Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

M Jameel yace.
“Iyeeeeh toh zo ka fesa min mana tunda angumtsa maka na hannun damana”.
Tsayuwa M Jameel ya gyara tare da cewa.
“Sirrine sai da nayi al'ƙawari bazan fesa maka ba kafin ake fesa min”.
Moddibo kuwa murmushi yayi tare da shafa sajensa kana yace.
“Toh yanda kayi lallaɓa nima zanje inyi lallaɓan afaɗa min”.
Cikin dariya M Jameel yace.
“Toh kaje ka gwada sa'arka, amma yanzu kam kasani bana cikin duhu”.
Taɓe baki Moddibo yayi kana yace.
“Iyyeeee wato gulmana nema kuka tayi”.
Agogon dake ɗaure atsintsiyar hannunsa ya kalla ganin da ɗan sauran lokacin salla ne ya juyo ya kalli Moddibo tare da faɗin.
“Ba wani gulmarka da muka tayi na dai faɗa mata cewa kana ɓuƙatar aure yanzu”.
Cikin sauri Moddibo ya juya tare da watsa masa Harara Dariya M Jameel yayi tare da buɗe motarsa yashiga mazaunin Driver key yayi wa motar tare da saita hancin motar ya fara tafiya.
Shi kuwa Modibbo da ƙafa ya nufi masallacin.
A hanya ya tsaya yayi salla kana ya ƙarasa cikin gidan.

Parking aharabar gidan cike da nutsuwa ya fito tare da nufar falon bakinsa ɗauke da sallama ya shiga.
Ahankali yake bin cikin falon da kallo batare daya shiga ba cikin hasken fari gloves ɗin da suka haska falon kana da murmushi afuskarsa yace.
“Ina Umminaaaa?”.
Ummi dake zaune kan 3sitter idanu ta zuba masa batare da tace komai ba.
Malam Ahmad dake zaune kan 1sitter ya kalli M Jameel dake tsaye ƙofar falon tare da cewa.
“Ƙara so mana Jamilu”.
Juyawa yayi ya kalli Ummi kana yace.
“Kin tsaresa da ido kuma baki ce masa ya shigo ba”.
Murmushi M Jameel yayi tare da cewa.
“Ummi nayi kyau ko?”.
Jinjina kai Ummi tayi still Idanunta na kansa tace.
“Sosai ma Babana”.
Murmushi yayi tare da Wara ido kana yace.
“Iyyeee naji daɗina yau kuma nine Babanki ko da yake Baban miji ai baba ne?”.
Kai Malam Ahmad ya gyaɗa kana yace.
“Sosai ma”.
Ummi kuwa still Idanunta na kanshi.
Bashir daya fito daga Bedroom ne ya kalli Ummi kana ya kalli M Jameel data tsirawa Idanu matsawa kusa da Ummin yayi tare da cewa.
“Yaya Jameel wallahi Ummi na sonka kamar me”.
Sai asannan Ummi ta ɗauke Idanunta daga kan M Jameel ta mayar kan Bashir tare da yi masa daƙuwa kana tace.
“Haka naka Bashiru”.
Asma'u data fitowarta kenan daga Bedroom tayi murmushi tare da zama gefen M Jameel.
Miƙewa Malam Ahmad yayi tare da nufar ɗakinsa bayan sun gaisa da M Jameel.

Kallon Asma'u M Jameel Yayi tare da cewa.
“Asmeey”.
Cike da ladabi ta ɗago kanta kana tace.
“Na'am Yaya”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da cewa.
“Zuwa yanzu kaso 85% cikin 100% na nauyin ku dake araina nake tunawa 85% sun sauƙa min saura shabiyar nake tunawa 15% ɗin nan kuma sune manya masu wuya”.
Ajiyar zuciya yauƙe tare da cewa.
“Ina so inga kinyi karatu kin gama, sannan na miki zaɓi da miji na gari Mumini, Salihi, Mai tsoron Allah, na Aura masa ke, sannan na danƙa masa Amanar ki.
Hakazalika Ina so inga Bashir ya gama karatunsa ya fara aiki ta yanda ko bana kusa zai kula da Ummin mu ba zata nemi komai ta rasaba”.
Cikin yanayin damuwa Asma'u tayi ƙasa da kanta lokaci ɗaya Idanunta suka ciko da hawaye yayin da taji zuciyarta yana masifar bugawa da ƙarfi Allah ya sani in ta tuna zatayi aure ta rabu da Unminta tanajin ba daɗi.
Cikin raunin murya tace.
“Bare ma Yah Jameel kai zaka yiwa Ummi komai kafin mu”.
M Jameel kuwa murmushi yayi tare da kallon Asma'u kana ya cije labɓansa na ƙasa tare da lumshe idanunsa yana sauraron bugun zuciyarsa ajiyar zuciya ya sauƙe tare da buɗe idanunsa akan Asma'u kana yace.
“To ai ita rayuwar dama ta gaji haka watarana ayi farin ciki watarana ayi baƙin ciki!”.
Girgiza Kai Bashir yayi tare da kallon M Jameel cikin yanayin tsinkewar zuciya ya gyara zamansa tare da cewa.
“Yah Jameel Meyesa kake karyar mana da zuciya ne!?”.
Girgiza kai M Jameel Yayi tare da kallonsu wani irin tausayinsu da kuma ƙaunarsu na ratsa dukkan zuciyarsa, bashi da wani ƙunci a rayuwarsa fiye da yadda ya kasance baya tare da Umminsa da ƙannensa a inuwa ɗaya, ciwon sakin mace ba iya kanta kawai yake tsayuwa ba, har kan ƴaƴan data haifa yake shafa.
Iska mai zafi ya fesar daga bakinsa kana yace.
“Ba karya zuciya bane Bashir burina ne, akan ku inaji kuma har yanzu akwai kason da ban idaba,
sabida ban zaɓawa Asma'u mijin aure a shine babban abinda yafi damuna sannan kai kuma kagama makarantar ƙuruciya ce sai jami'a gidan kazo nazo”.
Numfashi yaja tare da fesarwa Idanunsa nakan Bashir yace.
“Acan ne ake samun tarbiyya daban-daban da halayyar al'ummar matasa kashi-kashi ina tunanin kada ginin da mukayi nida Ummi wani yaje yayi yaɓe akai ya lalata kyakkyawan gini da kyakkyawan tubalin da mukayi maka”.
Da sauri Bashir ya jujjuya kai tare da cewa.
“In sha Allah haka bazai faruba”.
Cikin jin sanyi yace.
“Bashir kayi min al'ƙawarin zaka kasance nagari, kayi min alƙawarin zaka kasancewa Ummi farin cikinta”.
Lokaci ɗaya hawaye suka cika idanun Bashir cike da tsoron kalaman Yayan nasa.
Cikin wata razananniyar murya ya kalli M Jameel da Idanunsa ke lumshe kana yace.
“Nayi maka al'ƙawari Yah Jameel Nayi alƙawari zan kasancewa Ummi ɗa nagari zan kasance me share mata hawaye, zan kasance mai sata farin ciki idan Allah yayi duniya dan Manzo (S.A.W) ”.
A hankali ya ɗaga idanunsa tare da kallon Ummi da ta tsirawa M Jameel idanu cikin wani irin yanayi ko ƙyaftawa bata yi ajiyar zuciya ya sauƙe kana yace.
“Zan kasance mai sata farin ciki, nayi alƙawari Ummi ba zata taɓa shiga ƙunci ko damuwa ba in dai a kai nane in sha Allah”.
Ahankali M Jameel ya maida kansa jikin kushin ɗin ya jingina kana ya miƙe ƙafafunsa tare da riƙe hannun Bashir aciki nasa kana ya cije lips ɗin sa.
Ummi kuwa wani irin sanyi jikinta da zuciyarta keyi cikin wani irin yanayi ta zubawa M Jameel Idanu.
Anutse M Jameel ya buɗe Idanunsa dake lumshe ya sauƙe akan Ummi Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da furzar da iska daga bakinsa kana yace.
“Ummi ya dai kike kallona haka kamar na ƙarshe!?”.
Cikin saurin Ummi ta dafe ƙirjinta daya buga da ƙarfin gaske cikin raunin murya irin na wanda ke gab da zub da hawaye ta kallesa karo na farko arayuwarta data fara kiran sunan sa tace.
“Haba haba Jamilu”.
Cike da mamaki ya ɗago idanunsa da suka sauya launi ya kalleta, Asma'u ma da sauri ta kalli Ummi haka ma Bashir karo na farko kenan arayuwar su da suka ji Ummi ta kira M Jameel da sunan sa.

Ummi kuwa lokaci ɗaya wasu hawaye masu masifar zafi suka fara bin kuncinta Shar-shar.
Cikin yanayin tashin hankali M Jameel ya sauƙa tare da ƙara sawa gabanta ya durƙusa tare da riƙe hannun ta cikin sanyin murya yace.
“Ummi kiya femin Ummina kiya femin kada ki zubar da hawayenki akaina Ummi me nayi miki!”.
Damƙe hannunsa Ummi tayi cikin raunin murya da alamun tashin hankali tace.
“Meyesa kake zuwa kake karya mana zuciya nida ƙannenka, kasani ayanzu kaine Inuwata kaine mafakar da muke samu nida ƙannen ka muke fakewa. Meyesa wasu lokutan idan kazo kake min wasu maganganu masu wuyar fahimta”.
Ta ida maganar hawaye nabin kuncinta.

Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da yin murmushi yayin da Idanunsa ke sheƙi kana yace.
“Toh Ummi inada ikon canza ƙaddarata ce? Idan son samu ne Ummi zan kasance me Kula dake har iya ƙarshen numfashi na, kuma zan kasance me saki acikin farin ciki da walwala har numfashina na ƙarshe”.
Girgiza kai Ummi tayi still Hawaye nabin fuskarta tace.
“Ko yanzu ka sanya ni farin ciki duk kan wani farin ciki da jin daɗi ka bani shi Jamilu”.
M Jameel kuwa cike da mamaki ya ɗago Idanunsa dake jiƙe da ruwan hawaye yace.
“Ummi me kika ce?”.
Cikin Muryan kuka tace.
“Jamilu nace”.
Kallonta yayi cikin rawan murya yace.
“Ummi Meyesa?”.
Hawaye na zuba daga idanunta yayin da jikinta ke tsuma tace.
“Toh me zance maka? Kana tunanin bana jinka araina ne? Kana zaton bana jinka ajikina ne?
Ban taɓa ganin wani ɗa kafin kai bafa Jamilu, kaine ɗana na farko tsatsona, jinina, mallakina, kafin inga Asma'u da Bashir da dai abu ya sameka a ace ina da ikon canza ƙaddara da zan dawo dashi kaina, domin nasan ko bayan raina zaka kula da ƙannen ka fiye da yanda zan kula da su”.

Sauƙe ajiyar zuciya tayi tare da share hawaye masu zafin gaske da suka zubo mata kana tace.
“Kaga ma min komai Jamilu, kayi min komai Jamilu. Ubangiji Allah Yamaka albarka Allah Ubangiji ya rufa maka asiri duniya da lahira Allah yasa kagama da duniya lafiya”.
M Jameel kuwa sake Matsawa jikin Ummi yayi tare da ɗaura kansa akan cinyarta hawaye masu zafin gaske suka shiga bin kuncinsa Shar-shar-shar.
Ganin haka yasa Asma'u dake gefe ita hawaye suka shiga bin kuncinsa.
Kusa da Asma'u Bashir ya matsa tare da sanya hannu ya shiga share mata hawayen cikin raunin murya yace.
“Kiyi haƙuri Asma'u kada kiyi kuka kinga zaki ƙara karyarwa Ummi zuciya”.
Kai ta gyaɗa yayin da hawaye suka cigaba da zubowa daga Idanunta cikin sheshsheƙan Kuka tace.
“Ka gani fa Yah Jameel ma kuka ya keyi”.
Jin haka yasa M Jameel da Idanunsa ke jiƙe da hawaye ya ɗago kansa tare da sakar mata da murmushi kana yace.
“Hmmm Asma'u kinsan meyake sani kuka?”.
Kai ta girgiza still Hawaye na bin kuncinta.

Lumshe Idanunsa yayi tare da taune lips ɗin sa kana yace.
“Kada kiyi kuka saboda ke baki da abinda zai saki kuka”.
Cikin sheshsheƙan kuka ta kallesa still hawaye na zuba daga Idanunsa cikin wata raunan'niyar murya tace.
“Toh Yah Jameel me yake saka kuka Idan muna da iko zamu raba ka dashi”.
Girgiza kai yayi tare da rintse idanunsa kana yace.
“Ba zai rabu ba Asma'u tun tasowa ta aduniya bayan shekara goma sha huɗu bani da damuwar data wuce ganin Ummi bata gidan mahaifina, hankalina yana tashi akan hakan, kuma ina tunanin hakane badan faɗa da ƙaddararta ba, a'a saidai inajin maraici inajin kewar ta, inajin ciwon rashi mahaifiyata a cikin gidanmu, ina so ko yaushe Idan na tashi naga Ummi kusa dani haka zalika idan zan kwanta ya zama naje gareta taimin addu'a muyi saida safe”.
lumshe idonsa yayi yana mai jin wani irin yanayi azuciyar kana ya buɗe su tare da cewa.
“Ina so kafin naje na kwanta akowani dare in ganta kafin naje nayi bacci ina jin kamar nayi rashin komai na duniya da Ummi bata kusa dani ina jin mai zan mata na sauƙe hakkinta na uwa akaina”.
Shafa kansa Ummi tayi still hawaye nabin fuskarta kana cikin raunin murya tace.
“Toh wai meye rage da bakayi min ba? Ka kaini Makka, Ka kai ni Madina ka gina min kyakkyawan muhalli ka zuba min Kyakkyawan kayan ƙawa, ka riƙe cina shana suturata jinyata nawa dana ƙannen ka harma mijin da nake tare dashi har maƙotan dake tare dani baka barsu sun zubda hawayeba kanai musu dukkan abin buƙata”.
A hankali ta danne kukan dake ƙoƙarin sufce mata kana tace.
“Jamilu har maƙota nafa kagama yi musu komai”.
Murmushi M Jameel yayi still Hawaye na bin kyakkyawar fuskarsa kana yace.
“Har yanzu ban gama ba Ummi, sai dai ki tayani da addu'a Allah yasa in gama Allah yabani ikon gamawa”.
Sai kuma ya maida kallonsa kan Asma'u dake zubda hawaye har zuwa lokacin take kuka kana ya maida kallonsa ga Ummi yace.
“Ina Son inga na Aurar da Asma'u sannan inga Bashir ya zama babban mutum magidanci kafin wannan lokacin Ummi *INA SON INYI AURE”*.
Cikin sauri Ummi ta ɗago Idanunta dake jiƙe da hawaye ta kallesa kana tace.
“Me kace Jamilu?”.
Ɗago kansa yayi tare da kallonta kana ya jinjina mata kai tare da cewa.
*“Ummi ina so inyi Aure”.*
Cike da mamaki Ummi ke kallon aranta tace tunda nake arayuwarta Jameel bai taɓa faɗa min magana makamancin haka ba”.
Sake Kallonsa tayu akaro na barkatai kana tace.
Babana kaine? Kai da bakinka kake ce min kana so kayi Aure?”.
Jinjina kai yayi tare da faɗin.
“Ummi ina so inyi Aure in ɗaukeki ku dawo gidana dake da Malam sannan Asma'u da Bashir duk mu zauna tare dasu duk sanda gari ya waye na dawo gidana in ganki Kusa dani mu zauna afalonki ki bamu tea musha Idan dare yayi kafin na kwanta nazo na zauna afalonki ki bani Tea nasha”.
Sauƙe ajiyar zuciya yayi tare da lumshe idanunsa kana ya buɗesu tare da cewa.
“Sannan nayi hira da ƙanne na. Ina son haka Ummi shiyasa nake so nayi Aure Insha Allah Ummi zanyi Aure zanyi Aure”.
Ummi kuwa cike da mamaki da kuma jin daɗin kalamansa tayi yalwataccen murmushi kana tace.
“Haka naka”.
Da sauri ya rufe idanunsa tare da cewa.
“Ummi ni ɗin?”.
Cikin shafa kansa tace.
“Eh kai ɗin, wato dan kana son ka sanarmin zakayi aurene, sai kabi ka kashe min jiki, ka zauna ka tasani gaba harda kukanka, ko gaisawafa baka bari kunyiba, ashe du mgnar auren ce ke tsaburarka”.
Murmushi Asma'u da Bashir sukeyi cike da jin daɗi,
Shima M Jameel murmushi yakeyi tare da sunkuyar da kansa cike da alamun kunya.
Ita kuwa Ummi numfashin jin dadi ta fesar tare da cewa.
“Allah ya yarda Babana Ubangiji Allah ya nufa. Allah ya Al'barkanci rayuwar ka Allah ya nufa. Allah ya rufa maka asiri Allah ya maka kyakkyawan tanadi agidan Aljanna ya kuma yima zaɓi da mace ta gari”.

Murmushi yayi cike da jin daɗin Addu'ar ta ya shafa sajensa tare da cewa.
“Ameen Ummina”.
Asma'u da Bashir kuwa dariya sukayi suna jin ƙaunar Yayan nasu, miƙewa yayi tare da yiwa Ummi Sallama kana ya fice bayan tayi masa Allah ya tsare.

Kai tsaye gidansu ya nufa cikin nutsuwa yake Driving har ya isa gida bayan yayi Parking ya fito atsaye ya hango Abbansa akan barandar sashen sa ya goya hannunsa abaya.
Ganin Abba yasa ya nufesa Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe tare da kallon sa kana yace.
“Babana daga ina haka kake?”.
Langwaɓar da kai M Jameel yayi tare da sanyaya muryarsa kana yace.
“Abbah daga gidan Ummina nake”.
Numfashi Abbah ya fesar kana ya kalli agogon dake ɗaure atsintsiyar hannunsa tare da cewa.
“Babana kalli fa yanzu ƙarfe sha ɗaya da rabi Meyesa baka tsoro ne”.
Ajiyar zuciya M Jameel ya sauƙe tare da kallon Abba kana yace.
“To Abba tsoron me Mutum zaiji, duk guduna fa bazan guji ƙaddarata ba haka zalika duk saurina ƙaddarata ta fini sauri, kana duk hamzarina da kuma ɓuyana ƙaddarata tafini sanin inda nake”.
Jinjina kai Abba yayi kana yace.
“Duk da haka bana so Babana, duk inda kake indai ƙarfe sha ɗaya yayi ka kwana awajen, ba wani abin ni na amince ma nasan ba baza kwana alalaceccen waje ba ko kuma inda zai jaza min magana”.
Cike da ladabi ya jinjina kai kana yace.
“Toh Abbana”.
Kansa Abba ya shafa yace.
“Ubangiji Allah ya Albarkanci rayuwar ka Allah yatsareka da duk kan abinƙi”.
Murmushi yayi tare da faɗin.
“Ameen Abbana”.
Kana ya juya ya nufi ɗakinsa.

Acan gidan Lamiɗo kuwa Hajiya Aysha ce zaune da ƴaƴanta acikin falon su.
Ramadan dake zaune gefen Khausar ya ɗago kai tare da kallon ta kana yace.
“Addah Khausi ke kam kin huta da zuwa makaranta”.
Murmushi Khausar tayi tare da kallon Ramadan kana tace.
“Yanzu zan fara wani ai Ramadan”.
Ya mutse fuska yayi kana ya kalli Mommy dake zaune kan 2sitter yace.
“Mommy na”.
Ahankali Mommy ta ɗago kanta tare da cewa.
“Na'am Ramadan ɗina”.
Langwaɓar da kai yayi tare da marairaice murya kana yace.
“Ayyah Mommy am gobe abarni kar Inje makaranta mana”.
Kallonsa Mommy tayi tare da cewa.
“Toh Meyesa Ramadan?”.
Kai ya Girgiza kana ya marairaice murya tare da cewa.
“Mommy nidai kawai bana son zuwa Makarantar nan”.
Hankalinta ta mayar kansa kana tace.
“A'a Babana ba yadda za'a yi haka ace baka son zuwa makaranta. Ai yanzu ka fara zuwa ma”.
Araunace ya kalli Mommy tare da cewa.
“Dan Allah Mommy Gobe kawai.
Na goben nan dan Allah Mommy na kada Inje Mommy na goben nan kawai kada abarni Inje makaranta kada inje”.
Girgiza Kai Mommy tayi cike da kulawa tace.
“A'a Ramadan ya za'a yi inbarka ba kaje makaranta ba ai bazai yuwu ba dole ne kaje makaranta kam”.
Jan zuciya yayi tare da dafe kuncinsa kana yace.
“Mommy shikenan kin yarda in tafi?”.
Jinjina masa kai tayi tare da cewa.
“Na yarda mana kaje”.
Miƙewa yayi daga wajenta ya koma kusa da Khausar tare da riƙe Hannunta cikin yanayin roƙo ya langwaɓar da kai tare da marairaice murya yace.
“Addah Khausy ki tayani bawa Mommy haƙuri gobe kada Inje makaranta kice tabarni gobe kar Inje makaranta mu zauna da ita bana son zuwa makarantar nan Addah Khausi bana so ki faɗawa Mommy”.
Khausar kuwa Kallonsa ta riƙa yi har ya kai ƙarshe, ajiyar zuciya ta sauƙe tare da riƙe tafin hannunsa acikin nata kana tace.
“Toh Ramadan tun daga yanzun ka kana primary 3 sannan kace bakason zuwa makaranta Primary mafa yanzu kayi rabin gamawa ai Ramadan ka fara da wuri”.
Araunace Ramadan ya kalleta tare da cewa.
“Yanzu Addah Khausi zaki bari inje”.
Cikin rashin ɗaukar maganarsa da muhimmanci Khausar tace.
“Eh Sosai ma”.

Haiydar dake kwance kan 3sitter ya ɗago kansa tare da kallon Ramadan kana yace.
“Eh dolenka. Dolenka ma kaje”.
Sai kuma ya maida kallonsa kan Mommy dake kallon Ramadan kana yace.
“Allah Mommy Idan aka sakewa Ramadan ma bazai yi karatu ba”.
Tura baki Ramadan yayi tare da sake hannun Khausar ya koma jikin Mommy kana yace.
“Mommy ki faɗa masa ƙoƙarin da nake a hadda ai yasani ko.
Gasa akaje ni nake zuwa mana na ɗaya a sate ɗin mu”.
Jinjina kai Mommy tayi tare da cewa.
“Na sani Ramadan kana ma da kokari kawai dai da kake cewa kar abari kaje gobe abarka ka hutane bai yi ba. Idan ka tuna ma gobe Laraba ne idan kaje gobe jibi Alhamis zaka huta gata Friday shima zaka huta kaji ko Ramadan”.
Girgiza kai yayi still Idanunsa akan Mommy yace.
“Ayyah Mommy ni Banason zuwa ki barni mana”.
Khausar ne ta kallesa cike da mamaki tace.
“Ohh Ni Khausar yau kam naga ikon Allah da nacin yaro”.
Taɓe baki Haiydar yayi tare da cewa.
“Rabu dashi duk zai gama kuma dole gobe sai yaje makaranta”.

Acan Bedroom ɗin Hajiya Bunayya kuwa kwance take akan makeken gadonta daya ji shimfiɗa na alfarma kana kunnenta maƙale da babbar waya ta gyara kwanciyarta tare da cewa.
“Nama gama ɗaukar wannan matakin in Allah ya yarda in dai wannan anyi angama ya wuce Babban shima Insha Allah za asan abinda za'a yi akai”.
Daga ɗaya ɓangaren Hajiya Lami dariya tayi kana tace.
“Da dai yafimiki in ba Haka ba kina gani ƴaƴan ki zasu zama bayi, dan da zaran sarautar nan ta fita ahannun ku kinyi bankwana da ita ƴaƴan ki kuwa sun zama tamkar ba ƴaƴan Sarauta ba, duk da cewa Masarautar ba wata babba bace ai baka so ya wuce kaba ya fita ahannunka!”.
Ajiyar zuciya Hajiya Bunayya ta sauƙe kana tace.
“Hakane”.
Murmushi Hajiya Lami tayi tare da faɗin.
“Kinga ai Gimbiya Fadeela ta cikin Taraba Aminiya tace duk iya ƙoƙari tanayi dan ganin sarauta ya zauna ahanununta ke kanki kinsani ai ina faɗa miki saboda iya na cinka iya samun abin ka”.
Jinjina kai Hajiya Bunayya tayi kana tace.
“Hakane ai ma duk na gama shi in faɗa miki”.
Ajiyar zuciya Hajiya Lami ta sauƙe kana tace.
“Ai haka yafi kam kada ki tsaya kallon ruwa kwaɗo ya miki ƙafa”.
Dariya Hajiya Bunayya ta sheƙe dashi kana tace.
“Kede ki bari zaki sha kallo”.
Hira suka sake taɓawa daga haka Hajiya Bunayya ta katse kiran.


Washe gari.
Da safe baki ɗaya yaran aka shirya su cikin Uniform Bayan Khausar ta gama shirya Ramadan cikin Uniform ɗin sa tamiƙe ta shiga kichen dan ɗauko masa Lunch box ɗin sa.
Ramadan kuwa yana ganin fitan cikin sanɗa ya fice daga sashen nasu zuwa sashen Hajiya Bunayya ya ɓoye.

Khausar kuwa kai tsaye Bedroom ɗin su ta nufa bakinta ɗauke da Sallama Cak ta tsaya ganin Ramadan bai ciki ƙara sawa ciki tayi tare da kiran sunan sa amma shiru toilet da Wadrope ta buɗe still baya ciki.
Cikin sauri ta fito tare da nufar Bedroom ɗin Mommy kana ta kalli Mommy dake zaune gefen gado tace.
“Mommy na gama shirya Ramadan da Raudat kuma ga Raudat amma banga Ramadan ba har munje wajen mota bamu gansa ba”.
Miƙewa Mommy tayi tare da cewa.
“Ikon Allah to ina kuma yashiga?”.
Buɗa hannu Khausar tayi da faɗin.
“Allahu A'alam”.
Falon suka fito tare da duba ko ina amma baya nan.

Kallon Khausar dake leƙa bayan Kushin Mommy tayi kana tace.
“Khausar jeki duba ɗakin Haiydar ko yaje ya ɓuya acan yau, Bansan meke damun Yaron nan ba tun jiya baya so ayi masa batun zuwa makaranta abinda bai taɓa yi ba”.
Taɓe baki Khausar tayi kana tace.
“Iyayi mana Mommy daga anyi masa wasa shikenan ya ɗauka”.
Ta ida maganar tare da fita zuwa ɗakin Haiydar.
Abakin ƙofan ta tsaya tare da ɗan ɗaga sautin Muryanta kana tace.
“Ramadan kafito fa?”.
Shiru ba amsa jin haka yasa ta buɗe ƙofar ɗakin tashiga shiru ba kowa da mamaki take kallon ko ina dake kimtse tsaf har toilet ta ɓude still baya ciki siririn tsaki taja tare da ficewa ta koma sashen Mommy.

Ƙugunta ta riƙe da hannu ɗaya kana ta kalli Mommy dake tsaye tace.
“Mommy ban gansa ba fa”.
Girgiza kai Mommy tayi tare da faɗin.
“Toh kije ki duba sashen Ummanku ko yaje ya ɓuya acan kinsan itama zata iya ɓoyesa”.
Kai Khausar ta gyaɗa kana ta juya ta fice.
Bakinta ɗauke da Sallama tashiga falon zune ta samu Hajiya Bunayya akan 1sittee.
Kallon ta Khausar tayi tare da cewa.
“Ummah Ramadan yazo nan?”.
Murmushi Hajiya Bunayya tayi tare da gyaɗa kai kana tace.
“Eh gashi nan yazo ya ɓuya wai yau baya son zuwa makaranta”.

Ƙwaffa Khausar tayi kana tace.
“Aikuwa dole sai yaje”. ta faɗa tare da wuce Bedroom Kana tace.
“Wallahi Ramadan kafita idona”.
Jin muryan Khausar yasa Ramadan miƙewa tare da hawa can karshen gadon Hajiya Bunayya kana ya ɗaga sautin muryansa tare da cewa.
“Dan Allah Ummah ki hanasu kice yau dai kawai subarni kada Inje makaranta”.

Murmushi Hajiya Bunayya tayi tare da haɗa hannunta biyu waje ɗaya kana tace.
“Dole sai kaje maza ka fito ka tafi nikam kasan bazan hanaka zuwa makaranta ba, Ramadan dole zaka je”.
Dai-dai lokacin Sulaiman ya fito tare da faɗin..
“Ikon Allah yau Ramadan da kanka kake cewa baka son zuwa makaranta duk ƙoƙarin kan nan?”.
Shi dai bai ce komai ba Khausar na ƙoƙarin za gayawa gefen gadon ta riƙo sa yayi saurin ɗirƙa ta ɗaya side ɗin gadon ya fice waje da gudu.

Dafe kai Khausar tayi tare da bin bayansa yana cewa.
Ramadan kazo mu tafi Sulaiman duk sun shiga mota saura kai ka ɗai ake jira”.
Shi kuwa Ramadan sashen Mommy ya nufa da gudu yana shiga ya ɓuya abayan Mommy.
Muryarsa na rawa tamkar wanda ke shirin fashewa da kuka yace.
“Mommy dan Allah kar inje”.
Hararansa Mommy tayi kana tace.
“Sai kaje Meyesa ba kason zuwa Ramadan ka faɗa min dalili”.
Rau-rau da idanunsa yayi kana yace.
“Ni dai bana so bazan jeba Mommy”.
Dai dai nan Khausar ta shigo kansa ta nufa tare da miƙa hannunta da niyyar kamasa tayi saurin damƙe maranta tare da rintse Idanunta kana tace.
“Wayyo Allah na!”.
Cike da kulawa Mommy ta kalleta tare da cewa.
“Yau kuma ciwon cikin ki ko?”.
Kai ta gyaɗa mata cikin sanyi murya ta kalli Ramadan kana tace.
“Ramadan kazo mana kai kaɗai fa ake jira”.
Maƙale kafaɗa yayi dai-dai nan suka jiyo hong ɗin mota cikin sanyin murya Khausar tace.
“Mommy kin jifa shi kaɗai ake jira zasuyi letti fa Allah zaija idan sunje azanesu kinsan, Moddibo ba ruwansa ko yara sawa yake aci ƙaniyarsu!”.
Ta ida magansr tare da miƙa hannu da niyar janyo sa.
Cikin sauri Ramadan ya sake Matsawa baya tare da riƙe ƙafafun Mommy tare da fashewa da kuka kana cikin raunin murya yace.
“Mommy dan Allah kice abarni ni dai yau bana son zuwa makaranta bana so Mommy dan Allah ki barni”.
Mommy kuwa Kallonsa tayi lokaci ɗaya taji jikinta yayi masifar sanyi janye ƙafafunta tayi tare da Kallonsa kana tace.
“Kai Ramadan wai meyesa bakason zuwa makarantar?”.
Cikin kuka sosai yace.
“Ayyah Mommy dan Allah yau ɗin nan kaɗai ki barni kada Inje makaranta nafi so yau In wuni ina kallonki kina kallona”.

Girgiza kai tayi tare da cewa.
“Ramadan kaje yau kaga gobe idan Allah yakai mu Alhamis ne baza kaje makaranta ba zamu wuni agida juma'a ma zamu wuni tare kaga har Asabar ma baza ka jeba”.
Girgiza kai yayi still hawaye na bin Fuskarsa yace.
“Mommy ni dai bana so”.
Miƙewa Khausar tayi tare da kama hannunsa tana jansa shima hannun Mommy ya riƙe yana kuka Khausar na jansa yana jan Mommy da ƙar ta fincike sa suka fita kana ta sanya shi amota tana kallon Haiydar dake hararan Ramadan tace.
“Gashi ku tafi”.
Kana ta juya ta koma ci.
Da yake shi Haiydar haddan safe suke zuwa na maza.

Kusa da Mommy ta zauna tare da riƙe mararta tana yarfe hannunta kana ta runtse Idanunta tare da faɗin.
“Wayyo Cikina ciwo Mommy!”.
Mommy kuwa jikinta ne yayi sanyi kallon Khausar dake riƙe da marar ta tayi tare da cewa.
“Ke tashi kijeki ɗauko min Yarona, bana so yau abar minshi kada yaje makarantar

1 Comments On SAKAYYAH
avatar
fatima-8-5-3

6 months ago

Reply

Allah ya qara basira

Please Login or Register in order to submit comment