Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da yake ciki, ko kadan ba na son a sami
wani canji a game da rayuwarsa a dalilin auransa". Ya yi dariya yace
"Wannan ai babu canji, ko na yi aiki akai ko
ban yi aiki akai ba, ba za'a samu wani canji ba.

Page 67

Zai ci-gaba da zama a halin da yake ciki, auransa ba zai canja shi da komai ba”
Hajiya Kilishi ta ce "Godiya na ke" ta balle
jaka ta fito da kudì ta mika masa, ya amsa yana
godiya gami da kara karfafa mata guiwa akan
lamarin Musaddik, daga nan suka yi masa sallama suka fito.

Har sai da Hajiya Kilishi ta fara tuka mota,
sannan Hajiya Rakiya ta dubeta ta ce
“Amma yarinyar da za ta auri Musaddik
mahaukaciya ce ko?" Hajiya Kilishi ta ce "Ko daya da hankalinta ras, tasan abinda take yi”

''To idan ba mahaukaciya ba, me za ta ci da
Musaddik, wane jindadì za ta samu daga gare
shi mutumin da ina ganin ko wanka ba ya yi,
Kullum yana wurin *yan daba yana shaye-shaye, yana kuma
yawon bangar siyasa, ko dai suna tunanin za su
sami kudi ne a hannunsa?"
Ta girgiza kai ta ce "Ubanta ya fi kowa sanin
Musaddik baida ragowar sisin kwabo, ni dai ban
'san dalilin da mahaifinta yake son hada wannan
auran ba da zai zama masifa da fitina ga yarsa
dama shi mutum ne me kafiyar tsiya, amma
'tabbas ba na son Musaddik ya auri *Yarsa Afrah"
Hajiya Rakiya ta dubeta ta ce
“To ki na ganin za mu gwada sa'ar wani wajen ne?" Ta girgiza kai
ta ce "A'a Hajiya. A gaskiya na yarda da aikin Mai Rakwacam, kin fi kowa sanin cewa

Page 68
duk shekarun nan, shine yake taimaka min, bai
taba yi min aiki na ga rashin sa' ar aikin ba.
Idan kuma abu ba zai yiwu ba, zai gaya min,
ba zai cin min kudi a banza ba, na kuma sha
gwada wani wajen, idan ya ce ba zai yiwu ba.
Haka nan za'a ci min kudi kuma babu biyan
bukata, shi ya sa yanzu idan ya gaya min abu ba
Zai yiwu ba, na kan hakura gaba daya na
rungumi kaddara, kamar yanzu da na saduda na hakura akan maganar auran nasu”
Ta nisa gami da hadiye yawu kafin ta ci-gaba
da magana. Hajiya Rakiya ta ce
“ kina da gaskiya, tunda kin yarda da shi, gara ki
aje hankalinki waje daya, domin tabbas ya iya aiki”, Haj kilishi cikin fuska me cike da bakinciki tace “Hakane, amma nayi alkawarin bazan taba barin Afrah ta samu kwanciyar hankali ba,dole zansa auran ya fita a ranta da kanta zata nemi wajen gudu in dai nice”, Haj Rakiya ta yi dariya tace “ kin ji ki da wata magana za ki bata ma kanki lokaci, dai kawai domin rashin
kwanciyar hankali, har ya wuce wanda mijinta
Zai sakata a ciki? Halinsa kadai ya isa ya sa ta
gudu ta bar shi, wa zai iya da Musaddik”
Hajiya Kilishi ta yi dariya ta ce
"Kai Hajiya Rakiya sai a barki, kuma fa hakane”
Gaba daya suka kwashe da
dariya . Sai dai fa ba haka Hajiya Kilishi ta so ba,
domin har cikin zuciyarta auran nan yana daya
daga cikin binda ta tsana a duniya, amma babu yadda za ta yi, tunda haka kaddara ta riga fata, sosai take jin tsanar Afrah a cikin zuciyarta da mallam mahmud.

Page 69

Ta Bangaren gidan Malam Mahmud kuwa shirye-
shiryen bikin Afrah da Musaddik ya kankama, ita
kuwa Na’ima tunda ta dawo gidan, take ma Allah
godiya daya gajarce mata wahalar auran.
Musaddik . Inna Halima da kanta ta sai ma Afrah
gado da katifa da sauran tarkacen kayan kicin.
Kudin kuma da su Kabir suka ba mahaifinsu
a matsayin gudunmuwa, su ne ya ba Inna Halima
ta sayo kujeru kayan kallo da firij har da keken
dinki da sauran duk kayan da ake bukata.
Duk da haka sai da kudin suka ragu, su ne ya
yi amfani da su ya sayi kayan abinci. Mama
Hauwa kuwa tunda ta fahimci Mansur da Kabir
ne suka bada makudan kudin sayayyar Afrah, ta
ji bakinciki kamar ya kasheta, don sai da ta
Kirasu ta yi masu kaca-kaca. Ta nuna masu matukar bacin ranta.

Shirye-shirye sun yi nisa, sun kankama, amma
ga Afrah, al'amarin ya fara ba ta tsoro , saboda
tun daga ranar da Musaddik ya zo gidansu suka
Yi magana, bai kara dawowa ba.
Ba shi, ba labarinsa, dan ko, ta je gidan Inna
Halima ranar juma'a har ta gama kwanakinta ta
dawo gida, ba zai zo ba. A zahiri abin yana
damunta, tana matukar son ta san halin da yake
ciki Ga shi ba ta san inda za ta same shi ba,
balle ta neme shi ta ji lafiyarsa. Haka zalika bata nuna damuwar komai a gaban kowa

Page 70

Musamman mahaifinta da Inna Halima, haka
Zalika ko yaushe tana samun karfin guiwa daga Ya Sayyadi Habib
tare da addu'o'"i, wadanda a yanzu su Afrah ta
rike suka zamar mata garkuwa.
Idan ma akwai abinda ke damunta, to bai
wuce habaici da maganganu marasa dadi da
Mama Hauwa ke mata ba, tare kuma da nuna mata tana
cikin jin dadi, don ganin rayuwarta za ta lalace, a
dalilin auran Musaddik, amma da yake ba ta son
damuwar mahaifinta, haka ta dage tana hadiye
duk abinda Mama Hauwa ta yi mata ba tare da ta nuna damuwarta ba, don bata son mahaifinta ya dauka tana damuwa ne akan zata auri musaddik wanda ita zuwa wannan lokacin ta riga ta sa ma kanta auran musaddik bata jin wata damuwa a yanzu.

Har yau daya rage saura kwana shida daurin
auran Musaddik da Afrah, da yamma Afrah na
cikin wankin ragowar kayanta, gefe mallam
Mahmud ne zaune tun dazu, da alama wani yake
jiran zuwansa, dai-dai lokacin Musaddik ya yi
sallama ya shigo.Afrah ta yi saurin dago da kanta tana kallonsa, ko don ta dade ne ba ta gan shi ba? Sai ta ga yayi baki, ya rame duk bakinsa ya bushe kamar
wanda ya shekara bai sha ruwa ba, tausayinsa
ya Kara kamata, amma shi kallo daya ya yi mata,
ya dauke kansa ya wuce wajen Kawunsa, ya tsuguna a gabansa, da kayansa duk sun yi datti
ya gaishe shi Malam Mahmud ya dade yana Kure masa da ido cike da tausayawa, babu abinda bai saka a zuciyarsa ba, musaddik kyakkyawa me farar fata yau dubi yadda ya koma idan ba kyakkyawan sani kayi masa ba tabbas ba zaka iya gane shi ba a yanayinsa na yanzu.


Ku dakace ni

Daga taskar

Yar gidan imam ✍️
MUSABBABI

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM

Page 71

Mallam Mahmud ya numfasa yace “ina ka shiga kwana biyu,duk inda yakamata na nemeka na nemeka amma baka nan, haka kuma wayarka itama bata samuwa, lafiya kake ko?”
Musaddik Ya dan numfasa, sannan ya ce
"Kawu kasan idan zabe ya gabato bama samun zama, na dan kwana biyu ma bana garin, wayata kuma ta samu matsala sai da na gyarata

Mallam Mahmud ya girgiza kai yace
"Yanzu Musaddik don Allah ba za ka yi ma
kanka fada ka fita daga harkar nan ba, bangar
siyasa ba ta dace da kai ba, kana sane da irin
wahala da zubar da mutunci da ku ke yi akan
mutanen da su kansu ba su san darajar kansu
ba balle darajarar ku, ya kamata ace ka natsu
ka san inda duniya ta sa gaba."
Musaddik ya dan sosa keyarsa ya ce
“Sai hakuri Kawu, ayi ta mana addu'a dai har
zuwa lokacin da Allah zai kawo mana agaji, a kara hakuri da mu don Allah “ya gyada kansa
Cike da damuwar data riga ta zamar masa jiki yace “Allah ya kyauta ya kuma shiryaka”
Ya gyara tsugunnansa ya ce yana fadin
"Amin”
Malam Mahmud ya dube shi ya ce
“Kana Kirge da kwanakin da suka rage na
auranku ko ?”ya gyada kai alamar eh, sannan ya ci-gaba da magana
'"To shine dalilin nemanka, akan maganar wajen
da za ku zauna, ka na da wajen da za ku zauna
dunne ko kuwa babu ?" Musaddik ya zame ya zauna sosai a kasa ba tare da ya damu da kurar dake kasan ba, yace “ Eh kawu,nayi magana da Haj shekaranjiya, ko zata taimaka min da aron gidan da zan zauna, ko da nawa ne na da da na zauna da Hannatu

Page 72

sai ta nuna min ai ba ta da iko da gidan,
tunda na Hannatu ne, ba nata ba”
Ya dan yi shiru. Sannan ya dora da cewa
“Shine ta ce sai dai ta taimaka min da daki anan
cikin gidan namu, na kuma amince da hakan,
tunda banda sauran wani zabi, sai dai ban sani ba ko Afrah ba zata so zama tare da ita ba”
Malam Mahmud ya yi shiru na dan wani
lokaci, sannan ya dago da idonsa ya kalli Afrah
da take ta wankinta tamkar ba ta jin abinda
suke fada a hankali ya dawo da kallonsa ga Musaddik, sannan yace

"To shi kenan, Allah ya sa hakan shi ya fi
zama alheri. Allah kuma ya daidaita zaman da ita, domin nasan Afrah bata da wani jayayya akan hakan” musaddik ya kara risinawa ya na cigaba da yi ma kawunsa godiya har sai da ya dakatar da shi.
Daga nan Mallam Mahmud ya tashi ya shiga
cikin dakinsa, a nan ne Musaddik ya juya yana
kallon Afrah, ita ma ta juyo ta kalle shi, fuskarta
dauke da murmushi, cikin jin nauyinta ya dauke
idonsa a kanta.
Zuciyarsa cike da mamakin irin zuciyar
Afrah, ya kamata ace ta yi fushi da shi, a dalilin
rashin kara waiwayarta da bai yi ba, amma babu
alamar damuwar hakan ko tsanarsa akan hakan.
Dai-dai lokacin da Malam Mahmud ya fito
rike da kayan sawa. Mama Hauwa ta fito daga
daki ta tsaya ta kama kugu ta rike tana kallonsu.
Mallam Mahmud ya zauna, Sannan ya mika ma
Musaddik kayan, shaddoji ne da yadiddika masu kyau, akalla zasu kai kala bakwai yace “ Nasan babu abinda ka tanada na game da komai na hidimar bikin


Page 73

don haka ga kayan sawa nan, sannan ga
wannan”Ya mika masa Naira dubu goma yace
“Bance kaje ka kashesu a banza ba, ko kaje ka sha wani abun da su ba, na umarceka da ka aje
su ka yi amfani da su a bikin ko wata harkar ta alheri”.
Ya karba cike da godiya da yabo, ya yi ta godiya
Malam Mahmud yana fadin.
"Ka daina yi min godiya, don ban ga dalilin
yi min godiya ba, kai fa dana ne don
na yi maka wani abu, babu bukatar ka yi min
godiya."
Musaddik ya ce "Kawu karamcinka a gareni,
ya kai duk inda ya kai, godiya ba za ta isa ba. Sai
dai na ce Allah ya kara girma."Mallam Mahmud zaiyi magana kenan Mama Hauwa ta amshe.
"Ai dole ka ce godiya ba za ta isa ba, gata
mugun abu, aka ce inji wanda bai samu ba,
Yanzu wanda zai kawo kayan lefe, shi ake ba
Kayan sawa, wannan aure shine gallafiri, tunda na ke ban taba
ganin irin wannan auran gatan ba.ta juya ta kalli Afrah tace “ lalle Afrah ba zaki taba yin daraja a wajen musaddik ba, don baisan darajarki ba, balle tsadarki, daga sama kawai ya sameki”,
Malam Mahmud ya daga mata hannu, ransa a
bace yace “Na gaya miki, na Kara gaya miki, ki
fita daga cikin duk abinda ya shafi auran Afrah,
babu ruwanki, ki shiga taitayinki, na rantse idan kika kaini bango za’ayi auran nan bakya cikin gidan nan” , a hankali ta saki tsaki

Page 74

tace, a yayin da take shigewa dakinta "Kanku ake ji, ni meye nawa, iyakar mu ido” ta karasa shigewa daki harda turo kofa tana cigaba da maganganunta a hankali.
Malam Mahmud ya dawo da kallonsa ga
Musaddik, wanda fuskarsa ta nuna matukar
damuwa da maganganun da Mama Hauwa ta
fada, yace “Kada ka damu Musaddik Hauwa ce
fa haka take, ba za ta taba canjawa ba, don
haka babu dalilin da mutum zai damu da dabi'unta, kai ma ina umartarka da ka manta da duk zantukanta”, ya jinjina kai yace “ Hakane kawu, babu komai, nagode”
Daga nan Musaddik ya hada
kayansa a cikin leda, wanda zuwa lokacin Afrah
ta gama abinda take yi ta shige dakinta, ranta da hankalinta a tashe da maganganun da
Mama Hauwa tayi.
Wanda hakika ta san gaskiya ne. Duk abinda
ta fada, ba ta da wata daraja a wajen Musaddik
Ko ba'a kan rashin tsinana komai akan bikin ba,
Ko a cikin zuciyarsa, ta san ba ta da daraja,
domin daga dukkan alamu. Musaddik baya
sonta dole zai aureta, don Kawunsa, kamar yadda dole za ta aure don mahaifinta.

Malam Mahmud ya riga Musaddik fita daga
gidan, don a tunaninsa zai tsaya su tattauna da
Afrah, ita ma Afrah ta yi tunanin zai nemeta su yi
magana, musamman akan auran nasu, duk da ta
san ba wani shirye-shiryen da za su yi akan
auran amma ga mamakin Afrah, mahaifinta yana fita.

Page 75

MusaddiK ya tattara kayansa shi ma ya fice, ba
tare da ya nemeta ba, ko ya shigo dakinta sunyi magana ba.Shin wane irin aure za ta yi? Me Musaddik ya dauketa?”, wadannan tambayoyin Afrah tana matukar bukatar amsar su., amma ba
ta san inda za ta samo amsarsu ba.

Saura kwana uku daurin auran. Afrah ta nemi hutu a Islamiyyarsu, a ranar
Ya Sayyadi ya nuna matuKar damuwarsa na
rabuwa da yarinyar da zuciyarsa take muradi.
Iya yadda ya so ya boye damuwarsa a yau,
hakan ya faskara, yadda idanun Afrah suke fitar
da hawaye, haka idanunsa suka yi ta tsiyayar
hawaye shi ma masu matukar dumi da kyar ya samu ya lallashi kansa
Sannan ya ci-gaba da yi mata nasiha gami da
shawarwari a game da zaman auranta da za ta
fara da Musaddik, wanda ta ji dadin nasihohinsa,
domin tasan tabbas za su taimaketa.
Daga bisani ya ba ta wata takarda a matsayin
gudunmuwarsa. Ta karba ta yi godiya kwarai,
wanda sai da ta isa gida ta zauna, sannan ta san
abinda Ya Sayyadi Habib ya ba ta a matsayin
gudunmuwarsa, kudi ne kimanin Naira dubu
talatin . Ta kara tausaya ma Ya Sayyadi, ta kuma
kara tausaya ma kanta da wannan auran
Kaddarar daya gitto rayuwarta.
Hakika ba za ta taba mantawa da Ya Sayyadi
ba, kuma ba za ta taba daina yi masa addu' ar samun mace wacce ta fita komai ba.

Ku dakace ni

Daga taskar

Yar gidan imam
MUSABBABI

NA

HABIBA ABUBAKAR lMAM


Page 76
mace ta-gari ba, wacce ta fi ta komai. Ta dade
tana tunanin yadda za ta yi da kudin, domin dai
ba zata iya kai ma mahaifinta kudin ba, don ba
ta son ya san cewa akwai wani da namiji da take so a cikin rayuwarta
Don ba ta son ta sa masa damuwa na tunanin
ya hanata abinda take so. Ya hada ta da abinda
zuciyarta ba ta taba so ba, don haka ta adana,
Kudin ta Boyesu da kyau da tunanin bayan
bikinta za ta san abinda za ta yi da su.

Washegari daya kama sauran kwana biyu
daurin auran. Inna Halima da yayyin Afrah,
Naja' atu da Sakina da 'yan-uwan mahaifiyar
Afrah su biyu su ne za su je su yi ma Afrah danki,
amma kafin su tafi, sai da Malam Mahmud ya ja
kunnan Inna Halima akan duk abinda Hajiya
Kilishi ta yi masu, kada su biye mata, ko su
tanka Su yi abinda ya kai su kawai, su dawo,
domin ya san Hajiya Kilishi, ya san halinta. Inna
Halima ta yi masa alkawarin babu abinda zai faru, daga nan
suka dunguma tare da motar kayan zuwa gidansu Musaddik.
Amma ga mamakin Inna Halima, sai ta ga
Hajiya Kilishi ta yi masu kyakyawar tarba har da
lafiyayyen girki, wanda ya ji nama, ga lemo kala-
kala, ga sakin fuska da suka samu.
Wannan lamari ya ba Inna Halima mamaki,domin bata taba zaton haka ba, hakanan kuma ta ji bata samu nutsuwa da hakan ba. (Boys Quarters),

Page 77

Haj Kilishi ta ba Musaddik mai dauke da dakuna
biyu da bandaki, sai kicin, an yi ma Afrah
dankinta, dai dai karfinsu daki ya yi kyau matuka,
Domin ita kanta Hajiya Kilishi ta yi mamakin
irin kayan da ta ga an malala ma Afrah. Babu
makusa. Hakika Malam Mahmud ya yi matukar
kokari, wai ma ina ya sami kudin daya fitar da
Afrah kunya?
Domin dai ta san bai aje ba, bai ba wani ajiya
ba. Bayan komawarsu gida, cike da jin dadì da
farin-ciki Inna Halima ta ba Malam Mahmud
labarin irin karamcin da Hajiya Kilishi ta yi masu.
Wanda shi ma ya yi mamaki, ya kuma ji dadi
tare da addu'ar Allah ya sa har cikin zuciyarta ta
gyaru, ta kuma amshi auran Afrah da Musaddik
da zuciya daya.
Ita ko Mama Hauwa a lokacin da Naja'atu ta
gaya mata irin kyakyawar tarbar da suka samu a
gidansu Musaddik, gaba daya sai ta ji bakin-ciki
da 6acin rai ya cika zuciyarta, ko kadan ba ta so hakan ba, domin bata faran Afrah ta samu sassauci ko dadin aure ko yaya ne, tayi zaton Haj kilishi ta zabi zama da su Afrah waje daya ne ai sabida ta kuntata mata, amma kuwa yadda tasan bakin halin Haj kilishi anya dagaske take ta amince da Afrah?.ko kuwa dai wani tuggun ne.

Sai washegari wanda ya rage saura kwana
daya daurin auran, sannan Musaddik ya zo
ganin Afrah, shi da wasu abokansa guda hudu
marasa kyan gani, don da ganinsu ka san shaye-
shaye ya gama da su, banda wari ba abinda suke yi, hakan yasa
Afrah ba ta dade a wajensu ba, ta yi karyar za

Page 78

ta koma ta karasa aiki. Haka suka tafi babu wani
abin arziki Afrah na komawa gida, ta shige daki
ta kulle kofa ta shiga rusar kuka tamkar ranta
zai fita, ba ta taba ganin irin wannan auran ba,
wanda miji da mata duk ba sa dokin sa, auran da
Ko kawarta daya ba ta gayyata ba, auran da ko dan-kwali miji bai
kawo gidansu a matsayin lefen ta ba.
Anya kuwa ta yi ma kanta adalci? Na karbar
auran Musaddik? Sai dai ta Bangaran zuciyarta
daya tana kara karfafa ma kanta guiwa akan
auran don ba don farin-cikinta za ta yi ba, don
Farincikin mahaifinta* za ta yi, kuma biyayya ce
tasa ta sadaukar da farin-cikinta ga mahaifinta,
don haka tana addu'ar Allah ya ba ta ikon cinye wannan jarabawar, ta kuma sa a ranta zata jure komai har zuwa lokacin da burin mahaifinta zai cika akan musaddik, tausayin musaddik kuma zaisa ta kara jurewa da halayensa ko da bata sonsa.
Ta tashi ta goge hawayenta, ta bude kofa ta
fita, ta je ta dauro alwala ta shiga gabatar da
sallolin nafila , domin samun natsuwar zuciya da
Kuma yayewar bakin-ciki.
Dai-dai agogo ya nuna karfe daya da kwata na
dare. Afrah na kishingide kan darduma, tun
bayan da ta gama nafilolinta, barci ya kwasheta.
Malam Mahmud ya tura kofar ya shigo a
hankali, gami da sallama, ya dan jima tsaye a
kanta yana kallonta, kafin ya kira sunanta. A
gaggauce Afrah ta tashi ta zauna tana kallon mahaifinta.

Page 79

"Ki natsu Afrah, magana zan yi da ke". Ya
fada a lokacin da yake zaunawa a gefen ,
katifarta ita ma ta gyara zamanta sosai , tana kallonsa. tace “To baba”
- Malam Mahmud ya numfasa cike da
tsantsar damuwa, ya zuba mata ido, sannan ya .
fara magana”Na kwanta, amma barci ya kasa kwashe ni, iya
yadda na ke boyewa tare da danne darnuwata a
'wannan daren, na kasa, domin damuwata tafi ta
kullum kasancewar gobe ita ce ranar da zan
rabu da ke, itace ranar da za ki kafa sabuwar rayuwa a wata duniyar, da baki sababa”
Ya kara nisawa, sannan ya dora da cewa "Ina
matukar kaunarki fiye da duk yayan da na haifa
a dalilin ke ma kin fi su kaunata, na kuma fi
samun kulawa da mutuntawa daga gareki. Afrah
ina son ki sani, har ga Allah ba irin auran da na ke kwadayin ki yi kenan ba,
Kamar yadda ba mijin da na ke miki mafarkin
ki aura ba kenan, amma babu yadda za mu yi da
Kaddara da kuma abinda Allah ya hukunta a kan
mu Afrah ina son ki sa ma ranki cewa auranki da
Musaddik jihadi ne, ki kuma sa a ranki cewa kin
yi domin Allah ne, domin kuma taimakon rayuwar
dan-uwanki.sannan ibada zaki je yi gidansa”
Hawayen idanun Afrah suka balle ta shiga
zubar da hawaye, tamkar an bude famfo. Malam

Page 80

Mahmud ya muskuta, damuwarsa ta kara yawa
a hankali ya ci-gaba da magana cikin rawar
murya “Afrah na rokeki don girman Allah ki yi
hakuri da dukkan hali da dabi 'un Musaddik, na
san ba mutumin kwarai bane a yanzu, sabanin da amma muna da tabbacin
da ikon Allah halinsa na da zai dawo gare shi, ki
yi hakuri, ki yi juriya, sannan daga Karshe ina rokonki da ki yafe min Afrah ki yafe min” da sauri
Afrah cikin kuka mai karfi tace,

“Haba Baba me ya sa'ka ke neman gafarata? Babu komai, na riga na
daukar ma kaina yi maka biyayya akan duk
abinda ka ke so, na kuma yi imanin cewa Allah
zai taimakeni, na cinye wannan jarabawar.
Kuma can a allon kaddara ta , babu sunan
kowa a matsayin mijina, sai Yaya Musaddik,
saboda haka na karbi wannan kaddarar da hannu biyu”.
Malam Mahmud cikin sanyin jiki ya kara duban
Afrah, yace “Allah ya yi miki albarka. Allah ya ba ki abinda ki ke nema duniya da lahira,Allah kuma ya tabbatar da alheri a cikin rayuwarki da ta aurenki, Allah yasa wannan auran ya zama sanadiyyar dawowar musaddik hanya madaidaiciya”.
Wannan addu’o’in sa mahaifinta ke mata yana daya daga cikin abinda ke karfafa mata guiwa tare da jin tana samun nutsuwa a zuciyarta.
ta dube shi cike da kauna ta ce "Amen Baba, na gode sosai”, daganan
ya yi mata sallama, ya tashi ya tafi, jikinsa a
matukar sanyaye, yana fita ta kara rushewa da
kuka tayi ta kuka har ta ba uku lada.
Hakika dole ta sa ma kanta hakuri da
dangana, domin ba za ta taba ba mahaifinta
kunya ba, zata yi iya yinta domin cika masa burinsa, a wannan daren gaba daya ta aje dukkan burikanta a gefe.

Ku dakace ni

Daga taskar

Yar gidan imam
MUSABBABI

NA

HABIBA ABUBAKAR IMAM

Page 81

tasan babu so ko kaunar musaddik a cikin zuciyarta ,amma tayi alkawarin za ta ba shi dukkan kulawa da Kariya a gare shi, za
kuma ta yi zama na so da kauna tunda babu wanda ke da ikon ganin zuciyarta balle asan bata son sa, sannan kuma za tayi zama na
mutuntawa da Musaddik, za kuma ta dauke shi
shugabanta, kamar yadda addini musulunci
ya tanadar, don baida nutsuwa bazai bata lasisin wulakanta shi ba tare da muzanta shi ba.

Washegari kuwa Karfe biyu da rabi alkawarin
Allah ya cika akan Musaddik da Afrah, domin
Kuwa an daura auransu a kofar gidan Malam
Mahmud akan sadaki Naira dubu arba’in kacal! Wanda shi ma ba tare da sanin kowa ba shi ya biya kudin sadakin.

Bayan daura auran. Afrah ta ci kuka har ta
gaji, musamman da Inna Halima ta shigo dakin
nata, ta sa ta gaba da nasihohi da shawarwarin
yadda za ta zauna da Musaddik.
Har zuwa lokacin da za°a kai ta dakinta,
wanda abin takaici hatta motar da za'a kai ta
dakin mijin nata, da motar yayan ta Mansur aka ,
kaita Inna Halima da su Naja'atu da matar
Mansur Sai dangin mahaifiyarta su uku su ne
suka kai Afiah dakin mijinta, nan ma Hajiya Kilishi
ta yi kokarin wadata su da abinci har suka bar
gidan ba su yi kuka da komai ba. Inna Halima kuma addu’a take yi Allah yasa Haj kilishi ta dore akan wannan sabon canjin da ta samu rana tsaka.

Sun tafi sun bar Afrah ita kadai. Da kanta ta
tashi ta zazzaga dakin nata, hakika ta yaba ma
mahaifinta, domin dai dakinta ya kawatu, kamar
na kowace *yar gata, tabbas an fitar da ita kunya

Page 82

Bayan ta gama ganin ko'ina ne, ta dawo ta
zauna tana tsammanin shigowar angon nata.
Amma shiru, har zuwa lokacin da agogon
bangon ta ya buga karfe daya na dare ba
Musaddik, babu alamarsa, ta tashi cikin matukar
damuwa ta kulle kofar dakin, sannan ta wuce
bandaki, ta dauro alwala, ta kyautata niyyarta ta
shiga yin sallar nafila, zuciyarta cike da tsantsar
danuwa Afrah ba ta gushe tana sallah ba, har
sai da aka fara kiran sallar farko na asubah, dai-dai lokacin Afrah
ta ji ana bugun kofa da Karfin gaske, tamkar
za’a balle Kofar, ta mike a gigice zuwa bakin kofar tana kokarin sanin ko waye.
"Afrah ki bude kofar” muryar musaddik ta
daki dodon kunnenta, da sauri ba tare da tunanin komai ba ta bude kofar, tana
budewa, ya fado dakin a buge yake, koda Afrah
bata san warin giya ba, to tabbas Musaddik
tsami da warin giya yake, da sauri ta matsa, ya fada kan doguwar
kujera yana sambatun surutai.wanda bata gane ko kalma daya da yake fada ba.
A sanyaye ta maida kofar ta rufe, ta dawo ta
tsaya a gabansa tana kallonsa, hawaye na
malala daga idanunta, ya dago da idanunsa jajir!
wadanda ba su iya buduwa duka, ya ce
"Kin tsaya a kaina, ki matsa ki bani waje”
• Da sauri Afrah ta koma kan
daya kujerar ta zauna, tana goge hawayenta
Da kyar ta samu ta tashi ta yi sallar asubahi,
wanda kafin ta idar musaddik ya gama wanke

Page 83

Kasan dakinta da aman giya, me

Please Login or Register in order to submit comment