Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tunani, ta hana shi nutsatstsen bacci, kullum se tunaninta, da hango kyakkyawar fuskarta.

"Lallai Allah me halitta." Ya faɗa sanda Didi ta ƙaraso wajen, lokacin kuma da ya gama fahimtar lallai da gasken dole ne ya ruɗe, ya kasa bambance wadda ya fara gani har ta tafi da shi. Wani irin sabon sonta ya tsirga masa tun daga kansa har ƙafa. Ya ɗan lumshe idanunsa kafin ya buɗe yana amsa sallamarta ta kana ya ɗora da

"Amincin Allah ya tabbata a gareki ya ke wannan kyakkyawar ma'abociyar kwarjini."

"Ameen kaima haka." Didi ta faɗa tana ji kamar ta tashi daga wajen ta ruga zuwa cikin gida, musamman saboda yadda kanta ke ciwo, da kuma yanda take jin wani banbarakwai, tana kuma ji kamar saɓo take aikatawa zaman nata da wani namiji a irin shekarunsu.

"Kin wahalar min da zuciya Kyakkyawatah." Ya faɗa a narke kamar wani ƙaramin yaro, har se da hakan ya sanyata saurin ɗaga ido ta kalle shi. Ya sakar mata wani murmushi yana sake langaɓar da kai gefe kamar yaron goye lokaci ɗaya yana furta

"Da gaske na ke fa. Na san da yau ta wuce ban yi ido huɗu da fuskarki ba za a iya ganina a gadon asibiti, saboda yanda ko da yaushe zuciyata ke harbawa saboda ƙaunarki.." yanzun ma dai ƙare maganar ya yi a shagwaɓe. Daidai lokacin da wayarsa ta soma ringing kenan. Se ya kalleta a nutse yace bayan ya sakar mata murmushi

"1mint pls.." ya yi maganar yana miƙewa. Itama miƙewar ta yi ta soma takawa zuwa inda Lulu take. Haushi da takaici kamar su karta.

"Didi me ya faru?" Lulu ta tambaya tana kallan yanda Didin ta haɗe rai kamar wadda aka daka.

"Ɗan iska ne!.." Da sauri Lulu ta buɗe ido sosai tace cikin rashin fahimta

"Ɗan iska kuma?" Ta yi maganar manyan kyawawan idanunta a waje.

"Ehh mana.. Ni ze yi wa shagwaɓa." Didi ta faɗa tana harara kamar Kaseem ɗin na gabanta..


https://chat.whatsapp.com/BClMNPwWybg2n3oRvtemv8

*♡☆A JINI TAKE☆♡*
*(IZZATA)*


By
_*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_


*CHAPTER ONE*

Page_15

___Dariya Lulu ta sheƙe da ita har da sunkuyawa. Se da ta yi me isarta sannan ta ɗago tana kallan Didi tace

"Shagwaɓa kuma Didi? Ƙato da shi?" Taɓe baki Didi ta yi sannan tace

"Ehh fa, ba kyan gani.." ta ɗan dakata daga nan se kuma ta ɗora da

"Ke mu tafi gida, ni jikina ma rawa yake yi tun ɗazu.."

"Allah nima haka" Lulu ta faɗa tana riƙe hannun Didin dan komawa gida. Se kuma Didi ta dakata a hankali tace

"Amma kamar ba mu kyauta ba koh?" Cikin mamaki Lulu tace

"Me muka yi?"

"Da zamu tafi mana ba sallama" Shiru Lulu ta ɗan yi na sakanni, se kuma can tace

"Toh mu je mu ce masa se da safe." Duk se suka juya suka soma komawa zuwa inda Kaseem ɗin yake, aikuwa daidai lokacin da shima ya gama wayar da yake yi. Se da ya sakar musu murmushi sannan yace yana kallansu su duka

"Tabarakallah Masha Allah.." ya faɗa sanda ya sake tabbatar da lallai kamannin nasu sakk da sakk ne wanda shi dai be ga wani banbanci ba. Ba dan hijab ɗin jikinsu kala daban daban ba ne da babu yanda za a yi ya gane Didin tasa.

"Lafiya dai koh Gimbiyata?" Ya yi maganar yana kallan Didi. Sosai dariya ta ciyo Lulu se dai ta maza ta yi ta a cikin ranta, a kan laɓɓanta ta furta

"Wai gimbiya.." yayin da Didi kuwa waɗannan sunayen da yake ta kiranta da su ita haushi ma suke bata. Daga ganin mutum kawai se ya dinga ce mata Gimbiya. Gashi kuma dama tun ɗazu a tsorace take saboda wannan sabon al'amarin na keɓewa da namiji su yi magana.

"Tafiya zamu yi." Ta faɗa cikin sanyin nan nata. Lumshe idanunsa Kaseem ya yi yana jin muryarta ta har cikin zuciyarsa, sannan ya yi murmushi yace

"Kin gaji ne?" Da sauri ta jinjina kai. Se ya sake yin murmushin kafin yace

"Tohm shi kenan. Bari na tafi amma fa zan dawo. Ki kula min da kanki. Allah kuma ya tsare min ke a ko ina.." Wata irin kunya ce ta lulluɓe Didin, ita har ga Allah kunya yake ta bata, babba da shi ya dinga irin waɗannan maganganun. Se dai kuma haka kawai ta tsinci kanta da yin murmushi da kuma dena jin haushinsa da ta ji a farko. Ita kam Lulu se ta juya kamar ta fashe da dariya a wajen.

"Toh" shi ne kaɗai abin da Didi ta iya furtawa.

"Good nyt Twinnynmu" ya yi maganar yana kallan Lulu.

"Uhmm" Lulu ta faɗa bayan ta juyo tana ƙaƙalo murmushin yaƙe. Daga haka suka juya a tare zuwa cikin gidan. Se ya yi murmushi yana jin yanda zuciyarsa ta yi wani irin sanyi, yau ɗin se yake jinsa kamar yafi kowa dace tunda ya yi tozali da kyakkyawarsa. Kai tsaye ficewa ya yi daga gidan ya hau motarsa ya soma driving cike da farin ciki. Ba ya jin ze iya sake yin ko da kwana 1 ne be sanyata a idanunsa ko ya ji muryarta ba.

"Oh my god.." ya faɗa sanda ya tuna be karɓi contact ɗinta ba.

"Ya aka yi haka ne? Me ya mantar dani?" Ya yi tambayar kamar akwai wani a gefensa da ze ba shi amsar. Jin shiru ne ya sanya shi lalubo amsar da kansa, ya san tabbas ganinta da ya yi ne ya mantar da shi ma wata number. Aikuwa ya yi babbar mantuwa wanda dole ne ya koma ko dan nemo abin da ze sanya shi dinga jin muryarta ko da yaushe.

A compound ɗin gidan ya ajje motarsa kasancewar babu wanda be san shi cikin gidan ba, shi yasa be samu tsaiko ba a lokacin da ze shigo. Dan haka yana gama parking se ya sakko daga motar har lokacin murmushi yaƙi barin fuskarsa ya wuce parlourn Daddy bayan sun yi waya da shi. Da sallama ya shiga cikin parlourn, Daddy na zaune a kan wasu haɗaɗɗun kujeru da ke zaune a can wani gefe cikin ɗakin, waɗanɗa da alama an yi su ne dan hutawa ko kuma karatu. Daddyn na zaune kan kujera yana karanta jarida idanunsa sanye cikin wani glass da ya matuƙar amsar kyakkyawar fuskarsa me kama da ta Bad Man.

"Barka da wannan lokaci Daddy" Kaseem ya faɗa sanda ya nemi waje a ƙasan kujerar Daddy ya zauna. Murmushi Daddy ya yi yana ajje jaridar hannunsa sannan ya saka hannu ya sauke glass ɗin fuskarsa kana yace

"Barka dai Kaseem. Ka shigo?"

"Ehh Daddy.."

"Toh barka da zuwa.. Ina ɗan uwan naka?"

"Na ɗauka ma zan same shi a nan ɗin ai Daddy. Buh let me call him." Ya yi maganar yana fito da wayarsa dake cikin aljihu.

"Nop! let me call him my self." Daddy ya faɗa yana ɗaukar rantststsiyar wayarsa dake a gefensa ya ɗakko number Bad Man ɗin ya kira. Ringing 1_2 ya ɗaga.

"Kana ina?" Daddy ya tambaya. Daga can ɓangaren ya ɗora wata hula me kyau a kansa sannan yace

"Ina ɗakina."

"Amma ka manta maganar da muka yi?"

"Ohhh sorry Dad.. Bari na zo." Ya faɗa yana takawa zuwa kan gado ya zauna ya shiga gyara zaman takalminsa. Be daɗe cikin parlourn ba ya fito zuwa sashen Daddyn se zuba ƙamshin daɗɗaɗan turarensa yake yi, tafiyarsa kaɗai abin kallo ce, haka zalika kayan dake jikinsa ma na tashin kai ne. A haka har ya ƙarasa parlourn Daddyn.

"Sannu da hutawa.." Bad Man ya faɗa bayan ya zauna a kan kujerar gefen Daddy ya ɗauki ƙafa ɗaya ya ɗorata a kan ɗaya. Wani kallo Daddyn ya watsa masa ba tare da yace komai ba. Se ya ɗan buɗe baki sannan ya saka hannunsa ya sauke hular dake kansa kana yace

"Sorry Sir.." ya faɗa yana saukar da ƙafar da ya ɗora a kan ɗayar. Se a lokacin sannan Daddy ya kalli Kaseem yace

"Koma kan kujerar." Ya san halin Daddyn ba ƙaunar musu yake yi ba musamman kasancewarsa mutum me zafi dan haka kawai se ya hau kan kujerar kusa da Bad Man ya zauna. Se a lokacin suka gaisa, duk da basu daɗe da yin magana a waya ba. Bayan wajen minti 2 Daddy yace

"Amm kai Areef.. ga ɗan uwanka nan In Sha Allah zuwa nan da sati 2 nake so ku soma kasuwancinku na ƙashin kanku. Ba na so kowa ya zauna ƙarƙashina, hakan ba abin tutiya bane. Na fi so dukanku ku ci gashin kanku." Jinjina kai Kaseem ya yi sannan yace

"Muna godiya sosai Daddy. Allah ya ƙara girma da arziƙi me amfani."

"Ameen ya rabb" Daddy ya yi maganar yana maida dubansa kan Bad da ke danna wayarsa. Duk da ya ji abin da Daddyn ya faɗa se dai shi gaba ɗaya hankalinsa ma na kan Hero da suke magana, yanzu kuma ya ji Daddyn na maganar kasuwanci, hakan na nufin ko da yaushe ze iya fita daga gida ba tare da wani takunkumi ba.

"Heyy!" Daddy ya faɗa yana kallan nasa. Kamar kuwa ya san da shi ake, daidai lokacin da ya ajje wayar ya ɗaga kai ya kalli Daddyn kana yace

"Hakan ya yi. Duk da dai na so na ɗan ƙara hutawa amma babu damuwa." Ya faɗa cikin er basarwa yana cizon lips ɗinsa na ƙasa lokaci ɗaya wani ƙawataccen murmushi na tashi a kan kyakkyawar fuskarsa. Jinjina kai Daddy ya yi sannan yace

"Tohm shi kenan, Allah ya taimaka. Yanzu se ku faɗa min duk wani abu da kuke buƙata, ina so ne a yau na sallameku zan shiga wasu sabgogin ne."


.. A ɓangarensu Lulu kuwa lokacin da suka koma cikin ɗakin su Abba basa nan, hakan ne ya sanyasu wucewa nasu ɗakin kawai. Ajiyar zuciya Didi ta sauke sanda ta zauna a gefen gadonsu tana faɗin

"Na shiga ukuna." Ta yi maganar tana dafe ƙirji. Da sauri Lulu ta ƙaraso tana faɗin

"Me ya faru Didi?" Se kuma ta girgiza kai tace bayan ta ɓata fuska

"Ba komai fa. Amma kuma me yasa Abba yace mu je wai? Na ga dai idan mutum ya fara zance ai aure ake masa koh?" Didi ta faɗa tana kallan Lulu. Ɗan ɗage idanu Lulu ta yi kafin tace cike da tsokana

"Umm ƙila aurar da Didina ze yi." Duka Didi ta kaiwa Lulun, se ta yi saurin tashi daga wajen tana dariya lokaci ɗaya tana faɗin

"Sorry my luv. Da wasa fa nake wallahi." Ta faɗa dan ta ga alamar Didin ta ɗauka da gaske take.

"Ni dai zuwa zan yi na maimaita karatu, gobe islamiyya.." Didi ta faɗa tana ƙarasawa wajen jakarta ta ɗauka. Wani irin bugawa zuciyar Lulu ta yi sanda ta tuna da abin da ya faru, ita sam ta manta se yanzu da Didin ta yi maganar islamiyya sannan ta tuna. Se ta nemi waje kawai ta zauna tana lumshe idanunta. Bata ankara ba se ji ta yi Didi ta dafa kafaɗarta a hankali, cikin rarrashi tace

"Lulu me ya faru ne wai?" Da sauri ta riƙo hannun Didin sosai sanda farar fuskarta ta ɗan yi ja ta soma faɗin

"Didi mutane abin tsoro ne, na tsorata matuƙa. Na rasa yanda zan yi na faɗa miki ko ke ko Ammi. Amma ina tsoron na yi shiru ta je ta cigaba da jan mutane." Cikin rashin fahimta Didi tace

"Wai a kan me ki ke magana ne? Wace ce?"

"Abida.." Lulu ta faɗa. Daga haka ta shiga labartawa Didi abin da ya faru tun daga farko har ƙarshe. Gaba ɗaya Didin se ta ruɗe, ilahirin jikinta ya ɗauki rawa. Se ta ja Lulun jikinta tana faɗin muryarta na rawa, har idanunta sun kawo ƙwalla

"Babu abin da suka miki koh? Ba su miki komai ba koh?" Jinjina kai Lulu ta yi kafin tace

"Ehh fa Didi."

"Tashi mu je mu faɗawa Ammi." Didi ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa. Da sauri Lulu ta riƙota tana girgiza kai tace

"Kin san dai halin Ammi, yanzun nan za ta ɗaga hankalinta har abin ya zo ya dinga damunta. Ki yi shiru kawai tunda dai Allah ya kuɓutar dani.." girgiza kai Didi ta yi tace

"A'ah gwara kawai a faɗa mata ɗin."

"A'ah Didi, mu bar shi kawai a tsakaninmu se kuma a islamiyya da zan tona mata asiri." Buɗe ido Didi ta yi tace bayan ta girgiza kai

"Kin san mene tonon asiri kuwa Lulu? Ai ta riga ta san kin santa, ba za ta nuna halinta a makarantar nan ba. Se dai kawai a yi mata barazana saboda tsaro. Ke idan ma tana tsoron ka da asirinta ya tonu za ki ga ta ja baya da zuwa makarantar, mu kuma daga yau za mu dinga saka mata ido, idan hakan ya yi toh shi kenan, idan kuma be yi ba se mu sanar da wani malamin."

"Amma Didi.." lumshe idanunta Didi ta yi tana jinjinawa Lulun kai. Ba dan ta so ba tace

"Toh Allah ya ƙara tsarewa."

"Ameen." Didi ta faɗa tana tuna yanda tun farko ta kasa aminta da yarinyar, ashe mutuniyar banza ce, shi ne hadda ɗauko ƙazaman ƙafafuwanta ta zo gidansu. Se ta girgiza kai kawai, daidai lokacin da Ammi ta shigo ɗakin

"Me ya faru?" Ta tambaya sanda ta gansu kamar masu zaman makoki. Da sauri dukansu suka wanzar da murmushi kan fuskarsu kafin suka ce

"Babu komai Ammi." Duk da bata yarda ba, amma se ta bar shi ɗin kawai, a tunaninta may be magana ce a tsakaninsu da basa so ta sani, dan ta san idan da suna so ta sani ɗin su da kansu zasu zo su faɗa mata.


... Kiran wayar Ladi da ya shigo cikin ƙatuwar wayarta Abida ta kalla. ta ja doguwar ajiyar zuciya tana tunanin yanda za ta ɓillowa Ladi, tun farko ta sani ba ta kai mata zancen Lulu ba, da yanzu ita da kanta za ta dinga fakar Lulun tunda itama tana sonta. Se dai kuma tunda Ladin ta ƙyalla ido a kanta ya zama dole ita ta haƙura da ita. A karo na barkatai kiran Ladin ya sake shigowa cikin wayarta, se ta jefar da wayar gefe tana faɗin

"Na shiga ukuna.." ta yi maganar tana dafe kanta, ita kam yau ta ga ta kanta. Ba za ta iya ɗaga kiran Ladin ba, dan ko ta ɗaga ma ba ta san me za tace mata ba, saboda ta tabbatar maganar Lulu za ta mata. Se dai kuma ta san shi kansa rashin ɗaga kiran matsala ne, hakan ne ya sanyata janyo wayar ta kasheta gaba ɗaya. Tun ɗazu take kwance a gida ta kasa fita ko nan da can ne, ballantana kuma a yi zancen islamiyya, dan ita dai har yanzu tsoron zuwa take bare ta haɗu da Lulu, dan ita kanta za ta iya zama sheda a kan Lulun ba ta da kirki. Ta riga ta tsara yau ba za ta je makarantar ba, duk yadda ake ciki dai se gobe za ta je, kafin lokacin ta gama tsarawa kanta yadda za ta ɓillowa Lulun har ta yadda da ita ta sake kaita wajen Ladi. Hakan ne ya sanyata gyara kwanciyarta ta soma saƙawa da warwarewa duk a kan Lulun.


___"Duk wanda ba shi da littafin ya fita.." Gwani ya yi maganar lokacin da yake buɗe nasa littafin. Kallan Lulu Didi ta yi ganin tana shirin miƙewa, dama ita haka take so, dan ba ƙauna ma take ya dinga shigo musu aji ba.

"Wai dama ba ki zo da shi ba?" Didi ta tambaya ƙasa_ƙasa. Jinjina kai ta yi tana ɓata fuska

"Allah kuwa se na faɗawa Ammi wannan rashin kirkin da kike yi." Didi ta faɗa tana ɗauke kai ta maida kanta kan littafin hannunta. Ita dai Lulu burinta kawai ta fice daga ajin. Se kuwa ta saɓi jiki tana wani ciccin magani ita a lallai dole kar ya rainata. Ko kallan sharar da ta kwasota be yi ba, kai ba ma za ka ce ya san ta fita ba. Se dai tana ficewar ya yi gyaran murya sannan ya yi sallama cikin muryar nan tasa da duk lokacin da yake larabci ba za ka yi tunanin idan ka yi masa hausa ze ji ba. Cike da farin ciki Lulu kuwa ta nemi wani aji da babu kowa a ciki ta zauna, dama tana sane taƙi zuwa da littafin dan ya koreta. Se kuwa ta zauna abinta inda ta san har ya gama ba za ta jiyo muryarsa ba. Kafin a tashi Gwani ya bar makarantar zuwa asibiti, dan haka se Malam Ahmad ya shigo ya karɓi ajin. Se a lokacin sannan Lulu ta shigo ajin, tana ƙoƙarin ƙarasawa kusa da Didi ta jiyo muryar Malam Ahmad ɗin na faɗin

"Afaaf Muhammad Aji.." se ta dakata sannan ta ɗaga kanta ta kalle shi kana ta amsa da

"Na'am.."

"Daga ina?" Ya tambaya yana kallanta. Dan tsabar shaƙiyanci da rashin kirki irin na Lulu, se ta ɗan yi shiru a ranta tana tuna sunan da ya kamata ta yi amfani da shi ba tare da ta ambaci sunan Gwani ba, dan se take ji kamar ta manta sunan nasa ma, hakan ne ya sanyata faɗin

"Littafi ne ba ni da shi, shi ne ya koreni.."

"Waye..?" Ya sake tambaya. Ji ta yi kamar kawai ta yi wucewarta ba tare da ta amsa masa tambayar ba, se dai ba ta yi hakan ba. Amma kenan yana nufin dole dai se ta faɗi sunan kuma ta fara faɗar wata kalmar girmamawar kafin sunan shi. Duk da baya kusa amma ai mutane suna ji.

"Amma ya aka yi ke Afrah ki ke da shi?" Malam Ahmad ya katseta da faɗin hakan yana kallan Didi. Se da Didi ta sauke ajiyar zuciya sannan cikin niƙab ɗinta ta furta

"Ya mu'allim manta guda ɗaya muka yi a gida." Ɗan numfashi kaɗan ya sauke sannan yace

"Shi kenan, je ki zauna." A hankali ta ƙarasa cikin ajin ta nemi waje ta zauna. Didi ko kallanta ba ta yi ba, dan yau ɗin da gaske ta ji haushin abin da Lulun ke yi sosae.

"Idan Allah ya kai mu anjima, za a je dubiyar mahaifin Malam Affan kamar yanda muka sanar jiya. Waɗanda za su je se su jirani a harabar makaranta." Malam Ahmad ya faɗa. daga nan be wani daɗe ba ya fita daga ajin. Gaba ɗaya en ajin a harabar makarantar suka haɗu, dan kowannensu na son zuwa gaishe da mahaifin Gwanin ko dan kirkinsa a garesu. Se dai ita kam Lulu kallan Didi da har lokacin ba ta kalleta ba ta yi tace

"Bari na je na ɗauki Little mu tafi. Se kun dawo.." da sauri Didi ta kalleta cike da mamakin jin furucinta. "Wai me ke damun Lulun? Anya kuwa kanta ɗaya? Me ye haka take yi kamar wani maƙiyinta ne Gwani? Me yasa ta ɗauki abin da yake mata a matsayin tsana, bayan kullum ita ke janyowa kanta? Fuskarta a haɗe duk da tana cikin niƙab amma Lulu ta fuskanci hakan. Ta kuma sake tabbatar da fushin ne sanda ta soma faɗin

"Wai Lulu me ye haka ne? Abin da kike yi kina ganin daidai ne? Mene ne aibu dan kin je kin duba mahaifinsa ko kuwa za a gutsiri naman jikinki ne?" Ta ƙare tana kallan Lulun.

"Ba za a gutsiri naman jikina ba. Amma kawai na ɗauki ƙafa na je na duba babansu bayan wulaƙantanin da ya yi ɗazu? Ko ba ma wannan ba, duk tarin wulaƙancin da yake min a cikin makarantar nan ni kuma kamar wadda ba ta da zuciya a ƙirjinta se kawai na je duba wani na shi. Me ye haɗina da shi? Wallahi Allah ya kiyaye. Ni fa Didi in fito miki a mutum wallahi saboda Abba da Ammi nake zaune a makarantar nan, ba dan haka ba da ina da dama da tuni na chanjawa kaina makaranta kuma duk a dalilin wannan mutumin" Ta ƙare maganar tana yamutsa fuskarta da itama take a haɗe alamar zancen da take faɗa tun daga ƙasan zuciyarta suke fitowa kuma tana jin zafinsu. Kallanta kawai Didi take yi tunda ta soma maganar har ta kai ƙarshe cike da mamakin Lulun..


https://chat.whatsapp.com/BClMNPwWybg2n3oRvtemv8

*♡☆A JINI TAKE☆♡*
*(IZZATA)*


By
_*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_


*CHAPTER ONE*

Page_16


___"Ohk good.." Didi ta faɗa tana jinjina kai lokaci ɗaya tana juyawa ta bar Lulun a tsaye. Binta Lulu ta yi da kallo har ta koma inda en ajin nasu suke. Babu daɗewa suka fice daga makarantar da jagorancin malamansu mata da maza. Se a lokacin ta sauke ajiyar zuciya sannan ta kama hannun Little suka fara tafiya.

"Masoyiya don Allah ki taho mu je." Fatima Kabeer ta faɗa tana kallan Lulun. Kallanta itama Lulun ta yi kana tace bayan ta ɗauke kai

"Aou ai na ɗauka ke ma kin bisu ne." Girgiza kai Fatima ta yi sannan tace

"A'ah fa, ke na zo kira." Da sauri tace

"Kin ga idan za ki tafi kawai ki tafi, wallahi ba zan je ba."

"Shi kenan.. mu tafi kawai." Se suka cigaba da tafiya. Ba su yi nisa ba Lulu ta kalli Fatiman tace

"Ke wai kin fasa zuwa ne?"

"Ban sani ba!" Ta faɗa tana galla mata harara. Dariya Lulu ta yi kamin tace

"Sorry Masoyiya."

"Kya ji da shi." Fatima ta faɗa tana sake ɗauke kai.

"Wai ina Didi?" Little ya faɗa tana ɗaga kansa ya kalli Lulu. Cikin er basarwa tace

"Sun je gaisuwa." Shi Little ɗin ma be fahimci abin da take nufi ba, se Fatima da ta buɗe baki tace tana kallanta

"Kee Masoyiya ba fa mutuwa ya yi ba."

"Aou toh.." ta faɗa tana buɗe idanu itama kamar da gasken ba ta san ba mutuwa ya yi ba. Se ta ɗora da

"Ai da na ga an tarkata kawunanku ne na yi tunanin mutuwa ya yi. Lallae!" Ta ƙare tana ɗan taɓe baki.

"Er rainin hankali, da ban san halinki ba da kin gama dani." Se kuma suka yi dariya gaba ɗayansu. Har gida se da Fatima ta kai Lulu sunata hira. A parlour suka taradda Ammi tana karatun Qur'an. Jin sallamarsu ya sanyata kai ƙarshen ayar da take sannan ta rufe, ta ajje shi a gefe, kana ta amsa sallamarta su.

"A'ah Fatima!" Ammi ta faɗa tana murmushi.

"Na'am Ammi, ina yini?" Fatima ta faɗa sanda ta ke zama.

"Lafiya ƙalau, ya karatu?"

"Ammi kin san ina Didi ta ke?" Little ya faɗa yana buɗe idanunsa, bayan ya haye kan kujerar da Ammin ke kai. Girgiza kai Ammi ta yi tana ɗan murmushi dan ta san shirmensa ne kawai

"Gaisuwa.." ya faɗa yana jinjina kai. Se kuma ta maida dubanta kan su Lulu da ke zaune tace

"Gaisuwa kuma? Waye ya rasu?"

"A'ah fa Ammi, babu wanda ya rasu. Babansu Gwani Affan ne ba lafiya shi ne aka je duba shi." Ajiyar zuciya Ammi ta sauke sannan tace

"Toh Allah ya ƙara afuwa."

"Ameen." Fatiman dai ta amsa. Kallan Little Lulu ta yi tace

"Little kai min jakar nan ɗaki." Kafin ya kai ga cewa komai Ammi tace

"Toh me yasa ku ba ku je ba?" Da sauri Lulu ta yi caraf tace

"Ammi kaina ke ciwo sosai. Shi yasa ma Ya mu'allim yace a rakoni gida."

"Toh Subhanallahi Allah ya sawwaƙe. Sannu Fatima an gode." Murmushi kawai Fatima ta yi tana ɗan satar kallan Lulu ta maka mata harara. Ita kuwa ta ɗauke kai kamar ba ta san da ita take ba.

.. Se dab da maghrib Didi ta shigo gidan. Ammi da Lulu na parlourn a zaune. Lulu na koyawa Little home_work. Ƙarasawa ta yi ta zauna a kan kujera tana faɗin

"Ammi na gaji."

"Sannunki, ai kin yi ƙoƙari, Allah ya ba da lada. Ita waccan malalaciyar da ciwon kai ya hana zuwa yanzu ai kin ga tana nan zaune ke kin samu lada."

"Ciwon kai kuma?" Didi ta faɗa tana kallan Lulu. Da sauri Lulu ta soma kaɗa mata kai tana sake maida fuskarta kalar tausayi a kan ta tausaya mata ka da ta faɗawa Ammi gaskiya. Se kuwa ta ɗauke kai daidai lokacin da Ammi ke faɗin

"Ba ki ganta tana wani mashau_mashau ba kamar wadda Asibitin ke kanta gaba ɗaya."

"Kai Ammi!." Lulu ta faɗa tana tura baki.

"Tashi maza ki yi sallah, ki zo ki sha magani. Idan ba haka ba ranki ya ɓaci. Bana son irin ciwon Didi na ƙin shan magani." Ammi ta faɗa. Se da Didi ta saci kallan Lulu sannan ta soma faɗin

"Ammi wallahi ba wani ciwon kai." Ta faɗa dan yau ɗin kamar yanda ta yi alƙawari se ta faɗawa Ammin abin da ta sake yi tunda ba ta jin magana.

"Ban gane ba?" Ammi ta faɗa tana kallan Didi.

"Cewa ta yi wai ba za ta je ta duba shi ba, tunda ba su da haɗi.

2 Comments On A JINI TAKE (IZZATA) CHAPTER 1
avatar
abubakar-sunusi

10 months ago

Reply

avatar
abubakar-sunusi

10 months ago

Reply

Please Login or Register in order to submit comment