Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya isa ƙofar gidan mamaki be bar kansa ba. Ya rasa gane me ya kawo ɗan gidan Alhaji Matawalle gidansa? Me Didi ta masa da yazo wajenta? Mene ne ya sumar dasu gaba ɗayansu kuma lokaci ɗaya? Duk da likitan ya yi masa bayanin dalili amma yana buƙatar wani gamsheshshen bayanin, musamman a kan zuwan Bad ɗin cikin gidansa. Dan kuwa Habu Driver ya faɗa masa yanda komai ya faru, kamar yadda kuma ya zo ya gansu a sume hakan ya faɗawa Abba. Yanzu kuma shi ne ya ba shi shawarar zuwa ya sanarwa da Alhaji Matawallen abin da ya faru, sannan ya masa magana a kan ya jawa ɗansa kunne a kan zuwan da ya masa cikin gida.

"Yace ka jira shi a ɗakin can.." Wani ya faɗa yana kallan Abban. Kallansa Abba ya yi da ɗan mamaki, dan be taɓa tunanin a zuwan farko Alhaji Matawallen ze yadda ya gan shi ba, bayan yadda wasu ke faɗar shi yana da jin kai. Se dai tun a karon farko maganganun mutanen na ƙoƙarin tashi a matsayin ƙarya da baƙar hassada. Har ɗakin aka raka shi. Ya nemi waje ya zauna har kuma lokacin hankalinsa gaba ɗaya na kan Didi da aka tabbatar masa da babu abin da ya sameta. Cikin nutsuwa ya yi sallama cikin ɗakin. Abba ya amsa yana kallansa.

"Tabbas da gaske shi ɗin ne" Abba ya faɗa a ransa yana sake kallan Alhaji Matawallen. Se dai shi yau ɗin da ya gan shi a fili ma se ya ga kamar yafi kyau a kan yadda yake ganinsa a hoto.

"Barka da wannan lokacin.."

"Barka dai.." Daddy ya faɗa. Se da suka gaisa dai sannan Abba ya gyara zama yace

"Na san za ka yi tunanin ko me ya kawo ni gidanka? Toh dama dai magana ce a kan ɗanka.." Da sauri Daddy ya ɗaga kai ya kalli Abba cike da mamaki yace

"Ɗana kuma? Me ya faru da shi?" Ya faɗa hankali a tashe. Babu ɓata lokaci Abba ya shiga zayyana masa abin da ya faru daga farko har ƙarshe. Yana shirin zayyane masa dalilin zuwansa se ya ga ya miƙe yana faɗin

"Ya Subhanallahi.. Ya Salam.. Babu dai abin da ya sami ɗiyar taka koh?" Daddy ya tambaya cike da kulawa.

"Ehh.." Abba ya faɗa. Komawa Daddy ya yi ya zauna yana mamakin abin da Abban ya faɗa, kenan me ya kai Areef gidansa? Me ya sanya shi ya sha wani abu bayan be taɓa sha ba? Ko dai wasu ne suka ba shi ya sha ba tare da ya sani ba? Yana da tabbaci a kan ɗan nasa, dan kodayaushe cikin masa addu'a yake. Ya kuma san ba ya neman mata, ballantana yace kai tsaye ya je wajen yarinyar ne dan ya haiƙe mata. Toh amma me ya faru kenan?

"Mu je asibitin.." Daddy ya faɗa yana sake miƙewa. Miƙewa Abba ya yi yana kallan Daddyn cike da tausayawa. Haka kawai ya ji ya ba shi tausayi a kan yanda mutane ke kallansa. Ashe haka yake da sauƙin kai?. Duk yanda masu kula da Daddyn suka taho dan yin aikinsu, haka Daddyn ya dakatar dasu. Ya hau motar da kansa, sannan Abba ya hau ɓangaren me zaman banza, Daddy ya tashi motar.

Tunda suka shiga asibitin se idanu suka koma kan Alhaji Matawalle. Magulmata suka ƙaru, aka cigaba daga inda aka tsaya. Ko bi ta kansu Daddy be yi ba ya sauka daga motar zuwa cikin asibitin. Kai tsaye ɗakin da aka kwantar da Didi ya fara zuwa ya dubata. Tana kwance tana baccinta hankalinta kwance. Daddy ya sauke ajiyar zuciya sannan ya nufi ɗakin da aka kwantar da Bad Man. A hankali ya ƙarasa yana kallan kyakykyawar fuskarsa da ta yi fayau kamar mara lafiya. Cikin tausayawa ya kai hannunsa ya ɗan shafa goshinsa. Wayar Bad ɗin da ya gani ajje ya ɗauka ya ɗan soma dannawa. Kai tsaye message ya fara dubawa, ganin babu wani abun da ze gani ya sanya shi shiga call logs. Number Hero ce ƙarshen wadda aka kira. Hakan ne ya sanya shi kiran layin ya sakata a hands free yana kallan Abba da ya shigo cikin ɗakin. Kira 1 Hero ya ɗaga wayar cike da mamaki.

"Bad ba dai har ka dawo gida ba? Ina yarinyar take? Marin nata kawai ka yi kamar yadda kace ko kuwa dai wani abun ya faru? Ka na nufin kace min babu wani abu da ka mata? Ka bani labari don Allah.." Hero ya faɗa hankali a ɗan tashe. Dan ya san in dai har ƙwayar nan ta yi aiki a jikin Bad Man, toh ba ze samu damar da har ze iya kiransa a waya ba, dan ya san yanzu haka ma yana can a wata duniyar in dai ta yi masa aiki.

"Ƙitt!!" Daddy ya katse wayar. Se ya nemi waje ya zauna a cikin ɗakin ya kifa kansa a kan hannunsa. Ɗa ne Allah ya ba shi mara jin magana, ba dan haka ba ya daɗe da raba shi da irin waɗannan abokan. Yanzu ga shi suna neman tura shi ga halaka be sani ba, da tsausayi ya faru se dai su janyo masa azabar Allah da kuma kunyar duniya, da ɓacin suna. Yayin da suke gefe babu abin da ya damesu. Ko me ye ribarsu idan sun tunkuɗa wanda ba shi da ra'ayin aikata abu? Ko me za su ji a kan hakan?

"Ya ilahy.." Daddy ya faɗa. Neman waje Abba ma ya yi ya zauna. A hankali yace

"Lafiya kuwa?" Se a lokacin Daddy ya ɗago idanunsa ya kalli Abba. Ya gyara zamansa sannan ya soma faɗin

"Abokai ke neman ɓata masa suna. Se dai ban san dalilin da ya sanya suke so ya aikatawa ɗiyarka abin da suke so ya yi ba. Alfarma nake son nema a wajenka.. Don Allah ina so kafin mu bar cikin asibitin nan ka ba ni erka na aurawa yaron nan nawa.." Da sauri Abba ya kalli Alhaji Matawalle yana ji kamar ya yi wani saɓo ne. Cikin mamaki yace

"Aure kuma?".

"Ƙwarai kuwa aure. Tunda muka shigo cikin asibitin nan idan ka lura za ka ga idanun mutane a kanmu yake. Zan yi amfani da wannan damar ne wajen maidawa da munafukai fatan tsiyar da suke mana. Ko da an ɗaura auren ba za a fitar a yau ɗin ba. Se idan wani abun ne ya taso sannan za mu fito mu sanarwa da duniya dama can mata da miji ne. Idan dai har ka sanni ka san yanda nake da maƙiya a cikin garin nan waɗanda ban san dalilinsu na ƙina ba. Su nake tsoro, ɓacin sunan yarinyarka da yarona har ma da namu gaba ɗaya nake tsoro. Dan haka ka yadda a ɗaura auren nan a yau ba se gobe ba.." Har Daddy ya gama wannan bayanin Abba be ce komai ba, dan gaba ɗaya kansa ya kulle. Jin da Daddy ya yi Abba ya yi shiru ne ya sanya shi sake faɗin

"Na san ɗana yana da rashin ji. Se dai na isa da shi.. na kuma yadda ko da ba ɗana ba ne zan iya bawa 'yata aurensa ba wai kuma dan ka yadda ba. A'ah na shaidi ɗana.. Amma na faɗa maka aibunsa, kuma ina fatan idan ya yi aure matar ta chanja min shi. Tun kuma da na ganka na ji hankalina ya kwanta da kai.. Ina kuma da tabbacin kwatankwacin yanda kake haka ɗiyarka ma za ta kasance.." ya ɗan dakata anan sannan ya sake faɗin

"Ka yi duba i zuwa wannan abin alkhairin da muke ƙoƙarin aikatawa. Na farko za mu watsawa maƙiya ƙasa a ido. Na biyu muna ƙoƙarin haɗa aure ne sunnah babba. Sannan na uku daga mu har 'ya'yanmu za mu tsira daga zargin nutane.." Se a lokacin Abba ya sauke ajiyar zuciya sannan yace bayan ya ɗan runtse idanunsa

"Allah ya tabbatar da alkhairi. Idan babu alkhairi ya kawo sanadiyyar wargajewar al'amarin kafin lokacin da za a ɗaura auren.."

"Ameen.." Daddy ya faɗa cikin jin daɗi.

"Se dai wani hanzari ba gudu ba. Ina so a ba ni aron awa ɗaya na je na dawo.."

"Awa ɗaya?" Daddy ya tambaya. Kafin kuma Abban ya amsa yace

"Shi kenan.. Allah ya dawo da kai lafiya.."

"Ameen Ameen.." Abba ya faɗa yana miƙewa ya fice daga ɗakin. Daddy ya ɗan maida dubansa kan Bad cike da tausayawa.




... "Toh na san za ka yi mamakin zuwana bayan na zo ɗazu. Se dai wata muhimmiyar magana ce ta saka ni dawowa, amma ban san yanda za ka ɗauketa ba." Murmushi Abeey ya yi kafin yace

"Babu damuwa, kar ka ji komai ka sanar da ni. Na riga na fahimci maganar na da muhimmanci, dan haka kawai ka sanar da ni." Se da Abba ya sauke ajiyar zuciya sannan yace

"Mun riga mun san cewa iyayen ɗa namiji su ke zuwa neman aure wajen iyayen 'ya mace. Se dai a wannan karon abin ya chanja, duk da mun san hakan ba laifi bane. Ni da kai na na zo neman iri, neman alfarma, neman haɗa iri da kai Malam. Ina neman alfarmar 'yata ta auri ɗanka Affan.."

"Ikon Allah.." Abeey ya faɗa yana jinjina kai. Se kuma ya yi murmushi sannan ya soma faɗin

"In dai har mahaifin yarinya ze nemawa 'yarsa auran wani ɗa, toh lallai tabbas wannan ɗa ya cika ɗa, tunda har uba da kansa ya ga dacewar haɗa ɗiyarsa da shi. Dan haka ina me sake godewa Allah da wannan ni'imar da ya min, wannan ma kaɗai ya isa ya nuna min hankalin Affan ko kuma wasu abubuwan nasa ne suka birgeka har ka ji kana sha'awar haɗa alaƙa da shi. Saboda haka ka kwantar da hankalinka, In Sha Allah wannan ɗin duk ba me wuya bane. Ya ya sunan yarinyar taka?" Cikin matuƙar jin daɗi Abba yace

"Afaaf.. Ɗalibar shi Malam Affan ce.."

"Ikon Allah. Masha Allah, Masha Allah.. gaskiya na ji daɗin wannan al'amari.. Hakan kuma yana nuni da komai ze zo mana cikin sauƙi. Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa.."

"Ameen Ameen. Na gode sosai Malam, Allah ya saka da alkhairi.. Se dai kuma na zo da wata magana ne Malam.."

"Toh ina jinka.." Gyara zama Abba ya yi yana tunanin ta inda ze fara wannan maganar. Se dai kawai ya daure ya soma faɗin

"Wato Malam ina me roƙo da neman alfarmar ɗaura auran a yau ɗin nan idan babu damuwa. Da yake ita yarinyar tana da er uwar tagwaitaka, se auranta ya tashi itama a yau ɗin saboda wani dalili. Hakan ne ya sanya ni tunanin na nemawa er uwarta alfarmar auran Malam Affan saboda ba tun yau ba hankalin yaron ke burge ni Malam. Dan haka nace bari na zo da ƙoƙon barata ko za ka amince ka yadda yau ɗin a haɗa auransu gaba ɗaya.." Shiru Abeey ya yi na tsawon sakanni yana nazarin maganar da Abban ya faɗa. Se can ya sauke Numfashi kafin yace

"A yau yau ɗin za a ɗaura auran ita er uwarta ta?"

"Ehh Malam. Nan da anjima kaɗan.."

"Shi kenan.. Amma bari na fara sanarwa da shi yaron.."

"Toh.." Abba ya faɗa a sanyaye dan yana tunanin idan har Gwani ya ji wadda Abeeyn ze aura masa ba lallai ne ya amince ba. Dan babu wanda ze so aurarwa 'ya'yansa uwa wadda ba ta gari ba. Se dai ya yi hakan ne da zuciya me kyau, yana fatan idan har Gwani ya auri Lulu ya chanjata da ikon Allah. Ya kuma yadda ze aurawa ɗan gidan Matawalle Didi ne saboda itama ta chanja shi, duk da be san yana shan wani abu ba, kamar yadda Daddy ma da kansa be san yana sha ba. Se dai ya fahimci wasu daga cikin halayen nasa. Ya kuma yadda da Didin ɗari bisa ɗari, ya san da yaddar Allah za ta chanja yaron shi ma.

"Ka da fa ka damu. Affan ba ze taɓa cewa a'ah ba. Kawai dai dan na fita haƙƙinsa ne, da kuma na mahaifiyarsa.." Abeey ya faɗa yana kallan Abba da jikinsa ya yi sanyi.

"Toh godiya nake.." Kai tsaye Abeey shigewa ya yi zuwa cikin gidan. Ummeey da ke zaune a ɗaki ya kalla bayan ta amsa sallamar da ya yi.

"A'ah Malam sannu da dawowa.."

"Yawwah.." Abeey ya faɗa yana neman waje ya zauna. Miƙewa Ummeey ta yi da nufin kawo masa ruwa, ya yi saurin katseta da faɗin

"Dawo ki zauna. Magana zamu yi.."

"Toh.." ta faɗa tana komawa ta zauna. Wayarsa Abeey ya ɗakko daga aljihu, ya kamo number Gwani ya kira. Babu jimawa kuwa ya ɗaga. Da ɗan murmushin da idan ka ga ya yi za ka iya tunanin na yaƙe ne, se dai ba na yaƙen bane, haka yake a halittarsa, dan shi ɗin ba shi da wata fara'a a halitta. Se dai wannan murmushin ba ƙaramin kyau yake masa ba. Yace

"Abeeyn Affan.." ya faɗa kamar yanda ya saba faɗa wani lokacin. Murmushi Abeey ya yi kafin yace

"Na'am Affan. Ka na ina ne?"

"Ina wani masallacin ne Abeey. Musabaƙa ake yi, yanzu ma haka an samu er matsala ne, kafin mu koma na ga kiranka.." ya faɗa.

"Toh madallah. Kana dai ji na koh?"

"Ehh Abeey.."

"Na samar maka mata" Abeey ya faɗa. Se ya ɗan yi murmushi, dan ya ɗauka ko zalayar Abeeyn ce da ya saba lokaci zuwa lokaci.

"Tohm Abeey.."

"A wannan karon da gaske nake Affan. Na sama maka mata.."

"Toh na gode. Allah ya ƙara girma.." Gwani ya faɗa a nutse.

"Ameen Ameen. Idan kuma har ka amince toh ina so ne na ɗaura muku aure a yau ɗin nan ba se gobe ba.." Ɗan tsayawa ya yi kamar be ji abin da Abeeyn ya faɗa ba. Dan se ya ji kamar wani wasa. Jin shiru ne ya sanya Abeey faɗin

"Ka na tare da ni Affan?"

"Ehh Abeey.."

"Toh ka amince? Ko kuwa akwai damuwa? Ba a ina nufin damuwar gida da sauran kayayyaki ba a'ah ina magana ne a kan zaɓin da na maka. In dai har ya maka toh kar ka damu.."

"Toh Abeey. Allah ya sa albarka.." Ya faɗa da nutsuwar nan tasa.

"Allah ya yi albarka.. Se ka dawo.." Abeey ya faɗa. Tunda ya fara maganar Ummeey ke kallansa. Ya yi murmushi yana kallanta sannan yace

"Ina fatan kin ji abin da nace koh?"

"Wai kuma Malam kana nufin abin da ka faɗa ɗin?" Se da ya jinjina kai sannan yace

"Ƙwarai kuwa.. yanzu haka ma zan fita na samu uban yarinyar za mu je a ɗaura auren. Kar ki damu kin ji?"

"Ai dole ne na damu Malam.." Ummeey ta faɗa tana girgiza kai.

"Toh ai yanzu so nake ma na ji kema kin ce kin amince.."

"Anya kuwa?" Ummeey ta faɗa.

"Sosai ma kuwa.. Babu damuwa In Sha Allah alkhairi ne kin ji?"

"Toh Allah ya sa.." Ummeey ta faɗa bayan ta sauke ajiyar zuciya. Se a lokacin sannan ya fita daga ɗakin zuwa inda ya bar Abba. Babu ɓata lokaci suka ɗauki hanya zuwa asibitin. Fita suka yi daga asibitin zuwa wani masallaci dake nesa da asibitin bayan sun bar masu kula da marasa lafiyar. Cikin ƙanƙanin lokaci aka tara mutane. Daddy ya bayar da sadakin Didi, yayin da Abeey ma be yi ƙasa a gwuiwa ba wajen fito da kuɗi daidai shi, kuɗaɗen da be daɗe da samun su ba, ya bayar dasu a matsayin sadakin Lulu. Babu ɓata lokaci aka shiga shirye shiryen ɗaurin aure. Cikin lokaci ƙanƙani kuwa aka ɗaura auren AREEF ABUBAKAR MATAWALLE da amayarsa AFRAH MUHAMMAD AJI. Se kuma AFFAN ABUBAKAR AHMAD da amaryarsa AFAAF MUHAMMAD AJI.. (Ƙaƙaƙaraƙaƙa🤭🤐)



... Tunda suka shigo gidan Ammi ke ta duba ɗaki ba ta ji motsin Didi ba.

"Wai ina yarinyar nan ta shiga ne?" Ta faɗa sanda ta buɗe ƙofar toilet. Ganin nan ma babu ita ne ya sanyata sake fitowa parlour inda Lulu ke zaune. Tana shirin yin magana Abba ya yi sallama cikin ɗakin shi da Didi. Ajiyar zuciya Ammi ta sauke tana faɗin

"Yallaɓai na shiga tashin hankali fa. Na kira wayarka ba ka ɗauka ba, na yi duban duniya ban ga yarinyar nan ba. Ashe fita kuka yi ." Ta ƙare tana kallan Didi. A hankali Didi ta nemi kusa da inda Ammi ta tashi ta zauna a sanyaye. Abba ma neman waje ya yi ya zauna daidai lokacin da Ammi ta sake faɗin

"Lafiya kuwa?"

"Nemi waje ki zauna.." Abba ya faɗa yana nuna mata kusa da shi. Babu musu ta zauna, se dai haka kawai ta ji jikinta ya ɗan yi sanyi. Kallan Lulu da ke kwance kan kujera ya yi fuskarsa a haɗe yace

"Afaaf tashi ki zauna.." A hankali ta ɗan fara ƙoƙarin tashi irin da gasken bata da lafiya. Abba be ce mata komai ba har ta sauko ta nemi kusa da inda Didi ta zauna a ƙasa tun zaman su Abba a kan kujera. Bayan shuɗewar wasu sakanni ba tare da kowa yace komai ba Abba ya soma faɗin

"Ashe suspension aka baki?" Ya yi maganar ba tare da ya ambaci suna ba. Da sauri Lulu ta ɗaga kai ta kalli Abba ƙirjinta na bugawa. Ganin shi ma itan yake kalla ya sanyata yin ƙasa da kai sannan ta soma haɗo maganganu tana inda inda.

"Suspension kuma?" Ammi ta faɗa cike da mamaki. Jinjina kai Abba ya yi kafin yace

"Ƙwarai kuwa,. Ta sake fusata malamin da rashin ɗa'a irin nata, shi ya sa ya bata hutun kwanaki, se dai be sani ba a shashanci irin na yarinyar nan daɗin hakan za ta ji.. Se dai wannan ɗin ba abin damuwa bane, dan kuwa ba ma bada kwanaki da aka yi ba, dama ko ba a yi hakan ba, daga yau kowaccensu ta gama zuwa makaranta se da izinin mijinta.." Ammi, Lulu, Didi gaba ɗaya kallan Abba suka yi jin wani saɓo da ya yi. Cike da mamakin furucinsa duka suke kallansa, se suke ganin kamar Abban be san abin da ya faɗa ba. Ganin kallan da suke binsa da shi ne ya sanya shi kallan Ammi da mamakinta yafi na kowa bayyana yace

"Ƙwarai kuwa a yau ɗin nan na aurar da Afaaf da kuma Afrah.." Cikin matuƙar tashin hankali Ammi tace ƙirjinta na bugawa

"Aure kuma? Aure na gaske kake nufi ko kuwa wanne Abbansu?" Ta tambaya fuskarta ɗauke da zallar mamaki da tashin hankali. Ajiyar zuciya Abba ya sauke dan ya ga alamar Ammin ta gama rikicewa, yace

"Aure dai kamar yadda muka yi ni dake.." Numfashi Ammi ta sauke da ƙarfi tana ɗauke kai a kan laɓɓanta ta furta

"Ya ilahy!" Se kuma ta kalli Abban a nutse tace

"Wa ka aurawa su Abba?" Ammi ta faɗa bugun zuciyarta na ƙaruwa. Kallan Twins Abba ya yi waɗanda kowaccensu su take kalla, jin abin suke kamar a mafarki, bama su yadda da gaske Abban yake ba. Kawai sun ɗauki hakan a matsayin wasa ne yau Abban yake musu. Wasan da idan dai har ba a yi saurin ƙarƙare shi ba zuciyoyi biyu na dab da bugawa.

"Na aurar dasu ne ga waɗanda suka dace, don kuwa ina fatan ko kuma nace idan Allah ya yadda ta silar auren nan wasu ɓangaren za su taimaki wasu ɓangaren, har su yi amfani da damar da Allah ya ba su wajen gyara abokanan zamansu, wanda kai tsaye zan iya kiran hakan da jihadi. Ki bari zan miki bayanin komai, kada ki tayar da hankalinki, dan kin riga da kin san uba ba ze taɓa zaɓarwa 'ya'yansa abin da ze cutar dasu ba. Dan haka ki kwantar da hankalinki.." Ita gaba ɗaya ma wasu maganganun na Abban ba fahimtar su take ba, dan haka ta ɗan girgiza kanta sannan tace

"Zan kwantar da hankalina Abbansu, amma bayan ka faɗa min wanda ka aura musu. Sannan kuma ka tabbatar min ni da 'ya'yana da gaske abin da kake faɗa gaskiya ne?"

"Ki dena tantama da wannan maganar, ba wasa bace. Da gaske na aurar da yaran nan a yau ɗin nan.." ya ƙare maganar yana kallan Twins da ke zaune kamar wasu shashashu ko waɗanda ba sa hayyacinsu. Gyara zama Abba ya yi sannan ya kalli Lulu ya ɗan yi murmushi kafin ya soma faɗin

"Shi dai wannan malamin naki da kika ɗauke shi ba a matsayin malaminki ba. Ki ke masa kallan wanda kike taimakawa kina zuwa makaranta bayan shi yake koyar dake. Ki ke masa kallan wulaƙantacce dan yana Malamin Addini. Ki ka yi watsi da tarbiyyar da muka baki ki ke rashin daraja gare shi. A yau ɗin kuma cikin ikon Allah na ba shi auranki... Ma'ana dai na aura masa ke, yanzu haka kin koma ƙarƙashinsa ne, dan kuwa ya zama mijinki.." Ɗan runtse idanunta Lulu ta yi sanda gaba ɗaya kanta ya buga. A hankali kuma ta ji wani jiri jiri na kwasarta duk da a zaune take, se ta ɗan yi gefe sannan ta kai hannunta ta riƙo kanta, daidai lokacin da take sake tuno maganganun da Abban ya faɗa, dan sake tabbatar da abin da kunnuwanta suka ji.

"Malam Affan!" Abba ya bawa Ammi da ta masa magana amsa. Wata ƙara Lulu ta saki sanda ta gama fahimtar inda zancen Abban ya dosa, gaba ɗaya idanunta suka makance a lokacin, kunnuwanta suka yi wani dumm, gangar jikinta ta kasa riƙeta, ƙirjinta ya cigaba da bugawa da gudun da ya mugun wuce na ƙa'ida. Saboda yanda ta ji kanta ya ɗaure tamau kamar wadda aka ɗorawa wani ƙaton abu akai, ya sanyata riƙo kan lokaci ɗaya tana faɗin

"Na shiga uku..." Tun kafin ta ida faɗar hakan ta yi wani baya kamar wadda aka ja, se kawai ta zube a wajen sumammiya. Abba, Ammi har ma da Didi duka kanta suka yi. Ammi na kiran sunanta cikin tsananin tashin hankali. Da ƙyar Didi ta iya ƙarasawa inda Lulun take, se dai ta kasa aikata komai, dan gaba ɗaya jikinta wani irin rawa yake kamar mazari. Haka zalika idanunta sun cika fall da ƙwalla, ita kaɗai kuma ta san yanda take jinta a cikin tashin hankali, har taso ta ɗan dena fahimtar wasu abubuwan saboda yanda ƙwaƙwalwarta ta toshe a lokacin. Tunda Abba ya ambaci sunan Gwani Affan a matsayin wanda ya aurawa Lulu, jikinta ya ɗauki zafi, ba ta taɓa zata ba, ba ta taɓa tsammani ba. Ga kuma er uwa rabin jiki a kwance kamar matacciya. Wannan tashin hankalin shi ne ya sanya ƙwalla zubowa daga cikin idanunta, se kuma wanda yafi kowanne, wato jiran jin sunan wanda Abba ze faɗa a matsayin wanda ya aura mata itama...



ALHAMDULILLAH! Anan na kawo ƙarshen A JINI TAKE Chapter one. Me son cigaba da karanta littafin A JINI TAKE Chapter two, ze tura ₦300 ne ta 8124818273, Zahra'u Yusuf Ishaq, Opay. Shedar biya ta 08124818273.

Don neman ƙarin bayani za a iya tuntuɓata ta 08124818273.

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge

2 Comments On A JINI TAKE (IZZATA) CHAPTER 1
avatar
abubakar-sunusi

1 year ago

Reply

avatar
abubakar-sunusi

1 year ago

Reply

Please Login or Register in order to submit comment