Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana yin gaba.

"Shi kenan. Na gode." Mami ta faɗa. Se ta juya ta kalli Lulu bayan fitar Abba ta kama hannunta zuwa cikin ɗaki. Janta tayi cikin jikinta ta rungume kana ta soma faɗin

"Ka da ki damu kanki, halin Abban naku ne baki sani ba? Shi faɗansa kin san dai na lokaci ɗaya ne koh? Daga zarar ya wuce shikenan. Saboda haka ki samu ki bashi haƙuri, zan zo gidan da kaina na ɗaukeki mu dawo." Ita dai Lulu saurararta kawai take yi ba dan tana fahimtar abin da take faɗa ba. Da kanta Mamin ta haɗa mata kaya, har lokacin Jadwa na baccin takaicin da ya ɗauketa. Har compound Mami ta rakosu cike da kewar Lulun. Haka dai suka shiga mota, ta ɗaga musu hannu suka bar gidan. Ita dai Lulu ta kasa ko da ƙwaƙwƙwaran motsi ne dan har lokacin jikinta a sanyaye yake da Abban.



... A ɓangaren Bad Man kuwa, tun lokacin nan da ya kwanta bacci, se da ya ɗauki fiye da awa 3 sannan ya tashi. A nutse ya shiga buɗe sexy eyes ɗinsa da suka sake lumshewa saboda baccin da yayi, su a maimakon su yi rashin kyau, se ƙara kyau da suka yi na musamman. Ya kalli cikin ɗakin da yake kamar ne neman wani abu. Se kuma a hankali ya zura ƙafarsa ƙasan gado, ya saka takalmi sannan ya sauko yana ɗan lumshe ido, tun yanzu har ya soma missing na kayan maye, dan haka ya zama dole ya samarwa kansa mafita. Kai tsaye toilet ya faɗa, ya ɗauki fiye da 30min yana wanka kamar me shirin chanja fata, sannan ya fito yana ta zuba wannan ƙamshin nasa kamar na ko yaushe da ke ratsa zuciyar me shaƙarsa. Kamar ko da yaushe yanzun ma cikin riga da wando ya shirya, se dai wannan karon ma cikin crazy jeans ya shirya. Ya riga ya saba duk sanda ya fito daga wanka ya kan tsaya ya chanja ɗan kunnen da yake sakawa, yana shirin juyawa wajen da ya saba ajje su, se ya tuna nan ɗin fa ba California ba ne. Ɗan ƙaramin tsaki ya saki yana sake jin rayuwar Nigeria na sake fice masa a rai. Kawai se ya ɗauki face cap ya ɗora a kan kyakkyawar sumar kansa da ke kwance kamar wadda aka shafawa mai. Tsaff ya gama shiryawa, ya fito sak a Bad Man ɗinsa, se dai abubuwan da ba'a rasa ba waɗanda be yi amfani da su ba dan kasancewarsa a Nigeria. Ɗakin Mom ya wuce kai tsaye, dan ya san ta daɗe tana jiransa. Idan yaso in ya fito se ya je wajen Mommah su gaisa. Shi ya riga ya saba, ko ina ze shiga kai tsaye yake shiga babu sallama, hakan ne yasa yanzun ma a haka ya shiga, hannunsa ɗaya cikin aljihun wandonsa. Wannan ɗin sam ba damuwar Mom bace, tunda dai ya shigo shi kenan. Dan haka tasowa tayi cikin jin daɗin ganinsa tace

"Oyoyo my Boy, yanzun nan nake so na zo na tasoka, baccin haka ba ka ci abinci ba ya isa." Ɗan murmushin gefen baki yayi wanda ya mugun ƙawata fuskarsa sannan yace

"So gani dai.." ya faɗa yana soma takawa. Sallamar da aka yi daga bakin ƙofar ne ya sanya Mom kallan ƙofar, yayin da shi kuma ya cigaba da takawa cikin tafiyarsa me cike da kuzari. Cike da mamaki take kallan Hajiya Sa'adah da er aikinta Atine da ke shigowa cikin ɗakin. Wani irin takaici da baƙin ciki ne suka kamata lokacin da ta hangi warmers a hannun Atinen. Daidai lokacin da yake ƙoƙarin zama idanunsa suka sauka a kan Hajiya Sa'adah, se ya miƙe da murmushi kan fuskarsa ya ƙarasa inda Mommahn ke tsaye, yana zuwa ya bata side hug yana faɗin

"I missed you Mommah." Daskarewa Mom tayi ta kasa ko da ƙwaƙwƙwaran motsi ne. Murmushi Mommah tayi tace

"Missed you more Areef. Ka dawo lafiya?"

"Yeap!" Ya faɗa a gajarce bayan ya koma gefe ya tsaya yana kallan wayarsa da kira ya shigo cikinta. A hankali Mommah ta ɗaga ido ta kalli Mom da har lokacin take tsaye, ta riga ta san halin Hajiya Sa'adahn, duk yadda aka yi wani abun take shirin yi. Ita bata san me tayi mata ba, bata san me yasa bata san alaƙarta da ɗanta ba. Ita har ga Allah, Allah ma ya ga zuciyarta tana ƙaunar Areef ɗin ne da zuciya ɗaya, amma Mom ɗin ta kasa fahimta, dan ba tun yau ba take raba duk wata alaƙa da zata shiga tsakaninsu, se kuma aka samu sauƙi ya tafi ƙasar waje karatu, shi ne abin yayi sauƙi. Tana so ko yaya ne ta yiwa Areef ɗin wani abun na burgewa a matsayinsa na wanda ya dawo gida daga can wata ƙasa, se dai ta san ba lallai mahaifiyarsa ta bar shi ya shiga ɗakinta ba. Hakan ne ya sanyata ɗakko abin da tayi masa ɗin zuwa ɗakin nata, ta ba shi a gabanta. Atine da ta gaji da tsayuwa ne ya sanyata faɗin

"Hajiya na ajje kayan ne?" Jinjina kai Mommah tayi tana kallan Mom tace

"Barka da wannan lokaci." Se ta maida dubanta kan Atine tace

"Ki ajiye ki fita." Cike da girmamawa Atine tace

"Toh Hajiya." Ta faɗa tana yin gaba. Cikin hanzari Mom ta saka hannu ta janyo hannun Atine da ƙarfin gaske tace cikin ɗaga murya

"Gidan uwarki zaki je?" Taga_taga Atine tayi kamar zata faɗi, tana ƙoƙarin ganin ta tsaya a kan ƙafafunta amma hakan ya citira, se kuwa ta yi baya, hakan ne ya bawa warmers ɗin da ke hannunta damar faɗuwa a ƙasa da ƙarfi. Cikin lokaci ƙanƙani faɗuwar da suka yi ya bawa abin da ke cikinsu damar tsarwatsewa cikin parlourn..



*♡☆A JINI TAKE☆♡*
*(IZZATA)*


By
_*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_


*CHAPTER ONE*

Page_09


___Kusan a tare dukkansu suka kai dubansu inda abincin ya zube. Ɗan runtse idanunta Mommah tayi har cikin ranta tana jin ɗacin abin da Mom ɗin tayi. A hankali ta mayar da kanta kan Atine da ke zaune a wajen kamar wadda aka koro, tayi zuru_zuru, cike da mamakin abin da Mom ɗin tayi, da kuma tausayin Mommah da ta tabbatar ta shafe awanni da dama tana yin girkunan nan duk dan Areef ɗin.

"Mu je." Mommah ta faɗa cikin sanyayyiyar muryarta me cike da nutsuwa. Bata jira Atinen tace komai ba tayi sauri ta fice daga ɗakin. Se a lokacin sannan Atine ta ɗaga ƙafafunta itama ta fice daga ɗakin ba tare da ta bi ta kan warmers ɗin ba. Ɗan lumshe ido Bad Man yayi yana cije lips ɗinsa na ƙasa, se kuma ya ɗan furzar da iska daga bakinsa sannan ya sauke ajiyar zuciya ya soma takawa dan ficewa daga ɗakin. Sam Mom bata lura da shi ba, se da ya wuce ta gabanta har ya kusa fita daga ɗakin sannan ta gan shi. Cikin sauri ta bi bayansa tana faɗin

"A'ah, Areefullah ina zaka je?" Ta ƙarasa maganar sanda tazo dab da shi.

"Pls ki bani hanya." Yayi maganar gaba ɗaya fuskarsa a cunkushe babu fara'a ko misƙala zarratun. Cikin kwantar da murya tace tana ɗan murza hannunsa

"It's ohk..it's ohk Uhmm?" Ta faɗa cike da rarrashi.

"Pls Mom." Ya sake ambata ba tare da ya kalleta ba. Da dai ya fahimci ba matsawar za ta yi ba, kawai se ya zagayeta ya fice daga ɗakin ya barta tsaye a wajen.

"Oh my goodness.." ta faɗa tana yarfe hannunta. Ta riga dama ta san halin Bad Man ɗin amma bata san wannan ɗan abun da tayi ze fusata shi haka har ya ƙi cin abinci ba.

"Munafukar mata!" Ta faɗa tana jin yadda ɓacin rai ke taso mata musamman idan ta tuna da Hajiya Sa'adah.

Yana fitowa Compound ɗin yayi daidai da lokacin da Daddy ya sauko daga cikin motarsa. Se ya ƙarasa a nutse fuskarsa na sassautawa daga ɗauretan da yayi kamar ba shi ba. A nutse ya ƙarasa ya rungume Daddyn yana faɗin

"Welcome Daddy.."

"Welcome my Son.." Daddy ya faɗa yana ɗan dukan bayan Bad Man ɗin.

"Ina zaka je?" Daddy ya faɗa bayan sun saki junansu. Ɗan shafa sumar kansa Bad Man yayi kafin yace

"Amm, zan ɗan fita ne.. in zaga gari.." Jinjina kai Daddy yayi yace

"Hakan ma yayi. Buh zuwa anjima ina so muyi hira sosai.. Amma yanzu let's go to mosque, kaa ji ana kiraye_kiraye.." Babu musu yace

"Ohk.." daga haka be sake cewa komai ba. Kai tsaye masallacin suka wuce, wanda ke cikin tafkeken gidan nasu. Tare suka yi Sallahr cikin ƙaton masallacin. Cigaba da zama suka yi na tsawon mintuna, har lokacin Daddy addu'a yake, yayin da Bad Man tun kusan minti nawa baya ya idar da tasa addu'ar. Kallan Daddy yayi, sannan ya fito da wayarsa ya duba tym. Ya san idan dai har ya ƙara mintuna a gida ba ze samu abin da yake so ba. Dan haka cikin muryar nan tasa yace bayan ya ɗan ranƙwafo kusa da Daddyn.

"Daddy! Tym na tafiya.. Zan tafi.." se da Daddy ya kai ƙarshen abin da yake kafin ya kalle shi yace bayan yayi murmushi, a ransa yana farin ciki da yadda ya ga Areef ɗin nasa ya girma sosai yayi kyau, kuma da alama babu wani shashanci da yake yi, dan kwata_kwata yanayinsa be nuna ba. In banda askin da ke kansa da cikin ruwan sanyi ze san yanda ze yi ya sauya shi. Yanzun ma ya bar shi ne dan ya san hakan ba komai bane a can ƙasar da ya baro.

"Ohk.. Akwai yara za a haɗaka da su.." Cikin rashin fahimta yace

"Yara?"

"Yeap, yara mana.. waɗanda zasu kula da kai.." Se da ya soma ƙanƙantar da idanunsa sannan yace

"Kula da ni fa kace Daddy? Ba na buƙatar kowa. I can take care of myself couz am matured enough.." ya faɗa cike da jin haushin yanda burget ɗinsa ke neman rugujewa.

"Ga ka ga su ai Areef.. Je ka fita.." Daddy ya faɗa yana gyara zamansa ya cigaba da addu'oinsa. Har wani huci yake sanda ya miƙe ze fita daga masallacin. Tafiyarsa ta sake mugun ƙawatuwa saboda yanayin da yake ciki na fushi, se ya koma tafiya cikin wani irin taku kamar wanda baya son yin tafiyar. Se dai da yake tafiyar cike da kuzari yake yinta kasancewarsa ƙaƙƙarfan namiji ya sanya tafiyar tayi armashi. Kai tsaye wajen motarsa ya nufa ya buɗe ya shiga, ya ɗan lumshe idanunsa na tsawon sakanni sannan ya buɗesu lokacin da suka chanja colour. Abin da baya so kenan shi yasa be so dawowa Nigeria ba. Wannan wane kalan takurawa ne, a ce duk inda mutum ze je se da wasu a bayansa kamar wani ɗan fashi? Be taɓa tunanin idan ya dawo nan ɗin ze soma da wannan ƙalubalen ba. Amma a yau ɗin ze gama da wannan chapter, ya shiga next chapter. Idan kuma hakan taƙi toh dole se dai ya sake bar musu ƙasar.



.. Tunda Abba yayi parking sum_sum ta fice daga cikin motar, jin har lokacin bece da ita komai ba. Hakan ba ƙaramin sake sakawa jikinta yayi sanyi bane. Ammi da Didi na parlour suna kallan Sunnah TV. Ta shigo a sanyaye. Kowa ya ganta ya san akwai wani abun, dan da babu komai, tana shigowa zaka san ta shigo da maganarta. Se dai yau ɗin babu wanda ya jiyo muryarta, babu wanda ta nufa dan runguma, se ƙarasawa da tayi kan kujerar da Ammi ke kai ta ɗora kanta a kafaɗarta sannan tace

"Amminmu!" Murmushi Ammi tayi tana jin daɗin dawowar Lulun fiye da zato tace

"Na'am 'yan matan Ammi.."

"Kai Ammi" Lulu ta faɗa tana murmushin itama. Ɗan satar kallan Didi Lulu tayi, yanda take wani cika tana batsewa tana ɗaɗɗama rai ne ya sanya ta sake tuna abin da ya dawo da ita gida. Se kawai ta sake yin shiru tana kuma jiran shigowar Abban, dan ta san a yadda ta gan shi yau ɗin nan kam se ta sha faɗa. Se dai ga mamakinta har bayan wajen mituna 20 da shigowarta Abba be shigo ba, tun tana jin tsoro har tazo ta dena. Se kawai ta miƙe da sauri ta shige ɗakinsu. Didi na tsaye bakin wardrobe tana gyara kayanta. Lulun ta ƙarasa ta rungumeta tana faɗin

"Na yi missing na ki fa Didina.."

"Ni sakeni Malama." Didi ta faɗa tana mazewa. Maƙe kafaɗa Lulu tayi lokaci ɗaya tana faɗin

"A'ah, naƙi ɗin.."

"Toh jikinki ne?"

"Ehh mana, ai dai na Didina ne." Lulu ta faɗa tana murmushi. Jin Didin ba tace komai ba ya sanyata faɗin

"Abba ne fa ya ɗakkoni. Kuma ya min faɗa na dena abin da nake yi In Sha Allah.."

"Ke ɗin?" Didi ta faɗa tana juyowa ta kalleta. Se ta jinjina kai tana sake marairaice fuska kamar wata marainiya. Yadda tayi ɗin ne ya tilastawa Didi yin dariya. Se kawai ta rungume Twinnynta ta cikin matuƙar kewar junansu. Tun daga lokacin ma duk se suka sake suka manta ma da abin da Lulun tayi. Shi kansa Abba tun dawowarsu gidan basu sake ganinsa ba, kamar ma baya cikin gidan kwata_kwata. Hakan ne ya ƙara sawa Lulu karsashi wajen sakin jikinta ta cigaba da harkokinta. Har zuwa washegari kuma Abban be yi mata magana ba, hakan ne ya sanya ta soma tunanin ko ya manta, ko kuma ya bar maganar. Ita idan haka ɗin ne ma tafi kowa farin ciki, dan haka ta sake sakin jikinta, ta dinga kakkaucewa duk wata hanya da zata haɗata da Abban, duk da yadda daga jiyan zuwa yau be samu zama a gida sosai ba.


... Ammi ce kaɗai cikin parlourn tana kallan tashar Arewa 24 inda suke nuna shirin Akushi da rufi. Da yake Ammin tana son shirin ya sanyata zama tana kalla, duk da ita ɗin ba ma'abociyar kallo bace. Babu daɗewa se ta miƙe zuwa wajen fridge ɗinsu da ke cikin ɗakin dan ɗaukar ruwa. Sallamar da taji cikin parlourn ita ce ta sanyata juyawa. Se tayi murmushi ganin me shigowar tace

"A'ah... Sadiya! Sannu da zuwa." Ammi ta faɗa tana ƙarasowa cikin ɗakin cike da mamakin ganin Mamin, tunda dai ta ga jiya Lulu ta dawo, ba dai tana nufin ta zo ta sake tafiya da ita ba ne? Idan kuwa haka ne gaskiya a wannan karon dole ne ta magantu. Zama Ammi tayi tana ajje ruwa da lemon da ta ɗauko cikin fridge. Yayin da Mami ma ta ƙaraso ta zauna kan kujerar kusa da Ammin tana murmushi tace

"Se kuma kika ganni?" Itama Ammin murmushi tayi kafin tace

"Uhmm. Kina lafiya? Ina Jadwa?"

"Alhamdulillah. Ina 'ya'yana?" Mami ta faɗa tana ɗan duba bayanta.

"Suna ciki.. Ina ga ko bacci suke"

"Toh madallah. Yayan na nan ne?" Mami ta faɗa tana miƙewa.

"A'ah ya fita dai."

"Toh bari na je kafin ya dawo" Inji Mami.

"Toh." Ammi ta faɗa tana binta da kallo sanda take dab da shiga ɗakinsu Lulun. Kamar kuma wadda aka tambaya se ta juyo tace

"Kin san na zo ne na sake bawa Yaya haƙuri, sannan na yiwa ɗiyartawa faɗa." Jinjina kai Ammi tayi tana ɗan murmushi tace

"Uhmmm." Daga haka ba ta sake cewa komai ba har Mamin ta shige ɗakin. Suna zaune kan gado, Didi da Little ke kwance a jikinta na karanta musu wani English novel da aka basu a school Mamin ta shigo. Da gudu Lulu dake sanye cikin doguwar riga kanta babu ɗan kwali ta miƙe ta rungume Mamin tana faɗin

"Oyoyo." Hugging nata back Mami tayi tana murmushi lokaci ɗaya tana faɗin

"Wannan kannaki daughter.." ta faɗa tana riƙe baƙin gashin Lulun. Er ƙara ta saki tana saka hannu ta riƙo hannun Mamin. Se a lokacin ta saki sannan suka ƙarasa cikin ɗakin. Ajiye littafin hannunta Didi tayi, tana kwantar da Little da yayi bacci a kan gadonsu. Sannan ta juyo tace a nutse

"Sannu da zuwa Mami."

"Yawwah Afrah. Ya karatun?"

"Alhamdulillah.."

"Toh madallah."

"Daughter ina fata dai Abba be sake miki faɗa ba?" Mami ta faɗa tana kallan Lulu da ke zaune kusa da ita. Se da ta ɗan turo baki sannan tace

"Ehh fa. Ai be ma yi ba fa, inaga se yau.." ta ƙarashe maganar a narke. Shafa kanta Mami tayi kana tace

"Shi kenan, shinkenan. Didi.." ta kai ƙarshen maganar tana kallan Didi.

"Uhmm" Didi ta faɗa cikin sanyin nan nata.

"Ɗan bamu waje zan sake yi mata faɗa.." kusan a tare Lulu da Didi suka kalli junansu, sannan Didi ta maida duban nata kan Mami, kamar za tace wani abu se kuma ta fasa, kawai ta miƙe ba tare da tace komai ba. Riƙo hannunta Lulu tayi da sauri tana faɗin

"Didi ki zauna.." Lulu ta faɗa har lokacin fuskarta a narke. Hannu Mami ta kai ta zare hannun Lulu daga cikin na Didi tace

"Barta ta je, ina son na yi miki faɗa ne sosai. Idan tana nan zata dinga rarrashinki, idan kuwa bata nan fa? Didi je ki abinki.." tun kafin Mamin ma ta gama maganar Didi ta fice daga ɗakin. Lulu ta bita da kallo har ta fice ɗin. Sannan ta dawo da dubanta kan Mami da itama ta bi Didi da kallo har ta fice. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta saka hannunta a cikin jakarta ta ɗauko waya, kana ta ɗago tana kallan Lulu ta soma faɗin

"Kina ji na?" Tayi maganar tana juya wayar hannunta..



*♡☆A JINI TAKE☆♡*
*(IZZATA)*


By
_*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_


*CHAPTER ONE*

Page_10


__"Ehh Mami." Ta faɗa tana kallan wayar. Se da Mamin ta gyara zama sannan tace

"Riƙeta ki ji." Tayi maganar tana miƙa mata wayar. Babu musu ta saka hannu ta karɓa tana kallan Mamin, dan ta ƙagu ta ji abin da zata faɗa matan.

"Ki ajjeta a wajenki, za a kiraki zuwa anjima. Kada kice ba zaki ɗaga ba dan na san halinki, kin ji koh?" Baki ta tura gaba tana ajje wayar kamar wadda ta ga wani abun tsoro, ta kuma soma yamutsa fuska. Harara Mami ta jefa mata sannan tace

"Bana son iya shege Lulu.."

"Ni wallahi a'ah Mami, bana so. Ni nace miki ina son waya?" Iska Mami ta furzar tana tunanin yanda zata yi ta shawo kan Lulun.

"Tsaya ki ji, ki ajje wayar nace a wajenki koh? Na ji ba za a kiraki yau ba, se gobe uhmm?"

"Wai ke ce zaki kira?" Ta tambaya cike da sakarcinta.

"Wayyo Allahna Lulu.." Mami ta faɗa tana dafe kanta gami da sauke ajiyar zuciya.

"Bani wayar" tayi maganar tana ɗaukarta daga inda Lulun ta ajjeta. Kasheta tayi gaba ɗayanta sannan ta miƙe ta ƙarasa zuwa wajen wardrobe ɗinsu, ta buɗe ta Lulu ta sakata a ƙasan kayanta sannan ta dawo ta zauna tace

"Na san Yaya da kuma Amminku ba za su barki yanzun ki fara kula samari ba. Toh wata gagarumar dama ce ta samemu Lulu, saboda haka wannan wayar ki kunnata zuwa gobe zan kiraki. Sannan kuma ko da an kiraki ki ɗaga, wani ne ya ganki yace yana so. Ki ba shi haɗin kai kinji? Idan komai ya daidaita ni da kaina zan sami Yayan da maganar. Me ye dan kin fara soyayya a S.S 1?" Ita tun ɗazu da ta fara magana sam bata fahimci abin da take so ta faɗa ba, se yanzu da ta ambaci soyayya. Dan haka cikin sauri ta soma ƙoƙarin miƙewa tana faɗin

"Kaii!!" Tayi maganar tana fiddo da idanunta waje. Hannunta Mami ta janyo, tana tunanin yanda zata ɓillowa Lulun kada ta ɓarar musu da wannan gwagwgwaɓar damar. Se dai ta riga ta san halin Lulun wani lokacin a botsare take. Dan haka cikin rarrashi tace tana murmushi

"Dawo ki zauna daughter."

"Ni wallahi ki sakar min hannu Mami. Hmm uhmm jam!" Ta faɗa ainahin ƙuruciyarta na bayyana, wanda hakan har se da ya sa Mamin ta sake murmusawa.

"Ke da wasa fa nake. Dawo ki yi zamanki, ni ce na siyo miki wayar saboda na ga kina sonta.." Se a lokacin sannan Lulu ta tsaya tana kallan Mamin.

"Don Allah?"

"Ehh mana, ko ba kya so?" Se tayi murmushi tana komawa ta zauna cike da jin daɗi. Se kuma ta ɓata fuska tace

"Toh ta yaya zan yi amfani da ita? Idan kuma Abba ko Ammi suka gani fa?"

"Ba ma zasu gani ba, se dai idan ke ce kika yi niyya." Mami tayi saurin bata amsa. Ta buɗe baki za tayi magana Ammi tayi sallama cikin ɗakin. Se ta fasa cewa komai. Ammi ta ɗan kallesu sannan ta ƙaraso ta nemi waje ta zauna.

"Uhmm bari ki ga na zo na tafi.. dama unguwa fa zan wuce daga nan ɗin." Mami ta faɗa tana miƙewa. Kallanta Ammi tayi da ɗan mamaki, se dai kawai ta basar tace

"Haba dai, har kuma zaki tafi?" Yaƙe tayi tana faɗin

"Wallahi kuwa, gwara na tafi.." ta faɗa tana yafa mayafinta. Lulu da Ammi suka miƙe, suka fito parlourn tare. Da sauri Didi da ke zaune a ɗakin ta kulle idanunta kamar me bacci, dan ita dai haka kawai yau ɗin take jin haushin Mamin.

"A'ah Afrah bacci take kenan?" Mami tayi tambayar ba dan tana buƙatar amsa ba. Har compound suka rakata, suka yi sallama. Har kuma suka koma Ammi bata basu damar keɓewa sun yi magana ba, wanda hakan ba ƙaramin sosa zuciyar Mami yayi ba, dan dai kada a fahimci wani abun ne ya sanyata mazewa.


.. Sanye cikin ƙananan kaya kamar yanda kuka san Bad Man ɗin ma'abocinsu ne yake, kansa ya ɗora masa wata haɗaɗɗiyar facing cap da ya juyar da ita ta baya. Hannunsa ɗaya na cikin aljihun wandonsa yayin da shegiyar hamshaƙiyar wayarsa ke ɗayan hannun nasa kafe a kunnensa yana amsa waya. A haka ya cigaba da takawa har zuwa wajen motarsa. Kai tsaye ya shige, bayan ya katse kiran ya tasheta. A bakin tanƙamemen gate ɗin gidan nasu ya tsaya yayi horn, da yake yana idar da Sallahr isha'i ya fito, se ya kasance yawanci duk suna cikin masallaci, se ɗaiɗaiku saboda ba a barin wajen haka babu kowa. Be haƙura ba ya sake danna horn fuskarsa a matuƙar haɗe yana kallan wanda ke tsaye a wajen. Daga gefe yaji an yi knocking glass ɗin gefensa. Kamar ba ze juya ba, se kuma ya juya a hankali ya watsawa wanda ke tsaye a wajen idanun nan nasa bayan ya sauke glass ɗin kaɗan. Cikin lokaci ƙanƙani ya ɗan daburce, da ƙyar ya iya soma faɗin

"Yallaɓae sun ce kada a buɗe gate ɗin. Wai kada kowa ya fita. Kayi haƙuri yallaɓae." Ya ƙarasa maganar cike da girmamawa.

"Kai! Ni sa'anka ne?" Ya ƙare ransa a ɓace, yana jin yanda zuciyarsa ke tafasa.

"Will u just open the gate for me ko kuma.." Tun kafin ya ƙarasa Idi yayi gaba da sauri ya ƙarasa jikinsa na rawa ya buɗe gate ɗin. Me gadin da ke zaune a wajen yana kallansa. Se dai bece komai ba har Bad ɗin ya fice daga gidan. Se a lokacin ya kalle shi yace

"Shi ne ka buɗe masa kofar koh? Idan suka fito me zaka ce musu?" Cikin fushi Idi yace

"Me yasa da na buɗe a gabansa ba ka zo ka rufe ka ce ba ze fita ba? Se yanzu zaka wani zo kana faɗa min magana."

"Ni dai wallahi idan suka zo babu ruwana, ban ma san kayi hakan ba." Tsaki Idi ya ja duk da yadda shi ma yake a tsorace, amma tsoron Bad Man ɗin yafi tsoron mutanen. Dan kuwa ya san idan da be buɗe masa ƙofar ba ko me nene ya biyo baya shi ya jawa kansa.
Wani ƙaramin joint se dai haɗaɗɗe Bad Man ya wuce. Ya sauka ya soma takawa zuwa ciki, gefen swimming pool inda mutanen da ke zaune a wajen basu da yawa, se dai kowa da abin da yake yi.

"Heyy Bad!" Na ji an faɗa cikin er ɗaga murya. A nutse ya ɗaga lumsassun idanunsa ya kalli Hero da ya kira sunansa. Ya ɗan yi murmushin da ke ƙawata kyakkyawar fuskarsa. Cikin sauri Hero ya ƙaraso ya rungume shi yana faɗin

"Wai dama da gaske kake?" Be ce komai ba se

"Uhmm" kawai da yace.

"Let's go Friend.." Hero ya faɗa yana jan hannunsa suka ƙarasa suka nemi waje suka zauna. Ɗan kishingiɗa Bad Man yayi yana sauke ajiyar zuciya ganin tarin drinks a wajen kala_kala se wanda ya zaɓa.

"Kana nan kana sharholiyarka koh?" Yayi maganar a hankali kamar wanda aka ma dole. Ɗan shafa kansa Hero yayi yace

"Ba zaka gane ba ne Friend.. dole se ana yi ana ɗan ehh yaaa..nee." Hannu Bad Man ya saka ya janyo wata hamshaƙiyar kwalba wadda da alama ma ko taɓata ba

2 Comments On A JINI TAKE (IZZATA) CHAPTER 1
avatar
abubakar-sunusi

10 months ago

Reply

avatar
abubakar-sunusi

10 months ago

Reply

Please Login or Register in order to submit comment