Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hannunta ya sage aranta tace.
“Insha Allah Ina komawa gida zan nemi ɗankwali mai shara-shara mara nauyi wanda kodan irin rana ta yau ta faru zaimin sauƙi.
Cike da gajiya ta miƙe ta riƙe ƙugunta da hannu ɗaya ta lumshe idanunta sosai ta gaji.

Shi kuwa Moddibo daga can sama acikin ajinsu Khausar yake kallonta tana kaɗe-kaɗen ganin ta tsaye ta riƙe ƙugu gaban ƙirjinta duk ya jiƙe da fuskanta, ganin ta tsayanne yasa ya buɗe glass ɗin window dake saitin ta tare da ziro hannunsa ya ƙyasta yatsunsa da ƙarfi wanda hakab yaja hankalin Khausar da saurin ta ɗaga kanta.
Ganin abinda yayi yasa da sauri ta cigaba da kaɗewa tana mai rintse Idanunta.

Har Moddibo ya gama teaching ɗinsa ya fita Khausar nakan punishment Koda ya saƙƙo ya ganta Harara ya watsa mata kana a kufule yace.
“Ba zaki shiga ajiba yau har sai kin gama abinda nasaki”.
Fuska ta Shagwaɓe tare da langwaɓar da kai tace.
“Ayyah Malam dan Allah kayafemin duk ɗan Adam ajizine!”.
Harara ya watsa mata ya wuce batare daya bata amsa ba,
bayansa tabi da kallo tana tura ƙaramin bakinta, to har wani malami ya sake shiga yayi darasi Khausar bata gama ba sai sha biyu dai-dai lokacin tashin matan Aure sannan Yara da ‘Yan mata suyi suci abinci su koma ajin boko.

Hajiya Ruƙayya ce da Aunty Khadija ne suka fito tare da ƙarasawa kusa da Khausar dai-dai lokacin da Khausar ke faɗin.
“Wayyo hannuna”.
Ta faɗa tana matsa yatsunta dake raɗaɗi.

Dafata Hajiya Ruƙayya tayi kana tace.
“Ayyah sannu Khausar kece bakyaji me kika yiwa Moddibo!?”.
Langwaɓar da kai Khausar tayi tare da marairaice murya tace.
“Allah babu abinda na masa kawai ina tahowa ne mukayi karo dashi har System ɗinsa ya faɗi kuma ma naji malam Jameel yace System ɗin beyi komai ba amma sai da ya sani wannan kaɗe-kaɗen sabida in baici zalina ba baya jin daɗi rayuwarsa ta duniya”.
Ta ida maganar da faɗin.
“Affan zo”,tare da miƙa masa hannu.
Murmushi Aunty Khadija tana mai jujjuya kai.
Ita kuwa Hajia Rukayya
Miƙa mata yaron dake ta faman ƙyalƙyala mata Dariya Aunty Ruƙayya tayi Sai kuma tayi saurin janye hannunta tana cewa.
“Wayyo Aunty Ruƙayya hannu na ya gaji yaukam bazan iya riƙe sa ba”.
Ta ƙare mgnar tana ƙara matsowa kusa da Aunty Ruƙayya kan kumatunsa ta sumbata tana faɗin.
“Affan gaye".
Shi kuwa yaron sai dariya yake ƙyalƙyala mata tare da miƙa mata hannu alamar yana so ta ɗauke sa dan sosai yaron ya saba da ita saboda Aunty Ruƙayya na zumunci da Mommy Khausar sannan Khausar na shiga lokaci zuwa lokaci.

Samira Sani da Abeeda Sule ne suka ƙaraso wajen Kallon Abeeda Sule Samira tayi da faɗin.
“Ai Moddibo shike maganin tantirai marasa mutunci ’ya'yan Fitsararru awannan makarantar yana min dai-dai!”.

Sake hannun Affan Khausar tayi ta juya ta kalli Samira da kyau tace.
“Waye ‘Yar marasa mutuncin?
Akwai ‘Yar marasa mutunci daya wucike ne ‘Yar magulmata Munafuka kawai! Inbanda munafurci da gulma da biye-biyen bokaye Me kuka iya!?”.
Afusace tace.
“Ke Khausar zanci Ubanki fa!".
Wara ido Khausar tayi kana tace.
“Ubana kuma, uhmm saide Kici naki uban domin ni kam nawa Ubana tuni Ubangiji ya daɗe da yimasa sutura sai dai kije kici naki ‘Yar matsiyata?”.
Ta ida mgnar cikin tsiwa,.

Abeeda Sule ne tace.
“Ke akwai ma ƴar matsiyata irinki, kina tsammanin bamu san cewa munsan ke Agwola bace acikin gidan sarki da kike nunawa kamar gidan ku ne?”.

Dariya Khausar tayi kana tace.
“Dan Allah rufe mana baki ‘Yar Alhaji sule baka layya kibari tukunna in Babanki ya fara layya saiki faɗa wa mutane Magana?”.

Zare ido Abeeda tayi tare da hayayya ƙowa tace.
“ ‘Yar iska ni zaki cewa Ubana baya layya”.
Taɓe baki Khausar tayi tare da faɗin.
“Ke rufe min baki ai bani na faɗa ba Inkiyarsa ce hakan, ko ba sunan sa bane? Alhaji Sule baka layya!! ko kuma ni nasa masa ko kuma dan tsoronki sai inki kiransa da sunan da aka sa mishi”.

Hajiya Ruƙayya ce tace.
“Khausar rabu dasu”.
Gyaɗa kai tayi.
Ita kuwa Samira cikin takaici tace.
“ ‘Yar banza kawai agola”.
Dariyar rainin hankalin Khausar tayi sannan tace.
“Eh koma menene inma ni Agolace inada daraja sannan ina da tushe dama ni ban ɓoyewa cewa Agola bace Ni saboda idan kinga sunan su Amina da sunana kin san ba yar gidan bane,
Ni sunana Khausar Usman Abubukar Lelewal sukuwa kinga ba haka sunan su yake ba daga nan ma mutum yasan Ni Agola ce ko dama anɓoye miki ne?”.

Hannunta Hajiya Ruƙayya taja suka bar wajen zuwa gefe tace.
“Khausar kifita har ƙansu kiyi abinda ke gabanki kinga duk yau baki samu karatu ba”.
Kai Khausar ta gyaɗa mata sannan tayi mata Sallama ta tafi.
Asma'u ce ta ƙaraso wajen Idanunta akan Samira da Abeeda dake zagin Khausar cikin yanayin sanyin muryanta tace.
“Khausar kifita sabgar wa'annan yaran dan Allah keda su ba ɗaya bane kada ki ringa biye musu muta nen da ƙwaƙwalensu basa ja, kinga fa yanzu da ya kamata suna SS 3 nefa daƙiƙancinsa kesa kullum basa gaba sunan a jaɓe har muka isosu”.
Yamutse fuska Khausar tayi kana tana matsa yatsun hannunta tace.
“Kinsan Allah Asma'u Indai basu fita sabgata ba zan basu mamaki zan nuna musu Khausar Usman Abubakar Lelewal ba kanwar lasa bace”.

Hannunta Asma'u ta riƙe tace.
“Ni dai dan Allah ki fita sangarsu ai ko kare bai haushi shi kaɗai tukunna wai me kika yiwa Moddibo ya saki Punishment?”.

Rau-rau da ido Khausar tayi sai kuma ta ya mutse fuska tare da jan tsaki kana tace.
“Mutum yana nan kamar wani sabon boss sam fuskarsa babu fara'a yana nan sai baƙin mugunta.
Kuma wallahi Wuta bal-bal ban yafe masa ba, ai bani kaɗai nayi kuskuren ba shima yayi yana tafiya kamar makaho, kuma yaseen saƙo na baki ki faɗa masa ehe”.
Ta ida mgnar cike da tsiwa da murguɗa baki
Asma'u kuwa dariyar dake cinta ta danne kana tace.
“Aikuwa gashi nan abayanki yana ma jinki ba sai na faɗa masa ba”.
Arazane Khausar ta saki ihu tare da rintse Idanunta cikin tsananin tsoro da rawan jiki ta juya tana mai faɗin.
“Dan Allah! Dan Allah!! Dan Allah!!! kayi haƙuri Allah bada kai nake ba kuskuren harshene ni da kainama nakeyi”,
Ta ida maganar tana buɗe Idanunta jin be tanka taba ga mamakinta bata gansa ba.
Kallon Asma'u tayi wacce zuwa lokacin ta saki dariyar ta tace.
“Fattanah sarkin tsiwa dama gwada ki nayi inga da gaske saƙon kika bani”.

Harara Khausar ta zabga wa Asma'u amma batace Komai ba.
Murmushi Asma'u tayi tare da jan hannunta zuwa resting chair dake cikin harabar makarantar suka zauna Asma'u ta fito da kula da ɗauke da pride rice da yaji kayan hadi da namar kaza suka ci.
Bayan sun gama cin wannan Khausar ta buɗe bata kukan.
Peper checking ne guzurin zabbin data dawo dasu.
Sunaci suna ɗan hirarsu dai har suka gama, suka mike tare da zagaya classes din makarantar suna kallon yanda aka tsara makarantar kamar ba shiba.
12:10 suka koma aji.
Bayan komawar su Malam Isa dake ɗaukar su Economist ya shiga ya koyar musu sosai Khausar da Asma'u ke fahimtar karatun 1:15 dai-dai suka fita sallah.

Bayan sun fita Al'wala sukaje wajen da aka tanada dan alwala sukayi gefen maza da ban na mata da ban Amma masallacin guda daya ne saidai anraba daga tsakiya anyi katanga mata zasu shiga ta gefen dama maza tagefen hagu.
Bayan sun idar da Sallah ƙarfe 1:30 suka koma aji wasu Malaman suka sake shiga.
Sosai Malaman suka dage wajen koyar dasu domin anƙara musu Salarie sannan ankawo sabbin Malamai hakan yasa babu period din dake wucewa ba tare da anshiga ba 5:00 dai-dai suka tashi motar su Khausar tazo ta ɗauke su.

Washe gari.
Ma haka suka gudanar da karatunsu kamar na jiya.
Acikin satin karatu suke gadan gadan babu kama ƙafar yaro saboda suna son dai-dai-ta komai na lokacin daya wuce ahutu koda wasa Khausar bata sake yin ganganci wani abu ya haɗa ta da Moddibo ba bare tayi masa laifi da zaran ya shiga ajinsu zata tattara duk kan nutsuwarta akansa tana sauraron abinda yake koyar musu kuma sosai take fahimta yayin da ita kuma Samira Sani zata tsaya aikin Kallonsa aduk sanda ya shiga musu shikuwa Moddibo duk yana lura da yanayin ko wannensu.

Yau Alhamis ya kasance babu makaranta suna hutu.
Khausar ce zaune a falon Mommy ta tana duba Mi'atu Hadith,Mommy dake Bedroom ta ƙwala mata kira Amsawa tayi tare da ajiye Hadith ta fita.
Bakinta ɗauke da Sallama tashiga Bedroom din Kallonta Mommy tayi tace.
“Khausar ɗibi wannan kayan ki kaiwa Hajiya Bunayya kala ɗaya nasiya mana”.
Kallon mamaki Khausar ta yiwa Mommy anma wannan basabon abu bane ko yaushe Mommy na zaune zuciya ɗaya da ita tana kyautata mata, amma ita Hajiya Bunayya ba da zuciya ɗaya take zaune dasu ba.
Gyaran Murya Mommy tayi tace.
“Khausar tunanin me kike?”
Murmushi Khausar tayi tare da ɗiban kayan tace.
“Toh”,Mommy sannan ta fice.

Bakinta ɗauke da Sallama ta shiga falon Hajiya Bunayya kana ta nemi waje ta zauna aɗaya daga cikin kujerun dake falon tace.
“Ummah gashi Mommy na ta siya musu iri daya”.
Washe baki Hajiya Bunayya tayi tare da kallon turamen Zannuwa da tsadaddun less ɗin tace.
“Aaaa lalle kam Khausar Nagode Allah yayiwa ƙanwata al'barka muje inyi mata godiya”.
Kai Khausar ta gyaɗa tare da miƙewa dai-dai lokacin Hajiya Lami mahaifiyar Samira Sani tayi sallama suka shigo atare.
Kallon Khausar Hajiya tayi tace.
“Khausar jeki nayi baƙi kice mata Nagode zan shigo anjima”.

Kai Khausar ta gyaɗa tare da ficewa yayin da Samira ta bita da mugun kallo.
Kallon Hajiya Lami Hajiya Bunayya tayi kana ta mika mata hannu suka tafa Dariyar ƙeta Hajiya Bunayya tayi tace.
“Kalli Sokuwarki wai kaya ta saya mana iri ɗaya”.

Dariya Hajiya Lami ta fashe dashi tare da cewa
“Aaaa Ikon Allah sokuwa ta ƙarshen zamani kuwa wato hadda siya muku anko”.
Tsaki Hajiya Bunayya tayi tace.
“Bar ‘yar banza mai kama da ‘ya‘yan mayu tazo ta liƙewa mijina”.

Hajiya Lami tace.
“Aikam wa'annan mutanen sai Allah aike kika sake kika basu dama, kika bar mijinki ya ƙara aure ni yanzu Baban Samira ya isa yace zai ƙara aure ne, sannan bayan kin bari yayi auren ma kika barta tahaifi santalelen yaro me jikin girma bayan shi hadda ‘yan biyu da kawunansu kamar ‘Ya‘yan ruwa ga shegen gashi kamar ‘ya‘yan Aljanu”.

Ƙwafa Hajiya Bunayya tayi kana tace.
“Ai wallahi nayi sake amma daga ‘yan tagwayen babu ita ba sake haihuwa ina lura da ita kwannan kamar cikine da ita to bazan bari ta haife sa ba zanje wajen boka Kar'uzu azubar dama duk cikin ta uku kafin ’yan biyu ni nake sawa azubar shegiya ai bazan barta ba kenan yanzu ma inada niyya zanje wajenki jibi muje wajen Malami”.

Gyara zama Hajiya Lami tayi tare da faɗin.
“Aini ma abinda ya kawoni kenan Hajiya Bunayya in sanar miki”.
Kallonta Hajiya Bunayya tayi tace.
“Toh Meye faru?”.
Ajiyar zuciya Hajiya Lami ta sauƙe tace.
“Akwai wani Malami ne amakarantar su Samira take sonshi”.
Cikin don jin ƙarshen zancen Hajiya Bunayya tace.
“Toh wani Malami?”.

“Wai shi malam Moddibo tana masifar sonshi shi kuma yana nan kamar Waliyi ko ta kanta bayayi”.

“Ikon Allah”.
Cewar Hajia Bunayya

“Toh fa shine nake son zamu kai sunansa wajen Malami ya jawo mana hankalinsa da tunaninsa”.
Jinjina kai Hajiya Bunayya tayi kana tace.
“Eh hakan ma yayi shine dai-dai, gwara ajashi ya dawo yana binta, nima dama abinda zai kaini kenan harda batun Amina itama wani Malamin su take so”.

Cikin mamaki Hajia Kamu tace.
“Ita kuma wani Malamin take so?”.
Da sauri Hajiya Bunayya tace.
“Eh wani Malami take so wai shi M Jameel shi kuma baki ɗaya hankalinsa nakan wannan ‘yar matsiyatan!”.

Cikin zato ido Hajiya Lami tace.
“Wa kenan?".

“Khausar mana”.

Hajiya Lami kam baki ta saki tare da riƙe haɓa kana ta saki salati tace.
“Ikon Allah Uwarta ta hanaki rawan gaban hantsi, sannan itama Khausar tun yanzu zata hana ‘yarki rawan gaban hantsi, ta hana ta samun abinda take so, to ko lallai kinada aiki ja a gabanki
Yakamata muyi aggawan zuwa mu ɗauki mataki dan bata isa ba amma shi Jameel din ɗan gidan waye!?”.

Murmushi Hajiya Bunayya tayi kana tace.
“Ɗan gidan Alh Bashir Mafindi.
Ko da yake yanzu anfi saninshi da Maidala ne”.
Kai Hajiya Lami ta jinjina tace.
“Kai-kai lallai kice babban kamu ne ina zamu yarda muyi wasa dashi waye bai san Alhaji Bashir Maidala ba”
.
“Ai dai kam ɗan masu kuɗi ina zamu bari muyi wasa da wannan damar tamu.
Ai wlh koda zan tafi tsirara bazan taɓa bari ya auri Khausar ba, sannan Insha Allah zanyi kokarin ganin anja mana hankalinsa yaji ya tsaneta ya riƙa cin Ubanta kamar yanda Moddibo keyi mata amakaranta shine abinda yafi mana a'ala da kwanciyar hankali”.

Acan waje kuwa Khausar ce tsaye aƙarshen Barandar Hajiya Bunayya cikin tarin al'ajabi da mamaki ta jinjina kanta bayan ta gama sauraron abinda suka faɗa.....!



*GARKUWAR* taku ce dai MA'AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike maimaita muku dararen forkon kuruciya*

Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara.

Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida.

Ga masu buƙata ga number' wayata wanda nake whatsApp dashi 09097853276 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu, ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so.
0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki Ka mota, duk ƙasar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nane🤝🏻sayan na gari meda kudi gida.


GARKUWAR MA'AURATA




By
*GARKUWAR MARUBUTA*

[19/07, 7:44 PM] Halimatu A/rahman Sadeeya: 📝🍇✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇

*SAKAYYAH*
_Page10_

_NA_
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*NA DAI FA KUSA GAMA FREE PAGE, SAURA KAƊAN. Yar uwa baki makara ba ki biya ki karanta cikin Aminci, littafin SAKAYYAH 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. Kana in saki a Groups ɗin dana buɗe na littafin SAKAYYAH wanda in dai ba a cikinsa kikeba toh yar uwa na sata kike gani. Amman na yanzu dai Free page ne*


Ita kuwa Khausar Jinjina kanta tayi, yayin da idanunta ya cika da ruwan hawaye aranta tace.
“Ta Allah bata ku ba amma kam yardan da Mommy na tayi miki ya ƙazanta ta gaza gane cewa ke ɗin kara da kiyashi ne ɗaukar rashin sani.
Sai kuma ta juya cikin mutuwar jiki ta juya ta koma falon nasu bakinta ɗauke da Sallama.
Zaune ta samu Mommy afalo Idanunta alumshe yayin da ta jingina bayanta da jikin kujeran.
Ƙara sawa kusa da ita Khausar tayi tare da zama tace.
“Mommy yadai baki shiga kichen ɗin ba?”.

Ahankali Mommy ta ɓude Idanunta dake lumshe kana tace.
“Wallahi Khausar bacci nake ji duk jikina babu ƙarfi!”.
Jinjina Kai Khausar tayi cikin sanyu tace.
“To kiyi baccin Mommy bari nashiga kichen nayi girkin”.
Kai Mommy ta gyaɗa still Idanunta alumshe tace.
“Toh”.
Juyawa Khausar tayi ta shiga kichen ajikin sink din ta jingina asaman laɓɓanta tace.
“Kenan yawan baccin da Mommy na keyi kwanan nan, ciki ne da ita wanda Hajiya Bunayya ke ƙoƙarin zubarwa”.
A hankali ta saki Ajiyar zuciya da faɗin.
“Allah mai iko”.
Sai kuma ta juya ta ɗauki tukunya tasa ruwa ta ɗauraye cikin sannan ta tari ruwa da yawa aciki tarufe Sannan ta juya ta kunna Gas ta ɗaura ruwa,
Jiki a mace ta buɗe drower Na'a na'a ta ɗiba tare da citta, kanamfari, da masoro kaɗan, gyara su tayi kana ta ɗaureyesu sannan ta saka cikin tukunyar.

Doya ta ɗauko manya guda huɗu, ta fara ferewa.
Hummmm taja sassayan numfashi lokacin da taji tea ɗin data ɗaura yanata baza ƙamshi alamun ya dafu, da sauri ta ƙarasa free doyan, kana ta wonkesu fes bayan ta rarraba su.
Hannunta ta ɗauraye bayan ta stabtace wurin da ta feren.
Flacks ta ɗauko guda huɗu cikasu tayi baki ɗaya, kana ta maidasu wurin zamansu.
Wannan tukunyar ta kuma ɗaurayewa kana tasa ruwa ɗan madaidaici.

Doyan ta ƙara sassarewa tayisu yan ma dai-dai-ta dai'dai sawa a baki, kana ta kuma wankewa ta tsanesu, kana ta juyeshi a tukunyar, gishiri ta ɗan tarfa a kai, sannan ta rufe tukunyar tare da ɗan dai-dai-ta wutan.

Drower gefen dama ta ta kuma buɗe wa, wani farin roba ta jawo mai cike da ƙuli-ƙuli irin dogayen nan plate ta ɗauka saida ta cikashi kana ta maida ta rufe.
Sannan ta ɗebi borkono dai-dai misali.
Tasa a turmi kana ta sa kanamfari tare da Maggi star, Noo, Tera, Rayco, da dai sauransu, dakasu tayi , sannan tasa ƙaragon duk ta haɗa su ta dake su luƙui.
Kana ta kwashesa a wasu ƴan robobi masu masifar kyau da yan marafensu guda huɗu.

Fridge ɗin dake gefenta ta bude ta dauko goran ma shanu, ɗan wani tukunyan ƙasa ta ɗauka tare da tsulala manshanun,
Daya gefen ta kunna gas ɗin, kana ta ɗaura, sai kuma ta ɗauki manyan albasa har guda huɗu, gyarasu tayi kana ta yayyankasu.
Tukunyar da doyan ke ciki ta buɗe,
Kai ta jinjina ganin ya kusa dafuwa, da sauri ta watsa rabin albasan da ta yanka ɗin a kai.
Kana ta maida marfin ta rufe, tare da rage wutan.

Ɗan ludayi, tasa cikin man shanun jin ya daina bada sauti alamun ruwan ciki ya ƙare, sake raba albasan biyu tayi ta watsashi cikin man shanun.
Hhummmmmm taja wani dogon numfashi sabida wani irin masifeffen ƙamshi mai tsinka yawun mutun daya buɗe illahirin gidan.
Kashe wutan babbar tukunyar tayi dan ya dafu albasar, ta razanu.

Kana ta ɗauko kulli ta kwashe na sashin Hajia Bunayya tare dana Gimbiya Dadu.
Sai kuma na Abbansu,
Sannan na side dinsu.
Sauƙe man tayi kana ta cire wannan albasan daya fara ƙonewa, sai kuma ta juye wannan sauran, shuyuuuu ya bada sautin soyuwa da zafin man.

ɗaya daga cikin manyan ƙullin naman dake cikin fridge ta ɗauka mai sokoki zalla anyi ta kansu dogo-dogo.
Ɗaurayewa tayi tasa a yar madaidaicin tukunya ta zuba naman,
dama already ta jajjaga ɗanyen citta da tafarnuwa ta buɗe ta zuba aciki sannan ta Marmasa Maggi da time kana ta jajjaga attaruhu da albasa ta zuba tare da diban man shanun data soya ta watsa a ciki da duk sauran spices,Cikin Mintuna kaɗan kichen ɗin ya ɗauki mayataccen ƙamshin girkin dana man shanu daya wadata aciki zazzafan gashin da takeyiwa Abban.

Mommy kuwa ahankali ta miƙe tashiga kichen ɗin Idanunta akan Khausar dake wanke yan kwanunkan data ɓata, cikin alamun bacci tace.
“Ƙamshin girkin ki ne ya tasheni da gaba baccin.
nazo in tayaki gashi kuma naga kamar ma kin gama”.
Murmushi Khausar tayi tana motsa gashin naman mai romon da takeyi wanda tuni yanata ɓararraka kai ta jinjina kana tace.
“Mommy kije ki huta nama gama fa”.
Murmushi Mommy tayi kana tace.
“A'a kada ki damu ai baccin ya sakeni”.
Kai kawai Khausar ta gyaɗa sannan ta cigaba da aikinta tana sauƙe gashin Mommy ta taimaka mata suka juye kulan Abba da kuma na Dadu, saura kuma suka sawa Hajia Bunayya saura kuma suka barwa kansu.
“Yauwa ɗauki na Ummanki ki kai mata”.
cewar Mommy, cikin sauƙe numfashi Khausar ta ɗauka bayan ta sa jera yan robobin man shanun da yajin ƙuli-ƙulin, sai yar kulan gashin naman.
Kana ta nufi sashen bakinta ɗauke da sallama tashiga.
Amina dake zaune riƙe da waya ahannu ta watsa mata kallon tsana batare data amsa sallamar taba tace.
“Agola kin zo kina wani tunƙaho kamar gidan tsohonki ne Masarautar very soon zaki bar gidan nan dan nafi ƙarfin nayi shearing abinda nake so dake”.
Ya mutsa fuska Khausar tayi tare da jan siririn tsaki tace.
“Iska na wahalar dame kayan kara wannan ƴar masarautar kike mgn a kai har wata siyace”.
tana ida maganar ta fice batare data jira jin abinda Amina zata ceba.

Kai tsaye kichen ta nufa tsaye ta samu Mommy tana ɗauraye tukwanen da Khausar tayi amfani dashi kallon ta tayi tace.
“Ki ɗauki kular Gimbiya Dadu ki kai mata”.
Langwaɓar da kai Khausar tayi tace.
“Ayyah Mommy Haiydar ya Kai mana”.
Juyawa Mommy tayi ta kalleta da faɗin.
“Wai Khausar Meyesa idan na aike ki sashen Gimbiya Dadu sai kice in aiki Haiydar bana jin daɗin abinda kike min fa wato kina nuna min cewa ke ba jikarta bace?”.
Girgiza kai Khausar tayi tace.
“Wallahi Mommy Ina tsoron zuwa wajenta bana shiri da ita”.
Kallon Mamaki Mommy tayi mata kafin ta watsa mata harara da faɗin.
“Rufe min baki zakiji tsoronta ita ɗin kurace? wato kinje kakar ki tasa Miki ra'ayi da batun cewa ita Mayya ce da sauransu ko?”.

Girgiza kai Khausar tayi Idanunta cike da ruwan hawaye aranta tace. har yanzu Mommy ba zata gane ba taya zan ganar da ita cewa ni kaina na gamsu da cewa matar nan Mayya ce.
Amma nasan kona faɗa ba zata yarda ba dan yanda take haƙiƙan cewa akan ba Mayya bace ko ‘ya‘yan cikinta basa haƙiƙan cewa akan hakan, ita babu dama ace Gimbiya Dadu Mayya ce bayan ni da kaina naga alamomin hakan kuma ya fito da bakinta ta faɗa min ita Mayyace kawai ya rage amma sam Mommy taƙi yarda idan taji mutum ya fadawa Gimbiya Dadu Mayya aita bala'i da ita se kace Uwarta aka kira Mayya.

Ita kuwa Mommy ganin yanda Khausar ta tsirawa waje ɗaya idanu yasa aɗan fusace tace.
“Khausar ba magana nake Miki ba ko baza kije bane Inje da kaina?!”.
Asanyaye tace.
“Ayyah Mommy kiyi haƙuri zanje”.
Ta Faɗa tare da ɗaukar kulan ta fice tana furta.
”اعذبكلمتلله تممت منشررم حلق“.
Bakinta ɗauke da Sallama tashiga falon akan darduma taga Gimbiya Dadu na sallar maghariba cikin sauri ta ajiye kular.
Ita kuwa Gimbiya jin Muryan Khausar yasa cikin hanzari tayi sallama batare data idar ba ta juya ta zuba mata Na mujiya.
Ita kuwa Khausar cikin sauri ta juya ta fice daga sashen ta nufi sashen su tana sakin Ajiyar zuciya sai kuma ta furta.
“Alhamdulillah”.
Sosai tayi farin cikin tarar da Gimbiya Dadu tana Sallah.
Koda ta shiga Falon nasu bata samu Mommy ba da alama tana ciki tana sallah kai tsaye Bedroom ɗin su ta wuce tare da shiga toilet bayan tayi addu'a.
Anutse tayi alwala tare da fitowa da ƙafar dama.

Darduma mai taushi dake fitar da sanyayyan ƙamshi ta shimfiɗa kana ta sanya dogon hijabinta ta fuskanci alƙibla cikin nutsuwa tare da maida komai zuwa ga mahalicci ta gabatar da sallah bayan ta idar ta ɗaga hannunta biyu sama tare da lumshe Idanunta cikin tsantsar nutsuwa tare da ladabi alokacin neman wani buƙata ga Ubangiji mabuwayi gagara Misali ta ɗaga hannunta biyu tace.
“Ya waduud,Ya zul'arshil Majeed,Ya fa'alil lima yureed As'aluka bi

1 Comments On SAKAYYAH
avatar
fatima-8-5-3

6 months ago

Reply

Allah ya qara basira

Please Login or Register in order to submit comment