Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE



You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da yake mallakarku, kuma mafi ɗaukakarsu, ga darajojinku, kuma mafi al'khairi gareku daga ciyar da zinariya da azurfa, kuma mafi al'khairi gareku daku haɗu da abokan gabanku ku riƙe dukkan wuyoyinsu kuna dukan wuyoyin suba?)

Duba Sahihul Bukhari, tare da sharhinsa Fathul Bari (11/208) Muslim ya ruwaito da lafazin:
Misalin gidan da ake ambaton Allah a cikinsa da wanda ba'a ambaton Allah a cikinsa kamar misalin rayayya ne da matacce, (1/539)
Sai Sahabbai Sukace ka bamu labari.
Sai yace musu.
(Ambaton Allah madaukaki sarki)
Kuma yace:
Allah madaukaki yana cewa:
(Ni ina tare da zaton bawana dani,
Kuma ina tare dashi idan ya ambaceni, cikin ransa, zan ambaceshi a cikin raina,
Idan kuma ya ambaceni a cikin jama'a zan ambaceshi a cikin jama'ar da ta fisu al'khairi, in ya kusanceni taƙi ɗaya, zan kusancesa kamu guda, in ya kusanceni kamu guda, zan kusancesa tsawon gaɓa guda, in yazo min yana tafiya zan zo masa ina gaggawa)”.
Sai kuma ya fesar da sassayan numfashi a hankali tare dasa tafin hannunsa ya shafa tattausan sajensa, yana mai lumshe idanunsa alamun cikekkiyar nitsuwarsa buɗe idanun yayi a hankali tare da cewa.
Tirmizi (5/459). da Ibn Majah, (2/1245). duba Sahih Ibn Majah (2/316). da kuma Sahihul Tirmizi (3/139). Bukhari (8/171). Da Muslim (4/2061) lafazin riwayar na Bukhari ne.
Cikin nitsuwa ya kuma juyowa ya fuskacesu, murya cike da kamala, da tashin lafazi yace....!



*WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*

_Ina kuke Ma'aurata masu sha'awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan kaɗen gida Shararriya kuma ƙasaitacciya data saba kawo muku nau'ikan sirrin sahihan magungunan ma'aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma na dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki...Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba'a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al'khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi Gumbar Ukku al'khairi, Dukansu garukan da gumbunan akan dubu uku uku ne sai gumbar Riɗi da uku khairi su dubu biyar biyar ne ! Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace ta koma tamkar budurwa 7k, kana masin Daɗi har Maɗigan mai masifar kyau da kwaranyo da ni'ina 5k
Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni'ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa 8k, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni'imantaccen damshi duka a dubu uku-uku ne ƙananan robobinfa, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, kana akwai maganin sanyi sadidan, set dinsa dubu goma in kuma komai rabi-razi zan sa miki 5k ne butar sirri da dai sauransu...Se kuma fannin ƙamshi kasance da Shu'umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba...._ _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu'uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_
_Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)...Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu'uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa 'yar sha bakwai duba littafin (Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma'aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba'a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma'aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 09097853276 muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah 'yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci ga kuma account no 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA, kina iya tura kuɗinki kafin ma ke min mgn duk abinda na irga akwaisu Available...._



🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida,




By
*GARKUWAR MARUBUTA*
[19/07, 7:44 PM] Halimatu A/rahman Sadeeya: 📝🍇✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇

*SAKAYYAH*
Page 2

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*FREE PAGE*

*LITTAFIN SAKAYYAH NA KUDINE, WANNAN FREE PAGE NE, ƳAR UWA KI BIYA KI KARANTA CIKIB AMINCI BA HAƘƘIN WANI GABA GAREKI 1k ne kacal kuɗin littafin duk da yawa shi. 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, ta nan zaku biya, sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. In kuma baki da account ko matsalar Network ZAKI IYA SAYAN KATIN MTN sai ki copy number's ɗin katin ki turo min ta WHATSAPP. 09097853276. Kada ki kirani in kin san ba kayan Ɗa'a kike soba. In dai littafine kiyi min mgn a whatsapp ɗin.*

*WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*

_Ina kuke Ma'aurata masu sha'awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun da zuƙatan mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida, kai har ma da tan kaɗen gida Shararru kuma ƙasaitattun magungunan matan dans saba kawo muku nau'ikan sirrin sahihan magungunan ma'aurata daga hannun. *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Ma'aurats ayau ma na dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki, ko ƙanwarki, ko ƴarki, ko a miniyarli, damake kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki...Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Dukansu ƙananan robobin akan dubu uku uku ne kacal Gumbar da ba'a baiwa mai kishiya, koriyar gumba, gumbar madara, Gumbar kolli mai kellin al'khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, dukansu a kan dubu uku uku ne ƙananan robobin, sai ta kwalli da ridi da Uku al'khairi da 3 in 1 su dubu biyar biyar ne. Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace, ta dawo da sabon budurci shi ƴar mitsilar robar 7k ne kana ga masin Daɗi har Maɗigan 5k ne kacal Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni'ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa, 8k ne Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni'imantaccen damshi, su duka dubu uku uku ne, haɗin Cida kaza, kala biyu ne akwai na 18k shi yanada su tsumi da kwai da rubutu, sai kuma ɗaya haɗin shi 13k ne Ciccibi Abodi, shi 19k ne Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, duk 3k ne kana akwai maganin sanyi sadidan, wanda bani da haufi a kansu set ɗin 10k ne, rabinshi kuma 5k. Ko mai ciki zata shashi baida matsala, infection ko na cikin mahaifane yana magninsa da uzin Allah. Sai su butar sirri, audugar babbar mace, da dai sauransu...
Sai kuma fannin ƙamshi kasance da Shu'umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba...._ _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu'uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_
_Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)...Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu'uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa 'yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma'aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba'a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma'aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 09097853276. muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah 'yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci idan kuna ga account no da zaku tura kuɗinku ta ciki masu son kayan Ɗa'an 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276...._



🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida,


Cikin fesa sassayyan numfashi, Modibbo ya ci gaba da faɗin.
“Kuji falalar Allahu rabbil samawati garemu, ubangiji yana sonmu yana tausayin mu, yana kuma jinkanmu."
Ya dire mgnar yana ɗan sauƙe wani numfashi dan Allah ya sani ya fara jin bakinshi ya gaji da mgna. Cikin tattausan muryarsa yaci gaba da cewa.
Daga Abdullahi ibn Busr, Allah ya yarda dashi, yace:
(Ya ma'akin Allah! Shari'o'in Musulunci sunyi yawa a gareni, saboda haka ka nuna mini wani abu da zanyi riƙon da shi.
Sai Manzon Allah (S.A.W) yace masa.
(Kar harshenka ya gushe yana ɗanye daga ambaton Allah.
Kuma mai tsira da amincin Allah yace:
(Wanda ya karanta harafi ɗaya daga littafin Allah yana da ladan kekkyawan aiki ɗaya, shi kuma kekkyawan aiki ɗaya yana da ladan misalin goma.
Ba ina nufin Alif lam Mim harafi bane,
A'a. Alif harafi ne, Lam harafi ne, kana shima Mim harafi ne.”.

Wani irin mayataccen kallo Samira ke bin lips ɗin Moddibo dashi, tana mai kallon dukkan yadda yake motsasu, da yadda tattausan sajensa ke zuba ƙyalli ƙawarta Ikilima Ibrahim ce ta ɗan taɓata da kafa alamun wannan wanne irin kallo ne.
Yayinda gefen damansu kuwa, wata madaidaciyar macece, Hadiza Muhammad Yahaya, wacce take cikin sabbin dalibai.
Kallon da Samira Sani keyiwa Moddibo ne ke bata mamaki.
Shi kuwa Moddibo a hankali yaci gaba da cewa.
Kuma daga Ukbatu Ibn Amir Allah ya yarda dashi yace:
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Ya fito alhalin muna cikin rumfa sai yace:
(Wannene daga cikinku zai so ya fita kullum da safe zuwa ƙoramar Buɗhan ko Aƙiƙ ya dawo da taguwa biyu masu manyan tozuna ba tare da yayi wani laifi ba ko yanke zumunta ba?
Mukace masa muna son haka.
Yace:
(Ɗayanku yaje Masallaci ya nemi sani, ko ko ya karanta ayoyi biyu daga cikin littafin Allah, mabuwayi mai ɗaukana, yafi masa taguwa uku ayoyi huɗu sun fi masa taguwa huɗu da kwatankwacin adadinsu na raƙuma.)
Kunga ashe muna ɓarar da damarmakinmu riƙe da waya ba tare da mun samu mun ribaci ilimin da iyayenmu da malanmu suka bamu ba.
Kuma mai tsira da Amincin Allah yace:
(Wanda ya zauna a wani waje, bai ambaci Allah a wajenba, wannan zai zamanto masa abin bibiya a wajen Allah, wanda ya kwanta a makwanci bai ambaci Allah a wajenba shima zai zamanto masa abin bibiya a wajen ALLAH.
Kuma mai tsira da amincin Allah yace:
(Babu wasu mutane da zasu zauna a majalisi da basu ambaci Allah a cikinsa ba, kuma basu yi salati ga annabinsu ba, face ya zamo musu abin bibiya, in Allah yaso yayi musu azaba, in yaso kuma sai ya gafarta musu.”
Jujjuya idanunsa yayi fuskarsa cike da shauƙin son Mahaikin Allah Muhammadu Rasulullah, da sahabbansa,
Wani irin sassayan numfashi ya fesar tare da lumshe idanunsa, wanda yakan shiga wannan yanayi a duk lokacin da yakeyiwa ɗalibansa nuni da al'khairan dake cikin ammaton Allah da bin sunnar manzonmu abinkoyinmu abinsonmu da sahabbansa masu daraja.
Ita kuwa Khausar ƙasa tai da idanunta.
Sai kuma ta ɗan ɗago ta kalleshi jin tattausar muryarsa yaci gaba da cewa.

“Kuma mai tsira da amincin Allah yace:
Babu wasu mutane da zasu tashi daga wani majalisi da basu ambaci Allah a cikinsa ba, face sun zama kamar sun tashi daga kan *mushen jaki ne* kuma zai zamanto musu abin dana sani)”....
Ya ƙare mgnar da haɗe kan yatsunsa duka, kana sai ya buɗasu a tare da ware tafin hannunsa kamar ya sake abu,
alamun ya dasa babbab ɗamba, ya gama da wannan yankin.

Gaba ɗaya hankalinsu tunaninsu duk yana kansa, domin suna matuƙar jin dadin yadda wasu lokutan idan ya shiga aji yake tunasar dasu mahimman abubuwan da suka cancanci musulmi ya lizamcesu.
Yayinda wasu kuwa da sam baya shiga ajujuwansu cike da son salon sa suke sauraronsa, kasan cewar makarantar nada yalwar malamai kuma shi aiyuka sun mai yawa shisa ba dukkan class da suke dashi yake shigaba.

Shi kuwa Moddibo cikin alamun gajiya da yawan motsa lips nasa da yayi yaci gaba da cewa a gaggauce.
“Mu farka mu ribaci wannan shekarar dukanta kada muce dan wannan wata na Ramadan daya shuɗe, zamu bar wasu ayyukan ibada, mu jure mu zamo dasu ɗabi'armu a kullum domin shi ubangiji ka gafartawa bayinsa, a duk sanda yaso ya ainta wasu daga azaba zuwa rahmarsa madaumiya, mu wasar da wayoyin nan mu ruggumi Alqur'ani mai girma da tasbihai ya zama dai ita wayar nan sai time to time zamu riƙe ya ke mai karatu dake nake."
Ya faɗi hakan yana nuna gefensu Samira dake buɗe da littafi a gabansu.
Sai kuma ya ɗan gyara saƙale Lapel Microphone din a wuyar jallabiyar jikinsa dan yaji muryarsa tana ƙasa sosai alum yadan zame kaɗan, da ɗan sauri yace.

“Zaku iya duba Muslim (1/554) Abu Dawud (4/264) da waninsa duba Sahihul Jam'i, (5/342). Tirmizi duba Sahihul Tirmizi (3/140) Abu Dawud (4/264) da Ahmad (2/389) duba Sahihul Jami (5/176) Allah shine mafi sani... Abinda nace dai-dai Allah ya haɗamu a mizanin ladan abinda nai kuskure Allah ya gafartamin.”

Ya rufe mgnar da addu'a tare da juyawa ya fita.
Sukuwa gaba ɗaya numfashi suka sassauƙe, yana fitowa Malam Jamil na isowa wurin, dan shi zai shiga ya shaida musu kwanakin da aka ƙara.

Kai Modibbo ya kauda gefe, jin Aminin nashi na cewa.
“Fattanah maza yi gudu ki shiga aji kada in rigagi, shiga, dan in na rigaki nima yau gadin aji zansa kiyi mana”.
Da sauri Khausar din ta juyo tare da kallon shi cikin alamun yanai musu barkwanci tace.
“Malam ko ta window ma zan shiga”.
Murmushin yayi tare da cewa.
“Har yanzu baki girmi shiga ta window ba FATTANAH”.
Da sauri tace.
“Toh ai banyi jikiba, ka gani”.
Kawai sai ta kama jikin window alamun zata zauna ta wajen sai ta juya ta ciki.
Cikin yamutsa fuska Moddibo yace.
“Ke bar nan,”.
Ai da sauri ta diro tare, da nufar ƙofa, tana tura baki.
Shi kuwa Malam Jamil cikin tsananin son yarinyar sabida ƙwazonta da jan da kwanyarta keyi kana da ƙawancenta da ƙanwarsa Asma'u Ahmad ya bita da ido.
Rungume Moddibo yayi tare da yin mgn murya can ƙasa.
“Tuba mukeyi Moddibo ai mana tsawan a hankali ka mance baka cire Lapel Microphone ɗinba, har nima tsawar ta razanani”.
Wani irin nannauyan numfashin Moddibo ya sauƙe tare lumshe idanunsa.
Shi kuwa M Jamil murmushin yayi kana kuma ya sake shi yace.
“Lokaci na tafiya sai na fito na sallami maza kam”.
Kai Moddibo ya gyaɗa tare da sauƙa ƙasa.

Goma dai-dai aka tashi islamiyan gaba ɗaya duk ɗaliban suka koma gida bayan M Jamil ya musu bayanin dalilin ƙarin hutun, wanda kuma suma sunga hakan.

Ƙarfe ɗaya dai-dai suka tashi daga taron tattaunawa da malaman nasu baki ɗaya.

Bayan sunyi sallan azahar ne, kana duk suka tafi, ma'aikata sukaci gaba da aikinsu.

A gidansu Khausar kuwa.

Khausar ce kwance bisa 3 str daga ita sai yar doguwar rigar material mai taushi a jikinta, Pink collor, sai hular sanyi data sa a kanta, yayinda himilin gashinta yayi tub-tub a ciki.
Da alamun bacci take sonyi.
Cikin sanyi ta buɗe ido ta tare da juyowa ta kalli Momynta dake fitowa daga kitchen ɗinta, hannunta riƙe da plate da yankakkun fruits a ciki masu sanyi, gefen ta ta zauna bisa 1 str ta ɗaura plate ɗin kan cinyarta tare kallon Khausar ɗin data miƙa mata hannu alamun ta bata.
“Tashi kije ki ɗebo Uniform ɗin ku, nasan yanzu ya bushe kizo ki goge muku kafin a kira magriba”.
Numfashi mai ɗan sanyi Khausar ɗin ta fesar tare da miƙewa zaune, ita kuwa Momy tafin sawun ɗiyar Tata take kallo cike da ganin kamannin sawunta dana ahlinta.
Hannu tasa ta ɗauki inabi guda uku. Kana ta miƙe tsaye tare da juyawa ta fita.
Ita kuwa Momy da idanu ta rakata.

Tana fita a barandar ta tsaya tare da ɗan sa hannunta na dama ta riƙe ƙugunta.
Amina ce ta fito daga side din Gimbiya Bunayya, mahaifiyarsu kenan, uwar gidan Lamido,
Wacce daga itana sai Maman su Khausar wacce itace amaryarsa.

Wani irin kallo Amina tayiwa Khausar tare da cewa.
“Hamshaƙiya, cin abu a tsaye ba koyarwar musulunci bane”.
Fuska Khausar ɗin ta ɗan yamutsa tare da cewa.
“Ngd”. Sai kuma ta miƙawa Aminu ƙanin Amina wanda yake gefenta.
Da sauri Amina ta kwaɓe hannun yaron da bazai gaza shekara goma sha ɗaya ba tare da cewa.
“Makwaɗaicin baza, in zakaci akwai a fridge kaje a baka”.
Ido Khausar ɗin ta zuba mata, sai kuma ta sauƙe numfashi dan batayi mmkin hakanba, cikin alamun kasalan da baccin da takeji ya sakar mata, ta nufi wurin shanyan nasu, a hankali take tafiya, dan ganin shanyan nasu yana can har bayan Part ɗin Hajia Bunayya Umma.
“Wannan daga gani ma aikin Ramadan ne, shine zai zo yayi mana shanya har nan, zaice waɗan can igiyoyin tsawonsa bazai kaiba”.
Ta ƙare mgnar tana nufar can.
A hankali ta fara janye shanyan, har ta isa dai-dai window Hajia Bunayya, cikin mamaki ta ɗan tsaya jin yadda Umman ke mgn da faɗa-faɗa.
“Kada in damufa kake cewa.
Kasan kuwa irin tashin hankali da nake ciki duk sanda na buɗi idanuna na kalli Haiydar a matsayin ɗan Lamido Yariman Gembila kuwa, ko ka mance shine ɗan sa na miji babba, shin baka ganin iyakata da mulki sai dai gani sai hange tunda shine ɗa babba akan Aminu na.
Kai bakaga yadda komai zai juye min ba a gaba, ina gani sarauta zata koma ɗakin Aysha ƴaƴanta ne zasu mulki masarautarmun”.
Sai kuma tayi shiru alamun tana sauraron abin da ake cewa a ɗaya sashin.

Ita kuwa Khausar cike da tsoron halin irin na Umma, gashi dai abinda taji, amman koda zata kwana gayawa mahaifiyarsu bazata taɓa yardaba, domin Umma bata taɓa nuna kishinta a kanta, shiyasa ta ɗauki dukkan yarda ta bata.

Cikin tsananin tsoro Khausar ɗin ta zaro ido ta tare dasa tafin hannunta ta dafe ƙahon zuciyarta, jin Hajia Bunayya na cewa.
“Wallahi tallahi billahil azeem zanyi komai dan ganin bayan Aysha da yaranta, zanyi duk abinda ya kama domin in kauda Haiydar a matsayin yarima mai jiran gado, dan wlh Allah zan iya kasheshi kowama ya huta!...”.
Cikin tsananin kaɗuwa Khausar ta juya da sassarfa ta koma sade ɗin Maminta, tana isa kawai sai ta watsar da kayan bisa kujera.

Da sauri ta kamo hannun mahaifiyar tata tare da cewa.
“Momy! Momy dan Allah ki biyoni zo kiji wani abu”.
Ta ƙare mgnar a matuƙar kiɗime, wanda hakan yasa dole Hajia Aysha ta bita a baya.

Ita kuwa da sauri take jenta, har zuwa bayan window Hajia Bunayya.
Cirko-cirko suka tsaya,
Ita kam Khausar cike da firfito da ido waje take sauraron abinda Hajia Bunayya ke faɗi.

Momy kuwa wani irin...!


A hankali M Jamil yayi parking a bakin gate ɗin gidansu Moddibo juyowa yayi ya kalli Moddibo dake gefensa yana lallatsa system nasa.
“Toh wazai fita ya buɗe mana gate ne kam?”.
Ba tare da ya ɗago ya kalleshiba ya ɗaga kafaɗarsa ɗaya tare buɗe tafin hannunsa alamun
Oho.
Kai M Jamil ya jujjuya tare da cewa,
“To bari ni buɗe”.
Kai ya kuma gyaɗa masa alamun.
“Toh”.
Murmushin M Jamil yayi tare da fita ya buɗe gate ɗin, kana ya dawo yaja motar suka shiga ciki.

Parking yayi kana suka fito suka nufi cikin gidan,

Kai tsaye sashin Innayin suka wuce.

Wani irin yalwataccen murmushin M Jamil yayi tare dayin saurin ya haura kan barandar zama yayi daɓas bisa tattausan carpert ɗin dake shimfiɗe a barandar.
Innayi na kwance yayinda Ummin Jamil kuwa ke gefenta tana ɓare mata banana.
Itama yalwataccen murmushin tayi tare da miƙawa Moddibo ayaban data ɓaren.
Amsa yayi tare da juyowa ya ɗan kalli M Jamil da ya zame ya kwanta bisa carpet ɗin tare da ɗaura kansa bisa cinyarta, cike da so, ƙauna, shaƙuwa, tausayawa, yace.
“Ummina kin san irin farin cikin da nakeji a raina kuwa in na ganki?”.
Murmushin kawai tayi dan ita bazata iya cewa komaiba a gaban Innayi sabida Jamil shine ɗan ta na fari, kuma su nan Gembila sashine na cikakkun Fulani.

Kawai dai abinda ta sani a baɗini tasan ta fishi farin ciki.
Shi kuwa Moddibo gefen Innayi dake kwance da alamun har yanzu nitsuwarta bai ida dawowa jikintaba, hannunta ya riƙe tare da kallon M Jamil.
“Kai dan Allah ɗagata kada ka karya mana cinyarta da katon kankan nan”.
Ya ƙare mgnar yana gutsuran banana.
Shi kuwa Jamil da sauri ya tashi zaune jin Umminshi na ture kanshi tana cewa.
“Ai kam gskyarka Moddibo”.
Tashin nasa ne, yasa ta miƙe ta nufi kitchen, trayn data shirya kulolin abincinsu ta kawo musu.
Ta ajiye a tsakiyar su,
Shi kuwa Modibbo a hankali ya kamo hannun Innayin tare da tallabota alamun so yake ya ganta a zaune.
Sai kuma duk suka kalli Innayi data buɗe kwayar idanunta jin yana tallabota.
Zaunar da ita yayi cikin kulawa yace.
“Yanzu me yake miki ciwo?”.
Cikin sanyi tace.
“Nima kaina ban saniba, kawai dai zuciyata ke a tsinke tsoro nakeji Moddibo”.
Da sauri Jamil yace.
“Toh Innayi tsoron me kuma kikeji?”.
Cikin sanyi tace.
“Tsoron kada mutuwa tai mini zuwan ba zata”.
Wani irin masifeffen tsinkewan zuciya ne ya riski Moddibo jin Jamil ya ɗan yi yar dariya tare da cewa.
“Kada ki damu Innayi ki dena jin tsoron mutuwa, domin ita wajibinmu ne ita.
Kuma tsufa ba shine hanyar mutuwaba, ba abin mamaki bane ki rayu ni nan Jamilu in mutu in barki, in bar Ummina da rashina, in bar Aminina Moddibo da rashin Aboki kamata, tabbas a al'amarin ubangiji zan mutu in barku a raye da kuma ƙunar rashina”.
Da sauri Moddibo yace.
“Yah Salam wai kai J meyasa ne wasu lokutan kalamanka a baibaisuke? Dan Allah kasan abinda zakana cewa”.
Murmushin mai sauti Jamil yayi tare da cewa.
“Zanfa mutu kam, dole zan mutu to kai dama a gani kake a haka zamu tabbata ne?”.

Da hannu Moddibo ya nuna masa Umminsa da haka kawai taji wasu irin zafafan hawaye sun zubo mata.
Da sauri Jamil yasa tafin hannunsa ya sharce mata hawayen tare da cewa.
“Kada kiyimin kuka kodama na mutu kada ki damu Ummina kinga aminina Aliyu ko to shi zai zame miki madadina”.
Da sauri tayi mishi dakuwa.
Sai kuma yayi dariya mai sauti tare dace.
“Oh su Ummi ana son ɗan fari wato irin bakya son Jamilunki ya mutun nan ko”. Ya ƙare mgnar cikin tsigar wasa kamar dai kakarsa ce,
Hakanne yasasu yin murmushin ganin zata kai mishi duka ya ɗan zille yana cewa.
“Haka kawai wai kunya wai ni ɗan fari bazakice kina sonaba, toh ni kam ina sonki ina sonki ina sonki Ummina”.
Ƙeyarsa ta ɗan buge, kana ta tura musu plate ɗin dake cike da fruits sai kuma ta mimmiƙa musu fork,

Innayi kuma yar wannan hirar da sukayi yasa ta ɗan sake kaɗan, duk da har yanzu in ta rufe idanunta tana ganin abinda Allah ya nuna mata daren jiya.

Jamil ne ya kalli Innayin tare da cewa.
“Dr Jamila tazo ta dubaki ko, dan da safe kafin mu wuce makaranta na kirata tazo”.
Kai Ummi ta gyaɗa alamun eh tazo.

Frutis ɗin kawai suka ci kana suka miƙe suka nufu part ɗin Moddibo.
Suna shiga falon,
Cikin sanyi Jamil ya zauna bisa kujera tare

1 Comments On SAKAYYAH
avatar
fatima-8-5-3

1 month ago

Reply

Allah ya qara basira

Please Login or Register in order to submit comment