Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abinda yace knn sannan yaci gaba da fad'in "ina nufin yayana mukhtar yazo wajen yayarki firdausey ne?"
sai lokacin ta gane zanxen nasa tace "eh ina tunanin ma kuma ya tafi dan dana fito d'azun nan na barsu da yaya firdausey din.
har zata wuce ciki yayi saurin cewa "bakiji ba fa"
shi kansa yarasa miyasa ya tsaidata sai sai yasan cewar zuciyarsa na masa kwadayin sake son ganin fararen idanun matashiyar budurwar sosai.
juyowa tayi, karaf idanunsu suka sarq'e ana juna saida gaban kowanensu ya buga damm!!!
sannan cikin kunya zainab ta mayarda kanta qasa jijinta na rawa rawa da batasan miya jaza mata hakan ba a take.
"dan Allah zaki ce kina sona nima innace miki ina sonki? bansan miyasa naji zuciyata ta harbu dake ba dudda ban ta6a ganin kiba sai yau, kawai naji ina sonki ne har qasan raina wlh da gaske nike ki yarda dani, gashi kuma ko sunan ki ban saniba amman har kikayi qoqarin daukemin zuciyata haka urgently?
a kunyace sosai Zainab ta boye fuskarta cikin hijab ita knta taji abunda yaji a zuciyarta tun kallon junansu da sukayin nan nan take, to mike nn hkn? itama tana sonsa knn?
Jitayi yasaki Murmushi yace " ashe rabo ya tasoni gada gida neman yayana wajen gimbiyarsa ashe nima da rabon nayi gamdakatar da tawa sarauniyar kyawawan a wannan kyakkyawan daren knn? da sauri zainab tanufi cikin gida dan wata sabuwan kunyar tasa ke qara shigarta intaji kalaman bakin nasa zuwa gareta.
da sauri yace "dan girman Allah ki tsaya kiji" cakk kuwa ta tsaya daga inda take kuwa baifi ta qara taku 4 ba tayi cikin gidansu ba.
har inda take yazo ya tsaya sannan yace " kibani amsa dan Allah ko na samu na zauna lpia da zuciyar nan tawa yau" kuma dan girman Allah ki fada mun sunani nidai sunana Ismail qanen mukhtar saurayin yayanki firdausey, a tsananin kunyace tace "sunana zainab maganar amsar ka kuma ka bari sai nan da jibi ka dawo kaji" daga haka ta ruga da gudu ta shige cikin gidansu ya bita da kallon murmushi shi knsa yasan ya samu karbuwa sosai a zuciyar zainab kawai da iriyar abinnan ne na mata masu fulako na maimakon a baka amsa kai tsaye sai an wainaka sannan,
daqyar yabar wajen fuskarsa qunshe da murmushi na shima yai yayi budurwa Lallaikm yaya zakasha labari yau.
zainab da gudu ta fad'a bisa tabarmar dake shinfede qasan dakinsu tana sauke nunfashi maman kuwa cewa take "ke zainaba lafiyanki lau kuwa?
da sauri zainab ta daidaita nutsuwarta ta dubi maman tace
"laa babu komi mama, " a'a Zainab indai da wani abun fad'a mun kinsan yanzun babu sama da ni wanda zakiyi maganar sirri dake dashi dan haka ki fad'a mun" saddar da kanta Zainab tayi qasa cikin kunya tasake cewa " to mama ki bari sai abun ya daidaitu zakiji koma miye" tana gama fad'in hakan tayi kuryan dakinsu da sauri,
murmushi mama Jameela tayi kawai a zuciyarta tace " to Allah shi tabbatar da mafi kyawun alherin " sai kawai taji daga bakin qofar dakin nata ance "mtsss muna funci dai uwa da 'ya matsiyatan kawai baku iya koman kuba face munafurci a d'aki"
muryan firdausey knn da mama Jameela taji sai lokacin tayi saurin kallo bakin qofa taga wucewarta tabita da kallo wato yanzun ma harda la6e ake masu kenn?
"Allah shi kyauta muku" cewar mama Jameela taci gaba da goge kayansu.
firdausey kuwa tana shiga dakinsu saman cinyar meron tsimbe uwarta ta kwanta tana faman zage zage mero tace "miya faru ke kuma? "nida wadannan marassa mutuncin mutanen mana mama, wai dan tsabar iskanci d'azun muna waje sanda mukhtar yazo saiga wannan shegiyar yarinyar zainab ta fito tawani maqe wannan mummunan qaraman muryan tata da wannan shegunayen farin idon nata tana wani yin rawa dasu take gaida mukhtar har yana wani yabawa da ita shikuma"
mero ta zabura tace "kam uban malhwar hular mlm zayyanu,, kujimin 'yar iskar yarinya hasararriya, toke kuma dan ubanki daya haifeki uwar wa tasa baki dauke mata haske ba (mari) a lokacin? firdausey tace "haba kekuwa mama yaya zan mareta a gabansa? ai saiya gasgasta gaakiyar rashin mutuncin namu da mutane keta fad'a masa ay ko? meron tayi shiru tace "kumafa hakane kinyi dubara kuma, abarma wannan zancen matsiyatan ni yanzun, miya baki yau shi mukhtar din dayazo?
tsuke baki tayi tace
"ke mama wlh kin cika son abin duniya da yawa Allah kuwa ( kuji rashin tarbiya d'a ya iya furtawa uwarsa wannan mummunan kalma hankali kwance.
nikam nace duniya dai firdausey)
daq'uwa mero tai mata tace "dan uwariyonki waye bai son alheri koya baki kin b'oye dan nasanki da mugun hali?"
"nifa wlh mama babu wani abunda ya bani ki yarda man, ni haushinsa ma naji wai d'azun yaje ya saida wayarsa ya siyawa qanensa handout wlh mama bakiji ba kamar na kashe kaina naji sanda yake fad'a mun abinnan,
mama mero tace
"ki iya takunki fa firdausey kada ki kuskura ki nuna masa kina jin zafin alherin da yakewa wani nasa dan ina mai tabbatar miki zaki rasashi yanda na fahimci mukhtar bai daukar tozarci ga wani bare kuma ahalinsa ma, dan haka kiyi musu kwantan 6auna har mu samu ayi auren kinga daga nan komi kikayi dai dai da kene fatan kin fahimce ni? (kuji mummunan hud'ubar uwa ga 'yarta wacce zatakai gidan miji? Allah tsaremu da iriyar halayen iyayen nan masu 6ata 10 2 bata gyaru ba).
kashewa sukayi da uwar firdausey cikin dariya tace "kai kina masifar wuta mama wallahi kin iya komanki fa"
meron tsimbe tace "ahaf naci duniya ninan da kike gani ba qaramar 'yar bariki bace ninan da kike gani bata wasa bace ko ubanki marigayi wlh shima ya q'arda da halina dan kanya rasu kadanne daga cikin azabobin fitinonina ban kwankwad'a masa yashanye ba, danma ya mutu faqiri matsiyaci babu gadon uwar da yabar mana na arziqi, da yabar mana wani abun aida bnga tsautsayin dazaisa na auri zayyanu ba wlh da gida zan kama naita facaka ta da kud'i na zamo hajjaju dan zuwa mecca wlh akan kari dud hajji"
6ata rai firdausey tayi dan ta tsani zagin da mero kewa ubanta haka nan dudda ya rasun ma bazata shafa masa lpia ba ya samu salama.
lura da 6acin ran firdausey meron tayi tace "tofa an ta6o masu son uba ko? sai kiyi haq'uri ay kinsan dai bakina ba haila ne dashi ba komi yazo kan harshena na kowace iriyar magana ne tofa saina furzosa waje fit nike samun lpia"
"to amman mama inda ya rasu saiki qyalesa ai yamaji dabaqin cikin da kikaita qunza masa kanya rasu, kin korar masa mata da yara har kika d'ora masa hawan jini wanda yakaisa ga faralise ta samesa yana halin hkn ne har ya rasu haba mama ai masifar ta isa haka, dan ni dai gskia da inada wayau ne lokacin banbari kiwa babana haka"
banza mero tai mata taci gaba da cin kwadon tuwonta mai daddawa danshi akayi gidan da dare harda almajirai na mlm din.
"kizo kici abunci shine ya fiye miki da wannan shegen surutun naki marar ma'ana" cewar mama meron.
"nikam bazanci tuwon mai daddawa ba bakina yaita wari" mero tace "inye sannu d'iyar obama, zakiyi kwanan yunwa knn dan wlh ko sile bazan baki ba ki siyo abinci waje kici"
Firdausey tai komawarta quryan daki ta bude jikkarta ta fiddo wani dan qaramin lemon roba da biscuit tahau cin abinta tana kurbn lemonta hankali kwance.
koda mero ta shigo dakin ta iske saura kad'an lemon da biscuit din ya qare aiko takai musu wafta ta warcesu daga hannun firdausey din tace"dan ubanki ai bake kad'ai zakiji dad'in ba, tayi maganar tana mai tura biscuits din a wawagegen bakinta tana korawa da ruwan lemon ta ce
"anya kuwa firdausey zakiyi jinqai na in kika samu gidan nera kuwa?
"eh man mama ina mai tabbatar miki innayi kud'i kema kinyi su ai, dan sawa zanyi a gina miki qaton gida kema ki fantama a cikinsa.
hararta meron tayi bayan ta tillar da empty din robar tace "au a hakan kina 6oyewa d'akan kina danq'arar dad'i nikuma kin barni can da tuwo mai daudawa zakice hakan?
"wallahil azeemu da gaske nike mama ki yarda dani indai nayi kud'i kuwa zaki shaida hakan, banfa da kowa saike"
murmushin jin dad'i mero tayi dan tasan kimi firdausey ta rantse dashi tofa zatayi abun kuwa.
"yawwa d'iyata aminn to inko haka ne zaa wulaqanci da hura hanci dan tsab mlm zayyanu mai almajirai zai dawo nice mijin shine matar dukknsu suka bushe dariya har suna ta6awa.....


*Xexen Fasaha*
[1/17, 3:10 PM] Xainab Documen: πŸ‘πŸ‘
πŸ₯‘πŸ₯‘
πŸ‘πŸ‘
*DA SAURAN KALLO !!!*

Story and writing
by
Xayyneb πŸ’€πŸ’€

Fasaha online writers f. o.w.

*🌳imparting valuable knowledge and entartaiment is our concern*🌳.

-https://www.facebook.com/Fasaha-Online-Writes-751775151851852/?referrer=whatsapp.

πŸ‘πŸ₯‘πŸ‘
πŸ…Ώ8⃣.
*M* ukhtar kuwa suna rabuwa da salis gida ya wuce, anan qofar gidan yaga babansa da su baba yawale maqotan su, saida ya durqusa ya gaishesu sannan ya wuce ciki,, kai tsaye dakin su ya wuce ganin baiga qanen nasa ba yasashi tunanin koyana dakin innon tasu mafarin knn yasa kai dakin inno din bayan yayi sallama,
zama yayi ganin inno dun tana salla yasan shafa'e ne take yi, inno kam nada q'oqarin ibada hatta ta cikin dare kam bata shallaketa saita tashi tayi sallolin dare na nafiloli ta roqi Ubangiji Allah buqatunta na alheri akan mijinta da iyayenta da suka jima da rasuwa da kuma 'ya'yanta da kuma sauran jama'ar musulman Allah.
saida ta sallame ne ta yi lazuminta tareda addu'a sannan ta shafa ta juyo tana duban mukhtar d'in tunkan tace wani abu yayi saurin furta"inno ismail bayya gida ne? inno tace "nikam dai ban saniba mukhtar nida ina cikin d'aki, ka duba d'akin naku kaga bayya ciki ne?
"na duba inno ban gansa ba, " qilan ya dan fita ne to" cewar inno din.
"ga alama dai kam inno bayya gidan dn nima yanzun na shigo"
"halan daga wajen salisun kake taron tuzurai ko?
wai nikam mukhtar har yaushe zakusan kun girma kaida salisu ne har ku ajiye iyali kuma em? yanzufa ba kuba ko ismail da yayi aure da yana nan da iyalensa shima bare ku" mukhtar ya maida kansa qasa yana murmushi yace " nifa inno kin gane ko nafiso na fara samun aiki tukunna in yaso saina fara ginin gida dan matsalar matar da zan aura babu ita inda na sameta harma mun daidaita kanmu"
inno tace "rabani da wani zancen samun aikin nan mukhtar kaji, yanzun kana nufin zakaita zama ne har sai kasamu aiki zakai aure? wannan kam ba maganar ji bace, d'azun da safe bayan fitarku munyi magana nida baffanku cewa wannan d'ayar gonar tasa zai saida ta ya siya muku gidaje wanda aka gina guda biyu 'yan madaidaita, saurin kud'in kuma sai a baku kuyi hidimar biki dasu koba shikenan ba?
cikin sauri mukhtar ya dubi inno yace
"amman inno baffa zai siyarda gonansa tomi zai kama kuma? inda yanzun dai wannan gonar ita kad'aice tai mana saura fa"
Inno tace "mun tattauna akan wannan zancen shima, kaga ai munada garken awaki da raguna da kuma tumaki ko?, to akansu zai koma kasuwanci dud ran kasuwa yana kaiwa yana siyar da jariran da suke haifa insun tasa fatan ka fahimce ni?"
girgiza kai mukhtar yayi, matuqa gaya yaji dad'in hakan a ransa koba komi zai rayu da firdauseyn sa nan bada jimawa ba ya mallaketa mallaka kuwa ta har abada, kuma itama yasan zataji dad'i sosai inya fad'a mata manya zasu shigo cikin lamarin nasu.
dan haka cikin kunya ya ce "inno mun gode to Allah shi saka muku da alheri akan iriyar wnn kyautatawa da kuke mana muma kuma Allah shi azurtamu mu dad'ad'a muku fiye da yanda kuma kukai mana, Allah kuma shi jiqan iyaye"
cikin murmushi inno take furta "aminn, shima in ismail din ya dawo saika shaida masa hakan shima daganan in yanada wacce yakeson kaga da ya gama qarashe jarabawar makarantar sai a had'a ayi bikin naku lokaci day'a a huta, ko muma ma samu muga jikokin namu kafin muyi qaura daga duniyar,
jikin mukhtar yayi sanyi jin maganar da inno tai na mutuwa, dan haka sai yace"inno kikasan ma komu rigaki tafiyan ma? , Murmushi inno tai tace "kayya dai mukhtar babu wanda yasan *gawar fari* ay tsakaninmu, fatanmu dai Allah yasa mu cika da kyau da imani,,
sai lokacin mukhtar yasaki ransa yace "aminn inno,, amman ban tunanin ismail nada budurwa dan sai nikega ma tsoron matan yake bai iya musu mgn ma inno"
murmushi inno tai tace "miyasa kace baida budurwa to? yace "da kuwa yanada da nine mutum na farko da zan sani inno" dariya inno tai tace
"hmm komi zai iya canzawa lokaci day'a mukhtar,
kai bagashi kaima da banyi tsammani kanada budurwar ba daga ta6oka da zancen aure har kayi azarbabin fiddota to bare shi ma saurayi mai quruciya bisaga kai tuzuru?"
dariyar kunya kawai mukhtar yayi yace "baffa ya ta6a ganinmu wajen gidansu rannan amman na boye a ranan amman kuma jikina ya bani ya ganni inno fa shareware kawai yayi" yayi maganar yana 'yar dariya itama inno dariyar take sai daga bisani ta dubesa tace ''ince kai wacce kakeson auren nan kusa take dai ko?"
"eh inno nan qasan layinmu take ma ay, yarinyar gidan mlm zayyanu mai almajirai ce ma ai"
Inno tace "to to af kaddai ince Zainab d'iyar jameela,?
kai amman ko kayi sa'ar mace mai tarbiyya Allah yasa alheri....... "aa inno bafa ita bace,, mukhtar ya katse inno da fad'in hakan, tace "ikon Allah, tofa wacece a gidan knn? "
yace "inno d'iyar matar mlm zayyanu ce ita sunanta firdausey mamanta kuma meron tsimbe ake ce mata, da ita tazo gidan mlm zayyanu din dayake baban yarinyar ya rasu."
cikin tsananin fad'uwan gaba inno tace "mukhtar???! meron tsimbe fa kace?! amaryar mlm zayyanu mai almajirai? wannan matar da kowa yasan halin rashin kirkinta shine zaka jajibowa kanka iriyar wannan *babbar annoba* haka? to nikam dai ban yarda ba ban lamunce ba kamaji na fad'a maka kafita harkan wadannan mutanen marasa mutunci dan haka maza tashi ka bani waje kuma mlm zai shigo saina fad'a masa halinda kakeson tsoma kanka muma kuma ka tsoma mu a ciki wanda ba mai 6ullewa bane.
haka mukhtar ya miqe fuskarsa taf taf da hawaye ransa na masa zafi yabar dakin ya shiga d'akinsu, kwanciya yayi zuciyar sa na cewa "hoooo kaiko mukhtar miyajaka yin abinda har ran mahaifiyarka ya 6aci akan wata mace wacce batasan dukkanin d'awainiyar da mamarka tai dakai ba tun kana cikin ciki har zuwa sanda ta haifeka itadai kawai ta ganka da girman kane har kuka fara soyayya.
to kayi gaggawar samarwa kanka mafita,, a fili ya furta "kiyi haquri firdausey kiyi haquri na barki na barki kiyi rayu.... jiyayi an dafa sa ta baya,
da sauri ya goge hawayen da sukayi nasarar zuraro masa a kuncinsa guda day'a kuma yayi shiru.
Ismail ya zauna gefensa fuskarsa wacce ke ciki da farinciki amman ganin yanda yayan nasa keta sabbatun damuwa ne yasashi jin jikinsa yayi sanyi zuciyar sa nai masa babu dad'i kwata2.
"mike damunka yayana" ismail ya tambayesa,, amman sai ganin mukhtar yayi ya qaqalo wani sanyayyen murmushi yace "babu komi qanena ina ka tafi ne inata nemanka dana dawo,, girgiza masa kai ismail yayi yace "a'a yaya mukhtar dud yanda akayi akwai abinda ya faru dan girman Allah ka fad'amun mike damunka yaya na, wlh zuciyata har bugawa take ganin hawayen daka share a fuskarka yanzun" runtse idanunsa mukhtar yayi yajawo dan uwan nasa ismail yana firarda qwalla, rungume juna sukayi cikin rawar murya mukhtar yace ''q'anena inno bata amince mun na auri firdausey ba kuma ni na haqura da ita koda kuwa son ta zai zama ajali na kuwa bazan ta6a bujirewa inno ba wannan alqawali ne"
da sauri ismail ya janye jikinsa yana duban yayan nasa sannan yace"kuma baffa yasan da hakan? gyad'a kai mukhtar yayi yace "a'a bai basani ba" miqewa tsaye ismail yayi yace bari ma dawo yaya" da sauri mukhtar ya jawo hannunsa yace "ina zaka qanena kuma?
"yaya wajen baffa zanje in durqusa gabansa na roqesa akan ya lallashi inno tabarka ka auri za6in zuciyarka" murmushi mukhtar ya qaqalo yace "zauna nan qanena kaji" bayan ya zauna yasake dubnsa yace "qanena kaga inkajewa baffa da zancen nan inno zatai tunanin bata isa damu ba inda gashi mun kaita qara wajen baffa ko? shiru ismail yayi zuwa can yace "hakane yaya to kaikuma fa" Murmushi mukhtar yayi yace " mu kwanta hakanan qanena barci nikeji gobe in AllAh ya kaimu saimu yi maganar ko"
dubnsa Ismail yayi yace idan kuma har goben tayi baka bari mun qara tattauna maganar ba tofa sai nayi fushi dakai na tsawon minti day'a yaya" dariyan qarfin hali sukayi dukknsu bayan sun riqe hannun juna alamun amincewa.
badon yasoba ismail ya kwanta saman shimfidarsa shima mukhtar kwanciya yayi, daman yayi hakanne dan yasamu yayi kukansa a 6oye koya samu radadin zuciyarsa tai masa sauqi.
haka suka kwanta barci zuciyar kowa na masa saqe saqe.
washe gari dukkansu suna dakin inno bayan sun gama karin safe kamar yanda suka saba har zasu tashi suje su shirya baffa ya dubesu yace " ku koma ku zauna zamuyi magana daku" kowanne saida gabansa ya fadi tsakanin ismail da mukhtar, musamman ma mukhtar da yasan komi ma dai za'ace tofa akan sane baffa zaiyi maganar.!


*Xexen Fasaha*.
[1/17, 3:10 PM] Xainab Documen: πŸ‘πŸ‘
πŸ₯‘πŸ₯‘
πŸ‘πŸ‘
*DA SAURAN KALLO !!!*

Story and writing
by
Xayyneb πŸ’€πŸ’€

Fasaha online writers f. o.w.

*🌳imparting valuable knowledge and entartaiment is our concern*🌳.

-https://www.facebook.com/Fasaha-Online-Writes-751775151851852/?referrer=whatsapp.

πŸ‘πŸ₯‘πŸ‘
πŸ…Ώ9⃣.
*S* aida baffa ya d'an yi shirun daq'iqa biyu sannan ya sake duban kowa dake wajen da duba, sannan daga qarshe ya tsaida fuskarsa kan mukhtar yace
"mukhtar kana jina kuwa? cikin mummunan fad'uwan da gaban mukhtar d'in keyi yace " eh baffa ina jinka"
baffa yace jia da na shigo da dare innonka ta fad'a mun maganar da kukai da ita gameda matar da kake so zaka aura hakane?
"eh baffa hakane munyi maganar da inno jian har ranta ya 6aci wanda hakan yasa ban samu barcin kirki ba sabida ban so ace nine sanadin 6acin ran nata akan yarinyar dan haka na yanke hukunci na fad'a muku cewa na haqura na janye daga batun nawa, ya dubi inno yace cikin rawar murya
"inno kiyi haquri ki yafemun 6acin ranki dana yayi dan girman Allah, kuma nai miki alqawalin ki za6a mun ko wace mace dake duniyar wacce ranki ya kwanta da ita wlh inno komin tsufanta zan aureta domin farincikin ku shine nawa" yana maganar ne wasu hawaye na zuraro masa ta idanunsa.
har cikin ran inno ta qarajin tausayin mukhtar d'in sosai har tayi dana sanin fushin ta data nuna masan ga jiyan dan itama tasan yaranta masu tarbiyya ne koda bata nuna fushinta akan abuba muddin ta nuna qyamarta kan abun tofa sun barsa knn komin sonsu da abun kuwa, muddin ba itace tace si dawo ga abun ba tofa sun basa baya knn badawa ta har abada, jiyayi baffa yace "a'a mukhtar ay bama akaiga hakan ba, tun jia mun gama mgnr da ita kuma Alhamdulilla ta fahimci zancen nawa sosai, na nuna mata shi aure hadin Ubangiji Allah ne tun fil'azal abinda Allah ta qaddaro babu mahani garesa, dan haka inma kace zaka hana yuwuwar abin rabo mai tsanani sai yazo ya kaudaka daga rayuwar ma gaba day'a kuma azo ayi abun bayan ranka, anan ta nuna mun cewar daman ita bawai ta hana bane dan son ranta a'a taguji ne ko ace ita yarinyar ta biyo halin maman tane, to nikuma sai nike nuna mata duda munsan halin ita babar yarinyar batada da kirki kowa ya sani a anguwar nan, to saidai kuma ita yarinyar babu wanda ya ta6a cewa ga wani abun assha datai masa a anguwar nan dan haka wannan nikega ba hujja bane dazata sa ace ba za'a aureta ba, dan muna kyautata zaton cewa bata d'auko halayen maman tata ba, dan haka komi mutane zasu ke fad'a to akan ita maman tane bawai kan yarinyar ba, dan haka itama maman tata muke mata adduar Allah ya shuryeta ya ganar da ita hanya madaidaiciya (niko nace ayya baffa firdausey kam ta rigaya da ta tsotso mugun nono dan haka Allah dai shi kyauta kam, dan abinda Allah yayi kam Annabi kuma sai dai ceto).
mlm Abdullah yaci gaba da cewa ''dan haka nike mai shaida maka kaje kaci gaba da neman yarinyar Allah ya sanya albarka a lamarin, kuma insha Allah zanma su yawale magana cikin wannan watan dan muje wajen mariqinta mlm zayyanu din atsaida ranar bikin naku" farinciki kamar kamar me mukhtar yake jinsa a ransa kannewa kawai dai yayi yace "Allah shi qara girma baffa da inno" ismail dayake cikin farinciki shima na ganin komi yayi normal tsakanin iyayen nasu yace "aminnn yaya baffa mun gode inno kema mungode" yayi maganar baki gar kunne.
inno tace "ba godiyarka muke so ba amsarka muke sauraro kaima " cikin mamakin rashin fahimta ismail yace "amsa kuma inno tami? duban mukhtar inno tai tace "au mukhtar badai baka fad'a masa maganar da mukai ba jian nan? cikin kama baki mukhtar yace "ya subhanalla,,,! wlh inno na mance ne,, cikin zuciyar ismail ya kalli yayan nasa yace "ba dole ka mance komi ga jiyan nan ba yaya kaji zancen za'a rabaka da masoyiyanka, nima nan da nike farin shiga har mafarkinta tawa na dingiyi kan gari ya waye bare ku da kuke tsofaffun hannu a harkan.
maganar da mukhtar keyi masa ne yasashi dawowa tunanunsa, mukhtar yace "inno tace in fad'a maka.... nan ya kwashe komi na maganar da sukai jiya da inno akan shima ya kawo tasa matar ahada ayi bikin tare.
Ismail baisan sanda wani Murmushin farinciki ya baibayesa ba, Lallaikm Zainab haske ce a rayuwar sa, daga haduwarsu jia sai batun aure kuma dudda bai ajiye ko sisi ba? lallaikam na maganar mutane da suke cewa hidimar biki temakon Allah ne ga marassa shi zai buda musu ta inda basu tsammani dan albarkacin raya sunnar manzon tsira dan samun zuri'a ta gari wacce zai alfahari dasu ranan gobe.
gurgiza kafadansa mukhtar yayi cikin murmushi yace "kaifa muke sauraro mlm" tuni ismail ya fara sosa q'eya yace
"na.... nam ya.. yaya ehmm..." sai kuma yayi shiru yakasa mgn kansa na qasa cike da kunya,, zaro idanuwa mukhtar yayi yace "laaaaaa qanena kaddai maganar inno ta zamo gskia kanada budurwa ka boyen"? da sauri ismail ya dubi yayan nasa yace"wayyo yaya mukhtar wlh jia kawai muka fara ganin juna da ita fa ka yarda dani ban boye maka ita ba"
dariya mukhtar dasu baffa sukai masa ganin yanda ya duburce lokaci day'a.
tsaida murmushin fiskarsa mukhtar ya dan rage ya qara duban ismail din yace "naji to amman ka bawasu inna bayani akai to dan su fahimta a ina ne ita ahalin yarinyar yake ko?
cikin kunya gamida saddar da kai qasa ismail yace "eh to ku nimadai ku bani kwana biyun kamar yanda nima tace mun in bata kwana biyu sannan na dawo naji amsar amincewar ta gareni, sannan kuma 'yar nan anguwar ce kuma zainab qanwar firdausey ta gidan mlm zayyanu mai almajirai d'iyarsan"
ay yana gama fad'in hakan ya tashi ya gudu d'akinsu cikin kunya shi dariya ma kunyar tasa taci gaba da basu a haka mukhtar ya biyosa dakin ya iskesa zaune sai murmushi yake, bayan mukhtar ya zauna gefensa ne yace "amman dai qanena indai haka ne kaima to kayi dacen tsarkakakkar mata ta q'warai, dan ni ganau ne ba juyau ba akan tarbiyya ta zainab, kuma nasan koda tace makan ka bari nn da kwana biyu ka dawo nasan kunya ce ta hanata baka amsa nan take, amman ai qanena yanda ya had'un nan babu wata yarinya wacce zai nuna yana so taqi amunce masa ko?"
murmushi ismail yayi yace "kaima indai batun haduwa ne da gayu ai ban kai yakai ba yayana"
Murmushi mukhtar yayi yace ''mu tashi mu tafi dai kada time ya qure mana danni yau inada aiki sosai

Please Login or Register in order to submit comment