Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta soma magana Hajiya Sa'adah ke kallanta, ba tayi mamakin soma maganar da tayi ba dan dama ba yau ne karon farko da ta ke faɗa mata makamancin waɗannan maganganun ba, se dai yau ɗin mamakin yafi kamata sosai musamman da har se da ta shigo ɗakinta sannan take jifanta da waɗannan kalaman. A nutse ta buɗe baki duk da yadda take jin wani irin ɗaci a cikin bakinta, maganganun Hajiya Salman tabbas sun daketa sun kuma taɓata sosai

"In Sha Allah." Shi ne abin da ta iya furta wa sannan ta ɗauki wayarta tayi stairs ɗin da ke cikin ɗakin nata. Tsaki Hajiya Salma ta ja tana bin ta da kallo, a ranta tana fata da addu'ar Allah yasa ta bar mata ɗanta, ta dena wannan shishshigin ta bari idan ta haifi na ta se ta yi duk abin da za ta yi.




... A ɓangaren Twins kuwa ko da suka isa makaranta kai tsaye aji suka nufa, lokacin babu wanda ya shigo ajin, da yake ajin ba baya ba wajen sanin ya kamata se kowaccensu ta ɗauki Qur'an ta soma bitar haddar da za a karɓa yau ɗin. Kallan Lulu Didi tayi tace a hankali saboda karatun da ake yi

"Ki maimaita karatun mana" ta faɗa ganin ta ɗauki wani hadith tana dubawa.

"Didi na iya fa, ba se na maimaita ba." Sanin Lulun na da kaifin hadda ne ya sanyata yadda da hakan, ta rabu da ita, ita kuma ta cigaba da karatunta. Duk da yadda idanun Lulu ke kan hadith ɗin da take karantawa amma gaba ɗaya hankalinta ba ya kai, duk taurin kanta se take ji kamar ta ɗauki Qur'an ta yi haddar, amma se ta ji zuciyarta ta ƙeƙashe, hakan ne ya sanyata jan tsaki da siririyar muryarta ta cigaba da karatunta. Dukan da aka ɗaka mata a kafaɗarta ne ya sanyata saurin juyawa bayan ta ɗan saki ƙara saboda yadda dukan ya shigeta.

"Masoyiya!" Ta faɗa tana buɗa baki. Galla mata harara wadda ta kira da Masoyiyar tayi kana tace

"Ni zaki wa rashin mutunci koh? Ya miki kyau" ta faɗa tana neman waje ta zauna kusa da ita ta haɗe rai.

"Ke dallah makara fa muka yi, na ɗauka kin tafi" Lulu ta faɗa tana kallan Fateema Kabeer wadda ta kasance babbar ƙawarta a Islamiyyar ta su.

.. Sanye cikin wata lallausar brown ɗin jallabiya, sumar kansa saye cikin irin wannan naɗin da larabawa ke yi a wajen goshi zuwa bayan kansu. Kyakkyawa ajin farko, fari me ɗauke da wasu idanu masu mugun kyau, manya masu ɗauke da baƙar ƙwayar ido me shegen kyau, wata irin gira ce da shi wadda take a jere kamar wadda aka saita ta ta zauna akan fuskarsa ta matuƙar ƙawata ta, hakan ya sa har haɗewa da junansu se da suka yi, saboda se da suka bada wani irin shahararren kyau a tsakiyar goshinsa. Bakinsa ɗan ƙarami ne kamar na mace, kuma ja kamar wanda yake shafawa jan baki ko wani abun makamancinsa, se dai sam ba haka bane. Hannunsa ɗauke da wasu littattafai na Addini kasancewarsa ɗaya daga cikin manyan Malaman Addini a makarantar, ba ma a makarantar kaɗai ba hatta a yankin yana ɗaya daga cikin manyan Malamai, duk da ƙarancin shekarunsa da ba zasu wuce 25 ba amma da yake gada yayi daga wajen mahaifinsa da ya kasance Babban Malamin Addini a garin. Se hakan ya sake siyo masa soyayya daga wajen mutane da dama, ba ga mata ba ba ga maza ba, kowa ƙaunarsa yake. Se dai kuma shi ɗin mutum ne me matuƙar bauɗaɗɗen hali, idan dai har ka fahimce shi a bai_bai ba zaku taɓa zauna wa lafiya ba, zamanku baze taɓa daɗi ba, se dai kuma idan har ka fahimce shi shi ɗin mutum ne me matuƙar kirki da sanin darajar ɗan adam. Abu ɗaya ne yake sakawa a kasa fahimtar inda ya dosa kasancewarsa miskili na ƙin ƙarawa, hatta da magana bata dame shi ba, za a iya masa wani abun ko kuma ayi abu a gabansa amma ba ze ta tanka ba. Sam baya ɗaukar raini, ba ya ma bada fuskar da za a raina shin shi yasa ba a taɓa jinsa da wata ɗaliba ko ɗalibi ba, dan idan dai har ze shiga aji abin da ya kai shi ne kaɗai yake yi, daga nan ba lallai ma wata magana ta shiga tsakaninsa da wani ba. Sallamarsa da muryarsa me amo da daɗin sauraro yayi cikin ajin, se dai kasancewarsa mutum mara fara'a a halitta ya sa fuskarsa a cunkushe take, dan kuwa za a iya kiran Gwani Affan da "Sad Man" Gaba ɗaya ajin suka haɗa baki wajen amsawa, se ya sako kansa cikin ajin cikin nutsuwarsa da tayi matuƙar haɗuwa da tsarin halittarsa. Ɗan lumshe manyan idanunta Lulu tayi tana jin yanda ƙirjinta ya buga sanda ya shigo cikin ajin, tsoron da ya lafa mata tun ɗazun yanzu ya dawo sabo, amma saboda ƙeƙashashshiyar zuciya irinta ta se ta sauke ajiyar zuciyar tana tsara abin da zata faɗa idan ya zo kanta a karɓar haddar.

Tsayawa nayi ina kallan ikon Allah sanda na ji bakinsa ya furta

"Ina Hafsa Abba?" Dan ban taɓa tunanin za a iya yi masa Hausa ya ji ba ballantana ya furta da bakinsa saboda daga yanayin halittarsa har shigarsa da larabawa yayi kama, se dai maganar da yayi ce ta sanyani fahimtar tabbas bahaushe ne, se dai a cikin hausawan irin na daban ɗin nan ne, wanda za a iya cewa sun samu komai, musamman ma dai a wajen Gwani Affan da aka ba shi kyau, da kuma ilimin Addini, se dai kamar kowanne ɗan adam ba za a rasa wani abun da ya rasa ba, ban san a wajen Gwani Affan ko akwai abin da ya rasa ba dan ni dai a fili ban gan shi ba. Zumbur Hafsa Abba ta tashi bayan maganar da Gwani yayi, tace a hankali

"Malam ga ni!" Ba tare da ya kalleta ba ya jinjina kai sannan ya fita daga ajin, bin bayansa tayi zuwa wajen tana ɗan gyara tsayuwarta.

"Se gobe idan Allah ya kai mu zan kar6i hadda! Ki sanar da en ajin"

"Toh Malam" Daga haka ya juya ya soma takawa dan barin wajen cike da nutsuwa, se da ya ɓacewa ganinta sannan ta juya ta koma ajin ta sanar da su saƙon shi. Lulu kaɗai tayi farin ciki da hakan, dan kuwa gaba ɗaya en ajin farin ciki suke da dawowar Gwanin ajinsu. Haka dai ba dan sun so ba suka haƙura. Yau ɗin sosai take cikin farin cikin tun da suka fito daga makarantar murmushi yaƙi barin baby face ɗinta. Didi na lura da ita kuma ta san dalili amma bata kulata ba. Maganar da Fatima Kabeer ta yi ne ya sanyata kallanta

"Masoyiya baƙuwa na miki magana tun ɗazu." Juyawa Lulu tayi ta kalli wadda Masoyiyar ke magana a kanta, itama ita take kalla tana murmushi, yaƙe tayi kana tace

"Sannu!" Daga haka bata sake cewa komai ba. Daidai lokacin da suka zo zasu rabu, se suka yi sallama da yake ita baƙuwar zuwan makociyarsu Fatima Kabeer ne ya sa suka yi hanyarsu.

"Wallahi ƙawar nan ta ki ta min Fatima, kyakkyawa da ita kamar ita tayi kanta" Murmushi Fatima tayi tace

"Allah koh?" Ba tare da tunanin komai ba Abida tace

"Wallahi kuwa dama zaki haɗani da ita!" Kallanta Fatima tayi cikin er rashin fahimta da maganar ta ta sannan tace

"Ban gane ba?" Dariya Abida tayi kana tace

"Mu yi ƙawance mana"

"Uhmm ai ga ki ga ta, dan in dai Masoyiya ce wallahi dizgaki za ta yi" Se da Abida ta tsaya ta kalli Fatima har se da Fatiman ta tsargu sannan tace

"Shi kenan!" Daga haka babu wadda ta sake cewa komai suka cigaba da tafiya.



_Claremont California U.S
Tunnel Rd Berkeley
East Bay Hotel_


.. Haɗaɗɗen ɗaki ne da ke cikin East Bay Hotel wanda ya amsa sunansa ɗaki me kyau, ado da ƙawa, ya matuƙar ƙawatu da wasu Furniture 'yan ubansu. Kiɗa ke ta shi a cikin ɗakin cikin wata ƙatuwar speaker da ke gefe guda, sosai waƙar ke tashi da ƙarfi kamar ba mutum ɗaya ke ji ba. Babu kowa cikin ɗakin bayan speaker da ke cigaba da aikinta. Taɓa ƙofar toilet da na ji anyi ne ya sanyani saurin kai idona wajen. Farar ƙafarsa da ke cikin wani takalmin wanka itace na fara hangowa lokacin da yake zame takalmin kafin ya kai ga fitowa gaba ɗayansa. Singlet ce a jikinsa se towel ɗin da ke ɗaure daga ƙugunsa yayin da ya ɗora wani akan kafaɗarsa. Yanayin rigar da ke jikinsa itace ta fallasa halittar ƙaƙƙarfan jikinsa da ke ɗauke da wasu lafiyayyun kwantattun gargasa baƙa wuluk, wadda ta zauna ɗass akan farar fatarsa da ta gaji da gyara, hutu gami da jin daɗi. Ƙarasawa yayi gaban mudubi yana ɗan kaɗa kansa dake ɗauke da tulin suma wadda aka yiwa gyara na musamman, hakan ne ya bani damar ganin kyakkyawar fuskarsa da ke ɗauke da wasu shu'uman idanu, wanda kallo ɗaya idan yayi wa mutum ze iya rikicewa, ba ga mace ba hatta ga maza idanunsa kan firgita wasu mazan, idan kuwa mace ta bari ya ɗora shu'uman idanunsa akanta idan dai har bata rikice ta faɗa ƙaunarsa ba toh ba za ta bari ta sake iya haɗa idanu da shi ba saboda yadda idanun nasa suke kamar suna ɗauke da wani maganaɗisu ne, a iya idanunsa kaɗae an ƙure kyau, dan kuwa idanunsa na ɗaya daga cikin abin da ya kwashe kaso masu yawa daga cikin kyawun da Allah ya bashi, se kuma dogon siririn hanci da ke zaune akan fuskarsa kamar an zana. Duk da yanayin yadda kiɗan ke tashi da ƙarfi hakan be hana shi rage sautin ba se ma buɗe baki da yayi ya shiga bin sautin waƙar da se ka rantse shi yayi ta saboda yanda yake bin kowanne waje cike da ƙwarewa da muryarsa me daɗin sauraro. Ya ɗauki wajen rabin awa yana shiryawa sannan ya gama cikin wata haɗaɗɗiyar riga da crazy jeans da suka matuƙar yi masa kyau. Wata er ƙaramar abin hannu me kyau da tsada ya ɗauka ya saka a hannunsa da shi kansa yake ɗauke da kwantacciyar suma me matuƙar kyau. Wayarsa da ke ajje kan gado ta shiga ruri, se a lokacin ya ƙarasa ya rage sautin kiɗan da ke tashi, wanda da alama ba dan kiran da aka masa ba ba ze rage sautin ba. A nutse ya koma ya jingina da jikin mirror shu'uman idanunsa a ɗan lumshe kamar yadda suke a halitta, shi ba irin manyan idanun nan gare shi ba, basu da girma can kuma ba ƙanana ba ne se dai tasirinsu da kuma kyansu na musamman ne kamar yadda shi ɗin ya kasance na musamman.

"Bad!" Shi ne abin da Lucky da ya kira wayar ya faɗa bayan ɗaga kiran da Areef yayi.

"Yeah Lucky, What's going on?" Yayi maganar da muryarsa da ita kanta ta daban ce, me daɗin sauraro gami da wani amo da ke ɗauke da ita.

"Amm ka jirani harkar nan ta samu zan kawo maka har ɗaki."

"Nop, Let's meet at school couz mutanen Dad na nan." Da mamaki Lucky yace

"A'ah Bad kada kace min tsoro kake ji?" Ya tambaya dan ya san halin Bad Man ɗin. Wani murmushi Areef ya saki kamar ba zece komai ba se kuma yace

"Lucky! Just let's meet there" ya faɗa yana taune lips ɗinsa na ƙasa idanunsa a lumshe..





Me son karanta A JINI TAKE (IZZATA) har ƙarshe ze tura ₦300 ta 8124818273 Zahra'u Yusuf Ishaq Opay. Shedar biya ta 08124818273.




https://chat.whatsapp.com/LH7GN3pMRE26T5G5xcTmmw



*♡☆A JINI TAKE☆♡*
*(IZZATA)*


By
_*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_


*CHAPTER ONE*

Page_03


"Ohk mu haɗe a can ɗin." Lucky ya faɗa. Zare wayar daga kunnensa Bad yayi lokaci ɗaya yana ɗaukar karin waƙar da yanzun ke tashi cikin ɗakin. Soma takawa yayi dan barin wajen, wayarsa da ya ajje ta soma ƙara. Ɗan ƙaramin tsaki ya ja yana miƙa hannunsa kan tulin kwantacciyar sumar kansa, kamar ba ze dawo ba, se kuma ya dawo ya ɗora idanunsa akan wayar. Ɗan lumshe idanunsa yayi yana murza goshinsa kaɗan, ya san idan har ya ɗaga kiran Mom ba zata bar shi ya fita da wuri ba, shi kuma gaba ɗaya hankalinsa ya tafi wajen kayan da Lucky ɗin ya samo musu a sirrince. Wayar na dab da tsinkewa ya ɗaga duk da sautin kiɗan da ke tashi har lokacin se dai ba kamar ɗazun ba, hakan be sa shi ya kashe gaba ɗaya ba. Cike da soyayyar ɗan nata tace

"Boy!" A hankali yace

"Yes Mom!"

"Kana lafiya? Ya zaman kaɗaici?" Wani miskilin murmushi ya saki wanda ya matuƙar ƙawata kyakkyawar fuskarsa haka waɗannan idanun nasa se suka ƙara yin wani kyau na musamman. Kafin yace komai ta ɗora da

"Ai dai ya kusa ƙarewa, ka fara shirye-shiryen ne?" Ɗan shiru ya sake yi dan shi kam da za a bi ta tashi da ya cigaba da zama a ƙasar nan yanda ze cigaba da cin karansa babu babbaka, babu me saka shi babu me hana shi, amma se ya basar kawai yace

"Yeah Mom!" Murmushi Mom tayi sannan tace

"Ni fa na fara shirye-shiryen dawowarka tun yau, hope dai ba zaka wuce jibi ba?" Kamar me nazari ya ɗan yi jimm, lallae tabbas yau ɗin dole ne yawa kansa charge me lasisi, dan ya san idan har ya dawo Nigeria Daddy se yafi sakawa an saka masa ido fiye da yadda yanzun ake saka masa.

"Ehh ba zan wuce ba" shi ne abin da ya faɗa, kafin Mom ɗin tace komai ya ɗora da

"Amm Mom, zan ɗan shiga school ne. Zan kiraki later" Sauke ajiyar zuciya Mom tayi sannan tace

"Ohk Boy." Ko ajje wayar be yi ba bayan katse kiran Mom kawai ya jefata cikin aljihu sannan ya fice daga ɗakin jikinsa se tashin ƙamshin turarensa me matuƙar daɗi yake, wanda in dae ka shaƙa se ka so ka sake shaƙa saboda daɗinsa. Angry face ɗinsa ya sake tattarowa waje ɗaya ya ɗorata akan fuskarsa, cike da izza da isa yake takawa bayan ya sakko daga stairs inda ɗakin da yake ciki yake. Kai tsaye ya ƙarasa inda motarsa take, duk da uban mutanen da ke zagaye da ita hakan be hana shi saka hannu da niyyar buɗewa ba. Wani baƙin mutum me sanye da baƙaƙen kaya yayi ƙarfin halin faɗin

"Yallaɓae ina zamu cewa Mai gida ka je?" Dakatawa yayi daga niyyar buɗe motar da yayi, a yadda ya dakata kawai ba zaka yi tunanin ze amsa ba se kuma ya ɗaga waɗannan idanun nasa ya kafe wanda yayi maganar dasu. Da sauri ya janye saboda yadda ya duburburce lokaci ɗaya.

"Aikin da aka sakaku kenan?" Ya tambaya cikin tsare gida kuma cikin basarwa. Ɗaya daga cikinsu wanda da alama duk tare suke shi ne yace

"Sorry Ranka ya daɗe. Sabon ɗauka ne be san yanda abin yake ba." Be tanka ba duk da yaji abinda ya faɗa ɗin se buɗe motar da yayi ya shiga ya tashi motar ya bar Hotel ɗin zuwa makaranta. Ɗaya daga cikin mutanen Daddy ne ya bi bayansa a bisa umarnin Daddyn. Be kuma bar shi ba har se da ya tabbatar ya shiga cikin makaranta sannan ya dawo, dan su basu taɓa tunanin tantirancin Areef ɗin ya kai ya dinga shan wani abun a cikin makaranta ba, shi yasa daga zarar sun gan shi a makaranta hankalinsu ke kwanciya. A inda suka saba haɗuwa yayi parking na motarsa, saboda yanda ya taho a guje ya sa ya ɗan tunkuɗi wani keke yayi gefe sannan ya faɗi ƙasa. Duk da ya ga hakan amma be saka shi yayi yunƙurin yin wani abun ba, se ma ɗauke kansa da yayi kamar be gani ba ya sauka daga motar hannunsa ɗaya saye cikin aljihun wando. Lucky da ya hango shi ya ƙaraso yana kwashewa da dariya. Hannu ya ba shi suka tafa kana yace har lokacin yana dariya

"Mutumina gaskiya kai shege ne. Wai bayan duk waɗannan mutanen se da ka fito?" Ɗan murmushi ya saki wanda na fahimci murmushinsa kodayaushe baya wuce wannan miskilin murmushin da kamar ya san kyau yake masa idan yayi. Kamar ba ze ce komai ba se kuma yace

"Mu je kawai Lucky!"

"Bad Man!" Lucky ya sake faɗa yana jinjina basirar abokin nasa da yace su haɗu a makaranta.



.. Da sallama ɗauke a bakinsa ya shigo cikin soron gidan wanda Abeey ke zaune da wasu ɗalibansa yana karantar da su. Dakatawa yayi anan ɗin ya zame takalmin ƙafarsa sannan ya zauna akan tabarmar da ke shimfiɗe a wani ɓangare na soron gidan kasancewarsa me yalwar girma sosai.

"Barka da wannan lokacin Abeey"

"Barka dai Affan, ka dawo lafiya?" Dattijon mutumin da kana kallansa zaka san shekaru sun ja masa sosai ta faɗa, se dai duk da haka hakan be hana shi karantar da ɗalibai ba wanda kusan kullum cikin hakan yake.

"Alhamdulillah" ya faɗa a nutse lokaci ɗaya yana karɓar hannayen masu miƙo masa suna gaisawa cikin mutunci. Be daɗe a soron ba ya miƙe zuwa ɗakinsa da ana shiga tsakar gidan yake. Kai tsaye toilet ɗin da ke cikin ɗakin ya faɗa yayi wanka, ya ɗauki wajen minti 20 sannan ya fito ya sake shiryawa cikin manyan kaya, sosai kyawunsa ya sake fitowa musamman da ruwan da be gama bushewa ba na jikinsa ya sake kwantar da kwantaccen sajen da ke zagaye akan kyakkyawar fuskarsa, ɗaya daga cikin abin da ke sake ƙawata fuskarsa kenan. Se da ya gama shiryawar sannan ya koma ya zauna akan madaidaicin gadonsa ya ɗauki littafan da ya shigo da su ya shiga dubawa yana ware waɗanda ze fara yiwa ajinsu Twins wanda yanzu su ne babban aji. Sallamar Ummeey cikin ɗakin nasa ne ya sanya shi ɗaga manyan idanunsa ya kalli bakin ƙofar. Murmushin da ban taɓa gani akan fuskarsa ba ya wanzu, se a lokacin na sake fahimtar lallai murmushi ma wani abun ne, dan kuwa wani shahararren kyau Gwanin ya ƙara yi, kai ba zaka taɓa ɗauka shi ne a waje ba a yanzu da yayi wannan murmushin.

"Sannu da zuwa Ummeey" ya faɗa yana miƙewa daga inda yake.

"Yawwah sannu ka dae Affan.. Ka ci abinci?" Ta haɗe tayi maganar lokaci ɗaya. Girgiza kai yayi yace

"A'ah Ummeey zan dai ci tukunna" Itama girgiza kan tayi dama ta san halin Affan ɗin, shi ba damuwarsa ba ce ya yini be ci abinci ba, se dai idan ita ta tilasta shi, hakan ne ya sa idan dai ta fita unguwa toh tana dawowa zancen abincin take fara masa dan ta san da wuya idan ya ci.

"Ajiye littafan nan, yanzu zan kawo maka." Bata jira yace komai ba ta wuce Kitchen. Ajiyar zuciya ya ɗan sauke, a ransa yana sake godewa Allah da irin wannan uwa da ya ba shi, dan haka se ya koma kawai ya zauna har Ummeeyn ta dawo hannunta ɗauke da abincin ta ajje masa. Babu musu ya ɗauka ya soma ci ko dan faranta ran Ummeeyn. Se ma ta zauna tana masa fifita shi kuma yana cin abincin.





... A harabar gidan driver ɗin da ya saba kaisu makaranta ya saukesu. Dukkansu suna sanye ne cikin Uniform na makarantar boko me kyau, kalarsa nutsatstsiya ce sam babu hayaniya, ga kuma yanayin yadda ɗinkin da aka musu yake me kyau, wanda aka yi shi cike da ƙwarewa. A gajiye dukaninsu suka shige cikin ɗakin nasu da sallama, yayin da Little ya faɗa ɗakin a guje yana kiran Ammi. Ammi da fitowarta daga kitchen kenan ta amsa sallamar tasu lokaci ɗaya tana riƙe Little da ya rungumeta.

"Ammi mun dawo." Ya faɗa bayan shi ma ya rungume Ammin.

"Sannunku da dawowa yaran kirki" tayi maganar tana ɗago shi suka ƙaraso zuwa cikin parlourn. A tare Twins suka zube akan kujera sannan kusan a tare suka ce

"Washh!" Se da Ammi ta zauna sannan tace

"Da alama kun gaji?" Yamutsa fuska Didi tayi tace

"Wallahi kuwa Ammi"

"Toh maza ku tashi ku watsa ruwa, ku zo ku samu ku ci abinci." Ta ƙarasa maganar tana kallan malalaciya Lulu da har ta kwanta akan kujerar ɗakin. Se dai da yake ta ji maganar Ammin ya sanyata miƙewa ta bi bayan Didi suka wuce ɗakinsu.

.. Parlour ne madaidaci wanda adon da aka masa ya dace da zubinsa, ya matuƙar ƙawatu da kayan da ke cikinsa. Daga kan kujera wata matashiyar budurwa ce da aƙalla za ta yi 20years, zaune cikin riga da wando wanda ta ɗaga shi zuwa ƙasan gwuiwarta. Hannunta ɗauke da waya tana dannawa yayin da kunnenta ke saƙale da bluetooth, da alama waƙa take ji dan kuwa lokaci lokaci ta kan tsaya ta ɗan jinjina kanta sannan ta cigaba da danna wayar. Ba wata kyakkyawa bace se dai ba za a kira ta da mummuna ba, dan kuwa tana da kyawunta daidai misali. Kanta babu ɗan kwali se zallar gashinta da ba shi da wani yawa da ta ƙulle shi a saman kanta.

"Jadwa!" Maganar da naji daga gefe itace ta sanyani juyawa dan ganin wadda tayi ta. Babbar mace ce wadda aƙalla ta bawa 40 baya, ko kuma 40 ɗin ciff, se dai idan har kace daga yanayin shigarta zaka faɗi shekarunta toh se dai ka ce ba tafi ashirin da wani abu ba. Dan kuwa wani riga da wando falazo ne a jikinta, yayin da ta saka wata hula a kanta wadda ta zameta har wajen rabin kanta a waje yake. Hannunta ɗauke da waya ta ƙaraso cikin ɗakin ta saka hannu ta cire bluetooth ɗin kunnen Jadwa guda ɗaya. Se ta juyo da sauri, ganin Maminta ne ya sanya ta faɗin

"Ohh Mami! Kin saka nayi loosing." Ta faɗa tana yamutsa fuska. Neman waje Mamin tayi tana faɗin

"Kin ƙure uban volume, idan kin gama ji se ki tashi ki yi sallah." Se da ta sake yamutsa fuska kafin tace

"Tohm" ta cigaba da danna wayarta. Se kuma ta juyo ta kalli Mamin da take danna waya tana ɗan tauna chewing gum ɗin da ke bakinta.

"Mami wa za ki kira ne haka?"

"Ammin twins!" Se ta juyo sosai tace

"Mami me ya faru?" Ta faɗa daidai lokacin da Mamin ta kai wayar kunnenta sannan ta amsa mata da

"Ki jira ki ji!" Babu musu kuwa ta gyara zama tana kallan Mamin. A ɗaya ɓangaren kuwa Ammi na zaune kan kujera, Didi na kusa da ita tana koyawa Little home_work. Wayar Ammin da tayi ƙara ne ya sanya Lulu da tafi kusa da ita ɗauka ta miƙawa Ammin ba tare da ta kalli me kiran ba. Karɓa Ammi tayi ta ɗaga wayar, suka gaisa da Mamin sannan ta ɗora da

"Ina Twins su ke?" Murmushi Ammi tayi kana ta amsa da

"Ga su a kusa da ni" Kamar Mamin na kusa da Ammi tace

"Na san wannan maƙalalliyar uwar miskilanci tafi kowa kusa da ke a yanzu haka" Kamar kuwa ta sani hakan ne, kuma da yake sun ji abin da ta faɗa ɗin se Didi ta ɗora kanta akan kafaɗar Ammi tana tura baki da murmushi akan fuskarta. Hannu Ammi ta saka ta shafa kan Didi sannan tace

"Aikam dai.."

"Ina Lulu?" Ta sake tambaya. Da sauri Lulu ta taso daga inda take dan dama babu ƙarya suna ɗasawa da Auntynta su. Karɓar wayar tayi daga hannun Ammi suka gaisa sannan Mami ta ɗora da

"Yaushe zaki zo?" Kallan Ammi tayi sannan tace

"Idan an yi hutu!"

"A'ah babu wani hutu, ki zo kawai tunda idan kika zo ɗin zaki dinga zuwa makarantar anan ɗin ma, Uhmm?"

"Toh Mami" Daga haka ta miƙawa Ammi wayar, suka sake magana sannan suka yi sallama. Abba da ya shigo kafin su yi sallama yace

"Sadiya ce?"

"Ehh.." Kafin Ammin ta gama faɗar abin da tayi niyya Lulu tace

"Abba zan je gidan Mami pls.." se da ya nemi waye ya zauna yana riƙe da hannun Little sannan yace

"Makarantar fa?"

"Abba ai za a dinga kaini a can ɗin ma" Kallan Ammi Abba yayi dan jin abin da zata faɗa, se dai ba tace komai ba hakan ne ya sanya shi faɗin

"Ita ce ta nemi ki je ne?" Ɗan shagwaɓe fuskarta tayi sannan tace

"Ehh Abba"

"Ki shirya, gobe idan Allah ya kai mu se na saukeki acan ɗin." Cikin jin daɗi tace

"Toh Abba." Ta faɗa a ranta tana tuna yanayin rayuwar gidan Aunty Sadiyan, da take babu takura, komai ka ga damar yi daidai ne, ta san idan ta je can

2 Comments On A JINI TAKE (IZZATA) CHAPTER 1
avatar
abubakar-sunusi

10 months ago

Reply

avatar
abubakar-sunusi

10 months ago

Reply

Please Login or Register in order to submit comment