Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

mamanshakur Is all about novels.
Skip to content
Home
About
TSAFI 1to 11
← KABILAR MU 45 TO ENDKAINE SIRRI NA 9 &10 →
KAINE SIRRI NA 1 TO 8
Posted on April 28, 2016 by mamanshakur
[4/25, 1:25 PM] Aishat Muhammad: [4/25, 9:10 AM] Aishat Muhammad: 🖌KAINE SIRRI NA🖌
1
Sakamakon jin danayi anyi littafi maisuna “RA’AYINA”yasa na chanza na maidashi “KAINE SIRRI NA”.

Ahankali nake tafiya cikin wani babban wuri wanda aka radama suna THE ATTORNEY ‘S WORLD. Office din lawyoyi ne sunfi dari aciki,an kawata su da fulawowi da wasu irin madubai da wutan lantarki masu kyau daban shaawa, koni m shakur na shigo wurin ne Dan neman lawyer dazan bude company a wurin shi. Tafiya na cigaba dayi harna kai gaban wani office sai naji ana hayaniya dariya nadanyi nace nafasa bude kampanin dole na daukoma matsoyana wanga rahoto lol.

Bismillahi Rahmanir Raheem.

“RA’AYINA ne MUZZAMIL bazan auri wacce batai graduating ba,bazan auri under graduate ha, nafison na auri wacce ta gama school,ta waye, duk inda zan shiga zan iya zuwa da ita batare dajin ko darr araina ba”…da sauri dayan ya tari numfashin shi yace “B maisa kakeda tsatsauran RA’AYI? Kaga niko Kullum burina na auri yar sacandari, wacce zan koyamata komi,soyayya,girmamawa, biyayya, tsorona everything B,duk yanda naso tayi zatayi,zan lankawasa na tankwara ta zuwa kowani position danaga dama, kai mesa ka banbanta da sauran mutane?” Dan murmushi B yayi yace “RA’ AYINA kenan”, daukan keys din motarshi dake kan table yayi ya dago yana gyara buturan gaban rigan shi daya bude idanunshi nakan bituran dayake makalawa yace “dama na shigo ne nafada ma gobe zan shiga minna,Niger state, akwai wasu case danakeda shi akasa, 3 days zanyi in sha Allah”. Muzammil yadan zaro ido yace “garin da akai earthquake(girgizan kasa) jiya ne zaka?” Yakarasa maganan yana kallon B dake kokarin makala neck tie dinshi batare da wani damuwa akan fuskarshiba, Muzammil yace “badakai nake magana ba,earthquake akayi fa koyau saida nakara karantawa a news kuma daga site wanda basa sa karya wato Vanguard news…” B ya dafe kanshi murya chan kasa yace “God!” Dago kanshi yayi ya kalli Muzammil yace “will you just listen to me, ba earthquake akayiba, Wani babban ginin bene ne ya rushe mutane 5 sun mutu Allah ya jikansu, Gobe nidai zanje nai abunda yakaini” Muzammil yaraka shi har wurin mota, shiga motar yayi ya zauna zaro taba kwara daya yay ya makala a bakinshi, lighter ya dauko zai kunna yaji an fizge taban Muzammil yace “Allah nakusa fadama mum kanashan taba,kasan baida kyau amma kaitayi niba gashi nadena ba amma kai kaki”… B na ganin zai batamai rai yaja motan yay gaba batare daya ce mai komiba.

Su uku aka zakulo daga ginin daya rushe ayau ranan jumma’a, inda jiya aka samo biyar matattu,wurin gabaki daya bama ka iya ganin kona kusa dakai saboda kura dake tashi,sai kukan mutane kakeji wayanda yan uwansu suka mutu sakamakon rushewan da gidan benen yayi. Daya daga cikin Daktan da gwamnati ya kawo wurin dan bama wayanda sukaji rauni taimakon gaggawa. duba mutane ukun yayi wanda da alamu baba Mata da yarsu ne, ya dago ya kalli sauran yan uwanshi dasuka zageyeshi cikin rashin kuzari yace “parent din are already dead yarinyar kuma ta bugu but tanadai rai, yanzu ai informing government mutane 7 suka mutu, wayanda suka samu injury 35 hade da yarinyar nan”.

Wani irin ihu yarinyar tasaki ta zabura tafado daga gadon, wurin iyayen nata tayi tana kuka sosai babu wanda yahanata zuwa inda suke, tsayawa tayi tana kallonsu idanunta sunyija sosai, tai shiru ganin haka likitan yabada umarni a wuce dasu asibiti inda ake ijiye gawawwaki idan aka nemo yan uwansu sai abasu suje su burne. Itakuma aka daurata kan gado ganin yanda jikinta ke rawa, aka bata magani sanan suka cigaba da duba sauran wayanda sukaji ciwo. saukowa tayi daga gado batare da kowa ya lura da itaba tafita daga barandan da gudu.
Gudu take iya karfinta tana share hawaye bata ganin na gabanta bata ganin na bayanta ita tadaisan tana daga kafa tana gudu iska na kadata kwakwalwar ta abu daya kawai take hango Mata lokacin da suke kan dining suna breakfast da Abba da Umma da ita, sai sukaji Kara sukaji ginin na rawa ji tayi Abban ya janyota ya turata cikin jikinshi ya daura bayanshi kan nata daganan saitaji jikin Abba yay Kara kaman ballewan kashi, ahankali ya furta laa’ilaha illallah, tadaiji nauyi sosai ajikinta takumaji abu nabin jikinta kaman ruwa, ihu ta dingayi tana neman taimako tana kiran umma harta sume. Saikuma yanzu data farfado taji Abba da Umma sun mutu. Kara gudu tayi na bala’i hawaye na tsiyaya daga idanunta Abba maisa baka bari ginin yafadomin ba nima dukanmu mu mutu tare Maisa? Kummmm kakeji tabugu dawani gini block tafadi a wurin sumammiya jini nafita daga goshinta.

Maman Abd Shakur😘
[4/25, 11:23 AM] Aishat Muhammad: 🖌KAINE SIRRI NA🖌

2
*washe gari*

11 na safiya tamai cikin garin Minna ahankali yake Jan motarshi ganin yakusa kaiwa inda zaije. dan gajeren tsaki yaja awahale “mtswww” ya paka motar a gefen hanya,juyowa baya yay ya mika hannunshi yadauko goran ruwan polar water dake back seat, sanan yay amfani da dayan hannun ya bude motar yafita yafara waige-waige, wurin shiru babu mutane dayawa sai kwarori dake wucewa, tafiya kadan yayi ya shiga wata yar karaman hanya haka jikin wani dan gini inda yaga babu mai wucewa ya tsaya yay abunda zaiyi ya maida zip yaja sanan ya juyo zai koma wurin motarshi yaji alumun numfashin mutum, cigaba da tafiya yayi dan atunaninshi wani naman daji ne, kaman ance ya kalli kasan wurin saiya ga jini, tracing dige digen jinin ya dinga bi haryakai bakin wani gini da anfara ba’a karasa ba, tsayawa yayi shi bai shiga ba shikuma bai juyaba waigawa ko ina yayi yaga babu kowa awurin yakara kallon kasan yadaiga ga jinin da alamun koma wanene yana cikin ginin, bismillah yayi ya shiga kai tsaye yafarabin sahun jinin harya kai bangon karshe, ganin mutum yay akwance shame shame baya ganin fuskan daga inda yake saidai yaga zanin atampa ajikinta, karasa wa yayi ya tsugunna gabanta yana kallonta sama da kasa, numfashi yaji tanayi ahankali awahale hakan yasa yakai hannu ya juyo da ita yana mai karema fuskan ta kallo “Subhanallah” ya furta ganin yanda goshinta ke fitar da jini da sauri yasa hanunshi a aljihun wandon shi handki yaciro yadaura akan goshi yafara kallon ko ina ko akwai any clue dazai gane daga ina take Kokuma yan uwanta,ko waya kowani abu, dawo da idonshi kanta yayi jin tafara numfashin tana fito da harshe hakan yasa yagane ruwa takeso rike kanta yay yadau ruwan yana bata ahankali ta shanye tass sanan jikinta gabaki daya ya saki a hanunshi da sauri ya dagata yafito da ita daga wurin har bakin titi yasata cikin motarshi sanan yaja da sauri dan nemamata lpy, agaban wani babban hotel yay horn aka bude ya shiga ciki yay parking a wurin paka motoci wasu mutane uku dukansu maza kowananen su rike da wata yar karaman littafi a hannu suka budemai motan da sauri daya daga cikinsu yace “is already 12:PM, and case din damuke dashi 12:10 za’a shiga” Fuzar da iska yayi ya dafe kanshi batare dayace komiba, daya daga cikinsu yace ” your breakfast is ready ” da sauri na ukun yace ” you have visitors sir” gajeren tsaki yasaki yay gaba, sai kuma yajuyo akasalance yace ” akawai yarinya a mota, Johnson take her inside,and u Solomon ka kira Dr ya dubata” yajuya yahau bene, dakin da aka tanada mussamman saboda duk lokacin daya sauka ya shiga direct bayi yaje yay wanka ya chanza kaya suwa suit baki da wandon shi sai takalmin min baki cover mai sheki, ya cire tabaran idonshi da ruwan wanka ya tsalla akanshi ya goge ya mayar, ya fesa designers turare mai suna kingdoms ya mike tsaye ya daura necktie sanan yafito daga dakin. dakin dake kusa da nashi ya shiga yaga Dr Faruk yana dubata, kallon agogon hanunshi yayi sanan ya kalli Dr Faruk yace “am late, anjima I will see yhu” ya bude kofa yasakai yafita saikuma ya juyo kallon fuskan yarinyar yayi nadan tsawon sakonni sanan yasakai yafita daga dakin P.A na binshi abaya da jakan laptop dawasu takardu a hanunshi.

Maman Abd Shakur😘
[4/25, 1:23 PM] Aishat Muhammad: 🖌KAINE SIRRI NA🖌

3
Karfe 4 na yamma yagama abunda zaiyi shida P.A a high Court na Minna suka fito, saida yay sallan la’asar sanan suka dauko hanyar gida. yay wanka ya chanza kaya zuwa na Shan iska ya zaro taba yana zuka anishadan ce wakan awww na tashi, idanunshi a lumshe yaji anyi knocking bude idonshi yayi sanan yabada izinin shigowa P.A ne ya shigo yace “kanada baki sir, tunna dazu ne basu tafiba” wani kallo yama P.A tareda busar da hayakin taban sanan yace ” waiba nace karku fadama kowa zan zo Minna ba, cases dake kaina are enough, banason anymore wahala” da sauri P.A yace “ka gafarce ni, wasu couple s ne for d past one month sukeson ganinka kullum suna kira nace musu bakanan, saisa nafada musu yanzu kazo” batare daya kalleshi ba yace “sujira ni, ina zuwa”, saida yagama Shan taban sanan ya mike yadau lemon mint yajefa abaki, yafito zuwa office dinshi nacikin hotel din yabada izinin ashigo dasu, yana zaune aka bude kofa aka shigo Babban magidan cine da matarshi fara kakkyawa mai kama da balarabiya, da sauri ya mike ya mikama mutumin hannu suka gaisa ya nuna musu kujera suka zauna Alhajin yay magana da murmushi yace “BARRISTER BARRAQ,tun randa mukaga firan da akayi dakai a African independent television (AIT) my wife here, ya nuna hajiya tace dole mune meka,kallo daya mukaima mukasan kanada gaskiya, kallo daya mukaima mukasan zamu iya fadama matsalan mu,haka kuma kaji kakuma taimaka mana, kanadaga cikin lawyoyin kasar Nigeria masu tsayawa kan gaskiya,da bima talakawa hakkinsu ga yawon taimako,kafin mu sanka muke jinka da alkhairan ka ga jama’a” yakarasa maganan yana kallon fuskan B da kanshi ke kasa baka gane yanayin dayake ciki, Alhaji ya cigaba ” yace aranan ashirin ga wata agusta ta shekara 2015 muka wayi gari bamuga yarmu tilo maisuna RUFAIDA ba,munsan agidan ta kwana tare mukaci abincin dare komi tare amma muna tashi bamu gantaba, saidai mukaga dakin ta abude da alamun tafita, tundaga ranan babu inda bamu shiga nemanta ba, mun sanar a kafafan sanar wa amma babu ita babu alamunta gashi shekara na neman tafiya batare da munga yarmu ba har polisawa mun sanar mawa amma shiru,tunda mukaji kana Minna yasa mukataho tundaga legas dan sanar dakai komi” Matar da idonta yaciko da kwalla tace “Barrister shekaran yata 16 kacal a duniya,dan Allah ka taimake mu ka nemo mana ita” takarasa maganan bakinta na rawa, B ya sauke ajiyan zuciya yace “am sorry but aikin polisawa ne neman wanda yabata baniba… Da sauri matar tace “Barrister ni nasan wani abu akaima yata amma Alhaji yaki yarda,inaji ajikina wlh batun yauba dan Rufaida banda makaran babu inda take zuwa”, Alhaji ya kalleta yace “zaki farako” tafashe da kuka sosai B ya saukar da kanshi kasa dan ya tsani yaga manya na kuka, Alhaji yace ” Barrister wato tanada abokiyan zama ne,sai jiya taji abokiyan zaman tana waya tana fadin suda ganinta har abada wlh tariga ta shiga duniya kaman yanda tsuntsun ya shiga duniya… Shine fa tunda taji take cewa itace tama yarta wani abu ta bace” B yadade yana nazarin zancen, daga bisani ya kalle matar yarasa dawani suna zai kirata sai kawai yace “Umma” ta dago tace “naam Dana” yace “zanyi nazari,zan kuma nemeku akaro na biyu in sha Allah yarku takusa bayyana”, ya yagi wata paper yace “gashi komi kan yarku Ku rubutamin, nadaga shekarun ta, yanayin ta,makaran ta datayi kawayen ta dadai komi” Alhaji shiya rubuta sanan yabashi ya karba, Alhaji ya yaga check yarubuta kudi mai yawa ya mika mai B ya girgiza kai yace “ganinta shine farko kafin payment Alhaji nabarku lpy” yarakasu suka shiga mota matar nata godemai tana yaba halinshi na kirki saida sukabar haraban hotel din sanan yakoma ciki, dakin yarinyar daya tsinta ya wuce kai tsaye dan duba lafiyarta.

Tsayawa yayi akanta yana kallonta, ansa mata Karin ruwa ga bandeji a goshi, sai ciwukan jikin ta da hanunta an wanke su,tai wani fayau da ita tai haske kaman Mara jini. Murmushi yadanyi tunawa da duk inbaida lafiya Mum na zama taita Karanta mishi English novels masu dadi tun yana Yaro,duk in yatambayeta maisa takeyi mai haka in baida lafiya, saita cema Karanta ma Mara lafiya stories yana sa ya warke da wuri. Murmushi yadan karayi yace ” O mother I missed yhu dayawa dayawa” yace “nima bari na karantama dis little lady stories, yadan tabe baki yace who knows maybe itama ta warke da wuri takoma wurin iyayenta dan anywhere dey are suna nemanta suma” yajuya dan zuwa dakinshi ya dauko novel ya karanta ma yarinyar haryasa hannu zai bude kofa yafita yaji tana magana” Mami tsuntsun mai dago baki yana Jana,zai tafi…Mami dani zai tafi…Mamina “.

Maman Abd Shakur😘
[4/26, 9:02 PM] Aishat Muhammad: 🖌KAINE SIRRI NA🖌

4
Dawowa cikin dakin yay ya tsaya gaban gadon, addu’oi ya tofa mata saiyaji tai shiru ta sauke ijiyan zuciya ta cigaba da bacci. Ya tsaya akanta nadan sakonni sanan ya juya yabar dakin. ya dauko novel yana karanta mata a natse.

Karfe 10 na safiyan washegarin ta farka da addu’a a bakinta,ahankali take bude ido bataga kowa a dakin ba, sai wani bakin akwati a gefen gadon,da katon littafi akan drawer, mikewa tayi tadan zauna dudda batajin karfi ko daya a jikinta tana karema dakin kallo komi pink. ruwan dataga yanabin hanunta ta cizge tareda wata yar Kara “wayyo umma zafi” fadin sunan Umma yasa ta tuna da sun rasu fa yanzu, ta fashe da matsanancin kuka.

Tsagaitawa tai da kukan tafara kalle-kallen dakin “to ina nake? Inane nan?wanan hadadden daki fa?” Dakyar ta tashi tsaye taje gaban kofan data gani tana jijjigawa amma taji arufe bayama girgiza,zama tayi a wurin ta dasa sabon kuka na rashin iyayenta,masu sonta,masu walahan neman kudi dan suga tai karatu,wayanda suka mutu ta sanadiyya ta tafashe da wani kukan toni maisa ban mutuba, banda kowa banda DUDUWA.

Haka tacigaba da kuka sai Wuraren sha biyu sanan ta share hawayen, ta mike tsaye tana neman makewaya dan fitsari takeji sosai, ganin wani kofa yasa tafada ciki takoga bayine batasha wahalan bude shawan ba saboda inda Abba yasamu aiki irin bayinne a wurin, wanka tayi tai brush ta wanke kayan data cire, sanan ta daura sabon towel din data gani tafito tana dingisawa, akwatin kayan data gani gefen gadon tabude, kaya tagani aciki kala biyu da hijabi baki, daguwan rigan ciki ta dauka tasa tadau hijabin tasa ta kabbara salla, da kyar take sallan saboda jirin datake gani, tana idarwa ta tashi zata koma gado, saidai tana mikewa ta zube a tsakar dakin saboda jirin daya dibeta, adaidai lokacin ya bude dakin da sauri ya shigo yana sanye da kayan Shan iska yakaraso da ya dagata ya daurata kan gado. Juyo da fuskanta tayi dan taga Wanda taji yadaga ta, idanuwanta suka sauka kan kakkyawan namiji, shiba saurayi ba shikuma ba Babban mutum ba,farine tarr kana ganinshi kasan akwai jinin bature tattare dashi,idanunshi dauke da farin glas maikama Dana masu ciwon ido.

Dago kanshi keda wuya sai idanunsu suka hade, kulle idonta tayi da sauri ta kankame jikinta ganin yanda yacika mata ido,dakuma yanda kwayar idonshi ke bata tsoro.

Baice mata komiba,ya komar da kanshi ga wayan dayake dannawa. Bude kofa taji anyi, saikuma taji ance thanks Johnson, saitakara jin an bude kofa anfita. kara kankame jikinta da idanunta tayi dan tsoron shi taji Allah ya saukar mata shikenan gidan yan yankan kai! Cikin natsatsiyar murya taji ance “tashi kici abinci”, ko motsi batayi ba, takarayin lamo, ahankali yakai hanunshi bakin katifar yadan bubbuga ” Hi tashi kici abinci ” da sauri ta tashi zaune ta bude idanunta ahankali ganin abinci tayi agabanta mai rai da lafiya,tea mai kauri saikuma faten wake dake dauke da hanta da green vegetable sai aka zuba soyayyen plantain a sama,Satan kallonshi tadanyi taga news paper yake Karantawa. zamo jikinta tayi ta zauna akasa dan ita ko agida saidai Umma a Abba su zauna a dining ita akasa takeci, data zauna ta sauko da Trey din abincin a gabanta, tadau tea din tafara sha harta shanye tass, sanan ta jawo faten waken tana wasa dashi, tun tana yar karama batacin wake, sai kallon waken take ita bataci ba ita batai magana ba,bude kofa taji anyi an shigo yace “gani sir” batareda ya kalleshi ba yace “take d Beans away,ka kawo mata wani abinci batacin beans” da sauri ta kalleshi saikuma ta sauke kanta tana mamaki ya akayi yasan batacin wake?

Maman Abd Shakur😘
[4/27, 9:30 PM] Aishat Muhammad: [4/27, 8:35 PM] Aishat Muhammad: 🖌KAINE SIRRI NA🖌

5
Shinkafa Johnson ya kawo mata ta karba tadanci kadan tasha ruwa ta tura gefe taci gaba da wasa da yatsunta. kaman daga sama taji yace” kina bukatan wani abu kuma” girgiza mai kai tayi, bai Kara cemata komiba yacigaba da karatun news paper dayake yi.

Karfe 6 ya linke newspaper ya kalleta yaga har yanzu tana zaune a kasa da zumbulelen hijabin tai wani iri kaman marainiya, tausayi kawai yaji tabashi yakaraso gaban gadon ya tsugunna kusa da ita da sauri ta kulle idonta gam, dan murmushi yayi sanan yace “ya sunanki?” Batace komiba, akaro na biyu yace “bude idonki” ahankali take budesu tadan kalleshi ganin ita yake kallo yasa ta kauda kanta ta kalli gefe, hannunshi ya daura akanta ya juyo da fuskanta suka fuskanci juna yace”I said ya sunanki?”

Kukan datake kokarin hadiyewa ya kufce mata ta fashe da kuka sosai ko ina na jikinta na rawa,ganin haka yasa yacire hanunshi daga kanta yadan ja baya. a natse yay magana ganin ta tsorata dashine”Hi am not going to hurt yhu, taimakon ki zanyi karki tsorata dani kinji? dazaran kin warware zan maidake,don’t be afraid of me” shiru yadanyi ganin ta tsagaita kukan tana share jajayen idanunta tana kallonshi adan firgice,yakara kwantar da murya irin na lallaba wanda ya tsorata yace ” ki kwantar da hankalin ki kinji,zanje masallaci kinason na siyo miki wani idan zan dawo?” Ta girgiza kai tana share hawaye, yace “ok,oya tashi kije kiyi sallan kema” da sauri ta mike kaman jira take tayi hanyar bathroom tana kallonshi kaman zaibita kumm! ta bige kanta da kofan bayi garin kallonshi rike goshin tayi ta shiga bayi da sauri ta Danna key. Girgiza kanshi yay yatashi yafita daga dakin.

Bayan sallan isha ya bude kofa ya shigo dakin tana zaune kan dadduma da sauri ta mike tsaye ta make ajikin bango, ajiye abunda ya shigo dashi yayi yajuya yafita daga dakin. sauke ajiyan zuciya tayi sanan tacire hijabin jikinta ta zauna abakin gado ta bude ledan, lemun kwali ne da kaza,dayan ledan kuma chocolates ne da cingums, ajiyesu kawai tayi tafada kan gadon ita kadai tasan yanda takeji.

Maman Abd Shakur😘
[4/27, 9:28 PM] Aishat Muhammad: 🖌KAINE SIRRI NA🖌

6
Kwananta uku tana jinya harta warke tai ras,tsawon kwana ukun nan magana baitaba hadata da mai gilashi ba( sunan data rada mishi) saidai abunda tagane game dashi “mutum ne mai tausayi gashi da lallaba Mara lpy, kullum haka yake riritata yana tambayan metakeso yakawo mata,kayan kwalama kala kala yake kawo mata kaman baby, amma bazata taba bashi amsaba, yacika tausayi danta lura ya tsani yaga tana kuka. Itadai har yanzu mai gilashi tsoro yake bata saisa ko eh bai taba hadata dashiba baitabajin ya muryarta takeba”.

Tana cikin tunani taji anbude kofa, da sauri ta gyara hijabin jikinta, kallonta yadan yi wani abu yadan gitta zuciyarshi me yar yarinyar nan ke nufi? Maisa duk lokacin dazata ganni sai tawani sa hijabi? Mezanyi da ita? Mezan gani? Metake dashi? Abun yadan batamai rai amma saiya basar yakaraso ya zauna akan kujera. kanta na kasa yace ” petient naga kin warke ko?” Ta girgiza kai,yace “to Alhamdulillah, inaso nasa a komar dake gidanku ne dama saboda nasan duk inda iyayenki suke suna neman ki, and also maiya faru dake harna ganki a wurin nan a sume?”

Dago kai tayi zatai magana saitaga ita yake kallo. kaman kullum jikinta yahau bari ta fashe da kuka, kuma takasa daina kallonshi, mamaki take bashi wai yarinyar nan is she alright, anya batada matsala, da sauri yadan ja kujeran shi ya matso kusa da gadon ahankali yace “ke kurma ce?” Da sauri ta dagamai kai, tausayin ta yaji sosai yace “to ai basaikinyi kuka ba idan namiki magana kinji?” ta girgiza kai, yace “to share hawayen ki” ta share da gefen hijabin jikinta, “Kinyi iya rubutu?”

Please Login or Register in order to submit comment