Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bakomi ay"
haka baba isma'il ya juya ya fara tafiya yana cewa "nagode sosai to haruna AllAh jiqan mlm musa" (mahainsa)
"aminnn baba"
ganin da haruna yai heenduh na shirin tafiya tabi bayan babanta yasashi saurin cewa "ah hm gimbiyar kyawawan matan duniya ko zama baki ba da kika zo kinata tsayuwa fa?
wata q'atuwar harara heendu ta sakar masa daman tun zuwanta wajen dud take a tsarge sakamakon wannan shegunayen masa'idawan idanuwa na abokan haru din na nan majalissar sa da sukaita binta dashi uwa mayu, dan haka cikin mafisar sauke hushinta akan haruna din ta sake watsa masa fararan tas qwayar idanun tan nan tace "anqi a zauna d'in, koko zama ya kawo ni ne bare kace in zauna cikin qatti ko ance maka ni yar iska ce?,, da sauri haruna ya kama bakinsa da hannun sa guda na haggu yace "tooo afuwan gimbiyar mata hjy heenduh abin baikai haka ba wlh ba haka niki nufi ba ni sam dam wlh, nasan tsayuwar ne babu dadi ay kuma shiyasa kikaji nace hakan"
wata sabuwar hararar ta sake sakar masa bayan ta saki qugunta taja tsoki tace"wannan kuma ya rage ya ruwanka mlm"
daga haka bata sake furta masa komi ba ta bi bayan babanta daya fara tafiya a hankula sabida taka qafar.
tana barin wajen kuwa abokan haru suka fasa ihu da sowa,,, isa kabeer yace "kai billaheel azeem ajin yarinyar nan yaimun a duka rayuwa fa sosai" musa dake gefensa yace "hm kaima ke fad'i anaji ay"!
nan kowa yaita tofa nasa tawun a wajen kuwa.
zama haru yayi yace "to yabon nata ya isa haka 'yan karere bansan iskanci fa kun zauna sai mgnr matata kuke"
isa kabeer ya doki kafadansa yace "kai d'an iska matarka da ubanwa ye ya baka?,,,, ko damuwa ma batai dakai ba ka zauna kanata kyarmar jiki kan mace" haris da sai yanzun yasake bude bakimsa yayi mgn sakamakon wayar daya gamayi da budurwarsa yace "kai ku qyalesa dan rawar jiki ga mace kamar henndu namiji zaiyi fiye da hakam ma, dan kaf samarin anguwar nan babu wanda baiyi yaqi wajen waccen zazzafar babyn ba ya gaji ya daina badan yaso ba, kai bari in taqaice maka ciki har dani wlh amman ganin danai babu sarki sai Allah dan yarinyar tanaji da kyaun ta bata sauraran kowa shiyasa na haqura na sami tema ta, danna lura qilan sai manyan 'ya'yan manyan mutane take saurara irinsu musaddiq dan gidn Alhj musa kaita".
fashewa matasan suka karayi da dariya suna cewa "gaskia ka bada maza fa hakan yawa ne fa, wayace maka ana gudu kan neman kalar su heenduh beauty?
gskia haru ka qara wuta kada ka sake ka rabu da waccen hurul aini din har sai inda qarfinka ya qare" dariyar jin dadi haru yayi harda shaga dan dogon gemunsa daya aje yana cewa "Yawwa abokaina ai sainaga abunda ya turewa buzu nadi,
Hari's cikin dariyar mugunta yace "ai kam dai ina mai tabbatar maka abokina babu abunda zai turewa buzu nadin nan nasa face wahala wacce kake sa kanka a ciki akan heenduh beauty wlh, kaje kuma gata ga kana nn ay, zakaga wulaqanci kuwa inda har bata gayyaceka ba kk shirin sa mata kai a rayuwar ta, hmmn koda yake hausawa sunyi gskia da sukace mai rabon shan duka bayajin kwa6a sai yasha tukun, dan haka kaje insha maka Allahumma kuwa munanan zaka zo bamu lanarin ketaka da yarinyar can zatayi, zanga hmm sarewar ka ranar" duka haru yakai masa gamida cewa "mugu dan baqinciki sainayi power kuwa a gunta saidai baqin ciki ya kasheka,,, isa kabeer yace "wlh kuwa abokina saidai baqin ciki nasa fa ya kashen sa, yaci gaba da cewar guys
wai ashe har doctor khaleepa ya dawo? haru yace "eh man ya dawo wajen sati biyu knn ma" musa yace "kai guy din ai yayi wlh akwai harkar girma wacceb babu qaranta a cikinta sai dai kuma shegen fadin ran masifa ne dashi,,, dariya suka qara kwasa a wajen haru yace "mazaje mazaje mazajen kenan ay, danni wlh guy din takunsa yana burgeni kai kominsa gaba daya burgeni yake over2, cikin tsokana hari's yace ''inda yana kam burgeka mizai hana kaje ka basa shawarar ya auri Sister dinsa heendu dan wlh dud duniyar nan in maka na babban mahaukaci to sunyi masifar dacewa da juna bil haqqi nike fad'a maka hakan haru"
Isa yace "bala'e knn, kai km yanzun kana nema dauko dala ba gammo knn, alhj mukhtar din zai bari hakan ta faru yanda ya tsani qanen nan nasa dama talakawa duka tab? ai kama daina wanga zance d'an saurayin " kowa na wajen yace "wannan gskia ne isa qilan in za'ayi auran ma kuwa saidai in alhj mukhtar bai duniyar nan anje can qasan qasa".
haru yace "ku rabu da d'an isakan mai mummunan fata insha Allah heenduh beauty tawa ce" dariya kawai haris yayi a haka matasan sukaci gaba da firar su kan dai..
heendu kuwa tana iske babanta ta kama hannunsa sukaci gaba da tafiya mutane a hanya sai yiwa baba isma'il sannun ciwon nasa suke har suka isa gidan baba yawale kuwa.
nan suka iskesa yana sallatul tazbihi.
zama sukai nan kan buzunsa baba isma'il cikin maganarsa ta yanda bazai takura baba yawale dake halin sallar ba ya dubi heenduh yace
"heenduh gskia kam haruna ya....


By
*Xexen Fasaha*
[1/17, 3:10 PM] Xainab Documen: πŸ‘πŸ‘
πŸ₯‘πŸ₯‘
πŸ‘πŸ‘
*DA SAURAN KALLO !!!*

Story and writing
by
Xayyneb πŸ’€πŸ’€

Fasaha online writers f. o.w.

*🌳imparting valuable knowledge and entartaiment is our concern*🌳.

~dedicated to my mom Sadeeq hawwas~

-https://www.facebook.com/Fasaha-Online-Writes-751775151851852/?referrer=whatsapp.

πŸ‘πŸ₯‘πŸ‘
πŸ…Ώ2⃣2⃣.
*Z* ama sukai nan kan buzunsa.
baba isma'il cikin maganarsa yanda bazai takura baba yawale dake halin sallar ba ya dubi heenduh yace
"heenduh gskia kam haruna yaron kirkine dubi fa dan AllAh iriyar alheran magunguna daya bamu haka d yawa batareda ya kar6i ko sule namu ba"
baba isma'il yayi maganar yana mai cigaba da duba sunan magunguna, itako heenduh ta6e 'yan red lips d'inta tayi tace"baba dan ya bamu wannan 'yan magunguna din, shi yaga dama ya bayar ai ba wai dole mukai masa ba, to dan haka ni banga abin a jinjina masa ba inda dai shi yaga daman badawa ba kuma uzzurasa mukai ba ko babana?"
d'agowa baba isma'il yayi ya dubeta ya girgiza kansa kawai yayi murmushi,
sam shikam wnn halayen n heenduh wani zubin yakan kasa fassara mata su da awane matsayi ta dauki kanta?, yanaga heenduh data fito tsatson masu arziq'ina iyaye to daba haka ba, shikam ya godewa Allah dabai basa mahaukatan kud'i ba da zaisa 'yarsa tana jin ita watace wataqil har hakan yasata yaga jama'ar annabi danya kula diyar tasa akwai son taq'ama kalar ta 'ya'yan manya na masu dashi, banda haka har yausher wanda yai maka abun arziq'i ita a nufinta abun yayi qanqanta da agode masa knn koko?, murmushi ya sakeyi yace a ransa ''heenduh wannan halin dai naki ba nawa bane bana mamanki bane heenduh,, hmm rigimammiya ta, yarinta ne kawai ke d'awainiya dake nasan wataran zaki yi hnkali ki daina dud randa kikaje dakin mijinki zaman aure har kika fara hayyafa,
ina roqon Allah daya bani qarfin gwiwar ciyar daku da tufatar daku batareda gajiyawa ba har na gaza ya rabbu nakaiga sarewa ba amimn, hmmm rayuwa knn, lokacin daya tuno su baffa da inno da kuma abubuwan da sukaita faruwa na lokuttan farinciki da iyayensa da yayansa mukhtar amman yanzun gashi yazamo kmr ba aiba sam, Allah ya kawo mana qarshen abin. "aminn babana" cewar heenduh baisan addu'ar tasa ta fito fili ba.
sauke qarfaffan ajiyar zuciya yayi sannan ya dubeta heenduh yace "q'warai kuwa heenduh haruna ya cancanci godiya matuqa nidai a wajena, dan dayace kud'i zai kar6a da bansan yanda zanyi ba inda bani da isassu na siyan adadin yawan iya magungunan daya bani dan dud nayo siyayya da kud'in a kasuwa, duka duka a cikin aljihun nan nawa in q'ididdige kud'in ma zanyi sam bazasu gaza naira d'ari biyu da saba'en ba, to ki gayamun d'ari biyu da saba'en zata saimun maganin ne har haka kala shida fa heenduh na?
kan heenduh ta ce wani abun sai sukaji muryan baba yawale na furta cewa
"assha ya ilahi isma'il rauni kaji haka dayawa ne a q'afa?, juyowa baba isma'il yayi cikin q'ara sakin fuskarsa yace "wlh kuwa baba abinma yazo cikin sauq'i kuma, na fad'a rami mai kwata ne batareda na nasan dashi ba a wajen" baba yawale yace "ayya Allah kyauta gaba to" "amunn baba, daman munje dreesing ne nida heenduh ta raka ni to shine nace bari na daure na shigo na gaisheka daman naga ban shigo gaishen ka ba yau sammakon zuwa kasuwa saro kayan miyar da nayi" baba yawale yace "ai daka ma zaman ka isma'il dan ciwo ai ya kauda komi ko"
murmushi baba isma'il kawai yai baice komi ba,
baba yawale yakai dubansa ga heenduh dake 6oyewa bayan babanta dan tasan tsiyar data zo ta shuka ma baba yawale din d'azun bawai mntawa yayi ba, dan hk ya d'aga carbinsa kamar gaske zai shauda mata aiko ta fasa q'ara ta ida shigewa jikin baba isma'il tana fadin "wayyo mairan qarfe kayi haquri,(sunan da take kiran baba yawale dashi knn)
baba isma'il najin hakan yasan da abinda tai masa kuwa sababbar, dan haka saiya fara dariya yana qoqarin rabata da jikinsa ya nufi miqawa baba yawale d'in ita amman taqi yarda da hkn, jiyayi baba yawale yace ''kaji ja'ira 'yar albarkar yarinyar nan isma'il d'azun waini zata firgita batasan indai wannan tsoron ne ni maraba nike dashi ba konaje na tadda abokina ba dahar gobe rashinsa baibar bimin jiki naba (baffa marigayi),
miq'o mun ita na tsautsaula mata carbin nan inda ta maisheni kakanta na rugar su, wai fa in gaya ma isma'il yarinyar nan kawai tazo lafemun a cikin quryan daki ta sake maq'e waccen qaramin muryar tata wai itace mutuwa idan na shirya yanzun zata d'aukeni sauri take dan akwai sauran wujajen da zata je amman nine na farkon ziyara shiyasa tafara yowa nan wai na jima ban tafi ba yanzun lokaci na yayi... haba baba isma'il dariyar abun kawai yake da gudu heenduh ta hantsala ta miqe tsaye ta nufi q'ofa tana haki ta tsaya ta juyo ta dubi baba yawale tace cikin qyalqyatawan dariya wacce har fararen haqoranta suka fito reras dasu gwanin burgewa
"cab kujimin tsohon nan nizai daka da wannan dogon carbin yasamun ya fasan jiki ya cuci masoyina ta66 walle kam Yaseen bazan tsaya ba wlh kuwa,, mairan qarfe naso ka tsorata ka gudu insha dariya a d'azun din nan ay"
girgiza kai baba yawale kawai yayi yace"hmm kedai kika sani ay da shirmenki zan kuma riqeki da hannuna in saki mari sai maaoyin naki yazo belinki kinga daman sai ingansa inda daman rowarsa ake mana,dariya heenduh tai tace "ko aiko indai masoyina na haqiqa zaka gani kenan kana da sauran kallo a gaba dan ni kaina ban sansa ba bare na sanarwa wani dashi shi" yatsina fuska baba yawale yai yace "zancen 6ur knn, ashe abunma dud wobuwa ce da hayaniya, inda dai bakida saurayin kizo na taimaka miki mu qulla auran nan namun nan" turo baki tayi tareda juya fuska gefe bayan ta kaso kallabinta har goshi sannan taxe ''ta6 Saidai na had'a ka da goggo dahara( wata tsohuwa ce nan maqotan su heenduh dun take mai saida zogale da kuli kuli da man gyad'a kuma, batada miji danta daya kuma ya rasu ita kadai ce zaune a gidan sau tari sa'a da heenduh can suke zamansu na fira dan sun saba da ita sosai.
qyaleta baba yawale yai yadanyi murmushi tareda duban isma'il din yace "yarona isma'il tashi jeka gida haka ka huta rabu da shirmen heenduh, Ubangiji Allah ya sawwaqa kaji" "aminn baba'' cewar baba isma'il yana mai miqewa tsaye a hankali da qafar tasa, saida ya fita sannan heenduh ta juyo ta kalli baba yawale ta kashe masa ido guda d'aya na tsokana tace ''byeee mai ran qarfe sai gani na uku ko wajen kawo sabuwar ziyara dan nasan ka tsorata kadai mazge ne ka b'oye walle kuwa" yunq'urowa baba yawale taga yayi kamar zai nufota da doguwar carbin nan nasa aiko ta d'age siket dinta na atamfar nan sai kusada babanta dayake gabda shiga gida ta dura, dariya kawai take tuntsurawa dan matuqa takejin farinciki dud intana wajen baba yawale, wataran suyi firar arziq'i abinsu hankali kwance, intaja ruwa kuma nan take firar tasu zatai kwab'a ya korota gida.
suna shiga gida suka iske mama zainab zaune nan inda suka barta tana q'oqarin tashi zaune ne da sauri heenduh ta q'arasa ta riq'eta tace "sannu mama jikin yayi sauq'i dai ko? "yaya jikin naka mlm?"! tambayar da mama taiwa baba isma'il knn dan sam ita tafi damuwa da nasa ciwon akan nata.
''da sauqi zainabu dan wajenma da akai dreesing ya rage ciwon ba kamar d'azun ba da jinin ke zubowa" cewar baba isma'il din.
sosai mama zainab taji dad'i dan ya q'ara kwantar musu da hankalin da kansa ya tashi yaje ya d'auko musu zazafen tuwonsu na jiya wanda heenduh ta d'umama masa d'azun.
saida ya matsa sannan suka sa hannu sukaci dan mama Zainab baifi datai ci biyar ba taji cikinta na zafi dole ya haqura ya barta tad'an kwanta nan babu jimawa barci ya kwasheta sakamakon magungunan ta data sha wanda khaleepa ya bata.
bayan baba isma'il ya wanko hannunsa ya dawo ya zauna nan kan tabarmar ya dubi heenduh dake gyarawa mama Zainab lullu6in zanen data yane jikinta dashi yace"heendatu yau bakije school bane banga kinje ba?" saida ta d'an lawangwa6e kai sannan tace "eh baba bamuda lecture ne yau sai gobe sanna" sauke ajiyar zuciya baba isma'il yayi yace "to shiknn Allah shi kaimu lpia"
"amunn baba, kaima ya kamata ai kaje ka huta kan akira la'asar, tayi maganar tana duban qafar tasa. miqewa tsaye yayi yace
"hakane heenduh na bari na shiga d'aki to na d'an runtsa dan na gaji sosai"
"to babana afuta lpia saika fito"
daga haka ya wuce ita kuma taje ta kai kayan gwarin baba ma'ajiyarsu daga saman hnya data d'auke su, tana gamawa ta dawo ta d'an kwanta nan q'asan wajen tabarmar da mamar ta ke akai tana danna 'yar q'aramar gwaramar wayar nan tata tna tunanin miya hana sa'a kuma zuwa ne har yanzun?".
Khaleepa kuwa suna barin gidan saida ya jima nan zaune q'ofar gidan su shida su yunus sannan ya kwashi laptop d'insa da jikkarsa ya wuce cikin gida.
main falour nasu ya wuce kai tsaye saman dakinsa ya haura ya zube saman mahehen gadonsa laptop d'in na saman q'irjinsa idanunsa lumshe sai dan ya matuqar gajiya yau da aiki dudda ya kama ranar weekend ne kuwa amman saida ya fita aiki tun safe. wanka kawai yake son yayi koya samu jikin nasa ya warware masa gajiyar daya kwasa, bazato bare tsammani sai jiyai kawai ana shafa masa gefen kwantaccen sajen fuskarsa zuwa sumar kansa wacce ke kwance lub lub a saman kansa baq'a q'irin da ita kuwa wanda kaida gainta kasan ba qaramin kashe mata kud'i guy d'in
yake yiba wajen gyaranta, jin abun yaqi qarewa yasa da sauri ya bud'e idanunsu amma still yanadaga kwancen sa bai miq'e ba, caraff suka had'a ido da zarah 'yar hjy Hadeeza aminiyar firdauseey.
sosai ya tamq'e fuskarsa bayan ya miq'e tsaye ya zuba mata idanunsa fess bumisa fuskarta a kausashe,
tuni jikinta ya fara shaking dan ganin mummunan kallon da yake binta dashi, wai ita yaya zatayi da son khaleepa ne a rayuwar ta? tana tsoron fa kada hakan ya illata mata zuciya da yawan tunanin da zuciyarta takeyi na kaikawo a kansa, har jitake a iriyar sonda take masa babu abinda zai nema a gareta ta kasa mallaka masa shi koda kuwa gangar jikinta ne ya nema ta tabbatas to zata sallama masa ita dan wanna ba wai baq'on abu bane a gareta lura da yanda suke qazamtacciyar soyayyarsu da samarinsu na school kises in every were are her body and hugs wanna ba wani baq'on abu bane a gareta ba muddin zai nema a shirye take data sallama masa knta indai zaiyi farinciki harya kulata dai dai na munti daya cikin sakin fuska ba wannan fuskar shanun da yake ba kullum,
shiyasa ake tunanin jawo hankalin khaleepa ta wanna hanyar amman sam ko fuskar haka ta gagara samu a wajensa bare ta cimma burinta dan a haqiqanin gskia tana masifar son jin yanda zumarsa take danda gani zakin mazaje ne a iriyar kalar k'irarsa zai 6atawa mace tunaninta ta yai mata formating nasa gaba daya indai ta wannan fannin ne komin jarumrarta kuwa, shiyasa kawai ta shagala da kallon qirarsa dudda tsoron da takeji na kallon banza da take samu daga garesa ga kuma tsabar qwarjininsa dake kada hanjin kowace mace kuwa data yarda har ya saka mata kalar idanunsa cikin nata idanun.
anasa 6angaren kuwa dubnta yake sam ya tsani mace marar kamun kai a rayuwar sa, bare ita daya sha ganinta da 'yan iskn samarinta suna yanda sukeso kuma dud halinda ta ke ciki yasan tabbas mamanta tana sane ammam sabida tsabar son da take nuna mata ya hanata katsa mata, kuma shi koda habitat nata masu kyau ne sam batta daga cikin kalar suffar halittar macen da yakeso matarsa ta kasance dasu na jiki, ko daya batada shi amman sbd tsabar ta rainasa har take iya shigo dakinsa ta dunga ya mutsa sa ma knn, amman taci sa'a ta kuma godewa Allah dabata mallaki surar dirin kalar matar da yakeda buqata bane da saita raina kanta yau yau dinnan a hannunsa tabbas, dan a yanda yasan kansa baida excuse ga dud macen data shiga hannunsa, shiyasa bai cika son shiga harkar matan ba dan kiyaye kansa daga abunda ke sake girmama a jikinsa tabbas tabbas tabbas shi yasan yanada sha'awa bata wasa ba, hakan yasa yake dauke kai ga dud wata mace gudun kada ta rusa masa budget dinsa dan ya d'aukarwa kansa alqawali zai zama virginity shima kamar yanda zai karbi na matarsa shima zata kar6i nasa a ranan zata fara sanin sa itama, hmmm kunji fa, shiyasa ya qudurta worning zai bige wa zarah kan zuwan masa d'aki dan ko muddin ta ci gaba da taba masa jiki da wannan qazamin hannun nata wlh sai jikinta ya gaya mata, dan haka nn take ya q'ara fiddo idanunsa waje gaba daya tareda daka mata wata tsawa sai kuwa gata bakin qofar futa daga dakin yace "ubanmi ya kawoki d'aki na? yayi maganar yana mai zazzaro mata idanunsa waje, jikinta na buga rawa ta fara magana murya na sarkewa "ww.. wlh yaya khaleepa momynka ne tace nazo naga in kana ciki,,
"ok dan ina ciki shine akace in kinzo ki dinga shafa ni ke qaramar 'yar iska ko? yana maganar ne yana q'oqarin kwanto belt d'in jeans d'insa aida sauri ta sauka q'asa batareda ta q'ara cewa uffan ba.
wani dogon tsoki yaja tareda wurgar da belt d'in tsakar d'akin ya koma ya zauna bakin gadon nasa ya sa yatsun sa cikin sumar kansa ya dunga yamutsata sosai idanunsa a lumshe sam ya tsani yawan magana yanzun kwaratsin da ta sanyasa ji yake gefen kana na buga masa d'al d'al d'al ciki ciki, shifa harda haka ne yasa sam ya tsani harkar mata shiyasa babu shiri ya miq'e zuwa ma'ajiyar magun gunan sa ya d'auko na ciwon kai babba guda daya ya tura a baki tareda daura kofin ruwa akai ya hadiye maganin ya ajiye cup din cikin deep freezer dinsa sake kwance wajen, cire kayansa yai ya daura towel a iya qugunsa nan take faffad'an qirjinsa ya bayyana mai cike da mayalwacin kwantaccen gashi sai sheq'i yake, toilet ya wuce kai tsaye bai jimaba ya fito ya shirya kansa cikin wasu qananun kayan, baqin jeans ne sai Blue din riga mai qaramin hannu rigar tabi jikinsa ta kwanta ta yanda dud wasu zubin damatsam halittar karfi ta cikakken namiji gogaggen d'an boko kuma suka bayyana a kansa,
Black cambus dinsa yasa kalar na 'yan q'wallo amman su wanna new designer ne, bayan ya gama d'aure mad'auran takalman nasa ya d'auko wata farar rigarsu ta likitoci ya d'ora saman sheet din jikinsa ajiye medical glass dinsa yayi gaban aljihun rigar sannan ta fito daga dakin sa zuwa babban falon gidan nasu dake q'asa sai baza qamshin sa yake, taku yake cikin takunsa daya saba.
cin karo yayo da momynsa tana qoqarin shiga kicen dan ita bama ta gansa ba, dan haka a hankali ya sad'ad'a ya lallab'a tareda kai bakinsa ta bayanta daidai saitin kunnenta yace "momyyy na!!!" da sauri ta juyo tana murmushi tace "mai tsada na ka b'oye ina ka shige yaune? tayi maganar tana kallon had'adden saurayin matashin d'an nata kwalli d'aya wanda dud sonta na rayuwa yana garesa duka, shiyasa gata na gidan duniya babu wnda khaleepa bai samu daga iyayensa cikin ma samin wasu yake, kan ya bata amsa sukajiyo muryar dadynsa mukhtar daga gefensu yana fadin
"Masoyana fira kuke ne batareda an gayyace niba?" dariya sosai hjy firdauseey tayi shiko uban garin rungume dadyn nasa yai yana cewa "barka da fitowa dady, zama sukai kan kujerun falon hjy firdauseey tace "kagansa nan kyakkyawan saurayin d'an nan naka alhajina tun safe daya bar gida saifa yanzun na gansa alhalin yasan bana jure rashin ganinsa na sa'oe muddin ba yana office ba dan haka na kawo maka qararsa ya fad'a maka inda yaje dan nasan yau weekend ne babu hospital bare nace can yaje" Alhj mukhtar wani murmushi yasa ki sosai tareda dubn khaleepa dake wani langwave kai kamar maiji barci nanko tsoron klr doguwar tambayar da dadyn nasa zai fara masa ne gameda hkn gashi shi kuma ba gwanin doguwar magana ba bare ya basu amsa cikakka fatansa dai shine AllAh sa dadyn nasa ya taq'aita tambayer tasa domun yaji dadin basu qwararriyar amsa guda d'aya, shi kansa Alhj mukhtar yasan halin d'an nasa da kwaikwai wajen magana dan haka sai ya had'a masa tambayarsa waje d'aya a dunqule a sauqaqe tareda cewar " to my done boy kaji mmnka ta kawo qararka kan ka je ka dad'e a waje ina kaje amsar da take buqata knn? yaqarashe maganar cikin raha.
sam bai iya qarya ba baisanma ta yanda ake yinta ba dan haka kai tsaye yace "dady momy nifa yau naje hospital bayan na tashi da safe, shine naje na yiwa wata mata ne 'yar qaramar Theatre dan ranar nai alqawalin zan mata so kuma dady bacin na dawo ne na je gidan small father
(isma'il) na iske maman bata lpia shine fa na dubata tareda zuwa samo mata medicines dana futo ne kuma ina nn zaune waje nida freands nawa shinefa na shigo yanzu nai wanka zan koma hospital din na duba matar naga kota farko" gaba d'aya saida zuqatan su suka soya fuskarsu ta nuna hakan sakamakon ambatan zuwansa gidan isma'il kai tsaye da yayi dudda abinda ya faru jia kuwa dud a knsa,
to amman da yake firdauseey 'yar duniyar gske ce sai tayi gaggawar q'aqaro murmushi a fuskarta danta kula dud sanda ta 6ata masa rai akan maganar gidan matsiyatan can wuni yake yi mata fushi ita kuma fushunsa quna ne mai ciwo a gareta cikin zuciyar ta. harda mukhtar ya zuciya zai balbale khaleepa nan take a wajen da fad'a da sauri firdauseey ta girgiza masa kai alamun a'a kul kada ya soma.

By
*Xexen Fasaha*
[1/17, 3:10 PM] Xainab Documen: πŸ‘πŸ‘
πŸ₯‘πŸ₯‘
πŸ‘πŸ‘
*DA SAURAN KALLO !!!*

Story and writing
by
Xayyneb πŸ’€πŸ’€

Fasaha online writers f. o.w.

*🌳imparting valuable knowledge and entartaiment is our concern*🌳.

~dedicated to my mom Sadeeq hawwas~

-https://www.facebook.com/Fasaha-Online-Writes-751775151851852/?referrer=whatsapp.

πŸ‘πŸ₯‘πŸ‘
πŸ…Ώ2⃣3⃣.
Sauya fuskarsa mukhtar din yayi kawai yayi kwana da maganar da fadin "ok done boy jeka take care AllAh ya tsare mana kai" saida khaleepa ya d'an duq'o sumb'aci iyayen nasa a gefen fusakokinsu sannan ya fice da sauri yana fadin "ameen dady na da momy"
bayan fitarsa ne mukhtar ya dubi firddausy yace
"miyasa kika hanani aiwatar da manufata?
murmushi tayi sannan ta d'an kurb'i ruwan lemon hannunta sannan ta dubesa tace" hmmn, lokaci yayi da zamu canza

Please Login or Register in order to submit comment