Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Khausar tashiga ɗakin Adama ta kwanta Adama kuwa ta nufi ɗakin mijinta suka kwanta tare.

Can cikin dare kamar misalin ƙarfe biyu Baffa Umaru ya miƙe zaune, tare da kasa kunnensa sosai wanda hakan ya kasance ɗabi'arsa ne,
domin shine Garkuwar Rugar tasu, jin motsin tashin sa yasa Adama miƙewa ita ma ta zauna, kusa dashi tana faɗin.
“Lafiya”.

Ajiyar zuciya ya saki da faɗin.
“Naji tsayuwar mota daga can nesa sannan naga haske yashigo har cikin garin nan kamar da akwai wani abu ko dai munyi baƙi ko kuma wani abu!".

Ahankali tace.
“Toh yanzu fita zakayi kenan?”.

“Dole in fita ai Adama idan ban fita ba ‘yan uwana zan bari wani abu yazo ya ritsa da mune ai bazan bari ba dole in fita inga ko menene”.
Ya faɗa a hankali.
Ita kuwa Adama riƙe hannunsa tayi fuskarta na bayyanar da tashin hankali tace.
“Nikam ina tsoro wallahi”.
Da sauri yace.
“Kada ki damu Insha Allah babu abinda zai faru wanda Ubangijin bai sani ba”.

Kai ta girgiza kana tace.
“Kai rashin network ɗin garin nan yana damun mu wallahi, kaga da akwai network tunda yawanci kowa yana da waya zaka kik kira su awaya kowa ya fito kaga idan yaso sai sufito ku haɗu Atsakiyar garin amma Ni ina tsoron fitarka kai kaɗai”.
Suna cikin Maganar ne sukaji antura ƙofar gidansu anshigo Murfin ya fadi ƙasa Kifff kasancewar ba wani Murfin kirki bane gadon kara ne da gwafa aka haɗa.
Cikin han zari ya mike ya tsaya.

Itama miƙewa tayi da saurin ta riƙe hannunsa tace.
“Fita zakayi dan Allah kada ka fita ka tsaya dan Allah kar ka fita”.
Ya juya ya fuskanceta yace.
“Ya kike so inyi idan ban fita ba kina jifa anshigo gidan nan”.
Yana ida maganar ya fin cike hannunta dake cikin nasa ya fita.
Cikin sauri ta shari gabansa ta fito ya zama na itace agaba shi yana bayanta.

Suna fitowa idanunsu ya sauƙa akan mutanen uku dake sanye cikin baƙaƙen kaya hannunsu riƙe da bindigi da kuma toch ligh mai masifar haske.
Arazane Adama tace.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n Hasbunallahu wani'imal wakin”.
Ƙaran buɗe ƙofa da kuma sautin Muryan Adama ne ya fito da Khausar daga ɗaki wacce farkawanta babu daɗewa tana fitowa sukayi saurin kashe mata ido da hasken toch ligh dinsu ita da Adama.

Cikin daga Murya suka ce da Adama
“Ki matsa agabansa kada jini ya taɓa ki ki matsa kada mu illataki!”.
Aruɗe tace.
“In matsa agabansa!?Bazan matsa ba, ku suwaye ne? sannan me kuke nema? me kuka zo yimana acikin daren nan?”.

Ɗaya daga cikin sune yace.
“Kashe sa muka zo yi!”..
Cikin tsananin tashin hankali tace.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n hasbunallahiwani'imanwakil.
dan Allah kada ku kashesa,me yayi muku zaku kashe sa?,Meyesa?”.

Ɗaya daga cikinsu ba wanda yayi magana da farko ba yace.
“Saboda yana hanamu rawan gaban hantsi zamu kashe sa muga takan tsiya bashi yace taurin kai ba”.

Baffa Umaru kuwa murmushi yayi mai cike da Jarumtaka da kuma rashin tsoro yace.
“Ni zaku kashe?,To idan kunga na mutu kwana nane ya ƙare,Kuma Ubangiji shi ya ɗauki raina.
Amma ku baku isa ba babu mai rayawa babu mai kashewa sai ubangiji.
Dan haka raina baya hannunku kuma ajalina baya hannunku idan kunga na mutu ma kada kusa aranku ku kuka kashe ni!”.
Ya ida maganar tare da zabura zai shiga ɗaki dan ɗauko kwari da bakasan.
Ita kuma Adam da saurin riƙesa dai-dai lokacin da suka harbesa akafaɗarsa na dama.

Ƙaran harbin ne ya tashi gaba ɗaya ilahirin mutanen garin Aɓangaren Hajja Nana kuwa tana tashi daga bacci sanadiyyar ƙaran harbin ta dafe kanta da faɗin.
“Wayyo Umaru na Allah ka kare mana Umaru” domin shine mutum na farko daya faɗo mata arai cikin rawan jiki ta miƙe tare da ɗaukar zaninta ta ɗaura kana ta ɗauki mayani ta yana.

Aɓangaren Baffa Jauro yana miƙewa yace.
“Umaru”.
Ya kira sunan sa cikin daga murya.
Baki ɗaya ‘Yan uwansu da sauran jama'a babu wanda ya faɗo masu arai sai Baffa Umaru ko wannensu daya farka zai ce.
“Wayyo! Umarunmu”.

Shi kuwa Umaru juyawan da zai yi sai suka samu damar sake harbinsa ahaƙarƙarinsa na hagu.
Cikin ƙarfin hali da ɗaga sautin Muryar sa yace.
“La'ilah ha Illallahu Muhammad Rasulullahi(S.A.W) Adda Nana ki yafemin yau kam zasu kashe ni ki yafemin kece madadin Uwa awajena duk abinda nayi ki yafemin yau kam sun kasheni sun kashe ni,Yaya Jauro, Yaya Sadu, Yaya, GarGa, Yaya Liman, Yaya Garba,Yaya Sale yau kam sun kasheni sun cire muku ɗaya cikin goma kun zama ku tara!”.

Adama kuwa Aruɗe ta riƙesa jikinta na kyarma taja numfashi amma ta gagara sakewa.
Ita kuwa Khausar numfashin taja amma ta gagara sakewa saboda tsananin ruɗu da tashin hankali da tashiga kamar zata shiɗe!.
Ihun da kiran sunan da yake yasa suka janye toch ligh ɗin su dake fuskar Khausar da Adama suka mai dashi sama wannan dalili ya bawa Khausar damar kallon fuskokinsu da kyau amma baki ɗaya jikinta ya sandare bata da wani kataɓus ɗin motsawa.

Su kuwa ƙirjinsa suka saita suka sake harbinsa akwai wani ƙaton tukunya agefen ya ratsa ya ɓula.
Shi kuwa Baffa Umaru ƙirjinsa ya dafe da faɗin.
“Laila Ha'illalhu Muhammad Rasulullahi (S.A.W)” Shikenan rai yayi halinsa.

Su kuwa mutanen garin baki ɗaya gidan Baffa Umaru suka nufo ko wannensu na rataye da kwari da bakansa sukuwa jin hayaniyar mutanen yasa suka ɓulla ta bayan gidansa suka fice tare da zuwa inda suka bar motarsu suka shiga.

Shi kuwa Baffa Umaru ta cikin tukunyar gefensa ya faɗa jini nata ɓulɓula.
Hajja Nana ce farkon shigowa yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinta ke rawa tana isa tsakiyar gidan,
Ƙofar dakinsa ta nufa, tana isa inda yake ta janyo gawar ta rungume tana kuka tare da faɗin.
“Umaru! Umaru!! Umaru!!! Yau kuma mai zan gani gawar Umaru zan riƙe ahannuna kamar yanda na riƙe gawar Usmanuna!”.Cikin kuka sosai take maganar.

Su Baffa Jauro da sauran mutanen ne suka shigo sudai Allah Allah suke su ƙarasa cikin gidan suga abinda ya faru dashi sam basu yi tunanin bin bayan mutanen ba.
Ita kuwa khausar hanyar da suka bi suka fita take nuna musu da yatsa ta kasa furta komai bare kuma ta taɓuka wani abun Yaya Abba ne da ya shigo yace.
“Yayane Khausar!?”.

Cikin matsananci kuka da tashin hankali tace.
“Yaya Abba sun gudu sun kashe shi sun gudu sunbi ta nan na gansu sunbi tanan!”.
Azabure Matasan suka bi wajen ina tuni sun shiga motarsu sun gudu sukuma su Baffa Jauro, Baffa, Sadu da sauran rungume gawar ƙaninsu sukayi suna kuka.
Hajja Nana kuwa tattaɓa jikinsa tayi, Sadik yace.
“Baba mu ɗaukesa mu kaisa asibiti”.

Sake rungume gawarsa Hajja Nana tayi tace.
“Saddiƙu wani asibiti zamu kaisa bayan sun kashe sa baya numfashi bashi da rai!?”.
Jauro ne ya karɓesa ya duba shima ya rungumesa ganin ya rasu Baki ɗayan su akan Gawarsa suka kwana.
Ita kuwa khausar gaba ɗaya ta rikice ta duburburce bata taɓa gani ankashe mutum agaban ta ba sai lokacin tayi kuka har ta godewa Allah manyan Idanunta sunyi luhu-luhu dasu ba abinda ke faɗo mata arai kamar yanda sukayi hira dashi.

Washe gari akaje aka kira
Ƴan sanda acikin gari suka je sukayi bin cike tare da rubuce-rubucen su na banza da wofi sannan akayi masa sallah aka kaisa gidan sa na gaskiya.
Kana akazo aka zauna zaman makoki, Addar Khausar Ikki da zata je wajenta a Rugar Fulani ce tazo da taji labarin rasuwar Baffa Umaru tana zuwa kai tsaye gidan Baffan Umaru ta nufa duk ‘yan uwan suna can suna karɓan gaisuwa.

Khausar na ganinta ta tashi da gudu ta Rungumeta tana kuka tace.
“Addah Ikki agaba na agabana fa suka kashe shi sun harbesa sun kashe sa ya rasu har lahira!”.
Addah Ikki tace.
Kiyi shiru Khausar duk mai rai mamacine addu'ar mu yake buƙata”.
Kai Khausar ta gyaɗa amma ta gaza tsaida kukan ta Ganin haka yasa Addah Ikki taja hannunta suka fita zuwa gidan Hajja Nana.

Suna Shiga Khausar ta tsaya cikin Muryanta daya dishe da kuka tace.
“Ni ina tsoro bazan shiga ɗakinta ba akwai kuliya”.
Addah Ikki tace to kitsaya na koreta sannan tashiga ɗakin ta fito da kuliyar tasa awani ɗaki ta rufe.
Sai asannan Khausar ta yarda tashiga ɗakin bayan sun zauna Addah Ikki ta zauna ta riƙa yi mata nasiyya tare da kwantar mata da hankali.

Yaya Abba ne ya ɗauki wayarsa ya tafi Bishiyar ƙare zancenka ya kira duk dangi na nesa ya riƙa sanar da su har ya kira Baffa Hammadu na Ɓadamaya ya sanar masa.
Shima washe gari Baffa Hammadu ya ɗauko iyalansa baki ɗaya suka taho da yammaci gab maghariba motocinsi su guda biyu ajere suka shigo Rugar kai tsaye ƙofar Hajja Nana suka nufa sukayi parking motocinsu.

Ita kuwa Khausar na cikin ɗakin Hajja Nana manne da jikin Addarta Ikki suka jiyo Sallama,
Addah Ikki ce ta miƙe da faɗin.
“Laaa Umma na sannan sai Baffanta yashigo daga bayansa kuma wani kyakkyawan matsakaici mutun ne fari ƙal kamar balarabe yayin da Yaya Abba ke biye dasu abaya.

Durƙusawa Khausar tayi tare da fashewa da kuka kalaman Baffa Umaru ne kawai keyi mata suwwa akunne.
Rarrashinta Addah Ikki ta shiga yi tana bata haƙuri da kyar ta tsaida kukan tace.
“Addah Jiya da daddare Baffa Umaru kece min Baffana na Ɓadamaya yana da wani ɗan sa dake tsananin kama da Babana Addah Ikki wannan shine ke kama da Babana?”.
Cikin matsanancin kuka ta ida maganar.

Kai Addah Ikki ta gyaɗa mata alamar Eh.
Ita kuwa khausar kanta ta kife acinyar Addah Ikki ta cigaba da rera kukanta.
Baffan Hammadu ne ya riƙe hannunta ya cewa.
“Khausar kiyi shiru kada kiyi kukan rashin Uba nima Mahaifine agareki ni zan tsaya Miki madadin Uba ako ina dan dai Banason rabaki da mahaifiyar kice Shiyasa na barki kike zaune tare da ita muddin ina raye zan maye Miki gurbin Uba”.
Cikin raunin murya tace.
“ Baffa Allah hokke sabbugo”.
Ameen thumma ameen suka amsa.k
Kana suka tafi gida Baffa Umarun.

Bayan angama zaman Makoki Khausar tabi Addarta Ikki can Rugar Fulani tayi kwana biyu sannan suka dawo bayan sun dawo akayi addu'ar bakwai Baffanta na Ɓadamaya yafara shirin tafiya sai asannan Khausar taga sauran ‘ya‘yan sa daya zo dasu harda Mata bayan sun sake ganawa ne suka tafi.

Akwana atashi ba wuya Khausar ta cika Makwanni uku Arugar Jauro yaya yayin da Baffa Umaru keda mako biyu da rasuwa kullum ‘Yan uwansa matarsa kuma jama'ar gari cikin yi masa addu'a suke domin baza su taɓa mantawa dashi atarihin rayuwarsu ba da kuma irin gwagwarmayar da yayi adomin kare rayukansu.

GEMBILA

Acan ɓangare makarantarsu Khausar kuwa ayaune aka gama gyara ilahirin makarantar daga nesa idan ka hango ginin ba zakayi zaton cewa a Gembila makarantar take ba koda a ƙasashen turawa ne sai ’Ya’yan wane da wane saboda yanda aka ƙawata ginin Makarantar fentin ya kasance Maroon and White haka zalika gate din Maroon anda white ne daga sama An rubuta
*Al'ANSAR ACADEMIC SCHOOL* Rubutun ma Maroon and White ne.

Acikin harabar makarantar kuwa Moddibo ne tsaye hannunsa harɗe aƙirji ya yinda manyan idanunsa ke lumshe yana kallon tsarin ginin Makarantar da akayi wani irin Up stair cycle daga cikin harabar makarantar zagaye yake flowers masu kyau da tsari.
M Jameel ne yace.
“Gaskiya Moddibo kayi ƙoƙari makarantar yayi masifan tsaruwa”.

Murmushin gefen baki Moddibo yayi wanda ke ƙarawa fuskarsa kyau yace.
“Masha Allah haka akeso”.
Ya ida maganar tare da juyewa cikin nutsuwarsa yake tafiya har suka fita acikin harabar makarantar suka shiga motarsu dake gefe afake.
Moddibo ke Driving yayin da M Jameel ke gefen mai zaman banza ƙira'an Sudai's na tashi cikin suratul Nisi'i Moddibo kuwa jinjina kai yayi ayoyin na ratsa sa.
M Jameel ya juya ya kalli Moddibo da bakinsa ke motsi alamar karatun yake bi yace.
“Moddibo kamar akwai motar dake bin mu fa”.
Kai Moddibo ya girgiza yace.
“A'a ba binmu akeyi ba”.
Kai M Jameel ya gyaɗa still yana kallon mirror bai dai ce komai.
Daga nan suka ci gaba da tafiya ganin still kamar binsu akeyi yasa Moddibo ya tsaya.

Ga mamakin su ganin su tsaya yasa wancan motar tayo kansu gadan-gadan...!


*Wasan fa yanzu aka farashi. Bakin zaren labarin sun kai 12 dozi. Kenan. Akwai ababen dake a duhu fa. Saninsu sai kun bibiyu Al'ƙalamin Shatu yar Aliyu Garkuwa. Jikar Muhammad Babayo Maiturare. Kana kuma (BODDIN DEDDE)*



By
*GARKUWAR MARUBUTA*
[19/07, 7:44 PM] Halimatu A/rahman Sadeeya: 📝🍇✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇

*SAKAYYAH*
_Page 8_

_NA_
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


*Free page ne ƴar uwa in sun ƙare ko kinga littafin SAKAYYAH a a waje ba a cikin Groups na na SAKAYYAH ɗin da nabuɗeba, toh na satane kuma na Allah ya isane, kana na Yaseen doguwane😂 bulluƙutu kuma baƙar mutuwa... Dan haka biya ki karanta cikin Salamah yar uwa ba haƙƙin kowa kanki, littafin SAKAYYAH 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. Sai in saki a Group ki karanta abinki Nana lfy fata lfy*

Masu son kayan Ɗa'a akwaisu Available.

Motar tayo kansu gadan-gadan.
Aruɗe M Jameel yace.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n!Hasbunallahu wani'imal wakin!! A'a su waye wannan suna da hankali kuwa!?”.
Cike da al'ajabi Moddibo ya zuba musu ido tare da ƙoƙarin yiwa motar key sai kuma ya gaza yin komai ya zubawa motar ido ganin gada-gadan fa ta nufi kansu haiƙan ƙadaran.

Sai da motar tazo gab dasu sai kuma ta kauce ta hau titi ta wuce.
Wani irin nannauyan ajinyan zuciya mai masifan ƙarfin M Jameel ya dire tare da meda kansa ya jingina da kujerar.

Shi kuwa Moddibo Idonu ya tsirawa motar cike da mamaki sai kuma ya motsa laɓɓansa a saman lips ɗinshi ya furta.
“Wannan wani irin tuƙi ne?.
Tuƙin ganganci ne ko kuwa dai da nufi ne?”.
Dalilin da yasa ya tsaya ma atunanin sa ko ɗaya daga cikin ‘Ya‘yan Malam Arɗo ne sai kuma yaga saɓanin haka.
Key yayiwa motar tare da kallon M Jameel dake lumshe da ido a hankali yace.
“J nayi zaton ɗaya daga cikin ‘Ya‘yan Malam Arɗo ne ya biyo mu shiyasa na tsaya, amma inaga basu bane wata ƙil ɗan koyon tuƙi ne”.
Ya ida Maganar batare daya ɗauki abin da muhimmanci ba.

Kai M Jameel ya gyaɗa da faɗin.
“Allah ya kyauta amma na tsorata da ganin yanda sukayo kanmu kamar da gayya suka yi sun tsinka min zuciya saura kaɗan fa su hau kanmu”.
Girgiza Kai Moddibo yayi kana yace.
“Da alama dai 'yan koyo ne!”.
Kai M Jameel ya gyaɗa tare da gyara zamansa, kana suka cigaba da tafiya.
Kai tsaye masallaci suka nufa kasancewar lokacin sallar Azahar yayi, bayan sunyi parking ne suka fito suka nufi cikin masallacin, aƙofar masallacin suka tsaya kusan tare sukay addu'ar shiga masallacin.
_“Auzubillahil Azim,Wabiwajhihil Kareem,Wasulɗanihil Ƙadiym,Minal Bismillahi Wassatu Wassalamu Ala Rasulullah.Allahummaftahliy Abwabal Rahmatik”_.
kana suka shiga.

Bayan sun idar sun fito daga masallacin M Jameel ya juya ya kalli Moddibo yace.
“Muje gida muci abinci”.
Da gefen ido
Moddibo ya kalleshi tare damotsa lips enshi zaiyi magana.
M Jameel yayi saurin ɓata fuska tare da cewa.
“Ba zakaje ba ko?”.
Murmushi Moddibo yayi tare da juyawa akalar motar zuwa gidansu M Jameel.
Yanzu ƙira'ar Sheykh Jabeer suke saurara har suka isa.

Bayan sunyi parking suka shiga Babban falon gida Adining suka zauna sukaci abincin shikam Moddibo kaɗan yaci ya bari.

Miƙewa sukayi suka fita Fitowarsu daga falon yayi dai-dai da ƙarasowar Hajiya Karima wajen M Jameel yace.
“Aunty Karima ina yini”.
Ba tare data amsa ba ta watsawa Moddibo kallon tsana tace.
“Maƙale anzo kenan?”.
Cikin ɗan sakin fuska yace.
“Ehh”.
Cike da mamakin halayensa da ƙarfin halinsa tace.
“To wai kai dan Allah ka rabu da bawan Allah nan da dukiyar mahaifinsa mana ko zai samu yayi abin kansa!”.

Cikin takaici M Jameel yace.
“Dan Allah Aunty ki ƙyale Moddibo da irin wa'annan kalaman mana, na sha faɗa miki shi ba irin mutunen da kike zato bane, ta ya zan fahimtar da ke?”.
Baki ta taɓe tare da juyawa tabar wajen kamar zata tashi sama.
Shi kuwa Moddibo lumshe idanunsa yayi tare da cije laɓaɓɓansa na ƙasa tare da kiran sunan Allah aransa.
Araunane M Jameel yace.
“Dan Allah Moddibo kayi haƙuri da abinda Aunty Karima keyi maka”.

Cikin kula Moddibo ya dubesa cikin yanayin nutsuwarsa da kuma ƙasaitarsa yace.
“J.kada ka damu inda sabo ai yaci ace na saba da halin Aunty abinda tun tasowar mu a haka nake da ita abinda tun bamu wuce shekaru shida-shida a duniya ba take min, har yanzu da muka bawa talatin baya, ai ya zama man shafawa kawai dai abu biyu ke sawa ban taɓa yi mata wonkin babban borgoba”.
Ya ƙare mgn tare da nufar ɗakin M Jameel.

Cikin jinjina kai M Jameel ya bi bayansa yana mai al'ajabi abinda Modiyke ɓoyewa tsawon shekaru da yake cewa dalilin dake hanasa taka mata birki, yayi ya gaya masa kuma sam yaƙi.
A ha dai suka isa, suna shiga ɗakin Moddibo ya kwanta bisa kujera tare da lumshe idanunsa alamun bacci zaiyi.

Acan gidansu Lamiɗo kuwa Mommy ce zaune yayin da Asma'u ke zaune daga ƙasa gefen ƙafafunta ta ɗago kanta tace.
Mommy asatin nan zamu koma makaranta gashi har yanzu Khausar bata dawo ba”.

“Wallahi kuwa gashi duk kwana biyun nan ba muyi waya ba, dan munfi sati da yin mgn”.

“Ayyah Allah Andi Meyesa”.
Cewar Asma'u
Kai Mommy ta jinjina tare da cewa.
“Kuma Idan ka kiransu ba zai shiga ba sai dai idan su suka kira ka”.

Gyara zama Asma'u tayi tare da cewa.
“Gaskiya Mommy Idan ta kira kice ta dawo tasan ana komawa za'a fara karatu gadan-gadan”.
Mommy tace.
“Inasha Allah zan faɗa mata”.
Daga nan sai suka ɗan ci gaba da hida, daga bisani sukayi
Sallama sannan ta tafi.

Acan Rugar Jauro Yaya kuwa yau sati da rasuwar Baffa Umaru baki ɗaya basu da cikakkiyar walwala duk da cewa sun dawo da sabgoginsu kamar da sai dai ciwon na nan aransu.

Khausar kuwa sosai tayi sanyi tun da akayi rasuwar bata cikin hayyacinta shiyasa bata samu ta kira Mommy ta ba.
Kasancewar jiya akayi adduo'ar bakwai Baffanta da yaransa duk sun koma bayan sunyi exchange na number ita dai ta Mommy ta basu. tare da yiwa Khausar al'ƙawarin kai mata ziyara wataran...

Anutse Khausar ta juya ta kalli Yaya Abba cikin sanyin murya tace.
“Ayyah yaya Abba dan Allah ka bani wayarka zan kira Mommy na”.
Kallonta Yaya Abba yayi cike da tausayi duk tayi wata iri yace.
“Toh shikenan amma ki bari sai gobe ki kirasu dan yau network bashi da kyau koda kin hau kan Bishiyar ma ba zaki ji magana ba”.
Kai ta gyaɗa masa kana tace.
“Toh Allah ya kaimu”.
“Amin”.
Ya amsa tare da miƙewa ya fita.

*GEMBILA*
Washe gari da safe tunda gari ya waye Malam Arɗo ke ta kiran wayar Moddibo awaya amma ba'a ɗagawa.
Shi kuwa Moddibo Anutse ya farka daga baccin daya koma tare da furta.
_“Alhamdulillahil Lazi ahyana bada amatana wa'ilaihil nushur”_
Wayarsa dake gefe ya janyo ganin Miss call ɗin malam Arɗo bar katai da yayi ne ya sashi ajiye wayar.
Kana ya miƙe ya shiga toilet.
Tare da addu'a a baki nai

Wanka yayi wanda ya ɗauke sa kimanin minti talatin kana ya fito yana mai faɗin.
_“Gufranaka”_
Suman kansa yake tsanewa da baby pink towel mai taushi.
Yayinda yake sanye da jibgegiyar bathrobe pink color mai masifar taushi wacce ya saƙale igiyoyinta a ƙugunsa.
A hankali ya zauna agaban dressing mirrow tare da,
Jona handdryer kana ya kunna tare da gyara zamansa da kyau bisa kujerar, dressing mirror ɗin tare da fara busar da sumar kansa mai ɗan karen sulɓi.
56 seconds yayi zuwa 1 minute yayi yana jujjuya kan handdryer ɗin tare da sa hannunsa ɗaya dake riƙe da madaidaicin Kum.
A hankali ya ajiye dryer din tare, da buɗe wani gora mai haɗe da man gashi na musamman, wanda Ummi ce ke haɗa musu, ɗan tsiyaya yayi kana ya murza tafin hannunsa tare da shafa.
Wani irin sheƙi da ƙyalli mai ɗaukan ido suman nasa ya farayi tare da fidda wani ni'imtaccen ƙamshi.
wani ƙum mai laushi wanda yafi na farin ya ɗauka tare da bin gashin nasa ya mishi tafiyar tsutsa,
Wow masha Allah, kamar saƙan taburma haka gashin ya kwanta da salo mai burgewa.
Goge tafin hannunsa yayi da towel ɗin dake bisa ƙafaɗarsa, kanaya
lakato lotion ɗin sa mai daɗin ƙamshi ya shafa jikinsa baki ɗaya.
idonsa ya lumshe tare da kauda kansa lokacin da yake shafawa cinyoyinsa mayin,
fuskarsa ya ɗan shafawa, mai ɗin tare da sa yatsarsa babba ya kwantar da gashin giransa na gefen dama, kana yasa babbar yatsar na hagu ya kwantar da na gefen hagun. sannan ya ɗan tsiyayi man kanshin ya shafawa tattausan sajensa dake kwance lip-lip ya shafa, wani irin sheƙi sajen keyi yana fitar da sanyayyan ƙamshi.
Anutse ya Miƙe ya buɗe durowarsa ya ɗauki jallabiyarsa mai masifar tsada da taushi Kalar Army green, kana ya zaro tattausan boxer and singlet farare ƙal-ƙal,
ɗan sunkuyawa yayi ya sanya boxer ɗin ba tare da kalli surarsa ba.
Kana ya miƙa tare da dai-dai ta zaman robor a gugunsa,
Bathrobe din ya kwance, kana ya saƙalashi bisa wata yar Kekkyawar masaƙali dake gefen drowersa, singlet ɗin ya saka, kana ya zira tattausar jallabiyar dake zuba sheƙi da ƙyalli wacce kai da ka gani kasan taja kuɗi.
baƙin hirami ya jawo, sanya kana ya naɗe kansa da hirami tare da sako jelar ɗaurin ta gefensa na hagu tsayawa yayi agaban Dressing mirrow tare da ɗaukar kwalbar turaren mai masifar ƙamshi ya feshe ilahirin jikinsa dashi wayarsa ya ɗauka tare da sanya wa a aljihun gaban rigarsa kana ya fice.

A motarsa ya shiga bayan ya buɗe gate sannan ya fice kana ya sake fitowa ya rufe gate ɗin.

Aƙofar gate ɗin gidan Malam Arɗo yayi Hong mai gadi ya buɗe masa yashiga Babban gida ne sosai sai dai kallo ɗaya zaka yiwa gidan kasan mamallakin gidan mutum nai mugun maƙo da kirta babu wani fentin arziƙi ajikin ginin gidan haka zalika ginin ɗakunan single rooms ne cikin haraban gidan kuwa koda flow babu daga can kusan ƙaramin ƙofar da zai sadaka da cikin gidan rijiya ce babba anyi masa murfin ƙarfe fitowa Malam Arɗo yayi yana murmushi.

Ɗan guntun Murmushin gefen baki Moddibo ya mayar masa tare da cewa.
“Ina kwana Malam ɗazu ka kira ina bacci”.
Ya ida maganar yana shiga ɗakin ɗaya daga cikin matan Malam Arɗo mai suna Hajiya Zainabu domin Malam Arɗo ya ɗauki Moddibo tamkar jika.

Wara ido Moddibo yayi yana kallon Hajiya Zainabu yace.
“Hajiya ina kujerun ɗakin?
Indai ba kujera Ni gaskiya bazan zauna ba”.
Sai kuma ya juya tare da kallon Malam Arɗo yace.
“Malam dan Allah asamu kujeru saboda idan sukayi baƙi su samu inda zasu zauna”.

Hararansa Malam Arɗo yayi tare da cewa.
“Ba kai bane kake lissafin duk abinda zai cin yemin aljihu kasan yanda gyaran makarantar nan ya cinye min kuɗi kuwa?.
Yanzu ma abu biyune yasa na kira ka na farko motata ta ɓaci zaka kaini Rugar Jauro yaya sannan kuma muyi magana akan ƙara kudin school fees ɗin yara dan gaskiya saina fanshe kuɗin dana kashe a school fees ɗin forko Aradun Allah.

Kai Moddibo ya jujjuya tare da yar kwaffa hana yace.
“Toh ba matsala ai ka'ida iyayen yara.
Yau kuma mai yasami motar ta lalace ne? Ko kuma sa maine bazaka iya ba”.
Yana mai laluben aljihunsa yace.
“Duka biyu, ta lalacen kuma yau du-du-du da naira ashirin da biyar na tashi”.
Kai Moddibo ya sunkuyar yana mai kallon wayarshi yace.
“Kuma har ina Rugar Jauro Yaya yake da nisa ne!?”.

Da sauri Malam Arɗo Yace.
“Koma da nisa kai zaka kaini dan badan ka matsa min akan gyaran makarantar nan ba da wataƙil in canza mota kuma da ko ban canza a ai bazan rasa kuɗin da mai ba”.

Murmushi Moddibo yayi kana yace.
“Dama wataƙil ne Malam koba ayi gyaran makaranta ba da wuya ka canza wannan motar.

Dariya Hajiya Zainabu tayi tace.
“Aikam Moddibo ka faɗi gaskiya”.
Anutse Moddibo yace.
“Koma dai menene dan Allah Malam ayi ƙoƙari asa musu kujeru dubi fa ba laida ba Capet ba kujere ba tiles sai siminti kawai dan Allah ka daure kasamu tiles da kujeru”.

Murmushi Hajiya Zainabu tayi tare da yiwa Moddibo alamar jinjina da hannu kana tace.
“Allah ya maka albarka”.
Tayi maganar yanda Malam Arɗo ba zai jiba.

Kai Malam Arɗo ya gyaɗa da faɗin.
“Naji wuce muje".
Taɓe baki Moddibo yayi kana suka fita.
Ɗakin Uwar gidan Malam Arɗo suka

1 Comments On SAKAYYAH
avatar
fatima-8-5-3

6 months ago

Reply

Allah ya qara basira

Please Login or Register in order to submit comment