hannuta rike da kofa tana kallonshi ,ranta ya baci da zagin da yake mata ,amma sai ta basar kawai ta sassauta murya tana wani irin salo da idonta tace"A'a babu Wanda Na aje a ciki zan shiga mu gaisa da Momy ne"
[30/05/2019 9:50 AM] ®Binta Umar Abbale: "Wuce ki bamu guri munafuka kawai da baki zo kin gaida ta ba sai da ki kaga ina gida, wa zaki rainawa hankali ne, ni baki San ko inawarki bana kaunar gani ba"
Yafada cikin hargagi domin har ga Allah abinda yake zuciyarshi ya ke fada, Sam bashi da rufi ko munafurci shiyasa yake zaune lafiya,a sali ma baya shiri da munafiki

Shiru tayi kawai ta juya zata bude ta shiga Nasir ya fizgo ta ya yar gefe guda, ya nuna ta da hannu gami da cewa" sai ki bari in fita tukkuna sannan kyazo kiyi munafurcin naki, tunda kin zama mayya ke Duk in da nake sai ki je gurin"


Maryam ta mike tana karkade jikinta, kamar zatayi kuka tace"uncle Allah shine zai saka min da abinda kake min"

Ba tare da yace mata komai ba ya mai da hankalinshi kan Tony cikin bada Umarni yace"kaje Mota ganin zuwa"
da sauri Tony ya wuce, shi kuma ya sakai cikin falon bai kuma kallon gefan da Maryam take tsaye ba


A fili tace"yau zan nuna maka wannan maytar da dai da kake kirana kullum da ita.

Sai kawai ta rufa mishi baya

Momy Na zaune cikin kujera hannunta rike da romot tana canza tasha ta daga kai tana kallon Maryam cikin dariya tace"Dota yanzu nake zan canki a raina wallahi jiya kinsha aiki"


Maryam ta zauna kujarar dake fuskantar Momy tana murmushi tace"wane irin aiki kuma Momy"?


"Aikin towo mana , ai yayi albarka ma kiga my son duk rashin kin sa da abinci jiya towonki yayi mishi dadi gashi nan yana cin dumame"

Maryam ta kalli Nasir yana zaune kan daining, Yana cin towo,abin yayi mugun daure mata kai,tabbas da yasan itace tayi girkin tasan ba zai ci ba,amma dubi yadda ya zage yana cin yanzu.

Murmushi kawai tayi bata cewa Momyn komai ba


Momy tace"yawwa kafin ya kammala Dota gyara mishi dakin nasa,kin San dai halinshi"

Maryam ta ce"kai Momy wane irin hali ne da uncle din kuma"

"Rigama ne dashi kamar wani yaro kankani"
Momy tafada tana tabe Bak


Dariya Maryam tayi kawai ta nufi dakin Nasir din

Cikin mamaki ya bi bayanta da kallo ganin ta nufi Dakinshi ,ya girgiza kai kawai yace"wannan yarinyar batada zuciya wallahi amma yanzu yanzu zanyi maganinta.
[30/05/2019 10:10 AM] ®Binta Umar Abbale: Cikin sauri ya kammala ya mike yana gobe bakinshi da tussue, kai tsaye bedroom din nashi ya nufa ranshi a bace, Momy ta bishi da kallo tana cewa "ai yanzu nasa Maryam ta gyara maka dakin naka"


Bai saurari Momyn ba kawai ya Sakai cikin dakin nasa

Maryam Na jera filolilikan gado kawai taji an han kadata tafadi kan bed din kafin tayi wani yunkuri ya bita ya danne ta sosai ,suka fara kallon kallo ita dashi gabanta yana wani irin bugawa shi kuma fuskasa a hade take tamau ,kawai ya zira hannunshi guda cikin rigarta yana kokarin balle botiran rigar , Maryam ta gigice tana tunkude shi,amma kamar dotse ta ke turewa yace"uban wa ya baki izinin shigo min daki Dan uwarki"


Kai tsaye tace"Momy ce ta ce nazo in gyara maka"
Maryam tana sane tafadi haka in mai hankali ne shi ai Momyn ya zaga

"Vrygood"
Yarinya yau zaki san ni kike wa rashin kunya ,sai na yaga ki yanzu, kafin Maryam tace komai kawai taji yana kokarin tale mata kafafu, ta kwala kara tana kokarin mikewa zaune hannunta dafe da kirjinta sabida yayi nasarar balle mata botira duk mamanta sun fito a cikin briziyya.
[06/06, 01:48] +234 808 996 5176: [30/05/2019 10:51 PM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*98*

Sosai ya tale mata kafafu ya tsura mata kawai yana kallo , da kyar yace"mai yasa kullum kike zuwa kina damuna cikin bacci na yau sai kin fadamin ke mayya ce ko kuwa"
Yafada fuskarshi a murtuke

Kuka takeyi sosai tana dukanshi da duk hannunwata tace"Ka sakarmin kafafu mugu azzalimi Allah zai saka min"


Lumshe ido yayi yana bin ta da wani mayataccan kallo kanaganinshi kasan na tsantsar sha'awa ne.

Da kyar yace"in har kikaga na sake ki to ki tabbata kin yi min irin wannan abin da kikeyi min a cikin baccina"


Tana kuka tace"to zanyi maka ka sake ni"

Kirjinta ya zubawa ido yana kallo kamar wani tsohon maye

Tayi saurin sanya hannunta ta dafe

Ya sauke ajiyar zuciya sannan ya saketa har yanzu idonshi na kafe a kanta kamar zai cinye ta , shi kadai yasan abinda yake ji a jikinshi yarinyar ta tayar masa da muguwar sha'awa.


Mikewa tayi tana kuka ta kalleshi duk yayi bake bake a kan bed din ga kafafunta a cinyarshi cinyoyinta duk a waje ta janyo rigarta tana rufewa sai kukan bakin ciki takeyi Yau Nasir har pant din ta sai da yagani wannan abu da mai yayi kama

Ta mayar da botiran rigarta da sauri ta mike tsaye kan bed din tana kokarin dirga da kan gadon


Yayi saurin damkar hannunta idonsa jazir ya ce "na fada miki yau sai kiyi mini a zahiri sannan zan kyaleki ki tafi"


Cikin kuka ta fuxge hannunta tana nunashi da Dan ya tsa tace"Wallahi bazan taba yafe maka ba abinda kayimin mugu"


Cikin dauriya yace"nima bazan taba yafe miki ba abinda kike min muguwa azzalima kawai"


Maryam ta nufi kofa a fusace, yayi saurin tarar gabanta yana bin jikinta da kallo sosai yace"koma ki shiga toleit ki wanke fuskarki masharanciya wato zaki fita a haka Momy ta zaci nayi miki wani abu ko"
[30/05/2019 11:13 PM] ®Binta Umar Abbale: Domin ya kyaleta ta fita yasa ta nufi toleit din kamar yadda yace

Zama yayi gefan kadon sai nishi yakeyi sosai shi kadai yasan halin da yake ciki game da yarinyar


Maryam ta fito tana goge fuskarta , ya bita da kallo kawai har ta bude dakin ta fita


Momy na zaune a farlo taji shiru tayi yawa , ta kalleta cikin zargi tace" kin gama Dota Allah yasa dai bai ci zalinki ba"

Cikin "yar dariya tace" Momy kenan babu abinda yayi min na tsaya na hada masa wanki ne sannan Na matse masa kananun boxars din shi"


"To sannu Dota Allah yayi miki albarka"
Momy tafada cikin farin ciki


Maryam kwata-kwata bata son su hada ido da Momy sabida ta fuskanci kallon tuhuma Momyn take mata, sai kawai tayi mata sallama ta fice da Sauri


Momy ta bita da kallo cikin tsarguwa sai ta mike kawai ta nufi dakin Nasir din.

Maryam kuwa tayi da tasani yafi dubu da tasan abinda zai faru da bata soma zuwa ba



A kwance ta sameshi yayi rigingine ya zubawa POP din dake manne a saman dakin Momy tabi gadon da kallo ganin yadda duk ya hargishe ,wai nan an gyara,

Shigowar Momy bai sa shi ya dago kanshi ba sabida jikinshi ya bashi cewar ita ce


Ta tsaya a kanshi cikin kausassiyar murya tace"My son"


Ya dago kanshi ya na kallonta


Momy taga idonshi sunyi jazir sai gabanta yafadi, tabbas tayi ganganci da ta tura yarinyar dakinshi a halin tasan yananan


Jikinta a sanyaye tace"mai kayiwa yarinyar nan? naga kamar ta fita a hargitse"


Ya mutse fuska yayi yace"Momy ita baki tambayeta mai tayi min ba sai ni"


"Ba dole in tambaye ka ba, sabida nafi kowa sanin halinka"
Momy tafada cikin bacin rai


Mikewa zaune yayi jikinshi a sanyaye yace"Momy wane irin hali ne dani"?


"Kafi kowa sani ai"


Murmushi yayi mai ciwo yace"Momy kenan , ki tambayeta in da abinda nayi mata, wai mai yasa zuciyarki take wasiwasi a kai na ne , Momy mai zanyi da wannan zabiyar yarinya, ok tunda abin ya zama haka, kar ki kara turo ta tayi min gyara a dakina"
[30/05/2019 11:35 PM] ®Binta Umar Abbale: Momy tace"a kwai abinda ya faru tsakanika da ita myson ni ba Yarinya bace"


Dariya ce ta kashi sosai ya rika yi ganin yadda Momy ta dage tana tuhumarsa

Yace"ok toum Momy tunda kince haka sai kije kiyi mata ruwan zaki kawai"

Kunya ce ta kama Momyn ta kai masa duka a kanshi tace"baka da kunya ko Myson "

"To Momy kin dage sai tuhuma ta kikeyi wai mai nayi mata, ai in nayi mata wani abu daga lokacin da ta fita zaki ga alamu ko ta wurin tafiyarta ne"


Momy tace"to mubar naganar ma daga yau na daina sata tayi maka aiki yafi alkairi"


Tabe baki yayi kawai ya koma ya kwanta ,tace" ka fasa fita yanzu ne"

"Yanzu zan fita Momy ina hutawa ne"

"Ok sai ka fito"

Ya fi miti goma a kwance bayan fitar Momy din sai mutsu-mutsu yakeyi duk ya rasa inda zai sa kanshi da kyar dai ya mike ya nufi toleit ya sake yin wani wankan tun kafin ya gama yafara jin wani sanyi-sanyi yana ratsa shi a daddafe ya fito cikin karfin hali yake kimtsawa zazzabi ne yake so ya rufeshi ,haka dai ya daure ya gama kimtsawa ya fito cikin shirin fita

Momy ta kalli agogo tace"baka yi yamma ba kuwa myson dubi time"


"Momy karki damu Hospital kawai zan shiga daga nan babu inda zan je"

"To Allah ya tsare"
Momy tafada


Yana fita Giss dama yana tsaye ,sai kawai ya rufa masa baya Tony ya bude masa mota ya shiga yayi saurin zagayawa ya zauna gurinshi, Giss ya shiga Tony ya ja motar suka fita daga gidan.
[06/06, 01:48] +234 808 996 5176: [31/05/2019 8:53 AM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*99*

Bayan kwana biyu da faruwar al'amarin, Maryam ta rika kiyaye haduwarta da Nasir sabida wata irin kunyarsa take ji sosai kuma har yanzu soyyayrsa tana nan daram a cikin zuciyarta

Yau misalin Tara Na dare suna zaune ita da Abdul a harabar gidan suna hira cikin nishadi ,shima yau kwanansa biyu da dawowa sosai Maryam tayi kwalliya tana cikin atamfa "yar Ghana anyi mata duguwar riga mai babban hannu sosai tayi kyau ta yafa mayafi kalar kayan fuskarta ta sha kwalliya suna zaune a cikin wasu kujeru farare masu kyau


Abdul yace"insha Allahu a satinan za'akawo komai na aure za'a sa sati hudu daurin aure, in naje nadawo"


Maryam ta sunkuyar da kanta cikin jin kunya tace"to Allah ya kaimu"


Yace" maganar aikinki kuma zan samu Nasir da takkadunki nasan bazai ki daukirki ba tunda tunda takkadunki sunyi
kyau

Da sauri ta dago kai tana kallonsa jin abinda yace


Tace" Kana ganin zai dauke ni kuwa kasan bama shiri dashi"


Dariya Abdul yayi yace"karki damu nasan yadda zanyi dashi"


Sai wajan karfe goma da rabi Abdul ya mike da niyar tafiya bayan ya aje wasu manya manyan ledoji


Maryam ta mike ta biyo bayanshi suna tafiya suna hira har ya karaso kusa da motarshi, ya shiga yana kokarin fita , Mai gadi ya bude get din Nasir motar Nasir ta shigo cikin gidan


Sai ya kashe motar kawai ya fito yana jiranshi Maryam na tsaye a gefanshi kanta a kasa,Sam bataso ta hada ido da Nasir din



Giss ya bude masa kofa ya fito ,fuskarshi babu yabo ballasa ya mikawa Abdul hannu suka gaisa


Abdul yace" yanzu nake zan can kada ma"

Fuskarshi ya saki yace" yaushe kadawo ne Alhaji"


"Yau kwana biyu da dawowa wallahi, nazo ganin amarya na"

"Ok andawo lafiya ya aiki"?
Nasir yafada yana binshi da wani kallo jin abinda yace


"Alhmdullhi wallahi komai normal"


Nasir ya zare hannunshi cikin gajiya yace"zan shiga ciki Abdul nima Na gaji ,gashi gobe nake saran zan wuce america amma bazan dade ba"


"Allah ya kaimu da jirgin safe zaka bi ko na yamma"?

"Na yamma"
Nasir yafada yana kokarin barin gurin

Abdul yace "zan shigo da wuri insha Allahu a kwai alfarmar da nake nema a gurinka"


"Allah ya kaimu lafia"
Yafada yana wucewa Giss ya na take masa baya

Duk wannan abinda yake faruwa Maryam kanta a kasa tana jin duk irin share-sharen da Nasir yakeyi shi kuma Abdul din sai wani binshi yakeyi lallai ta yadda Farin jini da daukaka a jininsa take
[31/05/2019 9:17 AM] ®Binta Umar Abbale: Ita yanzu ta daina shiga sabgarsa ma kwata-kwata sabida ta lura ba karamin dan iska bane


Abdul yayi mata sallama ya wuce ita kuma jiki a sanyaye ta wuce bangarqnsu



Momy na zaune cikin kujera tana kallo kuma tana jiran shigowar Nasir din sabida bayan fitarshi dazu Alh Salisu yazo ya kare mata rashin mutumci wai itace take zigashi yakeyin duk abinda yakeyi cikinsu babu Wanda yake gani da gashi ,sabida haka lallai in ya dawo ta ce masa yaje yana naimanshi ,aura shi da Mubina babu fashi, tunda haka Mahaifinshi yace kafin rasuwarshi.


Momy ranta ya baci domin har kuka sai da tayi tunda take babu mutumin da ya taba tsayawa a kanta yayi mata cin nutumcin da Alh Salisu yayi mata yau, sabida haka mutukar ita ta haifi Nasir dole ne ya auri Mubina inyaso daga baya sai ya auri zabinshi.



Yayi Sallama ya shigo Momy ta bishi da kallo har ya karaso kusa da ita ya zauna, ita kanta tausayinsa takeji ganin yadda girma ya hau kanshi da kananun shekarunshi amma da yake *Yaron* yana da ilimi cikin nutsuwa yake tafi da komai


Yace"Momy na gaji wallahi"

Cikin tausayi ta kalleshi ,ta kasa cewa komai ma


Sai ya dago kai yana kallonta jin har ya shigo yayi magana Momy bata tanka mashi
Lallai akwai wani Abu


Ya gyara zamanshi sosai yace"Momy menene,? Bafa nasan in ganki cikin damuwa, uhmm lafiya lau Na fita na barki"



"Myson lafia ba lafiya ba"
Momy tafada tana gyara zama sosai tana fuskartansa


"Tell me"
"Momy fada min ko manene kinji"


"Dazu bayan fitarka Kawunka yazo har cikin falon nan ya karemin zagi sosai wai lallai sai ka auri diyarshi ,sabida haka mutukar nice Na haifeka dole ne ka aureta domin mu samu kwanciyar hankali"


Ranshi ya baci mutuka jin abinda Momy take fada masa


Yace"Momy kikace "uncle Salisu yazo gida ya zage ki to akan me"?


"Ga dalili nan na fada maka"
Momy tafada


"Ouk sabida a auri "yarshi yazo har gida ya zageki"
Yafada a zafafe sai huci yakeyi"

"Cam down My son, ban fada maka wannan magana ba fa domin ta daga maka hankali, kuma bance in kaje kayi mishi rashin kirki ba, ni dai kawai ga umarnin da na baka"



Shiru yayi kawai ya koma ya kwanta hade da rimtse idonsa lallai dole yayiwa tufkar hanci domin kuwa babu shegan da ya'isa yazo ya runka tadaga mahaifiyarshi hankali wallahi ,sabida a halin yanzu ita kadai ce ta rage masa
[31/05/2019 9:28 AM] ®Binta Umar Abbale: Momy tace"kayi shiru ba kace komai ba My son don Allah ka fitar dani kunya, wallahi nagaji da wannan cin mutumci"


Da kyar ya dago kanshi ya zuba mata idonshi wadanda suka sauya kala yace"Momy kinaso in auri Mubina ko"?


"Inaso mai My son"

"Ki kwantar da hankalinki insha Allahu zan aureta tunda kinaso"


Momy ta saki fuska sosai tace"Allah yayi maka Albarka My son Ubangiji ya shiga al'amarinka, yadda kake bina kaima In sha Allahu naka yaran zasu bika"


Mikewa tsaye yayi yace"Momy nagode da addu'a, zan shiga ciki"


"Ba zakaci abinci ba ne"?
Momy ta tambayeshi


Shiru yayi yana Dan murmushi

Itama Murmushin tayi tace"OK zakayi halin naka ko"

Sai ya saki dariya kawai yace" Momy ni tun a motana na cika cikina,in kinason saura in dauko miki"


"A'a rabani da kayan zaqi nan"
Momy tafada tana tabe baki
[06/06, 01:49] +234 808 996 5176: [31/05/2019 4:58 PM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*100*

Murmushi yayi kawai ya wuce dakinsa, zuciyarsa sai zafi take yi, shi yarasa mai yasa mutane sukeyin haka, amma dole zai tari Uncle dinsa, ya kiyaye zuwa gurin Momynshi yana bata mata rai duk abinda ya dameshi yafi mutumci ya tunkareshi da maganar
Amma Sam! Bazai yadda da bacin ran Momynshi ba.



Karfe goma shaura Abdul latif ya shigo gidan yayi parking din motarshi Nasir din ya kira a waya "hello Abdul din yafada bayan yaji andauki wayar

"Kashigo ne"?
Nasir din ya fada

"Eh kana part dinka ko kana gurin Momy"?

"Kashigo gurin Momy kawai"

"Ok"
Abdul yafada ya kashe wayar


Momy Na zaune cikin kwalliya kamar ko da yaushe, suka gaisa da Abdul cikin sakin fuska tana tambayarshi mutan gida

"Lafiya kalau Momy"

"To masha Allahu"

Nasir yana zaune kan kujera cin abinci ,hannunshi rike da waya yana latsawa Abdul ya karasa inda yake ya zauna kujara guda, gami da mika masa hannu
"Ya a kayi ne Alhaji"
Nasir yafada hannushi rike da hannun Abdul din


"Normal Alhaji"
Abdul yafada yana dariya


Yace"ya shirye-shirye"?

"Na kammala sai tafiya kawai"

"OK kasan abinda ya kawoni gurin ka"?

"Sai kafada"
Nasir ya fada yana danna waya


"Zan kawo maka takkadun Maryam ka duba don Allah ka dauke ta aiki a hospital dinka ,kasan a nan zan barta cikin Estet din mu Na family kafin in kammala ginina ,in kuma nasamu gurin zama zan dauketa mu tafi tare"


Ba tare da ya kalleshi ba yace"wacece Maryam"?


Abdul ya sha kunu yace"bana son iskanci fa"


Fuskarshi ya hade yace"ban fahimci wace Maryam kake nufi ba,ai shiyasa na tambayeka"

"Ok My wife dina yarinyar gidan nan"
Abdul yafada babu wasa a fuskarshi


Nasir ya dago kanshi yana kallonsa tsawon minti uku bai ce komai ba, ya saki Murmushi gami da cewa "a yanzu dai bama bukatar ma'aikata, in ma muna bukata to batayi ilimin da zata yi aiki a wannan asibitin ba"


"Mai kake nufi"?
Abdul yafada rai a bace


"Bana nufin komai"
Yafada hankalinshi Na kan wayarshi


"Look Nasir ka tsaya kayi min maganar da zan fahimta bafa na son wulakancin ka Wanda ka saba"
Abdul yafada ranshi a mugun bace


Momy ta waiwayo da sauri ganin yadda Abdul din yake daga murya tace"lafiya wai naji kuna magana Sama-sama"?
[31/05/2019 5:21 PM] ®Binta Umar Abbale: "Momy wai sabida yaron nan bai da kirki nace masa, ya dauki yarinyar nan aiki a asibitinsa, shine yake fada min magana"


Momy ta kalleshi tana murmushi tace"duk abin ai ba Na zafi bane Abdul wace yarinya kake magana a kai"


"Momy Maryam nake miki magana fa"


"Ok Dota wai"?

"Eh Momy"?
Abdul ya fada yana mikewa tsaye ranshi a bace


Momy ta kalli Nasir yana zaune har'ila yau hankalinshi na kan wayarshi


Tace"Myson Dan Allah ina Neman alfarma nima ka dauketa aiki,wai maiye duniyar ne ,tunda dai Abdul din ya amince tayi ai shikkenan , Wanda ya taimaki wani shima Allah zai tai makeshi"


"Momy ki rabu dashi don Allah kar Allah yasa ya dauketa zan cigaba da nema mata"


"A'a duk baza ayi haka ba , ka koma ka zauna mu kashe magana"
Momy tafada tana kallon Abdul din

A gogo ya kalla yace"Momy wucewa zanyi wallahi banason abin bacin rai , zamu iya rigima dashi yanzu"


Cikin mamaki Momy tace"akan mace zakuyi rigima da Dan uwanka Abdul"?


Kunya ta kamashi sai ya sunkuyar da kanshi kawai


Momy tace"koma ka zauna"

Ya koma ya zauna kawai gami da dauke kanshi yaki yadda ya kalli Nasir din

Shi kuwa babu abinda ya dameshi


Momy tace"Myson "mai kace a kan maganar"?


Tafi minti biyu kafin yayi magana, daga bisani yace"Momy ni a yanzu bani da lokaci amma zata iya zuwa gurin Dr Sofia tayi mata intervio shikkenan sai ta ajeta a matsayin da ya dace"



"To ai babu matsala sai taje din"
Momy tafada,ta cigaba da cewa kai Abdul kaji abinda yace"


"Momy babu komai ai sai taje tunda naima takeyi,Allah ya rufa asiri"


"Ameen ameen"
Momy tafada ta cigaba da cewa dan Allah kar Ku yadda wata mace ta farraqa tsakaninku kunji ko"


"Momy kar kidamu insha'Allah"
Abdul din yafada yana mikewa da niyyar tafiya yayiwa Momy sallama




Bayan fitarshi Momy tace"don Allah my son ka rage girman kan nan gami da izza domin babu inda zata kai ka"



Dariya yayi sosai har sai da habarshi ta lo6a yana kallon Momy din yace" Momy yaya ake girman kai don Allah mutane da dama suna fadin haka a gareni , basu San cewar ni haka nuture dina ne ba"



"E ai duk da haka my son kana karawa da wani ni dai nace ka daina"


"Insha Allahu Momy kiyi min addu'a"


Momy ta zauna suka cigaba da hira cikin so da kaunar juna.
[06/06, 01:49] +234 808 996 5176: [01/06/2019 5:11 PM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*101*
Nasir bai tafi America ba sai da yaje gurin kawunshi Salisu, sabida yadda yaga Hankalin Momy shi ya tashi a kan al'amari, nan uncle Salisu ya rika kwantar da kanshi yana rarrashinsa, da yayi hakuri ya auri Mubina, Nasir yayi mamaki ganin yadda yake kwantar masa da kai sai kawai ya basar , yace" magana ta wuce amma don Allah kar ka kara tayarmin da hankalin Momy domin abinda kayi mata ya daga mata hankali, zan wuce america, sati biyu zanyi zan dawo in yaso sai muyi maganar, Abin mamaki Dadyn Mubina ya dinga washe baki yana shi wa Nasir albarka nan Nasir ya tafi ya barshi sai mamakinshi yake,lallai mutane basu da kirki, wato in kana da kudi komai kafada dai-dai ne ,shi kanshi yasan ba don Allah uncle din nashi yakeso ya hadashi aure da diyarshi ba.


****
Yau satin daya da tafiyar Nasir ,Abdul ma ya tafi bayan ya kammala komai na maganar aure rana kawai ake jira,cikin so da kaunar juna sukayi sallama da Maryam.


Momy kadaici duk ya dameta sai ta fito harbar gidan ta zauna kan kujera kawai nan su Nafi'u suke zama da'ita suna hira Maryam ma sai ta samu gurin zuwa , siyi ta hira cikin fahimta



Ranar Momy ta tashi ta shiga ciki sai ta bar wayarta kan kujera Maryam na zaune suna chating da Abdul sai Murmushi takeyi kawai da'alama hirar tana mata dadi


Wayar Momy tafara kara da sauri ta kalli fuskar wayar, Myson ta gani yana yawo a fuskar wayar.


Gabanta ya fadi tayi kamar ta dauka wata zuciyar tace kar ki dauka, wayar ta katse kafin ta farga wani kiran ya kara shigowa,


Sai da takusa katsewa sannan ta daga batare da tace uffan ba


Ajiyar zuciya taji yana saukewa kafin taji wani irin voice da ya kusa sumar da ita a zaune Momynahhh"
Taji ya fada yana ajiye numfashi



Shiru babu magana

"Please Momy kiyi min magana mana yinin yau banji muryarki ba ayyuka sun dame ni"


Maryam tana ta kokawa da zuciyarta, jikinta yayi bala'in daukar dumi domin Nasir ya gama kashe mata gangar jiki, gaskiya tana bala'in kaunar Nasir



"Momy"
Maryam taji yafada da ainihin muryarsa ,sai taji kamar ma acikin damuwa yake

Sai tayi saurin kashe wayar tana sauke ajiyar zuciya daki-dai
[01/06/2019 5:38 PM] ®Binta Umar Abbale: Momy ta dawo gurin, ta kalli Maryam dake zaune tace"Dota na barki ke kadai ko"


Maryam tayi murmushi tace"A'a Momy chating nakeyi ma"



Wani kiran ne ya kara shigowa wayar Momy a karo na uku


Momy tayi saurin daukar wayar tana dariya


Tace"Myson yau nayi fushi ,nayi ta tsammanin kiranka tun da safe naji shiru nace Allah yasa lafiya"


Ajiyar zuciya ya sauke yace"Momy ina ta magana shine kika shareni ko"


Cikin mamaki tace"yaushe akayi haka, My son"?


"Yanzu Momy na kira sau biyu ina ta magana naji shiru"


Momy tayi murmushi tana kallon Maryam tace"ba nice na daga wayar ba Myson Dota ce wallahi ni Na shiga cikin gida"


Shiru yayi na minti biyu sannan yace"Momy mun gama magana da uncle ,in nadawo za mu tsayar da magana ina fatan haka yayi miki"


"Yayi dai-dai Allah yayi maka albarka"


"Ameen ameen Momyna"

Sukayi shira sama-sama sannan yayi mata sallama dama a cikin busy yake yanzu ma free ya samu shiyasa ya kirata sabida duk abinda

1 Comments On YARO DA KUDI
avatar
magaji-2

1 year ago

Reply

Allah Yakara budi

Please Login or Register in order to submit comment