Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawo komi a ransa ba inda gani yake insun gaisa dashi kmr sun gaisa dasu baffa din ne. yauda gobe inji yan magana asarar mai kwana har gashi an fara d'auko alhazawa 'yan makka.
dan yau kam tun safe firdauseey ake rawar jikin yin girki dan jirginsu mukhtar gab yake da sauka qasar Nigeria.
bata jimaba ta kammala masa hadaddeyar fridrice dinsa mai hadin coslow na barma a cikinsa, sannan tai masa tuwon shinkafa miyar ganye da kuma lemummuka har kala uku wanda tayi da kanta kuma dud cikin girkin babu wanda batasa masa ganyen maganin nan ba kuwa a ciki, yayin da ta girka wasu baffa suma abuncinsu na daban dudda ya kasance kuwa iri d'aya ne dana mukhtar d'in dandai su banbancin kawai bata sa ganyen maganin nn ba a cikin nasun, abinda kuwa yasa ta girka musu iri d'aya kuwa tasan mukhtar na iya cewan kalar abincinsa shi su baffa zasuci suma.
dan kokadan bai yarda yaci abu mai dadi ba batareda ya kawowa iyayen nasa nasu kason ba qa'idarsa kenan kuwa kullum leda uku yakeyi yakawo daya gidansa daya gidansu daya gidan Ismail cike da kaji yhugurt ice-cream dss.
hakama abincin karin safe da rana da akeyi da nama zu6u zu6u a ciki dole saiyasa an dibar musu yakai musu, hakan kuwa ba qaramin k'onawa firdauseey rai yake qara yiba da kuma tsanarsu baffan da ismail.
biyar dai dai su alhaji mukhtar suka dura airport, bada jimawa ba motar kamfaninsu tazo ta kwashesu da manyan jikkunansu na tsaravar mecca, gidan su mukhtar din suka sauka gaba d'ayansu. dudda mukhtar nason xuwa yaga firdauseeyn tasa dajin dumin babynsa amman kasa tashi yayi sabida jama'ar dake shigo musu barka da dawowa ciki kuwa harda surukansa maman Zainab da mlm zayyanu.
baba yawale bai jimaba yatafi gida dan hutun gajiyar
hnya, baifi minti biyar ba da fita saiga firdauseey ta shigo gidan cikin shigarta mai kyau wacce ta karb'eta, cikinta kuwa ya fito sosai dan wata matsayi ne take haihuwa, jar atanfa tasa riga da zani sai farin gyale mai ratsin jaja a cikinsa, nan taiwa su baffa barka da dawowa a zuciyarta cewa take "hmmmmm samun farincikinku ya kusan qarewa indai kuwa daga mukhtar ne tsoffin kawai"
ko kallon zainab bataiba bare ta tnka mata babu wanda lura da hakan kuwa wajen face Zainab din da ismail.
haka firdauseey ta ajiye musu abincin tadan jima a gidan sannan ta tashi ta fita ta koma gida.
shi kansa mukhtar yayi mamakin jimawarta gidan nasu dan zai iya q'ilgawa da aurensu zuwan firdauseey gidan basu kwata kwara baufi sau uku ba shima a tsattsaye, itakuwa yana lura da zainab matar ismail kusan dud ran juma'a da alhamus nan take wuni wajen inno, shiyasa ko shaquwa sunfi yi sosai tsakanin zainab da inno akan ita din firdauseey .
yaso ya cusa mata ra'ayinsa na zuwa kaida kai a gidan nasu dan su saba da inno itama sai iai daya lura bataso saiya barta dan babu takurawa a lamarin kowa yagyara dan kansa ay a cewarsa.
ganin baffa ya dubi abinci yakaiwa baba yawale yadawo nan inno da zainab sukai 1 plate baffa da ismail suma suka zuba nasu nan, har mukhtar yayi nufin sanya hannunsa cikin nasu baffa yaci aiko baffa ya dakatar dashi yace dole sai dai yaje can gidnsa yaci nasa wajen matarsa, ganin baffan bada wasa yake masa ba shiyasa ya tashi ya wuce zuwa gidan nasa, shi knsa gidan ba qaramin burgesa yayi ba matiqa gaya daya shiga cikinsa.
saida yaji dumun matarsa da babynsa sosai sosai sannan ya rabu da ita ya miqe tsaye tareda d'aura towel
Wanka kawai yayi tareda salla yana gamawa ya kuma nufi dining table dunsu inda firdauseey ke zaman jiransa yaci abinci , yana zama cikin murmushi ta matso da kujerata kusa da tashi tace.
"hm mikakeson fara ci ne alhajina?" murmushin shima ya mayar mata yace "ni wannan qamshin abuncin yayi dad'i fa hajiyata, fara samun fridrice ma dai to dan yau abincinnan naki mai dad'i yanda nai missing din nan nasa dud yau saina cinyesa rass"
fari tayi masa da ido tareda sakin 'yar dariya sannan ta fara zuba masa lemo ta ajiye masa agabnsa taresa tura masa plate din Friedrich din kamar yanda yace, babu wata wata ya d'auko spond da nufun fara ci tace "waitt alhajina aiki nane ay ciyar dakai" murmushi yayi ya sakar mata cokalin datake qoqarin kar6a garesa, nan ta d'ebo abuncin tasa masa abaki ya karb'a tareda taunawa a hankalin harda lumshe idanuwa alamun dad'in girkin yayi masa sosai, cup din lemon data hada da ganyen sihirin nan ta d'ora masa abaki nan shima yafara shan lemun, sannan daga bisani ya karb'i cokalin daga hannunta yana mai cigaba da cin abincinsa da kansa ita kuwa sai faman kallonsa take tana sakin murmushi na cin nasarar tasu ga alama...


*Xexen Fasaha*
[1/17, 3:10 PM] Xainab Documen: πŸ‘πŸ‘
πŸ₯‘πŸ₯‘
πŸ‘πŸ‘
*DA SAURAN KALLO !!!*

Story and writing
by
Xayyneb πŸ’€πŸ’€

Fasaha online writers f. o.w.

*🌳imparting valuable knowledge and entartaiment is our concern*🌳.

~Dedicated to my mom Sadeeq hawwass~.

-https://www.facebook.com/Fasaha-Online-Writes-751775151851852/?referrer=whatsapp.

πŸ‘πŸ₯‘πŸ‘
πŸ…Ώ1⃣2⃣
*T* a q'arashe maganar cikin huhhutai da mugun dukan qirjinta da hannunta.
firdauseey tace"kwantar da hankalinki mama nasan zamu sameshi yanda mukeso fiye ma da hakan inda har kika sanya boka marakusa a wannan zancen komi yazo ending ay, hmm mukhtar kenan nayi maka alkaqawalin saika manta da muhimmanci iyayenka na tsawon shekaru da dama"
"wannan haka shike fad'i ki q'ara dai kam d'iyata yar albarka mai iriyar hakin uwarta sakk".
nan sukaci gaba da had'a mugun nufin su ga bayin Allan da basuji basu gani ba. mero bata bar gidan ba har saida dare shima dan mukhtar d'in ya dawo gida sannan ta wuce.
hm ko kunya ta baje gidan d'iya suna fira suna shewa kamar qawarta, da yake dai abubuwan mamaki basu ta6a qarewa a duniya akwai masu hkn sosai na budurwar zuciya.
fitar da sukayi d'azun mukhtar da salis wajen camp din alhazai suka je cike wasu forms daga nan kuma sai suka dawo, mukhtar daga nan yaje inda masu ginin zamani suke yai musu bayanin ginin gidan nasa, nan batareda b'ata lokaci ba kuwa suka d'auko masu albums albums na gini mai kyau da tsari tamkar a turai, ismail yace ya zabar masa, nan take kuwa ismail ya zab'ar masa wani tsantsararren ginin gida wanda daga wajensa dud iriyan wannan manyan duwatsun ne masu jone da cut silver tayils, sannan ga wata makekeyar harabar cikin gida, can kuma gudan gefen wajen runfunan tampals tampals har guda 3 ne na saka motoci, sannan aka budo musu shafin tsarin falo.
suma d'akunan falon masu benaye ne hawa kusan biyar a kowane d'aki dake cikin falon, wato bedrooms, gashi kalar fentin gidanma abin a tsaya a kalla ne,
nan take kuwa yasa sukayi masa bill din kudin anan sukai masa shi kuma ya tura musu alert nn take da sharadin bayan tafiyarsu mecca bayan qaramar salla zasuje gidan sufara aiki in yaso kansu dawo an kammala komi, har zasu fito daga ckn ma'aikatar maginan manajan yace oga banda new fenuters modern ne xaku zuba a iriyan
Wannan gida haka? Mukhtar yace "za'a sanya su amman zan nema ai,,, manager din yace "ai muma nan muna dasu oga, zamuyi maka gini kuma ka siyi funature a gurinmu dud wanda kakeso shi zamu sanya maka a gida harda labulaye yan waje dud muna da".
nan yajasu wajen kuwa, sukai arba da kayakki iriyar na wajennan set set babu kalar da babu na q'asashen waje nanma ismail da kansa ya zab'arwa yayan nasa kayan daki, har set guda biyar, dan d'akunan ne guda biyar a saman benen ga yanda ginin zai kama inkun tuna.
suna dawowa kuma mai hilin kusada gidan Ismail mukhtar yasa a nemo masa dan suyi ciniki sbd ayi gyaran gaba daya sai dai kuma anyi rashin sa'a mutumin yayi tafia zuwa umara ance bama zai dawo ba sai bayan qaramar salla in yayi hajji sannan,
dole mukhtar ya haqura badan yasoba, ammam yaso ayi musu gyaran tare yanda da sundawo meccan kowa zai tare a sabon gidansa.
har saida Ismail ya nuna masa wannan ba abun damuwa bane inda duka saura kwana 2 azumi kenan hajji baifi wata daya da yan kwanaki ba,
dan haka koda mukhtar din ya koma gida yana gwadawa firdauseey yanayin ginin gidan da za'a musu tuni ta mnta da wani fushi da takeyi dashi ta dinga farinciki na dariya ganin qirar gidan dud a layin anguwarsu babu kamarsa a tsarin kyau koda kuwa a fuskar gidan nrma bare ciki, dudda akwai masu kudi da mnyan gidaje a anguwar kuwa amman na mukhtar end ne in aka zo, yanda kasan a qasashen qetare haka gidan yake ciki da waje dan komi na cikinsa dark pink ne, and white colour.
watan alfarma na ramadana ya kama har gashi anfara azumi cikin ikon Allah yau kwana 6 knn da farasa, a lokacin ne kuma aka fara gyara gidansu baffa yayinda suka dawo nan gidan mukhtar din da zama kamar yanda ya roqesu alfamar hakan dan baffak am yaso su koma gidan babban amininsa kuma maqocinsa baba yawale inda matarsa ta rasu shi daya ne a gidan kan aga gyara musu nasun,
koda wasa kuwa firdauseey bata nuna wa iyayen nasa ba mugun halinsu kamar yanda uwar ta gargad'eta akan cewa kada ta nuna musu komi harsai halin hakan ya bada sannan,
inda marakusa bai nan da taje, amman anmata bayani zai dawo garin in angama azumi dan shi bai iya zama garin indai watan ramadana ya kama kuwa, danji yakeyi a jikinsa kamar ana babbakasa da wata iriyar azabtacciyar zazzafar wuta mai q'una ne shiyasa yake had'a 'yan komatsansa yabar gari yakoma can cikin daji sosai a wani yanki2 na tsibirin matsafan yamma bazai yadda yadawo qauyen garinsu ba kuwa har sai an gama azumi sannan yake samun zama lpia.
shiyasa komi su inno sukeso take musu babu gardama sai bayan idanunsu taita tsine musu tana d'ura musu ashir tareda cewar lalatattun tsoffi kawai kunzo kun rashe mana a gida kun hanani rawar gaban hantsi hmmm! dani kuke zancen randa kuka tabvatas da cewa d'anku yabar hannunku ya dawo namu a lokacin ne zakuga samfur samfur na tozarci na d'aya bayan d'aya wlh muna fukai kawai.
ahaka azumin Ramadan yaita tafiya lpia lau cikin ikon Allah har yau gashi an kai na 22 ,a ranar ne kuma aka gama wasu baffa gyaran gidan washe gari kuma suka koma, gida kam Alhamdulilla komi yaji banda tsiya a cikinsa, su baffa su kansu abun ya burgesu kai lallaikan babu wanda yaqi wajen hutu dajin dad'i a duniya koda kuwa mukwan lpia ne kai wajen tsufa.
lokacinda aka shiga goman qarshe kuwa baffa kullum masallaci yake kwana yana adduoe da roqon Ubangiji Allah akan ya tsare sa da iyalensa da dukkan kullihin musulman Allah yakuma basu lpia mai d'aurewa ga ibadarsa, kullum adduarsa naga daurewar zumuncin 'ya'yan nasa ko bayan ransu kuwa,
a haka aka gama azumi lpia, azumi kuwa na bada baya yan mecca suka fara shirin tafiya, yau litinin kenan
ta kama ana ya gobe za'a tafi to adaren ranar bayan meron tsimbe tazo gidan sunyi magana da d'iyar ta tafi mukhtar na dawowa katsam firdauseey tasa masa kuka wiwi,, da sauri kuwa ya nemi waje ya zauna yaduveta sosai dud a rud'e ga tunaninsa ko ciwon cikinne yad'an juya mata dayake cikin yanzu ya shiga wata na bakwaiy ne yanzun kullum yau ciwo gobe sauqi haka take, ganin yanda ya rude ne yasa ta faki idanunsa tai masa gwalo( ashe daman sun shirya da mero kan zasuje wajen boka namarakusa goben tare kamar yanda ya buqata, inda ya dawo gari tun bayan gama azumin ma.
to tasan kotace masa bazata bisa mecca ba akwai matsala danzai tuhumeta akan dalili shiyasa kawai suka shirya itada uwar akan cewa zata zauna shan magani saboda bata da lpia inyaso daga baya sa koma tareda shin).
haka taci gaba da kukan munafunci kamar gaske, dan kuwa fuskarta tai kacan kacan da hawaye sai da qyar ta bude baki tace
"toni yama za'ayi naje mecca da wannan turtsetsen cikin mai bani wahala wanda ko tafiya ma daqyar nikeyi dud nabi na qara kunbura, ni bnma iya ibada dashi bayan kasan yanda kwananan yake wahalar dani ko yanzun ni bnma lpia ni kadai nasan ciwon da nikeji a jikina"! taqarashe maganar tana taune leb'e da daddafe ciki da qugu kamar gaske, dasauri yace "sannu to fiedy na ko muje asubiti ne yanzun? saurin girgiza masa kai tayi tace "a'a zan koma gida wajen mama ne dan tace zata dinga bani magunguna ina sha har ku dawo nasan zan samu sauq'i lokacin"
cikin rashin jin dadi yace"gida kuma fiedy?!, bakya gudun kije kinashan magungunan dabakan tsarin na likitoci ba aje kuma asamu matsala? muje asibitin zaifi kawai nikega ko?"
cikin murmushin yaudara na q'arfin halin qarya tace "kada ka damu mama tasan kowane magani daya dace mai ciki ta sha su fa to dan inganta lafiyarta indai na hausa ne kuwa dan tasansu kuma ta saidasu a baya ga jama'a da dama"
badan ya sova ya haqura sakamakon matsawa datai kan batun.
washe gari yaje ya fad'awa su baffa komi yaqara da cewa "ni baffa ma bansan wanda zan bawa kujerar tata bama, gashi baifi saura awa biyu ba yanzun jirgin namu ya tashi bafa......


*To dears wa za'a bawa kejerar nan ta mecca din nan datai saura?? Plss bnda rigima ku tsayu ku fidda gwani cikinku😜.*

Takun daice watoπŸ‘‡πŸ»
*Xexen Fasaha*
[1/17, 3:10 PM] Xainab Documen: πŸ‘πŸ‘
πŸ₯‘πŸ₯‘
πŸ‘πŸ‘
*DA SAURAN KALLO !!!*

Story and writing
by
Xayyneb πŸ’€πŸ’€

Fasaha online writers f. o.w.

*🌳imparting valuable knowledge and entartaiment is our concern*🌳.

~dedicated to my mom Sadeeq hawwas~

-https://www.facebook.com/Fasaha-Online-Writes-751775151851852/?referrer=whatsapp.

πŸ‘πŸ₯‘πŸ‘
πŸ…Ώ1⃣4⃣
saida mukhtar yaci abincin nan kuwa sosai, jin cikinsa na barazanar fashewa dan cikarsa shiyasa ya d'agawa abincin nan qafa fa.
koda ya gama cin abincin kai tsaye gidansu yaje ya kirawo Ismail dasu baffa harda baba yawale sukazo sukaga gidan sukaita sa alheri sannan suka juya, ismail ne kawai yai saura bai tafi ba inda suke tsaye cikin garden din gidan(lambu) suna q'ara yawatawa shida mukhtar din.
ismail yace "wlh yaya gidan nan yayi mun masifar kyau baka jiba, hmmmm Allah kuwa yaya kamar gidan turawa fa, gskia maq'eran gidannan sun baje iya fasahar su kam" mukhtar yayi murmushi sannan yace"wlh qanena in kana son gidan nan zan iya barar maka shi sai nasa ni a gina mun daga baya, danni komi nawa naku ne a rayuwa" da sauri ismail ya zaro idanunsa tareda kama baki cikin mamaki yace"wlh yaya bazan kar6a ba kamaji na rantse"
tuni ismail yayi hanyar gate din gidan da niyar ficewa dan har ga Allah ransa baison haka da mukhtar ke masa, ace ko yaya ya nuna abu yana burgesa indai mallakin yayan nasa ne saiya nemi barar masa shi? wannan ai abun yayi yawa danshi har kunya ma yakeji dudda kuwa yana yayansa, shiyasa kullum son junansu da shaquwa take qara ratsa dukkan zuciyoyinsu gaba daya so zalla bamai algush ba kuwa a ciki.
da sauri mukhtar ya bisa ya riqo hannunsa cikin damuwa yace "miyasa zaka tafi ka barni qanena?!, mukhtar yana gama fadin hakan kuwa take yaji gabansa yayi wani kalar mummunan faduwa kansa kamar yana jujjuya masa da sauri ya dafe kan tareda zuqunnawa wajen yana fadin
"ya salamullahe!,,, innalillahe'wainna'ilaihurraji'un,,, a zabure Ismail ya zube gabansa ya ruqo hannunsa daka saman kan nasa a rude yake cewa "subhanalla subhanalla
"yaya na?
yaya na miya faru dakai ne haka fad'a mun dan Allah, yana maganar muryasa na kyarma, mukhtar kuwa da kansa ya daina juya masa zuwa yanzun,yana dawowa hayyacinsa yaga Ismail zaune a gabansa riqe da hannuwansa da sauri kuwa ya fizge hannunsa daga na ismail din ya miqe tsaye danji dayai bai ma son ganin Ismail a lokacin yafi buqatar yaje ya kwanta ya huta dan har yanzun yanajin ciwo a tsakar kansa, jikinsa ma gaba daya yaji ya saki ya sauya masa kamar ba nasa bama.
ismail shima miqewa yayi yace "yaya fad'a mun mike faruwa dakai dan Allah?"
yayi maganar yana qoqarin sake ruqo hannun mukhtar din, jikin mukhtar na rawa ya goce hannunsa ya dubi ismail fuskarsa a sauye yace"kaje gida qanena kaina namun ciwo zanje nasha magani na d'an kwanta"
"to yaya sannun Ubangiji Allah ya baka lpia,,,, tunkan ma ya ida maganar mukhtar ya wuce baice masa komi ba yana shiga kuwa ya maido qofar tasu ya rufe da qarfi, haka Ismail yabi yayan nasa da kallon tausayi shi kansa yasan gajiya ne kawai ke d'awainiya da yayan nasa, haka dai badan yaso ba yatafi.
wasa wasa kwana uku ras a jere saida firdauseey ta ida ciyar da mukhtar abincin sihirin nan sannan taje ta jefasa a kwaminsu na toilet tareda floshin dinsa yayi qasa.
yanzun haka mukhtar ne zaune shida firdauseey bayan dawowarsa daga office sai faman manne masa take tana masa fira.
zuwa can tace "alhaji na yadace fa ace mamana itama an gina mata gidan zamani haka wanda zata dawo ciki ta zauna ko?'"
cikin fara'a batareda shayin komi ba yace "kin kawo shawara Matata,, to amman awane anguwa ne kike ganin yadace ace za'ai mata ginin ne ta zauna?"
saida tad'an muskuta tareda qara kwanciya sosai a jikinsa tana wani shafa fuskarsa yayinda shi kuma ke shafa cikinta wanda haihuwa yau ko gobe.
jiyayi tace"hmn ay alhajina inma ka tada su baffanka daga gidansu ka gyara mata can ai abun zaifi kusa nikega da ace kuma tai mana nisa in zata zo kuma zata sha wuya, kaga qwamma ace sudinne sukai maka nisan wato su baffa. babu musu mukhtar yace "lallai kumafa wannan gskia ne, yanzun abunda za'ayi zanje nasan yanda zanyi kan maganar gidan su baffan da tashin nasu kuma" farinciki aran firdauseey kamar zai kasheta kuwa, a zuciyarta kuwa tuni tabawa boka marakusa number daya daga cikin hatsabiban bokayen dudduniya dan gaba daya taga hankalin mukhtar yabarsa inba haka ba harya zai yarda yana'a cikin hayyacin sa ya tashi iyayensa daga gidansu, gidan daba mallakinsa ba shi 1?
ta6 lallaikam dole ta sara masa kuwa, cikin murmushi tace "nagode alhajina sosai" 6ata fuska yayi yace "haba matata miye kuma na godia dukiya ta fa dani kanki mallakin kine"
danta tsokanesa tace "amman kuma banji kace komi ba tun dawowarka gameda ginin da zakasa aiwa qanen namu ismail fa?"
gani tayi take yanke fara'ar dake fuskarsa ta gushe gaba dayanta sakamakon ambatar Sunan isma'il da tai"
fuska a daure yace "nafasa bazan yi masa ba, shima ay yana aikinsa na gobnati inyanada buqata ya tara kud'insa shima yaje ya gyara gidan nasa dan nama fad'a masa hakan shima.
kaini su baffa mafa kansu nayi dana sanin biya musu mecca da nayi sai naji da kudin na karba na kejerar tasu dana ida shurye shuryen bude gidan mai na da na fara ginawa" firdauseey tace "gskia kam dai asara anyita nima banji dadin faruwan hakan ba alhajina sai dai kuma a kiyaye na gaba dan kuwa dai wannan yarigaya daya faru"
q'utawa mukhtar yayi yace "hmn ai anyi na farko anyi na qarshe dan q'wadala ta bazan qara 6atarwa kan su ba, barima naje na dawo nasan abunda zan musu na rage asara."
(kai jama'a! kuji fa?)
yana gama fad'an hakan kuwa ya miqe ya fice daga falon.
wani iriyan dariya firdauseey tayi har saida dan cikinta ya wuntsula kuwa,
a fili tace "hmnnnn wnda rai ke a jikinsa nada sauran kallo, billaheel azeem su baffa wannan somin ta6i ne kuka soma gani ma daga garemu".
tana gama fad'an hakan ta jawo wayarta takira uwar tata ta sheda mata ai mukhtar yazama nasu harta bata labarin ginin da za'a fara mata itama, karkaso kaji yanda meron tsimbe ta kwarara wani uban ihun farinciki.
Mukhtar kuwa yana fita gidansu ya shiga kai tsaye ya fad'a ko sallama babu, anan ya iske baffa da inno suna zaune tsakar gida suna fira kwalin dabinon ajwad ne a gabansu suke ci.
tsaya musu yayi aka "sannunku su baffa" abunda yace knn ya kama qarfen barandar gidan nasu ya riqe, baffa ya dubesa sosai yace "ah mukhtar ya bazaka zauna ba kai tsaye haka akanmu?, fuskarsa kijin kijin ya dubi baffan yace "eh baffa hakanma yayi dama zuwa nai nace muku zansa a fidda kayanku zuwa gidan isma'il za'a dan d'ora muku wani sabon gyaran ginin ne na sama in yaso aka gama sai ku dawo.
Inno tace "aa mukhtar barmu haka dan iya haka ma ya ishemu wannan gida dai zaman duniya bana q'iyama ba ai yayi"
baffa ya amshe da cewa "gskia ne, dan haka mukhtar kaje mun gode AllAh shiyi albarka mungode hakanma" dai dai mukhtar zaiyi magana saiga isma'il ya shigo gidan yana ganin yayan nasa sai jikinsa ya qara sanyi dan tunawa da abinda ya faru jia, abunda ya faru kuwa jia ne lokacin mukhtar ya dawo office da marecen ranar yana qoqarin tura hancin motarsa gate din gidan nasa dan har ma maigadi ya bude masa wawakeken gate din, to shikuma ismail shima dai dai lokacin d'an aca6a ya saukesa daga mashin dawowarsa kenan ma daga makaranta dayake gyaran makarantar ake musu shiyasa aka maidata ta marece kafin a gama su koma ta safen.
da sauri ya bawa d'an mashin din kudinsa ya qarasa gefen motar mukhtar din yace "waitt yaya, yana maganar ne yana gyara jikkar sa da litittifansa na koyarwa ke a ciki.
dakatawa mukhtar din yayi Amman sam ko kallon isma'il d'in ma baiba still hanunsa na bisa styarin na motar dukkansu.
Isma'il yace "yaya harka dawo sannunka da dawowa, ya kuma qarfin jikin, kan mukhtar yace wani abu saiga alhaji tanimu yazo wucewa cikin motarsa shima, alhaji tanimu shine mai filin nan na kusa da gidan isma'il wanda mukhtar ya nema a kwanaki akace yaje mecca, dan haka parking yayi kusada motar alhaji mukhtar din daga cikin motar yace "alhaji mukhtar barka da ganinka, sai nan fa alhaji mukhtar yasaki fuskarsa yace "yawwa dai alhaji tanimu ya iyali da harkoki"
"Alhambdulilla haj mukhtar, dama naji ance kana nema nane, haj mukhtar yace "eh a kwanaki ba, akwanaki ne na nemeka dan inason siyen filinka ne, haj muntari yace ok wanne filin kenan nawa daga ciki? haj mukhtar yace nanan anguwar amman yanzun ma na fasa ay"
yana fadin haka kuwa Ismail din ya dubesa da sauri saidai baice komi ba ya maida kansa qasa sakamakon hada idanuwa da sukayi yayan nasa ya hangi wasu abubuwan marassa fasaltuwa a qwayar idanun nasa,
haj tanimu yace "shikenan to babu damuwa" nan sukayi musabaha sunadaga cikin motocin nasu sannan haj tanimu din ya wuce.
a sanyaye isma'il d'in yace "yaya naji kace ka fasa siyen filin kuma? baccin nina fad'a wa haj tanimu din kana nemnsa kuma gashi kagansa kuma kace a'a?
cikin isa da taqama gamida gadara mukhtar yadubi Ismail yace "eh na fasa, dukiyar kace koko dukiya ta??! dan haka kai tsaye nace bazanyi ba, kaima ai kana aikin kuma kana samun kud'i to kayi da knka, kai bari ma kaji kasan da sanin cewa daga rana mai kamar tayau dinnan kada ka qara tunanin zaka mori qwandala daga cikin arziq'ina, dan bazai yiyuba kudasu baffa da sauran jamaar anguwa kun maidani Baitul mali gidan tatsar kudi ba, dan haka kaji ma ka q'ara ji" yana gama fad'a masa haka ya bad'e isma'il da qurar wajen ya shige gidansa mai gadi kuma ya tura gate d'in gidan ya rufe...
da kallo kawai isma'il ya bisa yana tunanin kuwa anya wannan yayansa ne koko dai wani mai kama dashi ne?!...


by
*Xexen Fasaha*.
[1/17, 3:10 PM] Xainab Documen: πŸ‘πŸ‘
πŸ₯‘πŸ₯‘
πŸ‘πŸ‘
*DA SAURAN KALLO !!!*

Story and writing
by
Xayyneb πŸ’€πŸ’€

Fasaha online writers f. o.w.

*🌳imparting valuable knowledge and entartaiment is our concern*🌳.

~dedicated to my mom Sadeeq hawwas~

-https://www.facebook.com/Fasaha-Online-Writes-751775151851852/?referrer=whatsapp.

πŸ‘πŸ₯‘πŸ‘
πŸ…Ώ1⃣5⃣
dan haka jikinsa a sanyaye ya wuni yinin ranar.
dan koda ya koma gida Zainab taita tambayarsa akan "mike damunka?" taga jikinsa sukuku haka "bakomi" kawai yake cewa da ita.
mafarin knn daya shigo gidan nasu yanzun yaga yayan nasa abun ya fad'o masa arai.
isma'il yaji baffa yaci gaba da cewa "ida qarasowa isma'il, haka isma'il ya qaraso ya gaida iyayen nasa ya miqawa yayan nasa hannu yana mai cewa "barkadai da warhaka yaya" ga mamakinsu gani sukayi mukhtar din yaqi miqa hannunsa ga isma'il kamar yanda ya buqata, saima kallon su baffa da yayi

Please Login or Register in order to submit comment