Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

annabi muhmd ke ciki sai zuwa can sa'a tace''qawata muje gidanmu inason zamuyi wata mgn a nutse.
hakan kuwa akai bayan sa'a sun zauna a dakin mamarta da batanan ta dubi heenduh tace
"qawata dud duniyar nan banda qawa amintacciya sama dake kema kuma nasan hakan amman mizaisa ki dinga 6oyemun damuwarki? kwanan nan kowa ya ganki saiya san kinada damuwa dan har baba yawale saida ya tambayeni konasan damuwarki sakamakon kince masa lpian ki lau,naroqeki qawata dan Allah ki daure ki fadamun damuwar
ki ta d'oro ko inada shawarar dazan baki dan Allah qawata"
fashewa heenduh tai da kuka ta kwantar da kanta bisa qafar sa'a tace
"qawata so baimun adalci ba bai kaini inda za'a daraj tani ba nida iyayena ba,! ki gayamun miyasa zuciyata zatace Sai shi ne dan Allah? miyasa!!! miyasa?!!!!
ta fad'i hkn da qarfi.
duttabi ta rud'a sa'a sai haquri sa'a take bata gamida rarrashin ta.
daqyar ta samu ta baryin kukan
"kigayamun waye wannan Wanda ya ciri tuta cikin maza harya karya tattaurar zuciyar qawata ya sanya ta kuka?
kamo hannuwan sa'a heenduh tai tace"son doctor son Yaya khaleepa yaimun mugun zarge na qulli sa'a kuma wlh koda sonsa zai kasheni bazan ta6a bari yasan ina sonsa ba muddin bashine ya furta mun ba dudda nasan hakan bamai yuyuwa bane sa'a, cikin takaici ta cije le6enta na qasa tace" saidai na sani ne zanyi ta dakon sonsa a raina harna koma ga mahallici na ne sa'a!!"
mamaki yai matuqar kama sa'a sosai najin hkn daga bakin heenduh wanda tasan daba a bakin heenduh taji wannan zance ba da bazata ta6a yarda ba kuwa.
"walkahi qawata so masifane fa nikega mizai hana ki fada masan hakan inda shi d'in d'an uwanki ne?
da sauri heendu tace
"har abada wlh kima daina mun wannan maganar"
sanin taurin kai iriyar na heenduh da sa'a tai yasata cewa"to shiknn qawata ubangiji Allah yasawa doctor sonki shima a ransa fiye ma da naki addu'ar da zanta miki knn Kunlun"
sosai heenduh taji dadin adduar kuwa.
nan sa'a ta sake cewa"kinsan kuwa babana ya saka ranar d'aurin aurena da hussain d'an yayarsa dake garin bauci nanda sati hudu?"
da sauri heenduh tace"amman shine baki gayamun ba?!
sa'a tace"ai shine mgnr danaso miyi dake danace miki ina cikin matsala saikuma kema kika shiga taki matsalar mafarin knn na danne tawa matsalar da roqon Allah har gashi kuma naji sauqin abun"
daman nasa rai ne da auran mustafa saurayina, saigashi koda nai masa maganar ya turo magabatansa cikin wasa saiya kama kawomin dalilai wai shi baima tashi aure ba yanzun sai yayi masters degree nasa nan da tsawon shekara biyar daga nan na fahimci al'amarin nasa akwai yaudara dan damn ina zarginsa da son matan tsiya shiyasa na nuna masa babuni babu shi dan iyayena aure zasumun nan yakama borin kunya wai naci amanar qauna inda bazan iya jiransa ba just five years, kijifa?"
nan na barsa bai dawowa na gida jia wannan abun ya faru fa"
tsoki heendu tai tace "rabu dashi damn baimun ba ni wlh sabida mayen mata ne ko auren sa kikai bazai daina halin saba kawai ya maje ya d'aura miki damuwa,
ki haqura da Husain dan yanada nutsuwa sosai kuma"
sa'a tace"nima shawarar dana yanke knn nima bin umarnin iyaye sbd gobenka tai kyau, kuma sau tari abinda kkso ba alheri bane gareka sai wanda bama ka sa rai ba zaka ga yazamar ma alheri"
haka sukaita tattauna batun,
koda heenduh ta koma gida ta iske yunus ya kawo musu buhunnan abunci harda fridge da dubu 200 yace saqo ne daga khaleepa kamar yanda mama Zainab ta sanar da ita.
hakan kuwa baqaramin famin sonsa ya sake jazawa heendu ba har saida ta kwanta barci sannan fa ta sami sauqin lamarn a cikin zuciyarta.
akwana a tashi babu wuya wajen Allah tun satin da khaleepa yace zai heenduh taita fmn d'auki amman har satin ya wuce shuru bb doctor.
dole ta gaqura har yau gashi sun shiga satin bikin sa'a.
yau juma'a takama ake kamu gobe kuma daurin aure.
'yan mata cike a wajen kowace tasha ankon ta na kamu a cikin wani ash din lace mai d'igo d'igon baqi.
dayake wajen kamun anan cikin anguwar aka samu hall tareda qawata wajen sosai sai walainiya yake.
wajen cike yake da dangin amarya da ango tareda aminan arzuqa sai cashewa ake kan isowar amarya da ango da amarya kuma.
acan kuma gidansu amarya an gama shiryata an dauko masu makeup sun gwangwaje amarya sa'a da heenduh baqaramin kyau sukai ba, musamman ma heenduh da kyaunta ya fita daban a wajen wanda ma bai sani zaice ma itace amaryar kai tsaye.
dan kalar lace din ash colour da d'igon baqaqe nan a jikinsa ba qaramin amsar jar fatar ta yaiba, an gyara mata gashin kanta yai qwarya qwarya laya laya kwance a saman goshinta sannan aka daura mata wani farin flane da beba akai daurin dan kwalin yai kyau sosai yanda aka dan jasa baya bai 6oye gyaran gashin nata ba, sannan aka sa mata wata baqar duguwar sarqa mai yara yara da qulalai har saman qirjinta, sannan kuma da baqaqen 'yan kunnayen sarqar q'ananu.
an gyara mata girar ta data idanunta, idanun sunsha
eyeliner, yayinda idanunta suka qara wani mugun haske gwanin sha'awar mai kallonta, sannan aka shafe lips din nan nata da wani Jan baki pink colour hakan baqaramin kyau ya qarawa zagayayyar cikakkar fuskar heenduh ba har masu kwalliyan suka kasa jurewa suka dunga daukar ta fics tana dariya fararen haqoran nan nata reras dasu bari kalla masha Allah.
saida suka gama kintsawa ne sannan amarya ta fito waje nan suka jera da ango suka nufi hall dunda ake wasu daga dangin ango suna take musu baya.
da sauri heenduh ta fito daga gidansu sakamakon manto jikkarta datai.
zaune ta gansa cikin majalissar su datazo cewa nan saman fararen kujerunsu.
dayake hnyar ne ta kamun.
ga alama shima ya gantan duba da yanda ya wani tsareta da mahukuntan idanunsa kamar mai mata gargad'in data koma gida.
itako heenduh ta dage tambayar zuciyarta yaushe doctor ya dawo har bata saniba???
toko daren jia ya dawo inda gidansu amarya sa'a ta kwana ba gidansu ba?
zuciyarta ta bata amsa da cewa
"eh tabbas tabbas
haka ne kam kuwa heenduh........!!!!"""



~My jikas Zahra Mai Gari kina cikin ruwan raina fa~.😘

By
*Xexen Fasaha*.
[2/13, 10:19 PM] Xainab Documen: πŸ‘πŸ‘
πŸ₯‘πŸ₯‘
πŸ‘πŸ‘
*DA SAURAN KALLO !!!*

Story and writing
by
Xayyneb πŸ’€πŸ’€

Fasaha online writers f. o.w.

*🌳imparting valuable knowledge and entartaiment is our concern*🌳.

~dedicated to my mom Sadeeq hawwas~

*Ina miqo gaisuwa ga classic Fedo, gaisuwa taban girma gamida jinjina hajiyata Allah sa kinji kuma zaki gani*😍

-https://www.facebook.com/Fasaha-Online-Writes-751775151851852/?referrer=whatsapp.

πŸ‘πŸ₯‘πŸ‘
πŸ…Ώ3⃣1⃣.
*G* aba d'aya ta d'auke kanta daga setinsu kamar ma bata gansa ba tayi.
abun kuwa ba qaramin zafinsa yaji ba, wato shi yana can babu ranar da bazata fad'o masa a rai ba amman ita ta gansa ko'ajikinta barema tai masa sannu.
qutawa yayi tareda saurin niqewa tsaye daga saman kujerar da yake ake garin sauri har yana buge dan qaramin table dinda ke gabansu mai d'auke da cups na coffie wanda yasa asabe ta kawo musu, cikin tsautsayi kuwa har cups biyu suka fado qasa suka fashe amman shi sam hankalinsa yatafi ga Inda take dosa zata shiga.
Hafiz da yunus da farouq har hada baki suke wajen cewa"lpia friend doctor??
yunus ya sake dubnsa yace "miya rud'a ka haka kai saurin tashi ne kamar an mintsi
neka har kana
mana 6arin cooffies?"
"sry friends kujirani ina dawowa ynzu"!
abinda yace musu knn ya rufa mata baya cikin wani kalar qarfaffan takunsa.
tana gab da shiga get din hall din da ake kamun knn taji ansa hannuwa an figota baya, ganinsa datai ba qaramin faduwan gaba yasa taji ba dan bata ta6a tsammanin zai iya tasowa daga mazaunin nasu ba.
zubawa juna ido sikai na tsawon mintina 5 babu Wanda yace uffan ga dan uwansa face kallon junansu da suketayi kawai.
sosai ya gintse fuska bayan ya zuba hannuwansa duka cikin aljihun jeans dinsa sannan ya sake matsowa daf da ita danshi yama mnta a inda suke aiko da sauri ta d'anja da baya kad'an tace "a'a wai miye haka ne doctor a waje mike fa al'umma na wucewa"
sake watso mata wata harara yai yace"banda case da wannan kuma bashi nike sonjin amsa daga gareki ba tambaya na dazan miki shine miyasaki fitowa da wannan d'amammun kayan jikinki kowa na kallonki?!,
miyasa kikafi yarda da fidda tsarin sura ki futo waje ne? kazalika wannan d'an gyalen da kika sagala sa a wuya yayi zaga zaga kuma bnga amfanin sashi ba inda babu inda ya kare miki a jiki"
haushi taji ya cikata a ranta tace"to aifa shiknn ka dawo, dubesa dan Allah yanda ya tsareni da wasu tambayoyi to
miye ruwansa dani ma?
kamar yasan mitace aiko sai jitai yace
"kadafa ki tunanin ko wani abu, just ina fighting abun ne saboda gudun zubewar mutuncin iyayenmu dake zaki jawo masu sbd firsararriyar shigar da kikeyi ki fita ko'a jikinki kuma.
dubnsa tai tana yamutse fuska tace"to wai dan Allah ni kadai kagani da zakace haka? dubafa sauran matan dake wucewa kusanma nace gara shigana data wasu fa"
saida yadan harareta sannan yace "baishafeni ba su wannan,, kuma danke ce blood sister na kena sani kuma"
jitakeyi dutta tsani wajen da suke sakamakon kowace budurwa tazo wucewa tana lura da kalar nacin kallon da take bin khaleepan dashi dan haka tai shirin juyawa ta tafi babu zato taji yace "muddin kuwa kika qara taku daya daga nan sai kin raina rashin kunyar dake cikin kanki"
waimi ke damunsa ne yau? mutumin datasan mgn ma saita zamar masa tilas yake furtata amm@n shine yau ya nacewa yinta akanma abunda babu ruwansa da shi? tambayar da take yiwa zucuyarta knn.
kamar zatai kuka ta juyo dan ji datayi sauti na sake fitowa daga hall din ga alama an fara gabarta da komi na kamun kamar dai yanda suka tsara,
Kuma gashi kiran amarya sa'a sai shigowa yake a wayarta amman tsayen dayai mata a gabanta yasata kasa motsin kirki dan qwarjinin dayai mata yau gani tai dud ya cike wajen.
duban agogon hannunta tai taga 4:44 pm dan haka tasake dubansa a marairaice tace
"dan Allah doctor pleass ka barni na wuce man kaga sai kirana ake"
"nacefa baza kije inda mazan can ke gwamatsitsin shiga ba tun dazun"!
zaro idanuwa tai tace "wai kasan bikin wa ake kuwa kk fadamun cewa bazan jeba?
d'aga mata gira d'aya yai tareda ta6e red lips dinsa cikin ko inkula yace
''yeah iknow who is she, tunda mama ta sanarmun a jiya da naje kuna bikin babbar qawar kin nan ko marar ji kamarki, tabe baki taga ya qarayi sannan yace koda yake qwamma ita
ma dake a fagen azancin hankali dan haka maza ki koma gida na gaya miki"
adaidai nan hjy Hadeeza da hjy Firdausi suka wuce a mota amman hjy Hadeeza ta lura dasu tsaye wajen sa6anin Hjy firdauseey din da hankalinta ke kan driving.
shiko daman yana gama fadan hakan ya juya zai tafi yaga taqi barin wajen a zuciyarta sake cewa take"tabbb lallaima wannan mutumin qwarai yai masifar rainamun wayau aiko wlh abunda bazaI yuyuba knn"
wayarta ce ta sake sabon ringing tai saurin dauka tareda cewa"sorry qawata gani nan tafe yanz....jitai yasa hannun sa ya zare wayar tata tareda sakata a aljihunsa na wata baqar doguwar suwaiter tasa har laps dinsa ta sauko amman mai taushin gaske.
wannan karon kasa magana tai kawai ta zuba masa fararen idanunta da b'acin rai yasa suka fara canzawa.
wayarsa taga ya dauko ya kira babu jimawa taji yace
''yunus kawomin motor na anan inda kake hangoni yanzu"
abunda yace knn kawaj ya maida wayar aljihu.
ko minti 5 ba'aiba saiga yunus cikin mota yayi parking a gabansu ya fito ta reda miqa masa key din sannan ya dubi heenduh data cika da fushi har saura kadan ma ta fashe musu da kuka, ganin hakan da yunus yai yasan cewa wata matsalar knn ta sake had'osu da mutumin NASA.
dan haka cikin tsokanarta yace"yadai headache dinmu naga kamar kina cikin damuwa alhalin kuma gashi kunata hidiman biki_?
aiko wata doguwar harara yasamu daga heenduh tareda cewa cikin tsiwa"ban sani ba babu abunda yasha maka kai dani kuma malam 'yan sa ido kawai"!
cikin sonyin dariya yunus yace"ahh ranki shidade Allah huci zuciyarki inda bani nakar zomon ba bare a takura mun da ratayarsa ya matso wajen khaleepan yabasa hannun shima Yakama NASA suka jinjina sannan yunus yace ''to nina wuce friend doctor
"ok till we meet"
abinda khaleepan yace knn yana mai shiga cikin motar shima yunus saiya duqo setin kunnen khaleepa yace
"ah abokina yadai naga haka kaida mutuniyar taka kokun jone ne in between love bamu sani ba dan daman kunyi masifar dacewa fa wlh"
hararsa khaleepan yai yace"kaifa d'an iska be mtsss kama daina wannan maganar mai kama da tatsunniya,
harararsa shima yunus yai bayan ya miqe tsaye daga duqiyar sa yace ''hmnn kafiye kafiya ay amman komi knn lokaci zai nunasa a lokacin ni kuma zan baka amsa daya da daya.
nina wuce yayi mgnr yanaiwa khaleepan wani murmushi yayinda khaleepa yai dan tsoki a raine tareda kallon heenduh bayan ya bude mata gaban motar cikin nuna isa yace
"shigo"
ta fiddo idanuwa waje a d'an tsorace tace''ina zamu?
sake tamqe fuskar sa yai sosai yace
"saidoki zanyi inaga ay"
badan taso ba ta zagaya ta shiga motar ya sa mata key shi kuma.
tanaji tana gani suka bar anguwar takaici yasa batasan ma sanda ta fashe masa da kuka ba tareda d'ora kanta bisa saman cinyoyinta.
ko'a jikinsa haka ya hau titi yanajin wayar tata na sake sabon ringing ya daukota tareda sa mata Airplane ya maidata gaban motar ya aje.
yanaji tana koke kokenta ko uffan bai ce mata ba dudda jinda yake kukan nata na tsunkulin zuciyar sa sosai.
dole ta haqura da kukan ta koma hadiyar zuciya.
haka sukaita yawo a wunin ranar cikin gari har sadda aka kirawo sallar magrib sannan yai parking a gefen wani titi inda keda masallaci yake ya fita harta fara murnar ta dauki wayarta ta fice a motar kenan kuma
sai gashi ya dawo ya dan duqo tareda dauke wayar tata ya juyo fuskarsa gab da tata har suna shaqar numfashun juna yana kallonta itama ta kallesa saikuma ta dauke fuska daga tasa tana turo baki.
fita yai daga motar bayan yasa remote ya kulle ya shige masallacin.
sosai ta duqunqune kanta cikin cinyoyin
ta ta runtse idanunta a fili tace''wlh mutumun nan mugu ne daman bai dawo ba saida aka gama bikin,, mtsss dud yabi ya addabeni komiya sha masa kai da harka nama?
shiru tai tareda sakin wani tsakin bayan ta ajiye qafafunta qasa tace"ya matsawa rayuwata kwanan nan kuma haka nanma yake cemun wata headache bacin shine ya komamun qaton ciwon kai a rayuwa ta".
qoqarin bude murfin motar take danta fice amman jinta datai a datse hakan ya tabbatar mata da cewa yagama aikin tunda ya rufe.
hangawa tai ta gaban glass din motar ta hangosa can zuqunne yana alwala,, dawowa tai ta zauna wato ita gata kirista maras salla knn ko dazai tafi yabarta anan?
"selfishness man"!!!
abinda tace masa knn tana hararar inda yake sannan ta koma ta makure jikin motar ta rufe idanunta kamar maras lpia.
bai dawo cikin motar ba saida yayi sallar isha'e sannan kuma ya shiga wani restaurant dake can tsallake yayo musu takeaway sannan ya dawo cikin motar ya zauna.
lokacin har wani barci barcin gajiya ya dauki heenduh har bamatasan ya shigo cikin motar ba,
kallon fuskarta kawai ya tsayayi yanda take barcin ba qaramin kyau tai masa ba saidai harda busassun hawaye yagani a fuskarta a fili ya furta sory headache na ba'a sona na
hana ki zuwa ba banson naga kina cakud'uwa ne cikin maza dan ina jin zafin hakan sosai a raina"
matsowa yai tareda ja mata d'an hancin nata dayake matuqar burgesa sannan ya sauko da idanunsa a pink lips dinta har sauke ajiyar zuciya yayi lokacin tareda cewa "i miss dhis alot my sugar lips"!
matsoda bakinsa yai yai kissing saman tsinun hancinta da saman rufaffun idanunta sannan ya daura hannunsa akan lips din nata yana shafarsu da babban yatsan hannunsa 1,
babu jinkirin komi ya daura bakinsa akan lips din nata ya kamosu yana dan lallashe mata su daga saman su, can cikin barci taji ana tsotse mata baki dan haka tai tunanin cewa ko a mafarki ne data saba ganin doctor khaleepa nai Mata hkn tun bayan tafiyarsa dan haka bata yi jinkirin komi ba ta d'an motsa tareda kamo lu6ensa na qasa tana tsotsar masa shi da tausasan lips dinta, wani dadi yaji jin ta temaka masa a lamarun wannan karon, shima ko yai saurin kama lips dinta na saman yahau tsotsa, sosai suke sucking na lips din junansu har yana mamakin kaddai itama dai headache 'yar luv ce duba da yanda take masa a bakinsa cikin nutsuwa mai gigita tunanun wanda akewa.
jin jikinsa yafara canjawa hakan yasashi shirin zame bakinsa a nata amman tace inaaaaa wannan kam bazai kasantu ba, wuyansa ta saqalo hannuwanta akai ta ida janyosa cikin qirjinta taci gaba da kamo bakinsa tana tura masa nata a ciki idanunta arufen su still.
baqaramin juriyar barin jikinta yai ba tareda saurin sa hannuwansa ya kamo damatsen hannuwanta ya jijjigata da qarfi tareda fadin ke?! ke?! ke headache bazaki tashi bawai koko?
zumbur ta miqe zaune tareda waro idanunta waje tana dubansa da mamakin yaushe tai barci kuma yaushe ne ya dawo motar, jitai jikinta ya sauya duba da kalar halin data tsinci qasan ta a ciki.
dubnsa tai sosai ganin jan bakinta babu inda bai kama ba a cikin fuskarsa hakane kuma ya tabbatar mata da abunda ya faru ba a mafarki bane kamar yanda ta zata, ganin yanda yawani sha murr ita sai abinma ya bata daria ya iya lallabawa da wayau da dubara yai romance da ita amman sai ya samu yanda yakeso kuma zai yana basarwa.
itako yau bazata taba cewa ya goge ba fatama take Allah sa wani yaga fuskar tasa koyaji kunya.
gani tai ya d'aura mata takeaway dinta a saman cinyoyinta shima ya dauki yughurt dinsa yana sha ko magana bai sake mata ba.
sosai takejin yunwa dan haka bata wani yi jinkiri ba ta fara cin shawarma din daidai nan yaiwa motar key suka bar wajen bayan yasaka wani music a motar.
saida taji ta qoshi sosai sannan ta barsa.
kwanar anguwarsu taga ya shiga, satar hararasa tai a ranta tace "d'an kaga dama da miyasa ka dawon.
satar kallon agogon hannunsa tai da hannunsa me mirza styarin motar tasa wanda gashi ne kwance lub lub akai nan taga 9 da 22. dai dai qofar gidansu yai horn baba sani yai saurin bude musu gate yaje parking motors ya kashe motar tareda juyowa ya dubeta itama dubnsa take da tunanin miye haka kuma gidan nasu ma bazai bari ta koma ba ne koko?
kibiyoni ki dauki tsumman rubands dinki Wanda kika yarda mun a daki rannan, dan inna shiga gida bawai sake fitowa zanyi ba, kuma dan haka ke baki isa sani qara fitowa ba"
tun kafin ma ta basa amsa yunus ne ya shigo gidan har bakin motar ya iso daidai lokacin sunfito cikin motar hannu yabasa suka tafa yunus yace "kai ya inata magana yanzun baka jiba? khaleepa yace"Sry friend banji bane nadawo ne dud nagaji, murmushi yunus yai ya dubi heenduh dake tuquburi da gunguni ciki ciki yace
"headache barka da aiki fa sannu?yayi mgnr yana dariya,,ta lura da abinda yunus yakewa dariya wato jambakin fuskar khaleepan da lebunansa itama dariyar taji tai saurin barin wajen tai gaba ta tabarsu nan batareda tace komi ba tai shiga gidan tai sa'a kuwa babu kowa falon dan tai saurin hayewa samnsa danta dauko bands din kamar yanda yace taje ta dauko kayantan.
a can waje ko dariya sosai yunus ya tusa doctor din gaba yanai masa hardai ya qulu yace
"wannan dariyar haukan fa yunus anya kuwa brain dinka na lau?
daqyar yunus ya tsaigata dariyar tasa yace"Amman kai mugun dan iska ne wlh wato mune kake rainawa wayau da cewa ba soyayya CE tsakaninku da headache bako?
Ai ga alamun rashin so din nan mun gani a fuskarka duba madubi kaga", gaban khaleepa yaji ya bada dammm!!! damm!! sanda yaga fuskarsa dud shaitin bbki ne akai, ya rasa abunda zaicewa yunus saida qyar yace''dalla mlm dakata wannan bakin baby girl din wani abokina ce da muka hade dasu ynxun dudufa babyn bama ta wuce 7
years ba kake mun mummunan zato dan iska kawai"
dariya yunus yaqarayi bayan ya zari key din wata mota daga cikin keys din motocin gdn dake jikin key din motar da khaleepan suka dawo yanzun.
dubn khakeepa din yai yace''oh koba baby girl ba nixaka rainawa hnkali knn, hm ga baby can ai headache malam" yayi mgnr yanai masa dariya sannan ya dauki motar ya fuce.
dasauri khaleepa ya dauko hankicerp dinsa ya goggoge fuskar yana zagin yunus a ransa a cewarsa bai fada masa tun wuri ba kn heenduh ta lura baisan itace ma first ba wajen ganin inda itace tasa.
maida hankicerp din yai aljihu sannan ya shiga falon tareda hayewa saman sa aiko suka gabza karo da heenduh da tazo fitowa, sosai taji zafin karon takuwa wage baki knn zata fasa qara aiko yai saurin ida baya da ita zuwa cikin dakin tareda rufe mata baki ya fizgota zuwa cikin wasu Cotton's din dogayen labulayen dake jikin bangon dakin nasa suka lafe a ciki saka
makom muryar momyn tasa da sukaji itada Hjy Hadeeza sun shigo dakin.
cikin dabara ya saka wayarsa silent daidai lokacin ne Hjy firdausey tace
"aaha kingamin ikon Allah badai bai shigo dakinba?, Hjy hadeeza tace''ah bayanzun yashigo da motar saba lokacin muna garden ba?
"to babu shakka fita yasakeyi ko a qafa inda dai bainan" cewar Hjy Firdausi din bayan ta bude qofar toilet taga bai ciki.
zama sukai bisa gefen Mirrow Hjy Hadeeza tace"wlh inci gaba da gaya miki aminiyas bakiga yanda yaron nan ke dafifun shiga gidan matsiyatan mutanen can ba danko dazun tare na gansu da ita yarinyar nan heenduh, hmm wlh kuwa aminiyas kisan matakin da zaki sake dauka kan lamarin nan danda alama yanda yake manne mata da ace yasan cewa yarnyar nan matarsa ce ita Allah kuwa ina mai tabbatar miki dasai dai kiyi haquri dan gaba daya janye masa hankali zatayi da wannan shegem
Iyayen nata na kankanba itaga mai miji"
Hjy Firdausi tace''aiko billahel azeem uban kuturu ma yai kadan dan su Kansu iyayenta da suka San da auren nasu basu gigin fara fallasa shi duba ga yanda aka tsoratasu ga lamarun dazai faru dasu da kuma 'yar tasu gaba daya bare wannan shauran mutuwar yawale in aka masa qagen b'ata yaran mutane ai baqinciki ne zai ida qarasa shi koya kikace? snn itakuma yar banzar yarinyar hmmn barshi dai nafads miki plane din" dariyar mugunta Hjy Hadeeza ta saki sannan tace "wlh
Shiyasa nikesonki aminiyas bani mu
khashe nan suka tafa sannan Hjy Firdausi tace"muje can dakin nawa sbd my ida tsara yanda zakije wa maraqusa da saqon nawa inda kinga gobe ne tafiyar kada a tsara komi a lokaci qurarre asamu matsala dan nafison alhajina na dawowa asaka ranar auren zarah da maitsada na kinga shiknn mun ida zama daya daku zumunci babu kan gobe" ahaka suka bar dakin baccin sun rufe qofar.
Zufa sharkafffff sukayi baccin sun fito daga inda suka lafe jin abun suke kamar almara wai suna nufin sud'in ma'aurata ne koko ya'abun yake? tabbas haka sike nufi inda har gashi suna mgnr da ace sunsan sunada auren junan
su....cabb dijam danqari cewar heenduh bayan ta dubi sa tace"taya ne muka aurun ne?? wai suna nufin kai d'in miji na ne knn yanzun?
kwata kwata kasa mgn yai banda hautsinawa da brain dinsa keyi dn tsabar mamaki bayajin komi,, tsam yamiqe tareda kamo hannunta da qarfi, cikin mamaki take binsa da kallon yanda yake jan hannunta.
har suka bar dakin suka kuma bar gidan gaba daya babu inda ya tsaya face gaban baba yawale dake kan buzunsa yana jan cazbi.
durqushewa gabansa khaleepa yai bayan ya ruqo hannunsa cikin rawar murya mai shaking yace"baba yawale da gaske heendatu *matata ce*??????????,,
wani farinciki ne ya rufe baba yawale har yana cewa a ransa dad'ina da gobe saurin zuwa. kabbara yayi a fili cikin fara'a wacce rabonsa da ita tun da ran su baffa.
take yayi salati 100 a cikon zagayen carbin nasa sannan ya daga hannuwan
sa biyu Sama a fili ya dinga addu'oen godia ga ubangiji tareda fad'in "Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulilla ya ubangiji Allah nagode maka da baka dauki raina ba kamar yanda Nike roqonka harsai na bayyana gskiar lamarun nan ga

Please Login or Register in order to submit comment