Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kansa kafin tace

"A haka ka fi kyau My boy.." ɗan murmushi kawai ya yi dan ya ga alama Mom ɗin ba dena faɗar sunan nan za ta yi ba, saboda yanda ya gama zama a bakinta.

"Wai batun aiki ne?" Mom ta sake tambaya. Ɗaga kafaɗarsa ya yi lokacin da hannunsa ɗaya ke cikin aljihun wandonsa.

"A'ah.. zan ɗan ga gari ne.." Murmushi Mom ta yi kafin tace

"Ni wannan fice_ficen duk ba sonsu nake yi ba. Ba dan bana so ka sake yin nisa da ni ba, da nace Daddynka ya sama maka aiki a wata ƙasar, saboda nan ɗin akwai 'ya'yan talakawa sosai da za ka dinga hulɗa dasu.."

"Gaskiya kam, nima ina bayanki Mom. Amma dai mu yi haƙuri da nan ɗin. Abin da za a kiyaye kawai shi ne haɗa shi da 'ya'yan talakawa, wannan kuma aikinki ne tunda mijinki ne.." Aunt Makiyy ta faɗa tana kallan Mom. Jinjina kai Mom ta shiga yi cike da gamsuwa da zancen Aunt Makiyy ɗin, se can ta kalli Bad Man da ba za ka taɓa cewa ya ji abin da suka faɗa ba.

"Ga key nan, idan kun gama hirar se ku kulle min." Ya yi maganar yana nuna key ɗin part ɗin nasa. Daga haka ya soma takawa ze fice

"A'ah Son mu je. Me za mu yi anan ɗin ba ka nan?" Aunt Makiyy ta faɗa tana soma takawa, se Mom ma ta biyo bayanta suka fice daga part ɗin. A compound suka yi sallama sannan ya soma takawa zuwa parking space. Daidai yana ƙoƙarin buɗe motarsa dan shi ba ya buƙatar taimakon kowa, Mommah ma ta ƙaraso wajen sanye cikin wata atamfa me shegen kyau da babban mayafi da ya dace da atamfar. Murmushi ta yi tana jin daɗin ganinsa dan ta daɗe ba ta sanya shi a ido ba. Daddy da ke gefenta sanye cikin wata shadda jamfa da wando ya kalli Bad Man da ya ƙaraso wajensu.

"Barka da wannan lokaci.."

"Barka dai Areef.." suka haɗa baki wajen faɗa, kafin Mommah ta ɗora da

"Ina za ka je ne haka?" Se da ya ɗan saci kallan Daddy kafin cikin basarwa yace

"Ina za ki je? Lem me drop u.."

"A'ah haba, je ka inda za ka ke, ba se ka wahalar da kanka ba driver ze kai ni.." Mommah ta faɗa tana murmushi. Ɗan yamutse fuska ya yi yace bayan ya kai hannunsa ya ɗan shafi gefen kansa

"Babu wani takura fa.. Daddy bari na ajjeta.."

"Kinga Sa'adatu je ki ya kaiki. Ai hakan ya fi.." Murmushi ta sake yi kafin tace

"Tohm shi kenan.. Daddyn Areef bari na je se na dawo.."

"Allah ya tsare.." Daddy ya faɗa, kafin ya maida dubansa kan Bad Man yace

"Pls daga nan ka da ka wuce ko ina.." Murmushin da be shiryawa zuwansa ba shi ne ya ƙwace masa kafin yace

"Ohk.." Daga haka ya shige motar, yayin da Mommah ta shiga wajen me zaman banza kafin ya tada motar. Se a lokacin sannan Daddy ya soma takawa dan komawa ciki cike da nutsuwa gami da kamala a cikin tafiyar tasa.



..."Zo ku zauna nan, tun a ranar ban samu mun yi magana ba se yau.." Abba ya faɗa yana kallan Twins. Babu musu suka nemi waje suka zauna dan ba su san a kan me ma Abban ke magana ba.

"Mun yi magana da shi wancan yaron Kaseem. So ban dai gane takamaimai ma a kan wadda yake magana ba. Afrah ce ko kuma Afaaf?" Abba ya faɗa yana kallansu. Da sauri Didi ta yi ƙasa da kanta cike da kunyar Abban, dan ba ta taɓa tsammanin maganar da ze yi ba kenan.

"Abba wajen Didi fa ya zo.." Lulu ta faɗa tana satar kallan Didi tana ɗan ƙunshe dariyarta. Ammi da ke lura da Didin itama ta yi murmushi tana ɗauke kai.

"Toh ikon Allah.. ke Didi matso nan kusa da ni.." Abba ya faɗa yana yin alama da hannunsa. Cike da kunyar dai ta matso tana sake yin ƙasa da kanta.

"Ki nutsu ki faɗa min kin ji? Yaron da ya zo wajenki da gaske yake aure ze yi, saboda haka za ki faɗa min idan ya yi miki zan san yanda za a yi a tsaida magana, idan ya so kuna gama secondary ɗin nan se a saka rana a ɗaura aure. Saboda haka faɗa min kina son shi?" Kunyar da tafi ta ɗazu ce duk ta sake rufe Didi, se kace wadda ke gaban alƙali ƙirjinta har wani harbawa yake yi.

"Abba.." shi ne abin da ta faɗa kawai har lokacin kanta a ƙasa.

"Assalamu alaikum.." Mami ta yi sallama cikin ɗakin. Dukkansu suka amsa sallamarta ta suna kallan ƙofar. Da gudu Lulu ta miƙe ta faɗa jikinta tana faɗin

"Oyoyo Mamina.." Murmushi Mamin ta yi sannan tace

"Yawwah daughter. Na same ku lafiya?"

"Ehh.." Lulu ta faɗa. Se suka ƙaraso cikin ɗakin, Mami ta nemi waje ta zauna suka gaisa da Abba da kuma Ammi sannan suka ɗan shiga hira kaɗan_kaɗan. Zuwa can Abba ya miƙe saboda lokacin sallah da ya gabato, ya musu sallama ya fice daga ɗakin. Cike da jin daɗi Didi ta miƙe ta tafi ɗakinsu dan dama wannan titsiyen da Abban ya mata gaba ɗaya ta kasa sukuni. Se a lokacin suka ɗan cigaba da hira jefi_jefi da Ammi. Zuwa can wayar Ammi ta shiga ruri, se ta kalli Mamin tace

"Bari na amsa kira.."

"Toh babu damuwa.." Mami ta faɗa tana murmushi. Se ta miƙe da wayar a hannunta ta shiga ɗaki. Se a lokacin Mami ta kalli Lulu da ke kusa da ita ta maka mata harara sannan tace

"Ina wayar da na ba ki?" Buɗe ido Lulu ta yi gami da buɗe baki tana tuna wayar da Mamin ta bata, dan wallahi tun ranar da ta bata ta manta da babinta. Toh aba ce dama da ba ta gabanta.

"Wallahi na manta da ita.." ta faɗa tana tura baki.

"Shashashar yarinya.." Mami ta faɗa tana ɗan dafe kanta. Se kuma can ta ɗaga kai ta kalli Lulun tace

"Kenan ba ku taɓa waya da Kaseem ɗin ba?" Se a lokacin sannan Lulu ta yi murmushi kafin tace

"Albishirinki.." cike da farin ciki Mami tace

"Goro fari tass. Maza faɗa min kuna ta waya koh?"

"Toh ba ni ya gani ba, ashe Didi ya gani ya ɗauka ni ce. Kuma ma ya zo wajen Abba ya kuma zo wajen Didin ma sau biyu.."

"Didi kuma?" Mami ta faɗa cike da mamaki.

"Ehh.." Lulu ta faɗa da murmushin dai. Zuwa can Mami ta sauke ajiyar zuciya tana jinjina kai kafin tace

"Lallai" ta faɗa a kan laɓɓanta tana jinjina kai, kafin ta saki murmushi tana soma tsara yanda komai ze tafi.


.... "So nake na yi mata wani abun da har ta mutu ba za ta taɓa mantawa da shi ba, ba kuma tare da ta san ni ce na aikata mata ba. Dan idan dai har ta sani na san ba za ta dawo wajena neman taimako ba. Dan haka zan yi amfani da dabarata na sakata ta ji dole a wajena ne za ta zo ta samu mafita.." Dariya Abida ta kwashe da ita bayan gama sauraron abin da Ladi ta faɗa kafin tace

"Ina yinki Jakadiyarmu, Allah ya ƙara miki lafiya da kwanya. Kamar me za a yi mata?" Ɗan murmushi Ladi ta yi tana wani jujjuya kai irin ita shegiyar nan ana fasa mata kai kana tace

"Auruwa ne ba na so ta yi, dan idan dai har ta yi aure na san ba za ta taɓa amincewa da buƙatata ba, shi ya sa nake so in yi mata wani abun da za ta kasa auruwa, wanda daga ƙarshe idan ta rasa mafita dole ta dawo wajena" Cike da amincewa da zancen nata Abida ta shiga jinjina kai, dan itama ta daɗe da ƙuluwa da al'amarin Lulu, gwara a yi mata abin da ze tarwatsa wannan ji ji da kan nata da kuma taurin kan da take fama da shi.

"Ta ina za a fara kenan?" Abida ta faɗa tana murmushin jin daɗin yanda a wannan karon Ladin ke zama tana shawara da ita, se dai ta san hakan na da nasaba da kasancewar ita ta kawo Lulun. Amma dai koma menene ita hakan ma ya yi mata daɗi. Shiru na tsawon mintuna Ladi ba tace komai ba, se ƙurawa waje ɗaya idanu da ta yi kamar me nazari. Bayan shafewar wasu mintuna ukun Ladi ta saki wani murmushi tana sauke ajiyar zuciya gami da murza hannunta irin komai ya yi ɗin nan, kafin a fili ta furta

"Hero!!!" Ta faɗa tana sake jinjina kai gami da sakin wani murmushi..



Me son yin payment yanzu kafin mu gama Free pages, ze tura ₦300 ne ta 8124818273, Zahra'u Yusuf Ishaq, Opay. Shedar biya ta 08124818273.


https://chat.whatsapp.com/BClMNPwWybg2n3oRvtemv8

*♡☆A JINI TAKE☆♡*
*(IZZATA)*


By
_*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_


*CHAPTER ONE*

Page_18

__"Hero!" Abida ta maimaita sunan tana jinjina kai. Ba ta taɓa jin sunan a bakin Ladi ba, ba kuma ta taɓa ganinsa a cikin gidan nan ba. Dan haka maimaita sunan da ta yi tana jira ne ta ji Ladin ta mata ƙarin bayani a kan Hero ɗin. Kamar kuwa Ladin ta gane abin da take so, se ta yi murmushi kafin ta fara faɗin

"Cikin lokaci ƙanƙani kwanyata ta samo min mafita. Ba na buƙatar jigari_jigarin mutum, duk da ko cikin gidan nan ina da yaran da zan iya sakawa su min aiki a kan yarinyar nan. Se dai Hero tantiri ne kuma riƙaƙƙen ɗan duniya na bugawa a jarida. Shi ya dace na saka ya min wannan aikin, na san ze min yadda ya kamata har ma ya ƙara wani abun a kai.." Ladi ta ƙarasa maganar tana miƙewa. Cikin jin daɗi Abida tace

"Gaskiya ne, dama irinsa ya kamata a haɗa wannan shegiyar yarinyar me shegen taurin kai da shi, na san ze gyara mata zama.."

"Me kyan ma kuwa.." in ji Ladi.


... Tana zaune a gaban Kurfoti da ƙaramar tukunya ke kai tana yin miya, ƙamshi me daɗi gaba ɗaya ya cika gidan, dan kuwa Ummeeyn gwana ce wajen iya sarrafa abinci.

"Sannu da aiki.." Abeey da ke kishingiɗe kan dadduma ya faɗa yana murmushi. Itama murmushin ta yi sannan tace

"Yawwah.."

"Ni dai da ina da hali da na samo miki er aiki ta dinga rage miki wasu ayyukan.." Abeeyn ya sake faɗa.

"Uhmm, wacce er aiki kuma? Dukka ayyukan gidan ma nawa suke? Ni da yaron nan ze taimaka ya yi aure ai ka ga na samu er tayin hira nima.." Ummeey ta ƙare maganar tana juyo da kujerar da take kai ta koma tana kallansu Abeey. Kallan Gwani da ke zaune gefensa yana karatun wani littafin addini Abeey ya yi yace

"Toh kai ka ji.." Se a lokacin ya ɗaga kansa ya kalli Abeeyn, ya ɗan yi yaƙe sannan yace

"Abeey wai ni?"

"Ja'iri.. da wa nake nufi idan ba kai ba?" Ummeey ta faɗa tana kallansa.

"Ummeey idan aiki ya miki yawa ni me taimaka miki ne fa.." ya faɗa yana kallan Ummeeyn.

"Ni babu wani aiki da ya min yawa. Kawai dai ina buƙatar er tayin hira ne.."

"Tohm.." ya faɗa kawai. Murmushi Ummeeyn ta yi tana maida dubanta kan Abeey tace

"Ya jikin?"

"Jiki ya warware Alhamdulillah.. Anjima ma ina so na leƙa wajen ɗaliban can, saboda na kwana biyu ban yi musu karatu ba. Affan kuma kin ga akwai inda yake zuwa, ba ze yiwu ace kodayaushe kuma ba shi da lokacin hutu ba.."

"Abeey lokacin hutu kuma? Babu damuwa fa Abeey, ka cigaba da zamanka har zuwa lokacin da za ka warware gaba ɗaya se ka koma karatun." Ya ɗan dakata sannan ya ɗora da

"Zan je na musu karatun.."

"Allah ya yi maka albarka Affan. Allah ya albarkaci gaba ɗaya rayuwarka. Ya nuna min wata rana da ni da Ummeeynka muka daɗe muna jiranta kafin na bar duniyar nan. Idan hakan ta faru shi kenan ni kuma burina ya cika." Ya riga ya san maganar da Abeeyn ke yi a kan aure ce, dan ba yau ne karo na farko da ya saba yin makamanciyar wannan maganar ba. Se dai da yake shi ɗin ba ma'abocin magana bane ya sa be taɓa tambayar Abeeyn ba, se shi da kansa da ya fahimci aure Abeeyn ke nufi.

"Ameen Ameen.." Ummeey ta amsa itama tana murmushi.


... "Mami lafiya kuwa na ga kina ta murmushi?" Jadwa da fitowarta kenan daga cikin ɗaki ta faɗa tana kallan Mamin.

"Ke zo ki zauna ki ji min abin da ya faru." Mami ta faɗa tana riƙo hannun Jadwa suka zauna a kan kujera. Dariya Jadwa ta yi kafin tace

"Ke dai Mami duk sanda ki ka je gidan Abba se kin dawo da labari.."

"Ke dallah can ƙaruwarki ce yanzun ba tawa ba.."

"Ƙaruwata kuma Mami? Me ya faru?" Jadwa ta faɗa tana gyara zama.

"Ashe Kaseem ba Lulu yake so ba."

"Kamar yaya Mami? Toh wa yake so?"

"Afrah.."

"What? Didi kuma? Ta ya ya?" Ajiyar zuciya Mami ta yi kamin tace

"Ke ba wannan ba. Na haƙura ne dama saboda Lulu yake so, amma tunda na san Didi yake so ba zan haƙura ba, zan yi yanda zan yi na sama miki shi. Ke ki ka fi buƙatar shi ba wannan yarinyar me baƙin hali irin na uwarta ba.."

"Mami.." Jadwa ta faɗa tana buɗe idanunta.

"Ke ban son iya shege. Ba kya son Kaseem ɗin ne?"

"A'ah idan zan samu ina so mana.." Jadwan ta faɗa tana tura baki.

"Ja'ira.. Ahh toh.." Mami ta faɗa tana murmushi.


... Driving yake yi, babu abin da ke tashi cikin motar se sautin kiɗa me ɗan karen daɗi. Yana driving ɗin yana bin sautin waƙar cike da ƙwarewa. Hero da ke ɓangaren me zaman banza ma yana taya shi bin waƙar, se dai shi lokaci zuwa lokaci ya kan tsaya ya kalli wayarsa. Zuwa can wayarta sa ta shiga ruri daidai lokacin da Bad Man yace

"Wannan jahilin ringtone ɗin fa?" Ya faɗa yana yamutse fuska lokaci ɗaya kuma yana jijjiga kansa saboda bin sautin da ke tashi da yake yi.

"Kawai dai be yi maka. Right?"

"Ƙwarai.." Bad Man ya bashi amsa yana cigaba da driving ɗin.

"Hero!!" Shi ne abin da Ladi ta faɗa bayan Hero ɗin ya ɗaga wayar.

"Jakadiyar Mata.." Hero ya faɗa yana dariya.

"Shegen kaya, da alama yanzu haka kana wani hamshaƙin club ɗin ne koh?" Ta faɗa saboda yanda ta jiyo kiɗa na tashi sosai kamar a club. Se da ya yi dariya sannan yace

"Ko kaɗan fa.."

"Ah toh ai na san hali ne.." Dariyar ya sake yi sannan yace

"Yanzu dai ya ake ciki? Dan na san tunda na ga kiran nan na ki akwai wani abu.." Ajiyar zuciya Ladi ta sauke kafin tace

"Don Allah idan ba za ka damu ba ina son ganinka.."

"Toh fa. Ganina kuma?" Ya tambaya. Se da ta jinjina kai kamar yana gabanta sannan tace

"Ƙwarai kuwa don Allah. Taimakamin za ka yi ne a kan wata matsala da na san za ka iya magance min ita cikin ƙanƙanin lokaci.."

"Kina ina?"

"Ina gida." Ladi ta faɗa cikin farin ciki. Be ce komai ba ya katse wayar ya juya ya kalli Bad Man yace

"Pls Bad ajiye ni anan mana.." Kamar be ji shi ba ya cigaba da bin waƙarsa hankali kwance. Se kuma da aka ɗan wula sannan ya yi parking motarta sa. Hero ya sauka yana faɗin

"Zamu yi waya plss."

"Ohk.." ya amsa yana jan motar.


... "Na ji daɗin zuwanka Hero. Wannan na ɗaya daga cikin alfarma masu muhimmanci da aka taɓa yi min a rayuwata.." Ladi da ke sanye cikin ƙananan kaya babu ɗan kwali a kanta se tulin gashin doki da ke a kan nata ta faɗa tana kallan Hero. Murmushi ya yi yana gyara zamansa sannan yace

"Just tell me me ya faru? Kiran me ki ke min? Kin san dai ban fiye son harkar da babu ƙaruwa a cikinta ba.." ya faɗa yana gyara zaman hular kansa. Ajiyar zuciya Ladi ta sauke kafin tace

"Ka da ka damu mutumina. Wannan harka ce ta ƙaruwa irin sosai ɗin nan. Aiki nake so ka min a kan wata yarinya, na san wannan ɗin ba baƙon abu ba ne a wajenka musamman idan za a biyaka."

"Uhmm Ladi kenan. Ka da kice min aiki kawai zan yi miki babu wata ƙaruwa a ciki? Manta da batun biyana kuɗi, idan dai har zan ƙaru a tafiyar toh ba na buƙatar ko sisinki. Ke dai kawai ki saka a ranki komai ki ke buƙata kin gama samu.."

"Shi ya sa na yi yanda zan yi na nemoka Hero.."

"Akwai wata yarinya, ina sonta. Se dai ina so ne na ɗan saita mata zama dan ta nuna min ita ɗin mutuniyar kirki ce. Toh wannan batun na mutuniyar kirki nake so ya fita a kanta. A idanun kowa ta tashi daga me wannan sunan. Ni kuma daga nan ka gama aikinka zan ƙarasa sauran.." wata dariya Hero ya fashe da ita kafin ya soma faɗin

"Idan dai har na fahimci abin da ki ke nufi.. so ki ke a lalata rayuwarta, ta kuma zo ta rasa mijin aure, ta rasa kallan mutuncin da mutane ke mata, ta yadda za ta rasa mafita se kawo kanta gare ki?"

"Dalilin da ya sa nake ƙaunar aiki da kai kenan mutumina. Akwai ka da kwanya." Ta faɗa tana nuna saitin kanta fuskarta ɗauke da murmushi. Ajiyar zuciya Hero ya sauke sannan yace

"Ka da ki damu, har ma abin da ba ki ce ba za a yi miki, tunda dai nima ƙaruwata ce.."

"Hero kai ɗin na musamman ne. Allah ya ƙara maka kwanya.."

"An daɗe ana faɗa min hakan. Ke dai kawai faɗa min sunanta. Er gidan waye? Ya ya kamanninta su ke? Idan ze samu ma a samar min hotonta. Kwatancen gidansu kuwa ba wahala ze min ba idan dai har na san sunan ubanta.."

A yi manage da wannan pls, ba na jin daɗi ne. Da bama zan yi ba, kawai dae dan kar na barku a gantale ne shi ya sa na yi wannan ɗin.


https://chat.whatsapp.com/BClMNPwWybg2n3oRvtemv8

*♡☆A JINI TAKE☆♡*
*(IZZATA)*


By
_*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_


*CHAPTER ONE*

Page_19


___"Yanzu abin da za a yi zan haɗaka da yarinyar da ta santa sosai. Ta san gidansu, ta san sunan uban yarinyar, za ta kuma iya samo mana hotonta.." Jinjina kai Hero ya yi kamin yace

"Hakan ma ya yi.."


... Sake buɗe idanunta dai ta yi sosai dan sake tabbatar da da gasken Areef ɗin ne ya sauke Mommah a motarsa. Juyawa ta yi da sauri tana faɗin

"Mom... Mom kina ina ne wai?" Ta yi maganar ranta a ɓace.

"Gani nan. Wannan uban kira haka irin na tashin hankali.."

"Toh ai wannan ya fi tashin hankali, kin san abin da na gani yanzu kuwa?" Ta faɗa tana neman waje ta zauna har lokacin fuskarta a haɗe.

"A'ah se kin faɗa. Me ki ka gani?" Mom ta yi saurin faɗa tana neman waje ta zauna.

"Areef na gani fa ya sauke waccan matar a motarsa.." Cikin rashin fahimta Mom tace

"Wace matar kenan?"

"Wacce mata ce a cikin gidan nan bayan Sa'a..?" Aunt Makiyy ta faɗa tana kallan Mom ɗin.

"Bari mana Makiyy, ki bari mana don Allah.."

"Ke wallahi ba wasa nake ba. Ni abin ne ya ɗaure min kai wallahi, kina ina har haka ke faruwa cikin gidan nan? Wace irin sakewa ki ka yi har hakan ke faruwa? Drivernta ya zama ko kuwa me ne?" Jinjina kai Mom ta shiga yi cike da ɓacin rai. Shi Areef ɗin ne ba ɗan goyo ba, ba abun tace za ta masa faɗa ba yanzun nan ya tubure mata ya yi fushi da ita, abin da ba ta so kenan. Se dai koma dai mene ne dole ne ta masa magana tun kafin Mommah ɗin ta sake zaƙewa, duk da dai shi ke biye mata.

"Zan san abin yi.." Mom ta faɗa tana soma tafiya. Da sauri Aunt Makiyy ta miƙe tana faɗin

"Wane za ki san abin yi? Ai yanzu nake so mu je mu ɗauki mataki, babu wani za a san abin yi.." Komawa Mom ta yi ta zauna ta yi murmushin yaƙe kafin tace

"Ke daɗina da ke gaggawa. Halin Areef ne ba ki sani ba? Yanzu muna cewa za mu masa faɗa ko kuma mu ci mata mutunci fushin kanmu ze koma. Saboda haka ki bari kamar yanda na faɗa ɗin zan san abin yi.."

"Shi kenan ai. Koma dai me ya faru ki fara tuhumar kanki.." Aunt ɗin ta faɗa tana miƙewa dan ita kam ta fusata ba ƙarya.


... Cikin wata doguwar riga me kyau ta shirya, rigar da ta matuƙar amsarta. Ta ɗauki ƙaramin mayafin rigar ta yi rolling, kasancewar rigar me ɗan faɗi ce ya sanya ta saketa sosai, ta kuma matuƙar yi mata kyau.

"Ka ga fa en matan Ammi.." Lulu ta faɗa tana dariya ƙasa_ƙasa.

"Allah kuwa ba na so.." Didi ta faɗa tana jefawa Lulun harara. Wata dariyar Lulu ta sake sheƙewa da ita sannan tace

"En mata ce mana tunda ki ka fara zance. Dan ma ban ce en matan Kaseem ba.." Juyawa Didi ta yi tana neman abin da za ta iya jifar Didin da shi. Lura da hakan da Lulu ta yi ya sanyata miƙewa da gudu ta fice daga ɗakin tana dariya. Biyota Didin ta yi tana ta ciccin magani, ita kuwa Lulu tana zuwa ta faɗa jikin Ammi tana cigaba da dariya

"Tsokanar ce koh?" Ammi ta faɗa tana girgiza kai.

"Ammi dukanta ta yi koh?" Little da ke gefen Ammi ya faɗa yana kallan Lulu, se ta juya ta jefa masa harara daidai lokacin da Didi ta fito daga cikin ɗakin

"Awwwn Masha Allah.. ka ga en matana" Ammi ta faɗa tana murmushi. Dariya Lulu ta fashe da ita yanzun har da ƙyaƙyatawa, tana cigaba da dariyar kuma tace

"Ammi nima fa abin da nace mata kenan take jin haushina. Toh ai gashi nan Ammin ta faɗa miki da kanta.." ta ƙare maganar tana kallan Didi. Tura baki Didi ta yi tana neman waje ta zauna.

"Ammi ki ma Lulu magana Allah.."

"Ai dama na san tsokanarta ki ke yi ja'ira. Yoh ni ko yau Allah ya kawo miki miji ai aurar da ke zan yi na huta.."

"Chaaɓɓ.." Lulu ta faɗa tana jinjina kai lokaci ɗaya tana dena dariyar. Se a lokacin sannan Didi ta yi dariya har da yi mata gwalo.

"Tashi ki je Afrah an bar ɗan mutane na jira. Ki tsaya ki nutsu Afrah.. kin san dai Abbanki na dab da yanke hukunci, dan ina me tabbatar miki da cewar idan dai har ki ka amince toh a cikin satin nan za a iya bashi damar turo magabatansa." Ɗan numfashi Didi ta ja ba tare da tace komai ba se miƙewa da ta yi ta ja hannun Little suka fice daga ɗakin jikinta a sanyaye. Sallamar da aka yi a bakin ƙofa ne ya sanya su amsawa dukansu. Da sauri Lulu ta miƙe tana faɗin

"Oyoyo Masoyiya.." ta faɗa tana rungumeta.

"Yawwah.." Fatima ta faɗa tana ƙarasowa cikin parlourn. Gaisawa suka yi da Ammi. Da yake akwai sabo a tsakaninsu ya sa suka ɗan taɓa hira, daga baya Ammin ta miƙe. Da sauri Fatima tace

"Ammi wajenki na zo.." komawa Ammi ta yi ta zauna tana faɗin

"Toh ina jin ki.."

"Dama gobe Umma ce za ta aike ni, shi ne tace in miki magana se Afaaf ta raka ni.."

"Gobe..?" Ammi ta tambaya.

"Ehh Ammi.." Ajiyar zuciya Ammi ta sauke kafin tace

"Amma gobe ai akwai makaranta, me ze hana ku bari se Alhamis ko Juma'a?"

"Ammi ai saƙo ne za a karɓo shi ya sa." Shiru Ammi ta yi na tsawon sakanni sannan tace

"Toh shi kenan Allah ya nuna mana.."

"Ameen Ammi an gode.."

"Kun sanarwa da Ya Sayyadin naku?" Kafin Fatima tace komai Lulu ta yi caraf tace

"Ehh Ammi fa mun faɗa masa.."

"Toh shi kenan, babu damuwa.."

"Mun gode Ammi.." daga haka Ammin ta miƙe ta bar parlourn. Neman waje Lulu ta yi ta zauna, Fatima ta jefa mata harara tace

"Ta ya ya ma za ki ce mun faɗa masa? Bayan na yi na yi da ke mu je mu faɗa masa kin ƙi? Da kin bari nace ba mu faɗa ba ai na san Ammi za ta tura Didi ta faɗa masa.." Tsaki Lulu ta ja kafin tace

"Ke rabu da shi dallah. Sanin kanki ne dai ba ya karɓar uzuri idan ba daga wajen me yin uzurin ba. Da ki ka je faɗa masa ba har da ni ki ka ce ba? Amma me yace? Wai in zo da kaina. Toh ni a faɗan da Ammi da Abba suka min cewa kawai

2 Comments On A JINI TAKE (IZZATA) CHAPTER 1
avatar
abubakar-sunusi

10 months ago

Reply

avatar
abubakar-sunusi

10 months ago

Reply

Please Login or Register in order to submit comment