Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

28,
har suka isa gida suma suka wuce ciki, saida baba Abdullah ya gama musabaha da maqocinsa baba yawale da mlm zayyanu mai almajirai sannan shima yabi bayan samarin y'ay'an nasa nasa yashiga cikin gidan.
ya taras da matarsa wanda yaran y'ay'an ke kiranta inno,
a gaban murhu take duqe tana kwashe d'umamen tuwon nasu a wata roba mai murfi,,
har qasa ta zuqunna ta gaishesa ya amsa a fara'ance, shikam ba qaramin alfahari yake da hafsato ba a matsayin mata ta gari garesa ba tun zamanin aurensu kuwa, shidai kam Alhamdulilla ala kulli halin yana matuqar farinciki da ahalin nasa sosai,,
"sannu da aiki hafsatou" cewar mlm Abdullah daya duqa ya d'auki robar tuwon da nufin kai musu cikin d'aki dan wajen kwata2 batta zaunuwa saboda sanyi,, da sauri inno hapsatou ta ce ''a'a mlm kabari basai na qarashe samun ladan ba in nakai mana abincin d'aka ba?" tayi maganar a kunyace alamun fulanan takar tana kurkusa kenan,, murmushi mlm Abdullahi yayi yace "inason in ragewa uwargida na aiki ai nima ko? to dan haka nike roqon ta data haqura ta barni nakai mana abincin nn d'aki sai nasamu ladar temaka wa nima ko ba haka ba?"
cikin murmushi inno hafsatou ta janye hannunta daga kan robar tuwon tace
"haka,, to shiknn mlm aini banqi ace dud aikin da nike cikin gidan nan ba'a raba mana ladar ni da kai da yaranmu ba, kaga sai kowa ya q'ara samu akan nasa ladan ba" murmushi matashin dattijon yayi d'an kimanin shekaru 66 ita kuma inna hapsatou nada shekarun ta 55 sannan mlm Abdallah ya sake cewan "hmn hakane madalla da mata ta gari irinki hafsatou, muje to"
a tare suka shiga d'akin nasu suka zauna.
dudda sanyin da ake surarawa amman kuma d'akin nasu akwai gumi sakamakon rushin garwashin da inno hafsatou ta girke musu a d'akin tuni dakin ya d'auki daddaden gumi kuwa.
saida mukhtar ya sake gaida iyayen nasa sannan isma'il shima ya gaishesu cike da biyayya iriyar tasu wacce iyayen nasu suka d'urar dasu tun farko.
a tare suke cin abunci da iyayen nasu kullum karin safe, yanzun ma tare sukeci bayan sun gama ne mukhatar yaje dakinsu ya shirya cikin kayan aikinsu ganin baiga qanen nasa isma'il ba ya shigo shiryawan shima dan wucewa school dayake sun saba tare suke fita saisu rabu bakin titi shi mukhtar saiya wuce wajen sana'ar sa shikuma Ismail saiya hau school bus ya tafi shima, ganin shiru shiru ismail din bai shigo dakin nasu ba hakan ne yasa mukhtar fitowa dan ya kirasa ya shirya su wucen,
saidai abin mamaki yana fitowa nan tsakar gida ya hango qanen nasa ismail zaune kan wani bokitin qarfe ko sanyin nan baya ji yayi tagumi kansa saqe cikin jikinsa.
cikin mamaki mukhtar ya isa wajen nasa sai lokacin ne ma ya lura da yanda tsigar jikin isma'il d'in ke tashi ta wajen damatsan dukkan hannayen sa wanda mukhtar yasan ba komi bane ya jaza masa hakan face sanyin dake ratsa sa a wajen,
matsawa kusa dashi mukhtar din yayi sannan ya dafa sa yace ''q'anina yaban ganka ba kazo ka shirya zuwa school kada kayi late naji jia kuma kace around 8:30 kunada exam ko?, kuma gashi kazo ka zauna waje ga sanyi anayi bakka gudun mura ne ta kama ka?
sai lokacin ismail ya iya d'agowa da fuskarsa wacce hawaye ke bi dan tsabar damuwa,
cikin mamaki mukhtar yake kallonsa sosai,
zuq'unnawa yayi bayan ya kamo hannuwan ismail din fuskarsa cike da damuwa, dan kuwa cikinsu babu wanda keson yaga damuwar dan uwansa mafarin knn a matuqar d'imuwance yake qara ruqo hannuwansa yace ''dan uwa na qanena mike damunka? kasan bazan juri ganin damuwarka da kuma zubar hawayenka ba a rayuwa ba dai ko?
sanin kanka ne sai inda q'arfi na ya q'are akan hakan dan naga na faranta ma qanena dan uwa na guda day'a tal hm? , dan haka maza ka gayamun mike damuwar ka?
q'irqro wani kalataccen murmushi ismail yayi bayan ya dauke fuskarsa daga jikinsa yayi saurin goge hawayen nasa dan baiyi tsammanin zuwan dan uwan nasa ba wajen ba lokacin, yace
"laaa yaya mukhtar yaushe kazo nan ban sani ba?,
ni babu abinda mafa ke damuna fa kada ma ka damu kanka d'an uwa na"
yaqarashe yin maganar tasa tareda qara son 6oye damuwar tasa can qasan ransa.
kallonsa mukhtar din yake cigaba da yi sai kuma ya girgiza kai yace
"no q'anena kada kaimun qarya nasan bakayi mun ita, dan nasan halinka na kuma san in kana damuwa kokuma kana murna dan haka ka fad'a mun,
Saddar da kansa qasa yayi yana tunanin ta yaya zai fad'awa yayan nasa wannan iyayen kudin handout din da zai siyo kimanin 5000k (dubu biyar)? alhalin yasan ba wata riqaqqen sana'a yake ba, bayaga ta kanikanci kuma ba koda yaushe suke samu ba inda wajen nasu ba wani fice yai ba, kuma dudda shima yaya mukhtar d'in wannan year din yagama karatunsa a A. B. U. Zaria shima da qyar da zufar goshi da kuma temakon baffansu ta hnyar saida saida day'a daga cikin guda 2n gonakinsa da yayi har yasamu yayi degree d'inshi gashi kuma ya gaman aiki yayi wuyar samu dole yaje ya roqa ya samu aikin kanikancin a can bayan tasha,,
kuma duka duka aikin nasa ko wata day'a baiyi da fara sa ba, gudan gonar da ta ragewa babansu itace dud in lokacin noma yayi suke zuwa da baffan nasu suke girbewa amfanin gonar kuma in aka samu baffan yakan rabawa dangi da abokan arziqi kingin kuma a kawo gida aci, kuma tunda yayan nasa mukhtar ya fara aikin shike siyo musu kayan cefanen da za'a saffara abuncin gidan aci kullum, sannan ga kuma kud'in ruwa da kuma sauran buqatu na rayuwa,, topa tayaya zai fad'a masa damuwarsa ya tayar masa da hankali inda yasan ba halin hakan garesa ba?, jin mukhtar ya sake dafasa a karo na biyu muryarsa hatta fara canzawa sbd bacin rai yace
"wlh q'anena in baka fad'a mun damuwar kaba zanyi fushi dakai har na tsawon minti day'a fa danma kaji"
yana fad'in hakan kuwa ismail baisan sanda dariya ta subuce masa ba dudda halin damuwar da yake ciki kuwa,
dan yasan wannan wani salon sune na wasa tun suna q'ananan yara in day'a na cikin damuwa zai furta wa d'ayan hakan to zakiga nan take sunyi dariya dan sunsan koda dai dai da second d'aya ne bazasu iya fushi da junan suba bare har minti day'a kuma hakan sabon sune tun zamanin childhood nasu knn. murmushin jin dad'i mukhtar yayi ganin q'anin nasa ismail ya saki ransa har yy dariya sannan yasake cewa "to gayamun qanena miye damuwar ka dai yanzun?
cikin kararriyar murya ismail yace"wlh yaya kudin handout ne sukaimin tsaye na rasa yanda zanyi nida da sanaar da zanyi da naje nayi wlh na siyo su, to amman yaya lokaci ya rigaya daya qure min tunda saura kwana biyu knn lectures din zai yi mana exam dasu kai tsaye, kuma gashi yace dud wanda bai siyoba bazai zauna masa class exam ba kuma babban tashin hankalin yaya shine lecture din dake daukarmu topic din inglesh da math kuma yaya Allah kuwa baida mutunci nasan zayana iya bawa dud wanda bai siyo books dunnan ba carry over a exam dinsa to shine narasa ynda zanyi damuwa taimun yawa kuma gashi muna jarabawar qarshe ne ta fita makaranta"
mukhtar zaiyi mgn knn sukaji muryar baffan nasu a bayansu na cewa "ah mukhtar Ismail mikuke har yanzun baku tafi ba, ni da naji shiru ma nazata kun tafi ay,, ismail zaiyi mgn mukhtar yayi saurin cewa
"eh baffa yanzun zamu fita yayi maganar yana mai yiwa Ismail din alama da ido alamum kada yace komi kawai yaje ya shirya,sam mukhtar baisan iysyen nasu susan da mgnr kudin dan basu ke garesu ba saima suma su saka damuwar hakan a ransu, shi har mmki yake yanda ake cewa free education amman saika je school din kaga ba haka ba dan tafi karfin talaka maras galihu.
hakan kuwa akayi saida yaje ya shiryo suka wuce baffan nasu ya bisu da addu'an adawo lpia sannan ya d'auki buta ya fara alwala danyin sallar walha. suna tafiya har suka kai titi mukhtar ya fiddo wayarsa yace
''qanina bani sunayen handout din man" zuba masa idanuwa ismail din yayi sannan yace "yaya nasan bakada kudi ka barsa ni kawai zan haqura da zana jarabawar" yayi maganar kamar zaiyi kuka, girgiza kansa mukhtar yayi yace "kada ka damu qanina inabin salis abokin aikina wasu 'yan kud'i nasan zasu isa na siya maka books din. Insha Allah " da sauri ismail ya rungume yayan nasa baisan sanda hawayen farinciki suke zuraro masa ba fad'i kawai yakeyi " ngd d'an uwa na gari yayana Allah shi qara bud'i nasan in AllAh yai maka arziqi zamuji dad'i yayana kamar yanda kake cewa, murmushi sukai dukkansu kansu rabu saida ismail yakai bakinsa kan kunnen yayan nasa yace "d'an uwa ns Allah yabaka fiddausi,, cikin murmushi mukhtar ya dan kai masa dukan wasa yana fad'in kaiko kan dubamin waya na ko? da gudu gudu ismail ya shige school bus din nasu data tsaya a wajen datake daukar students din yana dariya tareda d'agawa yayan nasa hannu shima mukhtar d'aga masa hannun yake cikin fara'a sannan ya wuce wajen aikinsu yana tafe yana tunanin qaryar dayai ma qanen nasa ns cewar Yana bin salis abokinsa kud'i,, shi kansa yasan babu yanda zaayi ta bari burin qanen nasa nason ganin ya zama malamin makaranta ya kasa cika muddin yana a raye kuwa.
dam yasan burin qanen sane ya zama teacher tun yana qaraminsa yake riqe da wannan burin shikuma yai masa alqawalin tallafa masa harya kai ga gaci muddin ana rayuwa,, to yanzun baccin yasan yanda suke da salis abikinsa ne na qut qut kuma yasan salis din na aron yan kudade a wajen yayan nasa in yana dasu shima kuma haka salis din yana arawa abokin nasa mukhtar kudin dud in buqatar hakan ta taso kuwa, to yanzun dai a haqiqanin gskia babu wasu kud'i da yake bin salis saima shi salis din da yake
binsa dubu day'a daya karba jia yayo cefanen sati day'a yakai gida, dan yasan kafin nan da sati day'a za'a basu kudin aikinsu dubu uku da dari biyar da ake basu dud qarshen wata, kuma tabbas da ismail yasan aron kudin zaiyi wajen salis din dasai ya hanasa danba da san ransa yake amsar bashin ba, shima kuma dole tasa yake karbar bashin sbd ciyar da iyayen nasa tunda yanzun baffa bayya wata sana'a qarfi ya fara tafiya.
koda yaje wajen aikin nasu nan ya iske salis da sauran abokan aikin nasu suka gaisa nan ya fara cigaba da aikinsa wnda yatashi akai jia na gyaran wata mota ta shinkafa,, har sai wajen la'asar sannan yasamu ya ida gyara motar ya koma qasan wata bishiya ya kwanta yana maida numfashi danba qaramin gajiya yai ba, salis ya ajiye sukuddireba din hannunsa bayan ya zauna gefen mukhatar din yace "yadai abokina yau naga kayi weak fa da yawa tun zuwanka naga kamar kana cikin damuwa, mike faruwa ne?
tashi zaune mukhtar yayi yace "so nike in siyawa ismail wasu handout salis guda 2 dubu biyar suke kuma wlh gashi ko sisi bnda... nn mukhtar ya fad'a ma salis din yanda ismail yai masa bayanin exam din akan books din kmr ynda yai masa, shiru salis yayi yace"kashh kuma wlh abokina ni kaina yau bayaga naira dari hudu da hamsin dinnan bana maganin ko sisi a aljihun nan nawa" ya qarashe maganar yana mai zarowa mukhtar din kudin yana mai nuna masa , sannan yaci gaba da cewa suma yanzun nike jira mai abincin nan ta kawo na sai mana muci, in kuma kanada buqatarsu gasu saika cika saimu haqura da abincin inmun koma gida maci inda yiwa kaine za'ayi ko?
cikin fara'a mukhtar yace "haqiqa salis kacika amini na qwarai ngd da kulawar da kk mana, amman ka riqe kudin nan ai mutum bazai rayu babu abunci ba,
kuma bnda kud'i a jikina duka nera dari da hamsin ne bare nace na amsa na cika na siya masa books din, dana yanke shawara naje wajen oga Daniel ya temaka yabani aron kud'in in yaso in anyi albashi wannan watan da wata mai zuwa saiya fidda kudinsa saiya bani kingin cikin kaima na baka dubunka kingin sainai cefane nakai gida kaga shiknn ay,, kallonsa kawai salis yake cikeda mamakin yanda ashe har yanzun akwai 'yan uwa masu qaunar junansu haka? kalli dai yanzun shi ko tunanin kansa baiyi na buqatar rayuwa na iyayensa da kuma d'an uwansa kawai yake danya faranta musu, shiyasa bai qyashin bashi rancen kud'i dan yasan a hanyar daya dace yake biyar dasu kuma dud mai tallafawa zumuncin Allah bazai ta6a neman alfarma a duniyar nan ya rasa ba koda bai samu wani wajen ba to sai Allah ya buda masa ya samu tawani 6angaren,
dubnsa salis yayi sosai yace "gskia abokina bn tunanin oga daniel zai maka wannan alfarma d'in nan kuwa yanda yake da shegen masifar son kud'in tsiyan nan, kasan fa yare da mugun son kud'i abokina wlh?"
shiru mukhtar yayi yana nazari zuwa can ya miqe tsaye yana kakka6e rigarsa yace "bari naje dai,, 'yar dariya salees yayi yace "Allah a dace abokina daman sai an gwada ay ake sanin na qwarai, jeka ina nan har ka dawo kuma inai maka fatan sa'a"
daga haka bai sake cewa komi ba ya dauki haki qasa yana zane dashi a qasa rairayin wajen, da "amimm mukhtar ya amsa ya wuce,, saman wata mota marar body ya iske oga din yana qilga wasu kud'ade.
ya matsa kusa dashi yace "oga barka da hutawa,, ai danial na ganin mukhtar yayi wuf ya cusa kud'in qasan dam6areriyar cinyarsa guda day'a yace cikin hausarsa mai gargada" yaye ankaye mukhter kabalo aicinka kajo nan wulina kuma yanju?"
mukhtar yace yana d'an shafa sumar kansa ta fulani "am oga dama cewa nayi ka ara mani 5000 thousand a cikin kud'in albashina na wata 2 in yaso in wata 2n ya cika saika fudda kudinka ka bani sauran canjin please oga a temaka ina cikin buqata ne"
fiddo idanuwa waje daniel yayi yace da qarfi " wooooo 5000 k? kana nema wulina yanjun? "eh oga help me please help me "!! shiru oga Daniel yayi zuwa can yace "ok na yalda jan baka kutin ammannnn da sharad'i,, cikin tsananin farinciki na muhktar jin oga ya amince babu gargada yace "to oga sharadimmi?"
oga daniel ya d'aga cinyar nn tasa ya fuddo kud'in ya qirgo 5k din ya riqesu a hannunsa ya maida sauran aljihu sannan ya dubi mukhtar yace "inka yalda kingin canjin albashinka na wata 2n wato dubu biyuh jan liqesu a macayin baci da luwa?
zaro idanuwa mukhtar yayi tabbas inyayi haka yasan zai cutu, dami zai biya salis dubunsa day'a? dakuma mi zai riqe a hannunsa na amfanin gidansu?
batareda 6ata lokaci ba yace "a'a abarsa ma kawai na haqura" oga daniel yace ''ok no problem go, go,mukhtaro"
haka ya koma ya fadawa salis komi, salis yace " hmm nasan ai za'a rina dadai ba oga daniel bane, amman ka shawara man abokina mizai hana muje kasa wayarka kasuwa ka siyar in yaso saika siya masa handout din kaga nan gaba in kasamu wasu kud'in kasayi wata koya kace?
shiru mukhtar yayi dan babu wanda ya fad'o masa arai face masoyiyarsa fiddausi yanzun idan ya saida wayar shiknn bazasu sake firan dare ba na free cull wanda suka sabawa juna dashi kullu?
wata zuciyar tace qanen fa to yaya knn?
tuni kwanyarsa ta cakude yarasa matsaya ta shawara, ana haka kuwa saiga kiran fiddausi a wayar tasa ta shigo, kam ya d'aga harta katse, ganewa yayi plashing knn tai masa, jiki a sanyaye ya runtse idanunsa dudda kwad'ayin son jin muryar tata da yakeyi amman hakanan ya runtse idanunsa ya zare batir din wayar ya fiddo sim dinsa yasa aljihu ya maida murfin nokia din wayar tasa ya rufe yana binta da kallo a haka ya miq'e tsaye ya dubi salis yace "muje ka rakani to kasuwar saina siyar na siyo masa handout d'in daga nan,
kan salis yace wani oga daniel ya qwallawa salis d'in kira akan cewa yazo ya gwada inda ya ajiye tayar Pejo din motar da aka kawo gyara d'azun, haka ya wuce yabar mukhtar a nan gun tsaye zuciyarsa na masa saqe saqe akan shin ya saida wayar nan dai koko. dai???...


*Xexen Fasaha*
f. o. w.
[1/17, 3:09 PM] Xainab Documen: πŸ‘πŸ‘
πŸ₯‘πŸ₯‘
πŸ‘πŸ‘
*DA SAURAN KALLO !!!*

Story and writing
by
Xayyneb πŸ’€πŸ’€

Fasaha online writers f. o.w.

~A Ko ina nake kina raina aunty na ta kaina yayata me sona a koda yaushe wacce battason abinda zai ra6eni muddin ba alheri bane a cikinsa kuwa, my hawwas d'ina nike muku bayani my mom sadeeq tawa Allah bar jini da anta a had'e suci gaba da rayuwarsu muddin rai a lami lpia~❀

*🌳imparting valuable knowledge and entartaiment is our concern*🌳.

-https://www.facebook.com/Fasaha-Online-Writes-751775151851852/?referrer=whatsapp.

πŸ‘πŸ₯‘πŸ‘
πŸ…Ώ5⃣.
*Y* ayi zurfi a tunanin hakan sosai har baisan yawan adadin lokuttan daya d'auka ba haka, bai san sanda ma har salis d'in ya dawo ba sai dai jiyayi an dafa masa kafad'arsa salis d'in yace "abokina tunanin me kakeyi haka inata maka mgn baka jiba kuma? miye abin damuwa kuma inda mun samu maslaha ga lamarin?
kazo kawai muje daman na fad'awa oga daniel zamuje salla inda lokacin sallaer la'asar d'in yayi, kasan bawai barin fita yake ba bada dalili ba kaga daga nan in mun gama sallar sai mu wuce kasuwa mi saido wayar ka siya masa handout d'in"
salis din ya ida yin maganar yana mai duban lokaci a agogon hannun dake jikin hannun mukhtar d'in.
miq'ewa mukhtar yayi yace cikin 'yar fara'a yana mai miqawa salis hannu suka tafa yace "ya ilahi nagode maka da ka had'a ni da aboki na gari, dariya sukayi sannan suka tafi gefen titi inda can masallacin yake anan sukayi alwala suka shiga masallacin sukai salla suka fito lokacin qarfe hudu da kwata na marecen ranar ma.
kai tsaye kasuwar saida wayoyi suka isa shagon ya fiddo wayar ya miq'awa salis, salis ya kar6a shikuma ya nunawa mutumin yace "abokina wannan wayar mukeso ka siya, yayi maganar yana mai miqawa mutumin wayar, amsar wayar mutumin yayi ya hau jujjuya ta a hannunsa yana dubanta ciki da bai d'inta sannan ya d'ago kai ya dube salis yace "wannan wayar dudda dai alamun sun nuna cewa sabuwa sabuwa ce bataji jiki sosai ba to gskia duka duka kudinta bazasu wuce dubu 6 da d'ari takwas ba, sakin baki salis yayi yana jin kamar ya kaiwa mutumin wani iriyar kalar bahaggon kutufo na jini da majina dan takaicin cininkin wulaqancin da mutumin yai musu, kasa magana yayi kawai ya juya yana kallon mukhtar wanda jin kud'in da mutumin yace zai sayi wayar yasa tunanin to shi kansa nawa ya siyi wayar ma duka duka atata wata biyu da suka wuce? dubu 13 da d'ari biyar fa ya siyeta a sabuwan tama shima kud'in da suka rage ne lokacin dayai exam da aka siyar da gonan nan ta babansa bayan ya kaiwa baban nasa ragowan sune baban yace yaje yai wani abun dashi shine kawai ya ajiyesu ga lokacin baiyi komi dasu ba, sai bayan takardun sa sun fito na gama degree ya duqufa yawon neman aiki ko Allah zaisa a dace amman sama da wata guda shiru kkji, shi knsa sai lokacin ya yarda da batun mutane da suke cewa karatun talaka a wannan qasar in yagama yana nemn aiki to ya qwammace ace ya qara maimaita shekarun karatun nasa indai zai samu aiki in eagently da ace yaita yawo ofis ofis ma'ikata ana tozarta tasa, inda dai aikin yanzun daka gama karatu tofa babu mai samunsa a kn lokaci face yaran manyan qasan in kuwa kaga talaka ya samu aiki tofa wannan q'wacen Allah ne yabaka kyauta a garesu shiyasa kullum addu'arsa Allah ya azurtasu da shuwagabanni na qwarai wanda zasu kawo cigan qasa a kowace jiha.
haka ya gaji da neman aikin nn ga lokacin ko masinja na ofis bai samu aikin saba dole ya haqura ya dawo gida, ahaka ya yanke shawara shida ismail akan yasai 'yar wayar zamani mai kafafen yad'a labarai koya dinga tura request din neman aikin nasa a wurare daban daban wataqil ko Allah zaisa a dace tanan 6angare in anyi gamdakatar dacen daukar sabbin ma'ikata kamarsu,
hakan yaje shida salis suka siyo wayar fa kullum yana cikin internet aikin tura saqonni amman shiru kkji, bai damuba inda yasan yarigaya daya tura yakuma isa garesun yasan kuma dud daren dad'ewa zai samu saqon amincewa daga garesu kokuma akasin hakan,, alokacin ne yarasa ynda zaiyi ko sile biyar baya maganinsa a aljihun sa inda ya kwashe 'yan kud'in yasai waya, mafarin knn sai da yaje wajen salis akan yanason yakaisa wajen aikinsu na kanikanci dan yagaji da zamn rashin abunyi haka. akayi sa'a kuwa suna zuwa oga daniel ya d'aukesa tareda fara koya masa dabarun aiki, har aran mukhtar yaji dad'i yasan aikin daya samu ma harda add'uar da iyayen su ke binsu dashi kullum, dayake Allah ya basa qwalwa nan da nan kuma ya fara koyan aikin cikin nasara harya kaiga ya iyan shima yanda ya dace, hargashi kuma da albashin aikin yake tallafawa gidan nasu shima i yau,
katse masa dogon tunanin daya shiga salis yayi yace "yanaji bakace komi ba kuma?"
dubansa mukhtar yayi bayan ya sauke ajiyar zuciya yace "bansan ya zance bane salis wlh"
duban salis mutumin yayi shima salis ya dubesa ya daure zuciyarsa sannan yace " to yanzun ko 12k bazaka siya ba abokina? ka duba fa dakyau sabuwan modern ne fa babu inda ya koyi qwarzane jikinsa?
murmushi mutumin yy yace "eh na gani, a gaskia na siya 8k bayaga haka bazan qara ko sisi ba, kuma madai bari kuji kasuwar nan dud in zaku kewayeta bazaku samu sama da abinda na siyeta ba wlh Allah kuje nina gaya muku"
salis sarkin zuciya yaja wani tsoki ya fizgo wayar daga hannun mutumin yace muje mukhtar muje wani wajen an fasa siyar wan ma anan"
riq'o salis mukhtar yayi yace "tsaya sarkin fushi inda dai yace haka ya siya a siyar masan ba komi,, ai kasuwa ce ta juri hakan daman, badan ran salis ya soba ya bashi wayar mutumin ya karba ya ajiye a cikin dan akwakun qasan inda sauran wayoyinsa na siyarwa suke yana qirgo musu kud'in yana magana da cewa " mu ai wlh masu siyan wayoyin hannu nan bawai qaramin tasku muke gani bama, yau muci riba gobe mu kur6i asara dan yawancin wanda suke kawo mana siyan wayan dud 6arayi ne suke kawo mana muke saya, wannan harkar ai ataimaki juna sunanta kawai"
cikin fushi salis ya yunquro zai nufo mutumin mukhtar yayi saurin taresa jin salis d'in na cewa "ok mune 6arayin knn kake nufi,,?!! "
tuni mutumin yasha jinin jikinsa dan yasan ko warewa zasuyi babu abinda zai iya d'iba a jikin salis barcin shi yaci qaniyarsa ma ya rure masa jiki, shiyasa yayi saurin cewa ''a'a nifa yawancin mutane nace baku ba, amman in ranka ya 6aci abokina to kayi haq'uri ai abin bai kai nn ba"
dai dai nan ya miqawa salis d'in kud'in yana fad'in "gasu ngd... , a fusace salis ya fuzge kud'in a hannunsa har yana datsawa mutumin akaifar hannunsa wajen kar6a a fusacen snn yaja tsoki tareda riqo hannun mukhtar din suka bar wajen. mutumin na cewa a ransa wannan kam shegen zuciyar tsiya ne dashi amman kuma ga abokinsa silent man koya suke zaune tare lpia kuma da juna? ya dafe ha6a tareda furta Allah mai had'a jinin bayinsa dudda banbancin halayar dake a tsakani kuwa.
ahaka yaci gaba da harkokin gabnsa.
salis kuwa suna tafiya a hanya yace "wlh daka barni dashi da sai nayi maganin d'an iskan can, har ya isa yai mana habaici ma?"
mukhtar yace "mutane sai haquri ay abokina mu wuce kasuwar books din kawai

Please Login or Register in order to submit comment