Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sansti ya bayyana.

Baki ɗaya cikin motar a wadace yake da wani irin ni'imtaccen sanyayyan ƙamshi mai daɗin shaƙa yakeyi, Ahankali Khausar ta maida kallon kan bayan Moddibo da take fuskanta sanye yake cikin ɗanyen Boyel fari ƙal yasha guga sosai yayin da kansa ke sanye da hula zanna bukar wadataccen sumar ƙeyansa ya kwanto lib-lib gwanin kyau sai sheƙi da ƙyalli yake zubawa.
Ƙeyar tasa ta zubawa ido sai kuma ta gallawa ƙeyar tasa harara tare da murguɗa masa baki.

Tana ɗago Idanunta suka sauƙa akan Idanun Moddibo ta madubin jikin motar yana kallonta cikin mugun sauri tayi ƙasa da kanta zuciyar ta na mai bugawa da ƙarfin tsiya.
Moddibo kuwa Ƙoffa yayi tare da haɗa harshensa da hoƙorinsa ya fitar da wani sauti kana yace.
“Hmmmm!”.
Kallon sa M Jameel da Idanunsa ke lumshe yayi kana cike da kulawa yace.
“Ya dai A.J?”.
Shiru Moddibo ya masa tare da watsa masa Harara!.
Ware Ido M Jameel yayi tare da shafa sajensa kana yace.
“Ya dai kake ta harare-harare acikin mota!”.
Ƙin tanka masa Moddibo yayi ya cigaba da Driving ɗinsa tare da ƙara tsuke fuska.
Khausar kuwa shiru tayi sai kuma ta sake ɗago kanta ahankali ta kalli madubin ganin ya kawar da kansa gefe yasa ta sake liƙawa ƙeyansa harara tamkar idanunta zasu manne bisa ƙeyar tasa, kana ta ɗago hannunta na dama ta ɗan haɗe kan yatsun tare da buɗe su ta watsa masa alamar Jarabebbe! Mayatacce!! Masifeffe!!! Fitinenne!!!! sai kuma ta sake watsa masa Harara tare da kai hannunta ƙeyarsa kamar zata kai masa ronƙwashi.
A kuma dai-dai lokacin ya ɗago ya kalleta ta madubin.
Azabure taja baya tare da jinginar da bayanta da jikin kujeran zuciyarta na bugawa.
Cikin fushi Moddibo ya watsa mata mugun kallo tare da cewa.
“Anh zan karyaki wallahi kakkarya ki zanyi in watsar dake atiti inyi tafiyata, ƴar rashin kunya fitsararriya”.
Ita dai Khausar rumtse Idanunta tayi da masifan ƙarfi tare da sake rungume question peper ta aƙirji gam-gam.
M Jameel kuwa daya ta kure jikinsa waje ɗaya idanunsa alumshe saboda sanyi da ake yayi saurin buɗe idanunsa yayi tare da kallon Moddibo dake Driving tamkar bashi yayi maganar ba cikin tsaresa da Ido yace.
“Ha'a wai mai yake faruwa a motar nan ne kake abubuwa iri-iri daga Harara, Ƙoffa, tsaki, tsuke fuska, yanzu kuma sai cewa zaka kakkarya!,To waima wa zaka karya ne kam?”.

Cikin fushi Moddibo ya juya ya kallesa kana yace.
“Ai duk wanda zan karya ya sani!
Karya yarinyar nan zanyi fitsararriyar banza mara kunya idan kina sake kuskuren kallon min ƙeyata saina gutsitsi-tsiraki na ƙwaƙule miki manyan mayatattun idonun ki masu kama da na yan maye na jefar! A titi ko na samu salama”.
Lokaci ɗaya tsoro ya dirarwa Khausar jin wai zai Kakkarya ta ya ƙwaƙule mata ido cike da tsoro ta kuma ƙara rumtse Idanunta tare da ta kure jikinta ajikin kujera ita kanta batasan dalilin da yasa yake mata haka ba ita dai tasan da zata samu dama itama karyashin zatayi ta kuna tsitstsige gemunshi.
Akuma dai-dai lokacin suka isa ƙofar gidan su M Jameel Moddibo yayi Parking.
Ɓude Murfin motar M Jameel yayi tare da fita duk da ruwan da ake tsugawa bai hana sa saka kansa ta cikin glass ɗin side da Khausar take ba, cikin ƙasa da murya yace.
“Lelewal be careful don't Misbehaving kinga bana nan yaseen kika mishi ba dai-dai a titi zai wurgaki ya tafiyarsa”.
Kai ta gyaɗa masa cike da alamun tsoro sai taji kamar ta fita ta bisa.

Shikuwa M Jameel kallon Moddibo yayi tare da cewa.
“Toh Allah ya tsare Allah ya kaiku lafiya A.J Amana ce, dan amana A.J ka kularmin da ita”.
Daga haka ya juya da gudu ya nufi cikin gida zuwa lokacin duk ya jiƙe saboda yanda ruwan ke sauƙa da ƙarfi.

Acikin motar kuwa lumshe idanu Moddibo yayi ba tare da yaja motar ba.
Khausar kam ƙasa da kanta tayi aranta tace wannan dai akwai bahagon mutum, fisabilillah yana kallon yanda ake tsuga ruwa kamar da bakin ƙwarya amma yaja ya tsaya jifa yanda ruwan ke sauƙa.

*Littafin SAKAYYAH na kuɗine daga wannan na gama Free page, 1k ne kuɗin samun damar karantawa 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, biya ki karanta cikin Aminci*

Sun kai kusan minti biyar ahaka ita batace komai ba, haka zalika shima baice komai ba banda sautin ƙaran ruwa babu abinda ke sauƙa ɗago Idanunsa yayi dai-dai lokacin da itama Khausar ta ɗago Idanunta ta kalli madubin cikin motar,
idanunsu ne suka sarƙafe cikin na juna.
Harara ya watsa mata kana cikin wata razananniyar murya da shi kansa bai san yana da ita ba yace.
“Uban me kike abayan mota koni.
Driver kine harda wani hakimcewar ki abaya a dole kega Sarauniya kin samu Driver!
Kifita idona fa, nifa ba J bane zan karya kifa”.
Cikin sauri ta buɗe bayan motar ta fita aranta tace Gwanda inyi yanda yake so dan yanda yake kiran zai karya nin nan inda yazo da tsautsayi sai yajawa Mommy asarata, gaban motar ta buɗe ta shiga amma duk da haka saida ta ɗan jiƙe sabida ruwan da ya fara ƙarfi, tana zama yaja motar suka tafi.
Akuma dai-dai lokacin ruwan ya sake kecewa da ƙarfin gaske tamkar da bakin ƙwarya ake tsuga ruwan.

Khausar kam lumshe Idanunta tayi aranta tace ya Allah ka kaimu gida lafiya ka rabani da wannan bawa naka lafiya,
domin akwai rata tsakaninsu da gida sosai ahankali ta buɗe Idanunta ta kalli titin da yayi shiru babu hayaniyar sai ƙugin motarsu da kuma yanda tayun ke fesar da Iska da ruwan kan kwalta fuuuu kana har zuwa yanzu garin ɓakiƙƙirin yake duk da kuwa yadda ake sheƙa ruwan alamar har yanzu ruwan bashi da niyyar ɗauke wa.

Suna cikin tafiya akayi wani irin walƙiya mai haske.
Da sauri Khausar ta rumtse idonta tare da furta.
“Bismillahi”.
A lokacin guda kuma ta sake buɗesu da sauri sabida
jin wani irin rugugi da akayi mai bada sautin rududuuu-duuuuhhh kana ga walƙiya daya haska da wani irin sauri Khausar ta rungume jikinta waje ɗaya aranta tace.
_“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n Hasbunallahu wani'imal wakil Subhanal Lazi yusabbihul ra'adu bi handihi wal Mala'ikatu min hiyfatin”._

Cikin tsananin tsoro tayi addu'ar domin arayuwarta babu abinda take masifar tsoro a damuna kamar tsawa da walƙiya sam bata yarda ta haɗa ido da walƙiya da zaran taga za'a yi walƙiya zata rufe Idanunta ta sunkuyar da kanta.
Shi kuwa Moddibo tafiya ya cigaba dayi yayin da titin yayi shiru babu hayaniyar komai sai bishiyoyi dake rangaji ruwa na sauƙa akansu Sanyayyar iska mai cike da Ni'imah na kaɗasu baki ɗaya shaguna dake gefen titin arufe suke baki daya garin babu hayaniya sai jefi-jefi suke hango Mutane.

Suna cikin tafiyar aka sake wani walƙiya mai masifar haske ja, alamun yanzu za'a ƙara kecewa da ruwa.
Atsorace cikin ɗaga sautin murya tace.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n”.
Ta ida addu'ar tare da kife kanta akan gwiwarta yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinta ke rawa A ɗan juya kai Moddibo yayi kalleta, domin shi kansa zuciyarsa ta harba sabida walƙiyar saida ta ɗauke masa ido saboda yanda walƙiyar tazo da haske mai ƙarfin gaske sosai yaji tsoron walƙiyar amma sai yayi addu'a aransa kana yana cigaba da tafiya bai tsaya ba.
Bayan walƙiyar ba daɗewa aka saki wata tsawa mai sautin rututuuuu alokaci ɗaya zuciyarsu ta buga domin ji sukayi tamkar ƙasa zai tsage.
Atake wani matsananci tsoro ya sake lulluɓe Khausar yayin da jikinta yashiga rawa tamkar mazari kanta ta kife acinyarta zuciyarta na cigaba da bugawa da masifan ƙarfi kana har zuwa lokacin kanta na sunkuye akan ƙafafunta tun daga wannan rugugin.
Yayinda gaba ɗaya mazauna garin Gembu Mebila suke cike da taraddadi sabida bisa dukkan alamu yau da tsawa da rugugin ruwan yake sauƙa.

Acikin haka ne aka sake walƙiya mai masifar haske irin walkiyar nan mai zuwa tamkar an watsa dogon bulala koko tafiyar maciji,
Da masifar haske da tarsatsi yazo tamkar an watsa bulala Sharrrrrr sai kuma a take aka saki wata iriyar tsawa mai masifar ƙarfi yabi yo bayansa wanda ke fitar da sautin felelelelelelelen da masifar karaji da gigita dukkan bani adam

Cikin wani irin tsananin tsoro da gigita Khausar ta saki ƙara mai masifar sauti tare da furta. _“Hasbunallahu wani'imal wakil. Subhanal Lazi yusabbihul ra'adu bi hamdihi wal Mala'ikatu min hiyfatihi”._
Atake aka sake sakin wani walƙiyar haɗe da wata iriyar firgitacciyar tsawa mai masifar kara mai razana dan adam dasa hanjin mutum kaɗawa.
Cikin tsananin tsoro da masifar gigita ta dari ta ɗago kanta a kiɗime ta afkawa jikin Moddibo yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinta ke rawa shi kansa Moddibo wani irin tsoro ne ya kamasa saboda hasken walƙiyar saida ya tsaga glass ɗin gaban motarsa tare da bada sautin ƙarararassss!!!.
Wani irin bugawa zuciyarsa keyi da masifar ƙarfe yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinsa ya ɗauki rawa ƙoƙarin taka burki yake amma ya gagara saboda yanda ta takure jikinta ajikinsa ta kanainayeshi, bashida wani kataɓus ɗin motsa wa, sabida yadda ta kife kanta afaffaɗan ƙirjinsa hannunta ɗaya na zagaye da bayansa yayin da ta cusa hannunta na dama akan maransa.

Moddibo kuwa wani irin masifaffen rawa jikinsa ya farayi tamkar mazari yana wani irin tsuma ji yake tamkar ana tsikara masa allurai ne agaba ɗaya ilahirin jikinsa lokaci ɗaya wani irin baƙon yanayi ya ziyarcesa ga fargaban tsawar da har zuwa lokacin bai gama tsayawa ba.
Tsawan na tsayawa wani mai masifar rugugi ya sake sauƙa.
Wani irin masifaffen tsuma jikin Khausar keyi yayin da numfashinta ke fusga saboda tsananin tsoro Allah ya sani tana masifar tsoton tsawa hakan yasa ta sake ƙanƙamesa tamkar zata tsaga jikinsa ta shige ciki.

Shi kuwa Moddibo baki ɗaya jikinsa tsuma ya shiga yi saboda yanda ta kanainayesa kar-kar-kar haka jikinsa ke rawa yayin da baki ɗaya tsikar jikinsa ya miƙe daga tsakiyar kansa har zuwa babban yatsan ƙafarsa yaji wani irin yanayi wanda bai taɓa jiba a iya tsawon rayuwarsa, sai yau kuma yanzu ya jishi.

Wani irin harba zuyarsa da sashi mafi daraja a jikinsa sukayi a tare da wani irin azaban ƙarfi.
Akuma lokacin aka sake sakin tsawa da walƙiya.

Ita kam Khausar cikin tsananin gigita da tsananin tsoro kana da ficewar hayyaci ta sake rungumesu tare da sake tura hannunta ka maransa yayin da yatsun hannunta suka sauƙa akan cibiyar sa.
Tsawar da aka sake yine ya razana illahirin wani abu mai rai dake yankin Gembu,
yayinda hakan take a wurin Modibbo ma wani cikin rashin sanin makaman kamawa ya ya buɗe hannayensa ya rungumeta da azaban karfi tare da taka burkin motar da ƙarfi wani irin sautin ƙuuuuuuu motar tayi tare da cigaba da tafiya sabida tsantsin kwaltan da yayi sabida ruwan sama da kuma tsantsin sabbin tayoyin da ƙyar ya samu motar ta tsaya a tsakiyar titin, sake Rungumeta yayi da masifar ƙarfe kana ya cusa kansa atsakanin kafaɗarta da wuyanta.
Lokacin da aka kuma sakin wani irin rugugin nan da zakaji kamar ƙasa na amsawa.
Atake zuciyarsu ya buga da mugun ƙarfi tare da bada sautin dib-dab-dib-dab-difffh yayin da yake jin wani irin masifaffen abu na tsirgar masa lokaci ɗaya lafiyarsa sa ta shaida mushi kasantuwarsa cikekken Namiji.
Ita kuwa khausar tana jin yatsarta cikin ɗan hudan cibiyarsa amma tsananin tsoron da take ciki yasa ta kasa fahimtar menene sai cusa kanta da ta kumayi a kirjinsa.
Shi kam Moddibo wani irin rungumeta yayi da masifar ƙarfi yana mai sakin wani irin amintaccen nish....!

*Free page sun ƙare daga wannan, ko kin ga littafin a wani wuri na satane, littafin SAKAYYAH na kuɗine 1k ne 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. Sai in saki a Group ɗin da nan kadai zanke posting*


*WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*

_Ina kuke Ma'aurata masu sha'awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan kaɗen gida Shararriya kuma ƙasaitacciya data saba kawo muku nau'ikan sirrin sahihan magungunan ma'aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma ta dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki...Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba'a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al'khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace, ka masin Daɗi har Maɗigan Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni'ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni'imantaccen damshi, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, kana akwai maganin sanyi sadidan, da dai sauransu...Se kuma fannin ƙamshi kasance da Shu'umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba...._ _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu'uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_
_Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)...Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu'uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa 'yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma'aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba'a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma'aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 09097853276 muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah 'yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci...._



🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida,

*By*
*GARKUWAN MARUBUTA*














[24/07, 6:14 AM] Halimatu A/rahman Sadeeya: SAKAYAH

18

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


Spjt. Rungume juna sukayu tamkar zasu shige cikin jikin junansu, yayin da ruwan sama kuwa ke cigaba da sauƙa tamkar da bakin ƙwarya, kana ga walƙiya da tsawa dake cigaba da sauƙa.
Moddibo shi kam baki ɗaya ya burkice ya rasa tunaninsa, na wushin gadi, gaba ɗaya jinshi yake a wata duniya ta da ban,
ga wani matsanancin tsoro daya lulluɓe sa kana ga wani baƙon yanayi da yake ji yana yawo agaba ɗaya ilahirin ajikinsa, wani irin rawa lips ɗin sa keyi tamkar mai jin tsananin sanyi, ga kuma wani irin azabebben buguwan da zuciyarsa keyi da masifaffen ƙarfi yana bada sautin dib-dab-dib-dab.

Haka zalika Khausar dake rungume dashi, itama haka zuciyarta ke bugawa,
sake ƙanƙamesa tayi da ƙarfi tana mai tura kanta afaffaɗan ƙirjinsa da bottle din gaban rigar suka buɗe, hakan ya bawa fuskarta damar mannewa farar afaffaɗan ƙirjinsa dake ƙawace da tattausan gashi baƙi mai sulɓi.
Wani irin fusga numfashinta keyi saboda tsananin tsoro da firgici da tashin hankali, haka yasa idan taja numfashin sai ta ɗauki sekon talatin Kafin ya dawo.
Ko kaɗan Moddibo bai da wani kataɓus sabida yanayin da suka kasance a ciki, sake rungumeta yayi tare da cusa kansa atsakanin wuyanta da kafaɗarta.
Daga can bayansa yake jiyo sautin ƙaran mota tana danna masa ɗiyyyyttt-ɗiyyyytttt, yasan shi akeyiwa hon ɗin, amman sam baya jin zai iya koda kwakwaran motsine.
Shi kuwa mai motar dake bayansa, ganin shiru bai motsa bane, yasa ya ɗan ratsa ta gefensu ya fuce yana dan leƙawa ganin ko lafiya kasancewar. Atsakiyar titin suke ganin babu wani alamun hatsari ko damuwa yasa ya wuce.

Moddibo kuwa da ƙyar ya iya buɗe Idanunsa tare da ɗago kansa still ruwan ake sheƙawa zuwa yanzu harda ƙanƙara yana jin yanda sautin ƙanƙarar ke sauka asaman motarsa fat-fat-fat ko kaɗan baya kallon komai duk da kuwa gashi idanunnasa abuɗe suke, amman ina ganinsa ya ɗauke makanta ta meye gurbin ganinsa, ya zama sam baya gani, kana ji yake jikinsa kamar shanyeyye.
Daƙyar ya iya ɗaga hannunsa tare da dafe kansa da yake jin wani irin jiri na fizgarsa tare da sarawa, da sauri ya sake sunkuyar da kansa akan wuyanta kana ya sake rungumeta da ƙarfi baki ɗaya ya rasa wani irin yanayi yake ciki.

Khausar kam sam batama san wani irin yanayi take ciki ba sam bata cikin hayyacinsa, hakan yasa ta sake rungume Moddibo da ƙarfi,
Jin yadda take liƙewa a jikinsa ne, yasa shima ya saƙe yi mata wani irin amintaccen rugguma tare da fesar da wani irin raunataccen numfashin yana mai shaƙan ƙamshin jikinta.
Itama sake rungumesa tayi cikin mawuyacin hali tana neman numfashi domin numfashinta na ƙoƙarin ɗauke wa gaba daya tsananin tsoro da tashin hankali ya bayyana asaman fuskarta, duk da sanyi garin da kuma yanda ake tsuga ruwa amma goshinta na na tsastsafo da zufa kana jikinta ya ɗauki ɗumi.

Cikin wani irin yanayi mai wuyar fassarawa da ficewar hayyaci Moddibo ya sake rungumeta yana jin ɗumin jikinta kana yana mai furta.
“Hasbullahu wani'imal wakin, Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n La'ilaha Illah anta subhanaka Inni ukuntu Minal Zhalimin, Allahumma Ajirni fii musibati wa'ahlifli khairan minha”,Kana ya cigaba da karo to duk wata addu'a da tazo bakinsa cikin fitar hayyaci, Allah ya sani kuma shine shaidarsa ya rasa yanayin da yake ciki shin mutuwa zaiyi ne, koko kuma sumewa yake shirin yi,
domin jinsa yakeyi tamkar yana tafiya cikin sararin samaniya ne bisa gajumare,
ji yake tamkar fuka-fuki garesa ya kasa tantance shin mafarki yake ko kuma azahirance ne kana yakasa tantance shin a sumen yake ko kuma amace yake, cikin rashin sanin madafa ya cigaba da karanto duk wata addu'a da tazo bakinsa.
Yayin da numfashi Khausar ke cigaba da fusga,
adduo'i ya cigaba dayi cikin ikon Allah Albarkanci Adduo'i da yake da kuma zuciyar namiji dake da dakiya yasa yafara dawowa hayyacinsa amma still Idanunsa basa gani mai kyau.

Ganinta kwance ajikinsa tana fuzgar numfashi yasanya shi sa. Lallausan tafin hannunsa ya tallabo fuskarta tare buɗe manyan idanunsa da ƙyar dan har yanzu dishi-dushi yake gani, idanu ya tsirawa kan goshinta daya tsats-tsafo da zufa, sai kuma ya rumtse idanun da karfi kana ya buɗesu tare da zura ido na daƙiƙu bakwai sai kuma ya juya idanun zuwa kan wuyan hijabinta daya zame daga kanta zuwa kafaɗarta yalwataccen sumar kanta mai tsayi da ƙamshi ya zuba agadon bayanta, yayinda saura kuma ya zuba asaman fuskarta, kallonsa ya mayar kan fuskarta jin, yanda numfashinta ke fusga. Idanunsa ya mayar kan ƙirjinta da sauri ya lumshe idanun sai kuma ya buɗesu, ganin yanda numfashinta ke hawa da sauka alamun zata sume a ko wanne lokacin.

Ganin tana gab da sumewane ya sanyashi sun kuyar da kansa kaɗan, zuwa kan fuskarta kana ya ɗaura lips ɗin da suke masifar rawan sanyi akan karan hancinta, lumshe manyan idanunsa da suka sauya launi zuwa ja yayi, tare da fesa mata sanyayyan numfashinsa domin dai-dai ta mata nata numfashin, domin duk da tsoron da kuma firgicin da yake ciki hakan, bai sanya numfashinsa ɗauke wa ba, kana yana kallon fuskarta wanda akowani lokaci zata iya suma, sai kuma ya sanya hannu ya toshe hancinta tare da ɗaura sanyayyan lips ɗin sa akan nata ya riƙa hura mata iskar bakinsa mai ɗumi da kamshi ceto rayuwa zuwa gareta,
Wani irin dogon numfashi taja mai nauyi tare da fesar dashi da ƙarfi, cikin daƙiƙu kaɗan numfashinta ya soma dawowa dai-dai kana duk abinda ke faruwa idanunta na lumshe.
Sannan har zuwa lokacin hannunta na kan mararsa, saman yatsarta na kan hudan cibiyarsa, sannu ahankali numfashinta ya dai-dai ta sai dai har zuwa lokacin bata dawo hayyacinta ba, still kuma ruwan ake cigaba dayi tamkar da bakin ƙwarya ita ko sai wani irin sakewa tayi tare da lafewa a jikinsa tana shaƙar ƙamshinsa.
Shi kuwa Moddibo sannu ahankali ya fara dawowa hayyacinsa da nitsuwarsa.
Sake lafewa Khausar tayi ajikinsa tare da lumshe Idanunta domin ganin abun take kamar mafarki, ko kuma mutuwa tayi tsaban masifar tsoron rugugin da take.

Shi kuwa Moddibo sannu ahankali cikin ikon Allah ya dawo hayyacinsa, kana har zuwa yanzu tsikar jikinsa na tashi yayin da kansa ke juyawa jiri na ɗibarsa.
Ahankali ya sauƙe idanunsa akanta data manna a ƙirjinsa, yayinda tattausan suman kanta ya baje aƙirjinsa, kallonta yakeyi kamar ya samu sabuwar halitta, kana aƙasan ransa ke mgnar zuci,
Wai yaya haka ne? Mekw faruwa? Wai ma waye ni?
Ya tambayi kansa da kansa,
Kaine Moddibo, sannan wannan Khausar ce kwance ajikika tana rungume dakai cikin yanayin da ma'aurata ne kaɗai ya halatta su kasance ciki.
Wani sashi na zuciyarsa ya bashi amsa.
Lokaci ɗaya kuma jikinsa ya sake ɗaukar rawa far-far tamkar wanda ake sheƙa masa ruwan ƙanƙara lips inshi kuwa, wani irin masifeffen tsuma sukeyi,
lumshe idanunsa yayi jin jikinsa babu kuzari kona misƙala zarratin, ji yake tamkar an zare masa lakar jikinsa cikin sanyi da rashin kuzari dake tare dashi.
A hankali ya sake birkitota tare da ɗago kanta ya ɓanɓareta daga jikinsa gani yayi Idanunta alumshe.

Ita kuwa Khausar ji take tamkar cikin bacci take, ko kuma suma ta kasa fahimtar kalar yanayin
da dai take ciki,
Shi kuwa Modibbo kanta ya tallabe da hannunsa ɗaya yayin da ɗaya hannu yake ɗan marin fuskar yana faɗin.
“Ke! Keh!!”.
Shiru bata motsaba, hakan yasa ya sake ɗan fizgo muryasa tare da faɗin.
“Khausar! Khausar!!”.
har zuwa lokacin tana rungume jikinsa
For the first time arayuwarsa da bakinsa yafara kiran sunanta.

Fuskarta yake ɗan yiwa ƙananan maruka ahankali kana cikin wata Sanyayyar murya mai cike da tattausan lafazin yake fadin.
“Khausar!, Khausar!! Khausaaaar!!!”.
Lumshe idanunsa yayi shi kansa bai san yana da irin wannan raunataccen muryar ba, ya rasa taƙamemmen yana yin da yake ciki, yayin da aƙasan ransa so yake ya mata faɗa da tsawa da masifar ta sauƙa jikinsa, amma ya kasa kasancewar har zuwa lokacin bai gama dawowa cikin ainihin nutsuwarsa ba.
Kumatunta ya cigaba da ɗan mara yana faɗin.
“Khausar!, Khausar!!”.
A hankali kanta ya zame daga hannunsa ya tafi gefe luuuh kamar sumammiya.
Lokaci ɗaya zuciyarsa ta buga da ƙarfin gaske tare da jin tsinkewar zuciya ganin yanda Kanta yayi kamar ta mutu!.

Cikin ɗaga sautin murya ya sake ɗan marin kuncinta tare da cewa.
“Khausar, *Lelewal*”.
Khausar kuwa still Idanunta na lumshe take Jin sautin muryar Moddibo na kiran sunanta kamar amafarki ko kuma daga can sama.
Sai kuma ta sake jiyo sautin muryarsa da alamun kiɗima yake cewa.
“Ya salam Lelewal meya faru? me ya sameki?”.

Ahankali ya sanya hannunsa tare da ture hijabinta kana ya sanya hannunsa aƙirjinta wanda har yana iya jin tudun caɓɓullen ta ahannunsa ji yayi ƙirjinta na bugawa da ƙarfi-ƙarfi.
Hannunsa ya cire tare da sunkuyar da kansa har suna shaƙar numfashi bakin juna, bakishin yakai kan kunnenta kamar meyu mata raɗa yake faɗin.
“Lelewal tashi! Lelewal buɗe idonki!! Lelewal kalleni”.
Lumshe Idanunsa yayi akaro na barkatai tare da kai bakinsa cikin kunnenta kana cikin Sanyayyar murya mai taushi yace.
*“Fattanah!”.*
Dogon numfashi taja tare da sauƙe nan-nauyan ajiyar zuciya tare da buɗe Idanunta sai kuma ta sake runtsesu da sauri gani take tamkar har yanzu rugugin akeyi kana walƙiyar zai iya kashe mata Idanu.
Bayan kamar daƙiƙa ɗaya ta sake buɗe Idanunta still yana ronƙofe akanta yana shaƙar ƙamshin numfashin dana gashinta dake baje.
Yayin da har zuwa yanzu hannunta ke cikin sa yatsunta guda uku nakan cibiyarsa tafin hannunta da sauran yatsu biyun nakan ainihin mararsa ta danne.
Cikin wata sanyayyar murya ya tsira mata idanu tare da faɗin.
“Lelewal”,Ya faɗa still yana tallafe da kanta.
Buɗe Idanunta tayi sai kuma ta sake rufewa,
Akuma dai-dai lokacin Moddibo da itan duk suka gama dawowa cikin hayyacinsu tare da nutsuwar.
Cikin sauri tare da fushi
Moddibo ya kalleta a tsawace yace.
“Keee!!! Tafi can Mage uwar fitina tashi akaina ko in kakkaryaki”.
Ya dire mgnar cike da tsawa tare da yarfa mata mari da bayan hannunsa.
Shi kansa jin maganar yayi ta fito daga zuciyarsa kai tsaye kamar an fisgo a bakinsa.

Azabure Khausar ta buɗe Idanunta dake lumshe tare da janye jikinta daga nasa amma still hannunta na kan cikinsa tana

1 Comments On SAKAYYAH
avatar
fatima-8-5-3

6 months ago

Reply

Allah ya qara basira

Please Login or Register in order to submit comment