Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a ƙasa ya amsa da.
“Ameen Allah ya sawwaƙa”.
Sannan ya rufe musu mota.
Driver yaja suka tafi kana Moddibo da M Jameel suka shiga motarsu suka tafi.
Sannan Malam Arɗo da Malam Isa suka shiga mota suka tafi.

Ahankali Moddibo ke Driving yayin daya tsirawa titin Idanu,M Jameel dake gefe ya sauƙe ajiyar zuciya tare da cewa.
“Kai Allah ya gyara wannan al'amarin Ubangiji Allah ya ƙara tsarewa ya kare gaba!”.
Anutse M Jameel ya juya ya kalli Moddibo jin bai amsa addu'ar tasa ba cike da kulawa yace.
“Ya dai? A.J meyafaru ne kayi shiru? Ina ta magana ba reply?”.
Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe tare da furzar da iska mai zafi da kallon M Jameel kamar wanda aka fisgo maganar daga bakinsa yace.
“Wannan Accident ɗin shiryeyyene!”.
Zare ido M Jameel Yayi tare da cewa.
“Kamar ya shiryeyyene?”.
Ƙaramin tsaki Moddibo yaja kana yace.
“Akwai abinda ban gamsu dashi ba amma babu komai insha Allah zamuyi bin cike saboda na ɗauki number Motar Allah dai yabawa yaron nan Lafiya”.
Sauƙe numfashi yayi tare da fesar da iska daga bakinsa kana yace.
“Kaga yanda mahaifiyarsa tashiga tashin hankali amma matar nan da suka zo da ita hmmmm”.
Sai kuma yayi shiru tare da faɗin.
_“Astagfirullah Wa'atubu Ilaik ³_”.
A hankali ya numfasa tare da cewa.
_“Azzanna zambu walau kana haƙƙun,_
Allah kagafar ta min Allah kaya femin munana zato dana yi mata”.
Kallon M Jameel Yayi kana yace.
“J bangamsu da yanayinta ba”.
Jinjina kai M Jameel yayi tare da cewa.
“Sosai ma nima na lura da wani yanayi atare da ita amma dai Astagfirullah Allah mun tuba”.
Har suka shiga makarantar ba wanda ya sake magana Moddibo na Parking ya fita.

Acan gidan Lamiɗo kuwa bayan sun isa Lamiɗo ya riko Ramadan aka kafadarsa Already mai ɗaurin yazo kai tsaye sashen sa ya nufa dashi cikin sauri Mommy ta tsaya daga gefensa cikin raunin murya tace.
“Mai Martaba akaishi wurina kawai aje amasa acan”.
Kallon ta Lamiɗo yayi kana yace.
“Aysha aje amasa awaje na kawai ni yakamata inyi jinyarsa tunda yaro na miji ne”.
Girgiza kai tayi kana cikin sanyin murya tace.
“Zaka bar uzurorin kane ai ƙaramine zan iya yi masa komai yanzu da Haiydar ne zaka iya cewa zai fi ƙarfin indinga ɗaga sa ko kuma yi masa wani abu”.
ta faɗa Idanunta na zubar da hawaye
Jinjina kai Lamiɗo yayi tare da cewa.
“In dai har kina so in Samu ƙarfin gwiwa kidena zubar da hawaye kin san Banason ganin hawayen ki”.
Khausar kuwa tuni ta bar wajen.
Bayan sun shiga falon Mommy Malam Bala ya ɗaura ƙafar cikin tsanananin azaba Ramadan ke kuka saboda zafi da raɗaɗi daya ke ji miƙewa Mommy tayi tashiga Bedroom ɗin tana hawaye cike da tausayinsa Khausar ma miƙewa tayi ta shige Bedroom ɗin ta yana sheshsheƙa ba zata iya juran Kallonsa cikin ciwo ba Lamiɗo kuwa riƙe sa yana rarrashin sa bayan angama ɗaurin Malam Bala ya basu magunguna da za'a shafa ledan da M Jameel ya bashi ya ɗauko tare da ɓalla masa maganin ya bashi sannun ahankali Ramadan ya fara sakin Ajiyar zuciya nan da nan bacci ya ɗauke sa miƙewa Lamiɗo yayi ya kwantar dashi akan 3sitter kana ya nufi Bedroom ɗin Mommy.

Hajiya Bunayya kuwa ganin ba kowa afalo yasa ta sanya hannunta abakin zaninta tare da ciro wayarta kana tayi dearling wani Number tana Jin anyi picking tayi ƙasa da murya tare da cewa.
“Ya haka? Shima wanda kuka buge ɗin karaya ne fa kaɗai!?”.
A kuma dai-dai lokacin Khausar ta fito daga Bedroom ɗin ta jin falon yayi shiru ta ɗago manyan Idanunta da sukayi ja ta kelleta.
Cikin basarwa Hajiya Bunayya tace.
“Wallahi Allah ya taƙaita karaya ce kaɗai toh Nagode”.
sannan ta katse wayar.
Jinjina kai Khausar tayi tare da Kallon ta babu walwala atare da ita tace.
“Hmmm Mai rabon ganin baɗi dai zai gani koda ana kamawa ana sawa aturmi ana kirɓawa, kana zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana ga muzuru ga shaho sai yayi”.
Hararan ta Hajiya Bunayya tayi tare da cewa.
“Ni tsiyata dake kin cika habaici da zaurance gaki Bafulatana amma kamar ba haushiya”.
A kuma dai-dai lokacin Mommy da Lamiɗo suka fito daga Bedroom ɗin suna murmushi Mommy na Kallon Hajiya Bunayya tace.
“Yaya keda Khausar dai”.
Murmushin yaƙe Hajiya Bunayya tayi tare da cewa.
“Ai lallai dai kam”.
Kallon Lamiɗo Mommy tayi kana tace.
“Yayi bacci”.
Jinjina kai yayi tare da cewa.
“Eh kafin ya tashi ya kamata adafa masa kaji ahaɗa da maganin da Bala ya bada yana tashi sai abashi yaci”.
Kai Mommy ta gyaɗa tare da karɓa, Khausar ta kalli Mommy tare da faɗin.
“Mommy kawo inje in dafa masa ainaga kamar akwai sauran kaji a fridge kana ta wuce kichen ɗin”,
Jinjina kai Mommy tayi tare da miƙa mata.

Acan Makaranta kuwa Haiydar na ganin Moddibo da M Jameel sun shigo ya miƙe da sauri tare da riƙe hannun Raudat da har zuwa lokacin take kuka kana ya nufi wajensu.
Cikin sanyun muryan yace.
“Malam ya jikin Ramadan?”.
Cike da kulawa Moddibo ya kallesa cike da tausayi ya riƙe hannun Haiydar acikin nasa tare da cewa.
“Bakomai fa ya samu lafiya karaya ne kaɗai Abbanku yaje ya ɗauke sa ankoma dashi gida za ayi masa ɗaurin gida ka kwantar da hankalin ka Haiydar ba komai insha Allah”.
M Jameel kuwa Raudat ya ɗauka tare da kallon Moddibo kana yace.
“Ita wannan kam Malaman su sunce ba tayi karatu ba sai kuka”.
Ahankali Moddibo ya juya ya kalleta baki ɗaya fuskarta yayi ja Idanunta sun kumbura kana jikinta ya ɗauki zafi cikin sanyin murya yace.
“Kiyi haƙuri Hassan ɗinki yana lafiya babu abinda ya sameshi zaki koma ki same shi agida cikin ƙoshin lafiya Insha Allah”.
Kallonsa tayi tare da cewa.
“Da gaske!?”.
Kai ya gyaɗa mata.
“Toh zamu koma gida yanzu”.
Ta faɗa tare da fashewa da kuma hadda sheshsheƙa.
Ajiyar zuciya M Jameel ya sauƙe tare da kallon Moddibo kana yace.
“Ina ganin ya kamata abarsu su koma gida dan yau ɗin nan ko sun zauna bawani karatu zasuyi ba ga Haiydar dake Babba ma baki ɗaya agigice yake bare ita yarinyar sai kuka take duk jikinta yayi zafi”.
Jinjina kai Moddibo yayi idanunsa akan Raudat yace.
“Eh hakan yayi sai su koma gida kawai”.
M Jameel na Kallon Haiydar yace.
“Bari akira gida sai aturo Driver yazo ya ɗauke ku”.
Kai Haiydar ya gyaɗa kana ya nufi Office ɗin Malam Arɗo ya sanar masa nan Malam Arɗo ya kira Lamiɗo babu daɗewa Driver yazo ya ɗauke su.

Suna isa gida Raudat ta fice da gudu tare da shiga falon Idanunta ya saƙa akan Khausar dake zaune gefen Ramadan tana bashi kazar da already ta gama dafawa shi kuwa yana amsa yana ci Zugin ƙafar yayi sauƙi Sosai sai abinda ba arasa ba da gudu Raudat ta shiga tare da ƙara sawa ta rungume kan Ramadan cikin sauri ya ɗaga mata hannunsa na hagu tare da nuna mata ƙafar sake sa tayi tare da komawa gefensa ta zauna kana tace.
“Ya ƙafan ka?”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Da sauƙi”, Langwaɓar da kai tayi kana tace.
“Allah ya ƙara sauƙi sannu³”.
Haiydar kuwa zama yayi agefensa tare da rintse idanunsa hawaye masu zafi suka zubo masa ahankali ya buɗe Idanunsa tare da sauƙe su akan Mommy kana yace.
“Mommy tamkar gimmawar walƙiya haka naga motar nan tazo ta bugi Ramadan sanda yayi sama kafin ya faɗo Mommy banyi tsammanin kansa ba zai fashe ba”.
Khausar dake cirewa Ramadan ƙasusuwa ajikin kazar ta ɗago kanta tare da miƙawa Ramadan tsokar kana ta mayar da kallon ta kan Haiydar tace.
“Allah ne ya kare Haiydar saboda addu'ar mahaifiyarmu saboda haka Ubangiji zai ci gaba da kare mu yana mana katangar ƙarfe da magauta!”.

Da sauri Mommy dake cirewa Raudat Uniform ta ɗago ta kalleta kana tace.
“Khausar wasu magautan kuma wannan ai ƙaddara ce wacce ta riga fata”.
Murmushi mai ciwo Khausar tayi kana tace.
“Hmmm Mommy kenan”.

Acan ɓangaren Hajiya Bunayya kuwa bayan tashiga ɗaki zaune ta samu Amina hannunta riƙe da Tuffa tana ci,
Amina na kallonta tace.
“Mommy ba abinda ya sameshi ko?”.
Ƙwaffa Hajiya Bunayya tayi tare da zama kana cike da takaici tace.
“Ai shi Haiydar ba abinda ya sameshi ko ƙwarzani bai yiba. Ramadan ne kaɗai ya bugu ba wani na arziƙi ba Karayane kaɗai”.
A kufule ta ajiye Mayafinta tare da kallon Amina data tsareta da ido kana tace.
“Na kirasu munyi magana dasu sannan na nuna musu ɓacin raina sai suka ce wai abinda yasa haka saboda lokacin Malamai sun fara zuwa idan suka tsaya za'a iya kama su”.
Ya mutse fuska Amina tayi kana tace.
“Ai dai kam sai ahankali”.

Hannu tasa tare da ɗaukar Ayaba a Plate dake gaban Amina kana tace.
“Ɗazu bayan kin dawo ina kika tsaya dana shigo ban ganki bane?”.
Murmushi Amina tayi tare da cewa.
“Ina side ɗin Gimbiya Dadu nida Uncle Naseer”.
Wara Ido tayi kana tace.
“Allah ko?,Ni dai Amina da zaki yarda sannan badan Masifar Son da yake yiwa wannan shegiyar Khausar mai kama da sadaka Yallanba yanda yaron nan ya samu cigaba da arziƙi ga kuma arziƙin da Iyayensa suke dashi da kin haƙura da Jameel din Nan duk da kuwa arziƙin da Mahaifin sa yake dashi”.

Ƙwaffa Amina tayi tare da cewa.
“Nifa Mommy Ina son Uncle Naseer kuma Ina son Malam Jameel saboda gaba ɗayan su suna da kuɗi kuma dama Ni ko Malam Jameel saboda kuɗin sa nake son sa”.
Sai kuma tayi saurin cewa.
“Yawwa Ummah ni kuwa Akwai Aure atsakanin mu Uncle Naseer?”.
Jinjina kai Hajiya Bunayya tayi tare da ajiye ɓawon Ayaba kana tace.
“Sosai ma kuwa Akwai Aure atsakanin ku ko a musulunci ya halatta”.
Kai Amina ta gyaɗa tare da faɗin.
“Ummah kiga yanda yake kashewa yarinyar nan kuɗi kinga wayar daya siya mata kuwa wayar kusan dubu ɗari huɗu da hamsin kinga siye-siye tunda kinga Malam Jameel Anyi anyi aka mashi awajen Boka an kasa tunda shi wannan yana da riƙo da Ibada shi kuma wannan shgirigirbaune za'ayi saurin kamashi”.
Jinjina kai Hajiya Bunayya tayi tare da cewa.
“Hakane fa Amina nima na fara wannan tunanin ga abu mai sauƙi sawa zamuyi asa ya tsani Khausar ɗin ya soki shidama in anyi auren bazaku wuce wata uku ba anan zaku tafi india”.

Murmushi Amina tayi kana tace.
“Eh kuma wannan abu mai sauƙi ne duk da masifar son da yake yiwa Khausar tun tana ƙarama amma yau ɗin nan tun da muka zauna tsawon zaman mu ya sake min fuska kamar zai iya maraba da duk abinda naje masa dashi”.
Cikin jin dadi ta saki wani murmushi tare da cewa.
“Tun da muka zauna yau ko yawan kiran sunan Khausar da yake yau be yawaita ba Ummah”.
Ajiyar zuciya Hajiya Bunayya ta sauƙe kana tace.
“Bari zamu duba mu gani sannan zamuyi magana akai ai ɗazun muka rabu da Jameel da wannan ɗan banzan Moddibon ko yaushe ka gansa da Jallabiya kamar ɗan Larabawa”.
Dariya Amina ta fashe dashi kana tace.
“Aini shiyasa Samira Sani ke bani mamaki da take son Moddibo me yake dashi meya mallaka komai fa idan kika ganshi dashi sai dai idan Malam Jameel ne ya bashi kullum yana nan acikin Jallabiya bashi da kayan daya wuce Jallabiya ko motar da yake hawa daga kin gani kinsan mahaifin Malam Jameel ne ya saya mishi”.

Ta gumi Hajiya Bunayya tayi kana tace.
“Ikon Allah shi kuma haka yake ashe se Uban faɗin rai kamar ɗan ƙaruna saboda arziƙi yana abu kamar mai rawani gashi da uban kwarjini”.
Tsaki Amina taja kana tace.
“Ko sutura kika gansa dashi sai dai in Malam Jameel ne yasaya mishi saboda duk yawanci kayansu iri ɗaya ne na rasa Meyesa Samira Sani take son shi koda yake inaga tsabar kyansa da ƙwarjinsa take so”,
Sai kuma ta gyara zamanta tare da taɓe baki kana tace.
“Inba hakaba me abin so ajikin talaka faƙiri komai sai aboki ya masa, arayuwa gashi ba kuɗiba se shegen jijji da kai da taƙamar banza da ɗan karen ƙasaita”.
Dariya Hajiya Bunayya tayi tare da kallon Amina kana tace.
“Nima kaina abin ya ban dariya Amina da Hajiya Lami tazo tana ta haukan bin bokaye akansa yaron da ko wa'azin sa kake kallo yana cikin Jallabiya da Hirami kamar rainon Saudi”.
Dariya Amina tayi kana ta taɓe baki tare da faɗin.
“Ai dai kam ni dai mai ruwana su suka sani mu dai yanzu mun canza shekarar mu daga kan Malam Jameel zuwa Uncle Naseer”,
murmushi ta saki tare da kallon Hajiya Bunayya kana tace.
“Idan kuma za'a tayi akansu su biyun muna raba ƙafa da duk wanda yazo tun da duka Iyayen su nada arziki kuma suma suna dashi duk kansu babu wanda yayi karatu aƙasar nan ko wannensu mijin nunawa sa'a ne da zaran na auri ɗaya daga cikinsu zan zama big Girl acikin garin nan”.

Acan ɓangaren Gimbiya Dadu kuwa Uncle Naseer ne zaune akan 2sitter hannunsa riƙe da wayarsa yana latsawa Gimbiya Dadu na zaune kan Sallaya tunda ta idar da maghariba bata motsa ba suna taɓa hira jefi-jefi.
Cike da nutsuwa Lamiɗo yayi sallama ya shiga, tare da miƙawa Uncle Naseer hannu sukayi Musabaha kana ya gaishe da Gimbiya Dadu.
Cikin sanyin Murya Lamido ya kalli Gimbiya Dadu kana yace.
“Ɗazu fa Ramadan ya gamu da hatsari ya karye”.
Da sauri Uncle Naseer ya ɗago kansa kana yace.
“Subhanallah³ ikon Allah”.
Gimbiya Dadu ma cikin sauri ta ɗago kanta tare da kallon Lamiɗo cikin yana yin damuwa tace.
“Subhanallahi bari idan na idar da Sallar Isha'i zanje in duba sa”.
Miƙewa Uncle Naseer yayi tare da cewa.
“Bari naje na dubasa”.
Ya faɗa tare da ficewa.

Kai tsaye sashen Mommy ya nufa bakinsa ɗauke da Sallama Ahankali Idanunsa suka sauka akan Khausar dake zaune gaban Ramadan kallon falon yayi yaga ba kowa sai su kadai.
Ahankali Khausar data ji Sallamar sa ta juya ta kallesa.

Cike da duniyan ci ya sakar mata da mayaudariyar murmushi kana ya kashe mata ido ya wani langwaɓar da kai tare da Shagwaɓe fuska kana yace.
“Ya dai Matas?”.
Shiru Khausar tayi tare da yin ƙasa da kanta cike da mamakinsa aranta tace Uhmmm Uncle Naseer da tsaurin Ido duk abinda ya aikata ashe zai iya zuwa inda nake.

Cikin rashin damuwa ya matsa kusa da ita idanunsa akan Ramadan yace.
“Ayyah Ramadan sorry Allah ya sawwaƙa³”.
Kai Ramadan ya gyaɗa kana yace.
“Ameen Uncle Naseer”.
Hannun Ramadan ya riƙe tare da cewa.
“Me kakeso in kawo maka”.
Kallonsa Ramadan yayi tare da cewa.
“Komai ma ka siya min ina so Uncle Naseer ”.
Kai ya gyaɗa tare da cewa.
“Toh Autan Mommy”.

Ahankali Naseer ya juya ya kalli Khausar da Idanunta ke kan Ramadan ya narkar da murya tare da faɗin.
“Mommy fa?”.
Kamar ba zata ce komai ba sai kuma tace.
“Ta shiga ciki tana Sallah Isha'i ne”.
Jinjina kai yayi kana yace.
“Ayyah Allah ya bashi lafiya”.
Ta lumshe Idanunta tare da cewa.
“Ameen ya Allah”.
Ahankali ya juya gareta tare da gyara zamansa akan rock ɗin kamar yatsun hannunsa zasu taɓa yatsun Ƙafarta.

Ya karyar da kai tare da sanyaya muryarsa kana yace.
“My dear yau kusan kwana uku kenan koda naki ra wayar ki bata shiga idan wani laifi na miki sai ki faɗa min laifina in baki haƙuri duk da cewa ina da yaƙinin bani nayi miki laifa kece kikayi min laifin, gashi ke kuma baki iya bada haƙuri bako”.
Saurin Kallonsa Khausar tayi tare da maimaita bani nayi miki laifi ba aranta.
Kamar yasan tunanin da take ya jinjina kai tare da narkar da murya kana yace.
“Yes My Khausi Kece kika yi min laifi amma baza kiban haƙuriba to naji na amshi laifina.
Ni zan baki haƙuri duk da cewa kin ɓata mana aiki”.
Sai kuma ahankali ya juya ya kalli ƙofar Bedroom ɗin Mommy kana ya kalleta duk ya koma kalar tausayi kana yace.
“Kin ɓata mana aiki My Khausi baki damu da rayuwata ba ke baki damu da in mutu ko ina rayu ba abinda na faɗa miki ai ba jini kawai ake buƙata ba tunda ba Jinin mutum kawai ba jinin ma na Period ɗin mace magani za'a haɗa min”.
Ta gefen ido ya saci kallonta tare da fesar da numfashi kana yace.
“Amma kika je kikayi min abinda bashi bane, Wallahi kin yimin muguwar fahimta wallahi ba wani abu bane saboda yanda kika ɓata kikasa na dabba shiyasa aka samu akasin da aka samu”.

Anutse Khausar ta ɗago manyan Idanunta dake cike da mamaki ta tsaida su akan sa.
Ganin kallon data ke jifansa dashi yasa ya dake tare da langwaɓar da kai kana ya marairaice murya tare da cewa.
“Wallahi na rantse miki da Allah My Khausi gaskiya nake faɗa miki ki yarda dani”.
Still Ido Khausar ta zuba masa aranta tace Ohhh lalle Uncle Naseer baya tsoron Allah ya aikata abu sannan yazo yana rantsewa da girman Allah saboda baisan girman Allah ba.

Hannun Ramadan ya riƙe acikin nasa tare da sake Matsawa gabanta kana yace.
“Na rantse miki da Allah My Khausi ban aikata abinda kike zargina ba wallahi tallahi ai babu wani abu sama da Allah?”.
Wani irin kallo ta watsa masa tare da Kallonsa kana tace.
“Ni dai awajena da duk wani Muminin duniya babu wani abu sama da Allah.
Amma awajen matsafi yana da abu da yake ganin zai bashi abu sama da Allah yana da dodon tsafi! Kuma dama yawan rantsuwa a mgn ai masiface”.

Zare Ido Uncle Naseer yayi cikin yanayin ruɗewa ya kalleta tare da cewa.
“Innalillahi wa'inna Ilahi rajiu'n Khausar!, Khausar!!, Khausar!!! Nine matsafi?, Hasbunallahu wani'imal wakil, ya Salam Khausar Ashe dama kallon da kike min kenan?. Kai cona da wannan zargi da matar aurena take min”.

Lokaci ɗaya jikin Khausar yayi masifsr sanyi kallon fuskarsa tayi taga duk yanda ya wani susuce aranta tace To Uncle Naseer ko dai dan naji tsoron abin ne amma kayi haƙuri na zarge ka akan abinda baka aikata ba.
Uncle Naseer kuwa jin bata ce komai ba yasa ya sake narkar da murya tare da cewa.
“Sam ban taɓa zaton zaki yimin irin wannan mummunar fahimtar ba, My dear koda ace ina tsafi tasirin soyayyarki ba zaisa inyi tsafi dake ba shin idan nayi tsafi dake dawa zan rayu? kece rayuwata My life is nothing without you Khausi”.

Dai-dai lokacin Mommy ta fito daga Bedroom.Jin motsin fitowarta yasa Uncle Naseer ya juya tare da dai-dai-ta nutsuwarsa kana yace.
“Mommy ya mai jiki ashe abinda yafaru Allah ya sawwaƙa”.
Ba yabo ba fallasa Mommy tace.
“Ameen mun gode”.
Kana ta nufi kichen tare da cewa.
“Khausar zo muje mu ƙara sa aiki”.
Ahankali Khausar ta kalleta tare da cewa.
“Toh”.
Mommy kana ta miƙe idanu ya zuba mata har ta ɓacewa Kallonsa.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da miƙewa ya fita.

Acan ɓangaren Moddibo kuwa Anutse suka fito daga masallaci bayan sun idar da Sallar Isha'i suka nufi gida suna shiga coumpund ɗin M Jameel ya tsaya.
Anutse Moddibo ya juya ya kallesa tare da cewa.
“Ya dai J”.
Lumshe idanu M Jameel Yayi kana cikin sanyin Murya yace.
“A.J muje wajen Ummi mana nayi missing ɗin ta”.
Kallonsa Moddibo yayi kana yace.
“Kai J ina yau da safe ma kafin muje makaranta sai da muka biya?”.
Kai M Jameel ya gyaɗa kana yace.
“A.J Ina son ganinta ne wallahi A.J inajin zanyin Aure kwanan nan”.
Cike da Mamaki Moddibo ya juya ya kallesa kana yace.
“Aure J?”.
Kai M Jameel ya gyaɗa kana yace.
“Eh zanyi Aure”.

Jinjina kai Moddibo yayi kana yace.
“Toh babban magana J wannan magana ce mai girma ai mushiga daga ciki muyi ta”.
Girgiza kai M Jameel Yayi kana yace.
“A'a mushiga mota dai muje muyi ta agidan Ummi”.
Wara Ido Moddibo yayi tare da saurin kallon M Jameel kana yace.
“J baka da kunya agaban Ummi?”.
Murmushi M Jameel Yayi tare da faɗin.
“A.J ni kake cewa bani da kunya ba gwara niba cewa nayi inason Aure, kaifa jikinka ne ya nuna kana son Aure na riga dana fadawa Innayi na faɗa mata komai na kuma zaɓa maka matar da zaka aura ma”.
Cike da mamaki Moddibo ya juya ya kallesa tare da sakar masa da murmushi kana ya shafa sajensa tare da cewa.
“Iyeee sannu Babana”.
Dariya M Jameel Yayi kana yace.
“Ayaaa kana wasa ne?, Wallahi da gaske nayi maka zaɓin mata kuma na faɗawa Innayi sannan ta aminta da hakan kana na shaida mata cewa A.J ɗina yana ɓuƙatar Aure”.

Juyawa Moddibo yayi ya kallesa tare da Matsawa kusa dashi kana ya ɗan mari fuskarsa.
M Jameel kuwa dariya ya fashe dashi wanda ya bayyanar da Fararen haƙoransa kana ya shiga tsinkar fulawar dake wajen yana sunsunawa tare da watsa su sama ga hasken farin wata da da gloves ɗin ya haska wajen.
Moddibo kuwa idanu ya zubawa M Jameel yana sakin murmushi akai-akai wani irin amintaccen kyau M Jameel ya masa fuskarsa kuwa sheƙi da ƙyalli takeyi more especially gishinsa, lumshe idanu Modibbo yayi kana Aransa yace.
“Masha Allah J kayi kyau sosai baka taɓa yin kyau irin na yau ba”.
M Jameel kuwa still dariyar ya cigaba dayi yana mai buɗe hannayensa tare da cewa.
“Allah ko A.J nayi kyau, kace inje amaryata ta ganni”.
Ahankali Moddibo ya sauke Ajiyar zuciya tare da cewa.
“Au ashe mgnar ta fito fili.”
Cikin sakin yalwataccen murmushin da yasa kyawawan haƙoransa bayyana ya gyaɗa mishi kai.
Shi kuwa Modibbo a hankali yace.
“Sosai ma kuwa J kayi kyau, fara'a nayi maka kyau idan kana dariya kana kyau sosai”.
Ahankali M Jameel ya ɗago ya kallesa still Yana cigaba da dariyar yace.
“Ai kaima in zaka yi fara'a haka yana maka kyau A.J”.
Girgiza kai Moddibo yayi har zuwa lokacin da murmushi afuskarsa yace.
“Bazan iya dariya yanda kake yi haka ba J”.
Wara Ido M Jameel Yayi kana cikin dariyar yace.
“Zaka iya A.J”.
Harɗe hannunsa yayi a ƙirjinsa tare da ɗan jingina da jikin mota, kana ya zubawa M Jameel ɗin idanu yana kallon yadda yaketa dariya har maƙolloton wuyanshi yana ɗan haurawa sama kana ya yi ƙasa, sannan haƙoransa nata sheƙi.
Innayi ce ta fito daga sashen ta tare da kallon M Jameel kana tace.
“A'a Jamilu yau mai ya maka daɗi haka?”.
Cikin dariya sosai ya kalli Moddibo kana ya nuna masa saitin Dick ɗin sa da ido.
Da sauri Moddibo ya sunkuyar da kansa tare da kallon inda M Jameel ya nuna da sauri ya lumshe Idanunsa ganin yanda Dick ɗinsa ke miƙe tun ranan da abin ya faru tsakanin sa da Khausar har yau Dick ɗin sa bai sake kwanciya ba koda na second ɗaya sam yaƙi kwanciya ya koma Normal yanda yake cikin dabara ya sanya ƙafarsa ɗaya agaba ɗaya abaya ya matse cinyarsa kana ya cije lips ɗin sa.

Wani sabon dariya M Jameel ya fashe dashi tare da riƙe cikinsa kana ya kalli Innayi tare da cewa.
“Wayyo Allah cikina hahahaha khhykhy Innayi wai dan nace masa na zaɓa masa mata shine yake cewa, nine Babansa kuma na faɗa masa akan na faɗa miki cewa wallahi Aure yakeso ya girma yanzu shine yake wata magana Innayi ki faɗa masa bana zaɓa masa mata ba?”.

Murmushi Innayi tayi kana tace.
“Sosai ma”.
Moddibo kuwa sajensa ya shafa tare da kallon su kana yace.
“Iyeee kune ma masu tsara min rayuwata toni nace muku ina bukatar aure ne?”.
Still cikin ƙyelƙyala dariya sosai M Jameel yace.
“Ai bai sai kafaɗa da bakin ka ba A.J dama ai body language ɗabi'ar kace to ganganar jikinka ta faɗa min kana son Aure”.
Moddibo kuwa cikin sauri ya juya tare da nufar mota jin M Jameel na Shirin tona masa asiri batare daya juya ba yace.
Toh kazo mu tafi Innayi bari muje gidan Ummi”.
Kai Innayi ta gyaɗa da murmushi afuskarta tace.
“Toh Allah ya tsare”.
Bayansa M Jameel yabi tare da buɗe motar yashiga har suka isa gidan da zaran M Jameel ya Kalli Moddibo zaiyi dariya shi kuwa Moddibo sai ya sakar masa da murmushi.
Suna isa Moddibo yayi Parking suka fita akan baranda suka hango Ummi hannunta riƙe da kayan shanya da alama akan igiya ta ɗebosu, ƙara sawa Moddibo yayi kana yace.
“Ummi kawo in karɓa miki”.
Miƙa masa yayi.
Cike da so M Jameel yace.
“Umminaaa”.
Kallonsa Ummi tayi tare da ƙara sa shiga falon ya suka biyo bayan ta atare.

Akan capet Ummi ta zauna tare da jingina bayanta da jikin kushin kana ta miƙe ƙafafunta ahankali Moddibo ya zauna daga gefenta tare da ajiye kayan wankin ganin kayanta ne yasa ya fara ninkewa.
M Jameel kuwa ahankali ya kwanta tare da ɗaura kansa akan cinyar Ummi kana ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya kana ya lumshe Idanunsa tare da cewa.
“Ummina kenan”.

Ahankali Ummi ta juya ta kalli Moddibo kana ta mayar da kallonta kan M Jameel sai kuma ta ɗaga kanta ta kalli haɗeɗɗen agogon dake manne abango kana ta sauƙe Idanunta ƙasa tare da cewa.
“Ayana yin garin nan da yake ga alamun yau akwai hadari sannan baku zo da wuri ba dubi time fa har kusan 8:30 kodai zamu kwana ne?”.

Murmushi M Jameel Yayi tare da ɗago kai ya kalleta kana ya langwaɓar da kai tare da cewa.
“Ummi dana fi kowa farin ciki ace yau gani gaki muna kwana gida ɗaya”.
Juyawa yayi ya kalli Moddibo kana yace.
“Shiyasa ma nake faɗawa A.J nifa Aure zanyi”.

Cikin sauri Ummi ta juya ta kallesa kana cike da Mamaki wannan shine karo na biyu da yake faɗa mata Kalmar

1 Comments On SAKAYYAH
avatar
fatima-8-5-3

6 months ago

Reply

Allah ya qara basira

Please Login or Register in order to submit comment