Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

buƙatarsa cikin ɗakin ne, hakan ne ya sanya shi zama ɗin se dai gaba ɗaya hankalinsa na kan wayarsa ne.



... A karo na barkatai ta sake kiran layin da ta ɗora shi a kan wayar da ta bawa Lulun, se dai kamar ko yaushe yanzun ma faɗa mata suke yi a kashe layin yake. Ta yi tsaki babu adadi, ta shiga zagaye ɗakin tana jin ɓacin rai na taso mata. Jadwa da tun ɗazu take ankare da ita tace

"Mami wai har yanzun?" Kamar jira take dama, se kuwa ta soma faɗin

"Ki bar min ja'irar yarin mana. Ina ganin jiki zan saɓa na sake zuwa can gidan ko zan samu Kaseem ya ƙyaleni na huta." Mami ta faɗa tana komawa ta zauna a kan kujera. Tana zama kuwa se ga kiran Kaseem ya sake shigowa wayarta. Kamar ba za ta ɗaga ba, se kuma ta ɗaga ɗin ta kara a kunnenta. Daga can ɓangaren yace

"Amm Madam dama cewa na yi, why not ba za ki ba ni address na gidansu ba? Idan ya so kai tsaye se na je wajenta. Ko ma na fara zuwa wajen mahaifinta saboda wallahi da gaske na ke aurenta zan yi." Ajiyar zuciya Mami ta sauke kafin ta soma faɗin

"Kaseem ka yi haƙuri, ka san fa yarinyar nan dududu a S.S 1 ta ke.. Abbanta kuma na so ta yi karatu. Ko ma ba haka ba bana jin ze aurar da ita ba ta gama secondary ba, shi ya sa na ke nema maka wata hanyar da zaku samu dai kuna gaisawa." Kamar yana gabanta ya shiga girgiza kai sannan yace

"Ki yi haƙuri, don Allah ki ba ni address ɗin. Idan na je wajen mahaifin nata ina so ne kawai a san da zamana ko da ba yanzu ze aurar da ita ba. Amma na fi so ko me zan yi na yi shi ne da sanin mahaifin nata." Shiru Mami ta yi se kawai ta amsa da

"Toh shi kenan.." Daga haka ta katse kiran. Duk abin da dama suke cewa Jadwa na ji, se da Mamin ta katse kiran sannan ta soma faɗin

"Mtswww, wai shi a lallai dole mutumin kirki.. duk ƙoƙarin da kike yi be gani ba shi uban iya. Aikin banza" ta ƙare maganar tana maida kanta kan wayar da take dannawa. Ita dai Mami ba tace komai ba duk da dai ta yadda da abin da Jadwan ta faɗa.



.. "Abeey wallahi ba ka da lafiya.. ka bari na kira mota mu kaika asibiti.." Murmushin ƙarfin hali Abeey ya yi yana kallan Gwani kafin yace cikin ƙarfin hali

"Na sani.." ya ƙare maganar yana ɗan sauke numfashi kamin ya ɗora da

"Idan ma asibitin kuka kaini wani abun za su ƙaƙalo su ce a yi aiki kamar wancan karon.. toh ina kuɗin su ke? Ina za a nemo kuɗin?" Ɗan lumshe manyan fararen idanunsa Gwani ya yi sannan ya buɗe yace

"Allah ze kawo Abeey. In Sha Allah ma ba wata babbar damuwa ba ce.."

"In Allah ya yadda.." Ummeey ta faɗa cike da tausayin Abeeyn da ke sauke taggwan ajiyar zuciya kamar wanda ya yi aikin wahala..


https://chat.whatsapp.com/BClMNPwWybg2n3oRvtemv8

*♡☆A JINI TAKE☆♡*
*(IZZATA)*


By
_*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_


*CHAPTER ONE*

Page_12


___Cikin mamaki Didi ke kallan Abida da ke cigaba da shigowa cikin parlourn. Abida ta saki murmushi sanda ta ida shigowa cikin ɗakin. Har ta ƙaraso ɗin Didi ba ta dena binta da kallan mamaki ba. "Me ya kawota gidan?" Ita ce tambayar da ke ta lugude cikin zuciyarta.

"Wannan daga gani Didinmu ce.." Abida ta faɗa tana murmushi. Ɗan lumshe idanu Didi ta yi tana ɗauke kai sannan ta dawo da shi kan Abidar tace

"Lafiya dai koh?"

"Eh fa. Kawai dai na zo ne mu gaisa da Umma. Ina Afaaf?" Ta yi maganar duka a haɗe. Sauke ajiyar zuciya Didi ta yi, se ta shiga lalube cikin zuciyarta ko da za ta iya hasaso dalilin Abidar na zuwa gidansu, bayan ba su da wani haɗi da ita, daga ita har Lulu?. Kawai dai se ta fice daga ɗakin zuwa na su ɗakin inda Ammi da Lulu ke zaune.

"Ammi kin yi baƙuwa." Didi ta faɗa tana neman waje ta zauna. Da mamaki Ammi tace

"Baƙuwa kuma?"

"Ehh ƙawar Lulu ce." Da sauri Lulu ta kalli Didi jin ta ambaci sunanta.

"Ƙawa kuma? Ni ɗin?" Ta tambaya cike da mamaki

"Fatima?" In ji Ammi. Girgiza kai Didi ta yi sannan tace

"A'ah wannan wata sabuwa ce.." ta faɗa tana ɗaukar littafinta da ta ke karantawa. Babu shiri Lulu ta sakko daga kan gadon tana faɗin

"Am eager na ga wace friend ɗin ta wa.." ta faɗa da iya gaskiyarta. Dan da gasken ta ƙagu ta ga wacce me ƙarfin halin ce har da biyota gidansu? Dan ita dai ta san ba ta da wata ƙawa bayan Masoyiya.

"Ke ce?" Ta faɗa cike da maɗaukakin mamaki a kan fuskarta. Gyara zama Abida ta yi tana ji kamar ta tashi ta rungume Lulun, se dai ta basar tace tana murmushi

"Wallahi kuwa.." taɓe baki Lulu ta yi lokaci ɗaya tana jinjina kai.

"Ikon Allah.." ta faɗa tana ƙarasowa ta zauna kan kujerar da ke kusa da wadda Abidar ke kai. Tana zama se ga Ammi ta fito. Cikin sauri Abida ta sauko daga kan kujerar da take kai ta tsuguna har ƙasa, tun kafin Ammin ta gama ƙarasowa cikin ɗakin tace

"Ina wuni Umma? An yini lafiya?" Ta tambaya lokaci ɗaya.

"Lafiya ƙalau Alhamdulillah.." Ammi ta faɗa tana neman waje ta zauna. Se Abidar ta cigaba da zama a ƙasan tana ɗan murmushi jefi_jefi, wai ita a lallai dole me hankali.

"Ki koma kan kujerar mana." Ammi ta faɗa tana murmushi. Da sauri ta girgiza kai tace

"A'ah Umma nan ɗin ma ya yi.." miƙewa Ammi ta yi tace tana kallan Lulu da tun shigowar Ammin ba ta sake cewa komai ba

"Ki kawo mata ruwa mana?"

"Toh" ta amsa da hakan, yayin da Ammi ta shige ɗaki. Tashi tsaye Abida ta yi tana faɗin

"Ki bar shi ma kawai wallahi, gida zan tafi. Ai mun gaisa da Umman. Bari na wuce.."

"Toh ki gaida gida.." Lulu ta faɗa.

"Gida ze ji.." Abida ta faɗa tana ficewa daga ɗakin. Lulu ta bi ta da kallo har ta fice, kafin ta ɗaga kafaɗa tana taɓe baki ta wuce ɗaki.



... Jikinsa a matuƙar sanyaye ya fito daga cikin office ɗin. Se ya ɗan dakata a gefe, ya jingina jikinsa da jikin bango idanunsa a ɗan lumshe. Gaba ɗaya tunaninsa ya tafi ne wajen yadda ze dinga samun kuɗin da za a dinga yi wa Abeeyn wankin ƙoda duk bayan sati 2. Bugun zuciyarsa har wani ƙaruwa ya yi, sanda ya ke wannan tunanin. Sam be lura da tsayuwar wani a kusa da shi ba, se lokacin da ya ji magana kamar daga sama

"A'ah Malam Affan.. Lafiya dai koh?" Abba da tun ɗazu ya hango shi ya faɗa bayan ya ƙaraso dab da shi. Se a lokacin ya buɗe idanunsa da sauri ya sauke su a kan Abban. Shaida fuskar da ya yi ne ya sanya shi ƙaƙalo murmushin yaƙe yace

"Lafiya ƙalau.." ya yi maganar yana miƙa masa hannu suka gaisa. Girgiza kai Abba ya yi yace

"Anya kuwa?" Ƙarya ba halinsa ba ce, hakan ne ya sanya shi gyara tsayuwarsa sannan yace

"Ehh toh.. Abeey ne babu lafiya..Amma In Sha Allah babu wata damuwa, dan yanzu haka ma fita zan yi, daga zarar na dawo za mu koma gida ne.."

"Ikon Allah.. Toh Allah ya ba da lafiya me ɗorewa."

"Ameen Ameen.."

"Mu je na gaishe shi koh?" Abba ya tambaya yana kallan Gwanin.

"Eyyah da yake ya samu bacci yanzun.." jinjina kai Abba ya yi cike da gamsuwa da maganar Gwanin, tun kafin ya ƙarasa yace

"Toh shi kenan, Allah ya ƙara afuwa."

"Ameen na gode." Gwani ya faɗa da ɗan murmushi kan fuskarsa, dan sosai ya ji daɗin yadda Abban ya nuna kulawarsa a kan Abeeyn. Dama tun sanda ya zo wajensa ya fahimci mutumin arziƙi ne, se dai yanzun ma se mutuncinsa ya ƙaru sosai a cikin idanunsa. Sallama suka yi, Abba ya yi inda ze je, yayin da shi kuma Gwani ya tafi wajen Ummeey da ya tabbatar tana can tana jiransa ne. Aikuwa tun kafin ya ƙaraso ta miƙe cike da zumuɗin jin abin da ze faɗa ɗin. A nutse ya ƙaraso wajen yana kallan Ummeeyn da duk damuwa ta gama bayyana a kan fuskarta yace

"Ummeey.. ki kwantar da hankalinki. In Sha Allah babu damuwa me yawa. Zan fita yanzun, zan yi ƙoƙari na samu na haɗa kuɗin da za a yi masa wankin ƙoda ko na wannan satin ne.." ya ƙare yana ɗan ajje numfashi gami da lumshe idanunsa.

"Wankin ƙoda kuma Affan?" Umma ta faɗa tana buɗe ido sosai. Cikin kwantar da murya yace

"Ki kwantar da hankalinki Ummeey.." ya yi maganar yana kallanta. Girgiza kai Ummeey ta yi ba tare da tace komai ba, se komawa da ta yi ta zauna a kujerar da ta tashi daga kanta tana ji kamar ta yi kuka. A yanzu dai a yanayin da suke ciki samun kuɗin da za a dinga yiwa Abeeyn wankin ƙoda se dai idan Allah ne ze kawo musu wata hanyar.

"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel." Ummeey ta faɗa sanda ta ke kai hannunta kan fuskarta cike da tausayin kansu. Kusa da ita Gwani ya zauna, ya sake ƙasa da murya cikin rarrashi yace

"Ummeey ka da ki ɗaga hankalinki. In Sha Allah kuɗin nan za su samu."

"Allah ya yadda." Ummeeyn ta faɗa ba dan tana da tabbacin za su samu ɗin ba, se dan sunan Allah da ya ambata.



.. Bin ta da kallo Ammi ta yi sanda take ƙoƙarin ɗaura niqab cike da ƙarfin hali. Cikin tausayawa Ammi tace

"Afrah ajje niqab ɗin nan, da lafiya ake yin komai. Saboda haka ki bari idan kika warke se ki je.." Ammin ta faɗa saboda yadda ta lura da Didin kawai ƙarfin hali take yi amma ba ta da lafiya. Duk da haka kuma ba ta haƙura ba take shirin tafiya. Se da Lulu ta tura baki gaba, dan ta san idan da ita ce cewa za a yi ta tafi ta warke a can, dan kowa ya san halinta, abu kaɗan ne ze sanya tace ba za ta je makarantar ba, ko da kuwa lafiyarta ƙalau. Saɓanin Didin da koda yaushe cikin son zuwa makaranta take ko da kuwa ba ta jin daɗi.

"Didi fa baki da lafiya.. kawai ki bari se gobe idan Allah ya kai mu." Itama Lulu ta faɗa tana kallan Didin da har ta koma ta zauna. Se kawai ta koma ta kwanta a kan gadon tana jin wani irin sanyi na ratsa ƙasusuwanta. Ɗaukar katon blanket Lulu ta yi ta ɗora mata a kai sannan ta kalli Ammi tace

"Ammi mun tafi."

"Toh Allah ya kiyaye."

"Ammi mun tafi." Little ma ya faɗa yana yin gaba. Shi ma da addu'ar ta bi shi da ita tana murmushi.


Ko da suka je makarantar yau Gwani be zo ba, dan haka wani malamin ne ya shigar musu ajin. Hakan ne ya sa yau ɗin da wuri aka tashe su. Dan haka ana tashin nasu Lulu ta kama hannun Little suka fito daga makarantar tare da Masoyiya.

"Aou Fatima da tafiya za ki yi ki bar ni?" Abida ta faɗa sanda ta ƙaraso inda suke.

"Eyyah a'ah fa. Kin ga mun tafin ne?" Fatima ta faɗa.

"Toh don Allah idan ba zaku samu damuwa ba ku ɗan raka ni wani gida mana?"

"Gida kuma?" Fatima ta tambaya.

"Ehh pls ka da ku ce a'ah.."

"Masoyiya ni fa tafiya zan yi, kin san Didi ba lafiya.." Lulu ta faɗa tana kallan Fatiman.

"Wani gida fa kawai za ku raka ni.." Fatiman ta sake faɗa se dai yanzun Lulu take kalla.

"Pls mu rakata ɗin.." Fatima ta faɗa tana kallan Lulu. Da sauri Lulu ta girgiza kai sannan tace

"A'ah ku yi haƙuri pls.."

"Pls mana." Fatima ta faɗa tana riƙo hannun Lulu. Se da ta jefa mata harara sannan tace

"Mu yi sauri don Allah.." Wani irin murmushi ne ya suɓuce wa Abidar. Se ta soma takawa tana tunanin yanda za ta yi su rabu da Fatima a yanzun. Cigaba da tafiya suka yi jefi_jefi suna ɗan taɓa hira kaɗan. Little kuma na ƙarawa tafiyar tasu armashi ta hanyar surutansa wasu na hankali, wasu na shirme. Dakatawa Fatima ta yi tana ɗan yamutse fuska sannan tace

"Ina ganin fa baƙon watana ne wallahi.." ta yi maganar tana ɗan riƙe cikinta. Kallanta dukansu suka yi. Lulu tace

"Toh mu koma gida kenan?"

"A'ah mu ƙarasa gidan mana, ae za a samu pad." Abida ta yi ƙundunbalan faɗin hakan, cike da fatan ka da Fatiman tace "Toh" Aikuwa addu'arta ta karɓu dan kuwa buɗar bakin Fatima se cewa ta yi

"A'ah Abida. Kin ganni fa a gida, gwara na tafi gobe ma haɗe, ki yi haƙuri.."

"Babu komai ai, tunda ga Afaaf za ta raka ni."

"Waye Afaaf?" Lulu ta faɗa tana kallan Abidar.

"Ke mana, ko ba za ki raka ni ba dan Masoyiyarki ta tafi? Don Allah Fatima ki ce ka da ta ƙi raka ni. Ni kaɗai zan je kamar wata mayya." Ta ƙare kamar me neman taimako. Cikin rarrashi Fatima ta kalli Lulu tace

"Pls ki rakata mana." Ba dan ta so ba, se dan kawai dai ka da Abidar tace ta wulaƙanta ta ne ya sanyata faɗin

"Na ji.." ta faɗa tana sake kama hannun Little suka cigaba da tafiya. Dan farin ciki Abida ji ta yi kamar ta tsaya ta taka rawa. A haka suka cigaba da tafiya, har suka ɓillo wani bakin titi. Cike da ƙosawa da tafiyar, dama kuma abinka da ba ta yi niyya ba, Lulu tace

"Ni fa gaskiya am tired. Har yanzu ba a zo ba?" Murmushi Abida ta yi kana tace

"Mu na tsallaka titi gidan ya ke.."

"Ah toh.." Lulu ta faɗa. Daidai lokacin da suka tsallaka titin ya yi daidai da lokacin da Gwani ya ke saukowa daga cikin Napep tare da wani ɗalibin Abeey. Shi ya soma sauka sannan Gwani ya sauka, ya miƙawa me Napep ɗin kuɗinsa. Yayin da ɗalibin Abeey ɗin me suna 'Abbati' ya ɗan miƙe hannunsa kamar wanda suka yi tafiyar awanni ya gaji. Daidai sanda ya ɗan juya yayi daidai da lokacin da su Lulu suke ƙoƙarin shiga gidan hannunta riƙe da Little. A haka sam ba zaka gane ma gida ba ne, saboda yanda wajen ya ke kamar ba ƙofar gida ba, sannan kuma shaguna da yawa sun yi ƙoƙari wajen kare gidan, dan idan dai har baka san da zaman gidan a wajen ba, toh ba za ka gane akwai gida a wajen ba. A kan Lulun kuwa idanunsa suka sauka sanda ta ida shigewa cikin gidan. Tsaki Abbati ya ja yana girgiza kai, cike da takaicin wannan abu da ke faruwa. Ya kasa shiru har se da ya kalli Gwani da ke ƙoƙarin sake tare musu wani Napep ɗin saboda wannan ɗin tayarsa ce ta samu matsala.

"Wallahi ya kamata a saka ido a kan gidan nan sosai. Iyaye ma kuma yana da kyau su sake saka idanunsu a kan 'ya'yansu. Wallahi Malam yanzu ba ka ga wata yarinya da na gani ba dududu a shekaru ba zata wuce a ƙirga su ba, amma ta shiga gidan nan. Ban san me yasa kamar hukuma na tsoron gidan nan ba ne." Girgiza kai kawai Gwani ya yi sannan yace a nutse

"Allah ya kyauta, ya kuma shirya.." ya yi maganar sanda ya ke hawa cikin Napep ɗin da ya tare musu.

A ɗan mamakance Lulu ta dinga bin gidan da kallo, dan gaba ɗaya ta rasa a wane muhalli za ta aje gidan. Ta kasa gane me ake yi a gidan, suna ake yi ko biki ake yi? Duk ta kasa ganewa.

"Wai biki a ke?" Little ya faɗa yana bin wani waje da a ke kiɗa da kallo.

"Ehh" ta faɗa, dan itama a yanzun ta gane bikin a ke yi, saboda yanda ta ga taron mata ne a ko ina, se jefi_jefin maza kaɗan kaɗan.

"Kar ki damu Afaaf, ai mun zo." Abida ta faɗa tana jin ita kam yau burinta ya gama cika, tunda har ta iya ɗauko Lulun ta kawota gidan nan, ai komai ya ƙare kuma. Har cikin wani parlour suka isa, ita dai Lulu ta gama ƙuluwa, ta gama fusata dan har ta riga ta ƙudura a ranta cewar, ko me Abidan za ta yi ba za ta sake rakata wani wajen ba, se dai ta ji haushi ta dena kulata. Ita kaɗai ce a cikin ɗakin sanye cikin wasu riga da wando waɗanɗa suka bi lafiyar jikinta suka zauna sosai. Siririya ce se dai ba can ba, amma da ke tana da diri ya sanya a kallo ɗaya ba zaka kirata da siririya ba. Kanta babu ɗan kwali se tulin attach ɗin da ke zaune a kanta kamar ba ɗorawa a ka yi ba, saboda yanda suka zauna sosai.

"Yallaɓiya saukar alkhairi.." Abida ta faɗa tana murmushi gami da ƙarasawa kusa da matar. Da sauri Ladi ta juyo tana kallan Abida kafin ta maida kanta kan Lulu da har lokacin take tsaye a bakin ƙofar, ta daɗe da ƙaguwa a kan Abidar ta fito su tafi. Lumshe idanunta Ladi ta yi kafin ta koma kan kujera ta zauna yaɓar har lokacin idanunta a kan Lulu. Se ta nuna wa Lulu kujera tana faɗin

"Ki zauna mana Baby.." Ladin ta faɗa tana wani maƙe muryarta da tafi kama da ta wani ƙaton gardin. Ita sam Lulu ba ta kawo komai ba, dan ba ma ta ji sunan da Ladin ta kirata da shi ba. Haka zalika shigar jikinta ma bata damu da ita ba, dan tafi tunanin me aure ce, kuma yamma ta yi shi ya sa ta yi wa mijinta kwalliya. Se ta ɗan zauna kaɗan tana sake riƙe hannun Little fuskarta a haɗe saboda yanda ta riga ta ƙulu da Abida.

"Duk yanda ki ke kwatanta min ita ai ta ninka hakan sau 10 Abida. Wannan aba haka kamar ita ta yi kanta? Kalleta fa don Allah? Ke na ninka miki kuɗinki sau 3, dan na tabbatar yau ɗin nan akwai ƙurewa daɗi maleji.." Ladi ta faɗa tana sakin wani shu'umin murmushi har lokacin idanunta na kan Lulu tana binta da wani irin kallo kamar tsohuwar mayya..



https://chat.whatsapp.com/BClMNPwWybg2n3oRvtemv8

*♡☆A JINI TAKE☆♡*
*(IZZATA)*


By
_*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_


*CHAPTER ONE*

Page_13


___Cikin er rashin fahimta Lulu ta ɗaga kai ta kalli matar da a lokacin ta miƙe daga inda ta ke zaune ta soma takowa zuwa wajen Lulu, lokaci ɗaya tana furta

"Karɓi yaron ki ajje mata shi.. Me ya sa ma ku ka taho da shi?" Ta yi maganar sanda ta ƙaraso dab da Little. Ta saka hannu ta riƙo hannunsa. Da sauri ya fuzge hannunsa yana ɓata fuska gami da shigewa jikin Lulu. Tashi ta yi daga kan kujerar tana sake riƙe hannun Little da ke kuma ƙanƙame hannunta. Se dai ga mamakinta se ta ji matar na faɗin bayan ta kalli Abida

"Ɗauke shi ki fita da shi, ze hanamu rawar gaban hantsi.." Ba ta ƙarasa maganar ba se kuwa Abida ta ƙaraso ta kai hannunta wajen Little dan ɗaukarsa. Iya ƙarfinsa ya saka ya fashe da kuka daidai lokacin da Lulu ta gama fusata da su gaba ɗayansu. Cikin fushi tace

"Wai meye haka ne? Ina za ki kai Little ɗin? Ina ruwanki da shi? Idan za ki gama abin da ya kawoki gidan nan ki zo mu tafi toh. Idan kuma ba za ki tafi ba ki faɗa min na kama hanya.." Da mamaki Ladi ta kalli Abida cikin ƙasa da murya tace

"Ki na nufin ba ta san abin da ya kawota gidan nan ba?" Se da ta ɗan yamutse fuska sannan tace

"Da ta sani da ba ki ganta cikin gidan nan ba.."

"Ohhh.. na gane.." Ladi ta faɗa tana jinjina kai daidai lokacin da ta maida dubanta kan Lulu. Ɗan lumshe idanunta Lulu ta yi saboda yadda ta ga Abidar da matar na neman maidata er iska, ta yi magana ma sun juya suna wasu maganganun. Hakan ne ya sanya ta saɓi Little da ke matse ƙwalla a kafaɗarta sannan ta yi hanyar fita. Da sauri Ladi ta yi maza ta tare hanyar tana faɗin

"Na shiga ukuna, ina kuma za ki je?" Cikin rashin fahimtar dai Lulu tace

"Ban gane ba? Nan ɗin gidanmu ne da in zan fita za a tambayeni inda zan je?" Ta tambaya tana watsa mata wani kallo. Ajiyar zuciya Ladi ta sauke tana tunanin ta yadda za ta ɓullowa Lulun, dan daga yadda ta ke magana kaɗai ta fahimci ita ɗin ba irin matan da ake kawo mata ba ne. Dole se ta yi da gaske, idan ba haka ba tana ganin wannan ganimar haka za ta tafi ba tare da ta ƙaru da komai ba. Cikin rarrashi ta soma faɗin

"Kin ga ki kwantar da hankalinki, ba wani abun tashin hankali ba ne. Kawai fa harka ce ta jin daɗi da za ki samu kuɗi bayan jin daɗin.. Ke Abida zo ki buɗa mata bayani yanda za ta fi fahimta.." ta ƙare maganar tana kallan Abida. Kamar wata doluwa Lulu ta bi Abidan da kallo tana jin yadda jikinta ya yi wani mahaukacin sanyi, har wani rawa ya soma yi, dan kuwa hatta hannunta da ke ɗauke da Little se da ya ka sa riƙe shi, ta ɗan sassauta riƙon sanda shi kuma ya ke sake riƙeta kamar ze shige cikinta.

"Kin ga Afaaf, ki kwantar da hankalinki, ka da ki tashe shi. Ba fa wani abu ne me wahala ba, kawai dai za ku ɗan shafe mintuna ne fa da Jakadiya ku ɗan jiyarwa kanku daɗin jikinku.." Runtse idanunta Lulu ta yi sanda bugun zuciyarta ya ƙaru, yanayin yanda jikinta ke rawa ma ya ƙaru. Ta kai wajen second 20 idanun na ta a lumshe, wanda farin ciki har ya soma cika zuciyar Ladi da ke ganin Lulun za ta amince da buƙatarsu. Se dai me? Cikin sakannin da basu wuce 3 ba Lulu ta buɗe idanunta a kan Ladi da kuma Abida da ke kusa da juna, muryarta har rawa take yi sanda ta soma faɗin

"Ashe Abida ke ɗin mutuniyar banza ce? Ashe mutuniyar wofi ce ke mara tsoron Allah? Ashe shi ya sa tun kallan farko da na miki na ji ba ki min ba? Na kasa sakin jiki da ke duk saboda yanda zuciyata taƙi aminta da ke? Amma ki ka yi yadda za ki yi, ki ka yi amfani da muguwar zuciyarki da muguwar manufarki ki ka sakani na soma kulaki, har na iya ɗakko jiki na rakoki wani wajen? Tirr da irin wannan rayuwar taku. Tirr da wannan ƙazamar rayuwar taku da ba kwa jin kunyar idanun mutane ballantana ku ji tsoron Allah. Wa'iyazubillahi, Allah ya kiyasheni da aikata aikin danasani da nadama.. Matsamin na wuce.." Ta yi maganar sanda ta sake rungume Little.

"Babu inda za ki je. Ai kin shigo kenan.. ta yaya ma zan bari ki shigo gidan nan sannan na barki ki fita ba tare da na ji kalarki ba? Tun da Abida ta ke kwatanta min ke na ji na ƙawatu da son ganinki. Daga kuma lokacin da na yi ido biyu da ke na ji duk wani burina na son ganinki ya ruguje, abin da kawai na ke buƙata shi ne kasancewa da ke.." Ladi ta faɗa tana matsowa kusa da Lulu. Wani irin hawaye me zafi ne ya zubo daga idanun Lulu na dama na tsantsar takaici da kuma sake yin tirr da halin Abidar da Ladin. Ganin yanda ta ke matsowa kusa da ita ne ya sanyata saurin matsawa gefe tana faɗin

"Ka da ƙazamin jikinki ya soma gangancin taɓani.. ki matsamin na fita idan ba haka ba wallahi zan miki abin da ba za ki taɓa mantawa da Afaaf a rayuwarki ba.." Lulu ta faɗa duk da yanda take jin ƙirjinta na wani irin bugawa cike da tsoro.

"Bana son taurin kai Malama Afaaf.. kawai ki yi biyayya, salin alin za ki fice daga gidan nan da kuma damin kuɗi a hannunki.." In ji Ladi tana sake matsawa kusa da Lulu

"Ke ce matsiyaciya ba ni ba, ke kuɗi suka dama.." Kafin Lulu ta ƙarasa faɗa ta yi gefe saboda yadda Ladi itama ta yi gefe dan so take kawai ta ƙwace Little daga hannun Lulu sannan ta san yanda kuma za ta yi da Lulun. Hakan ne ya janyo Lulu ta taka

2 Comments On A JINI TAKE (IZZATA) CHAPTER 1
avatar
abubakar-sunusi

1 year ago

Reply

avatar
abubakar-sunusi

1 year ago

Reply

Please Login or Register in order to submit comment