Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

👸 QUE*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION🖊*
( _Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers_)






👸🏻👸🏻 *QUEEN FARHA* 👸🏻👸🏻
👸🏻 *Matar Sarki* 👸🏻





Writing
And
Story



*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
® *FAUZAH*




*Wattpad👉🏻* *realfauzahtasiu*



MARUBUCIYAR

JAGORAN RAYUWA
AMINIYA KO KISHIYA
FADIMATUL ZAHRAH
HABIBULLAH


WANNAN SHAFI NA MUSAMMAN NE DOMIN SADAUKARWA NE GA QUNGIYARMU MAI ALBARKA TA BRILLIANT WRITTERS ASSO..., WADDA TA QUNSHI FASIHAN MARUBUTA DA AKE ALFAHARI DASU A DUNIYAR ONLINE WRITTEN ALLAH YA QARA DAUKAKA MU YA RABAMU DA SHARRIN MAQIYA DA MAHASSADA AYI DAMU YAU AYI DAMU GOBE HAR JIBIN GATA YAZAM MUNE DAI AKE GANI.



SADAUKARWA GAREKU


HALIMATUS SA'ADIYYA MUHAMMAD (COPPER DAN BAUTAR MATA)

JAMILA MUSA (KWARATA)

SURAYYAHMS ( AHUMAGGAH)

ASMEENAT ZEEYAN (RAYUWAR BANUJJAH)

REAL OGANNIYYAH

SISTER LEEMART

MARYAM (YAR BUZUWA)


AND OTHERS



INA JINJINA MUKU DAMIN KUMA KUNA JINJINA MIN



AUNTY BILKISU (MAMAN ABBA KD)

AISHA GAIDAM

FALTEX FARHANA

MMN NABIL

UMMUH SAFWAN

NAEEMA BALA

HAJJARAH HUSSAIN

HAJJARA IBRAHIM &

KAJURU


*BISMILLAHIR RAHAMANUR RAHIM*

aside�1⃣



Yarinya ce qarama da bazata wucce 14 zuwa 15 ba tana tafe cikin uniform din islamiyyar ta da yasha guga tana tafe tana yauqi tana yatsina kamar wata macijiya “Farha! Farha!! Ke Farhana wai ba mgn ake miki bane kika share mutane” tsayawa tayi cak daidai wani dan gulbi da ruwan damuna ya tare a gefan titin ta kebe baki zatayi bala'i kenan wata zindimemiyar mota qirar Jeep tazo giftawa kawai bisa tsautsayi taji ruwa facal a jikinta saurin kallon jikinta tayi tare da cewa “ kam ubancan wlh yau zanyi rotse dagowar da zatayi taga motar tayo ribas a hankali, wawurar wani dutsi tayi ta wulwula kawai sai saman glass din motar ji kake tatsatsaarr da sauri mutun biyu da suke cikin motar suka fito kasancewar gurin babu yalwar mutane sosai yabawa dayan ma damar fitowa daga motar ya tsaya jikinta ya zuba musu ido.


Daya cikin mutanen ta sanya hanu ta cukuma tana surfa bala'i tana cewa“ku wadannan irin unliterers ne kuna tafiya kamar makafi bakusan haqqin hanyaba balle me tafi a qasa daqiqan banza daqiqan wofi wannan ma ai zalinci ne yanzu kunjamin yauma sainayi wankin uniform bayan...” saukar mari taji a kuncinta tayi saurin dafe gurin tare da cewa“Allah ya isana mugu azzalumi kuma wlh bazan fasa fadaba ba ku jahilai ne baku da ilimi Kona sisi” sake daga hanu yayi zai yarfa mata mari can a bayansu taji ance “Na'im karka qara mace ce fah kuma yarinya qarama kuzo mu tafi” juyawa tayi ta kalleshi gabanta taji ya fadi amma saboda bala'in da yake cinta haka ta taka tana daga hijjab dinta saboda tsoron kada ya manne mata a jiki ta qarasa gabansa ta qare masa kallo a-z sannan tayi tsaki tace.


“Aikin banza waishi mutumin kirki daka kyaleshi ya kasheni ai yagani in zai sha kaima din baka wucce in ketaka ba balle shi da qilama taimakonsa kayi ka rage masa hanya dubeka kamar aljani ka wani tara Suma a kanka kayi mata shampoo wait dole saika zama India to ba India ba niko bayahude zaka zama Farha bata da kaice dalla malam kauce na wucce” kaucewa yayi ya bata hanya saboda tsananin mamakin jarumtar yarinyar tunda yake a cikin rayuwarsa babu namijin daya taba yimasa rabin wannan tsagerancin balle mace macen ma yarinya qarama irin wannan jaririyar yar.


Damqe hanunsa yayi ya bita da kallo harta shiga wata kwana ya daki saman motar yace “like this girl” wanda ya ambata da Na'im dazu shine ya rusuna yace “ Allah yaja zamaninka daka barmu mun canza mata halitta ai irin wadannan yaran basuda tarbiyya ko kadan basusan mudin suwaye ba da mun gwada mata qarfin iko mun gwada mata bata wucce kucakar baiwa ba a sashinka da ta shiga hankal....”



Daga masa hanu yashi ya dubi na gefensa yace cikin murya mai nuna isa da qarfin iko “Shahid kaje ka nemo mana inda gonarmu take tabbas zamuyi shuka a gurinnan” dagowa Shahid yayi da mamaki zaiyi mgn ya daga masa hanu tare da nuna masa hanya, rusunnawa yayi yace“angama yamai Bauchi da jama'ar cikinta dolene nayi biyayya wa umarninku” daidai lkcn wata motar tazo suka shiga suka tafi shikuma Shahid yabi bayan sauran yan matan guda biyu saida yaga zasu shiga wani gida ya tsayar dasu suka juyo a tsorace babu alamun rahama a fuskarsa yace “wannan mara kunyar yarinyar nakeson sanin wacece ita kuma inane gdansu?”


Kallon juna sukayi duk a firgice suke dayarce tayi qarfin halin cewa“qanwarmu ce sunanta Farhanah nan...uhm nan shine gdanmu amma don Allah ka taimakemu ka rufa mana asiri kada ka fadawa babanmu wlh duka zaiyi mana Farha ta saba jamana duka ka tausaya mana don darajar wannan watan da muke ciki” ganin yanda suka rikice dinne yasashi juyawa ya tari sahu ya nufi inda zai isar da saqonsa zuciyarsa cike da takaici tare da tambayar kansa meyene dakilin da yasa Mai martaba HAFEEZ yasashi bin diddigin yarinyar a zuciyarsa yace “Allah yasa dai ba wani makircin zai shirya mata ba saboda yasan ta tabowa kanta bala'i duk da a rashin sani tayi itama qila da tasan wayeshi da batayi masa ba”



Tana shiga gdan ta jefar da hijjab dinta ta saka kuka Ummah da Mama ne suka fito daga dakin da suke kallo sukace “To yau kuma wa kika tabo ya tabaki uwar rigimammu” jikin Ummah ta fada tace “wasu yan iska ne suka batamin uniform dina kuma wlh bazan wanke ba ke zake wanke ko Mama ai dama saida nace bazanje ba kuka dage sai naje yanzu ga irinta nan” tsaki Mama taja tace “kwaji dashi wlh” shigowar sauran yammatan ne yasasu juyawa suka kalleta dayar tana shigowa ta jefar da jakarta ta nufi bandaki da gudu dayar kuma ta zube tana fadin “yau mun shiga ukun mu a gidannan Allah ya isa tsakanin mu dake Farha ke kullum saikin janyowa mutane bala'i yanzu gashi har biyomu daya yayi yana tambayar mu sunanki da gdanku na tabbata Baffa zasu fadawa shi kuma ya kamamu ya zanemu bamuji ba bamu gani ba”


“Uhm ai dama na sani wlh yau bazata jamuku duka ba Anass zai dawo shi zansa yaci qaniyarta tunda ita bata da kunya” Rahina ce ta fito daga bandaki ta ajiye butar ta koma gefe tayi tagumi tana zubar da hawaye tace “ni takaicina ma Rahmah Farha batasan suwaye tayiwa rashin kunya ba wlh motar data fasawa glass number Emir palace ce da ita ni addu'a ta Allah yasa ba dan sarki bane yasa a koremu daga garin nan Baffa baijiba bai gani ba” murguda mata baki tayi tace “idan dan sarkin ne ya tsireni da tsinken tsire banza matsoraciya kawai toni ko sarkin ubansa zan...” faff taji an zabga mata mari tare da rufeta da duka ehu ta rinqayi tana neman taimako kowa daki ya shige daki ya qyaleta saida yayi mata tilis tayi laqwas sannan yace “duk abinda kikayi ina kallonki to wlh tallahi duk abinda ya faru dake ke kikajawa kanki tunda kika tabo gidan sarautar garin nan dama wani kika taba da sauqi amma fah Mai martaba HAFEEZ da kansa kikayiwa rashin kunya harda zaginsa to ki jirayi sakamakonki kuma saina sanar da Baffa komai”


Qanqameshi tayi cikin kuka tace“don Allah don Allah Yaya Kada ka fada masa hakama na daku nayi laushi wlh na daina har abada bazan qaraba tureta yayi yayi ficewarsa yana fita ta saka sabon kuka tana cewa“kuma wlh wayo nayi maka bazan fasaba gobema idan naganshi saina jefeshi shege azzalumi kawai wayace ya batamin kayan makarantana da shegiyar motarsa...” saurin yin shiru tayi ganin dawowar Yaya Anass din ta kama goge fuska kallonta yayi yace“ me kikace?" Kada kanta tayi tace “wlh godiya nayi maka ba zaginka nayi ba” kwafa yayi ya shige cikin gdan.



Washe gari da wuri ta tafi makarantar yau batabi ta hanyar da sukabi jiyaba ta qofar fada tabi ita da qawarta Binta suna tafe suna hira hira fada fada saboda Farha bata daukar raini ko kadan yanzun ma nasiha Binta take mata akan abinda tayi jiya amma ta hauta da masifa dole tayi shiru daidai makarantarsu ta hangi jerin gwanon motocin Emir palace din sun fito daga gdan sarki tsaki tayi tace“ga shegunnan sun fito nifa Allah na tsanesu” tana fadin haka ta shige ajinsu, tana tsaye gaban malamin nasu tana bada hadda saida ta gama tsaf sannan ta koma ta zauna zamanta kenan wani mutum ya shigo da sauri ya qarasa gaban malamin nasu batasan me suka tattauna ba taji malam Nuhu yace “Farhana Usman Giyyade kije ana nemanki a waje” banza tayi dashi kamar bataji abinda yake fadaba, saida ya kuma magantuwa yace “Farha kefa nakewa mgn ko baki jinane?" Miqewa tayi tana qunquni ta fita mutumin yana gaba tana biye dashi a baya har suka fito tsayawa tayi turus gaban wata zundumemiyar mota qirar Annaconder ta jima a tsaye kafin taga anyi qasa da glass din baya wani mutumin sabanin na dazu ya leqo yace“zaki iya amsa kiran Mai martaba?”


Yanda yayi mgnr da sigar tambaya yasata dariya ta bude baki zatayi mgn sai kuma ta tuna da jibgar da tasha jiya gurin Yaya Anas takawa tayi a hankali harta isa daf da qofar motar ta tsaya bude mata akayi da zunmar ta shiga taja da baya da sauri tace “aa kunga ku dakata ni banason wayon satar mutane saboda wani kinibibi harda wani budemin mota yo wannan motar da tsautsayi na shigeta aisai buzuna” matsawa tayi ta leqa idonta yayi arba da wanda yake cikin motar jikinta ne ya dauki tsima ganinsa zaune a hakimce ya dora qafa daya kan daya yasha rawani irin nasu na sarakai mai kunnuwa biyu shaidar dai da gaske sarki ne qara kallonsa tayi tanaso ta ganeshi kamar na jiyannan wanda yasa qananan kaya yace a daina marinta amma kuma kamar bashi ba miqewa tayi da sauri tayi qasa da kanta tace “am..en gani” tunda tazo gurin ya zuba mata ido yana mamakin fitsara da rashin tsoron yarinyar ji yayi tana qara birgeshi da shiga ransa ya rasa meyasa tun jiyan daya ganta ya kasa samun nutsuwar zuciya.


Daga mata hanu yayi alamar jinjinawa ya dubi wani cikin mutanen dake motar ya matsar da kunnensa daidai inda yake dagowa yayi yace “angama sarkin duniya" dubanta dogarin yayi yace “kina iya tafiya” tabe baki tayi ta kalleshi tace “hmn Allah ya kyauta mutum ko zafi bayaji ya wani nade fuskarsa” dogarin ne ya daka mata tsawa yace“ahir yarinya saita bakinki kafin fushin Mai martaba ya sauka akanki” daga masa hanu yayi ta murguda baki tayi gaba tana harararsa” duk da fuskarsa a rufe take amma saida kumatunsa suka lotsa tsiwar yarinyar tana burgeshi kowa tsoronsa yakeyi hatta matarsa ta aure tana tsoronsa bata iya fada masa komai amma ita babu ruwanta duk abinda taga dama fada masa takeyi daga jiya zuwa yau wani nishadi yakeji saboda a rayuwarsa yanason ya samu wanda zai rinqa sanyashi dariya da nishadi kuma ya lura da gaske yarinyar comedians ce.


Labewa tayi har saida taga tashin motar sannan ta koma ciki ta zauna gabanta naci gaba da faduwa “to waima meye dalilin dayasa yazo ya tura a kirata kuma ma wayene shine kodai da gaske shine dan sarki Hambali wanda bayan mutuwar sarkin ya zama sarki? Kai bashi bane ba da shine yanda ake fadar izzarsa da qarfin ikonsa aida yanzu yasa anyi gutsu² da namanta, tabe baki tayi tace “Hmn sudai suka sani saji da gulmarsu munafukai kawai, da aka tashesu ma su biyu suka tafi suna tafe tana bawa Binta labarin irin tsagerancin da tayi mawa mutumin da ya watsa mata ruwan kwata yau tayi dariya tace “kuma kinsan wani abu Binta har rawani yakeyi Ina tunanin dai wani mai muqamin sarautar ne tunda yanzu dama ance fadar ta zama ta yara sune suke mulkarta ance shima sarkin ba wani babba bane bai wucce 37 year's ba” murmushi Binta tayi tace “kinsan babar su Ammi tana aiki a gdan sarautar wlh ance bashida kirki ko kadan gashi dajin kan tsiya da izzah baya karbar uzuri sannan itama matarsa batada mutunci amma mugun tsoronsa takeji bata iya motsin kirki idan yana gdan shekararsu shida da aure amma ko batan wata matarsa Amna bata tabayi kum ance matsalar a jikinsa take kinsan sarakunan nan da kauce hanya wai yanzu yarinya qarama akace ya aura wadda bata fara al'ada ba kuma wai har suffofin yarinyar an fada masa ya zana hotonta yananan qato a turakarsa manyan bayinsa da suke shiga bangaransa sune sukasan wannan sirrin itama maman Ammi jitayi suna hirar ta labe”



Dariya Farha tayi cike da mugunta tace “shege Allah yasa kada ya samu Allah yasa ranar da zai ganta ita kuma ta mutu basai muga ta tsiya ba” dariya itama Binta tayi tace“wlh Farha ke muguwa ce” murmushi tayi tare dayin qwafa tace “nifah na tsani sarkin nan duk da bansanshi ba saboda rashin mutuncinsa yayi tambari a garinnan.









*UMMUH HAIRAN CE...*


*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION🖊*
( _Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers_)






👸🏻👸🏻 *QUEEN FARHA* 👸🏻👸🏻
👸🏻 *Matar Sarki* 👸🏻





Writing
And
Story



*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
® *FAUZAH*




*Wattpad👉🏻* *realfauzah*




🅿2⃣



Dariya sosai takeyi har suka gifta qofar fadar sannan suka rabu kowacce ta nufi gdansu da sallamarta ta shiga gdan tana qwalawa iyayenta Kira fadi take “Ummah Mamah albishirinku yaudai banyi tsokana ba nifa dama na fada muku yarannan Rahmah da Rahina su daina bina sune karfofi idan muka fita dasu sai sunsa na raba hali a titi amma kuma sheg...” hadiye mgnr tayi muqut saboda ganin fitowar mutumin da suka rabu dazu dashi a qofar makarantarsu da Baffanta daga turakar Baffan tsugunawa tayi tana gaida Baffa ya amsa da cewa “ uwata sarkin rikici duniyama tsoronki take ya karatun ” sosa hancinta tayi tana harararsa tace“to qlau amma wlh dukan da Yaya Anass yayimin jiya ya shigeni kuma bazan yafe...” sake hadiye mgnr tayi saboda kallon da taga Baffa yana watsa mata ta miqe tana dariya tace.



“Kayy Baffa irin wannan harara haka muje na rakaka ka raka baqon naka amma Allah Baffa ya fiye shisshigi da shiga sharo ba shanu nidai garama mutum ya fita daga rayuwata idan ba hakaba nidai kowa yasan ni aljana ce ehee” ba Baffa hatta Mai martaba HAFEEZ saida ya dara duka Baffan yakai mata yace “kajimin ja'irar yarinya wato dole sai kin qarasa shirmenki ko zaki bacemin daganan kosai na canza miki kamanni” daki ta shige tana turo baki binta yayi da ido harta shige dakin yanajin wata muguwar faduwar gaba yarinya qarama amma tana neman hana zuciyarsa kwanciyar hankali.



Suna fita sukayi sallama daidai lkcn driven sa da excourt dinsa suka iso suka buda masa ya shiga suka tafi. Juyawa Baffa yayi ya shiga gdan ya fara dokawa matansa kira fitowa sukayi da sauri suka isa inda mijin nasu yake, kujera yaja yar tsuguno ya zauna yana sharce gumi yace “akwai matsala Hajara da Inno tabbas akwai matsala FARHANAH ta debo ruwan dafa kanta da babu mai hanashi dafata sai Allah Mai martaba sarki Hafeez yazomin da wani rikitaccen al'amari wai auran FARHA yake nema kuma cikin sati daya tak” dagowa sukayi dukkansu sukace “Farha fah kace Baffan yara wannan shashashar yarinyar zaice yanason aure haba Baffa to kai kuma me kace masa?” qara share zufa yayi yace “to me kuke tunanin zance mawa wannan taqadirin isasshen sarkin namu ya fahimce ni na fada masa Farha yarinya ce qarama kuma quruciyarta da gyara tanada rawar kai yace shi yaji yagani kuma yanaso shima rainonta zaiyi harta hada hankalinta duk da haka na kuma nuna masa rashin amincewata qarshe sai yacemin nayi hqr kawai auransa da Farha rubutaccen Al'amari ne saboda haka nayi fatan alkhairi kawai”



Shiru gurin ya dauka cike da mamaki a fuskar kowanne Ummah ce tace “nidai gsky wannan lamari ban amince dashi ba dama Rahmah yace ko Rahina sunfi wannan dukan taran hankali amma ace wai Farha ce matar sarki Hafeez gsky akwai matsala babba saboda ni nafi tunanin auran ma na manufa ne badon Allah zaayishi ba” Mama ce ta cafe da cewa “ to yanzu maye mafita kunsan dai tunda ya tako qafa da qafa yazo gdannan bai dauki abin da wasa ba kuma babu abinda zai fasar da aurannan sabida haka inaga mafita ya kamata mu naima" Baffa ne ya dago yace “to wacce mafita Inno ai kawai haquri zamuyi mu zubawa sarautar Allah ido tunda bamu isa mu kaucewa umarnin sarki ba kodan tsira da mutuncin mu ba abune me wahala a gurinsa ba ya tozarta mutum shiyasa tun mutuwar mahaifinsa Sarki Hambali na ajiye rawani na na shugaban malaman fada saboda shi amma duk da haka ban tsira daga kaidinsa ba saida mulkinsa da ikonsa ya ratso ta gdana bisa jagorancin fitinanniyar yarinyar nan, na tabbata da bata taboshi ba bazai san da zamana ba ni bammasan tsautsayin daya hadasu ba nasan Farhanah ta zama gawa ta gama”


Fitowarta daga dakin ce tasashi yin shiru ta kallesu tare da zama kusa da mahaifin nata ta dora kanta a cinyarsa a sanyaye tace “nifah banice na fara tsokanarsa ba shine suka batamin uniform dina da ruwan gulbi nikuma na fasa musu glass din motarsu kuma wlh bazan yafeba saina qara fasa mishi na wata motar tunda ya bata muku rai” shafa kanta yayi cikin tausayinta yace “da kina yafiya da kinfi haka Farha yanzu gashi inda rashin yafiyarki yakaiki Mai martaba zai kuleki yazo neman auranki a matsayin mata ta sunnah ba kuyanga ba ba baiwa ba kuma ya bada waadin kwana bakwai zaa daura auranki dashi a kaiki gdansa kinga sai kita ramawa da hujjah ko?”


Yana fadin haka ya tashi ya fice ta bisa da kallo saida yakai qofar gdan ta kurma ihu tace “na rantse da Allah zaa mutu har liman idanba idan ya kuskura ya aureni ba yasin saina zubar masa da mutunci saina mayar dashi kamar bawa a gdan sarautar Allah ya isana ma da yace yanasona zai kuleni mugu azzalumi macuci mema zaiyi dani yar qaramar yarinyata dani yasin wlh Allah sai nayi masa addu'a ya makance ya kuturce ya zama gurgu kuma ma Insha Allahu sai anyi masa juyin mulki muga ta tsiya yehhhh mugu mugu sarki Hafeez...”


Ganin tana neman tara musu jama'a yasa Mama rufe mata baki tace “waike dan uwarki bakida hankali ne wannan ihun da kikeyi shine zaisa ya fasa abinda yayi niyyah ko me sakarya kawai duk sa'anninki sun girma sunyi hankali amma bandake” turo baki tayi gaba tana qaqalo qwallah tace “to ba kune kuke gulmata ba wlh idan kuka sake ma wannan wawan dan sarkin ya aureni Allah saina daina kwana a gdannan kuma na daina cin abincin gdannan sannan idan naga dama na gudu daga garinnnan kowa ma ya huta” miqewa Mama tayi saboda bata jure haukan yar tata.




*WACECE FARHA*


Farhanah Usman Giyyade shine asalin sunanta Mahaifinta malam Usman Giyyade asalinsa dan Usulin Bauchi ne cikin qaramar hukumar Giyyade fulani ne na asali masu kiwon shanu mahaifin mallam Usman yayansa uku Baffa Jafar Baffa Balaji da Baffa Shehu wato mahaifinsu Farhanah shine qarami a jadawalin haihuwar gdansu shiyasa daya tasa maimakon kiwo da suka taso sunayi shi sai aka dorashi akan karatun Muhammadiyyah yawon karatunsa ya kawoshi cikin birnin Bauchi dake anan arzikinsa yake lkcn ya auri Ummah wato Inno harda yaronsu daya Anas.


Ya samu karbuwa gurin tsohon Sarki mahaifin sarki Hafeez wato sarki Hambali saboda dattako da kamalarsa yasa ya bashi matsayi mai girma na shugaban matasan malaman fada tafi tafi harya kasance shine shugaban malamai kuma shine limamin fada, yaransu biyu da Ummah Inno ya auro Fulanin Adamawa Hajjara wato Mama lkcn da aka kawota Bauchi ko Hausa bataji sai fullanci zamansu gwanin dadi da uwar gidanta komai tare sukeyi bazaka taba ganin daya babu daya ba Anass da Mussah sun tasa sannan Allah ya bawa Hajjara qaruwar da namiji Yusuf sai bayan shekaru biyu Ummah ta haifi Rahmah sannan Mama ta haifi Farhanah tun daganan Mama Hajjara bata qara aihuwa ba baby dadewa Ummah ta haifi Rahina shikenan haihuwa ta tsaya cak a gdan.



Kyau da wayon Farha da kuma shagwabarta shine yasa ta zama kamar itace qarama a gdan dayawan mutane suna dauka Rahina yayarta ce saboda kowa komai Farha saboda Allah yabata farin jinin mutane dayawan mutane sunfi kiranta da me kyau ko a makarantar bokonsu sai kace Pretty sannan zaa gane Farha kake nema, yanzu haka tanada shekara sha biyar kuma tana S S 2 a secondary school duk da bambadanci da fadan Farha sosai malamanta suke sonta saboda tana kwashewa a aji hakan yasa takejin kanta kirarinta kenan Duniya uwar rikici shikuma Baffan ta yace duniyarma tsoronki

Please Login or Register in order to submit comment