Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwata ya kasa magana dan tsabar baqinciki sai saqyar ya iya dubn iyayen nasa yace"baffa ashe yaya mukhtar da gaske yake zai rushe muku gida, wlh gashi can ya gama rushewa ku taso idanunku su gane muku,, aida sauri baffa ya fita inno ma ta janyo mayafinta suka fita suna isa wajen kuwa daqyar suka gane inda mukhtar yai musu ta'adar kuwa sakamakon mutane da suka iske wajen dayawa suna kallon abunda mukhtar yasa akaiwa gidan nasu dan yana tsaye lokacin har aka gama kuwa snn ya tafi.
nan kowa yaita tofa albarcin bakinsa, gameda rashin mutuncin mukhtar a yanzun kuma.
Allah sarki inno tana yin arba da filin gidan nasu ba gida ba tuni ta zame qasa ta sume, a rude jama'a sukai kanta ana mata fiffita amman shiru inno bata tashi ba, aida gudu isma'il ya sa6eta a kafada ya nufi wani asibiti dake tsallaken titin anguwar tasu, cikin tsautsayi wajen tsallaka titin baisan mota ta tafoba tuni kuwa ta kwashesu ta watsar shida inno din a gefen titi, mai motar kuma maimakon ya tsaya saima qarawa motar tasa gear da yayi sanin dayai koya tsaya aljihunsa ne zai koka haka ya wuce batareda ya damu ba shin mutanen nan daya buge ko suna raye ko suna a mace ba.
dudda mutane sunso kamo sa amman abun yaci tura baffa da baba yawale kamar su katse dan tsuma ganin jinin dake fitowa jikin isma'il da inno d'in.
nan aka ida isar dasu asibiti bayan an kai zainab gidansu wajen mamarta sakamakon gigicewa datayi tana shirin fara naqudar dole a saman titi.
daqyar likitoci suka tsaida jinin nasu,
saidai sunyi asarar jini da yawa saida aka qara musu jinin baffa da na baba yawale sannan aka dora musu drip.
saidai sakamakon gwajin da akaiwa inno ya nuna cewa jininta yayi mugun hawa ba kadan ba, dan haka likitan yaja su baffa office ya nuna musu cewar dud wani abu dazai sa hankalin ta ya dinga tashi to su kiyayesa matuqa dan zata iya rasa ranta ta sanadiyyar hakan.
wasa wasa saida su baffa suka qulla sati 3 a asibiti amman kuma mukhtar ko leqe tame AllAh bai leqosu ba dudda yaji labarin hatsarin kuwa.
a sati na hudu ne aka sallamesu suna shiga cikin anguwar kuwa sukaga har angama ginin shagunan inda gidan nasu yake har shago kusan ashirin da wani abu kuwa sakamakon wasu filin daya hada dasu ya siya din kmr ynda yace, yanzun haka fenti kawai ya rage a qarasawa gidan, AllAh sarki su baffan kallon wajen kawai sukayi tareda girgiza kai suka wuce gida kawai.
haka rayuwa ta dore mukhtar kwata kwata ya d'auke qafansa da zuwa gidan iyayensa suma kuma sun haqura sunsa masa idanu indai duniya ce ai tafi bagaruwa iya jima kamar yanda mutanen anguwa suke cewa knn ga mukhtar a vayan idonsa, dan yanzun taimakon ma da yake wa jama'a ya rage sosai saiya ga dama yake bayarwa.
watan haihuwar firdauseey ya tsaya dan haka kullum cikin saurare suke kamar yanda itama Zainab take sauraran tata haihuwar tunda satin ya kama bata komi face naqudar tsattsaye danma Allah yasa tanada juriya, gashi kuma itama ta kowane 6angare tana samun kulawa su inno da baffa da mmnta gakuma isma'il dan baffa kam cikin ragunansa daya siya guda uku harya bawa su isma'il din biyu yace a yankawa Zainab inta haihu, hakan kuwa ba qaramin dad'i yasa isma'il ji ba dan daman gashi duka duka yanzun wata yayi rabi bare yasa ran samun albashi har ya siya mata ragon sunan, danma sauqinsa sunada abinci da mahad'ensa.
yau Monday tun da safe su mukhtar da firdauseey suka nufi wata qatuwar private hospital wacce akwai mnyan likitoci a cikinta. harda baqin turawa maza da mata kuwa a cikin likitocin nata qwararrun gaske wanda suka qware ta kowane fanni. sakamakon ciwon da firdauseey ta kwana dashi a daran jia wanda kamar zata mutu, suna zuwa wani babban likita ya dubata yace nan da rabin awa zata iya haihuwa, shiru kakeji rabin awa ta koma awa daya, awa daya ta koma biyu biyu ta koma uku, abudai har marece bnda 'yar banzar azaba babu abinda take sha dole likitoci suka sa mata ruwan naq'uda sannan ta fara nishin gasken gasken na haihuwa, tasha baqar azaba kuwa dan aqarshe tana yin wani bbn yunquri kan baby ya fito likitoci na ida janyo mata babyn ita kuma tana sumewa.
mukhtar na waje amman hankalin sa baqaramin tashi yayi ba jin wani ihun kukn azaba da firdauseey keyi, jiyo kukan jaririn dayai ne yasashi hamdala dasauri ya nufi shiga dakin aikuwa security suka hana sa dole ya haqura ya tsaya, acan kuwa sunyi matuqar qoqari sannan firdauseey ta farfado.
haka suka gyara kyakkyawan jinjirin yaron wanda suka tabbatar ya zuwa yanzun yanada matsala danko numfashi ma saida qyar yake yinsa, nn suka ta masa aune aune har suka gano inda matsalar take.
wani baturen likita ne ya fito daga labour room d'in ya kira alhaji mukhtar d'in zuwa babban office dinsa bayan ya zauna nn ya dubi mukhtar yace cikin yarensu"yalla6ai babynka yasamu matsalar toshewar numfashi wanda har matsalar ta shiga cikin wasu hanyoyi dasuke da dan gan taka da numfashin sa wanda yake shaq'a, to zamu sanyashi a cikin wasu einges na na'ura har tsawon sati biyu dan munada tabbacin 2 in akai masa hakan zai dawo normal, zai yiyu kuma ya rayu ko akasin hakan"
cikin rawar jiki mukhtar yace "doctor ban... bangane ba? kamarya zai rayu bazai rayu ba?"
baturen doctorn yace ''eh, ina nufin a qa'ida naurorin sune zasu fudda masa sanyin da mamarsa ta dunga shayar dashi a ciki lokacin ta hanyar kayan sanyi data dunga sha, yanzun haka,
so yanzu zamu baka uniform saikasa kashiga ka gano su dan mu ba,a shiga room din saida uniform na hospital namu a jiki, haka kuwa aka bawa mukhtar wasu tsanwayen kaya da sunn hospital a gabn rigar sai wata farar hular leda yasa yashiga room din da sauri.
yana isa kan gadon
firdauseey yaganta rungume da jinjirin ansa masa kayansa blue amman sai kuka take, karbar yaron yayi.
"ya subhanalla" yace ganin gaba daya yaron kamar baffansa ya d'auko sak.
dogo ne sosai fari tas ga hanci sannan gashin kansa da jikinsa kwance laya laya alamun na cikakken fulanin usuli knn.
Amman kuma sai dai kash dud wannan baiwar kyan sura da AllAh yaiwa babyn bayya numfashi saida qyar da qyar yanda kasan bazai qara koda second ba kuwa a duniya saboda hatta mad"igar babyn nasa ana ganin tashin bugawarta.
kuka firdauseey take tana cewa "dan AllAh mukhtar kada yarona ya mutu ina sonsa wlh zuciyata zata fashe nima wlh inbisa, dutta rude ta gigice sai sambatu take.
rungume jinjirin mukhtar yayi a jikinsa ya zauna bisa wani gado dake gefen na firdauseey saboda yanda yaji son yaran na ratsa b'argo da tsoka na jikinsa kaishi fa jiyake baiqi a halin da ake yanzun ba ace yabada komi nasa ba saboda d'an nasa yasamu ingantacciyar lpia kamar kowa.
kawai sai qara rungume jinjirin mukhtar yayi yana kuka.
suna haka saiga wata 'yar tsamurarrar baturiya ta shigo room din ita da 'yarta.
nan baturiyar
ta cirewa firdauseey drip din ta fita yayinda 'yar tata ta matsa kusada mukhtar ta dan riqesa ganin yana kuka kamar qaramim yaro yasata fadin "oh sir yi hakuri kada ka damu babyn ku zai samu sauqi insha Allah"
amman ina kwata kwata mukhtar baisan ma tana yiba kuka kawai yake firdauseey na tayasa dan ganin
da suke a yanzun rashi zai risqesu dai dai lokacin da sukaga samu Allah kenan!


By
*Xexen Fasaha*
[1/17, 3:10 PM] Xainab Documen: πŸ‘πŸ‘
πŸ₯‘πŸ₯‘
πŸ‘πŸ‘
*DA SAURAN KALLO !!!*

Story and writing
by
Xayyneb πŸ’€πŸ’€

Fasaha online writers f. o.w.

*🌳imparting valuable knowledge and entartaiment is our concern*🌳.

~dedicated to my mom Sadeeq hawwas~

-https://www.facebook.com/Fasaha-Online-Writes-751775151851852/?referrer=whatsapp.

```Masoyana na gskia da gskia wanda na sani da kuma wanda bn sani ba ina godia gareku matuqa da nuna qauna, ina roqon Allah kuma alherin Allah ya isar muku kamar yanda nike samun managartan addu'oe daga gareku kuma```.
πŸ‘πŸ₯‘πŸ‘
πŸ…Ώ1⃣7⃣.
*M* ukhtar kam sai da qyar doctor merzan ya rarrashesa tun shigowan sa shima kuwa ya iske sa halinda yake.
kan dole mukhtar ya haqura ya basu d'an ya fita ya canza kayansa ya zauna nan office din doctor merzan kamar yanda ya umarcesa daya jirasa nan.
babu jimawa saiga likitan ya fito yayinda firdauseey ke biye a bayansa har zuwa lokacin fiskarta share share take da hawaye. mukhtar nan shima yaji zuciyar sa ta q'ara karewa dole yasa hankicerf wannan karon yana tafiyar da hawayen nasa a cikinsa.
bayan firdauseey da likitan sun zauna nan doctor merzan ya dubi mukhtar yace "ka daina saka damuwa a ranka kaji? babynka zai samu lpia insha Allah so dan yanzun haka mun kaisa can dakin da na'urorin suke mun kuma sanya sa ciki, sai dai kuma a qa'idar asibitin nan indai muka kwantas da iriyar wannan patient d'in to ba'a zama wajensa kuma adadin satikan da muka d'iba sai lokacin ake dawowa so dan hka be careful zaku iya tafiya sai nan da sati uku zaku dawo ku iske sakamakon, sannan ita kuma maman babyn munga babu wata matsala a jikinta kuna iya komawa gida yanzun tare da ita wannan shine cikakken bayanin zaku iya biyan bill namu sannan ku tafi"
da kuka firdauseey tabar office d'in shi kuma mukhtar saida ya biya bill na komi sannan ya fita daqyar ya rarrasheta suka shiga mota direbansu yaja su har gida.
koda suka koma gida bnda sabon kuka babu abinda firdauseey ta dasa dan gaba daya ta hayyaci kanta ta hana kanta sukuni.
dole mukhtar ya kirawo mairon tsimbe tazo.
tana zuwa kuwa ko sallama batai ba ta fad'o cikin falon gagaf tana fad'in "wai yaya ne mike faruwa nikejin kukn firdauseey ta?"
cikin ladabi mukhtar ya fito daga bedroom din ya gaisheta ko kulasa batai ba dan ita ta 'yarta kawai take da sauri ya matsa yabata hnya ganin yanda ta cusa kai cikin bedroom din nasu har tana qoqarin turesa.
firdauseey na ganin uwar tata da gudu ta miqe tsaye ta isa jikinta tana cigabada da kuka tana fadin "mama babu babyn babyna zai mutu ya barni mama? ita mero ma sai lokacin ne ta lura da babu cikin jikin firdauseey dan haka wata uwar ashariya ta ingizo tareda fadun"tooo ana wata ga wata fa, bantar ubancan,! gidan uwarwa aka kai mini jikan nawa eye? a fad'a mun inda aka saka mun jikina komuma billaheel azeem na rigizazo muku August a gidan nan" tayi maganar tana dukan qirji tareda cin d'amara da mayafinta tana duban mukhtar alamun dashi take.
kasa magana yai dan baq'aramin tsoron meron tsimbe yake jiba matuqa a rayuwarsa, dan haka muryarsa na rawa rawa yace
"ai...ai mama yana hospital ne.... "uban ubanmi yasa aka barosa a sosbitel d'in?, cewar meron tsimbe data katse mukhtar d'in dudda mukhtar na halin tsoro saida maganar mero taso basa dariya danjin dayai ko sunan ma hospital din takasa fad'a banda zagi babu abinda bakin ya iya da cin mutunci.
kamo hannunta firdauseey tayi suka zauna gefen gado nan suka zauna firdauseey ta fad'a mata da cewa "mama babyn ne bayya da lpia dana haifosa kuma.... nan ta kwashe komi ta fad'a ma uwar ta qarashe da matse qwalla tana cewa "wlh mama bakiga kyakkyawan babyn ba, AllAh kuwa mama inna rasa sa kema zaki rasani ne" kama hab'a mero tayi dayake zuciyar ta ta jima da qeqashewa shiyasa bataji ko d'ar na tausayin firdauseey dawani jinjirin ba, kawai fizgo hannun firdauseey tayi ta girgiza tace "toke dan ubanki uwar waye yace baki fad'a mun ta waya ba nazo munje asibitin tare? kuma uban waye yace kitashan abin sanyin ne eye bare kizo kifasawa mutane makoki?,
to wlh can saman kanki kuma marmaza kije ki d'umma jikinki da ruwan zafi dan maijego batta zama babu gashi"
haka firdauseey ta miqe ta nufi toilet amman gaba daya zuciyarta naga babynta, mero ta miqe tace "naga sanya kikewa batun bari kiga in shigo kewayen in gasaki da kaina dan ban yarda da kiyi ke kad'ai ba dan wannan in aka barki zaki lalata kanki ki
zama maras amfani fanko ga miji saidai yaje ya nemi wata kokuma ya aura kinaji kuwa kina gani kin zama foto a cikin gida bayanda zakiyi"
haka mairo taita sakin magana ko kunyar mukhtar dake wajen batayi ba harta bi firdauseey toilet din ta maido kofar ta rufe.
zama mukhtar yayi gefen gado tareda dafe kansa yarasa yanda akayi son babyn nn yai masa wawan kamu, zumbur kuma sai
ya miq'e tsaye ya koma falo ya d'auko wayarsa yahau kallon foton babyn bai aune ba sai yaji hawayen sa na d'iga bisa screen touch din wayar.
yajima a haka sannan yayi shirin office akan dole sakamakon wayar da aketa masa tun dazun akan zuwan wasu baqinsu haka yahau mota jikinsa a mace yabar gidan.
A can toilet kuwa kukan da firdauseey take tana kiran babynta kada ya mutu shine ya hassala meron tsimbe ta kufula tace "tace ke dan kan mataccen tsohonki kukan nn ya isheni haka, haba anyi d'iya sai shegen naci? kuma madai naga yaron nn bai mutu ba bare kita asarar hawayenki ko?, to inma ya mutu q'asanki amfanin ubanmi yake miki dabazaki qara iya daukar wani cikin ba ki haife?,,
shiru firdauseey tayi amman sai faman gunguni takewa uwar qasa qasa tareda satar hararata, basu baro kewayen ba saida meron tsimbe ta gashe firdauseey fiyeda qema ta qara shan wata azabar kuwa saida ta bud'e sabon famfan kuka sannan uwar ta barta.
haka ya kasance kullum mero ke kulaw da firdauseey kuma basu fad'awa kowa haihuwar ba dan a cewarsu sai sati ukun sun cika sun koma asibiti suga yanda lpiar yaron take ko akasin haka.
cikin ikon Allah kuwa yau Monday yacika sati uku knn da haihuwar firdauseey kuma yaune suke shirin komawa asibiti dan meron tsimbe saboda zumud'in ganin jikan nata datazo jia nan ta kwana gidan firdauseey kuma a bisa gadonta tayi shame shame a bisa uwa saniya wanda hakan tasa mukhtar dole barar musu d'akin ya kowa d'aya daga cikin d'akunan saman benen, dayake babu abinda babu a d'akunan dudda ba zamnsu ake ba.
6:22pm a hospital din tai musu suna nn zaune har saida lokacin yad'anja wajen 8 da wani abu sannan fa manyan likitocin suka fara shigowa asibitin cikin motocinsu, suna a haka saiga doctor sera ta shigo wato mamar yarinyar nan baturiya wacce ta rarrashe mukhtar jia dayaita faman sakin sambatukan kukan nn. Still 'yar tata raja tana biye da ita, raja iriyan matan nan masu 'yan mnyn shekaru a fuska amman jikinta ya b'oye mata hkn danko mama bata dasu yanda ya dace shiyasa ake kllonta qaramar yarinyane. bayan sun gaisa ne mmnta take cewa "kuna jiran doctor mezan ne ko?"
"eh cewar mero data riga kowa harshen mgn a wajen, sai tace "ok to ku qara haquri nan da mintuna 10 zaku gansa"
"ok ba matsala doctor thanks" cewar mukhtar su juya suka wuce yayinda meron tsimbe tabi 'yar baturiyan nan wato raja da kallo aiko saita bushe da dariya tana fadin 'o'o ni Allah mai halitta ita wannan jibeta da fuskar manya amman dubi qirjin kamar anyi shafen suminti akai... kanta qara cewa wani abu saiga doctor merzan yashigo aikuwa da sauri mukhtar da firdauseey suka miqe daidai nn doctor d'in ya iso garesu suka gaisa yajasu office dinsa ya aijye brifcase dinsa a side tareda zama kan kujera ya dubesu cikin fara'a yace"congrats ina tayaku murnar babynku ya samu lpia jia muka fiddasa a engies d'in yanzun kam bayada matsalar komi numfashinsa it's very very normal dan yanzun haka ma zamu iya zuwa ku d'auki babynku" tuni suka hau murnar gasken gaske kuwa sai hamdala mukhtar yake haka doctor merzan ya kaisu dakin da babyn yake ai mero na arba da tsantsar kyawun yaron saita dubi firdauseey tace" 'yar banza dole ki haukace kan jinjirin nn ashe? yaro kamar yasha hatimin annabi yusuf shima dai? itadai firdauseey batabi ta kanta ba shayarda yaronta kawai take kamar yanda doctor ya bata izini.
sai kallon yaron suke Itada mukhtar sai wutsil wutail dinsa yake na jarirai cikin kayansa an kuma nadesa a showel kaida ganin babyn kasan lafiyayyen baby ne, yanda kasan ka tabasa jini yai tsartuwa haka yake, danba qaramin kyau ya qara ba akanma wanda aka haifesa dashi d'in .
basu jimaba aka basu sallama da yake ranar suka kar6o babyn dan haka sai aka maida rad'in sunan yaron da kuma bikin sunansa rana ita yau watau Monday mai zuwa, tuni mero ta dunga fadawa yanuwa da aminan arziq'in haihuwar firdauseey kankace miye mutane sukaita shigowa ganin jariri kuma dud wacce tazo abunci da namomi da juice s saita ture kuwa dan masu aiki har uku mukhtar ya zube musu sannan dud wacce zata tafi sai an mata kyautar 1k sannan.
aIkuwa shiyasa a ranar mutane basu katsewa zuwa gidan danjin labarin kud'in da ake badawa wane yaji ga wane knn, kai baka bayarba kaje an baka tomiyafi wannan dadi cewar mutane.
koda wasa mukhtar bai taka q'afarsa yaje yafad'awa su baffa haihuwar ba dan tsanar sa da ismail bazai bari yaje gidan nasa ba, suma su baffan ya runtse idone kawai haryayi tunanin gaya musun bawai dan matsayinsu yakai ba na sujin a cewarsa, amman ya yanke hukuncin a ranar daren suna zai je wajenda su baffan ke firar dare saiya fad'a masa faqat yarage ruwansa yaje zanen rad'in suna ko kar yaje shidai yafita haqqi a ganinsa.
saidai abinda bai saniba har su baffa ma sunji haihuwar saidai sukayi shiru abinsu batareda sunyi gigin tunkararsa da wani abu wai shi barka ansa mu qaruwa ba,suna masa adduar Allah raya. to mutumin dayace babu kai babu shi babu ahalinsa babu naku kuma ya hanaka taka gidansa tomi zakaje kayo? suna matsa yin iyayensa aisu yakamata yabi basu su bishi ba kodan gobensa tai kyau, dan haka inda bai zo ya fad'a da kansa ba ai huta roro waken gizo yayi 'ya'ya cewar inno da suke tattauna maganar da baffa da ismail.
dan yanzun harsun manta ma su rabonda dasusa mukhtar idanunsu dama basusa aka ba bare abun yadamesu, danma musamma ma inno dake da hawan jini, takan qara da cewa "inda ya zabi mace akanmu ai shiknn haka duniyar take ay ba kanta farau ba haifarwa mace namiji tana masa fatan shirya dai.
suma kuwa abun Allah a ranar ne bayan gama sallar isha'e Zainab ta suntulo musu kyakkawar d'iyarsu mace barikallahu Masha AllAh, su baffa baqaramin dadi sukaji ba da Allah ya nuna musu d'an isma'il wanda bai yarda suba, shiyasa har nafila sukai ta godia ga Ubangiji,, ranar kam sunyi kwanan farinciki, danko washe gari aka farfado haihuwar maqota akaita shigowa kuwa tayasu murna dasa albarka kowa ya amshi jinjirar nan kuwa kamar karya badata yakeji dan yanda kasan zubin larabawa haka Allah ya basu ita.
mutane basu katsewa zuwa gidan kuwa kullum saboda sake ganin jinjirar zainab, dan kuwa wasuma dawowarsu ganin jaririyar yafi a qilga dudda sun zazzazo kuwa, mutane suknce dudda kyan da Allah ya qawata jinjirar dashi saida ya qara mata da farin jinin mutane ta ko'ina, Allah kenan buwayin sarki shi daya gagara misali, haka akaita zaman barka har yau gashi daren suna.
kamar yanda shi mukhtar ya tsara haka kuwa a daren suna yazo har wajensu baffa inda suke zama da baba yawale waje sallama kawai yayi batareda ya gaishe suba face "sannynku"' da yace yana daga tsayen sa kuwa, amsa sallamar baffa yayi shima dan ya zama dole kam, amman daga haka ko kallon mukhtar din baiba yaci gaba da jan carbinsa.
baba yawale yace "mukhtar kazo ganin jinjirar d'iyar qanen taka ne a fiddo ma ita ka gani? Mamaki mukhtar yayi daman har matar isma'il ta haihu bai gaya masa ba,( kujifa shi ya fad'a masa ne?)jiyayi nan take ya sake tsanar su gaba daya jiyake dazai iya raba jikinsa ya kwashe jinin jikinsa ya maida masu baffan abunsu dayayi koya huta da tunanin cewa dansu ne shi kuma shi dan uwan isma'il ne!
(ya subhanalla gskia mukhtar an nemeka an samu da yawa, AllAh shi kyauta dai to).
duan baba yawale mukhtar yayi jiyake kamar ya ida qarashe tsohon ta hanyar yi masa zazzafar shaqa danjin zafin mgnr dayai masa nawai yazo ganin jaririya wancen gidan da talauci da babu dake mamaye dashi.
shi koda yarinyar ma ta girma kowani yaji zaima je neman auren yar Ismail gidan aisai ya zugesa yadaina zuwa.
kuma ma ya d'auki alqawalin yar isma'il indai ta girma itada yin aure saidai taga mata nayi dan kuwa kowa yayi nufin aurenta zai sa mutanen sa su zugesa ne in kuma yaga mutum ya nace tofa numfashi zai gintase a rayuwar sa dan ya tsani dud wani cigaban isma'il koda na farinciki ne kuwa.
gani yake inyai masa hakan wata sabuwar hanya ce wacce zaisa maza su guji yarinyar insukaji lavarin kowa yazo neman aurenta yana mutuwa kuwa. tunanin hakan dayai ne yasashi sakin murmushi ya dubi baba yawale da baffa yace "baffa damn nazo fad'a muku zanen suna d'ana ne a babban masallaci bayan gama sallar asuba" ga mamakinsa saiyaga baffa yayi murmushi yace Masha AllAh damn gobe ake rad'in sunan 'yar isma'il kaga sai ayi duka a wuce wajen, baba yawale yace "gskia ne Allah dai shi kaimu lpia, aminn cewar baffa,
Juyawa mukhtar yayi yace "sai anjimanku" baba yawale ne kawai ya amsa masa baffa kuwa shiru kawai yayi yana cewa aransa "hmm ta yaro kyau take bata qarko ay."
Nansu baffa sukaci gaba da firarsu har lokacin tashinsu yayi sannan kowa ya wuce gida danya kwanta.
ana gama sallar asuba kuwa akai sanarwa a masallacin na zanen suna inda d'an mukhtar yaci sunan khaleepa, 'yar isma'il kuma taci sunan heenduh haka aka yi addu'a mutane suka fara fita yarage daga baffan sai baba yawale sai kuma mukhtar da baffan yace ya tsaya kada ya tafi, ala dole ya tsaya kuwa yana tunanin mi baffa zaice masa a masallacin bayan ko jia sun had'u?.
babu zato yaga baffa ya miqa masa hannun damarsa yace bani nan mukhtar?"
cikin mamaki mukhtar ya dubi baffan nasa yace "baffa mizan baka, dan jikinsa harya soma rawa ganin yanda fuskar baffa ta koma babu alamun wasa a cikinta ko masassaqo.
baffa ya qara tamqe fuskar sa yace"dud abunda ya sawwaqa cikin aljihunka indai kud'i ne su nikeson ka bani banson wani ja'inja bani kawai kayi abinda nace" mukhtar bai sake cewa komi ba ya tura hannunsa aljihu yaji babu wasu kudi komi face takardar dubu daya dan jallabiya ce kawai ya fito da ita a jikinsa, haka ya miqawa baffa.
baffa ya kar6a yace Allah sanya alheri cikin ta dan mafi qanqantar sadaqi yana habbaka albarka ta aure ai daman fiye da mai yawan ma, juyawa baffa yayi ya miqawa baba yawale dubu dayan shima baffan ya fiddo dubu daya cikin aljuhunsa ya riqe kowa sai binsa da kallo yake tsakanin baba yawale da mukhtar din dan basusan manufar maganar baffan fa, baffa yace "yawwa yawale inason kai ka zama waliyin jinjirin mukhtar wato dansa khaleepa .
ni kuma zanzama waliyin heenduh yar isma'il yanzun nan basai an matsa ba za'a daura wa jariran aure dan bazan juri ganin tarwatsewar zumunci tsakanin yayana ba ina raye ban mutu ba, kaga innai ma yaran aure tun yanzun kaga zumunci bai kauba dan zuri'ar mu zata qara yawa" ya juya ya dubi mukhtar daya daskare jin abunda baffan yace gaba daya jikinsa ya kab'e da kyarma ko motsi ya gagara yi, baffa yace "yawale kazama shaida ko bayan raina wallahi tallahi narantse da izzar mulkin Ubangiji Allah kuwa muddin mukhtar yasa d'ansa kaleepa ya saki heenduh yar isma'il dan wargajewar zumunci na har abada kamar yanda yk fata to wlh mukhtar kaji da kunnen ka indai ka kuskura kai hakan Allah ya isa!
Allah ya Allah isa!! Allah ya isa!!! tsakanina dakai dan haka ka kiyaye wannan umarni nike baka bawai shawaraba" mukhtar yanaji yana gani a haka kuwa nan take baffa da baba yawale suka daura auren jariran da basusan abunda ke cikin duniyar ba, suna gamawa suka tashi suka fice daga

Please Login or Register in order to submit comment