Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ma" kwanciya yaga ismail yayi harda jawo malullubi yace "nikam yaya sanyin safiyan nan bada niba yau, dan yau banda exam sai
2:pm."
"ayya qanena kace yau sanyin nan zai qara mun yawa inna fita, dan koba komi indai muna tare dakai sai na kanji sanyin nan ya ragemun yanda kasan ana lullu6eni haka nikeji kuma nasan hakan ba komi bane yajazasa face jinina dake gudana tareda matuqar qaunar qanena shiyasa".
Zumbur kuwa ismail ya yakice mayafin tareda miqewa tsaye yace "muje na rakaka yaya, bai jira komi ba ya fice mukhtar yabiyo bayansa har suka fito tsakar gida mukhtar ya leqa dakin inno yayi musu sallaman saiya dawo su kuwa suka bisa da adduar Allah temaka adawo lpia. sun fara tafia a hanya mukhtar ya lura da yanda tsigar jikin qanen nasa ke tashi sabida sanyi sakamakon wata riga marar hannu da ya ke a jikinsa, yarasa yanda zai masa yasan koda yace ya koma gida bazai koma ba inda yace har wajen aikin nasu zai kaisa ma, gashi kuma yasan qanen nasa da tsananin jin sanyi dole ya gaqura har saida suka isa wajen aikin nasu suka tarar da oga daniel da wasu sauran ma'aikata rsirarru dan yanzun ake ta zuwa ko salis ma kansa bai iso ba.
shima ismail gaisheda ogan yayi cikin ladabi kamar yanda yaga yayan nasa yayi har zasu wuce oga daniel daketa kallon ismail cikin mamaki ganin tsabar kamarsa da mukhtar sun koma masa ma tamka
'yan tagwaye dan bada wani abi sosai mukhtar din ya d'ara ismail ga tsawo ba,
oga yace "ahh mukhtaru wannan brother naki ne ko?
cikin murmushi mukhtar yace "yes oga" oga daniel yace ''bamta6a gani nasa ba kuma to, mukhtar yace ''hakane oga dayake yana zuwa school ne amman yanzun haka dhis month ne suke yin final year nasu a school din"
dubn ismail oga daniel yayi yace "ok no problem amman mi dai hana qane nakan nan shima yajo nan muna aiki tale dashi muna bashi albashi nasa in ya gama jalabawan nasa?
cikin tsananin farinciki mukhtar yace "ok thankyu sir thankyu,, shima ismail yai ma oga godia sannan suka jiya suka bar oga din yana cigaba da aikin sa na seta body na wata mota da yake gyara.
har inda su mukhtar suke aikinsu sukaje sannan cikin fara'a mukhtar yace "kaga amfanin adduar iyayenmu akan mu ko q'anena? kaga zuwanka alheri ni anan inda kaima gashi ka samu aikin kamawa, cikin murmushi ismail yace "hakane yaya na shiyasa kullum muma muke masu addu'a kamar yanda suke mana, amman yaya burina a rayuwa shine inganni a class ina koyar da students lesson wato teacing to kuma gashi ban samu ba inda na samu wani aikin" yaqarashe maganar fuskarsa tadan canza,, dafasa kad'an mukhtar yayi yace " wannan dinma daka samu ka godewa Allah q'anena, dan wlh wani ma Yana cen bai samu iriyar wannan dinba, batun son aikin teacher naka ni kamanta buri na ne? kallonsa ismail yayi a ransa ya tunano tun suna qananu kowanen su yakan cewa itayensu ga abinda yakeson zama inya girma, iyayen sukan fara da tamvayar yayan nasa mukhtar akan wane buri ne dashi na aiki idan ya girma, saiyace shi burinsa inya girma tasami aikin government yagansa a babban office nasa yana aiki tareda samun albashi maqudai wanda zai dinga kai su baffa da inno mecca cikin jirginsa da ya siya domin su da qanensa.
shikuma ismail saiyace " nikuma baffa so nike inna girma burina shine na zama malamin makarantar boko, nima inga ina koyarwa kamar yanda malamin mu ke koya mana yayinda yake mana rubutu da alli ga allo, insun fad'i hakan iyayen kan dinga bunsu da adduar cikan burin nasu na alheri ga rayuwa.
ta6asanda mukhtar yayone ya maidosa daga d'an balaguron tafiyar tunanin da yayi, ya sake maimaita masa da cewar " kamance ne q'anena? girgiza kai ismail yayi yace "ban mance burinka ba kaima yaya" mukhtar yace "to danmi zamu zauna babu abinyi alhalin Allah ya bamu wani? kawai kazo ka fara koyon aikin da zaman da zakai tayi in yaso kana aikin kana kai takardunka neman aikin teacing din a haka saikaga Allah yasa an dace wataran kamar yanda nima ban fidda tsammani ba, kaga daga zarar mun samu offer ta samun aikin aikaga sai mi saki wannan mu tafi can koya ka gani q'anena?"
miqa masa dunqulallen hannun sa ismail yayi shima mukhtar ya miqa masa nasa sukai πŸ€œπŸ»πŸ€›πŸ»ta'adar su sannan daga bisani suka cafke hannun juna🀝🏻sukai musabaha, cikin dariyar farinciki ismail yake cewa "hmmβœ”idear yaya na,, dariya mukhtar yayi shima baice komi ba ya cire jibgegiyar rigar sanyin dake jikinsa ya tsaya dagashi sai singlet kawai sai 'yar rigar aikinsu dake saman singlet din kawai.
mukhtar yayi hakanne danya kare qanen nasa daga sanyin daya lura yana addabarsa sakamakon qanqame jikinsa dayaga yanata yi tun d'azun, shi ya gwammace sanyin yai masa koma miye ajiki dadai ya ta6a lafiyar qanen nasa dan haka gudun kada ismail ya zargi wani abu ya sashi cewar "q'anena ka tafimin da wannan sweater din tawa gida ka ajuyemun dan banjin dad'in aiki da ita sabida nauyi" cikin tsananin mamaki ismail yace "to yaya yakuma zakayi da sanyi?
konaje gida na d'auko maka tawa qaraman wannan ne kasa? "
"a'a q'anena hakanma yayi ai, yanzun dai zan yi aiki kaje gida haka, Allah sarki dudda ismail baisan ta kan aikin ba sai yace " to yaya gwadamun yanda kuke aikin nima saina tayaka ko? d'agowa daga kwance qusan da mukhtar ya zuqunna yafarayi na wata taya ya dubesa yace "hmm kabari in lokacin koyon naka yayi zaka koya kaji ko q'anena? yanzun dai katafi gida dan Allah kaga sanyi fa"
badon ismail yaso ba yasashi furta kalmar ''to taya" mukhtar yace "yawwa dan qanen" muryan salis sukaji a bayansu yana cewa "ah yau baqon student mukai knn?"
murmushi ismail yayi cikin girmamawa ya gaisar da salis din ya amsa,ya dan qara jimawa sannan ya wuce gida sakamakon uzzurawar mukhtar da yai akan ya tafin.
bayan tafiyarsa ne mukhtar ya dubi salis dake cin waina da miya wacce yayo musu guzurinta daga gida yace "yau narigaka zuwa abokina"
bai samu salis ya amsa masa ba saida yakai komar wainar cikin bakinsa ya hadiye sannan yace "bismillah fa kasan ban jira nidai Indai akan ciki nane shiyasa kan na fara dumamuqan wadannan qarafan saina cika tumbina tsaf tsaf sannan na q'addamar musu a lafiye wallahi "
mukhtar yace "to nidai kam yanzun bannajin yunwa ci kawai ka ajiyemun nawa sai anjima naci"
salis yace "to lpia lau, nima abinda yasa na taushe hannu bari nai mama ta qarasa ida wainar sannan kuma daga nan na ajiyeta gidanku da mashin dina saida na shiga na gaisar da inno sannan kuma na yo nan".
wani d'an siririn murmushi mukhtar yayi yasan maman salis taje gidan nasu ne dan maganar sa da firdausey, hankali kwance yake tafiyar da aikinsa dan yasan baida matsala ga batun inda baffa ya daidaita komi yau.
hakan kuwa ya farun bayan maman salis sun gaisa da inno nan sukaita labarinsu har ismail ya dawo gida shima ya gaisheta sannan ya wuce dakin su, jiyake kamar ya jawo gobe tazo ko zai samu hankalin sa ya qara kwanciya daganin masoyiyar tasa da kuma samun amsarsa gareta zuwa garesa. sai gab da maman salis zata tafi har inno ta rakota nan tsakar gida sannan ta dubi inno tace
"nace inno daman tambayar ki nike sonyi,,,,,? shin da saninki mukhtar yafara neman auren yarinyar nan kuwah firdausey d'iyar meron tsimbe matar mlm zayyanu mai almajirai ? dudda halin mamanta kuwa marar kyau? bakkwa gudun nan gaba ta haifar muku da tarwatsewar iriyar wannan kyakkyawan ahalin naku mai cike da tsantsan son junanku? to wlh basuda kirki ko kad'an mutanen dan bai dace ace kamar mukhtar mai mutunci da d'a'a yaje neman aure wajen mero ba, ni na d'auki mukhtar kamar salisu ne, dan haka dud wani abu da nasan zai kawo cikas a rayuwar sa gameda danginsa bazan so shiba, shine nace bari nazo naji ta bakinki shin da sanunki koko?"
haq'iqa jikin inno ya qara yin sanyi dajin bayanan ta game da mero, tabbas kuma tasan gskia maman salis ke fad'a, dan mero kam abin gudu ce ga al'umma saboda munanan halayen ta maras kyau wanda babu wanda bai sansu ba kaf anguwar.
to amman kuma yaya zatayi inda har mlm ya amince wa batun an gama mgn?.
tuni zuciyarta ta shiga tunane tunane na anya bazata canza shawara ba kuwa?! daman tunda mukhtar yayi mata maganar auren firdausey tun jiyan nan gaban ta keta faman dukuwa kamar kamarmi, jitake a jikinta kamar wani babban al'amari marar dad'i yakusan kusantowa garesu a rayuwarsu haiq'an,,,,!


*Xexen Fasaha*
[1/17, 3:10 PM] Xainab Documen: . πŸ‘πŸ‘
πŸ₯‘πŸ₯‘
πŸ‘πŸ‘
*DA SAURAN KALLO !!!*

Story and writing
by
Xayyneb πŸ’€πŸ’€

Fasaha online writers f. o.w.

*🌳imparting valuable knowledge and entartaiment is our concern*🌳.

-https://www.facebook.com/Fasaha-Online-Writes-751775151851852/?referrer=whatsapp.

πŸ‘πŸ₯‘πŸ‘
πŸ…Ώ1⃣0⃣
*I* nno takusan munti uku cikin tunanin mafita maman salis ta ta6ota tace "in kuma kina ganin babu matsala a ganinku to shiknn babu komi Allah sa hakan kuma shi yafi alheri"
har zata wuce inno tayi saurin kamo hannunta tace
"tsaya kiji innar salis, dakatawa tayi tana kallon inno tace " to shikenan ina sauraranki rabi'a"
inno ta girgiza kai tareda sakin qarfaffan ajiyar zuciya sannan tace "maganar da naiwa mlm knn ga jiya gameda hakan wlh, dan nima Allah ne shedata ina matuqr shakkun mero da jinsinta, amman kinsan kowa da tunanunsa, shikuma mlm a inda yake nunawa bamai yi sai Allah, aure nufin Allah ne, dan haka a fawwalawa Allah komi babu abinda zai faru insha Allah, harya ke cewa yaji ai dud abinnan da ake fada gameda ita uwar 'yar a anguwar toshi bai ta6a jin komi dangane da ita yarinyar ba na wani hali marar kyau knta, ga alama wai bata d'auko halin ita mamanta meron ba" kama ha6a mamar salis tayi tace "a ina mlm Abdallah yaji wannan zance na iriyan gskiyar halin yarinyar? ta6 gskia kowa kuwa ya fad'a masa hakan ba shakka bai masa adalci ba ya fad'a masa san ransa ne kawai, amman dai shiknn, ni bazanyi ta jayayya ba inda shi mai gida da kansa ya goyi bayan auran ai babu matsala, Allah kuma ya bada zaman lpiar kamar yanda muke fata d'in, nina wuce sai anjima" daqyar inno ta had'iye wani maq'alallen yawu tace"aminn maman salis ngd sosai saina zagayoki"
ahaka maman salis ta wuce tana mai fatarwa mukhtar d'in zaman lpia a gidan auren nasa idan Allah ya nufi auren nasa da ita firdauseey d'in.
zama inno tayi saman tudunkar d'akin nata dake kusa danasu mukhtar d'in tayi tagumi dan gaba d'aya kwanyarta a tushe take da ga tsoro ga tunani.
Is'mail dake zaune cikin d'aki shima kuma yaji komi da suka tattauna da maman salis, jin shirun da yaji ne ya tabbatas mata da fitar maman salis d'in daga gidan nasu, fitowa yayi shima jikinsa a sanyaye, dan harga Allah yana q'in dud wani abu dazai raba tsakaninsa da d'an uwan nasa komi yeshi kuwa, amman kuma yafi son ganin farincikin d'an uwan nasa akan nasa farincikin, dan haka yasha alwashin bazai ta6a nunawa kowa na gidanba baison auren firdauseey da yayan nasa danshi kansa yanajin labarai wajen abokansa gameda halayyar firdauseey da mamarta, inda suke cewa masa wlh ba fata ba in ba'ai sa'a tsaf firdauseey da uwarta zasu iya janye musu d'an uwa, danma sauqinta shi mukhtar din bamai kud'i bane aida abinda suke fad'a masa saiyafi hkn, cewar abokan nasa, shiyasa tun lokacin shima jininsa yake shaye ga batun, basaja kawai yake bai bari a gane,
Inna dake zaune saiji tayi an dafa gwiwowinta an zuq'unna gefenta.
duba takai wajen da idanunta, ismail ne yace" inno dud naji komi gameda maganarku da maman salis da wannan zan ce inno kedai kibi mgnr baffa kamar yanda yace insha Allah babu abinda zai faru ga auren nasu sai alheri to muma kuma muna masu fatan hakan inno,dan Allah kuma ki daina damun kanki kan batun" sauke ajiyar zuciya tayi koba komi taji dad'in tunasarwa da d'an nata yai mata ga lamarin, da haka wani sabuwan ajiyar zuciya din ta sake saki ta dubesa sosai cikin fara'a tace "madalla da d'a na gari Ismail, qwarai naji dad'in hkn kuma ngd Allah shiyi maku albarka dai gaba dayan ku" "aminnn inno nima bari naje na karbo littafina wajen nuhu clasmate dina ne so nike na dubasa nima" inno tace shiknn to adawo lpia Allah shi taimaka kuma" haka ya wuce bayan ya zura takalmansa yana fadin aminn inna.
gashi cikin ikon Allah har ranar da zaunab ta dibarwa ismail akan ya dawo tazo, tun safe yaketa zumudi ayi magrib koya tafi, I mukhtar kuwa sai dariya yake masa yana fadin "ina ruwan sabon shiga"
shima dariyar ismail ya mayar yace" baji yaya komi zakace, dan nasan yanda ka saba nima hakan zan saba"
koda magrib tayi yaje wajen Zainab itama cikin kunya ta ke maida masa raddin kaunar da take masa, ay farinciki tuni ya mamaye zuciyar ismail, baibar wajen ba saida ya tabbatas daya qara dasawa zainab tsantsar qaunarsa a ranta, daqyar suka rabu a ranar.
haka ta kasance dud bayan kwana 2 sai yaje zanje, tuni firdauseey ta tseguntawa uwarta mero wai qanen mukhtar ke zuwa wajen zainab, anan uwar ke ce mata "to miye ruwanki? mi na sama yaci bare ya sakowa na qasa? sai ki bari muga iya gudun ruwansu, I qarshenta dai yace zai aureta kuma saimi danya aureta,
ni daman ai nafison matsiyatan suzo nmn aurenta dan na tsani inda Zainab zataje tai aure ta huta ta barki cikin wahala, to qwamma dud ku auri matsiyatan tare inda shima ke kika nacewa ma"
tuni firdauseey ta zunburo baki tana mai dana sanin fad'awa uwar hkn dan gashi itama har ta samu nata rabon wulaqancin, nikam nace kamataddini ta danu ay.
haka rayuwar taita tafiya yanzun mukhtar da Ismail tare suke zuwa zancenma kowa ya ke6e da tasa in lokaci yayi su dawo gida kuma.
tuni har mlm Abdallah yaja abokinsa baba yawale sunje sun kai kudin neman aure ga yaran nasa an kuma saka rana wata 2, dayake yanzun shima ismail d'in yana gama exam d'in ya soma bin yayan nasa zuwa aikin kanikanci yana samun abun rufawa kai asiri, wnda a cikin albashin ne har yakewa Zainab siyayya ta kyaututtuka da dama kamar ynda inno dinsu ke cewa su yawaita alhero, dan ance sadakin so kyauta.
tuni har baffa ya siyarda gonansa ya siyi gidajen 'yayan nasa guda 2 kamar yanda yace, can qarshen layinsu baffa gidajen suke.
har an musu fante dayake bikin Saura mako daya yanzun.
yanzu biki ya rage saura kwana biyu danginsu baffa da inno 'yan yola dud sunzo nan da nan aka shiga hidimar biki gadan gadan babu kama hannun yaro.
anyi biki lpia an gama lpia amare sun tare a gidajensu,
yau kimanin wata d'aya kenan da bikin nasu,
yau ta kama ranar juma'a ne da safe misalin qarfe 7:50 Am, mukhtar ya gama shiryawa cikin uniform dinsa sauri kawai yake yaje ya karya dan gudun kada mukhtar ya bugo masa waya kanya fito su wuce, yana fita ya tarar da firdauseey din a madafi tagama sheqa kunun gyad'a tana juye wa cikin plastic yaja ya tsaya cikin murmushi yace "amarya bakkya laifi, miqewa tsaye tayi, tayi dariya tace
"badai fita zakaiba baka karya ba, dan tabe baki yayi yace "sauri kawai nike gudun kada ismail ya jira ban fito ba, tabe baki tayi a ranta tace "nina tsani Ismail dinnan wlh kuma ba kowa yaja masa hakan ba face shegiyar yarinyar nn Zainab, amman a fili sai tace "gskia bazaka fita ba sai kayi kalaci" bata jira komi ba ta miqa hannunta ta riqo nasa suka koma d'aki ta zuba masa kunun gyad'a din yasha sosai sannan ya fita waje anan ya iske Ismail d'in waje cikin mamaki yace "ah qanena kana nn ashe? mimakon kamin waya na fito kokuma ka shigo"
murmushi Ismail yayi ya tuna jia daya buga waya firdauseey ta dauka kai tsaye tace " kada ya damar mata miji inya shirya ya fito,lokacin mukhtar din wanka ya shiga baima san an bugo ba, kuma tana gama wayar ta goge kiran.
shiyasa kawai yau yaqi kiran nasa gudun kada a maimaita 'yar gidan jia,, shi bama wannan ba farinciki kawai yake sakamakon kiransu da akayi interview na sabbin malaman makaranta da za'a dauka jia da aka nuno a labarai, haka suna tafia a hnya yake bawa yayan nasa labari, qwarai mukhtar ya matuqar yin farinciki yahau yiwa qanen nasa fatan alheri.
har suka isa gidan su( dayake kullum sai sunje gaida iyayen nasu sannan suke wucewa aiki. )
nanma koda su baffa sukaji maganar interview din sun yi masa addua matuqa nan suke cewa kaima mukhtar Allah ya cika maka burunka ns samun aikin d kk son" aminn baffa cewar su mukhtar d'in.
daga nan suka wuce wajen aiki.
cikin ikon Allah ismail yaje interview yakuma samu nasara a inda ya samu aikin koyarwa a wata bsbbar makarantar secondary schcol,
kankace miye tuni harya fara zuwa aikinsa da yake fannin social studes yake koyawa kuma ga albashin nasa har kusan dubu 30 ne zai dunga dauka a lokacin.
wayyo mukhtar yaji dadi harda hawaye dan ganin yanda dad'adden burin qanen nasa Allah ya cika masa shi.
wata biyr knn da fara aikin Ismail, dud inya kwashi albashin sa kuwa komi zai saya na abinci kashi uku yake siyansu komi yawansu da tsadarsu kuwa, kashi daya yakaiwa su baffa kashi daya ya baiwa yayan nasa sannan kuma kashi daya ya ajiye gidansa, yasamu qarfin gwiwar yin hknne daga shawarar da Zainab matarsa ke basa masu kyau na maimakon yadinga basu kudin qwamma yasai musu abinci, harta qara da cewa "kuma teacher ( dayake haka take ce masa mlm tunda ya fara koyarda karatu itama)saika dunga bawa yaya mukhtar koda dubu bibbiyu ne bayan ka siya musu abincin dan kaga shima iyalinsa, koba komi yanzun nauyi ya qaru shima inda yanada iyali,
haka Ismail kuma yaji dadin shawarar tata, dan haka saiya bari ma dud inya gama siyayya to kudin da suka rage masa suma uku yake kasasu yabawa su baffa kashi d'aya
mukhtar kashi d'aya shima saiya riqe kashi dayan, da basu amsar kudin dole tasa suke amsa sakamakon kukan dashi Ismail din ke shirin yi musu in sunyi nufin qin karbar, firdauseey kuwa baqinciki kamar ya kasheta danjin zafin budin da Allah yaiwa Ismail da Zainab qanwar tata dudda iriyar alheran da ismail ke masa kuwa sam batta gani sam bnda huznu babu komi a ranta da'iman hk tk.
ahaka har Ismail ya d'auki shekaru biyu da fara aikinsa na teacher.
yau ta kama ranar litinin da misalin qarfe biyar da rabi na yammacin ranar
da sauri mukhtar ya shigo gidan nasu dan dama yasan ismail na can, yana shiga kuwa ya taras da ismail shida inno da baffa zaune a tabarma suna fira,
yana shigowa ya rungume qanen nasa yace "baffa inno qanens kutayani murna yanzun aka turomin text na anyi accepting dina a matsayin ma'aikacin government a wata babban ma'aikata na fitar da tsirran amfanin gona da sauransu, dan yanzun nan daga can ma nike, sunce takarduna sunyi matuqar kyau sosai, kai qanena kaga ofis din kuwa? ga tv plasma da easy komi baja baja fa, gashi sati mai zuwa sukace zan fara zama kujerar office din nawa dan gudanar da ayyuka. kai alhamdulilla"
tuni ismail ya daka wani tsalle ya qwaqwume yayan nasa yana kukan dad'i yake cewa"dan Allah yaya da gaske? Wayyo ni Allah Alhambdulilla daka cika mana buruknmu a rayuwa, yana maganar yana qwallan murna jikinsa har rawar farinciki yaketa yi.
sosai suka rungume juna suna kukan farinciki.
baffa da inno nan take addua sukaita kwararo musu akan tabbatuwar alheri mai daurewa ga lamarin ayyukan nasu.
sai gashi kuwa sati na zagayowa mukhtar ya d'are kujerarsa ta office ya zauna,cike da adduar iyaye ya fara gudanar da aikinsa cikin nasara da qwarewa...



Kuyi hqr busy nk shiyasa kuka jini shiru,
Ynxunma n smu likaci ne

*Xexen Fasaha*
[1/17, 3:10 PM] Xainab Documen: πŸ‘πŸ‘
πŸ₯‘πŸ₯‘
πŸ‘πŸ‘
*DA SAURAN KALLO !!!*

Story and writing
by
Xayyneb πŸ’€πŸ’€

Fasaha online writers f. o.w.

*🌳imparting valuable knowledge and entartaiment is our concern*🌳.

-https://www.facebook.com/Fasaha-Online-Writes-751775151851852/?referrer=whatsapp.

πŸ‘πŸ₯‘πŸ‘
πŸ…Ώ1⃣1⃣
*W* asa wasa yau kimanin wata uku knn da fara aikin mukhtar, buhunnan shinkafa dasu kuskus macroni superghety indomi sha'er da dai sauransu haka mukhtar ya cikawa su baffa d'aki dashi,kuma haka shima yaje gidan ismail ya cike masa waje ma'ajiyar abincinsa dasu taff,
hatta abokan baffa su baba yawale saida suka shaida da arziq'in mukhtar dan saida yayi musu kyauta suma,
kan kace mi tuni anguwar ta dauka labarin cewar mukhtar yayi kudi,
alherin mukhtar bai yankewa ga jama'a shiyasa kowa zakaji yanda yake yabon kirkinsa a anguwar sukance sam baida qyamar marassa shi kamar yanda sauran masu kud'i sukeyi,,
tuni mukhtar ya sabarwa kansa dud ranar juma'a bayan antaso masallaci zakiga ya zauna a qofar gidansu shida ismail yana bada sadaqar Dari biyar biyar yayinda ismail din ke tayasa,, bazai bar wajen ba har sai ya tabbatar da kowa kuwa ya samu sanna.
salis yaji dadi qwarai da arziq'in abokinsa da Allah ya basa shi a cikin dare daya shiyasa shima mukhtar yaso salis din yabar aikin da yake yazo nan ya basa wani aiki ya dungayi a ma'aikatarsu amman sam salis yaqi yarda danshi a ganinsa mutane zasuyi surutu gameda hkn shi bama wannan ba yafiso ya samu aiki da qashin kansa kamar yanda shi mukhtar din ya samu kunga kowa saiya tsaya kan qafafunsa,
dan salis yana tsoron ai masa alafama gudun juyin rayuwa iriyar na mutumin yau. shima yasan bai fidda rai ba, inda shima ay ya bada takardunsa tuntuni cigiyar aiki gun wani qanen mmnsa dake bauci shima ma'aikacin government ne, danma ya riga bayarda cigiyar aikin nasa akan mukhtar daya bayar daga baya,
mukhtar kuwa ganin salis yaqi amince wa hakan ne ya sashi haq'ura dole amman kam yana masa kyaututtuka matuqa dan kaf fadin garin kaduna baida babban aboki sama da salis.
yau lahadi ta kama weekend kowa yana gida babu fita, mukhtar ya na zaune a dakinsa yana faman cike wasu daga cikin takardunsa n office, dan kam gaba daya hankalinsa ya tafi ga wajen lissafin abubuwan da yakeyi, saiga firdauseey ta fito daga quryan daki jikinta sanye da wata atamfa super English ta zauna kusa dashi fuskarta ahad'e ta dubesa tace "yalla6ai ina son magana dakai" bai dago kai ya dubeta ba saida ya ida had'e dukkan calculating din sannan ya kauda document din gefe ya juyo y zuba mata idanunsa yana kallonta cikin wani murmishi, hannunsa yasa ya kamo nata yace "ehm emmm to sarauniyar mata, amman kafin nan wai miye sirrin ne? nike ta jinki zam zam haka kwanan nan?, gashi kuma kin d'anyi haske dudda kalarki choculate color ne amman ta q'ara smooth fa sosai, kodai da ajiyar baby nane anan?" yayi maganar yana goga kuncinsa a saman cikin nata cikin wata fara'a.
ture kansa tayi tace "nidai ba wannan ba dan Allah ka saurareni dan maganar nada muhimmaci sosai,, tuni ya maida nutsuwarsa gaba daya gareta yace
" to ina sauraranki"
saida ta qara bata fuska tace "yanzu dan Allah yalla6ai dud iriyar wannan arziq'in da Allah yai mana yanzu mu ba abin kunya bane aganmu cikin iriyar kalar wannan dandaqaqqen gidan ba? dud gurori a cikin wajensa?
kuma gaskia byn haka ma gidan nan yayi kadan dan inna haihu taya mutane zasu wala a cikinsa ma tukunna dai wai?"
sai lokacin ya yi saurin cewa " oh my god,, are you pregnant my Queen? kinada ciki ne daman baki gaya munba?, yayi maganar cikin mamaki,, wani dan murmushi tayi tace "jia munje asibiti nida mamana sakamakon zuwa danai gida daga naci abinci naita amai kamar zan mutu wlh lokacin shiyasa hankalin maman ya tashi tasa mukaje asibiti a lokacin anan doctor ya min gwaje gwaje har suka tabbar da ciki ne a jikina d'an kimanin wata shida da kwana hud'u"
da sauri mukhtar ya rungume ta yana firda qwallan dad'i tareda godia g Allah da sauri ya ruq'o ta jikinsa yana fadin "firdy na mikeso na miki wanda zaisa kiji dadi dan wannan kyakkyawan

Please Login or Register in order to submit comment