Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

MUSABBABI.

NA

HAJ. HABIBA ABUBAKAR IMAM

https://youtube.com/@HabibaAbubakarImam?si=H7yQptZbm29jaY6x


Page 1

Fateema Mahmud wacce aka fi sani da Afrah,
a sakamakon sunan kakarta ta wajen uba da
ta ci, nagartacciyar yarinya ce, kyakyawa
haifaffiyar garin Minna.
Mai cikar kamala, hakuri, juriya, sune
manyan halayenta na-gari abin koyi, sai kuma
tsantsar ilimin Islama da Allah ya wadata ta da shi,
domin tun tasowarta take kokarin koyon addininta,
har zuwa yanzu da ta mallaki hankalin kanta.
Ta zama cikakkiyar mace, domin tuni
ta
kammala karatunta na sakandire, tana zaman jiran
sakamako ne a yanzu. Idan akwai abinda ya ragi
Afrah a rayuwarta.
To ba zai wuce maraicin rashin uwa ba,
domin ta dandani dacin maraici tun tana
'yar
shekara biyu, kuma ita ce kadai
'yar da
mahaifiyarta ta haifa tare da mahaifinta Malam
Mahmud.
Bayan rasuwar mahaifiyarta ne, rikonta ya
koma hannun matar Babanta. Mama Hauwa, wacce
a matsayinta na uwargidan Malam Mahmud, tana
da yayyi guda biyar biyu maza, Mansur wanda shi

Page 2
ne na farko, a yanzu ma'aikaci ne a hukumar wutar
lantarki, wato (NEPA).
Yana rife da babban mukami, ya yi aure har
da 'Yarsa daya, sai Kabir, shi kuma ma'aikacin
banki ne, shi bai wuce watanni uku da aure ba, sai
Naja"atu da Sakina, su ma duk sun yi aure. Na'ima
ce ta rage, wacce take tsarar Afrah, duk tare suka
kammala makaranta.
Sai dai abu daya da Afrah ta rasa a gidan
mahaifinta, shine kulawa da kowace
"Ya take samu
na uwa, domin irin rikon da Mama Hauwa ke mata,
ba irin riko bane na amana.
Wanda maraya ya kamata ya samu ba'a
kowane mataki. Mama Hauwa na nuna bambanci
kiri-Kiri tsakanin Afrah da 'ya' yan ta,
Ko kadan ba ta kyautata mata, rayuwa take a
gidan tamkar ba
"yar gidan ba, duk da Malam
Mahmud yana iya kokarin sa domin ganin marainiyar
'Yarsa ta samu riko me kyau daga
Mama Hauwa.
Amma hakan ya kasa tabbata, domin Mama
Hauwa ta zama tamkar tauraruwa me wutsiya,
domin shi kansa Malam Mahmud din ta fi karfinsa,
ta kan yi duk abinda ta ga dama ko a gaban idonsa
ko a bayan idonsa.
Inna Halima wacce ita kadai ce kanwar
Malam Mahmud. kuma ita kadai ce take iya

Page 3
takama Mama Hauwa birki akan irin mugun rikon da take ma Afrah
Hakanne ma ya sa, kusan rabin rayuwar Afrah
take yi a gidan Inna Halima, domin duka ranar
juma'a. Can take tafiya, sai ranar lahadi take
dawowa gida, wannan dalilin ya sa Mama Hauwa
da Inna Halima ba sa shiri ko kadan.
Makarantar Islamiyyar da Afrah take yi, anan
kuma take koyar
da kananan yara, saboda
hazakarta. Ya Sayyadinsu Habib ya maida ita
Malama, a ajin haddar Kur' ani ta kananan yara,
tana daukarsu gun koyon Kur ani da Tauhid.
Malam Habib shine mutum na farko da Afrah
ta fara tsayawa da shi a matsayin masoyi, ta kuma
amshi tayin soyayyarsa, domin yarda da ta yi da
irin son da yake mata na tsakani da Allah da kuma
hanyar Ubangiji da yake doreta akai.
Hakan ya sa take da tabbacin cewa daga gare
shi za ta sami kyakkyawar rayuwa, ko ba kudì da
jin dadi, to idan har akwai Allah a cikin rayuwarsu,
to ya ishesu daga dukkan komai, don haka ta tsayar
da zuciyarta gun mutum daya, wato Ya Sayyadinta Habibu.

Page 3

Yau asabar ne Afrah tana gidan Inna Halima, yau
gyara take mata na gidan gaba daya. Inna Halima
tana gefe a zaune, duk inda Afrah ta yi, tana bin ta da
kallo, tana matukar sha'awar yarinyar da halayenta,
domin duk inda ake neman yarinya me hankali
wacce ta rike maraicinta, aka sami Afrah, to an wuce wajen.
Tana matukar jindadin kasancewa da Afrah, a
duk sanda ta zo gidanta, ta daina aikin komai,
duk abinda za ta yi Afrah, ta kan dauke mata, hatta girki
ba ta yi, ta kan dauke mata komai.
Inna Halima. na tsaka da yin wannan tunani
aka bugo kofa da Karfi. Musaddik ya fado cikin
gidan, tamkar wanda aka jefo ba tare da sallama ba, Inna Halima ta mike tana kallonsa

'Musaddik". Ta Ambaci sunansa da karfi, a yayin
da Afrah ta yi saurin ja da baya, domin kar ya
bugeta.

Musaddik nagartacce,kuma kyakkyawan
matashi. wanda ya hada komai da za ka iya kiransa
da jarumin matashi, sai dai kallo daya za ka yi
masa.
Ka san ya rasa wani ginshiki na rayuwarsa,
wanda ya hana shi damar da za'a kira shi da
mutumin kirki, ba shi da natsuwa, da ganinsa ka
ga wanda ya yi nisa a shaye-shaye, ko a yanzu ba'a cikin hayyacinsa ya ke ba.

Page 4

"Inna abinci na ke so,yunwa nake ji” ya fada da wata irin budaddiyar murya
Inna Halima ta yi ajiyar zuciya,
sannan ta kalli Afrah ta ce
"'Afrah aje tsintsiyar nan,
ki zubo ma yayanki abinci.”

A hankali ta yi kasa da
tsintsiyar, sannan a sanyaye ta wuce kicin.
Inna Halima ta maida kallonta ga Musaddik,
wanda yake tsaye ya nannade kafafun wando
tace "Zo ka zauna"
Ta nuna masa tabarmar da ke shimfide, ya
wuce da takalmi da komai ya zauna akan tabarmar,
ba ta damu ba, domin ba yau ya saba yin hakan ba,
ta ja kujerar da ta tashi akai, ta koma ta zauna tana
kallonsa. Tana saka abubuwa da dama a ranta.
•Har zuwa lokacin da Afrah ta dawo dauke da
faranti cike da shinkafa da miya da ta dafa,a
hankali ta aje a gabansa, sannan ta juya ta wuce
Zuciyarta cike da tsananin tausayin Musaddik da
halin da yake ciki. Musaddik yace
"Inna na kan so na zo cin abinci gidanki duk
ranar sati, saboda na san Afrah tana gidan nan, ina jindadin abincinta, komai rashin gyaransa”
Maganar Musaddik ta katse mata tunani da take
yi ta juyo da idonta tana kallon sa, a yayin da Inna Halima ta jinjina kai tace

Page 5
"Ba kai kadai ke jin dadin girkin Afrah ba,
kowa yana yabawa, tun daga kan yara har zuwa
maigidan kansa.”
Ya yi dan murmushi, a yayin .da yake cin
abincin, ya dan waiwayi inda Afrah take wacce
Ke cigaba da karasa shara ya ce,
"Haka ne Inna, shi ya sa ni ma
na kan kwaso yunwata zuwa gidanki.
Don na san idan na ce kwadayin girkinta zai
dinga kai ni gidansu kullum, za mu sami matsala
da Mama Hauwa, don na san farantina ba zai
dinga cika ba kamar yadda yake cika a gidanki."
Gaba daya suka yi murmushi, a yayin da ya
maida hankali kan cin abincinsa. Inna Halima kuma
tana zube masa da ido, tana matukar tausayin
Musaddik da kuma rayuwarsa wacce bata taba
tsammanin zai koma haka ba. Duk tsananin
Kamun kansa ilimi da cikar kamalarsa.
Amma rana tsaka rayuwarsa ta koma haka. a
lokacin da ya kamata ace rayuwarsa ta inganta,
babu wanda zai ga Musaddik ya yarda ya kuma
amince Musaddik din da ne, lamarin yana da
matukar daure kai.
Inna Halima ta yi kasa da murya à hankali, ta
fara yi masa magana "Musaddik, anya ka na ganin
wannan rayuwar da ka dora ma kanka za ta kai
ka ga hanya madaidaiciya, wannan wace irin rayuwa ce?
Da mutuncinka da darajarka, rana tsaka duk ka
kore wannan, ka koma ka na Kaskantarciyar

Ku dakace ni

YAR GIDAN IMAM

bazan yarda da rashin yin comments ba don wallahi ina iya barin yin posting din idan bakwa comments.
MUSABBABI

NA

HAJ HABIBA ABUBAKAR IMAM


https://youtube.com/@HabibaAbubakarImam?si=8hYIJhGWi10v_gOI

Page 6
rayuwa mara dadin ji ko gani, shin meye dadin
wannan rayuwar?
A hankali Musaddik ya cire cokali a cikin
abincin, fuskarsa gaba daya duk ta canza ya
shiga cikin damuwa, ya ce a sanyaye,
"Inna babu wani
dadi ga rayuwar da na ke ciki, hakia inda ina da
ikon canja hanyar da na biyo, da na yi gaggawa
na canja, domin ko kadan ban jin dadin rayuwar.
Amma na rasa dalilin da ya sa na kasa yaki da
zuciyata na daina, duk da ina kyamar abinda na
Ke aikatawa ni ma,”

Inna Halima ta jinjina kai fuska cike da
tausayinsa tace
"Ka yi yaki da zuciyarka ne, ka
dage ka kori shaidan, domin hakika shine yake yi
maka huduba, ka tuna irin gata da arziki da ka taso a ciki Musaddik kayi tunanin irin girma da
kamalarka da dubban jama' a suke gani a da, sannan
ka tuna irin ilimi da hangen nesa da ka ke da shi
wanda a yanzu duk sun tattara sun gudu, a
sanadiyyar tsarin rayuwarka da ka canja, ka duba ka
ga yadda ka maida kanka, hakika lamarinka na
damun mu, yana kuma daure mana kai kwarai da gaske
Afrah da ke tsaye gaba daya sai ta juyo ta dora
ma Musaddik idanunta wadanda suka cika da
hawaye, zahiri tana daya daga cikin wadanda
lamarin yayanta Musaddik ke damu, ta kan shiga

Page 7
dimbin damuwa da tunani idan ta tuna halin da
yake ciki, Sannan ta kan rasa inda zata sa kanta, idan ta
kasa gane dalilin canjawar Musaddik, mutumin
da ya taso da nagarta, kamala, natsuwa, ilimi da
matukar hangen nesa, tana daya daga cikin
wadanda rayuwar Musaddik ke matukar burgewa.
Yana matukar ba ta sha'awa, rayuwarsa da
yadda yake tafiyar da lamuransa, abin a tsaya a
kalla ne a kuma yi koyi da su.amma meya kawo wannan canjin?.
"Inna kada ku gaji,
ku yi ta tayani da addu'a don Allah".
Furucinsa ya Kara dasa tausayinsa a zuciyar
Afrah. Inna Halima ta ce
"Addu'a muna nan muna
yi Musaddik. Allah ya shiryeka, ya dawo da kai
hanya madaidaiciya, ba za mu gaji da yi maka
addu'a ba."
Ya gyada kai ya ce
"Na gode Inna, bari na tafi” inna Halima tace
"Ka karasa cin abincin mana”
Ya girgiza kai lokaci daya yana mikewa.
"Na koshi Inna, na gode.” Ya juya ya dubi Afrah
Yace "Na gode da girki,." Yana gama fadin haka, ya juya da sauri ya fice.
Inna Halima ta numfasa cike da damuwa tace
"Allah ka yi
mana maganin abinda ya fi karfinmu."
Afrah ta amsa da "Amin."Sannan ta juya ta ci-gaba da aikinta,amma zuciyarta na cike da
tunanin Musaddik da tausayinsa, domin ta san hakika yana bukatar taimakon addau'a, ta kuma kara shan alwashin

Page 8
za ta ninka akan addu'ar da take yi masa
Haka ta kasance cikin tunaninsa da tausayinsa
a wannan ranar kamar yadda ta saba a duk lokacin da suka hadu da juna.
Washegarin lahadi. Inna Halima sai dare, sannan
ta sa Afrah a gaba zuwa gida, domin tana son
ganin Dan’uwanta Malam Mahmud, hira suke yi a
hanya har suka isa gida. Dawowar Mallam Mahmud kenan
daga masallaci sallar Issha"i, fuskarsa ta fadada
da fara' a yana kallon "Yar-uwarsa, ya ce.
"'Halima, ai na dauka "yar ta ki sai gobe za ta
dawo, da na ga dare ya rufa? “ Ta yi murmushi,
tace “a’a yaya. Na ce ta jirani ne mu taho tare,
saboda ina son ganinka, na san kuma iyanzu ne zan sameka a gida a tsanake”
Ta karasa maganar tana zama a kan
tabarmar da yake zaune akai.
A yayin da Afrah ta durkusa ta gaishe shi,
Cike da so da Kauna ya amsa mata, sannan ta
wuce dakin Mama Hauwa, domin ta gaida ta, amma haka nan
ta amsa ba yabo ba fallasa fuska a hade,
Na'ima ko tana kwance akan gado ko kallonta ba ta yi ba harta fice ta shige dakinta.

Mallam Muhmud ya dawo da kallonsa ga Inna
Halima bayan sun gama gaisawa, sannan ya ce
“Halima ina fatan dai lafiya ki ke son ganina, da
daddaren nan?"' Inna Halima ta gyara zamanta

Page 9
Tace “Yaya ba wani abu bane dama magana ce na ke son
mu yi akan Musaddik".
Mallam Mahmud ya jinjina kai ya ce
"Ya kara dakko wata maganar ne?”
Ta girgiza kai Ta ce
"*A'a, babu abinda ya yi, kawai dai wani tunani na yi akan halin da yake ciki,
wanda yaya ka fi kowa sanin duk duniyar nan.
Mu ke nan mu uku iyayen mu suka haifa, daga kai sai marigayiya Harirah mahaifiyar musaddik sai kuma ni, yadda ba za mu so mu ga 'ya ' yan
da muka haifa cikin wata fitina ba.
Haka shi ma. Musaddik ba shi da kowa duk
duniyar nan sai mu, kuma mu kadai ne ba za mu
juri ganinsa cikin wani hali ba, don ina da
tabbacin da mahaifiyar sa ce take a matsayinmu.
Ita ma sai inda karfinta ya kare akan
'ya yan
mu, shi kadai ta haifa a duniya kuma shine
sanyin idaniyarta, don haka duk yadda za mu yi, ya zama
dole a kanmu mu yi kokarin daidaita rayuwarsa.
Malam Mahmud ya numfasa, damuwarsa ta
Kara fitowa fili. Ya ce "Halima kin fi kowa sanin
duk duniya ba ni da wata damuwa da ta wuce
-damuwar Musaddik.ina cikin tsananin tashin hankali akan rayuwar da yake yi, ina kuma takaicin yadda na kasa
taimakonsa akan ya natsu, babu kuma abinda ba zan yi masa ba,matukar zai shiryu domin ba ni da wani burin da ya wuce haka, duk addu’ata akan musaddik take karewa Halima”.

Ku dakace ni

YAR GIDAN IMAM

Bazan yarda da rashin comments ba don wallahi zan iya daina posting din idan bakwa yin comments.
MUSABBABI

Na

HAJ HABIBA ABUBAKAR IMAM

https://youtube.com/@HabibaAbubakarImam?si=z2twfJh8yZkWrt_r


Page10
Inna Halima ta numfasa gami da gyara zamanta ta ce "Ni Yaya akwai hanyar da
na ke ganin wata Kila zai iya zama sanadiyar
shiryuwarsa". Mallam Mahmud yana kallonta
yace “Wace hanya ce wannan?”
Ta dan muskuta tana kallonsa sosai sannan
tace “Aure, yi ma Musaddik aure ina ganin zai iya
zama wata hanya ta samun nutsuwarsa, domin
duk rashin jin namiji , idan ya yi aure ko yaya ne
akan samu sauki, ko bai daina abinda yake yi duka ba,
zai rage". Mallam Mahmud ya ce.
"Haka me, aure hanya ce ta samun natsuwa,
zai kuma iya canja wa rayuwarsa tsari, amma ba anan gizo ke sakar ba, wacece
za ta aure shi, kada ki manta a dalilin halinsa ya
rabu da matarsa, sannan tun daga lokacin babu
wata da ta karav sauraronsa, saboda ba shi da natsuwa, to yanzu ina zai samo mata shi da ko lokacin kansa baida shi balle lokacin wata, wace ce za ta yarda da shi har
ta aure shi a haka?" Inna Halima Ta ce.
"Tabbas! Abinda kamar wuya, samun me
auransa,
domin kowace mace burinta ta sami
kintsattsen
namiji. Domin ta samu kwanciyar
hankali a gidan auranta, don haka yaya ya
zamar mana dole mu yi sadaukarwa saboda zumunci.?”
Malam Mahmud ya dubeta cikin rashin fahimta
Yace “Sadaukarwa? ban fahimce ki ba”Inna
Halima ta ce
"Ina nufin dole a cikin 'ya' yan mu mu
sadaukar da daya ga Musaddik ya aura, mu yi aikin zumunci”,
Ta gyara zamanta fuskarta ta canja
alamun damuwa ta ce.

Page 11
"Ban taba jin ciwon ba ni da ya mace ba irin yau, amma ko'ina da 'ya macen ma,
yaya ka san, babu aure tsakaninta da Musaddik
tunda Musaddik ya riga ya sha nono na, amma
yaya me ka gani akan shawarata?"
Mallam Mahmud ya dubeta ya ce "Shawararki
ta yi, abar kuma dubawa ce, kuma kada ki kara
tunanin ba ki da 'ya mace, domin 'yayana naki
ne haka zalika hada Musaddik aure da yar’uwar
shi kadai ya kamata, domin 'yar-uwarsa ita kadai
ce zata rufa masa asiri, za kuma ta yi hakurin zama da shi”.
Inna Halima Ta ce "'Haka ne". Ya ce "Saboda
haka, zan hada shi da Na'ima, tunda ita ce gaba
da Afrah, Inna Halima ta yi murmushi sosai.
tace “Allah ya saka da alheri ya kara dankon zumunci, yasa sanadiyyar shiryuwarsa ce”
Yace "Haba Halima wannan duk yi ma kai ne, na
kuma gode da wannan tunanin naki, wanda ni
ban yi irinsa ba, na kuma ba ki damar ki yi magana da
Musaddik ki gaya masa hukuncin da muka yanke"
Ta ce “In sha Allahu zan yi magana da shi."
Daga nan suka ci-gaba da tattaunawa na dan
wani lokaci kafin su yi sallama ta tafi, ba tare da
sun gaisa da Mama Hauwa ba, yadda ba ta fito
sun gaisa ba, haka nan ita ma ba ta bita daki sun gaisa
ba, dama sun saba yin hakan.

Page 12
Washegari bayan sallar azahar, Afrah na zaune
tana wanke-wanke. Na'ima kuwa dawowarta
kenan daga gidan kitso, tann zaune akan kujera
Yar tsuguno tana latse-latsen waya. Mallam Mahmud ya yi sallama ya shigo.
ya dawo daga masallaci, cike
da tausayawa ya dubi A frah ya ce.
"Sannu da kokari, har yanzu ba ki samu hutawa
ba, kin yi sallah dai ko?" Ta amsa “Na yi sallah
Baba” ya jinjina kai zai wuce “Sannu da zuwa”
Cewar Ni'ima, ya dubeta
fuska tamke ya ce.
"Yauwa, ke ba kya aikin komai ne?" Kafin ta
yi magana Mama Hauwa ta cafke a lokacin da ta
Ke fitowa daga daki "Ta gama nata, ko shi ma aikin sai ansa ido a kansa?”
Bai Kara magana ba har ya isa kofar dakinsa,
sannan ya Kwala ma Mama Hauwa kira, kai tsaye ta
nufo inda yake ba tare da ta amsa ba. "Ga-ni”
ya dubeta gami da girgiza kai sannan ya ce.
"Ba ni abin zama, magana za muyi me muhimmanci”
Nan ma ba ta amsa
ba, ta shige ta dauko. tabarma ta shimfida masa ya zauna, ita kuma ta jingine jikin katanga tana
kallonsa.
"Wace magana za mu yi?" Ya ce a yayin
da yake kallonta
"Ina bukatar natsuwarki, domin
magana za mu yi kamar yadda na gaya miki kuma me muhimmanci ce maganar” tace
"To ai ina jinka." Yace “Dama maganar
Na'ima ne, ina ganin lokaci ya yi daya kamata

Page 13
ace ta yi aure, don haka na yanke shawarar ni da
Halima akan zan hada ta aure da Musaddik”,
Haka nan Afrah ta ji gabanta ya fadì, wanda ta
rasa dalilin hakan, sai dai ta ji ta sami kanta da
matukar tausayin
"yar-uwarta, duk da ba wani shiri
suke yi ba, amma ya zama dole ta tausaya mata,
domin ta san auren miji irin Musaddik hakika
rashin dace ne ga ko wace ya mace.
Mama Hauwa ta zaro idanu waje, tamkar za
su fado kasa, bakinta na tsuma ta ce
"Wane Musaddik din?” Yana kallonta yace
"Musaddik din har nawa
garemu? Musaddik dai nawa mana”
Mama Hauwa ta saki salati tana tafa hannu,
Tace “Eh, sai yau na kara tabbatar da cewa Malam baka son yayana,sannan Halima ba zata taba barina na zauna lafiya ba, yau ko maza sun kare kaf a duniya.
Me Na'ima za ta yi da Musaddik? Sakaran
yaro mara natsuwa, babu wanda bai san halin
da yake ciki ba na barbada, da can sanda yake
na kwarai me ya, sa ba ka yi tunanin hada shi auran da
"yarka ba, sai yanzu daya zama lalatacce.
Sanda yake da kumbar susa yake shiga mota
yana fita, ai ba ka ce za ka ba shi 'yarka ba, duk
da a lokacin har tayin Sakina na yi maka, akan ya aureta
Ka ce ya riga ya sami mata, ba kuma zaka tursasa masa ba, yanzu ina matar,
halinsa ya koreta, ya zama shakulatin bangaro,

Page 14
sai da ya zama mara amfani shine za ka ce Na'ima ta
aure shi, to ba ka isa ba."
Malam Mahmud ya nuna kansa ya ce "Ban isa
ba a matsayina na ubanta?" Ta turo baki. "Eh, in
dai akan wannan maganar ne ba ka isa ba, kada ma ka kara
furtawa. Na'ima ta fi karfin Musaddik, ko shi ne
autan maza ba za ta aure shi ba."
Mallam Mahmud ya fusata ya ce. "To zan ga
wanda ke da iko da ita tsakanin ni da ke, domin
na riga na gama magana, na ba Musaddik Na'ima.”
Mama Hauwa ita ma ta fusata, bakinta na kumfar masifa tace
"To za mu ji, za mu gani, wai an binne
tsohuwa da rai, domin in dai ina raye Na'ima ba
zata auri wannan tambadaddan yaron ba, aniyarku duk zata bi ku kai da Haliman”
Ta juya fuuu! Ta tafi. Malam Mahmud ya
tashi ya bude dakinsa ya shiga cike da matukar
bacin rai. A yayin da Na'ima ta saki tsaki ta mike
tana turo baki, tana kallon Mama Hauwa "Allah
Ya yi min tsari da wannan mutumin, lallai babu kauna tsakanina da Baba”,
Mama Hauwa ta yi tsaki ita ma ta ce "In dai
kauna ce, ai baya kaunarmu gaba daya.
Musaddik din me. Allah ya tsari gatari da saran
Shuka, wuce ki shiga daki”
Na"ima ta shige daki
tana surutai na rashin tarbiyya da ilimi.
Haka Mama Hauwa ta wuni a cikin gidan tana
sababi, wanda duk akan Afrah ya kare.

Ku dakace ni

YAR GIDAN IMAM

Bayan yarda da rashin comments ba, wallahi ina iya daina posting din idan ba zaku dinga yin comments ba.
MUSABBABI

NA

HAJ HABIBA ABUBAKAR IMAM


https://youtube.com/@HabibaAbubakarImam?si=6OcF1jmDVM1SQHTK

Page 15

harara da hantara da sa aiki duk Afrah ta sha su a ranar,
don dai Mallam Mahmud ya tanka, ta kara juye
kwandon masifarta a kansa, duk dalilin haushin
hukuncin daya yanke akan Na'ima,

A yayin da Inna Halima a ranar dai ta nemo
Musaddik ta zauna da shi, ta yi masa bayanin
duk hukuncin da suka yanke a kansa. Musaddik
ya mumfasa gami da kallon Inna Halima.
Sannan ya ce "Anya Inna ki na ganin Mama
Hauwa za ta amince da wannan maganar, idan

akayi la'akari da abinda ya faru a baya
a game da sakina kuma ki na ganin ita kanta Na'ima za ta yarda ta
aureni, a halin da na ke ciki a yanzu?" Inna Halima ta gyara zama cike da damuwa tace
"Wannan duk ba damuwarka bace, kawai kai
ma na gaya maka ne saboda ka sani, ba don mu
zauna muna tattaunawa ba, abinda muka yanke kenan saboda wannan halin da kake yi ya na neman ya tagayyara duk kan tunanin mu, muna tunanin kuma wannan hanyar itace kadai zata iya taimakon mu dawo da kai hanya madaidaiciya, don haka babu ruwanka da abinda Hauwa zata yi, tunda Na’ima ba yarta bace ita kadai ba”. Ya gyada kai fuska cike da jimamin wai yau shine ake nema masa matar aure sabida babu wacce zata iya da shi, idan ya tuna yadda mata ke turo kansu a da wajensa, yakan ji komai ya tsaya masa a rai. A hankali
Yace “Shi kenan Inna. Allah ya yi mana zabin abinda ya fi zama alheri, nagode da kokarinku a gare ni”

Ta jinjina kai, cike da karin tausayinsa ta ce
“Amin Allah kuma ya sa sanadiyya ce ta shiryuwarka, Allah ya rabaka da wannan
'mummunan halin, ya dawo maka da matsayinka na da “ Ya amsa a sanyaye, “Amin” sannan ta kara dubansa tace,
"Zuwa yau da daddare ko gobe ina son ka
bulla gidan Kawun naka, domin ka yi magana da
Na'ima ka kuma samu Kawun naka, ka yi masa
godiya tare da nuna masa amincewarka akan
hukuncin mu”
Yace “To zan yi kokarin yin hakan."ta zuba masa ido sosai tace “Musaddik yaushe rabonka da wanka? Ka ga kayan jikinka , me yasa kake kokarin maida kanka mahaukaci ne” shuru ya yi ya maida kansa kasa , ta aje numfashi tace

Please Login or Register in order to submit comment