Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma Lulu ta ja hularta da ta saɓule ɗazun a gefe ta ɗora akan nata.

"Gobe zaku wakilceni wani biki. Na yi niyyar zuwa se dai kuma abubuwan sun haɗe min, ga bikin er gidan Honourable, so yafi zama min dole na je nata, dan haka se ku shirya."

"Ammi ban san zuwa ko ina ni fa." Jadwa ta faɗa tana yamutsa fuska.

"Bare kuma ni!" Lulu ta faɗa tana ɗan tura baki. Harara Mami ta jefa musu dukansu kafin tace

"Ban san shashanci malamai. Umarni ne na baku. And ku yi shiga me kyau wadda zaku janyo min mutunci, manyan mutane ne zasu je wajen, may be ma ku samo min sirikai."

"Kai!!" Lulu ta faɗa tana waro manyan eyes ɗinta gami da buɗe baki. Tare duk suka saka dariya na yadda Lulun tayi. Jadwa tace tana dariya

"Mami tamu ta gargajiya."

"Ban san shirme Jadwa" Mamin ta faɗa tana murmushi lokaci ɗaya tana jefa mata harara.

"Shikenan Mami zamu je ɗin."

"Ai ko baku yadda ba ma dole se kun je." Mami ta katse Jadwa da faɗin hakan.


.. Washegari wajen ƙarfe 8pm ne Didi da Ammi na zaune a parlourn. Tasowa Little yayi daga inda yake zaune ya ƙaraso wajen Ammi yace yana tura baki

"Ammi don Allah Lulu ta dawo" ya ƙare kamar ze yi kuka. Kamo hannun shi Didi tayi tace tana murmushi

"Har ka fara missing nata?" Se ya jinjina kai yana sake langaɓar da kai gefe. Kumatunsa Ammi ta ja lokaci ɗaya tana faɗin

"Idan da tana nan da tuni kun yi faɗa yafi sau a ƙirga, amma daga tafiyarta har ka fara kewa." Shi dai kallan Ammin kawai yake yi. Se ta saka hannu ta ɗakko wayarta da ke ajje a gefenta.

"Ammi kawo na kira." Didi ta faɗa cike da zumuɗi. Miƙa mata wayar tayi, da sauri ta shiga ta soma lalubo number Mami ta kira, se dai a karon farko aka faɗa mata ba zata shiga ba. Se ta yamutsa fuska cikin rashin jin daɗi.

"Didi ba tace komai ba." Little ya faɗa yana kallanta.

"Little wayar ta ƙi shiga." Ta faɗa a hankali dan itama ba ta ji daɗi ba kwata_kwata. Shi dai be fahimci abin da take nufi ba hakan ne ya sanya shi sake faɗin

"Didi ki kirata"

"Tohm zan kira." Ta faɗa tana janyo shi jikinta.

A ɓangarensu Lulu kuwa, kiran wayar da Mami tayi musu ne ya sanyasu soma shiryawa. Jadwa ce ta fara shiryawa cikin wata shegiyar straight gown ta atamfa wadda ta matuƙar kama ko ina na jikinta, ta ɗauki wani yalolon mayafi ta ɗora shi a gefen kafaɗarta. Ɓangaren Lulu kuwa ko da ta gama gyara fuskarta se ta ɗauki wata doguwar rigar abaya me kyau ta saka, da yake Abba ba daga nan ba wajen siya musu kaya masu kyau, hakan ne yasa wannan ɗin ma me kyau ce ta sosai.

"Don Allah ki yi sauri Lulu." Jadwa ta faɗa tana juyowa. Sakin baki tayi tana kallan Lulu ganin ta cikin doguwar riga sakakkiya ta yafa mayafin da shi dai ƙarami ne, tayi matuƙar kyau kamar ka saceta ka gudu.

"Wai kina nufin a haka zamu tafi?"

"Ban gane ba?" Lulu ta faɗa sanda girarta ta tattare waje ɗaya ta ɗan yi ƙasa.

"Kalleni fa Lulu, waye ze kalleni be sake kalla ba? Kalli yanda na shigar na fitar, don Allah ki saka gown kema."

"A'ah fa ni kam na gama shirina." Lulu ta faɗa tana ɗauke kai.

"Please..." In ji Jadwa.

"Idan in cire kayan na yi kwanciyata ne toh" Lulu ta faɗa tana gyara zaman mayafin jikinta.

"Shi kenan ki tashi mu tafi toh!" Se a lokacin sannan Lulu ta miƙe suka fita zuwa parlour. Ba su dai suka fita daga gidan ba se wajen 9 driver ya ɗaukesu zuwa wajen dinner.



CALIFORNIA U.S

Zaune suke su biyu akan kujerun da ke kusa da na juna, kowannensu hannunsa ɗauke da wani ɗan ƙaramin cup da idan mutum ruwa ze sha da shi be fi yayi ƙaramar kurɓa ɗaya da shi ba. Wani ke zuba musu wani abu daga cikin kwalba, daga ya gama zubawa kowannensu se ya kai bakinsa ya shanye. Goge baki Lucky yayi yana ajje numfashi lokaci ɗaya yana wani lumshe ido wanda hakan ze nuna maka a buge yake, yace

"Bad komai ya isheni.. na fara ganin.. ba daidai ba." Yayi maganar a rarrabe kamar me koyan yadda ake magana. Be ce komai ba se sake miƙa cup ɗin yayi aka sake zuba masa ya kai bakinsa, se da yayi hakan kusan sau 5 sannan ya soma sauke numfashi idanunsa da suka yi ja a rufe. Se kuma ya shiga buɗesu kamar waɗanda aka sakawa gum aka manne.

"Ka da da kayi Over dose Dude." Lucky ya faɗa yana kallan yadda Bad Man ɗin ke ta bankawa cikinsa abubuwa, duk da dai dama ya saba yin mankas amma yau ɗin ya ba shi mamaki. A hankali ya sauke idanunsa akan Lucky, dan shi kam da wuya ya sha abu yayi loosing hankalinsa, dan kuwa hatta maganarsa kaɗan take chanjawa, se ka iya rantse wa ma babu abin da ya sha idan ba waɗannan idanun nasa ka kalla ba, waɗanda ke sake ƙanƙancewa su sauya kala.

"Leave me pls! Gobe zan koma Nigeria, ina ƙaunar abubuwan wajen nan." Ya faɗa bayan ya janyo maganar da ƙarfi, sannan ya sauke numfashi lokacin da ya kai ƙarshen maganar.

"Zaka yi missing Dude." Dariya yayi har yana komawa jikin abin da ke bayansa, har kuma zuwa lokacin idanunsa a ɗan lumshe suke se dai ba a rufe ba

"Karka damu." Ya ƙare maganar yana sakin wani murmushi.




A can gidan na Alhaji Matawalle kuwa yau ɗin gaba ɗaya gidan sun tashi ne da shirye_shiryen dawowar Bad Man. Gaba ɗaya Mom ta kasa zaune ta kasa tsaye, duk hankalinta ya rabu ne kan masu girki, da kuma mabanbantan abubuwan da ake ta gabatarwa a gidan duk dan dawowar ɗa ɗaya tilo ga Alhaji Matawalle. Yanzun ma haka fitowarta kenan daga part ɗinta za tayi aike supermarket. A daidai part ɗin Hajiya Sa'adah ta dakata saboda yanda ta ji wani uban ƙamshi na tashi daga sashen. Ta san dama Hajiya Sa'adahn ba baya bace wajen iya girki, dan kuwa idan tayi girki tuni ze baɗaɗe ko ina da ƙamshi, shi yasa ma ita bata yadda da 'yar aiki ta mata girki ba. Se dai yau ɗin haka kawai take ji wannan girkin Hajiya Sa'adahn tayi shi ne ba dan kowa ba se dan Areef. Lallai dole ta sake tashi tsaye, ta sake ɓillo da hanyoyin rashin mutunci ta juye shi a kan Hajiya Sa'adahn duk dan ta fita daga harkar ɗannata. Dogon tsaki taja a ranta tana saƙa ko wannan ɗin wane irin shishshigi da naci ne haka?.



.. Ƙarfe 6pm jirgin da ya ɗakkosu ya sauka a filin jirgi na Malam Aminu Kano. Sanye cikin ƙananan kaya, riga da wando jeans, hannunsa riƙe da wata trolley, yayin da ɗayan hannun nasa ke ɗauke da haɗaɗɗiyar jaka me kyau ko a ido. Farar fuskarsa wasai take, se dai saɓanin yanda take a da yau ɗin cike take da annuri na son ganin Mom ɗinsa da Daddynsa. Duk da kuwa yanda kafin ya taho ɗin yake jinsa duk a takure, amma da ya tsinci kansa a cikin Nigeria, Nigeriar ma Kanon dabo tumbin giwa duk se ya manta da wannan ɗin. Kansa babu komai se tulin kwantacciyar sumar da ta sha gyara da maya mayai masu matuƙar tsada, haka zalika sajensa da ya taho tun daga kansa shi ma a kwance yake luff luff gwanin kyau. Annurin da ke kan fuskarsa ya sake bayyana waɗannan sihirtattun idanun nasa masu kyau da suka ɗan ƙanƙance suka sake kyau. Wasu manya manyan motoci ne na gani na faɗa masu mugun kyau da tashin kai, birjik a cikin airport ɗin, wajen guda 10, dukkansu kuma ɗauke suke da sunayen Matawalle, wanda hakan kaɗai ze nuna maka ko daga ina motocin suke. Ɗan lumshe idanunsa yayi kafin a hankali ya furta akan laɓɓansa

"Bismillahi.. Na dawo fa?!" Ya faɗa fuskarsa na komawa ainahin yanda take babu fara'a. Ya kai wajen minti ɗaya tsaye a hakan kamar ba ze je ko ina ba, se kuma ya soma takawa a hankali cikin tafiyar nan tasa me cike da mazantaka..


Ayi manage da wannan pls..


*♡☆A JINI TAKE☆♡*
*(IZZATA)*


By
_*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_


*CHAPTER ONE*

Page_06


__ Cike da nutsuwa da kuma takatsantsan duka motocin ke tafiya akan titin, kowannensu na kiyaye duk wani abu da ze janyo fushin Bad Man, ko kuma na mahaifiyarsa. Dan in dai har ta Alhaji Matawalle ne ko da laifi suka yi se dai yayi musu faɗa shi ma cikin dabara. Se dai ita Hajiya Salma abu kaɗan zasu kuskure ta juye musu kwandon rashin mutunci, wani lokacin har da barazanar rasa aikin da mutum ze yi. Toh bare kuma yau ɗin da suke ɗauke da shalelenta, ɗa ɗaya tilo da ta ɗauki soyayyar duniya ta ɗora masa, hakan ne ya sa suke takatsantsan kada a samu matsala. A hankali ya ɗaga idanunsa ya kalli titin da suke wucewa kamar masu tausayinsa saboda yanda drivern ke tafiya a hankali. Ya ɗan furzar da iska kaɗan sannan ya buɗe baki yace

"Malam! Wane irin driving ne wannan?" Da sauri drivern yace bayan ya sunkuyar da kansa ƙasa kaɗan

"Sorry sir, Hajiya tace mu yi driving na ka a nutse shi yasa muke kiyayewa. Sorry sir." Ya faɗa cikin girmamawa. Ɗan shiru yayi, ba dan ba dan ba fatali ze yi da maganar nan, se dai kuma tun da har Mom da kanta tace hakan, bari ya bari. Jin da drivern yayi yayi shiru ne ya sanya shi cigaba da driving din, yayin da Bad ɗin sam ji yake kamar yayi mene, dan shi sam be saba da irin wannan driving ɗin ba kamar na en ƙwaya.

Jerin gwanon motocin da suka soma tsayawa a parking space ne ya alamtawa Mom cewar lallai masu ɗakko mata ɗanta sun iso, hakan ne ya sanyata fitowa cike da zumuɗi ta ci ado kamar wadda ake biki, cikin wani tsadadden lace me shegen kyau. Ita tun da suka tafi hankalinta ke kansu dan dai Alhaji Matawalle yace a bar drivers kawai su ɗakko shi ne, ba dan ta so ba dan Alhajin na da power a gidan ya sa ta haƙura. Da sauri drivern ya fito ya saka hannu ya buɗe murfin gidan baya, inda Bad ke ciki, daidai lokacin da Mom ta iso wajen. Se ta saka hannu ta ƙarasa buɗewa tana jin wani irin farin ciki mara misaltuwa. A hankali ya zuro ƙafafunsa zuwa cikin gidan, ƙafarta sa dake cikin wani tsadadden haɗaɗɗen takalmi sau ciki, me matuƙar kyau da tsada. Cikin sauri Mom ta rungume shi tana faɗin

"Oyoyo my Boy." Ta faɗa tana ɗan shafa bayansa a hankali idanunta a rufe ciki da kewar ɗan nata.

"Noo pls Mom, Na girma fa yanzun. Ni yanzu ba yaro bane, look at me mana, Boy ɗinki ya zama Big.." ya faɗa kamar ba shi ba. Murmushi tayi daidai lokacin da ta ɗago tana kallansa tace

"Noo, kai yaro ne a wajena har yanzun.." ta faɗa tana murmushi tana kallan kyakkyawar fuskarsa da ta ƙara kyau na musamman.

"Mommm..!" Ya faɗa yana jan ƙarshen sunan.

"Let's get in." Ta faɗa hannunta riƙe da na shi. A hankali suka soma takawa zuwa cikin gidan. Cikin ƙanƙanin lokaci en aikin gidan suka soma shigar da kayansa ciki, wasu kuma na cigaba da ayyukansu.

"Bari na gaida Mommah!" Ya faɗa sanda suke dab da wuce part ɗin Hajiya Sa'adah. Wani kallo Mom ta watsa masa, daga zuwansa har ze fara ƙona mata rai? Da ƙyar ta furta

"Ba za ka je ba!"

"Reason..??" Ya faɗa sanda ya dakata hannunsa cikin aljihun wandonsa.

"Ka dawo koh? Ka da ka ɓata min rai daga dawowarka." Shiru yayi yana kallan Mom ɗin, so tana so tace masa har zuwa wannan lokacin tana nan dai kamar yanda take? Ya ɗan sauke ajiyar zuciya sannan yace

"It's ohk.."


Ƙaton parlourn Mom din suka wuce, dan Daddy baya nan yayi tafiya yau da safe. Zama yayi akan kujerar ɗakin ya ɗan lumshe idanunsa kafin ya furta a hankali

"I missed komai na nan.." murmushi Mom tayi kafin tace sanda ta zauna a gefensa

"Mu kuma mun yi missing na ka.." Buɗe lumsassun idanunsa yayi, waɗanda daga lumshesu har sun sake shanyewa, yace yana kallanta

"Wanka!" Shi ne abin da ya faɗa kawai. Miƙewa Mom tayi tana faɗin

"Let's go, se kayi a nawa.." girgiza kai yayi hannunsa cikin sumar kansa yace

"No Mom, I prefer to do it on my own.."

"Ohk mu je na rakaka.." Tashi yayi daga kan kujerar yace bayan ya ɗan yamutse fuska

"Ki zauna Mom, I will be back.." Ba dan ta so ba tace

"Ohk.." Amma duk da haka bata ƙyale shi ba se da ta raka shi har ƙofar sashensa, cike da takatsantsan kada a san da dawowarsa cikin gidan.


.. Wani ƙamshi ne ke tashi tun daga bakin sashen nasa, ƙamshii me daɗin shaƙa. A nutse ya saka hannu ya buɗe ƙofar da zata sada shi da parlournsa. Haɗaɗɗen parlour ne wanda ke ɗauke da tsala_tsalan kujeru ash colour, komai na ɗakin ash ne, light and dark ash, hakan ba ƙaramin ƙawata ɗakin yayi ba, se ya zama na musamman, yayi matuƙar haɗuwa. Be bi ta kan parlourn ba kai tsaye ya wuce bedroom ɗinsa. Ban sani ba ashe parlourn ba komai ba ne amma fa idan aka haɗa shi da bedroom ɗinsa. Wani irin bedroom ne wanda ko a ƙasar waje mamallakinsa se ya kasance wani shege ne, ballantana anan. Haɗaɗɗen bedroom wanda ya wadatu da kyawawan furniture masu shegen tsada, kyau da kuma ɗaukar ido. Wani shahararren gado ne da ke gefe ɗaya kame ya sha wani lallausan zanin gado, da pillows kai ba kace gadon mutum ɗaya ba ne. A gefe guda wata ƙaramar kujera ce er ubansu da ke ɗauke da ƙananan pillows, gabanta kuma da wani centre table me kyau. Wajen TV kuwa daban yake, wanda ke ɗauke da wata ƙatuwar TV kamar wadda mutanen cikinta zasu iya fitowa. Lolz 😹
A can gefenta kuma wata wuta ce ke ci a wani keɓantaccen waje, irin wadda ke bawa ɗaki ɗumin nan, tana ci a hankali babu hayaniya. Kai tsayawa ma faɗar abubuwan da ke cikin bedroom ɗin ɓata lokaci ne, saboda yadda ya ji kaya. A hankali cikin takunnan nasa me kyau da ɗaukar hankali ya ƙarasa wajen labulen da ke zagaye da ɗakin, ya saka hannu ya yaye ɗaya, nan take glasses ɗin da ke a wajen suka bayyana, wanda bayan glasses ɗin wasu uban shuke_shuke ne masu matuƙar ƙayatarwa da ɗaukar ido. A hankali ya ɗan sauke numfashi yana lumshe ido lokaci ɗaya kuma yana shaƙar ƙamshin da suka cakuɗe waje ɗaya da iskar da ke kaɗawa me daɗin shaƙa. Ya kai wajen minti 2 a haka sannan ya koma gaban wata muguwar wardrobe da tsayawa faɗar yadda ita kanta ta haɗu ma ɓata lokaci ne, ya buɗe ya ɗauki jerarrun kayansa da aka shirya su ciki kana ya wuce toilet. Kamar yadda bedroom ɗin ya haɗu haka shi kansa toilet ɗin ya haɗu kamar ba banɗaki ba. Yayi wajen minti 30 kafin ya fito ɗaure da towel babba, jikinsa babu abin da ke tashi se ƙamshin sabulunsa me daɗin ƙamshi da ya haɗe da ƙamshin jikinsa da kodayaushe baya barinsa. Kasancewar be hautsina kansa ba ya sanya shi ɗaukar comb ya taje shi sama sama, sannan ya shirya kansa cikin wasu riga da wando kana ya feshe jikinsa da turaruka masu ƙamshi sannan ya nemi waje ya zauna. Wayarsa ya janyo kai tsaye ya shiga wajen message, ya turawa Mom gajeren saƙo kamar haka

"Sorry Mom, ka da ki ji ni shiru, zan ɗan yi bacci kaɗan.." daga haka ya ajje wayar a gefensa, ya haye lallausan gadonsa kana ya ja blanket yana rufe jiƙaƙƙun eyes ɗinsa da har yanzun akwai ruwa a lashes ɗinsa.


.. Da mamaki ta kalli Jadwa tace

"Baƙuwa kuma? Anya ni?"

"Aikam dai wajenki ta zo, may be daga gida aka mata kwatance."

"Ohk" ta faɗa tana saukowa daga gado ta ɗauki wani ƙaramin mayafi ta ɗaure sassalkan gashin kanta da ke a buɗe kuma a tsefe. Ƙarasawa tayi da sauri tana faɗin

"Oyoyo Masoyiya!" Ta faɗa tana rungumeta. Rungume juna suka yi cikin farin cikin ganin junansu kafin suka saki juna kowaccensu ta nemi waje ta zauna.

"Sannu da zuwa." Lulu ta faɗa tana murmushi. Murmushin itama Fatima Kabeer ɗin ta maida mata da shi sannan tace

"Yawwah Masoyiya, se kika ganni a gidan nan kawai."

"Wallahi kuwa, amma fa na ji daɗin zuwan nan naki." Kafin Lulun tace komai Jadwa ta fito daga ɗaki sanye cikin riga da wando kamar koda yaushe, ta ƙarasa ta rungume wata budurwa da ta shigo ɗakin. Itama budurwar rungumeta tayi, Jadwa na faɗin

"Oyoyo Ƙawata." Kallansu Fatima tayi dan yadda suka bata mamaki, yanayin yadda suke rungumar ma kaɗai ba irin tamu ce, irin ta turawan nan ce da ake sumbatar gefen kumatu. Juyawa tayi ta kalli su Lulu tace

"Hey sannunku."

"Yawwah" suka amsa kusan a tare, sannan suka wuce ɗakin Jadwa.

"Kee!" Lulu ta faɗa tana kallan Fatiman. Se da ta sauke ajiyar zuciya bayan ta juyo sannan tace

"Masoyiya!"

"Na'am" Lulu ta faɗa.

"Life style ɗinku ba iri ɗaya da ta en gidan nan ba ce, kalli yanda suke abu kamar wasu turawa, kalli shigar er gidan, ina baki shawara da don Allah kar ki biyewa wannan yarinyar, ki din ga kaffa kaffa a komai. Amma kiyi haƙuri idan ba ki ji daɗi ba." Ta faɗa da ita gaskiyarta.

"Toh na ji." Harara Fatima ta jefa mata sannan tace

"Ai na san halinki ne, ni dai na faɗa miki." Ba dan bata so ta ja maganar da nisa ba da ta tambayi Masoyiyar meye aibun shigar Jadwa? Su suna rayuwa ne babu ruwansu da kowa, rayuwar 'yanci suke gabatarwa a gidan nan, kowa yayi abin da ya ga dama, babu me takura masa. Ba sa saka ido akan kowa, kamar yanda ba sa so a saka musu ido. Ba ta wani daɗe ba Fatiman ta yiwa Lulu sallama ta tafi, cikin jin daɗin zuwan nata Lulu ta rakata har gate sannan suka yi sallama ta koma cikin gida.





.. Kamar za tayi kuka tace

"Little don Allah ina ka jefa min shi?" Ta faɗa tana cigaba da duba cikin ɗakin.

"Yana can fa." Little da ke shirye cikin Uniform ya faɗa yana nuna mata gefen gado. Sake dubawa tayi, kamar ɗazun dai yanzun ma babu komai a wajen, hakan ne ya sanyata kallan Little ɗin ta galla masa harara daidai lokacin da Ammi ta shigo cikin ɗakin.

"Afrah wai me kuke yi ne har yanzun ba ku fito ba?" Ammin ta faɗa tana ƙarasowa cikin ɗakin.

"Ammi Little ne fa ya ɗaukar min niƙab, kuma be san inda ya jefa ba!" Kallan Little Ammi tayi tace

"Ina ka jefa mata?" Se da ya tura baki sannan yace

"Na manta" Maida dubanta kan Didi Ammi tayi tace

"Kin ga wuce ku tafi, kada ku makara, zan duba miki In Sha Allah kafin ku dawo." Kamar za tayi kuka tace

"Tohm." Tana jin duk babu daɗi, saboda ta saba fita da niƙab ɗin zuwa ko ina, idan har dai ba boko ba.

Hannunta riƙe da na Little suke tafiya, se hira yake mata yana tsalle_tsallensa, ita dai amsarta duka bata wuce "Ehh ko A'ah" gaba ɗaya hankalinta ya tafi kan makarantar da take Allah Allah su isa saboda rashin niƙab.

"Fatabarakallahu Ahsanal Khaliqin." Ya faɗa yana sake buɗe idanu dan cigaba da kallan wannan kyakkyawar halitta da a ganin farko ta tafi da shi. A karon farko ya ayyana wa kansa tabbas ya samu matar aure, dan a yadda ya ji zuciyarsa ta harba daga lokacin da yayi arba da Didi. Saurayi ne da aƙalla ze kai shekara 29 baƙi se dai ba can ba, babu laifi kyakkyawa ne, yana cikin manyan kaya masu haɗe da babbar riga, hakan ce ta kara masa kwarjini, yana kame cikin motarsa me kyau, shi yake driving da kansa, se dai ganin Didi da yayi ya sanya shi dakatawa. Ganin alamar tana neman kuɓuce masa ne ya sanya shi saurin cigaba da driving ɗin cikin takatsantsan ya soma binta. Sam bata lura da wata mota da ke binsu ba har suka isa makaranta.

Ko da taje makarantar ma duk se take jinta a takure, dan ta gama sabawa da niƙab ɗin musamman a Islamiyya. Lulu da ke kusa da ita tace

"Didi wai duk kin kasa sukuni akan wannan abun."

"Ina ruwanki?" Didi ta faɗa tana murguɗa baki. Murmushi kawai Lulu tayi tana maida dubanta kan Abida da ta juyo daga bench ɗin gabansu tace

"Hajiya Afaaf, kin dai ƙi zama ƙawata. Amma na fi tunanin Masoyiyarki ce ke hanaki kulani." Kallan juna Lulu da Masoyiyar suka yi se suka saka dariya. Ɗan cizar leɓenta na ƙasa Abida tayi kafin ta rufe idanunta sannan ta buɗesu a lokaci guda, Allah ma ya gani ba tun yau ba Lulun ke matuƙar birgeta, tana birgeta yadda ya kamata, se dai ta ga ita ɗin ba ta wasa bace, amma za tayi iya ƙoƙarinta wajen ganin tayi wani abun da ze sa su soma samun kusanci har ta saki jikinta da ita, kafin ta fito mata a mutum, se dai za ta bi komai a nutse ba za tayi gaggawa ba. Babu daɗewa Gwani ya shigo ajin kamar ko da yaushe cikin irin shigar nan da ya saba yi wadda ke matuƙar yi masa kyau da sake fito da ainahin kyawunsa da kwarjininsa. Daga shigowarsa kowa ya nutsu. Babu ɓata lokaci ya nemi waje ya zauna. Kamar ko da yaushe se ya soma karɓar hadda kafin yayi littafi, hakan ne yasa ya fara karɓa babu ɓata lokaci. Da yake a jere kawai yake karɓar haddar, yana gama karɓar ta Didi, se Lulu da ke kusa da ita ta gyara zama ta cigaba da zamanta tana ɗaɗɗaure fuska irin dan kada ma ya ga fuska bare yayi mata magana. Se dai ga mamakinta se jinsa tayi yace, bayan wajen rabin minti

"Kee!!" Bata juyo ba duk da tayi tunanin da itan yake, se dai ta nuna kamar ta ɗauka da wata yake. Da sauri Masoyiya tace ƙasa_ƙasa

"Lulu da ke fa yake.." Se a lokacin ta juya, bata kalle shi ba tace cikin dakewa

"Ban iya ba!" Shiru ne ya biyo bayan maganar da tayi, dan babu wanda ya taɓa tunanin abin da za tace kenan. Jin alamar kamar be ji bane ya sanyata sake buɗe baki za ta yi magana daidai lokacin da yace

"Tashi ki fita!"

"Ni?" Ta faɗa tana nuna kanta kamar da gasken bata san da ita yake ba. A karo na biyu bayan ɗaukar wasu sakanni ya sake furta

"Fita!!" Ya faɗa idanunsan nan cike da fushi, haka zalika muryarsa na fita da wani amo na ɓacin rai, yana jin a wannan lokacin idan dai har tace zata nuna masa rashin tarbiyya a gaban kowa ze hukuntata, hukunci me tsanani ma kuwa. Gaba ɗaya en ajin kallansa suke yi cike da mamakin yanda ya chanja ɗin lokaci guda, kowannensu ya san shi ɗin tsayayyen namiji ne wanda baya ɗaukar raini, baya bayar da fuskar da za a raina shi, se dai yau ɗin ya sake nuna musu real Affan ɗin ne. Kanta ta ɗauke duk da yanda ƙirjinta ke bugawa amma ta riga ta ɗaukar wa kanta alƙawarin babu wanda ya isa ya wulaƙantata musamman ma kuma Malamin makarantar islamiyya. Hakan ne ya sanyata yin shiru tana ɗan lumshe idanunta. Gaba ɗaya en ajin kallanta suke yi, wasu na mamakin taurin kai irin nata, yayin da wasu da suka santa suke jinjina yadda ta iya yiwa Gwanin taurin kai. A hankali Didi ta runtse idanunta tana ji kamar tayi kuka saboda takaicin abin da Lulun ta aikata. Cikin dabara ta kai ƙafarta kan ta Lulun ta taka sosai, har se da Lulun ta juya ta kalleta, suna haɗa ido Didi ta girgiza kai, kyawawan idanunta cike da ƙwalla. Da sauri Lulu ta ɗauke kai, dan sarai ta gane abin da Didin ke nufi. Sam bata son ɓacin ran Didin se dai ita bata bin bayan dizgi ko waye kuwa ze yi mata ba zata ɗauka ba. Se dai cikin dakewa da basarwa ta miƙe a hankali ta soma takawa hannunta harɗe a

2 Comments On A JINI TAKE (IZZATA) CHAPTER 1
avatar
abubakar-sunusi

10 months ago

Reply

avatar
abubakar-sunusi

10 months ago

Reply

Please Login or Register in order to submit comment