Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Wai dan ɗazun ya koreta daga aji saboda ba ta da littafi, kuma bayan tana sane taƙi tafiya da littafin." Ajiyar zuciya Ammi ta sauke tana maida dubanta kan Lulu da ta yi saurin ɗauke kai tun bayan da didi ta fara magana.

"Anya kuwa ba wasu ƙawayen ke hure mata kunne ba?" Ammi ta faɗa tana kallan Didi.

"Ammi ba wasu ƙawaye. Fatima ce fa kaɗai ƙawarta ta."

"Toh ita Fatiman me ya hanata zuwa?"

"Ita fa Fatiman har ta taho za mu tafi, da ta ga Lulun ba za ta je ba, shi ne ta fasa zuwa saboda Lulun ta nuna ta ji haushi."

"Shirmen banza kenan.." Ammi ta faɗa ranta a ɓace. Se ta maida dubanta kan Lulu tace

"Zo nan!" Ammi ta faɗa har lokacin tana kallanta. Se a lokacin ta ɗaga kanta ta kalli Ammin, duk rashin gaskiya ya gama bayyana a kan fuskarta. A hankali ta taso ta soma takawa zuwa inda Ammin take, a sukwane ta zame ta zauna a ƙasan ƙafar Ammin kanta a ƙasa bayan ta faki idon Ammin ta jefawa Didi harara, itama ta maida mata tana ɗauke kai. Hannu Ammi ta kai ta kamo kunnen Lulu ta ja shi, har se da Lulun ta ɗan saki ƙara tana kai hannunta kan hannun Ammin.

"Wato ba kya jin magana koh? Duk irin faɗan da Abbanku ya yi miki ba ki ji ba? Dan kin ga ban saka baki ba a lokacin, wallahi da kin bari na saka baki dukanki zan yi ko kuma na kaiki wajen malamin ya zane min ke da kanshi. Wai me kike taƙama da shi ne Lulu? Me kike ƙoƙarin ɗauka ki azawa kanki? Ke babu wanda ya isa ya sarrafaki kenan bayan iyayenki ko me kike nufi? Shi ba malaminki bane? Be isa ya sakaki ko ya hanaki ba? Kin yi laifi ya hukuntaki ta fatar baki kawai amma a wajenki laifi ya yi. So kike kenan duk abin da kika yi ya zuba miki ido kawai, saboda ke ce malamin shi kuma ɗalibin? Ashe ma tsoronki yake ji. Toh ki buɗe kunnenki da kyau, wallahi daga yau aka sake ce min kin yi wa wani rashin daraja, ba ma shi kaɗai ba zamu gauraya da ke. Kin ji dai na faɗa miki." Ammi ta ƙare maganar tana sakin kunnen nata. Se ta kai hannu ta riƙo kunnen da har ya soma mata zafi, haka kuma ya yi ja kamar wanda aka yi wa wani abun. Se ta ɗaga kai a hankali tace

"Ki yi haƙuri Ammi." Ɗauke kai Ammi ta yi kamar ba ta ji ba. Ta san halin Ammi ba kamar Abba take ba, ba ta iya fushi ba, idan tace za ta yi fushi da ke har se kin wahala, dan haka gwara tun wuri ta nemi sulhu, hakan ne ya sanyata tashi gaba ɗayanta ta hau kan kujerar, sannan ta ɗora kanta a kan cinyar Ammin tace

"Don Allah Ammi ki yi haƙuri, ba zan ƙara ba." Ta ƙare maganar hawaye na zuba a kan fuskarta. Se da Ammi ta ji saukar zubar hawayen Lulun a jikinta sannan ta dafa kanta tace a hankali

"Ka da ki ƙara." Da sauri ta jinjina kai tana ɗagowa sanda farar fuskarta ta gama yin ja sosai.

.. Har suka koma ɗaki ba wadda tace da er uwarta ko uffan, kowacce se wani ɗauke kai take ita a lallai dole ita aka yi wa laifi. Se dai duk so suke a cikin nasu ɗaya ta soma yi wa ɗaya magana se a shirya. A haka dai har suka yi magribh ba su kula junansu ba, kowacce na cigaba da basarwa.



... "Amm idan ba damuwa kafin ka tafi ko za ka mun magana da Abba mana." Kaseem ya faɗa yana kallan drivernsu Lulu wanda wani lokacin shi ke kai Abba ya kuma ɗauko shi daga duk inda ya je.

"Eyyah, ai ba ya cikin gidan ma gaskiya. Be dawo ba tukunna."

"Toh godiya nake. Bari na jira shi." Kaseem ya faɗa yana gyara tsayuwarsa a jikin motarsa. Se da drivern ya zo ze wuce se kuma ya sake katse shi da faɗin

"Yi haƙuri don Allah, ko za ka ɗan sanar wa da gidan Kaseem ne, da yake na zo mun yi magana da Abbansu so yau ɗin kuma dai zuwan na Afrah ne.." Murmushi Ado driver ya yi fahimtar abin da Kaseem ke nufi da ya yi.

"Toh babu damuwa.. bari na sanar da su." Daga haka ya juya ya koma cikin gidan. A bakin parlourn ya tsaya ya yi sallama. Ammi da ke zaune ta amsa tana faɗin

"A'ah ashe ba ka tafi ba."

"Wallahi kuwa Hajiya. Na zo tafiya ne se kuma na haɗu da baƙon da kuka yi. Yace min dai sunansa Kaseem kuma ya zo wajen Abban En biyu ne. Toh da na faɗa masa baya nan shi ne yace min ko zan kira masa Afrah.."

"Afrah kuma? Ikon Allah." Ammi ta faɗa, dan ita gaba ɗaya tama manta da maganar, ko tuntuɓar su ma ba ta yi ba bayan dawowarsu, dan ta yi tunanin ma za su mata maganar da kansu, se dai tunda su basu mata ba, gwara ita ta yi musu.

"Toh shigar da shi ɗakin baƙi.."

"Toh Hajiya." Ado driver ya faɗa yana wucewa. Miƙewa Ammi ta yi ta wuce ɗakin Twins. A kan gado ta samesu dukansu suna karatun wani english novel ba wadda ke kallan wani. A nutse ta ƙarasa cikin ɗakin ta nemi waje ta zauna a kan gadon tana kallan en biyun nata. Se ta yi murmushi kawai dan ta gane zaman nasu ba lafiya ba, kowacce haushin er uwarta take ji.

"Wajen wa Kaseem ya zo ne?" Duk tare suka ɗaga ido suka kalli Ammin kafin suka kalli junansu. Jin sun yi shiru ne ya sanyata sake faɗin

"Tambayarku fa nake."

"Ammi wajen Didi fa ya zo." Lulu ta faɗa tana tura baki, ita a lallai dole ba ta so faɗar sunan Didin ba.

"Allah ya shirya min ku. Duk ku zo nan." Ammi ta yi maganar duka a tare. Se suka sakko gaba ɗayansu zuwa ƙasa. Kusan a tare suka ɗora kansu a kan cinyar Ammin. Se ta ɗauki duka hannayenta ta ɗora a kan kowacce sannan ta soma faɗin

"Shi ne ba ku faɗa min ba? Ba dan na tambaya ba wato shiru za ku min koh?" Se suka girgiza kai a tare. Lulu tace

"Ammi ya ɗauka ni ya gani a ranar, shi ne na faɗa masa Didi ce, dan lokacin da ya ganta ma ni ina gidan Mami."

"Toh Masha Allah. Tashi ki ɗauko Little ya miki rakiya zuwa ɗakin baƙi ku gaisa."

"Ni dai Ammi Allah.."

"Allah me..? Je ki idan kin dawo se ki faɗa min idan ya yi miki toh shi kenan. Idan kuma be miki ba se mu bashi haƙuri." Ammi ta faɗa tana murmushi. Dariya Lulu ta yi tana ɗaga kai ta kalli Didi daidai lokacin da ta kulle fuskarta tana faɗin

"Ammiiiii.." ta ja ƙarshen sunan tana murmushi itama.

"Tashi maza." Ammi ma ta faɗa tana murmushin. Se ta miƙe a hankali ta ƙarasa wardrobe ɗinta ta ɗauko gogaggen hijab ɗinta jalbab ta saka sannan ta kalli Lulu bayan ta marairaice fuska tace

"Ki zo ki rakani kin ji?"

"Naƙi ɗin." Lulu ta faɗa tana murguɗa baki gani da ɗauke kai.

"Pls mana.."

"Kin ga, ɗauki Little ya rakaki, idan kin dawo har faɗan naku ma zan shirya.." Ammi ta faɗa tana kallan Didin da ko er shafa powder ma a kan fuskarta be dameta ba. Hakan kuma ba shi da wani muhimmanci dan kuwa ko a yanzun da bata shafa komai a kan fuskarta ba ta fito ta yi kyau abinta. Parlour ta fito ta kalli Little da ke kallan Mbc 3 hankalinsa kwance. Tace sanda ta ƙarasa kusa da shi

"Little zo ka rakani." Da sauri ya sakko daga kan kujerar da yake kai yana murmushi yake faɗin

"Toh mu tafi.." ya faɗa yana miƙa mata hannunsa. Se kuwa ta riƙe shi ɗin suka fita daga ɗakin zuwa ɗakin baƙin.

Cikin sanyayyiyar muryarta ta yi sallama cikin ɗakin. Kaseem ya ɗaga kansa da sauri yana kallanta, be san sanda ya sauke ajiyar zuciya ba a daidai lokacin da ya yi arba da kyakkyawar fuskarta.

"Kai!! Dama ba unguwa zamu ba." Little ya faɗa a shagwaɓe. Murmushi Kaseem ya yi yana kallan Little ɗin da ko ba a faɗa ba kamarsa ta gama fallasa cewa ƙaninsu ne. Se ya miƙe ya ƙaraso inda suke ɗin ya riƙo hannun Little yana faɗin

"Unguwa zamu je mana." Sakar masa hannu Didi ta yi, se suka koma cikin ɗakin yayin da ita kuma ta rufa musu baya.

"Barka da fitowa gimbiya.."

"Ina yini?" Ta faɗa dai a nutsen kuma cikin sanyi.

"Lafiya ƙalau Alhamdulillah. Kin fito lafiya?" Ya sake tambaya yana kafeta da idanu.

"Alhamdulillah.." ta faɗa tana ɗan satar kallan Little da be ce komai ba har lokacin. Se kuma can ta jiyo muryarsa yana faɗin

"Ina wuni?"

"Lafiya ƙalau Little.. me ye sunanka?" Ya tambaya yana kallansa

"Ai ka faɗa." Little ya faɗa yana buɗe ido.

"Me fa?" Kaseem ya tambaya dan be gane abin da Little ɗin ke faɗa ba.

"Little sunana."

"Ohhh! Haka ake kiranka da shi? Nyc name. Me ye sunanka na gaskiya?"

"Areef."

"Woww.. suna me daɗi..Sunan brother ɗina" Kaseem ya faɗa yana murmushi.

"Kai fa?" Little ya tambaya shi ma yana murmushi

"Kaseem!" Yamutse fuska Little ya yi kafin yace

"Nawa ya fi daɗi.." dariya Kaseem ya yi yana ji yaron na sake burge shi. Se ya saka hannu ya ɗora shi a gefensa sannan yace

"Zauna nan mu yi magana da gimbiyata." Ya ƙare yana kallan Didi da ta zauna lokaci ɗaya yana miƙawa Little wayarsa. Se kuwa ya karɓa cikin ƙanƙanin lokaci ya kamo game ya fara yi.

"Na san za ki yi mamakin sake ganina yau. Se dai ni a wajena idan kullum za ki amince na dinga zuwa gidan nan se na fi kowa farin ciki. Toh amma na san ko masauki ba a min ba ko da kuwa raɓani ne a yi a wani ɓangaren." Ya ƙare maganar kamar me neman taimako. Se ta ɗaga kai ta kalle shi. Ganin ita yake kalla ya sanyata saurin ɗauke kai. Jin ba tace komai ba ya sanya shi ɗorawa da

"Wata babbar mantuwa na yi a gidan nan. Na tafi ba tare da na karɓi abin da ze dinga sakawa kodayaushe na dinga jinki ba. Na tafi ba tare da na karɓi abin da ze sanyani na haƙura da zuwa gidan nan kullum, na samu ko da a sati ne na dinga zuwa sau 3 a lalace kenan." Yanda ya yi maganar ne ya tilasta mata yin ƙaramar dariya. Hakan da ta yi se ya ga tamkar ƙara mata kyau aka yi. Se ya gyara zama yana cigaba da kallanta.

"Allah kuwa a lalace mana."

"Sau ukun?" Ta faɗa tana buɗe ido.

"Tohm shi kenan zan rage. Amma dai yanzu ki bani number ka da Abba ya zo ya sameni yace na fiya naci har na dawo."

"Ba ni da waya."

"Da gaske?" Ya tambaya still dai yana kallanta. Se ta jinjina kai kawai. Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace

"Shi kenan, zan samu mu yi magana da Abba idan ya amince na kawo miki waya se na dinga jin muryarki ta nan, har kuma na samu na ƙarasa isar da saƙon zuciyata." Ya ƙare maganar yana murmushi. Da sauri ta girgiza kai kafin a hankali tace

"A'ah Abba ba ze bari ba.." Sosai hakan da tace ya sake birge shi, dan kuwa yanda yake gani emmatan yanzun masu irin shekarunta nawa ne ke riƙe da waya ba tare da hakan ya damesu ba ko ya dami iyayensu ba.

"Na san me yasa Abba ze hana.. toh amma kuma yanzu idan kin tuna ai da ni kaɗai za ki dinga waya. Ni kaina ba zan bari ki dinga waya da kowa ba, kuma ba za ki dinga amfani da wayar ba saboda karantunki.. saka miki ido zan yi.." se ta yi murmushi kawai ba tace komai ba.

"Didi bacci.." Little ya faɗa yana hamma. Se ta kalle shi sannan ta kalli Kaseem ɗin tace

"Bari mu tafi.."

"Kai haba tun yanzu?"

"Didi bacci.." Little ya sake faɗa yana riƙo hannun Didin, bayan ya sakko daga kan kujerar da Kaseem ke kai. Se ta miƙe kawai tana riƙo hannun shi. Ba dan ya so ba, se dai shi ma baya so ya zaƙe, hakan ne ya sanya shi miƙewa yace

"Tohm shi kenan.. Allah ya tashemu lafiya. A gaida min da Twinnynmu.."

"Tohm." Didi ta faɗa, se kuma a hankali tace

"Ka gaida gida." Lumshe idanunsa ya yi yana jin daɗin abin da ta faɗa ɗin.

"Gida ze ji kyakkyawata." Daga haka ta fice daga ɗakin, shi kuma ya bita da kallo har ta fice. Se ya koma ya zauna a kan kujerar yana lumshe idanunsa. Anya kuwa ze iya bari har se Didin ta gama secondary kafin a aura masa ita? Ba dan ba dan ba da yace Abban ya aura masa ita har secondary ɗin ta ƙarasa a cikin gidansa, se dai dan kawai ka da a ce ya zaƙe ne. Tana komawa gidan kai tsaye hayewa kan gado ta yi ta kwanta dan ba ta so kowa ya mata maganar dan wallahi kunya take ji. Ko Lulu sanda ta shigo cikin ɗakin tana toilet, dan haka da ta fito ma se ta ga Didin kwance kan gado kamar me bacci. Ita kuwa Ammi ta fahimci dalilin Didin na yin hakan, dan haka kawai se ta yi murmushi tana ƙyaleta zuwa gobe sa yi maganar har Abba.


... Tun ɗazu ta ke attempting na yi wa Lulu magana, se dai kuma yanda ta ga ta wani haɗe rai, haka zalika ta nuna ma kamar ba ta san da zamanta a wajen ba, ya sa ta maaze. Har dai zuwa sanda aka fita sallah. A daidai sanda Lulun ta ke ƙoƙarin shiga aji saboda mantuwa da ta yi Abida ta tareta da faɗin

"Afaaf!" Se ta ɗaga kai ta kalleta da mamakin yanda rashin kunyar ta ya iya barinta ta mata magana. Ɗauke kai ta yi da niyyar barin wajen, se ta sake matsowa da sauri tace

"Haba ke kuwa don Allah ki tsaya ki ji abinda zan faɗa miki." Jin abin da ta faɗa ne ya sanya Lulun dakatawa, dan ta ɗauka ko za ta bata haƙuri ne ko kuma ta sanar da ita ta yi nadama.

"Lafiya? Ki yi maza ki faɗi abin da za ki faɗa ina da abin yi.." Lulu ta faɗa bayan ta tsaya a wajen.

"Amm don Allah ki taimakamin Afaaf, ki taimakawa rayuwata, ki taimakawa shugabarmu da ke matuƙar buƙatarki ki zo na kaiki wajenta ko da zuwa ɗaya ne don girman Allah.."

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un." Lulu ta maimaita tana kallan Abida cike da maɗaukakin mamakinta. Bata taɓa tunanin maganar da za ta sake mata ba kenan, ashe da gasken ba ta da kunya? Ashe ba ta tsoron Allah da gaske?

"Ki kama kanki, ki fita a hanyata. Na ga wa'azi ba ya shiga jikin irinku, saboda haka wallahi zan tona miki asiri kowa ya san wace ce ke. Kin san kuma idan har en makaranta suka sani shi kenan se kowa ya ji a cikin unguwar nan. Shi kenan kuma ta ɓare da ke."

"Toh se me? Kin daɗe ba ki tona min asiri ba. Idan ki ka je ki ka faɗa ai za su tambayeki yanda aka yi ki ka sani, ko me za ki faɗa ba yadda za su yi da ke ba. Saboda haka yanzu ma ba se gobe ba ki je ki tona min asirin."

"Haka ki ka ce?" Lulu ta faɗa tana murmushi, dan ita sam wannan maganar da Abidar ke faɗa ta san kawai faɗa take yi saboda rasa abin faɗa. Ban da haka a irin wannan abun har se ta tsaya ma tunanin idan ta je faɗa za ta ɓare da ita?

"Haka na ce!" Abida ta faɗa itama tana kallan Lulun.

"Ohk.. ki tsaya ki yi kallo.." Lulu ta faɗa tana juyawa a fusace, tana tuna yadda Didi ta hanata tona mata asiri tun ranar farko, da ta barta tun a ranar ta sanarwa wani daga cikin malaman ta san da tuni yanzu an daɗe da korar Abidar daga makarantar..



Me son yin payment yanzu kafin mu gama Free pages, ze tura ₦300 ne ta 8124818273, Zahra'u Yusuf Ishaq, Opay. Shedar biya ta 08124818273.


https://chat.whatsapp.com/BClMNPwWybg2n3oRvtemv8

*♡☆A JINI TAKE☆♡*
*(IZZATA)*


By
_*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_


*CHAPTER ONE*

Page_17

___Ganin da gasken juyawa Lulun ta yi ya sanya Abida saurin riƙota tana faɗin

"Afaaf! Wai kin ɗauka da gaske nake? Wallahi da wasa nake miki. Kawai ina so ne na ga za ki iya abin da ki ka faɗa ɗin? Se kuma na ga ashe za ki iya ɗin?"

"Cikani malama. Ashe har yanzu ba ki san wace ce ni ba, ni za ki yi wa gatse?" Lulu ta faɗa fuskarta a haɗe tana kallan hijab ɗinta da Abida ta riƙe. Jin ta ƙi sakinta ne ya sanyata saka hannunta ta fincike hijab ɗinta sannan tace

"Dallah can cikanii!!" Daga haka ta juya. Cikin wani irin sauri Abida ta zo har gaban Lulun tace lokacin da fuskarta ta koma kalar tausayi

"Don girman Allah ki yi haƙuri, wallahi na tuba fa ba zan ƙara ba, kuma ki saka min ido."

"Matsa min hanya." Lulu ta faɗa ba tare da ta kalleta ba. Ganin dai da gasken so take yau ɗin ta tona mata asiri a bainar nasi ya sanyata zubewa a kan gwuiwoyinta sannan tace sanda idanunta suka cika da ƙwallar da ba ta tsoro ba ce, face ta zallar takaicin tsugunawa Lulun, lallai ko me Ladi za ta saka a yi wa Lulu ita me amincewa ce komai muninsa kuwa. Se a lokacin sannan Lulu ta dakata tana huci dan wallahi a yau ɗin ta yi niyyar zuwa wajen wani malamin ne ta sanar da shi abin da ya faru, se dai Abidar kuma ta bata tausayi dan haka ta fasa tafiyar. Kafin tace komai ta sake tsinto muryar Abidar na faɗin

"Nima ba dan komai ba ne ya sanya na dage a kan wannan maganar ba, se dan na san ba a yi wa Jakadiyarmu musu, babu wanda ke ƙaunar ja da abin da tace. Toh amma tunda ke kin ƙi yadda, kin kuma nuna ba ki da tsoro, ba ni da damuwa zan je na sanar da ita yanda muka yi da ke, kuma daga yau ba za ki sake jina na zo miki da wannan maganar ba. Ba ma ke kaɗai ba na riga na tuba nima. Ina kuma me sake baki haƙuri.."

"Ita ɗin banza! Wace ce ita? Ku dukanku ma su waye ku? Who the hell do u think u are da har kuke ganin ba za a iya muku musu ba?"

"Ai na ce ki yi haƙuri.." Abida ta sake faɗa kamar da gasken ta yi nadama. Tsaki Lulu ta ja kawai ta shige daga wajen ta barta a durƙushe. Se a lokacin sannan Abida ta bi Lulu da kallo, haushinta da kuma tattaurar zuciya gami da taurin kai irin nata na ƙara fusatata.

"Ki jira haɗuwarku da Ladi.." ta faɗa tana fidda wani huci cike da ɓacin rai. Daga haka ta cigaba da tsugunon tsawon mintuna kamar ba za ta bar wajen ba, se kuma can dai itama ta miƙe ta fita Sallahr rai a ɓace.


.. Gaba ɗaya kwanakin yana busy sosai saboda yanda Daddy ya sakasu a gaba a kan fara kasuwancin da za su soma. Sanye cikin gajeren wando da kuma wata hamshaƙiyar farar riga mara hannu, wadda ta gama bayyana halittar ƙaƙƙarfan damtsen farin hannunsa da baƙar suma ke kwance luff luff kamar ba jiki ba, saboda yanda ta ke jere kuma a kintse kamar wadda ya ke saka hannu da kansa ya ke jerata. Numfashi kaɗan ya ke ɗan saukewa kasancewar ya daɗe yana motsa jikin. Baƙar sumar kansa da gashi ke nan ajje tuli kamar ba ya askewa ta ɗan hargitse ta kuma jiƙe da gumin da za ka iya cewa ruwa ya watsa a kan. Se dai da ya ke shi ɗin ba gwanin gumi ba ne a jiki ko a fuska ya sanya jikin nasa gumin kaɗan ne babu yawa kamar wanda ma be yi wani motsa jiki ba. A hankali ya kai hannunsa ya ɗauki wani farin towel da ke ajje wanda yafi kama da sabo gall, ya ɗan buɗa shi sannan ya kai kansa ya shiga tsane gumin da ke cikin kan nasa. A hankali kuma ya koma ya zauna dan ya ɗan sake jin daidai kafin ya faɗa toilet dan yin wanka. Ɗan fesar da iska ya yi daga bakinsa sanda ya tuna nan ba da jimawa ba Daddy kan iya kiransa su ƙarasa magana. Lokaci ɗaya kuma ya tuna da Hero da ke ta kiransa tun ɗazu be ɗaga ba. A hankali ya kai hannunsa inda wayarsa ke ajje, ya jawota yana ɗan lumshe idanunsa, takurar Daddy ta yi yawa, har ya soma ƙosawa da ita. Tun yanzu kuma haƙurinsa na neman ƙarewa a kan rashin samu ya sha ishashshiyar giya. Dan tun lokacin da ya je joint ɗin nan ya sha ta hannun Hero be sake sha ba, couz he thought gaba ɗaya ta ƙasar nan haka take babu daɗi, ga kuma bugarwa da sakawa a dinga yiwa mutum kallan ɗan ƙwaya. Shi ya sa ya dakata se ya samarwa kansa irin wadda ya saba sha sannan ya yi kodimo son ransa. Se dai a dalilin wannan kasunwancin da za su fara ya sa komai ya dakata masa, ga shi kuma yanzu gaba ɗaya gangar jikinsa ta ƙi aminta da kwana biyun da be sha ba, hatta shi kansa jinsa ya ke yi wani daban. Number Hero ya kamo ya danna masa kira kafin ya saka a kunnensa. Tana shiga kuwa Hero ya ɗaga dan dama a ƙage yake da son ganin kiran Bad Man ɗin.

"Bad..!!"

"Hero." Ya faɗa har lokacin idanunsa a lumshe.

"Inata kiranka ba amsa.. Akwai daddaɗan labari.."

"Labari?" Bad Man ya faɗa. Dariya Hero ya yi kafin yace

"Yeap. maganar harkar nan da na ga ba ta maka daɗi ba, na samo maka the most expensive one, am sure u will enjoy it.."

"Really?" Ya faɗa yana ɗan ɗage girarsa gami da buɗe idanunsa.

"Offcourse yes!"

"Ohk nawa ne price nata?" Bad Man ya faɗa dan sake tabbatar da da gasken me tsadar ce ko kuma dai kawai zuzutawar Hero ɗin ne

"Na yi dropping maka message. Check ur DM pls.."

"Alright.. Thanks.."

"Haba haba, ka da ka sa na ji wani iri mana, da girmanka? Ai ko me na maka girmanka ne my Man.." Murmushin gefen baki Bad Man ya yi wanda ya matuƙar ƙawata fuskarsa kafin ya kai hannu ya ɗan shafa kwantacciyar sumar da ke zaune luff a kan fuskarsa wadda kallo ɗaya za ka mata ka san mamallakinta na kula da ita, dan kuwa ba ta da yawa irin wadda ake askewa ce a kai a kai, hakan ne ya sanya kodayaushe ta ke cikin nutsuwa babu hayaniya.


... "My son!!" Aunt Makiyy ta faɗa tana ƙarasowa cikin ɗakin ta yi hugging nasa cike da kewar ɗan yayarta ta. Ɗan murmushi ya yi kafin ya yi hugging nata back.

"Ba dai daga bacci ka tashi ba?" Ɗan yamutse fuska ya yi sannan yace

"Nop, na ɗan motsa jiki ne."

"Dole ko da yaushe jikinka ya ƙara murɗewa. Kana kallan yanda fatarka take sake yin kyau da sheƙi, gami da sake murjewa kuwa?" Ta yi maganar tana kallan yanda ya yi kyau cikin wasu tsadaddadun ƙananan kaya.

"Aunt.." se ta yi murmushi kafin tace

"Da gaske fa.." Daidai lokacin da Mom ta shigo ɗakin kenan. Da murmushi kan fuskarta ta ƙaraso tana faɗin

"Se yaushe za ku fito ne?"

"Yanzu ma kuwa.." Aunt Makiyy ta ƙare maganar tana kallan Bad Man, sannan ta ɗora da

"Yau da kaina na shirya maka abinci me daɗi. Hope dai ba fita za ka yi ba?" Hannu ya kai ya ɗan murza goshinsa sannan yace

"Eyyah akwai inda zan je buh idan na dawo zan ɓullo.."

"Ai kaa ji kuma." Aunt Makiyy ta faɗa tana ɓata fuska. Komawa ya yi ya zauna a kan ƙaton haɗaɗɗen gadonsa sannan ya soma saka takalminsa. Se da ya gama kafin ya miƙe yana gyara zaman hular kansa da ta mugun karɓarsa kafin ya kalli Mom da Aunt Makiyy yace

"Zan tafi.." Matsawa kusa da shi Mom ta yi ta gyara masa zaman hular

2 Comments On A JINI TAKE (IZZATA) CHAPTER 1
avatar
abubakar-sunusi

10 months ago

Reply

avatar
abubakar-sunusi

10 months ago

Reply

Please Login or Register in order to submit comment