Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗin babu me tilasta mata yin abin da bata ga dama ba, hatta da karatun ma idan bata yi niyyar yi ba ta san Mamin ba zata takura ta da se tayi ba, shi yasa take matuƙar ƙaunar rayuwar gidan Mamin. Kallan Didi tayi da har lokacin kanta ke ɗore akan cinyar Ammi tace

"Didi wankin kan."

"Ba za a yi ba" Didi ta faɗa tana galla mata harara. Rau rau tayi da idanunta tana kallan Didin, ta san ko me zata yi Didin ba zata bi ta su tafi tare ba, dan ita ɗin miskila ce irin ta sosai ɗin nan, ba kasafai ta fiya son shiga cikin mutane ba idan ba dole ba, shi yasa kullum tana gida kusa da Amminta. Se dai kuma ta wani ɓangaren zata ɗan ji daɗi, dan kuwa idan har Didin ta bi ta suka tafi gidan Aunty Sadiyan tare, zata zame mata cikas, ta san ita ɗin me sakata tayi ne. Ɗan sauke ajiyar zuciya Ammi tayi ba dan ta so zuwan Lulu gidan Aunty Sadiya ba, se dai komai lalacewar Aunty Sadiyan ita ɗin ƙanwar Abbansu ce, saboda haka ba zata iya kallansa tace masa Lulun ba zata je gidanta ba saboda yanayin tarbiyyarta sam be dace ba. Se dai koma me ake ciki ba zata bari Lulun ta wuce sati ɗaya bata dawo gida ba, dan haka kawai take ji hankalinta be kwanta ba tun da akayi maganar zuwan Lulu gidan nata..



Me son karanta A JINI TAKE (IZZATA) har ƙarshe ze tura ₦300 ta 8124818273 Zahra'u Yusuf Ishaq Opay. Shedar biya ta 08124818273.



https://chat.whatsapp.com/LH7GN3pMRE26T5G5xcTmmw


*♡☆A JINI TAKE☆♡*
*(IZZATA)*


By
_*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_


*CHAPTER ONE*

Page_04


___Ba su daɗe a parlourn ba Didi ta miƙe tana kallan Ammi tace

"Ammi bari na je na kwanta, bacci nake ji." Kallanta Ammin tayi na tsawon sakanni kafin tace

"Tohm" Daga haka ba ta sake cewa komai ba ta wuce ɗakin nasu. Da narkakkiyar fuskarta Lulu ta bita da kallo sannan ta dawo da dubanta kan Ammi.

"Ammi haushina fa take ji." Ta faɗa tana tura baki. Girgiza kai Ammi tayi kana tace

"Ai dai kin san halinta dama." Tasowa Lulu tayi daga kan kujerar da take, ta dawo wadda Ammin ke kai. Ta kamo hannunta har lokacin fuskarta a narke tace

"Ammi don Allah ki rakani in rarrasheta." Ta faɗa da iya gaskiyarta, dan kuwa tafi kowa sanin halin Didin musamman idan tazo tafiya wani wajen, ta dinga nunƙufurci kenan, kuma ko me za a mata ba za ta bi Lulun ba. Duk da itama Ammin ba son zuwan Lulun take gidan Mamin ba, amma za ta so su je tare da Didi, domin kuwa duk da kasancewarta mahaifiyarsu ita me iya buɗe baki ne ta faɗi cewar Didin tafi Lulu hankali.

"Ni ba inda zan je." Ammi ta faɗa.

"Don Allah, Don Allah, Don Allah." Lulu ta faɗa kamar za tayi kuka. Murmushi Ammi tayi tana miƙewa ta saka hannunta kan kunnen Lulu ta ja lokaci ɗaya tana faɗin

"Ke dai koh!" Se ta saka hannunta ta riƙe kunnen tana ɗan sakin ƙara a hankali gami da murmushi. A kwance take akan gadon na su idanunta a rufe kamar me bacci, se dai ba baccin take ba, amma dai jira take ya ɗauketa. A nutse suka ƙarasa cikin ɗakin. Ammi ta nemi waje ta zauna yayin da Lulu ta zauna a kan gadon, kusa da Didi da ke kwance. Motsin da ta ji a kusa da ita ne ya sanyata saurin buɗe ido, se ta ga Lulu a zaune, ta galla mata harara hadda murguɗa baki. Langaɓar da kai tayi gefe tana ƙiƙƙifta ido, duk Ammi na lura da su hakan ne ya sanyata murmushi tana girgiza kai.

"Didi tashi.." Ammi ta faɗa, itama langaɓar da kan tayi kafin tace

"Ammi bacci fa zan yi."

"Tashi dai." Ammi ta sake faɗa tana riƙota kamar zata ɗagata. Se a lokacin ta miƙe ɗin da taimakon Ammi.

"Ki shirya ku tafi tare zuwa gidan Mamin taku." Ammi ta faɗa bayan ta gama gyara zamanta akan gadon. Girgiza kai tayi da sauri sannan tace

"A'ah ni kam Ammi."

"Pls my Didi" Lulu da ke gefe ta faɗa a narke.

"Na ƙi ɗin" ta faɗa tana jefa mata harara. Dama Ammin ta san ba zuwa za ta yi ba, idan ma aka takura se dai ta dami kanta dan haka se tace

"Toh fushin na meye?" Se da ta ɗan yi shiru sannan tace

"Toh Ammi ba komai fa." Ta ƙare tana cuno baki.

"Kin tabbatar?" Ammi ta faɗa. Kafin ta kai ga cewa komai Lulu tace

"Allah kuwa Ammi ba wani nan, fushi take da ni fa."

"Ni ba wani fushi da nake fa."

"Toh in ga alamar hakan." Ammi ta faɗa tana murmushi. Ba tare da Lulu ta ankara ba se ji tayi Didin ta rungumeta. Cikin farin ciki itama ta rungumeta tana murmushi. Ammi ma da ke gefensu murmushin tayi a ranta tana sake addu'ar Allah ya ƙara haɗe mata kan 'ya'yanta.


... Washegari se bayan sun dawo daga makaranta sannan Abba ya ɗauki Lulu da ta gama shiryawa tsaff da kayanta zuwa gidan Mamin. Tun a ƙaton compound ɗin gidan suka haɗu da Mami sanda ya ida parking ɗin motarsa. Mamin na sanye cikin wata doguwar riga ɗinkin hijab bubu da mayafi fuskarta ɗauke da glass, hannunta kuma ɗauke da wata ƙaramar jaka. Cikin farin cikin ganin nasu tace

"Oyoyo! Sannunku da zuwa." Ta faɗa da murmushi kan fuskarta. Fitowar da Lulu tayi ne sanyata buɗe mata hannu tana faɗin

"Welcome my dear." Babu ɓata lokacin Lulu ta ƙarasa jikin Mamin suka rungume junansu kowaccensu ɗauke da murmushi a kan fuskarta.

"Toh ko dai na koma ne?" Abba ya faɗa yana murmushi. Itama murmushin Mami tayi tana sakin Lulu kafin tace

"Haba dai Yaya. Barkanka da zuwa, ka zo mu ƙarasa ciki mana." Girgiza kai Abba yayi yana ƙarasowa inda suke lokaci ɗaya yace

"A'ah akwai inda zan je, naga kuma kema fita za ki yi. Saboda haka mu gaisa anan."

"Kai Yaya haka za a yi?"

"Hakan kuwa za a yi" Abba ya faɗa yana murmushi. Gaisawar kuwa suka shiga yi, saboda Abban sauri yake ya sanya babu daɗewa ya wuce. Ita kuma Ammin ta saka hannu ta ɗauki jakar Lulu sannan suka soma takawa zuwa cikin gidan.

"Mami da kin bari na ɗauka." Lulu ta faɗa. Hararar wasa Mamin ta jefa mata kafin tace

"Ke ban son iyayi." Dariya suka yi kusan a tare daidai lokacin da suka shiga cikin parlourn. Har ɗakin Jadwa Mamin ta kai jakar Lulu. Jadwan na kwance kan gadon tana danna waya, kamar ko da yaushe kunnenta ɗauke da ear piece. Sam bata ji shigowarsu ba, se da Mami ta saka hannu ta karɓe wayar sannan ta juyo da sauri dan ta san dai sun riga sun yi sallama da Mamin kafin ta fita. Tana juyowa se taga Lulu a tsaye tana murmushi, da sauri ta diro daga kan gadon lokaci ɗaya tana faɗin

"Oyoyo.." ta faɗa tana rungumeta. Murmushi Mami tayi tace tana kallansu su duka bayan sun saki junansu, se kuma ta maida dubanta kan Lulu tace

"Lulu za ki je makaranta ne yau ɗin?" Girgiza kai tayi tana tura baki, tace a hankali

"A'ah Mami, daga zuwana kuma?" Dafa kafaɗarta Mami tayi tana faɗin

"Kwantar da hankalinki my dear, ba wanda ze miki dole. Nemi waje ki kwanta ki huta, gobe se ki je." Cikin farin ciki tace

"Yawwah Mamina." Itama murmushin tayi kana tace

"Jadwa ki kula da ita kafin na dawo. Duk abin da take so a sama mata shi, ina dawowa kuma zan ɗora daga inda kika tsaya." Sunkuya wa Jadwa tayi irin alamar girmamawan nan sannan tace

"An gama Mami." Tayi maganar tana dariya. Dukansu dariyar suka yi. Mami ta sake yi musu sallama ta fice daga gidan.


.. A ranar da Didi taje makaranta tana ta jiran zuwan Lulu amma shiru bata zo ba, bata damu ba tunda ta ga yau ta je gidan Mamin, dan kuwa ze yi wuya idan ba Mamin ce za tace yau ɗin su yi hira ba tunda dai yau ta zo. Aikuwa ta sha tambaya a wajen Abida, har se da ta gaji. Dan haka kawai ta ji yarinyar ba ta birgeta ba, rawar kanta ya fiya yawa, se wani rawar kai take akan Lulun da sau 1 ta taɓa ganinta. Idan ma da ta san halin Lulun da bata din ga zaƙewa haka ba, dan ba abu ne me wahala a wajen Lulun ta dizgata ba, dan wani lokacin halinta se ita.



... "Kin gama shiryawa?" Mami ta faɗa tana kallan Lulu da ta fito cikin Uniform ɗin da kamar kodayaushe ana ƙara mata kyau ne idan ta sakasu.

"Ehh Mami."

"Toh mu je!" Mami ta faɗa tana yin gaba yayin da Lulu ta bi bayanta. Compound ɗin gidan suka nufa kai tsaye suka hau motar da zata kaisu inda zasu je. Har bakin makarantar driver ya kaita ta sauka sannan ya ja Mami da ze kai unguwa. Kai tsaye ita kuma Lulu ajinsu ta wuce cike da zumuɗin ganin twinnynta. Aikuwa tana shiga ta sameta zaune kamar kodayaushe a inda suka saba zama. Da sauri ta rungumeta tana faɗin

"Didina" Cike da farin ciki itama Didin tace

"Luluna" se ta koma ta zauna tana ɗage niƙab ɗin fuskar Didin lokaci ɗaya tana faɗin

"Bari na ga ko kin rame saboda bana nan." Hannunta ta bige kafin tace

"See u. Kwana ɗayan koh?" Kafin Lulu tace komai se ga sallamar wani Malami nan ya shigo cikin ajin, hakan ne ya sanyasu yin shiru bayan amsa sallamarsa.

"Masoyiya fa?" Lulu ta tambaya ƙasa_ƙasa.

"Ba ta zo ba, itama mutuniyarki bata zo ba" Didin ta bata amsa itama ƙasa_ƙasa. Cikin rashin fahimta tace

"Wace mutuniyata?" A hankali Didi tace

"Ki yi shiru zan faɗa miki" Daga haka babu wadda ta sake magana. Se dab da za a tashi sannan aka aiko cewar duk wanda be bayar da hadda ba jiya ya je ya bada, wanda ma yayi fashi shi ma ya je. Kallan juna Lulu da Didi suka yi, cikin sarewa ita dai Lulu tayi shiru tana jiran ganin wasu sun miƙe, se dai shiru bata ga kowa ya miƙe ba. A'ah abin dai kamar haɗa baki se ya kasance ita kaɗai ce wadda bata bayar da haddar ba, haushi kamar ya kasheta, takaici kamar ta yi kuka. Se kawai ta gyara zama a inda take zaune fuskarta a haɗe

"Lulu ki tashi ki je, meye amfanin abin da kike yi? Haddar ce baki iya ba ko me?" Didi ta faɗa tana kallanta. Se da ta sauke numfashi sannan tace

"A'ah fa Didi kawai dai.."

"Kawai dai me? Ki tashi ki je kawai." Miƙewa tayi ba tare da ta kalli kowa ba ta fice daga ajin kyakkyawar fuskar nan ta ta a haɗe. A filin makarantar ta hange shi zaune da wani a gefensa, da alama magana suke yi. Gefen fuskarsa kaɗai ake iya hanga wanda hakan ya matuƙar bayyana kyawunsa musamman da fuskarsa take a juye. Sosai wata zuciyar take zugata akan kada ta je, kawai ta koma, se kuma wata ta zugata akan kawai ta je, ai ba wani abun taje nema wajensa ba. A nutse ta cigaba da takawa zuwa inda yake ɗin, se da taje inda take da tabbacin ze ganta sannan ta tsaya kanta na kallan gefe tayi shiru, dan ta san ya ganta, kuma shi ne ya nemi ta zo ba ita ce ta zo wajensa neman wani abun ba. A nutse Gwani ya cigaba da tattaunawa da mutumin nan, sam be nuna ya san akwai wanzuwar wata halittar a wajen ba. Hakan ba ƙaramin baƙantawa Lulu yayi ba, ga shi yana wani magana a hankali daga shi har wanda suke maganar, se dai shi ta shi ko sautinta ba a ji saɓanin ɗayan da ake iya jiyo sautin tasa muryar. A hankali ta ɗan saki tsaki tana runtse idanunta, wannan faɗin ran nasa da nuna shi wani ne bayan shi ɗin ba kowa bane yana ɗaya daga cikin abin da ke sanyawa bata yinsa ko kaɗan. Uwa uba kuma yadda kowa ke son shi, kowa ke nan nan da shi, se take ɗauka duk suna yi saboda kyawunsa ne da ke yaudararsu, shi yasa ita sam be taɓa birgeta ba se ma haushinsa da take ji daga shi har mutanen da ke son shi, dan gani take yadda suke son na shi ne yake sanyawa baya ganin girman kowa, baya tsayawa inda Allah ya ajiye shi. Tafi ƙarfin minti 5 tsaye a wajen, zuwa lokacin ta gama fusata, duk da Malaminta ne amma se take ganin kamar idan ta buɗe baki ta masa magana, ko da ba a tausashe ba ne ba ze ɗauka itama ta yaba da shi ɗin ne, kamar yadda kusan kowa yake yi. Ji take kamar ta tafi ba tare da tace komai ba, yayin da wata zuciyar ke faɗa mata ta masa magana ba ze ɗauki komai ba, haka dai ta daure, ta cije ta haɗa rai ta juya ta kalli inda suke tace murya a cunkushe

"Malam, ga ni!" Se a lokacin ya ɗaga kyawawan idanunsa ya kalli inda take tsaye, cikin er basarwa yace

"Assalamu alaik." Daga haka ya maida kansa wajen mutumin suka cigaba da magana. Runtse idanunta tayi tana jin wani irin takaici da kunya da haushi duk sun taru sun rufeta. Me yake nufi da ita? Kafira ce ita ko me yake nufi? Ƙirjinta har wani bugawa yake saboda tsabar takaici da haushi. Yanzu duk da irin wannan dizgin da rashin kirkin da yake a haka ɗalibai da yawa ke son shi, a haka suke cigaba da mu'amalantarsa kamar wani mutumin arzik'i. Yadda zuciyarta ke tafasa ta san ko ta buɗe baki ma ba abin da zata iya faɗa, dan haka se da ta ƙara wajen minti 2 tsaye a wajen. Se da ta ji ta ɗan soma dawowa daidai sannan ta sake juyawa cikin rashin mafita tace

"Ga ni!" Sarai ya jita, ba ya kuma san yayi shiru dan ya san hakan be kamata ba, se dai kuma yanda take magana kamar da sa'anta ko ma ƙaninta ya ga lallai ya kamata ya koya mata hankali, dama ya daɗe da gane take_takenta tun ba yanzu ba. Toh a yanzu kuma da ya zama malamin ajinsu shi ba ɗaukar kowanne hauka ze yi ba, dan haka ya zama dole ya taka mata birki. A nutse ya sake ɗaga kansa a karo na biyu ya dubi inda take ba tare da ya kalli fuskarta ba yace cikin basarwa

"Ba a koya miki sallama ba? Toh ki je ki koya se ki dawo!" Daga haka ya miƙe a nutse hannunsa ɗauke da wani littafi ya bi bayan wanda suke magana dan ya riga shi tashi. Bin sa tayi da kallo tana jin yadda zuciyarta ke tafasa tana mata zafi, wani irin baƙin ciki da ɓacin rai duka suka haɗu suka tarar mata. Kawai se ta ji ƙwalla a cikin idanunta, gaba ɗaya ta gama muzanta, ya gama yarfata, ya gama wulaƙantata. Se ta buɗe ido ta fara duba gefe da gefenta ko da akwai wani a kusa da ita. Fatan ta guda ɗaya Allah yasa babu wanda ya ga wannan cin mutuncin da yayi mata, ga shi kuma wani ƙarin baƙin cikin ya tafi ya barta a wajen, wato ga mara aikin yi, idan ta gaji da tsayuwar se ta ƙara gaba. Ganin da tayi kowa da abin da yake yi, se kuma waɗanda ke fitowa daga aji saboda an tashi, se dai da alama kowa harkar gabansa yake yi, ya sanyata soma takawa a hankali kamar babu laka a jikinta tana jin yadda gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, haushi da takaicin Gwanin na sake cikata. Gaba ɗaya ta ƙi barin zuciyarta ta huta, se tunanin abin da ya faɗa mata ɗin take cikin wannan muryarta sa me kauri da daɗi. Duk da kalaman da ya faɗa ɗin basu da yawa amma ita a wajenta ji tayi kamar an gama muzanta ta muzancin da ba a taɓa yi mata ba, wai yau ita ɗa namiji ke faɗawa magana. Cigaba da takawa ta cigaba da yi har zuwa sanda ta ƙarasa ajinsu, ko lura da masu fitowa ma ba ta yi ba, se da Didi ta kamo hannunta tace

"Kee!" Se a lokacin ta kalli Didin da idanunta da ƙwalla ta gama taruwa se dai taƙi bata damar zubowa saboda kada wani ma ya gane akwai abin da aka mata, bare ma a tambayeta kuma idan ta faɗa ɗin ita ce zata ji kunya.

"Me ya faru?" Didi ta tambaya tana kafeta da idanunta. Duk da basa ɓoyewa junansu komai amma yau ɗin so take kawai ta kwanta tayi bacci ta manta da abin da ya faru ba tare da kowa ya sani ba, dan haka tayi ƙarfin halin faɗin

"Kaina ke ciwo!" Duk da bata wani yadda ba, amma ta san koma mene idan ta matsota zata faɗa mata ne, hakan ne ne ya sanyata faɗin

"Ki wuce gida, kina zuwa kuma ki sha magani kin ji koh?" Didin ta faɗa cikin kulawa. Jinjina kai Lulu tayi kawai se ta cigaba da bin Didin da ke riƙe da hannunta suka fito. Suka yi sallama cike da kewar junansu sannan Lulu ta shige cikin motar da ta zo ɗaukarta, yayin da Didi ta kama hannun Little suka tafi gida.

Tun da ta shigo Jadwa ke binta da kallo, ganin ba a irin yanayin da ta saba ganinta ba yau ɗin ta ganta a ciki. Hakan ne ya sanya lokacin da ta nemi waje ta zauna kan gadon, se itama ta zauna tana kallanta tace

"Sistor wai me ya faru?" Murmushin yaƙe Lulu tayi kafin tace

"Babu komai fa. Me kika gani?" Yamutsa fuska Jadwa tayi tace

"Kin ga yanzu dai babu Didi a gidan nan, idan zaki faɗa min damuwarki mu haɗu mu yi maganinta toh. Idan kuma ba zaki faɗa min ba se in san inda kika ajjeni." Kallan Jadwan Lulu tayi kamar ba za tace komai ba se kuma tace

"Babu komai fa nace miki" ta faɗa fuskarta a haɗe saboda tuna abin da ya faru ɗazun.

"Akwai ɗin kenan. Just tell me, mu haɗu mu yi finding solution." Jadwa ta faɗa bayan ta tauna chewing gum ɗin bakinta ya bada sautin 'ƙaƙas'. Ji tayi kamar yanzun ne Gwanin ya faɗa mata maganar, ji take kuma kamar yanzun ne ya shayata a tsaye kusan mintina nawa. Kamar za ta fasa ihu tace

"Jadwa ki ƙyaleni don Allah. Malaminmu ne ya ɓata min rai." Cikin rashin fahimta Jadwa tace

"Ban gane ba? Kin je wata makaranta ne hajjaju? Yaushe kika fara zuwa University bani da labari?" Kallan rainin hankali Lulu ta bi Jadwa da shi jin maganar da tayi ɗin irinta rainin hankali, se kawai tayi mata shiru fuskarta a haɗe cikin zuciyarta na cigaba da tafasa.

"Common Babe, Allah kuwa ban gane me kike nufi ba" Jadwan ta faɗa tana riƙo hannun Lulu.

"Idan nace miki Ya Sayyadi zaki gane? Toh shi ne ya gama yarfani da girmana da mutuncina." Kallanta Jadwa ta cigaba da yi tamkar wata sabuwar halitta, se kuma daga baya kawai ta sheƙe da dariya hadda riƙe ciki. Haushi gami da tuƙuƙi suka sake cika Lulu, se ta miƙe a fusace zata bar ɗakin, Jadwa tayi saurin riƙo hannunta. Fuzge hannun tayi kamar zata rufe Jadwan da duka. Ganin hakan ne ya sanya Jadwa miƙewa tana maida dariyarta ta soma faɗin

"Sorry my love. Tun farko ce min zaki yi Malamin Islamiyya. Ni da kika ce min Malami na ɗauka wani shahararren Malamin University ne, shi yasa nake dariya. Kin ga mu je mu zauna." Ta faɗa tana jan hannun Lulun. Yanzu dai se ta bita ɗin suka zauna. Da rarrashi ta haƙura ta bata labarin abin da ya faru ɗin. Se da suka ɗauki wajen minti 1 bayan gama bada labarin sannan Jadwa tace

"Wai kina nufin Malami, Malamin ma Malamin Addini shi ne kika zauna yana ƙoƙarin manna miki hauka?" Jadwa ta faɗa cike da mamaki wanda ya gaza ɓoyuwa har akan fuskarta..



Me son karanta A JINI TAKE (IZZATA) har ƙarshe ze tura ₦300 ta 8124818273 Zahra'u Yusuf Ishaq Opay. Shedar biya ta 08124818273.



*♡☆A JINI TAKE☆♡*
*(IZZATA)*


By
_*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_


*CHAPTER ONE*

Page_05


___Shiru Lulu tayi, dan ita maganar ma da Jadwan ke yi sake tunzurata take yi, tana sanyawa tana tuna abin da ya faru ɗazun, tana kuma sake sakawa tana jin Gwanin yayi mata ƙarshen cin mutunci. Kamar ba za tace komai ba se kuma can tace muryarta a cushe

"Toh da wa nake nufi?" Ɗan lumshe ido Jadwa tayi tana furzar da iska daga bakinta. Tayi shiru na tsawon mintuna kamar me tunani, dan hadda sunkuyar da kai tana jinjina kai. Se can ta ɗago kai ta kalli Lulun, ta sauke ajiyar zuciya kana ta soma faɗin

"Wallahi kin bani mamaki Lulu. Kamar ke big gurl ace kin zauna kina saka damuwar wani ƙaramin alhaki a cikin ranki? Me aka yi akayi Malami? Malamin ma na Addini? Me yake taƙama da shi? Kuɗi? Ɗan gidan uban waye shi? Na san babu yadda za a yi ya kasance ɗan gidan wani hamshaƙi se dai na matsiyata. Ke kuma fa? Kyau, aji, kuɗi duk kin haɗa, toh meye zaki tsaya kina ɗaura damuwar talakawa a kanki?" Se ta ɗan dakata anan, ta sanya hannu ta kamo hannun Lulun sannan ta ɗora da

"Kin ga kiyi amfani da halinki a wajen nan Lulu. Shi ɗin ba kowa bane, saboda haka duk wani abu da kika san ze haɗaku da shi ki ƙaurace masa. Ke hatta haddar ma ki dena bayarwa, kar kiyi tunanin ze takura miki akan se kin bayar, idan dai har kika bi abin da nace miki toh ba ze takura ba, tun da dai ai yin haddar ba dole bane. Dan haka ina so in sake tabbatar miki da in dai kika bi waɗannan hanyoyin toh ze kama kansa ne, ya gane ke ɗin ba sa'arsa bace." Shiru Lulu tayi tana saurarar maganar Jadwan tun da ta soma magana, har ta ƙare. Tabbas duk wata magana da ta faɗa ɗin ta riƙeta hakan ne ya sanyata tsayawa tana warwaresu dalla_dalla dan ta sake fuskantarsu yanda ya kamata. Anya kuwa abin da Jadwan ta faɗa shi ne mafita? Ko kuwa dai tayi ƙoƙari ta bi abin da Jadwan ta faɗa ta gani ko hakan ze yi aiki, dan tabbas itama zata ji daɗi idan kwata_kwata wata harka ta dena shiga tsakaninta da Gwanin.

"Amma Jadwa..!" Ta faɗa a raunane, narkakkun oily eyes ɗinta na wani irin sheƙi kamar waɗanda aka zuba musu zaiba. Numfashi Jadwa ta sauke tace bayan ta girgiza kai

"Uhmm wai Lulu yaushe kika chanja ne haka? Ko dai ba so kike ki kawo ƙarshen izzarsa ba? Ko da ze gwada wa wasu ya kasance banda ke a ciki?" Se ta jinjina kai kawai.

"Toh abin da na faɗa shi za a yi. Shi ne kawai mafita. Ke ko ma dai kin manta abin da ya miki ne?" Ajiyar zuciya Lulu ta sauke tana ɗan lumshe idanunta sannan ta buɗe tace

"Haka za a yi Jadwa!" Shi ne abin da ta faɗa bayan murmushi ya suɓuce akan fuskarta. Se a lokacin ta ji tabbas abin da Jadwan ta faɗa yayi daidai. Za kuma tayi amfani da shawarar Jadwan ta gani ko za a dace.

"Thank you so much sistor." Lulu ta faɗa. Itama murmushin tayi sannan tace

"Ko babu komai na sakaki murmushi bayan da wancan Malamin Addinin ya ɓata miki rai." Dariya Lulu tayi jin da tayi har Jadwan ta laƙabawa Gwanin sunan "Malamin Addini"

"So yanzu dai ki zo mu buga game. Ki manta da wancan useless person ɗin." Babu ɓata lokaci Jadwan ta ɗakko wayarta suka shiga yin game ɗin, Jadwan na sake iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta saka Lulun ta manta da abin da ya faru.



... Tsaki ta saki tana miƙewa tana ajje wayar akan kujera sannan ta miƙe. Kai tsaye ɗakin Jadwa ta wuce inda ta tabbatar suna can. Aikuwa suna can ɗin zaune suna game lokaci ɗaya suna shan yankakken fruits ɗin da ke cikin wani plate.

"Game ɗin ce?" Ta faɗa tana ƙarasowa cikin ɗakin.

"Wallahi kuwa Mami" Lulu ta faɗa tana tashi zaune daga kishingiɗen da take.

"Toh yayi kyau.. Jadwa tashi.." tayi maganar tana neman waje ta zauna. Tashi Jadwa tayi akan gadon. Ita

2 Comments On A JINI TAKE (IZZATA) CHAPTER 1
avatar
abubakar-sunusi

10 months ago

Reply

avatar
abubakar-sunusi

10 months ago

Reply

Please Login or Register in order to submit comment