Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙirji, fuskarta a haɗe ta fice daga ajin. Duk da abin nan da ya faru har ta fita ɗin ba ka jin motsin kowa, ko na surutunsa, kowa ya bar maganar ne a ransa, imma dai idan Gwani ya fita su tattauna ko kuma idan aka tashi. Kwantar da kanta Didi tayi akan bench ɗin gabanta tana sauke ajiyar zuciya.

"Why Lulu?" Ta faɗa akan laɓɓanta har zuciyarta tana jin babu daɗi sam. Se dai a wannan karon tana ganin dole ne ta faɗa wa Ammi abin da Lulun take yi dan ayi wa tufkar hanci tun yanzun.

Da sallama ya shiga Office ɗin me makarantar, ya nemi waje ya zauna fuskarsa a cunkushe babu fara'a, da yake dai dama can ba wata fara'a gare shi ba so yanzu ma idan ka ganshi ba zaka gane a wane yanayi yake ciki ba, se dai shi kaɗai ya san yadda yake jin ɓacin rai a yau ɗin.

"A'ah Malam Affan, Barka da zuwa." Malam Ahmad ya faɗa yana murmushi.

"Yawwah." Ya faɗa a nutse. Baya san ɓata wani lokaci hakan ne ya sanya shi faɗin

"Amm, wata magana ce.."

"Toh Ikon Allah, ina jinka." Malam Ahmad ya faɗa yana kallansa cike da mamaki, dan kuwa ba kasafai Gwanin ke zuwa da wata maganar ba. A nutse ya soma faɗin

"Magana ce a kan er uwar Afrah Muhammad Aji, na koreta daga ajina!" Numfashi Malam Ahmad ya sauke yana tuna Afaaf ɗin, tabbas ya san yarinyar ba ta ji, amma be taɓa tunanin har zata iya yiwa Gwani wani abun da ze sa har ya koreta ba. Ya riga ya san Gwanin ba ze yanke hukunci babu ƙwaƙwƙwaran dalili ba, dan haka tambayarsa dalilin yin hakan ma kamar ba shi da wani amfani, dan haka yace

"Kayi haƙuri Malam Affan, kayi haƙuri. Wallahi ka san yarinyar muna fama da ita, ba dan ma muna da tsayayyun malamai ba. Duk da yarinya ce amma gani take kamar kanta ɗaya da kowa, amma In Sha Allah zamu san yanda za a yi a yiwa tufkar hanci." Furzar da iska Gwani yayi lokaci ɗaya yan ɗan lumshe idanunsa kafin ya buɗesu yace

"Ka yi haƙuri Malam Ahmad, amma se dai ko ni na zauna a ajin, ko kuma ita ta zauna ni na bar ajin.." Wajen second 30 Malam Ahmad ya soma faɗin

"Da ka duba al'amarin nan Malam Affan, ka yi haƙuri, ba wai dan ina sama da kai a cikin makarantar nan ba ne, dan ka san idan Addini ne kai ɗin number ɗaya ne. Ba komai ne ya sa nace kayi haƙuri ba se dan kai ɗin na daban ne, kai ɗin me iya zama da ɗalibai ne masu kowanne irin hali sannan ka chanja su cikin ƙanƙanin lokaci. Zaka iya zama da wannan ɗalibar Malam Affan, kamar kuma yadda nake fata ta chanja, ta koma kamar er uwatta. Se dai a wannan karon ba ze yiwu a barta haka ba, zata iya kasancewa mahaifinsu be san abin da take aikatawa ba, saboda mahaifinsu mutumin kirki ne na sosai. Dan haka zan saka a sanar da shi muna son ganinsa, idan ya so se ku yi magana da shi." A wannan karon shiru Gwani yayi sanda ya gama saurarar maganar Malam Ahmad ɗin sannan ya gyara zamansa a kan kujerar da yake kai..



*♡☆A JINI TAKE☆♡*
*(IZZATA)*


By
_*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_


*CHAPTER ONE*

Page_07


"Shi kenan!" Shi ne abin da Gwani ya faɗa yana miƙewa, ya miƙawa Malam Ahmad hannu suka sake gaisawa sannan ya fice daga Office ɗin.

A tare suka fito daga cikin makarantar, se dai Didi ba tace da Lulu ko uffan ba, wanda hakan ke alamta mata fushi take da ita. Ita kuma a yanda take jin zuciyarta dama yanzun ba za ta iya cewa komai ba. Idan kuwa tayi ƙoƙarin furta ko da kalma ɗaya ce to kuka ne ze ƙwace mata, and idan hakn ta kasance kuma ba zata taɓa yafewa kanta ba, hakan ne ya sanyata sake haɗe fuska waje ɗaya tana iya ƙoƙarinta wajen ganin ta riƙe kanta kukan be taho ba dan kada ta yarfa kanta.

"Se da safe." Didi ta faɗa ba tare da ta kalleta ba, daga haka tayi gaba hannunta riƙe da na Little. Binta da kallo Lulu tayi, mamakin yadda tayi fushin na sake kamata, bata taɓa tunanin akan Gwani Didin kan iya fushi da ita ba. Da dai ta ga alamar da gaske Didin take ta tafi kenan, se ta soma jan ƙafafunta kafin ma en ajin na su su gama fitowa tayi inda motar da zata ɗauketa ke tsaye. Daidai lokacin ya ɗago kai cike da sarewa, dan a yanzu kam be taɓa tunanin ze iya ganinta ba, ya gama fidda rai, bayan daɗewar da yayi a wajen ta sama da awanni. Se dai me? Yana ɗaga kai ya hangi Lulu na neman shiga motar. Cikin matuƙar farin ciki ya furta

"Alhamdulillah!" Yana tayar da motarsa. Babu daɗewa driver ya ja motar da Lulu ke ciki ya soma tafiya, cikin ƙwarewa shi ma ya soma binsa har zuwa sanda suka isa gidan Mami. A bakin gate ɗin ya tsaya yana kallan gidan, ba dan akwai abin da ze yi yanzu ba, da tun yanzun ze fara zuwa wajen nata, se dai kuma ance gaggawa aikin sheɗan ne, dan haka gwara ya bari zuwa goben se ya zo. Hakan ne ya sanya shi tashin motarsa ya bar layin cike da farin cikin samun gidansu Lulun. Ko jakarta Lulu bata iya ɗauka ba ta fice daga motar da gudu.

"Subhanallahi, daughter me ya faru?" Mami ta faɗa tana miƙewa tsaye, babu ɓata lokaci Lulu ta ƙaraso ta faɗa jikin Mami tana fashewa da kuka.

"Na shiga uku ni Sadiya, Lulu me aka miki ne? Waye ya taɓa min ke?" Se da tayi me isarta sannan ta buɗe baki ta soma korawa Mamin abin da ya faru tana jin kwata kwata babu daɗi.

"A gaban en ajin ya yagaki haka? Shi be san wacece ke ba? Be san kin fi ƙarfinsa ba shi ne ze miki haka? Toh makaranta ce kin dena zuwa daga yau, zan yi magana da Yayan." Mami ta faɗa a kufule. Cikin jin dadi Lulu tayi murmushi kafin tace

"Ko Mamina?"

"Ƙwarai kuwa ɗiyar albarka, ai kin fi ƙarfin wulaƙancin kowanne ɗa namiji ballantana kuma malamin islamiyya. Kada ki damu daga yau kin dena zuwa makarantar nan." Miƙewa tayi duk da yanda take jin zuciyarta na zafi amma sosai taji dama_dama da maganganun Mamin, ko babu komai sun sanyaya mata zuciya, hakan ne ya sanya ta wuce ɗaki.



.. Ko sallamar da yayi a ciki_ciki yayi ta, Ammi da ke zaune kan kujera ta amsa sallamar tana kallansa. Se ta miƙe tana faɗin

"Sannu da zuwa"

"Yawwah, maza ɗauko min takaddun nan zan fita ne."

"Ikon Allah, sake fita kuma zaka yi?" Ammi ta tambaya, se dai ganin yanayinsa kamar a ɗan fushi ya sanyata faɗin

"Allah dai yasa lafiya!" Ajiyar zuciya Abba ya sauke sannan yace

"Ni dama na san kiran nan da aka min a makarantarsu yaran nan akwai wani abun, dan kuwa basu taɓa yi min haka ba. Ashe ban sani ba kara suke min, suna ta ɗaga min ƙafa ban sani ba. Ashe yarinyar nan tana can tana ƙoƙarin zubar min da mutunci da kimata wajen malamanta, bata duba girmansu, darajarsu da kuma kimarsu, tana yin abu kamar bamu bata tarbiyya ba?" Abba ya ƙare cikin fushi kamar Lulun na gabansa.

"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel!" Shi ne abin da Ammi ta faɗa tana komawa kan kujera ta zauna. Se dai kafin ta gama tunanin ballantana ta kai ga cewa komai ta jiyo muryar Abban na faɗin

"Zuwa zan yi na ɗakkota, ta dawo ta cigaba da zama a gidan nan, a gabana ina kallan abin da take yi hankalina ze fi kwanciya. Sannan kuma tun a can ɗin wallahi zan hukuntata tun da bata da kirki." Se a lokacin Ammi ta miƙe tana girgiza kai tace

"A'ah Abba kayi haƙuri don Allah, kome zaka yi mata ka bari ku dawo gida tukunna, sannan ka ɗan sassauta fushin nan naka kafin ka fita, ka san fushin ba shi da wani alfanu.." Sauke ajiyar zuciya Abba yayi yana faɗin

"In Sha Allah.."



A ɗaya ɓangaren kuwa su ukun ne zaune a parlour suna kallo a ƙatuwar TVn da ta ƙawata parlourn. Jadwa da ke zaune kujera ɗaya da Lulu ta juya ta kalli Mami sannan tace

"Mami wae yaushe Abbu ze dawo?"

"Baki na fiki koh?" Mamin ta faɗa tana jefa mata harara. Kafin Jadwan ta kai ga cewa komai se ga sallama daga bakin parlourn. Jin sallamar me gadinsu ne ya sanya Mami faɗin

"Shigo!" Duk kuwa da irin shigar da ke jikinsu hakan be sanyasu tashi sun ɗauki ko da mayafi ne sun rufe jikinsu ba ko dan kasancewarsa ba muharraminsu ba. Babu daɗewa kuwa se ga shi ya shigo cikin ɗakin. Ya durƙusa har ƙasa yana faɗin

"Hajiyoyi barkanku da wannan lokaci.."

"Barka dai" Jadwa da Mami suka amsa da hakan, yayin da Lulu hankalinta gaba ɗaya ke kan TV saboda ana haska wani favourite movie nata ne.

"Me ya faru?" Mami ta katse shi da faɗin hakan.

"Kun yi baƙo ne, yana ƙofar gida, yace yana buƙatar ganin wata daga cikin gidan nan, nafi tunanin irin baƙin nan naki ne hajjaju, shi yasa nace bari na zo na faɗa miki!"

"Yana tsaye a bakin gate kuma?" Mami ta faɗa tana kallansa. Se ya girgiza kai yace

"A'ah da yake a mota yake, toh har yanzun ma yana ciki.."

"Ohk, ka faɗa masa ya shigo, ka kai shi ɗakin baƙi, gani nan zuwa." Mami ta faɗa tana miƙewa. Babu musu ya miƙe yana faɗin

"Toh Hajiya." Ɗaki Mami shiga, babu daɗewa ta fito, kai tsaye ta wuce ɗakin baƙi. Da sallama ta shiga cikin ɗakin, hannunta ɗauke da wayarta, ba yau ne karon farko dama da take karɓar baƙi kala_kala ba, musamman akan aikinta, se dai yau ɗin bata san da zuwan wannan ɗin ba, abin da ya bata mamaki kenan. Sanye yake cikin shadda, ɗinkin babbar riga kamar ranar farko, yau ɗin ma sun amshe shi babu laifi, yana kame a cikin kujera. Amsa sallamar yayi sannan ya juyo yana kallan me shigowar. Kusan a tare suka faɗi sunan junansu kowannensu cike da mamakin ganin ɗan uwansa.

"Kaseem!" Mami ta sake faɗa tana ƙarasowa cikin ɗakin.

"Kai ne a gidan nawa?" Ta tambaya tana neman waje ta zauna a kan kujera. Duk da yayi mamakin ganinta a gidan hakan be hana shi faɗin

"Wallahi kuwa ni ne Madam."

"Ikon Allah, toh ya kake? Ya aiki?" Ta tambaya. Nan dai suka gaisa cike da sabo sannan Mami tace bayan shuɗewar wasu sakanni ba tare da kowa yace komai ba

"Anya kuwa gaisawa da ni ka zo yi?" Murmushi Kaseem yayi yana ɗan gyaran murya sannan yace

"Madam ina ganin fa da alama kina dab da zama sirikata.." buɗe ido Mami tayi kafin tace

"Woww, da gaske?" Se da ya jinjina kai sannan yace yana murmushi

"Ƙwarae kuwa, dan kuwa a jiyan nan na ga ɗiyarki, na kuma ga nan gidan ta shigo, hakan ne ya sanyani biyo sawu." Cikin matuƙar farin ciki Mamin tace

"Woww, amma gaskiya na ji daɗi, na yi farin ciki Kaseem." Ta faɗa tana jin wani irin daɗi na ratsata, dan kuwa tun da yayi maganar ita Jadwa kawai ta hango ta kuma san ita yake nufi, idan kuwa har Jadwan ta amince to fa shi kenan ta samu mijin aure na nunawa sa'a, dan kuwa Kaseem ɗin akwai abin hannu. Be ce komai ba ban da murmushi da ya sake yi. Sakkowa daga kan kujerar Mami tayi tana faɗin

"Bari na kira maka ita." Ɗan zamowa yayi daga kan kujerar da yake kai yace

"A'ah da kanki kuma." Ya ƙare yana murmushi. Itama murmushin tayi kana tace

"Toh mene ne Kaseem? Kada ka damu." Tayi maganar tana ficewa daga ɗakin. Ajiyar zuciya ya sauke yana jin lallai tabbas komai ze zo masa da sauƙi In Sha Allah.

Cikin matuƙar farin ciki da jin daɗi Mami ta faɗo dakin fuskarta murmushi yaƙi barinta tun ɗazu.

"Maza maza tashi ki je kin yi baƙo." Mamin ta faɗa tana dukan ƙafar Jadwan.

"Baƙo kuma?" Jadwa ta faɗa cike da mamaki, dan dai ita ta san ba suyi da kowa ze zo wajenta ba. Jinjina kai Mami tayi tana faɗin

"Ƙwarai kuwa, tashi.. Lulu maza tashi ki tayata shiryawa kin ji?" Ta ƙare maganar tana kallan Lulu. Babu musu kuwa Lulu ta miƙe daga kan kujerar tace tana kallan Jadwa

"Mu je!"

"Kin ji ki kema, in je ina?" Tsaki Mami ta ja kafin tace

"Shashasha sakarya, da alama yau kin yi babban kamu, kamun da idan dai har ba wasa kika yi ba kin yi dace da smaun miji me kuɗi kuma na gari.. Ina Kaseem da kika sani a baki?" Da sauri Jadwa tace

"Ehh.. ehh.."

"Toh shi ne yazo wajenki." Mami ta faɗa. Da sauri Jadwa ta diro daga kan kujerar tana faɗin

"Kai Mami.." Hannunta Mami ta kama tace

"Maza mu je ki shirya pls, ka da a ɓata masa lokaci" Yanzu kam babu musu Jadwan ta bi Mami zuwa ɗaki. A wannan karon ita dai Lulu taɓe baki tayi kawai ba tace komai ba se bin bayansu da tayi. Wasu haɗaɗɗun kaya Mami ta fitowa da Jadwa su, babu musu ta ɗauka ta saka, sosai kayan suka mata kyau, suka zauna ɗass a jikinta, ta ɗauki ƙaramin mayafi ta saka sannan ta shafe fuskarta da powder.

"Ki ɗan yi kwalliya mana ko yaya ne!" Mami ta faɗa tana kallan Jadwan, dan ita dai tafi so ta ƙure wanka a yau ɗin.

"Mami haka ma fa ya isa." Ta faɗa tana ajje turaren da ta gama fesawa. Da sauri Mami ta karɓa tana faɗin

"Shashasha, har kin gama sakawa? Ni gyara min na sake feshe miki jiki da shi, so nake na ji ko ina na jikinki na tashin ƙamshi." Ta faɗa tana sake feshe turaren a jikin Jadwa..


Ku yi manage da wannan pls, mu haɗe gobe idan Allah ya kai mu.




*♡☆A JINI TAKE☆♡*
*(IZZATA)*


By
_*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_


*CHAPTER ONE*

Page_08

___Ita dai Lulu binsu kawai take da kallo, se kace waɗanda aka ce an musu albishir da wani abun na musamman, ko kuma za su je su ga wani abun na musamman ne. Sosai Mamin da ita kanta Jadwan suka bata mamaki, duk yanda suke amma a kan namiji sun bi sun ruɗe kamar ba su ba. Ɗan taɓe baki kawai tayi tana bin Jadwa da kallo sanda ta zo gaban mudubi tana juyi tana kallan jikinta. Zagayeta Mami tayi tana murmushi tace bayan ta ɗaga yatsanta ɗaya alamar jinjina

"U look so take away.." Murmushi Jadwa tayi sanda take faɗin

"Awwwn, Mami ki bar zugani haka nan." Komawa Mami tayi ta zauna kusa da Lulu sannan tace

"Heyy! faɗa mata tunda ni sa'arta ce" yaƙe kawai Lulu tayi kamar ba za tace komai ba, se kuma tace

"Sosai ki ka yi kyau fa.."

"Mami, bari na je, kada yayi ta jira." Jadwa ta faɗa bayan ta sakarwa Lulu murmushi.

"Toh se kin dawo." Mami ta faɗa, ita kuma Jadwa ta fice daga ɗakin. A hankali take takawa tana wani rangaji kamar agwagwa, ƙafarta dake ɗauke da hill shoe tana bada sautin 'ƙwas_ƙwas'. Ɗan lumshe idanunta tayi sanda tazo dab da shiga ɗakin tana sauke numfashi, dan bata taɓa ganinsa a fili ba. Da sallama ɗauke a bakinta ta shiga ɗakin, cikin matuƙar farin ciki yadda yake tunanin ze yi arba da kyakkyawar fuskar da ta hana shi bacci tun ranar da ya soma ganinta ya ɗaga idanunsa ya sauke a kan Jadwa da ke cigaba da takowa cikin ɗakin. Shi da ya buɗe baki da niyyar amsa sallama cike da karsashi duk se yaji jikinsa yayi matuƙar sanyi, hakan ne ya sanyashi ƙarasa sallamar a hankali. Ba tare da ta kalli inda yake zaune ba, ita a lallai dole me kunya, ta nemi waje ta zauna sannan tace

"Barka da zuwa. Ina wuni?" Ta ƙare maganar tana ɗago wa ta kalle shi. Ƙaƙalo murmushi yayi yace

"Yawwah, barka dai." Se dai duk hankalinsa yafi tunanin meyasa ya ga daban da wadda ya gani a jiya? Toh ko dai rakiya tayo ne? Abar ƙaunarta sa na ciki? Hakan da ya tuna ne ya sanya shi ɗan gyara zama sannan yace

"Sannu koh? Ya makaranta?" Wani irin daɗi ne ya ziryarceta tace bayan itama ta gyara zama tace

"Alhamdulillah."

"Madallah." Ya faɗa. Daga haka se shiru ya mamaye ɗakin, ita tana jira yace wani abun, yayin da shi kuma yana jira ne ya ji tace 'yar uwarta ta na nan zuwa. Jin shiru ya sanya shi faɗin

"Amm sisterta ki fa?" Ya tambaya yana murmushi. Da mamaki ta ɗago ta kalle shi, se kuma ta ɗan basar tace

"Sisterta kuma?" Ta tambaya a mamakance. Yanzu kam shi kansa abin ya bashi mamaki, shi dai ya san tabbas ba wannan ya gani ba, amma ya tabbatar wadda ya gani gidan nan ta shigo kuma yanzu an turo masa wata a matsayin ita ya gani. Shi kam sam ba ze yadda yayi saki na dafe ba, hakan ne ya sanya shi faɗin

"Amm, na haɗu da wata ne tana shirin shiga Islamiyya, so na bi bayanta na ga kuma gidan nan ta shigo." Cikin mintuna ƙalilan Jadwa ta ji jikinta yayi wani bahagon sanyi, duk wannan kunyar da ta aro ta yafa ta ji tana warewa zuwa na ta wajen. Se kawai ta basar tace

"Ohh lem me call her." Ta faɗa tana miƙewa.

"Ohk.. Thanks sistor.." ya faɗa yana murmushi gami da binta da kallo sanda take ficewa daga ɗakin. Haushi ita kuwa ya sake cikata, wato har da wani kiranta da sister duk wannan uban kashe kalar da tayi. Cikin sauri da kuma takaicin da ya cikata take tafiya har zuwa parlourn. Jefar da mayafinta tayi a kan kujera, tana tuna yanda mutuncinta ya gama zubewa a wajen Kaseem ɗin.

"Kee! Me ya faru?" Mami ta faɗa tana ƙarasowa cikin ɗakin. Saboda yanda take jin zuciyarta na wani irin zafi yasa ta kasa furta ko kalma ɗaya se ajiyar zuciya da take ta saukewa.

"Oh ni Sadiya, ba dai wannan banzan halin naki kika nuna masa ba?" Mami ta faɗa bayan ta zauna. Shirun dai Jadwa tayi har lokacin tana tuna wannan cin mutuncin.

"Wai ba za ki min magana ba ne?" Mamin ta faɗa a ɗan zafafe, dan zuwa yanzun ta fusata.

"Mami dama kin san ba wajena ya zo ba amma kika ce na je? Ba kya tsoron mutuncina ya zube?" Hannu Mami ta saka ta dafe ƙirji kafin tace

"Ke ban san shashanci mana, kamar yaya? Toh idan ba wajenki ya zo ba, wajen wa ya zo? Ko ina da wata ɗiyar ne bayan ke?"

"Lulu!" Jadwa ta faɗa kai tsaye. Shiru Mami tayi tunda Jadwan ta ambaci sunan Lulu. Daga lokacin da Kaseem yayi zancen ya ga wata a gidanta ita sam ta manta da Lulu, kawai Jadwa ta hango, ashe ta manta akwai wata a gidan bayan Jadwa. Ajiyar zuciya ta sauke tace tana jinjina kai

"Tirƙashi!"

"Mami ba tunani zaki tsaya yi ba fa, nace masa zan kira masa ita ne, and am sure yanzu haka jiranta yake." Jadwa ta faɗa. Kallanta Mami tayi tace

"Ina zuwa!" Ta faɗa tana miƙewa ta fice daga ɗakin. Daidai lokacin da ta fito yayi daidai da lokacin da motar Abba ta shigo gidan. Se kawai ta ƙarasa wajen, daidai sanda ya fito daga cikin motar.

"Sannu da zuwa Yaya." Ta faɗa bayan ta ɗan rusuna.

"Yawwah." Ya faɗa ba yabo ba fallasa. Hakan da Mami ta lura da shi ne ya sanya ta ji duk jikinta yayi sanyi, se ta kalli Abban da ke faɗin

"Ina yaran suke?"

"Suna ciki.." ta ɗan dakata anan sannan ta ɗora da

"Ka shiga Yaya, ina da baƙo ne. Zan je na sallame shi yanzun nan se na zo."

"Toh ki yi da jiki." Da "toh" ta amsa tana yin gaba, yayin da ita kuma ta shige cikin parlourn. Duk jikin nata a sanyayen dai ta ƙarasa ɗakin da Kaseem ke ciki, yanzun ma ya ɗauka ze ga Abar begen tasa ne se ya ga Mami ta shigo. Se da suka sake gaisawa sama_sama sannan Mami tace

"Wato Kaseem ka taki rashin sa'a dan kuwa yarinyar da kake nema bata nan, kuma yanzu haka Yayana yazo. Amma In Sha Allah zamu yi magana da kai ko da ta waya ne se na haɗaka da yarinyar.." Ba dan ya so ba ya amsa da

"Toh, na gode sosai Madam, Allah ya kai mu. A gaishe min da Yayan."

"Toh ze ji. Ka gaida gida." Ta faɗa sanda yake dab da ƙarasawa bakin ƙofa. Se da ya fice da motarsa daga gidan sannan ta sauke ajiyar zuciya tana dawowa cikin gidan. A parlour ta samu Abba zaune ta ƙarasa suka sake gaisawa sannan ta miƙe tana faɗin

"Bari na kirasu, da alama basu san da zuwanka ba." Be ce mata komai ba ta shige ɗakin.

"Lulu fito ga Abba ya zo." Ta faɗa bayan ta shiga ɗakin. Da sauri ta ɗauki hula ta ɗora a kanta tana faɗin

"Don Allah Mami?." Ta faɗa tana jin wani irin daɗi, dan ba ƙarya tayi missing Abban nata sosai. Murmushi Mami tayi kana tace

"Ke dai fita ki tabbatar." Se ta fice daga ɗakin da sauri cike da zumuɗin son ganin Abban nata.

"Abba sannu da zuwa." Ta faɗa sanda ta zauna a kusa da shi tana murmushi. Se ya kasa ƙin amsa mata saboda fushin da ya taho da shi yace

"Yawwah.."

"Abba na yi kewarku sosai." Ta faɗa tana kwaɓe fuska da iya gaskiyarta.

"Je ki ɗakko kayanki ki wuce mu tafi." Abba ya faɗa, ita sam bata kawo komai game da maganar Abban ba, hakan ne ya sanyata miƙewa dan zuwan Abban ya sa ta tuna yanda tayi kewar gida.

"A'ah Yaya lafiya kuwa?" Mami ta faɗa tana riƙo hannun Lulu. Abin da ya dakatar da ita kenan, se kuma itama ta juya tana kallan Abban

"Ba lafiya ba. Daga yau ta gama zuwa ko ina, gwara ta zauna a gabana na dinga ganin duk wani abu da take yi." Da sauri dukansu suka buɗe ido suna kallan Abban. Anya kuwa da gaske Abban yake? Me Lulun tayi? Me aka ce masa tayi? Jan hannunta Mami tayi dan zama a kan kujera, se ta zame ta zauna a ƙasa, yayin da Mamin ta zauna a kan kujera tana kallan Abba tace

"Me aka ce maka tayi Yaya? Me ya faru?" Shiru Lulu tayi tana jin yanda jikinta ke rawa, musamman yanda ta ga lokaci ɗaya yanayin Abban ya chanja kamar ba shi ba, har idanunta se da suka kawo ƙwalla, dan kuwa kafin Abban yayi fushi da su ana daɗewa.

"Ashe abin da take yi kenan a makaranta? Ni zata zubarwa da mutunci? Afaaf ni zaki zubarwa da mutunci?" Abba ya ƙare maganar yana kallan Lulu. Zuwa lokacin oily eyes ɗinta sun gama cika taff da ƙwalla ƙiris ya rage ta zuba. Sosai ƙirjinta ke bugawa, tana tsoron fushin Abban, dan a lokacin da yayi fushi se ka ji ka tsani kanka. Kafin ya sake cewa komai Mami tace

"Wani abu aka ce maka tayi Yaya? Hala basu faɗa maka abin da suke yi mata ba? Wallahi nan yarinyar nan ta dawo gida tana kuka kamar wadda akama mutuwa. Ni maganar ma da nake cewa nayi zan maka magana a cireta daga makarantar, ko anan unguwar ne in sama mata wata ta shiga, tunda dai ba iya makarantar ce kawai a duniya ba. Wallahi cin kashin da suke wa Lulu yayi yawa, nan ta zauna tana faɗa min abubuwan da ake mata kamar nayi mata kuka. Haka kawai sun tsaneta babu gaira babu dalili." Ta dakata anan. Kusan second 10 sannan Abba yace

"Kin gama?" Shiru Mami tayi tana yin ƙasa da kanta, dan ta san ma'anar wannan tambayar tasa.

"Nace kin gama?" Ya sake tambaya.

"Ka yi haƙuri Yaya.." shi ne abin da ta faɗa. Se a lokacin ya sauke ajiyar zuciya sannan yace

"Ke! Tashi ki je ki shirya ki fito mu tafi."

"Amma da baka tafi da ita ba don Allah. Idan ma wani abun tayi ni me iya yi mata faɗa ce." Ta faɗa sanda Abban ya miƙe. Ya san idan yace ba zata dawo ba be kyauta wa Mamin ba, dan haka yace

"Zata dawo tukunna. Amma yanzu kam se na ga kamun ludayinta." Shi ne abin da Abban ya faɗa

2 Comments On A JINI TAKE (IZZATA) CHAPTER 1
avatar
abubakar-sunusi

10 months ago

Reply

avatar
abubakar-sunusi

10 months ago

Reply

Please Login or Register in order to submit comment